Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Saida ya tabbatar da barcin ya fice idona kamin yace muje kiyo fitsari.

Taku biyu nai nakoma na lankwashe jikinshi ina dafe cikina.

"Subhanallah baby meya faru? Cikinki ne ke ciwo?

Kamun mu k'arasa toilet ciwo yafara fitar dani hayyacina muna shiga jini nafara biyomin k'afafu yana sauka akan farin tayils din dake bayin.


Wani irin rawa jikinshi ya d'auka kamin ya sulale mukai zaman dirshan cikin toilet din,Kuka nasaki jin yanda marata ke wani irin kartawa,Rungumeni yai jikinshi shima yasaka kukan.

Yanajin yanda naketa malelekuwa ajikinshi,Amma yakasa tabuka komai dan yasa rai sosai akan cikin,Damacan haka Allah ya halicceshi da son yara to ga khairat itakuma tunda kakanninta suka amshe dole Abba yaimishi akan ya kyalesu tunda abin yana nema yaxama rigima,Yanzu kuma yanata murna yasamu gashi ya zube,Saurin zabura yai ya fara hadamin ruwa dan babu allura ko daya da zaimin dole sai an fita.


Agaggauce ya kira abubakar duk da cewa dare yayi sosai lokacin dan shabiyu ta wuce sosai.

Shima dagashi Sai jallabiya yafito da key din mota hannunshi.



Bayan awa daya.

"Karka damu dr.insha Allah lafiya zata tashi Ammafa babu cikin dan ya zube kuma yakamata asamata jini ko leda d'ayane dan yazuba da dayawa,Cewar wata siririyar likita.

Ajiyar zuciya ya Sauke kamin yace"Nagode sister natasoki kina barci,Bari inga idan jinina zaimata.



"Kai abubakar ina kuka fitane haka cikin dare? Kuma inata kiran lambar ahmad din Amma batayi lafiya ko?


Cikin shegiyar hausarshi yace"Abba ayshace babu lafiya cikin jikinta ya zube,to jini za a sakamata kuma nashi beyi daidaiba shine aka dibi nawa gasucan za a sakamata yanzu.


Cikin tashin hankali Abban ke salati kamin yayi addua,Amma be gayama kowaba Sabida dare yariga yayi.




""""***""""
Tunda yadawo Sallar asuba ya gayamusu halin da ake ciki nanfa akafara jajanta juna yayinda maman katsina hadda hawayenta sabida sosai ta kwallafa rai akan cikin tasan duk tsiya dai zataga gilmin jikoki gabanta kuma na autanta.

Shiyasa maman kano saita daure bata nuna damuwartaba sosai sabida kadda aga kamar ta zake da yawa.

Tun asubar abban yaje asbt,Nan ya taddasu ko wanne zaune ido jajir dan tsakanin Dr. Din da abubakar din babu wanda ya rintsa cikinsu,Shiko dr.ai harwata rama yai ta musamman saikace shine me jinyar.



K'arfe bakwai nasafe duk suna asbt d'akin ya cika amma har lokacin ban farkaba sai barci nake.

Saidaga baya jinin ya k'are sabida kwata kwata be tafiya da sauri.


Fes na sauke idanuna akan mamana wadda tai zuru idanunta akaina Amma idan ba lura kaiba bazaka ce nidin take kalloba.


Afusace aka turo k'ofar bakuma tare Da anyi Sallamaba.


Harni Saida na waiga na kalli kofar.

Alhaji adamu ne yashigo cikin cikin fusata saikace wani bijimin sa"Ina mara mutuncin yake dan ubanshi har ni zai tozarta dan iskanci? To gani sai ya hardani akulle sannan zan gane shi tantirin d'an iskane.


Wani irin tsitt d'akin yayi sabida sudai baki basu sanshiba,Mama kuwa sadda kanta k'asa tai,Shiko dr.wani wuri yake kalloma.


Shigowar Abba dakin yana fadin"Yaya lafiya meya faru?

Fuskarnan cike da masifa da bala'i yake fadin"Wancan d'an iskan dan naka shi zaka tambaya Yo haka kawai tunsafe yasa 'yan sanda su kamamin yarinya banda bugun da yaimata? To wallahi yayi kadan kai har kai baka isaba balle shi wallahi.

Kallo daya Abba yaima ahmad din ya fahimci abunda yake nufi,Matsawa yai gabanshi kamin yasaka hannunshi cikin aljihunshi ya fiddo wayarshi"Anshinan ahmad yi hakuri kirasu kace su saketa dan Allah badan halinsu ba,Kaji yarona? Ya idasa maganar yana bubbuga kafadar ahmad din wanda kirjinshi keta hawa da sauka tsabar bacin rai.


Saida yai kamar yadda abban yace Sannan yamike yabar d'akin zuciyarshi nawani irin zafi da zugi.


"Wawa kawai kagama bugarmin yarinya na kyaleka shine kuma yanzu zakasa akamata saikace wata barauniya to kanka ka tonama asiri dan ina nan inamaka shirin aurenta tunda tana sonka.


Daga kwancen da nake Saida naji yanda kirjina yaiwata mummunar bugawa haka mamana,Yayinda Abba da maman sukabishi da kallo me tattare da tsananin mamaki lallai ma.


Wani uban tsaki yaya halima tasaki kamin tace"Aikuwa zata mutu babu aure kuwa,Duk da irin kallon da abban kemata besa tai shiruba dan gaskiya wulalancin ya isa hakanan.


Lumshe idanuna nai wata kwalla na zubomin Sabida tashin hankali,Zainab ce ta dawo kusa dani ta damke hannuna cikin nata tanajin wata irin damuwa da bacin rai.

Abubakarne yashigo d'akin akaro na biyu cikin hargagi yace yafita dan sai yanzu ya fahimci waye,So biyu yana kiranshi da tubabbe bayan musuluntarshi domin dacan be San yaya suke da abban ba Sai yanzu da yabi bayan ahmad din yagayamishi.

"Maza wuce malam kana saka mara lafiya damuwa aje waje hakanan".


"Sakarai tubabben banza kaikuma awa?

Kunyace takama abban musamman daya kalli maman kano yana ta dafe kanta alamun akwai damuwa.tare da ita.
12/10/20, 9:47 PM - Naffy Aliyu Umar: 65



Bakajin sautin komai cikin d'akin sai fad'an yaya halima yi take tana k'arawa,Dama abba da abubakar sun fice waje dan dubo halin da dr.din yake ciki.
"Wai mama bakiji abinda wannan mutumin yace ba? Na tabbata tunda yafadi saiya aikata bansan me suke nufi damuba,Wallahi Abba beyi sa'ar 'yan uwaba.


Kwallar data tarar mata ta share kamin tace"To ya zamuyi dasu tunda haka suke? Amma babu wannan maganar auren dan wallahi ko abbanku ya amince Ahmad bazai taba yardaba kome za'ai kuwa danhaka kumadaina batama kanku hankali,Kuma ko yanzu abinda yasashi turamata police yayine dan yana zarginta sabida fadan da sukayi jiya.


K'arfe goma suka kwasa suka koma gida sabida suyima zainab shirye shiryen.dayakamata su wuce da wuri.

Maman Dr. tace mamana ta zauna dani kamin dr ya shigo dan tun safe dayafita bekuma shigowaba saidai sauran likitocin dake shigowa akai akai suyimin sannu kokuma su dubani.


Koda na farka mama nagani Saman kaina da alama addua takmin ma.

Riko hannunta nai yayinda idanuna ke cikowa da hawaye.


"Sakeni in hadamiki ruwan wanka saiki wanke bakinki ki wanka zakiji dadin jikinki sosai.



Da kanta taimin wankan takuma gashemin jikina,Musamman abuna dan sosai ta dumamamin jikina,Yayinda cikin ranta take fadin inama zasu bari data wuce da diyarta gida harta d'an huta tykunna.


Abaki tabani tea nasha Sannan taban magungunan da suke zube nawa.

"Aysha anya kinajin dadin zama gidannan kuwa?

Kaina na d'ora saman cinyarta tare da lumshe idanuna.

"Ki gayamin aysha hankalina yatashi daga jiya zuwa,Bansan kina cikin damuwa irin wannan ba,Kuma meyasa baki taba gayamin akwai matsalaba uhum?


"Mama wa inda nake tare dasu basu da matsala,Ya ahmad nasona sosai kuma yana kyautatamin duk da cewa kwanakin baya muna fada sosai dashi Amma yana kulawa dani,Haka mama yanda kikasan ina tare dake,Shima Abban haka sauran yayunshi ko a fuska babu wacce tataba nunamin wata fuska ta daban,suna sona sosai musamman idan kikaji irin shawarwarin da suke bani,Sannan duk wadda zatazo akwai abinda zata rikomin na amfani.

Matsalar kawai shine dangin abbansu Sam basu kaunarsu,Kuma bansan abinda ya shiga tsakaninsuba,Sannan duk kusan sunaso shi yayan ya auri 'ya'yansu Ammafa ayanzu.



"Hummm to Allah ya kyautamusu gashi na gani da idanuna wannan mutumin gashi da shekaru Amma na banza tunda gashinan yazo cikin mutane yai wannan abin,Be tsaya duba bak'in fuskokiba,Ni ahmad dinnema nake tausayawa dan yau kam angama kaishi k'arshe kawai dai dan ya kasance me biyayya ne.


"Mama zan biki gida dan Allah.


'"To aysha inda zai barki ainima da hakan naso kodan inkula dake sosai cikin wannan yanayin,Saidai ina ganin da kamar wuya shi mijin naki ya amince.



Juyawa yai yabar bakin k'ofar bayan yaji shiru.

Dama niyyar shigowa yai kamin yashiga office dinshi saikuma yazo ya tadda mama namin tambayoyi,Ba k'aramin farinciki yajiba da beji wani abun tonon asiri ya fita daga bqkinaba.




***

Anatse sukacigaba da duk hidimarsu tunda sunga naji Sauki,Saidai har wannan lokaci basu daina nanata abinda yafaru ba,Balle yayunshi wa inda saida maman ta taka musu burki waida zuwa zasuyi su dunduma ita ummin.




***""***

Suna tafe yanamishi bayanin duk abinda yafaru har zuwa shigowarsu cikin d'akin ,Daidai lokacin mama na sallar azahar yayinda nikuma nake kwance Amma kuma ba barci nakeba tunda yanzu muka gama waya da abbana.

Ahankali na bude idanuna jin yana kiran baby ko kunyar mama bejiba.

Wani irin mugun kishin ya nakeji,Wanda bansan idanashiba tunda naji maganar aurenan gashi yanzu na tsaya nakuma k'aremishi kallo,Yai shirinshi tsaf cikin blue jeans da t.shat me dogon hannu kanshi babu hula kuma kanshi babu suma me yawa anyimishi aski na zamani me kyau amma bana marasa ji ba.
Sai tashin k'amshi yakeyi.

Ahankali na gaida salim shikuma yaimin Sannu.
Magana bata shiga tsakanina. Da dr.ba dan wani irin haushinya nakeji,Gashi fuskarshi babu walwala har lokacin.

Saida mama ta idar suka gaisheta kamin su juya zasu fita.

Da sauri na riko hannunshi,Saigashi yayo dan baya yana min kallon lafiya?

Miyau na hadiye kamin nace"Dan Allah kasa asallameni inaso zanbi mama idan ka amince!!!

Kuma hade fuskarshi yayi kamin yace "Karma kifara wallahi babu inda zakije ki barni garama kiyi hakuri.
Yai maganar ne yana shafar gashin kaina kuma cikin rad'a babu wanda zaiyi tunanin ba lallashina yakeyi akan wani abuba nanko kashedi yake jaddadamin.


Kuka nasaka bayan fitarsu,Yayinda mama ta zubamin ido,dama tasan babu yanda za ai ya amince shiyasama bata sa aka ba.


"Garama ki daina wannan kukan kindai san Ahmad ba yarda zaiyi ba kema rigimace kawai kalar taki,Sannan gashi bawata lafiyace dakeba nasan insha Allah mamanku zata kula dake sosai.


"Mama ni bansan nan bazan zauna ba binki zanyi.

"Neman rigima dai kalar naki kuma wallahi babu ruwana,na tabbata idan abbaki yajima Sai ranki yabaci.


Shigowarshi cikin d'akin yasa mama yin shiru.

K'arfinshi yasa ya danneni Sannan yaimin allura,Ina rungume jikinshi ina kuka ya kalli mama"Mama mukoma gida kawai zan kula da ita acan Sannan yanzu mama takira wai sungama shiri.


"Kima daina wannan kukan.

Da kanshi ya tattare kayan yakai mota Sannan yadawo ya kamani dan jikina sam babu k'arfi gawani sanyi danakeji yana shigata,Yayinda naketa tunanin shikenan cikin da Dr. Ke d'agamin k'afa dashi ya bare toma mafarki yana zama gaskiya ne?

Nifa daga mafarki sai ciwon gaske ashe ana samun haka"Mama"

Ahankali ta amsa tare da kallona.

"Wai dama mafarki yana zama gaskiya ne?

Da mamaki take kallona kamin tace bayani zakimin yanda zan gane waye yai mafarkin?

Rage gudun da yakeyi yai cikin dibara yanda zaiji me zance.

"Mama mafarki nai guguwa nata bina,Amma inajin dariyar wata mace cikin guguwar har saida ta lillibeni Sannan ta barni wai na duk'a zanyi fitsari shine kawai naga jini,Waikuma dana farka sainaga ashe gaske ne.


Wani irin shiru motar tayi dan nima danagama maganar shiru nai ina kallon Maman wadda itama nidin ta zubama ido.

Dagashi har ita shiru sukaimin niko nakoma jikinta na kwanta.


.. .. ... ..

saida ya kwantar dani Sannan ya fita dan dama allurar barci yaimin Sabida inhuta sosai kuma su mama sutai cikin nutsuwa.,Batare da hankula sun tashi ba.



"To hajiya mudai gashinan zamu wuce ga yaranan har biyu munbaku sabida jin dadin rikon farin da kukai danhaka saidai mutayaku da addua Allah ya baku hakurin riko dan Allah aita kwabawa ba saimunji ba.


murmushi tasaki kamin tace mungode sosai da wannan karamci Allah yasaka da alkhairi ya barmu tare yakuma k'ara dankon zumunci.


Anrabu cikin mutunta juna gami da farinciki domin kowanne ya yaba irin tarbar dayasamu ga dan uwanshi.

Nan akabar zainab nata kuka.



**""**

"To Salim ya kakeganin yakamata ayi yanzu? Dan gaskiya hankalina yatashi Sannan nasan ko ita maman saitayi tunanin wata matsalarce tunda wani irin shiru tai nasan kuma ganina yasa batace komaiba,Ina cikin wani hali salim Bansan lokacinda wa innan abubuwan zasu wuce komai ya daidaitamin ba!!!!


"Ka kwantar da hankalinka insha Allah tunda wa incan suka wuce to Wannan ma zai wuce,Yanzu inaga wajan malam yahaya zamuje wancan me islamic chemis dincan,Sai muyi mishi bayani muji abinda zaice.



***

"Pls mana zee nagaji Allah ki barni in yi dan Allah.

Bakinta ta turo gaba tana kauda kai"Nidai wallahi a a toma ka iya adduar da akeyi ne?

Goshinya ya dafe kamin yace"Addua. Aweety? Ban iyaba amma fadi inji.


Koda tafara karantomishi adduar da shugabanmu yaimana umarnin yi yayi saduwa,Wani kwanciya yai yana sauke numfashi"Gaskiya tanada wahala dan Allah abiyoni bashi.


Wata dariya tasaki tana kallonshi"Lallaima saikace wani abin ci? To babu bashi danhaka ka iya addua ka kwashi gara malam.





Haske writer's association.
12/10/20, 9:47 PM - Naffy Aliyu Umar: 66




"Wallahi da gaske nake sai anyi addua akeyi ko kanaso idan muntashi haihuwa mu sami marasa ji?

Cikin Sanyin jiki ya girgiza mata kai,Lallai musulunci ba k'aramin gata yaima 'ya'yanshi ba tunda gashi harda wata addua zakayi kuma alhalin dadi zaka kwasa"To zee ya zanyi dake tunda kinfini wayau to ki koyamin ita yanzu dan Allah.

Tsabar mugunta 'yar guntu ta fadi mishi ta tashi tabarshi nan kwance yana nanatawa.



***
"Akwai inda ke miki ciwo ne?

Kuma kauda kaina nai ina matso kwallah,wani mugun takaicinshi nakeji cikin raina balle dana farka naji ko k'amshin su maman babu cikin gidan alamun sunjima da ficewa.

Rungumeni yai cikin jikinshi yana shafar bayana"kiyi hakuri idan kikasami Sauki zanbari kije kinji? Amma yanzu baki da lafiya kina buk'atar kulawa baby ko bakisan jikinki na buk'atar dumi da hutu ba?

Kuma bare bakina nai ina gogemishi kwalla akirji.

Duk hankalinshi tashe yake dan tun la'asar nake aikin.kukan gashi yanzu har dare ya rufa.


Sallamar mama ta katsemishi lallashina dayaketa aikin yi"Shigo mama,Shine abinda ya furta yana gyaramin kwanciya.

"Sannu aysha wai duk kukan zuwa gidanne ko wani wuri kemata ciwo?


"Mama batajin magana wallahi babu yanda banyi da itama tai hakuri Amma taki daina kukan gashinan har jikinta yafara dumi har so nai muje da salim samomata magani Amma nakasa fita inbarta tana wannan kukan Sam bata da lissafi Allah wane mahaukaci zaibarta zuwa gida ahaka? Ya idasa maganar cikin dan fusata.


"To kadaiyi hakuri hadda kuruciya ke damunta ai,Tashi ka gasamata jikinta da wancan ruwan ta zauna cikinshi,Kuma yakamata taci abinci hakanan kadda yunwa ta kamataba.

mikewa yai dani jikinshi yana kallona dawani irin yanayi na tausayi Amma fuskar nan sam babu walwala dan ran nan nashi adagule yake.

saida yasa hannunshi yaji yayi Sannan ya zaunar dani,Rikeshi nai ina hawaye.
"Baby kukanki yai yawa kwana biyu ko akwai inda kemiki ciwo ne?

Turo bakina nai gaba cikin.shagwaba nace ni dai gida zani.

d'allemin baki yai yana hararata"Wallahi ki fita idona baby,Idan nagaji fa zan saki kukan gaske ne.


Da kanshi yaimin wankan bayan na zauna cikin.ruwan maganin da maman ta kawo.


Jikina duk babu dadi bakina ma kamar nai watanni banda lafiya.



***

Cikin sati guda na warware nai kamar baniba sosai mama take bani kulawa ga wani irin farfesu da takemin kullun shine abincin dare na.

banda sauran kayan da zasu inganta lafiyata da kuma aurena,Babu ruwanta da wata kunya musamman idan ta lura da bansan sha kokuma ci yanzu zata fara fada tana nunamin abinda yadace.

'Yan uwanshi babu wadda bata dawo dubani ba,Suma dai tsarabar tasu ta inganta jin dadin k'aninsu ne.



**"""**
"Ahmad gayamin haka wannan adduar take ko?

saida yasaki dariya kamin yace eh haka take mana kayi daidai yanzu.


"To Alhamdulillah yau zanfara angwanci,Zainab tabani wahala Allah gashi har zanfara fita aiki naso ace ban komai in zauna in huta sosai.


"Hakan ma lafiya lau,Tunda dai anyi auren ai anyi me wuYa ammafa kayi k'okari wallahi Shanake tuni an wuce wajen ai?

"Ina ai babu abinda akai cewa tai wai ba ayi dole sai anyi addua,Har cewa nai abiyoni bashi Amma taki.


Dariya yasamai har yana duk'awa lallai ma baka da kai Adduar ce za a biyoka bashi? To yayi.Nidai zanbaka shawara kabita ahankali dan wallahi idon mama akan su yake kanayin ba daidaiba Zata wanke ka kilama ta kwace matar.


Atsorace ya fiddo idanunshi"Haba dan Allah fa? To ya zanyi kasandai ai dole Sai jikinta ya nuna dan gaskiya batasan namijiba daga yanayin yanda take shiga idan nai yunkurin tabata ni wallahi bammasan yanda zanyi da itaba yau.


"Yafa zakai da ita daya wuce lallabawa kabita ahankali amma ka nemi allura da magunguna ka ajiye komai ta fanjama to famjam din.


Riko hannunshi yai yana dariya "Nagode sosai ka kawo shawara wallahi.




. """"

idanunshi waje yake k'aremin kallo yayinda wani irin nishadi da farinciki ya sakkomishi dan idan be mantaba to yanaga rabonshi da walwala tun kamin inyi barin cikin nan Sai kuwa yanzu daya shigo ya taddani ina sallah Saida yagama lissafa kwanakin da jinin yaimin Sannan ya zauna.

Sam fuskata babu walwala naimishi Sannu da zuwa.

rikoni yai ya zaunar kan cinyarshi"Baby bansan ganin wannan damuwar a fuskarki dan Allah kiyi hakuri nayimiki alk'awarin duk randa Zainab zata ganin gida tare zakuje kuma kwanakin da zatayi kema shi zakiyi kuje tare ku dawo tare hakan yai miki?

kaina na d'agamishi ina share hawaye.

rungumeni yai yana shafar bayana"Baby yanzu rigimace dake wallahi sam kuka be miki wahala,Yaushe kikafara salla ban saniba?

Batare da wata damubawa nace jiya.



Amare.




wannan labari na kudi ne.
Idan kinga wannan labari waje to tabbas na siyarwane.Danhaka idan kinaso zaki tuntuni lambar maman khadija domin ki siya kiyi karatunki hankali kwance.


08142643253.





Haske writer's association.
12/10/20, 9:48 PM - Naffy Aliyu Umar: 67




Sam batai tunanin wai ya haddace adduar nan ba shiyasa ta bude ciki ta kwashi kazar ta da madara,Shiko hankalinshi kwance yake dariyarshi cikin zuciya yasan zuwa anjima kadan wannan murmushin da takeyi zai koma kuka,Yana fata da burin Allah yasa yasameta cikin aminci kamar yadda ake shedar yaran hausawa musamman wa inda basuyi irin shegiyar wayewar nan ta zamaniba.


da kanshi yajasu Salla kamar aka nutsar dashi,Sai lokacin jikinta yafara Sanyi,Bayan sun gama ne ta kalleshi"Wai murmushin mene kakeyi haka?

"zeetah ai dole inyi murmushi angwanci fa zan fara yau idan Allah yaso,Kingako ai dole inta murmushi inafatan dai kin shirya bani garar da kike fadi ko?


Tuni idanunta sun ciko da kwallah"Dan Allah da gaske kake ka iya adduar?

"Kaddai laifina zaki gani dan nayi Saurin iyawa? itace katangar data shiga tsakanina dake zeetah kuma kike tunanin zanyi wasa da ita? Lallaima na iyata tsaf kilama nafiki iya karantata yanzu dan d'azu da rana saida na nanatama malam isa ita yaji babu gyaran ko harafi daya(malam isa shine mutumin dake kula da gyaran addininshi) Hawaye takeyi tare da yarfe hannu"Dan Allah karkamin komai ni wallahi tsoro nakeji.


"To yanzu meye abin kuka dan Allah nimafa nan tsoron nakeji Allah bantabayin abunnan cikin jikin wataba kinga kenan nima nan atsoracen nake ko?

matsawa tai can nesa dashi kamin tace lallaima wallahi ban yardaba wayau kawai kakeso kaimin ka kaini ka baro.

sumarshi me yawa dake kanshi.yashafa yana dariya,Dan kullun sai malam yaimishi maganar sumar Amma saiyace ya rage.

hannuwanshi ya mik'amata"Zonan 'yammatana kinji,zo inji mene matsalar wai.

turo bakinta gaba tai kamin ta dawo jikinshi,Cikin dibara yafara shafarta yana gayamata kalamai masu dadi kamin wani lokaci.tasaki jikinta akanshi batare da sanin tayi hakanba.




***

"Aysha wannan rawar jikin da kikeyi fa? ko yau zanfara nemanki ne?

hawayena na share ina yarfe hannu,Dan Allah kai hakuri wallahi ban warkeba.

zubamin ido yai yana mamakin wannan tsoro da yake hangowa cikin idanuna,Hannuwana ya riko yana kallon cikin idanuna"Bansan wannan kukan dan haka karki fara,Gayamin bakiso ne?

da sauri na d'agamishi kaina.

"ok to sabida me bakiso Alhalin kinsan dama dauriya kawai nakeyi matse nake?

Shiru nai ina zare ido narasa ta ina zan fara gayamishi cewar tsoronshi nakeji,Toma ba wannan ba ni menene ya kawomin jin tsoronshi tunda ba yanzune farkon yi ba.

wara irin rawa jikina ya d'auka lokacinda yafara lalubata.

Tsoro karara ya bayyana akan fuskarshi kamin ya rungumeni muka kwanta,Ahankali yake shafar bayana"shiiishii Shikenan tunda bakiso yi kwanciyarki,Na hakura.


Tun yanajin yanda jikina ke rawa tare da bugun zuciya har yaji shiru Alamun barci yai awon gaba dani.


mamaki ya hanashi motsin kirki,To meke faruwa?



**

Aure yakin mata.
Tunda Allah ya temakeshi yasami hanya shikenan ya daina ji dagani.

shiyasa duk magiyarta be jitaba.


lokacinda yasami nutsuwa ko nishi me k'arfi bata iyawa dan sosai ya barje guminshi akanta.

kamin yagama hutawa yaji jikinta yafara d'aukar zafi,Shiyasa sai ya jawota ya rungume gara idan sun huta din Sosai Sai suyi wankan dan yanaso ta dubamishi ko babu matsala ya iya.



""***""

koda asuba taima Saida yakuma gwadawa saidai matsanancin tsoron dayagani tare dani yasashi hakura duk da cewa ba k'aramin matsuwa yai ba.



.....

"Hello kana jina ko? So nake kazo gida ka sameni zamuyi magana akan auran da nace zan had'a danhaka ina jiranka.




maman khadija.


Haske writers association.
12/10/20, 9:48 PM - Naffy Aliyu Umar: 68





Da safe.

Sosai taji saukin jikinta Ammafa babu k'arfi jikinta ko kadan.

yayinda shikuma ya like ko yaya ta motsa sai yai mata sannu.Dadi

Please Login or Register in order to submit comment