Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

gida.




Itama kamar saura haka ta taremu da murna sosai yaranta biyar maza uku mata biyu duk ma sunfara tasawa gakuma ta wajan hajiya halima shidda kenan.

Nan ma hirar muka shantake saidai anan hirar tamu tafi yawane akan dangin mahaifinsu da yanayin halayensu.
Itamadai kayan k'amshi tabamu Sannan mukaimata sallama d'ayar wadda Dr.ke bimawa abuja take aure,Shiyasa sai mukai kwana gidan maman muna tafe muna hira da usman sabida na lura akwaishi da barkwanci Iyayen Dr.dinne ke rikedashi tun bekai hakaba.



Sannu taimana kamin ta diremana abincin darensu kamar kullun tuwo ashe wai abban ne keson tuwo shiyasa kullun sai anyishi agidan saidai idan bako akayi aimishi wani idan bazaici tuwonba kokuma idan an rage na rana domin da rana akanyi kala kala ammafa na dare tuwon nan ne dole.


Saida mukai sallar magriba Sannan muka wuce gida tana kuma jadda da mana cewa karmu kuma fitowa sai ankwana biyu sai muzo mushiga danginta.



Falo mukadawo mukai zamanmu bayan munyi wanka da sallar isha'i.
Hira mukeyi duk akan karamcin 'yan uwan Dr.din kamin wayar ya fati tafara Ring.

"OK to ganinan sannu da zuwa.

Abinda tace kenan tatashi tabarni baki sake inagani taje ta d'auko hijab dinta Sannan ta wuce,Ban motsaba saigata ta dawo da wannan mayen abayanta wato Hafiz ashe shine yazo.

Wani haushi ya kumeni ganin yanda yake kallona Amma nafijin haushin ya fatin tunda tasan bako akai amma tashigo dashi batare da ta bari na shiryaba.

Ban kalleshiba nace ina yini.

Shima kauda kanshi yai ga barin kallona kamin yace" ya kk?

Harararshi nai tare da mikewa na kwashe kofunan da mukasha tea dasu na nufi kitchen,Har Neman faduwa nayi sabida yanda idanunshi suka addabi jikina.

Bayanshi ya jinginar kamin ya sauke wani numfashi daya jima yana rikewa sama sama yake amsama ya fatin maganar da sukeyi.

Saida na d'auraye kofunan Sannan nazo na wuce d'aki.

Da kallo ya bini kamin yace"oh aunty ita wannan k'anwar taki halan fadane da ita ko? Kinga hararar da takemin kuwa?

Dariya tasaki kamin tace gaskiya kam ba laifi tanada fada musamman yau daka ganta ahaka kila akan hakan take harararka,Amma data saba da mutun shikenan kuma.

Ledar daya shigo da ita ya ajiye gabanta kamin yace"Aunty muje ku rufe gidan dare yafara.

Godiya taimishi kamin tabi bayanshi sukai sallama.



"Wai ya fati sabida Allah kinsan shigowa zaiyi amma bakimin baganaba ko hijab insa ji yanda yakebina dawasu mayun idanunshi saikace tsohon maye.

Dariya tayi kamin tace to sarkin mita dan Allah kiyi hakuri zan kiyaye lokaci na gaba.


Yauma kamar jiya barinsu nai suna hirarsu nikuwa nai barcina dan bani da wata damuwa adai dai wannan lokacin.



Bayan kwana biyar.

Yau satina d'aya cikin garin katsina nasha yawo haka sosai dan tuni nasaki jiki da usman yanata zagayawa dani.
Hafiz kullun saiyazo gidan da dare dan wani lokacin ma nan yakecin abincin darenshi saidai tunda naga take takenshi na tattarashi na watsar hasalima ko zama falon banyi damma kadda in kalleshi daya shigo zan shige d'aki saikuma yatafi Sannan in fito duk da ya fati taimin fada tunda tasan danni yake zuwa Amma na basar dashi ni na tsani namiji miskili shiyasa ko Dr.din bewani yiminba danshima shegen jin Kaine dashi.

Tun safe mukatashi da gyare gyare sabida yau Dr. Zai dawo dan besami halin dawowa ba dayai kwana hudun dole sai yau yagamo abinda zaiyi.
Da kaina naimata kwalliya tunda mukaji ya sauka sosai ko INA ya d'auki k'amshi da sanyin dadi,Niko sai nishadi nakeyi sabida nifa inason irin wannan yanayin.

Nima kwalliya nayi kadan Sannan nafito wajanta dan tana zaune falo Sam takasa zama ciki tsabar zumudin son ganinshi.

Hafiz ya daukoshi Sam ban zataba sai gasu sun shigo yana rike da 'yar jakarshi.
Tuni nasaki baki da hanci wajan kallon tsantsar rashin kunya,Ya fati manne da Dr.sai bata wani zazzafan kiss yakeyi aduk inda yasamu wai oyoyo.

Hannuna nasa na rufe idanuna kamin in shige d'aki oh ni aiko yau bazan kwana gidan nan ba gara inbi Hafiz din zuwa gidansu da inzauna nan kunya ta kasheni.

Dariya yasaki bayan barina falon Zama yai shima yana kauda kanshi ga barin kallon uncle din nashi ah lallai anyi missing din juna.

Wata dariyar yasaki ganin nafito da hijab ahannu,Tuni su Dr.anshige d'aki.

Turo bakina nayi kamin ince katashi mutafi mana.

Kallon mamaki yaimin Amma tsabar miskilanci yakasa magana saidai ya mike ya fice nikuma nabishi abaya.

Farinciki yakejin zuciyarshi nashiga amma afuskarshi bazaka taba cewa hakaba sabida yanda fuskar take ahade.
Shiga motar yai ya tada Sannan na zauna gefenshi nima tawa fuskar ahade jinake kamar insaka ihu wlh.

Be tambayi ina zai kainiba nikuma banyi maganaba saida yagama shawagi dani Sannan ya kaini gidansu.




** **
Saida tai danasanin likemishi da tai dan sosai ya gurjeta son ranshi saida tafaramishi kukan shagwaba Sannan ya kyaleta bayan tai ligi ligi da ita.

Sai bayan la'asar sanan suka fito falo sai lokacin tafara nemaba nanfa hankalinta yatashi.
Shine ya kira Hafiz yana tambayarshi saiyace ai munwuto gidansu tare.

Turo bakina gaba nai sabida yana zaune falon lokacin,Dariya hajiyan tasaki kamin tace Aysha ya kike bata raine?

"Waifa kinji saima yanzu ta tuna dani,Saidafa nace tabarni in wuce yau Amma taki wai sai gobe kuma ji daga dawowarshi harta manta dani bazan kuma dawowa nan garin ba.

Azahiri saikace wayarshi yake latsa Amma a badini hankalin shi yana kan duk wani motsina,Lallai yarinyar nan itama ta iya rikici kenan.


Babu kalar kiran da bayaiminba Amma nace Sam bazan dawoba sai gobe shiyasa sukuma 'yan gidan sukaji dadi dan nan mukasha hirarmu na manta da wata ya fati yo itama ai mantawa dani tai.





Haske writer's association.
12/10/20, 7:50 AM - Naffy Aliyu Umar: 🇯 🇦 🇷 🇺 🇲 🇦.
14
Na maman khadija.




K'arfe goma nasafe na dira kofar gidan ya fatin dan so nakeyi in wuce da wuri,Su hasana da usaina suka rakoni saidai basu shigaba sabida saurin da sukeyi zasu makara islamiyya sabida yau lahadi.
Duk da cewa ummansu taso in zauna in jira wai Hafiz ya tashi saiya kawoni amma sai yagama ramuwar barci,Saikace wani Wanda yai doguwar nakuda nikam INA zan iya jiran wani k'ato.

Da sallama nashiga gidan dan abude yake Sannan na wuce falo.
Tsaye nai tsakiyar falon naita kwada sallama to bansan cikin wane d'aki sukeba kadda saina afka inyi mugun gani.

Dagashi sai jallabiya ya fito fuskarnan fes da ita harwani sheki yakeyi.
"Ah aysha kin dawo? Sannu da zuwa ki shigomana kika tsaya bakin kofa!

Akaikaice na kalleshi kamin ince ina kwana,Ya fatin fa?

Da hannunshi ya nunamin d'akinta shikuma ya nufi kitchen.

Zama nai bakin gado ina jiran ta fito dan naji motsin ruwa.

Ahankali ta fito tana wani ciccije baki kamar wani Abu namata ciwo.
Manyan idanuna na zubemata daga sama har k'asa kamin in saurin tashi na isa wajanta ganin hatta idanunta sunyi ja alamun tai kuka,Yaya lafiya kike kuwa meya faru?

Zama tai bakin gadon kamin tace lafiya lau nake shine jiya naita kiranki Amma kika ki dawowa ko?

" Kiyi hakuri nabaku lokacine dan naga kuna buk'atar hakan gashi kuma yanzu zantafi amma kamar baki da lafiya ko?

"Ni lafiyata lau,Ammadai babu matsala ko?

" Nacemiki babu komai ammadai ni gaskiya na shirya da wuri nakeso intafi.

A hankali ta nufi wajan kayanta tana yamutsa fuska"Dan Allah kiyi hakuri har zuwa anjima Hafiz zai kaiki inji Dr.to kinga zaki jirashi kenan tunda ance weekend be tashi da wuri.

Duk da inajin tausayinta Amma kuma haushinta yafi yawa dan nasan wannan yamutse yamutsen da takeyi be wuce tsayawa tai ya gama kwalkwaletaba tunda gashinan ko tafiyar kirki bata iyawa.

Shigowa cikin d'akin yayi da kofin tea ahannunshi da magani.

"Fatima lafiya naganku tsaye meya faru?

Saida ta zauna Sannan tace wai tafiya zatayi!!

" A a aysha kibari har Hafiz yazo dan Allah shine zai kaiki har gida Abba zaiyi farinciki dan ranar dana nemi alfarmar zuwanki magana ta farko dayafarayi shine beso kiyi tafiya ke kadai shiyasa na tura yayan abokina ya taho dake tunda shi direbane sana'arshi kenan katsina to kano,Yanzu bazai yiwu kitai ke kadai ba kinji ko? Karkiyi rigimar nan Dan Allah kinji?

Hararsu nayi tare da barin d'akin ganin ya rungumeta yana bata tea din ko kunya ta beji.



"Fatima aysha tasaba da harara idanunta har sun saba da yanda take juya abinta.

Murmushi tayi kamin tace uhumm haka dai take ai munyi arziki kaga k'anyawace Amma bancika yadda rikici ya hadmuba sabida bata da hakuri wani lokacin Ammafa tanada dadin zaka idan ka fahimceta,Ture kofin tea din tayi tana yamutsa fuska Dr.na koshi dan Allah kabarni hakanan.

" a a fati na shanyeshi zakiyi Allah saikisha magani,Ya idasa maganar yana matsar hannunta cikin nashi tausayinta yakeji yasan ya bata wahala tun dwowarshi domin har saida tasakamishi kuka alamar ya kure hakurinta Sannan ya daure ya barta.




****


Da fitarsu zuwa dawowarsu duk bansan anyiba,Wai sunfita siyomin tsaraba.


"Aysha tashi ki shirya har anyi azahar.

Da sauri natashi ina zare ido tsabar yanda
Mamaki ya kasheni ashe barci nasha sosai,Da gudu na nufi bayi yin wanka da alwala, Anatse nai shirina bayan nagama salla wata doguwar Riga nasaka ta kanti cikin lefen ya fati na d'auketa dangaskiya rigar rigace ta hadu.


Cikin shirina na fito tsaf dani sai tashin k'amshi nakeyi saidai na boye kwalliyar tawa cikin k'aton hijab dina Amma bansaba fuskata nikaf ba.

" Subhanillahi Abinda Dr.ya furta kenan cikin zuciyarshi kai itamafa yarinyar nan ta hadu gata kala,istigfari yayi tare da d'auke idanunshi.

Tsabar hankalinshi yai nisa Sam beji me uncle din nashi ke cewaba.

"Kai anshi kayan nace,Cewar dr. Din yana hararar Hafiz din ganin yanda ya maida hankalinshi kacokan akaina.


Rungumeta nai ina murmushi Amma ita tuni idanunta sunciko da kwalla,Dr.dinne ya rikota jikinshi kawai saita saki kuka tana fadin Dr. Zan bita nima gida zanje.


Da dariya yake lallashinta yayinda muma mukafita muna dariyar, Saidai ina zaman cikin motar nima nasaki nawa kukan da naketa rikewa dan kadda hankalinta yatashi.

Idanunshi ya zube kaina batare daya tankaba aranshi yake tunanin to dariyar da nakeyi duk dan kadda yayata taga kukanne kenan,Murmushi ya saki bayan barinmu cikin layin ita har kukama kyau yake mata.


Hawayena na share tare da harararshi ganin be lallasheni ina kuka,Ni narasa wane kalar mutunne haka.


Idona na maida kan wayata da kira ke shigowa.
Dan in bata ran Hafiz din na d'auki wayar danta malam ce mesona.

Ajiyar zuciya ya sauke dagacan bangarenshi kamin yace" Nayi kewarki sarauniyar mata dan Allah ki dawo hakanan.

Cikin sanyin murya na furta,Karka wani damu malam ina hanyar dawowa yau insha Allah kumama kasan me?

Cikin zumudi ya furta a a gimbiya.

Asace na kalli fuskar oga Hafiz tuni ta canza sabida jin haushi,Kuma kashe murya nayi kamin ince Anjima da yamma ka zo ka amshi tsarabarka kokuma itaho maka da ita makaranta kasan kai kadai nayoma tsaraba fa.


Dariyar farinciki yasaki kamin yace"Allah gimbiyata to godiya nake Insha Allah zaki ganni nagode sosai Allah ya tsare yasa ki sauka lafiya.

Amin na amsa kamin in jira ya kashe wayar kawai saina saki dariya tare da cewa I love you too. Na ajiye wayar ina sakin murmushi.

Bansan cewa Hafiz ya cikaba saida na kalli fuskar shi sainaga har wata ja take tsabar masifa nidai wlh saima naji tsoro lokacin, Huci kawai yake fitarwa ta bakinshi yana bugun sitiyarin akai akai.





Haske writer's association.
12/10/20, 7:50 AM - Naffy Aliyu Umar: 🇯 🇦 🇷 🇺 🇲 🇦 .
15
Na maman khadija.



Ta gefen idona nake kallon yanda yake fitar da numfashi tsawon lokaci kamin yafara sauka daga fishin da ya hau din.

Ni mamaki yakeban tun kwana biyu da zuwanmu gidansu na fahimci sona yakeyi Amma wai tsabar iskanci yakasa gayamin ni bansan namiji nada wannan jin kan ba.
Amma kuma kusan yanayinsu daya da Dr.ai Amma shi aigashinan yana lallaba matarshi.

Lamo nai cikin kujera yayinda tunanin 'yar uwata ya bijiromin, Nasan nabarta cikin damuwa tunda kuka takeyima,Saidai ina adduar Allah yasa kadda wani Abu ya sameta Dan tabbas akwai damuwa zan iya tsanar Dr.fiye da duk yanda zan fadi.


Saida muka shigo garin kano Sannan na gyara zamana ina kallon inda yakebi,Nai mamakin yanda naga yanabin santarmu kamar wanda yasan waje,Saida natuna da kila haddashi wajan 'yan d'aurin aure Sannan na daina mamaki.


Da guduna na shige cikin gida dan wallahi nayi kewarsu ni bantaba zuwa wani waje nai sati dayaba shiyasa yanzuma nake ganin kamar shekara nayi.

Girgiza kanshi yayi bayan na bulle cikin gidan kamin ya fito ya biyoni da jakar kayana.

Abbanmu na makalkale wanda yagama d'aura alwalar la'asar yana tsaye yana d'aura agogonshi,Dariya yasaki yana rikoni jikinshi"Oyoyo Uwar muminai barka da sauka JARUMA.

Oyoyo Abbana nayi kewarka ina yini?

Shigowar Hafiz cikin gidan yasa Abba yakiceni jikinshi yana fadin wuce ciki,Hafizu Kaine tafe Sannu da zuwa.

Saida ya duk'a har kasa Sannan ya gaishe da abban nidai lokacin nai nisa falon mamarmu.

K'annena guda biyu suna like dani duk sunyi shirin islamiyya umar da abdullahi shine auta amma ni kaina sukan kirani da autar tunda dagani mama batakuma haihuwar mace ba.

Tare da Abban suka wuce masallaci niko ina watsa ruwa nabi gado Dan marata ke ciwo.


Sai wajan biyar na yamma Sannan yace zai wuce,Abba ne yatasoni wai inzo muyi sallama idanuna sun canza sabida barci gashi inajin nagaji ajikina.

Daga bakin kofa na tsaya,Ka gaida gida Allah ya tsare na gode.


Da kallon mamaki yabini kamin yasaki murmushi,Yana hango kaurina ta k'asan dogon hijab din dana zumbula.

"Kibani wayarki zanyi turin wannan karatun danaji kinaji.

Saida na harareshi Sannan nakoma na d'aukomishi na ajemishi gefenshi nakoma can bakin k'ofa ina jira yagama yabani inkama gabana,Bansan abunda yai da wayarba,Sannan ya mikomin yana fadin gashi ni na wuce Sai gani na biyu kuma"

Yamutsa fuska nayi kamin ince ni dai Dan Allah basaika dawoba kai zamanka garinku ka gaidamin dasu hasana.


Murmushi kawai yayi tare girgiza kai,Wani irin jin dadi da nishadi yakeji musamman idan ya kalli idanunta Amma miskilanci ya hana ya nuna ko a fuska.




***

Cikin yanayin shagwaba take kallonshi Amma saiya kauda fuska danma kadda yakasa abinda yai niyya,Besan meyasaba tun bayan barin aysha garin takoma bata da walwala balle kuzari yarasa gane menene damuwar to yau cewa yai ta shirya zasuje gida tayo wanka Amma kuma takasa shiryawa wai kasala takeji.

" Dan Allah Dr.kabarni wallahi zazzabi nakeji.

Cikinta yashafo kamin yasaki murmushi "To Fatima kodai mun sami baby ne damafa naji alamu cikin jikinki gakuma rikici hadda na gangan kamar aysha tabar miki nata kamin ta wuce ko?

Shigewa tai jikinshi tana dariya kai Dr.wane irin ciki ana zaune qalau kofa wata daya bamu idasaba,Kumama nidai gaskiya ba yanzuba.


Shima dariyar yake kamin yace to ai zaki iya samu ko satinmu biyu,Musamman idan kikai la'akari da irin namijin k'okarin danakeyi wajan har kannan ko?

Harararshi tayi tare da barin wajanshi dole ta shirya dantasan bawai barinta hutu zaiyiba tunda yau asabar.yar

***

"Aysha wannan yaro Hafiz ya turo k'anin babanshi akan bashi izinin fara Neman aurenki saidai na dakatar dashi sabida wani dalili nawa Sannan banso kifara soyayya da wani harsai lokacin da na amincemiki da hakan inafata zaki bani hadin kai?

Banwani damuba nace karka damu Abba insha Allah babu matsala ni hakama nafiso bakace karatu zanyiba?

Shafar kaina yayi yana murmushi" Karki damu duk abinda kikeso shizan yi miki nidai fatana Allah ya sanyawa karatun albarka.


Tsam natashi nabar falon ina mamakin halin Hafiz kenan sona din yake Amma girman kai ya hanashi yaimin magana saidai ya zagaye wajan Abba sabida abban zai aura,Hummm Allah ma ya k'ara wallahi ni inama zankai mutun me hali irin wannan ai inaga Sai mun kone gidan wataran.

Ina kwance saman darduma nagama littattafaina na boko naji wayata na ringing banza nai da ita Sai karo na uku Sannan na d'auka sallama kawai nayi nakoma nai shiru ina jiran inji wake magana.

Ina niyyar ajewa jin shirun yai yawa sai naji yafara magana"Sunana Hafiz Attahir daga katsina.

Gatsine naima wayar kamin ince sannunka ina yini ,Ya aiki?

"Komai qalau tunda nakawoki bansamu lokacin kainaba,Inataso in kira.

" Karka damu ai babu matsala nagode sosai inasu aunty,Mahaifiyarshi tunda naga haka yaya fati take cewa.

"Duk lafiya dama cewa nai bari na kiraki mu gaisa tunda ke kam baki Neman mutane.

Dan murmushi nayi kamin ince to ayi hakuri dayake munata jarabawa to lokutan namune babu yawa nagode.


Ajiye wayar nayi bayan ya kashe, Ina mamakin k'arfin hali irin nashi.




**"""**


Atsaye batasan da abinda zata kwatanta girmanshiba Shiyasa wani irin tsoro ya dabaibayeta,Saidai tagaza motsawa balle ta gujemishi mummunane na kin kallo sauran kadan ya fita daga jinsin mutane sabida tsabar yanda kamarshi ta munana,K'aton bakinshi da yake kamar na jaki yafara k'okarin kawowa kusa da nata da alama so yake yai kissing dinta,Tunanin mutuwa tafara idan hakan ya kasance,Ga wurin babu kowa balle tasaran wani zai temaketa.
Jin sautin kuka yasata Dan juya kanta kadan saita hangi Dr.zaune da kayanshi duk sunyi d'auda yana kuka yana murzar hannunshi Amma yakasa motsawa daga inda yake balle ya temaketa.

Jikinta yafara saki alamun jigata zata iya mutuwa kowane lokaci Saikawai taga gilmawar aysha k'anwarta fuskar nan Sam babu walwala sabida bacin rai.






Haske writers association.
12/10/20, 7:50 AM - Naffy Aliyu Umar: 🇯 🇦 🇷 🇺 🇲 🇦 .
16
Na maman khadija.




Adduan da taji ayshan tafara yasa itama tafara tun tanayi cikin zuciyarta har sautinta yafara fitowa kamin shirgegen mutumin yasaki wuyanta ya juyamata baya.


Da sauri yake jijjigarta tare da kiran sunanta har saida yaga ta bude idanunta saidai tsabar gigita da tayi yasa Sam bata gane Dr.dinne gabanta ba.
"Fatima Fatima bude idanunki kalleni nan nine anshi nan meya meya faru Fatima ke Fatima"
Shigewa tai jikinshi tana sauke numfashi da ajiyar zuciya innaliahi wa inna alaihirraji'un yake nanatawa cikin ranshi tare da yimata addua sosai yakejin wani irin tashin hankali yana dabaibaiyeshi.

Saida yaji ta daina rawar jikin Sannan ya jawo robar ruwan dake gefen gadon dama kullun yakan ajeta sabida tsaran lalura,Sai da tasha sosai Sannan ya ajiye tare da matseta jikinshi jiyake zuciyarshi kamar zatayo tsalle waje sabida tashin hankali,Har lokacin be daina tofeta da addua ba.

Rigarta yasaka mata shikuma ya maida gajeran wandonshi Dan dama irin barcinnan ne me dadi na bayan amsamu gamsuwane yai gaba dasu🥴.

Saida sukai wanka gamida d'auro alwala sannan suka fito har lokacin be tambayeta meta gani ba,Kome ya tsoratata.



** **

Yaya cewa nai me zaihana muje wajan wannan malamin mu nemama Ahmad magani kaga mu abinda ya kaimu daban Amma ga abinda ke faruwa dashi ban Wannan zalumcine kuma natabbata wanine yaima Ahmad din wannan abun.
"Hamisu ni kaina ina cikin damuwa wallahi sabida shahida ta nace Ahmad takeso to nikuma wallahi bazan iya bawa Ahmad aureba tunda matanshi mutuwa suke bansan yanda zanyiba.


" Yaya ta inda aka hau tanan ake Sauka gaskiya idan akwai wanda yai wannan abun cikinmu gara kawai ya warwareshi haba ai abun yai yawa.


"Kai kamal bansan haukan banza kana tunanin cikinmu akwai wanda zai iya kulla wannan mugun abun?

" To yaya ai komai mutun zai iya kumama tunda ba son yayan kukeyiba ai babu abinda bazai faru ba.

Sassauta murya yai kamin yace Amma kai kamalu idan kace haka bakaimana adalciba wallahi kumafa abinnan da shawara mukeyinshi domme yanzu zaka kawo maganar nan? To wallahi nidai babu ruwana banje wajan wani da niyyar yasa matan Ahmad suyita mutuwaba gaskiya.



Please Login or Register in order to submit comment