Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Allah,Kuma saikuje kuci gaba da shirye shirye Allah ya shigemana gaba yasa karshen jarabawarka ne wannan.




***

"Yauwa hadiza kinajina ko? Auran Fatima yakoma yakoma ranar juma'a insha Allah sabida wasu dalilai danaga ya kamata ai hakan sabida haka dazu baban yaron ya kirani inda yake shaidamin cewa zasu iya kawo lefe gobe danhaka saiku kasance cikin shiri.
Idanunta gabadaya ta fiddo tana kallonshi sabida tsabar yanda maganar ta bugeta" Shikenan Allah yasa hakan shine alkhairi.

Duk da tabashi tausayi Amma be nunaba sabida beso ta koyi tirjiya tsakaninsu domin sabon haline data tsiro dashi yanzu.

D'aki ta shige taita kuka sabida damuwa Amma ganin babu abinda zai canza saita tashi ta d'auki wyarta ta fara kiran yaranta na ma aura da sauran duk Wanda yakamata yasan an jawo bikin baya dan asamu ayi komai anutse,Tunda dama Abban yagama siyen dukkan wani Abu na b'ukata wajan hidimar.



Bayan kwana biyu Alhamdulillah ta kowane bangare an kacame shiri yayinda zukata suka cika da zullumi musamman na tunanin mezai faru bayan auren Amma amarya ko a jikinta domin burinta kawai ta mallaki Dr.Ahmad dan tariga tai imani da cewa Allah ne ya halicceta kuma zai iya kasheta aduk lokacinda yaso danhaka bata da matsala da wannan.

Kuzo kuganni a wannan kwanakin nai kuka nai kuka harnakoma jin haushin yaya fati ganin yanda suketa shirye shiryensu saikace wani Abu bazai faruba wani abun haushi saima ta tattarani ta watsar saikace batasan me nakeyiba.
Dole Nima na watsar Ammafa zullumin danake ciki daka kalleni zaka iya fahimtarshi.



Ranar Alhamis





Haske writers association.
12/10/20, 7:44 AM - Naffy Aliyu Umar: JARUMA.
4

Na maman khadija.



"Kai amadu tashi kasha wannan babu madara ciki kataba ganin inda ake so a warke amma babu cin abinci?

Cikin yanayi na ciwo damuwa da tashin hankali wa inda suka hadu suka kuma danneshi ya fara magana " Baba dan Allah kabarshi na koshi nasan amai zanyi idan nasha.

"Kai bansan hauka ka tashi ko saina bigeka yanzu? Maza tashi gobe iwar haka insha Allah kazama ango amma ji yanda ake fama dakai saikace wani junior'sunan yaron Ahmad din.

Bakinshi Asama saikace baby ya tashi zaune drip din da akasamai ya zare sannan yai kokarin tashi Amma yakasa saida mahaifin nashi ya temakamishi ya rakashi bayin ruwan ya tsaya watsowa duk dan ya batama baffannasu lokaci Amma ya shareshi dan yana sane abincinne beso yaci.
Gidan cike yake da mutane 'yan biki shiyasa maman saita sami lokaci take lekoshi.

Da kanshi yabashi tea din ya doramai da farfesun kaza ko zaiji dadin bakinshi Sannan yabashi magunguna" Ko kaifa amadu ? Amma adinga fama dakai kan cin abinci kana nokewa haka amaryar zatazo ta taddaka babu lafiya ko?
Dan Allah ka kwantar da hankalinka insha Allahu komai zai wuce kaji ko?

Kanshi kawai ya d'aga tare da gyara kwanciyarshi.

Wayarshi ya jawo ganin missed call rututu yasa shi fara bin numbers din daya bayan daya yana kira kusamma duk masuyimishi Allah sanya alkhairi ne.
Saikuma test message daga salim Wanda kemai bayanin inda suka kama bayan gama d'aurin auren inda zasuci abinci su huta kamin su juyo da amarya.

Fatima ya kira daga k'arshe,Yanajin yanda ta d'aga wayar da zumudi yasan tajima tana Neman shi.

"Sorry Fatima inata barcine bansan kin nemeniba yi hakuri ya taro?

" Alhamdulillah ya jikinka ammadai da sauki ko?

"Yes naji sauki sosai,Babu wata matsala ko?

" Eh babu saidai nayi kewarka tun jiya rabona dakaifa kuma baka gayamin jikin ya kwantar da kaiba saida salim ya kirani dazu yacemin zai shigo mu gaisa tunda yana cikin garin dan Allah ka dinga gayamin komai kaji???

"Naji Fatima kiyi hakuri zan kiyaye insha Allah,Zan kwanta yanzu Amma danatashi zan kiraki kinji ko?


Ajiye wayar yayi yana sauke numfashi dan sosai yakejin wani irin shegen nauyi da taimishi.
12/10/20, 7:45 AM - Naffy Aliyu Umar: JARUMA.
5


Na maman khadija.




Alhamdulillah mun isa lafiya kunsandai yanda ake tafiya idan aka d'auko amarya.
Kai tsaye gidan iyayenshi muka nufa lokacin daf da magriba.

Sosai aka taryemu Dan yi suka rinkayi kamar zasu goyamu dangin angon.
D'akin mamarshi aka kai yaya fati kuma har lokacin ina tare da ita sosai zazzabi ke buguna lokacin,Musamman idan naji Jan majinar yayan nasan kuka takeyi har yanzu.

Gwaggo asabe ce k'anwar abbanmu ta shigo cikin d'akin tana fadin "ina ayshan taho ga angon zaimiki allura ai bakin kwana da wannan zazzabiba taso gashinan yana jiranki.

Ihun kuka nasaki ina tirja k'afafuna kasa alamar banso Dan ko magana ma nakasa.

Cikin shesshekar kuka yaya fatin tace Dan Allah a kyaleta gwaggo damafa batason allura ya samomata magani saitasha.

Saida tagama mitarta sannan tabar d'akin tanafadin saura shima tace bataso.


11;17 pm.

Gidan yai tsit kamar babu kowa na cikin gari duk sun wuce na nesa kuma sun nemi wajan kwanciya.
Ido biyu lokacin sabida hirar da yaya fati takeyi da mijinta jinake kamar zan mutu tanaji inajan tsaki Amma tai banza dani bataso ta biyemin Dan tasan gobe iwar haka to munfara kewar juna.

Bansan lokacinda barci yai gaba daniba Dan sunjima sunashan love dinsu.


Da safema haka mutanen nan sukaita nan da nan damu kamin akwasa atai gidan Dr.din Dan kai amarya d'akin ta.

Gaskiya gidan ya tsaru bawani babba bane Amma gaskiya an tsaya an tsarashi Sannan Abba ya kashemata kudi kodan yajima be aurarbane ? Sosai gidan ya burge kowa dakuna shiddane nashi biyu nata uku saikuma Wanda babu komai ciki saiwani green din cafet da aka malala koshi yai kyau gaskiya,Balle nata kuka ciki daya dayane wannan akasamata kayan gado wannan kuma kujeru dayan kuma ciki da falone shimadai haka akasamata Saikuma babban falon Wanda da kanshi ya zuba kujerun ciki gaskiya ya kashe kudi ba sai an gayamakaba.
Shima d'akinshi haka yake daya kujerune kawai sai kayan kallo dakuma kantoci wa inda aka shirya wasu tarin littatafai akai saikuma dayan Wanda aka zuba gado miro dakuma ma'ajiyar kaya Dan ga komai nan ashirya.
Ah gidafa babu makusa gaskiya Dan babu ta inda zaka kusheshi kitchen shake yake da kayan amfani Haka store inda akayishi daga gefen madafar. Gakuma wajan cin abinci shima akebace yake.


Saida akai Sallar azahar akaci aka koshi domin daga gidansu aka kawo abincin bayan mungama gyaramata gidan kuma akafara haramar tafiya.

Wani irin kuka taitayi lokacin tafiyarmu muna tayata saikace ba itabace me zumudin auran nan.
Haka tanaji tana gani mukabarta daga ita sai halinta Dan wa inda suke dangin Dr dinma sunata haramar wucewa Dan dama suma tsirarine.


Nidai babu abinda zan iya k'ararwa na hanya dankuwa da zamuzo kuka nake kuma ga duhu yanzukuma zazzabi ta sakamin barcin dole.



**
To gadai amarya,Tunda kowa ya watse batawani tsaya nuna bakuntaba ta fto tafara ayyukanta Dan idasa kintsa gidan ahankali tagama kallon dukiyar da aka tsaunamata lallai iyayenta sun gamamata komai saidai fatan alkhairi tsakaninsu.

Sai bayan magriba yashigo gidan bayan yagama jera addua kamin shiga gidan sosai yakejin zullumi da fargaba.
Fatanshi Allah yasa mummunar adduarshi ta k'are.

Tsaye ya taddata gaban madubi tana cire d'an kunnen dake kunnenta.
Ganinyaja yai tsaye yasata k'arasawa gareshi cikin zumudi Dan rabonta dashi tun shekaran jiya ko jiya basu haduba.
Rungumeta yai tsam cikin jikinshi yana sauke ajiyar zuciya hak'ika mata ni'ima ne ga maza kamar yadda mazan suke akan mata yaushe rabonshi da ya rabi jikin mace har ya manta saidai marasa lafiya tunda shidin likitan mata ne kwrarre Wanda yai duk karatunshi a waje.

"Nagaji Fatima jikina babu inda bemin ciwo wlh,Ya idasa maganar gajiyar nakuma bayyana a fuskarshi.

" Sorry da wuri ta shige bayi ta hadamishi ruwan dumi domin yayi wanka Sai tabashi magani Dan da alama har yanzu be warwareba.

Godiya yaita yima Allah yanafatan zamansu ya dore ba tare da wani mugun Abu ya biyo baya ba Dan sosai yakejin tana shiga inda babu wata mace da ta shiga Dan y a lura ba k'aramin so takeyimishi.

Taso tayashi shafar ganin yanda yakeyin komai alakace saidai tanajin kunyarshi Sannan bataso shima yaga zakewarta daga tarewa.

Kamo hannunta yayi ya zaunar da ita kan cinyarshi yana yanda take wani k'amshi,Yasan Abu na farko shine fara kusantar iyalinshi Dan indai zai fara to yanaga shine farkon matsalar gashi bazai iya zubama fatiman idoba Dan ya jigatu shekaru uku ba bawasabane amatukar takure yake komai dandai kawai bashi da yanda zaiyine.

"Cikin murya me sanyi ya furta Fatima". Shigar da kanta kirjinshi tai ta lumshe idanunta kundaisan haduwar namiji da mace yanda yake musamman Wanda yai kewa da kuma sabbin shiga.

Ganin dai ba magana zatai mishiba yasashi mikar da ita " muje ki rakani insa kayana sai in wuce masallaci Amma dagacan zan wuce gida.

Marairaicewa tayi zata saki kuka dan gaskiya tsoro takeji.
Murmushi yasaki ganin tana bata fuska."Karki damu ba jimawa zanyiba insha Allah da anyi isha'i zaki ganni kima rufe gidan idan nadawo saina bude ok?

Kai ta d'agamishi tana Dan turo baki.,Dan itafa bata tashi tuna maganganun mutaneba sai yanzu shiyasa takejin tsoro.

Da lallashi yasamu yabar gidan Dan wasu masallatan har sunfara salla.




***

Abbanmu na tasa da kuka bayan mun koma gida to tarodai yagama watsewa tas gida yakoma sai IMU IMU.

"Aysha wannan kukan duk na menene kodai kema kina cikin masu tuhumatane da yin wannan auran? Cewar Abbanmu.

Kaina na girgiza mishi ina kokarin tsagaita kukan da nakeyi,Abba inason yaya fati kasani duk cikin 'yan uwana nafi shakuwa da ita Dan Allah mu nema musu magani ita da Dr.din kadda ta mutu ta barmu Dan Allah Abba wallahi gaskene ko gidansu saida naji anata hirar yanda matan nashi ke mutuwa kuma har yanzu babu Wanda yasan dalili ko sila Dan Allah ka duba Abba.

" hummm aysha kenan wani lokacin idan kina magana sai mutun ya d'auka kinkai shekaru 40 aduniya tsabar nazari da tunanin dake cikin maganar amma wani lokacin idan kikai magana saiki koma kamar me shekara 9-10 tsabar wautar dake cikin maganar Amma dai zan fahimtar daku wani Abu yanzu jeki kiramin mamanku.

Saida ta kammala sallar da take Sannan na gayamata aiken Abban lokacin nagama kukan saidai ajiyar zuciya da nake saukewa akai akai.

"Aysha badai wata maganar kika jawominba ko? Danni yanzu lamarin abbanku yafara bani tsoro gara in zubamishi ido kawai.


" Dafarko dai inaso inbaku hakuri musamman ke k'anwata mama kenan Dan dama idan yaso zolayarta haka yake cewa,Yana kallonta yake maganar da alama shima yagama sauka daga fushin da yakeyi tun gabatowar bikin.
"Kuyi hakuri Abu daya nakeso in tuna muku anan dannasan babu jahili cikinku shine shi aure rubutaccen lamarine Sam bazai yiwuba idan ba Allah ya qaddarashiba Fatima diyatace kuma INA sonta to Amma wannan auran yana cikin qaddararta nayi bincike fiye da Wanda shari'ah tace ayima akan Ahmad saidai duk labarin dayane yasha gwagwarmayar rayuwa duk da cewa yanada uwa kuma yanada uba Amma shi kadaine namiji d'akinsu gidansu gidan yawane kamin yaima iyayenshi gini suka tashi gidan gandun,Fatima Ahmad kuma shima yanasonta tsoron abinda zaifaru gaba yasa yake janyemata.

Ku kwantar da hankalinku idan Allah yasa Fatima zata mutu tofa wannan dolene koda ba cikin gidanshiba danhaka banson inkuma jin irin wannan maganar ko tunaninta Dan gaskiya tunanine na marasa imani da Allah ko kuma jahilai,Yaronnan abin a tausayamishi ne wallahi bashi da laifi cikin abunda ke faruwa qaddarace wadda ta hada da sunanshi Amma yanzu inda shi ashararine me mutane ke zato game da hanashi auran yaransu da sukayi,Na tabbata da zuwa yanzu Allah kadai yasan iyakar yaran daya bata danhaka hanashi aure ba mafita bane,Danhaka saimu dage da yimusu addua muga abinda Allah zaiyi ban yarda cikinku wani yakumasa damuwa cikin ranshiba ciki hadda wa inda basu gidannan Dan zan nemesu awaya ma.
Aysha tashi kije idan Allah ya kaimu tai sati biyu saikije ki kaimata ragowar kayanta kaminnan ankuma natsawa kinji ko?

"To Abba.

Tashinai na baro mama d'akin ammafa har lokacin nauyin daya danne zuciyata be saukaba.





***


" yakamata kizo ki kwanta hakanan dare yayi sosai kiyi fatan Allah ya amsa kawai.
Cewar abban Ahmad ganin yanda suka hana idanunsu barci tsabar fargabar auran dan nasu.

"Banni alhaji wallahi yanda kasan inyi aman zuciyata in huta haka nakeji sabida tsabar zillon da takemin ,Kaga yarinyar nan iyayenta ba k'aramin tawakkali sukai suka bamuba yanzu idan wani Abu yasameta ai inaga babu Wanda zaikuma bamu.
" babu abinda zai faru insha Allah.

Kusandai kwanan zullumi sukai a wannan rana.




**

"Fatima ina zamu kwana yau?
.
Dariya tasaki kamin tace kawai ka kwana d'akinka nima inkwana nawa.

Murmushi yayi kamin yace lallai yarinya bakiji da kyau ba Ai yau sainaji duminki yanda yakamata.

D'akinshi ya jata bayan suncika cikinsu,Har mamakinta yakeyi dan Sam bata da bakunta abunta take babu wani nuku nuku kuma ahaka saiyaga tanajin kunya wani lokacin.


Zaunar da ita saman cinyarshi yayi yana kalloncikin idanunt, " Yimana. Addua kamin mu kwanta barci Allah ya karemu daga sharrin dukkan abinda ya halitta Sannan yabaki ikon jure dawainiya dani dan bazan boyemikiba wallahi na Tara da yawa.

Narai narai tayi da idanunta alamun tsoro shikuma yakama dariya dan beyi tunanin zataji tsoronba.
"Naimana addua tun lokacinda muna sallah Dr.Insha Allah babu komai kuma ai kaima naga kayi adduar so kawai mu kyautatawa Allah zato ya amsa kuma zai karemu din.


Rungumeta yayi tare da kashe fitilar,Wani irin matsanancin bugu kirjinshi keyi Amma bejin zai iya hakura dan yakai makura.

Lokacinda yafarajin kukanta alamun ya shiga jikinta to daidai lokacin wani al'amari yafara faruwa.😳.





Haske writers association.
12/10/20, 7:46 AM - Naffy Aliyu Umar: JARUMA.
6


Na maman khadija.




Wani irin matsiyacin gurnani ya kaure d'akin Wanda ya tilastama kukan fatiman d'aukewa yaso kwarai alokacin yasamu ya barta Amma halin daya shiga ya litastamishi kasa barinta.

Cikin muryar kuka tace" Dr.namun daji sun shigomana ka barni haka dan Allah zasu cinyemu.

Rufemata baki yayi amma be tankaba yajima rabonshi da mace yanzu jiyake kamar zai mutu tsabar yanda hankalinshi yai gaba.

Kukan jaki ya karade d'akin bacin wancan gurnanin Amma yana like jikinta saida yasami nutsuwa sannan ya kwanta gefenta ya jawota jikinshi.
Tsittt wani shiru d'akin yayi, Kenan duk irin zaman da yayi koma menene yana tare dashi kenan tunda ba laifin gida bane tunda inda laifin gidane da tuni abun ya barshi dan wannan gidan shine na biyar daya Canza.

Yanajin yanda take sauke ajiyar zuciya dan ba k'aramin kuka ta hadiye ba, Matseta yayi cikin jikinshi yanadan shafar bayanta gamida jijjigata fainciki fal cikin ranshi duk da cewa tawani bangaren kuma yana cike da zullumi da tunanin mafita.





***

Tunda nai sallar asuba nake kiran wayar yaya fatiman Amma shiru babu wani bayani dan dama nasan inzata kwanta kashewa takeyi Amma dag a asuba tayi take budewa,Ajiye wayar nayi ina tunanin to wai lafiya shiru har yanzu ko makara sukayi ne yau.


Sumul tatashi saidai d'an abinda baza arasaba.
Da kanshi ya amso musu abin kari gidansu dan ba wani shahararren nisane tsakaniba.

Zaune suke kanta nabisa cinyarshi yanata wasa da kitson dake kanta itako idanu alumshe sotake taji yayi maganar darensu na jiya Amma shiru kakeji tunani takeyi Anya kuwa ba aljanu bane ke rayuwa tare da mijin Nata ? Tanaso yabata wani labari Wanda yashafi abinda ya wuce Amma batasan ko beso ba tunda taga har yanzu bece komaiba.
Idanunta arufe tafara magana tana kuma fatan Allah yasa kadda yaimata shiru kokuma maganar ta bata ranshi.

"Am Dr. Dama nace kodai saukar alk'ur,ani za ayima gidannan?

Murmushi yasaki kamin ya juyo da fuskarta tana kallon tashi fuskar," A a Fatima ko daya bawai a gidan matsalar takeba inajin ajikina damuwar take domin wannan shirun da kikaga nayi mamakin sauyawar matsalar nake dan sauran matan Dana aura babu wacce haka ya faru da ita daren farkonta shiyasa nacika da mamaki Wallahi Fatima idan da ace su mama zasu yadda da bazan kuma aure ba zan zauna ahaka har zuwa lokacinda nima kwanakina zasu k'are Sam bansan wannan qaddarar taimin nauyi da yawa waima kinsan kallon dan mafiya akemin cikin garinnan?

Tashi tai zaune Amma duk da haka saida ya jinginata jikinshi dan yaga lokacinda ta cije baki alamar tanajin wani Abu ajikinta har yanzu.

"Banganeba kamar ya zasu maka wannan kallon suntaba ganinka cikin wani yanayi irinn Wanda zai zama na zargi akan ka? Meyasa mutanenmu yanzu basuyima Kansu adalci shikenan yanzu qazafi da mummunan zargi ya yawaita cikin al'umma kowa kokarin bin 'yan uwanshi da sharri yakeyi tunda wannan ai sharrine abarka da abinda ya dameka mana.



Dariya yasaki ganin yanda ranta yabaci ,Yasani cewa basai an gayamishiba Fatima na sonshi sosai saidai shi Sam besan abinda yasa matan basu cika shiga ranshiba Saidai dan zaman sabo Wanda sukayi.

" karki damu hakan bazai zama matsalaba Fatima Allah yasani bansan yanda zanyiba Amma nima inajin babu dadi.
Bansan ko nine mayen ba.

Dariya tasaki kamin tace waifa maye lallai ma to idan da kai mayene ai da inaga zuwa yanzu kafara cin na makota da kuma 'yan uwa da abokan arziki,Koba hakaba?

Murmushi kawai yayi amma beyi maganaba tashi muje kikuma shiga ruwan dumi inaga har yanzu jikinki be sakiba kina dai daurewane kina boyemin.
Turo bakinta gaba tayi kamin tace nidai gaskiya a a wallahi da zafi ka gasamin dazu.

Marairaicewa yayi kamin yace "Haba mana teema nifa zaki temaka mawa anjima da dare insami hanyar bi lafiya Amma idan wajan be gyaruba ai akwai matsala ko?

K'okarin mikewa tagudu tafara ya riketa yana dariya dan yasan dama za ai haka dauriya kawai take Amma taji jiki.
" kinga wasa nakemiki mujedai ki gasa jikinki zanje masallaci idan Allah yasa nadawo sai inzo inbaki labarin aure auren danayi dama abubuwan daya kamata ki sani ko?

Da zumudi tabi bayanshi domin kin yarda ta shiga gaba tai wai kadda yaimata dariya.

Da kanshi yaimata abinda dayace duk da saida yai fama Amma takumajin dadin jikinta.

Saida ya fice daga gidan
Sannan ta lalubo wayarta.
Tana budewa kira yafara shigowa na aysha wani irin tausayinta taji yakamata ta tabbata da wuya idan jiya sunyi barcin kirki.

"Hello autarmu ya kk kuntashi lafiya ko?

Saida na tunzuro bakina gaba kamin ince yaya tun asuba nake ta nemanki fa!!!

" kinjiki da wani batu dan Allah mace da mijinta zaki wani dinga dokamin kira me zaki bani.

Cikin shagwaba nace kai yaya Fatima dan Allah kibar fadin haka,Yanzu dai ki gayamin ya kika tashi badai matsala ko?

Zamatai baking gado kamin tace komai qalau Alhamdulillah k'anwata ashedai andamu dani sosai wannan damuwa haka!! Yasu Abba?

Duk lafiya lau munyi kewarki sosai wallahi.

"Nima inanan ina kewarki Amma dai bani da matsala ki kwantar da hankalinki yanzu zan shirya wasu kaya Amma anjima kadan zan kiraki zamuyi wata magana.



Zaman jiranshi taitayi amma taji shiru dole takoma falonshi ta zauna gidan yaimata wani irin shiru Wanda bata saba dashi ba.




**
" Ka zauna kai shiru amadu ko akwai wata matsala ne?

D'an Sosa kanshi yai kamin yace baba dama kan wannan damuwar ne dankuwa kwana mukai cikin jin wasu sautuka na koke koken dabbobi to shine nace ko zakaima malam baba magana ne tunda kaga bama ataba ganin hakanba.
Kallon juna sukai tsakanin maman da kuma baban kamin ya sauke numfashi "Ikon Allah kenan kisan zai canza salo ko? To koma menene wannan karon insha Allahu saika rayu da matarka wannan jaraba har ina barima inje wajan malam din yanzu kaikuma katashi ka koma gida kamin tsoro ya farmata dama ga abincinku nan babu me kaiwa dan Allah ka cire damuwar komai cikin ranka kaji??

" To baba insha Allah zan kiyaye.



Tana zaune zaman ya isheta sotake kawai taji labarin abinda ke kashemishi mata Amma yaki shigowa sai wajan 3:00 ya shigo gidan hannunshi da dauke da kwando Wanda aka jero duk abincin.

Da sauri ta tareshi tare da amsar kayan hannunshi tanamishi sannan da zuwa.

Rungumeta yayi jikinshi yana shakar kamshinta kamin yace barkanki da gida yammata ya zaman kadaici?

Cikin yanayin shagwaba tace " Wallahi babu dadi tunfa dazu nake leken ta inda zakashigo waima ba kacemin kanada yara ba? Dan Allah ka kawominsu nan mu zauna tare.

Saida ya zauna ya dorata saman cinyarshi sannan yace"Karma ki fara wallahi

Please Login or Register in order to submit comment