Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ko?

Bakinta ta kuma barewa tana tureshi daga jikinta Shikuma yana kuma matseta jikinshi,Mamakin rigima kalar tata yakey" Nika sakeni wallahi sainaje gida tunda aka kawoni garinnan bantaba zuwa gidaba wajan wata uku Amma yanzu ka hanani to idan naje gidannan bazan dawo wannan gidan ba can zanyi zamana.

Rungumeta yai yana sharemata hawaye,Kallon agogo yai tsabar rigimarta gashi harya makara wajan aiki shikam yanacikin damuwa.
"Tsaya inji yanzu me kikeso inyi?

Hadiye kukanta tayi kamin tace, Dan Allah kabarni inje wallahi nayi kewarsu da yawa inaso in gansu muyi hira dasu kaji.

" Naji Fatima kuma zanyi yanda kikeso Ammafa bisa sharadi idan na kaiki gobe to kwana uku kawai zakiyi inje in d'aukoki kin yarda?

Bata fuska tai kamin tace haba Dr.saikace zan gudu in barka? Idan kuma mutuwa nai yazakayi? Nidai gaskiya kwana biyar yanyi.

Kwallar dake fuskarta ya kwashe da hannunshi kamin ya mike yana gyaramata kwanciya"Baki da hankali yarinya kwana biyar yayi yawa indai baso kikeyi inkoma zararreba,Dan Allah kibari sai jibi kinga juma a saimu tafi tare idan nai weekend dina acan saina dawo inafatan haka yaimiki saikiyi kwana biyar din Amma asabar da lahadi zakiyishi dani sauran kwana ukun kuma saikiyishi ke kadai randa zaki dawo sainaxo na daukeki,Kadda kimin gaddama Fatima ba halinki bane zanje aiki kinga yau rikicinki yasa na makara mutane nacan suna jirana.



Ajiyar zuciya ta sauke bayan barinshi gidan kamin tasaki murmushi ta tabbata dabatayi mishi wannan borenba to ba bari zaiyiba.
Tashi tai tafara hade kayanta atsanake dukkan wani Abu datasan yanada muhummanci agareta saida ta d'aukeshi hakanan takejin kamar takusa barin gidan bari na har abada.

Bayan tagama shirya kayanta shima ta shiryamishi na kwanabiyun sannan ta d'auki abinda zata kaima mejego da kuma Sauran dangi tunda wannan shine zuwan farko bayan aurenta.




***

Inna lillahi wa inna ilaihirraji'un wayyo Allah nabani.

"Ke aysha meya faru ya akai?

Fifita nafarayi da hular data zame daga kaina sabida yanda naji wata irin zufa tana tsattsafomin" Wallahi yaya mafarki nayi Wai munkwanta gado daya da yaya Dr.inata tureshi yana likemin nashiga uku shed'anune wayyo Allah.


"Tsaki tasaki kamin tace kefa wani lokacin shirmene dake wallahi,Dama rannan naji kince kinyi mafarkin kun haihu dashi to wallahi ki dage da addua yanzu haka wani aljaninne yake nema yasami mafaka ajikinki yake yomiki siffar Wanda kika sani danhaka ki kiyaye,Tashi ki canzama Abbas wajan kwanciya ki mikama Honey abincinshi inaga yafito falo yanzu.



**

" Kin tasani kin yi shiru kinda damuwane?

Tasan halin mijinta fiye da kowa shiyasa lokuta da dama take shakkar gayamishi wata maganar dantasan hali.

"A a babu komai yaya damadai akan maganar Fatima ne danaga har yanzu batazo gidaba tunda akai aurannan to yanzukuma ga haihuwa shima naji shiru shine nace ko magana za aima mijin nata yabari tazo gida taga 'yan uwanta?

Murmushi yasaki kamin yace Wallahi yanzu kin baci da son 'ya'ya dakuma naga babu ruwanki to ki kwantar da hankalinki gobe zasuzo ita da mijin danhaka ki daina damuwa zakiga diyarki shikenan ko?


Akunyace tatashi tabashi gu datasani da batayi maganaba ,Saidai tanajin tsoron kadda ya hanata zuwane.

Da murmushi yabita yana mamakin kulafucinta akan yaranta gashi batasan zafin rashiba dan har yanzu mahaifiyarta na raye haka mahaifinta sannan yarantama babu wanda tataba rufewa,Jaridar dake hannunshi ya rufe kamin ya kishingida awajan hakanan yatashi kwanakinnan Sam bejin dadin jikinshi.




*""*

" Aysha kadda ki dizgani dan Allah kizo muje Ku gaisa kawai saiki dawo haba Amaryata.
Turo bakina gaba nai kamin ince haba yaya dalha dan Allah ni wallahi ko ganinshi bansan yi dama ba babyn yazo ganiba zaiwanifake dayin barka Allah sai in hadaka da Abba.

"Naji yi hakuri sawo hijab dinki muje daga yau bazai dawoba zance yai hakuri saikin fara aiki k'arewar karatu hakan yai miki ko?

Kaina na d'agamishi kamin na jawo hijab dina na kama hannun Abbas daketa bina tun farkon zuwana gidan.

K'aramin yatsanshi ya d'agama matarshi kamin yabi bayana yana sakin murmushi,Wani abikinshine tunda yazomai barkar baby shikenan kuma ya likemin wai sona yakeyi niko ko kadan beminba musamman da na luradashi irin mutanen ne masu shegen kallon tsiya.

Ban fahimci komaiba daga maganar da yaimin saita barkar da yakuma yimin daga karshe yaimin sallama yace ituromishi dalhat din zai wuce.


Hararar yaya dalhat din nayi lokacinda na zauna falon,Saiwani turo baki nakeyi.

" k'anwata andace kuwa?

Ni wallahi yaya sai inbarmaka gidanka idan haka zaka dingamin Abba yacefa karna kula kowa shine kace inje wajan wancan me shegen kallon tsiyar Anyama ba maye bane?


Da dariya yafice d'akin yana fadin maryam kinajin Wannan sarkin sharrin ko?



Gobe suna.

K'arfe shadaya nasafe suka iso cikin garin kano.

Sanye take dawani arnen less ruwan sararin samaniya wanda yaji wani dinkin doguwar Riga ma matukar kyau da tsari,Sai bula k'amshi takeyi jitake kamar tayi shekara cikin katsina tsabar yanda tai kewar gida.

Rikemata hannu d'aya yayi yana gyara ajiyar motar daidai kofar gidansu ganin tana nema ta bude ta gudu tunkamin ya idasa tsayawa.

Bakinta ta turogaba gamida harararshi,Amma batace komai.


Tare suka shiga gidan tanagaba yana bayanta,Tare da k'arema mazaunanta kallo kawai gani yake kamar ankuma canzata cikin kwanakinnan koda yake yasan hadda yaron cikin dake jikinta.


Ihun data sakine yasashi dawowa hayyacinshi daga Dan guntun tunanin daya tafi.

Tuni ta makalkale maman tana murna nanfa gidan ya kacame da farinciki sabida anan za ayi duk wani girke girke shiyasa gidan yake cike.
Kunyace tadan kamashi ganin yanda idanun matan tsakar gidan sukadawo kanshi gashi har jakarta tana hannunshi.

Yaya safiyya ce ta wuce falon Abban Dan yimai masaukin dayakema Abba din bawani nisa yai ba sabida hawan jininshi daya tashi kwana biyu.


"Ke ni d'agani hakanan kije kikaimishi ruwa mana kinzo kin d'afemin saikace wata baby" Cewar maman ganin yanda fatiman ta hanata motsin kirki sai kuma likemata takeyi.

Cikin shagwaba tace kai mama Dan Allah kibarni wallahi nayi kewarki da yawa d'uminki nakeso intaji Dan Allah kibarni.


Dariya mutanen d'akin keyi sabida sosai take kuma shigewa jikin maman saikace wadda zatasha nono yayinda mutane suketa yaba kyan datayi Dan kallo daya zakaimata ka fahimci tana cikin jin dadi.

Mamance tasa wayarta ta kira Abban akan Ahmad din na jiranshi bayan ankaimishi ruwa da lemo Dan anyi anyi da ita Amma taki ko motsin kirki ma.


Shigowar Abban gidan yasa sukaita hira da Ahmad din sai bayan azahar sundawo masallaci yace ka zauna muci abinci sai in kiramaka ita ta rakaka kaga babyn kamin Allah yasa ka wuce.

Akunyace yace to Abba nagode.


"Banso inji kanamin godiyarnan ko jin kunyata likita sai inga kamar baka d'aukeni mahaifi ba.

Kuma sadda kanshi k'asa yai kamin yace ayi hakuri Abba.


Tare sukaci abinci kamin akira Abban waje, Ya mike yanafadin bari inturomaka ita saiku wuce idan ka dawo saimuyi sallama gaisuwa zamuje can kurna Dan Allah karka wuce fa!!!



Idanunshi ya zubamata tuni tai wanka tasaka wata rigar material ta aysha Mara nauyi Dan hannuwan shimi ma akai mata Ammata rigar tayi kyau, Hannuwanta ya riko yana sunsunar wuyanta kamin ya Zaunar da ita saman cinyarshi yana shafar mazaunanta" Shikenan Dan kawai kinzo gida saiki mance dani ko?

Murmushi tasaki tare da sumbatar kuncinshi"To kayi hakuri wallahi nayi kewar gidane sosai Amma yaushe zaka dawo tunda kace ka fasa kwana?


Hannunshi yakeson sakawa cikin rigarta Amma babu hanya dole ya rungumeta yana Sauke numfashi,D'auko hijab dinki muje inyimata barka in wuce kinsan yanzu hanyar nan bawani kyaune da ita ba, Randa zan dawo zan kiraki saiki shirya,Amma idan muka koma keda kuma dawowa sai Allah yakaimu kinzo yawan Arba'in.



***
Da mijin suka fara cin karo shima shigowarshi gidan kenan, Kai tsaye ya wuce da Dr.din falonshi yanatamishi sannu da zuwa bayan yagama tsonakar fatiman kamar yadda yasaba.
Cikin gida ta wuce da gudunta,Saida ya rufe idanunshi sabida tunanin yau d'an tayinshi yaga ta kanshi.

Dariya dalhat din yayi kamin yace"Saikayi hakurifa duk mata haka suke kuma basucika girmaba.

Da kanshi ya wuce kiran mejegon.

Tuni kowa yanata rungumar ya fatin tare da yaba kyawun da tayi.

"My mero taho Ku gaisa da mijin Fatima zai wuce ne yanzu.

Babyn ta mik'amishi ta juya Neman hijab din da zata saka.
Tare suka shiga falon inda ya mikamishi babyn yaro tubarkalla dashi.Akunyace ya gaisheta tare dayimata barka kamin ya kalli dalhat din yana tambayar sunanshi.

" Aiko sunan Abba yasamu Abdullahi Amma zamu dinga kiranshi da abulkhairi.

"Ah lallai ka kyauta ai Abba surukine na gari Allah yasakamishi da alkhairi ya raya takwaranshi.

Kudi masu yawan gaske ya nade cikin shawul din babyn kamin ya mik'amishi yaron yanafadin banga aysha ba ko batanan gidan naga canma ban gantaba.


Mikewa tai tanamishi godiya kamin tace" Aiko tana nan gidanma tunkamin haihuwar bari inturota saiku gaisa yanzu zaka wuce Ashe?

"Eh yau zan koma insha Allah.


Shi kadai na tadda cikin d'akin" Yaya INA yini yasu mama?

"Lafiya lau aysha ya kwana biyu ke ko kirkin Neman mutane bakiyi ko?

Sadda kaina k'asa nai ina mirmushi kamin ince to ayi hakuri zan dinga kira.

Kudi yazaro masu yawa yabani waina k'ara kayan kwalliya,Naso inki karba Amma yanuna beso dole na karba kamin yace turomin yayarki zan wuce,Amma idan kika idasa jarabawa zanxo in daukeki da kaina zaman da kikayima yaya maryam muma ki rama mana.

Dariya nayi kawai nafice cikin d'akin.



Sosai yake gwadamata soyayya sabida tunanin missing dinta da zaiyi,Kuma itama tabashi hadin kai sosai,Saida yagama lalubeta Sannan yasaketa yana maida numfashi" Dan Allah kiyi hakuri idan kinyi kwana uku inzo mutafi wallahi zansha wahala.

Kanta kawai ta iya d'agamishi Itama kudin yabata wai kozata nemi wani Abu.



**

Kusan kwana mukai hira gidan kowa cike yake da farinciki Sannan mungama kammala duk wani Abu daya kasance za anema gobe wajan sunan.

Haka muka wayi gari cikin farinciki da hada hadar jama'a kundai San gidan hidima.


Dare.

Zuwa darennan munyi lis damu musamman ni danakeganin an rainani Dan kome nene saidai akirani nagaji iyakar gajiya Hutu kawai nake buk'ata gidan yakoma dagamu sai mu.
Wajan goma nadare muka gama gyara gidan naso inkwana nan Amma ya fati tace tare zamu koma gida Dan tanaso tai hira da Abba.

Yaya dalha ya maidamu gida.

Wanka kawai nayi nabi gado itako tanayin wanka ta wuce falon Abba wai hira.



** **

"Fatima bintu zahra duk ke kadai shanake zaki kwanta ki huta gobe saimuyi hira ko? Cewar Abban yana kallonta.

Murmushi tasaki tare dakuma matse hannunshi dake cikin nata,A a Abba nai kewarka da yawa kuma bamu haduba shiyasa naji ban iya barci sainayi hira dakai.

" To Alhamdulillah Allah yaimiki albarka inafatan babu matsala ko?

Sadda kanta k'asa tai kamin tace babu matsalar komai Abba yana sona sosai yana kula dani beson bacin raina Amma yanabani tausayi Abba.

"Babu komai Fatima komai lokacine kedai ki kwantar da hankalinki ki dage da addua babu abinda zai faru da izinin Allah sai Alkhairi kinji ko?

Gajiya yai da hirar tata yace tatai ta kwanta dasafe zasuyi hirar tunda babu inda zaije.

Kira goma tagani na Dr. Amma ganin shabiyu nadare ya wuce yasa dole batabi kiranba Saidai ta tsaya ta rubutamishi wani zazzafan message na soyayya da kwantar da hankali Sannan ta turamishi tayo alwala ta kwanta bayan ta yi adduarta.




MAFARI.




Haske writer's association.
12/10/20, 7:52 AM - Naffy Aliyu Umar: 🇯 🇦 🇷 🇺 🇲 🇦 .
20
Na maman khadija.




Ina zaune ina lazumi bayan idan da sallar asuba danai,Sai naji muryar mama tana kwalama Abba kira da k'arfin gaske.
Wani irin mummunan faduwan gaba tasameni kamin in mike ina nade sallayar.

Kusan tare mukashiga cikin d'akinta da abban.
Zaman dirshan yayi ak'asa inda kan yaya fati yake Dan kwance take akan darduma da alama tuni ta idar da salla nibammasan lokacinda ta dawo d'akin maman ba tunda dafarko d'akina ta kwanta.
Tarairayota cikin jikinshi yai yana salati kamin ya rumgumeta tsam yanamata addua gamida fatan alkhairi.
Cikin sautin kuka mama tace "Yaya kadda kacemin rasuwa tayi Dan Allah wallahi lafiya lau natasheta tai sallah innalillahi wa inna ilaihirraji'un.

Hannuwana na Dora akaina ina niyyar sakin ihu,Saidai tuni na maida hannuwana saman bakina na danne sabida wani irin kallo da Abba yaimin.

Sautin kukan mama ke tashi ahankali yayinda take addua gamida yimata fatan alkhairi arayuwar dazata fara yanzu.
Niko nama kasa kukan sai wata irin suya da kirjina keyi wanda na gwammace ace kukan nakeyi.

Gyara mata rufa yai kamin ya shimfideta yana kallonta fuskarnan fes saikace me murmushi besan lokacinda murmushin ya kwace mishi afili ya furta Allah ya sadaki da wannan farinciki Fatima.

Tsabar gizon da idona kemin sainaga kamar motsawa takeyi Dan haka azabure na furta Abba ta motsa wallahi Dama nasan ba mutuwa tai ba.

Shi kanshi saiyai azamar komawa ya zauna yana kuma dubawa Dan zaiso ace doguwar suma tayi shima tunda yafara haihuwa matarshi bata tabayin ko barin ciki ba balle me wayau ya rasu saifa yau dinnan Dan haka yanajin tashin hankalin da be isa ace ya misaltashiba saidai me shi musulmine kuma Wanda ya yarda da k'addara me kyau ko akasinta Dan haka bazai bari shedan ya ribaceshiba yasan gizone kawai amma Fatima bata motsaba.

"Ki nutsu jaruma Fatima ta rasu bakuma zata kuma dawowa ba saidai muyimata fatan dacewa kinji ko?
Daga durkushen da nake saidai naji wani duhu ya mamaye ganina daganan bankuma sanin me akai ba.


Beyi tunanin yayyafamin ruwaba balle in farfado saima maidani saman gado da yayi, Mikar da maman tsaye yai ya hadata da jikinshi ya rungume" Bazan hanaki kukaba Amma inaso in tunamiki cewa kisan kalar Wanda zakiyi mata Dan bashi take buk'ataba yanzu kadda kiyi kukan da zai zamemata azaba Dan Allah.



Kamin garin Allah ya waye duk Wanda ya kamata yaji mutuwar yajita kamin kace me gidan ya cika makil da jama'a haka waje, Allah kenan jiya ancika anyi taron samun k'aruwa anata murna da farin ciki yaukuma gashi an taru Amma kowa kuka yake.


"*"*"

Bayan sun gaisa "To Dama alhaji zan gayamakane Allah yayima Fatima rasuwa bayan asuba sabida haka za ai jana'izarta da misalin goma nasafe sabida kusami isowa Dan Allah asan yanda za agayama ahmadun Sabida kadda yashiga wani hali,Cewar Abban dake gayama mahaifin Dr.din.

Lokaci guda suma suka rude abin yazomusu amatukar bazata babu Wanda yazaci abun nan kusa kusa sannan masuyimishi kyakkyawan zatoma sunata mishi fatan matsalar ta wuce.
Wannan karan kasa daurewa sukayi saida suka zubar da hawaye sabida tausayin tilon d'ansu namiji wai Wannan wace kalar qaddarace wadda batajin addua ne?

Tunanin yanda zasu gayama Ahmad din yakuma tashin hankalinsu amma ganin lokaci nakuma kurewa dole yafara kiran waya sabida asamu ahalarci rakon gawar.
Allah kenan yanzu kake da mutun yanzu yazama gawa,Allah kasa mucika da kyau da imani ka yafemana zunuban da mukeyi dare da rana.


Biye yake dasu kamar bindi amma kallo daya zakaimishi kasan yafice cikin hayyacinshi Dan tunda yaga yanayin mahaifanshi da nasihohin da abokanan mahaifinshi kemishi yasan wani mugun Abu ya afku balle dayaga sunkamo hanyar kano.

Lokacinda da suka iso tuni har an kammala shiryata,Ina zaune gaban gawar danni banwani cika jin tsoron wasu abubuwaba haka sai sauran yayuna dake gefe ko wacce ta kunshe tana sakin shsssheka ashe dama haka mutuwa takeda zafi da radadi alokacinda akaimaka ita?
Lallai me rai yana cikin gararin rayuwa haka zamu kasance tun muna kukan rabuwa da wasu har muma azo kanyin namu innalilillahi wa inna ilairraji'un.


Jikinshi babu inda be rawa sabida kukan daya taso mishi bayanshi daga Abba saikuma mahaifinshi"Haba Fatima Dan Allah karkimin haka kefa kikacemin kome yazo k'arshe kince bazan kuma kukaba damme zakimin haka yanzu ki rufamin asiri Fatima gara ni in mutu ke ki zauna Dan Allah kitashi wayyo Allah ka d'auki rayuwata nima Allah idan laifi naimaka ka jarabceni da Wannan k'addarar Allah na tuba ka yafemin ka tasarmin Fatima Allah ka yafemin ka tasarmin ita ta haifi abinda ke cikinta ya Allah.
Kifuwa yai saman gawar yana hawaye sosai yakeji aranshi inama shine nan kwance ba itaba.

Lokaci guda yai dif jikinshi yasaki, Nanfa hankula suka kuma tashi nidai ina gefe ina share hawayena yaban tausayi amma ba sosai ba.

Dole saida akabari yadawo hayyacinshi sannan aka mik'ata gidanta na gaskiya abun kamar almara jiya iwar haka da ita ake shagalin suna yaukuwa gata nade cikin kabari.


Bayan kwana biyu.

Gidan har yanzu kullun cike yake Dan 'yan katsinan ma basu komaba Abba yace sujira ayi adduar uku Dan ita kawai za ayi kowa ya watse,To shiyasa gidan yake cike Dan kullun akwai motocin dake zuwa daga katsinan walau dangin Ahmad din ko abokai kokuma na mahaifinshi.

Irin figewar da Dr.din yayi dole ka tausaya mishi babu mutuwar data bigeshi irin Wannan Dan yariga yasaran yin doguwar rayuwa da ita yai tunanin k'addararshi ta k'are Ashe akwai saura,Yakoma saikace yaro Dan ko ruwa idan ba a matsamishi yashaba to kuwa bazai shaba balle ai maganar abinci,Tun kayan dayazo dasune ajikinshi duk da cewa ankawomai wasu Amma yaki canzawa duk salla saiyayi kuka kamin yagama Dan yana tunanin daidai lokacinne Allah zai tausayamishi ya yayemishi wannan masifar Dan Wannan abun yariga yazama masifa irin wacce kowa yake gudu.

Mama tayi matukar kokari da juriya Dan tuni tai tawakkali sai addua dataketa jerama diyar tata,To muma ganin irin yanda ta dake shiyasa duk muka kara karfafama kammu guiwa daidai kuka kam saidai ahankali,Tuni kewarta tagama baibayemu.



"Wai kai Ahmad dama haka kake baka da dauriya? Da abinda zaka sakawa matarka dashi kenan kuka Ahmad? Cewar Abba ganin yanda Dr.din ya kode ya fice hayyacinshi idanun nan jajir sabida yanzu aka gama sallar la'asar.

" Abba inason Fatima na shirya rayuwa da ita kullun gayamin take bazan kuma kukaba Ashe wasa takemin yanzuma zan fara!!! Abba nagaji wallahi Dan Allah Ku kasheni nima in huta kirjina zafi yakeyi.

Janshi yai jikinshi ya rungume yanajin yanda kukan Dr.din kekuma karyarmishi da zuciya Allah har yanzu yana cikin d'acin mutuwar.

Mahaifin Dr.dinne ya kauda kanshi tare da share hawayenshi yaronnashi nacikin wani hali gashi tun shekaranjiya daya suma aka tabbatar da cewa jininshi ya hau Amma yakasa daurewa balle asami cigaba akan lafiyarshi wata irin tsotsewa yakeyi atsaye saikace zakaran mayya.



Washe gari.

Sosai 'yan katsina sukazo musu kara sabida yin adduar bayan Sallar juma'a cikin babban masallaci.

Haka abokan Dr.din suma sunzo sosai da wa inda basu samu sun zo wajan gaisuwarba.


Sosai tasami adduar mutane masu dumbin yawa Sannan akai sanarwar d'aurin aure.

Babu wanda yasan abinda yake shiryawa sai sirikinshi Wanda yake amatsayin mahaifinshi Dan shine abokin sharawarshi.

Sadaki ya fiddo daga aljihunshi ya mik'ama yayan matarshi Wanda yake k'ani wajanshi mesuna habibu yace To habibu Ga sadakin aysha daga d'ana Ahmad muna buk'atar a d'aura auren yanzu idan kun amince.


Wani irin tsitt ciki da wajen masallacin yayi domin hatta Dr.da kanshi ke k'asa yana hawaye saida ya dago kuma yana kallon Abban.

Kawu habibu da mamaki da tsoron Allah ya daskarar dashi yakasa wani motsin kirki Dan sosai yaji abun azata.
Amsar sadakin yai nan da nan aka d'aura auran Ahmad da kuma aysha akan sadaki naira dubu hamsin kacal.

Nanfa guri ya kacame da addua gamida fatan alkhairi Dan sosai Abban ya birge mutune musamman wa inda sukasan qaddaran Dr.din.
Yayinda mamaki ya kashe Dr.da mahaifinshi Dan basu taba ko tunanin faruwar hakanba.



Saidai masallacin ya koma babu kowa Amma Dr.yakasa ko motsin kirki Dan har lokacin jinin jikinshi becigaba da aikin daya daceba.


Suko sauran tuni sunacan suna sallamar mutane.


**""**

Tsaye ta mike tana dafe kirji yayinda jikinta keta kyarma Sam tunaninta basu jiyemata daidaiba.

"Kai awwal me kekecewa ne? Cewar yaya safiyya.

" Wallahi da gaske yanzu aka gama daura auren aunty aysha da Dr.mijin auntyfati.

Duk matan dake d'akin saida suka mike sabida tsabar kaduwa da razana ciki hadda maman Dr. Din.

Kamin asami Wanda zai motsa cikin d'akin tuni maman ta yanke jiki ta fadi shikenan itama ayshan rasata zatayi.






Haske writer's association.
12/10/20, 7:52 AM - Naffy Aliyu Umar: 🇯 🇦 🇷 🇺 🇲 🇦 .
Na
Maman khadija.

21.




Nan fa mata aka rude kamin kace me hankalin kowa yatashi masu salati nayi masu kuka nayi.

Ina zaune dagacan can gefe na kife kaina cikin cinyoyina wani irin zazzabi naji ya sakkomin abazata Amma Sam babu hawaye cikin idanuna.

Bamusan Wanda yafita yakira Abba ba Saigashi yashigo ya shigo cikin gidan fuskarshi awashe saikace beyi wani abun da zai tashi hankulan mutaneba.



Please Login or Register in order to submit comment