Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

yakeji da betabayin zina ba duk iskancin da yayi be wuce ya rungume mace ba.Sai idan sha'awa ta matsamishi yai da hannunahi,Shiyasa koda yaji masifun dake akan mazinaci saiyaji dadi tunda be cikinsu,Gashi yanzu Allah yabashi mace lafiyayya me tarin ni'ima kuma shi da kanshi ya samar mawa kanshi hanya ba tare da wani din yataba bi ba.

"Zaki iya fita falo kuwa ko naje na amso mana abin kari?


cikin sanyin murya kamar wadda tasha ciwo ta girgiza kai tare da cewa"Ni bazan iya fitaba kunya nakeji kuma banso agane mama zata gane.

"Ok to zauna ina zuwa bari naje na karbo.



....
Nai tunanin zai tashi da jin haushi ko bacin rai,Amma ga mamakina qalau yatashi dan saida yakamin ma muka gyara d'akin Sannan mukai wanka,Amma hankalinshi tashe yake dan sosai yakejin matsananciyar sha'awa daga yanayinshi ma kawai mutun zai iya fahimtar hakan.

Da kanshi yaimin shafa duk yaga latsemin kirji Amma haka nai hakuri har ya gaji ya kyaleni nasaka kawa Sannan najirashi yagama kintsawa dan tafiya office, Ina rike da jakarshi haka muka nufi falo.



"Yau bazan dawo da wuriba zamuje wani waje da Salim ina fatan babu matsala ko?

gurgiza kaina nai ina k'okarin had'amishi tea"A a babu matsalar komai Ammadai zanshiga wajan zainab anjima idan nagama abinda nakeyi.

"Ok hakan yayi,Allah yaimiki albarka.


d'akin mama na nufa Amma bata ciki Shiyasa na fito nasan bata wuce wajan Abba tunda yau be fita da wuri ba.

dawowa nai falon na zauna Amma hankalina yana kan wayata dannaga yaya maryam online.

Bansan ya dawo kusa daniba Saidanaji ya fige wayar"Ke da waye haka naga sai murmushi kikeyi uhum?

juyamishi fararen idanuna nai kamin na turo baki.

Sumbatar goshina yai yana murmushi"To shikenan dai ni zan wuce,Banso in makara idan akwai wata damuwa kimin waya kinji ko?


"To yaya adawo lafiya Allah ya tsare yabada sa'a.

"Nagode babyna,Zan kira mama anjima tunda naga bata fitoba.


sai wajan tara nasafe sannan mama da abba suka fito be zaunaba ya fice bayan mun gaisa,Yayinda nacigaba da gyaran falon muna hira da maman.


"Wannan shirun na zainab na lafiyane kuwa ajiye wayar nan aysha ki lekota ni ko abubakar dinma banga giccinshiba yau.

Ahankali na fice na nufi bangaren nasu.



"""***"""
Gajiya da Sallama nayi na kutsa Kaina cikin falon wanda zai sadani da sauran d'akunan barcin.


Da k'arfi na kwada Sallama tare da zama saman kujerar.


Sanye da jallabiya ya fito Sai bula k'amshi yake kamar alokacin ya fesa turaren"Ah madam kece Sannu da zuwa"

"Yauwa ina kwana? mama ce tace taji shiru shine nazo inga lafiya.


Shafar kanshi yai yana mirmushi"Wayyo bari in shirya Sainaje na dubota Yau zeetah batajin dadi kumafa d'azu naje na debo Abinci Amma lokacin babu kowa,Shiga tana wancan d'akin dama fita zanyi.



Inda ya nunamin nashiga da Sallama,Can cikin bargo na hango muguwar taiwani lakur da ita.

jikinta nakai hannuna inajin zafin jikin tare da tashinta.

Idanun nan duk sun tashi kuma sunyi jajir dashi Daga gani dai tasha kuka.


Tasota nai niyyar yi Amma tasaki wani k'aramin ihu tana yarfe hannu,Atsorace na zaro ido ina fadin"Subhanillahi meya faru haka?

"Mutuwa zan yi Aysha wallahi yakusa kasheni.

"Toh Sannu tashi zaune,Tuni jikina ya d'auki rawa sabida hasaso azabar datasha da nai.


Duk iyakar kokarina kasa tashinta tsaye nai Sosai takejin jiki.

Cikin tashin hankali nafita kiran mama,Saigashi mundawo tare.


"Innalillahi Sannu zainab Ashe babu lafiya shiyasa shirun tai yawa? Bacin ma rashin hankali na abubakar ai da tuni kunje asbt kokuma yaimin magana yana ina? Aysha kiraminshi can Dakinshi.



tsaye nai ina kwankwasawa saigashi ya fito cikin wata lafiyayyar shadda rigar iyaka guiwa dinkin zamani dayake farace saiya koma kamar wani ango fuskar nan awashe.

"Kaje mama na kira"

atsorace ya fiddo ido kamin ya wuce gaba nabi bayanshi.


Harara take aikamai da ita kamar idanunta zaso fado dan duk tunaninta ciwo yajima zainab din.

sadda kanshi k'asa yai kunya nakuma kamashi.


"Tashiga ruwan.dumi ko?

girgiza kanshi yai batare daya kalletaba.


"Banganeba kamar yaya?

"Mama kuka takeyi wai bataso shine Saina kyaleta.


innalillahi wa inna ilaihirraji'un.,Ammadai baka da hankali kaima Sam kuma dan bataso Saika kyaleta abu? Saikace ba likitaba.




***
"Ai kamata yai ace ahmad din kataso kuzo tare yanda za ai komai gabanshi dan gaskiya so nakeyi ayi hidimar akan lokaci.


Kasancewarshi mutun me tsananin biyayya mussaman ga mutun nasama dashi,Saiyafara magana ahankali.
"Yaya ai yafita wajan aiki indai ba kiranshi zanyiba yanzu yazo din?

"Eh ka kirashi mana ganinan zaune ai ina jira sonake ayi komai gaban idanunka Shima haka dan bansan wannan rashin kunyar tashi.





"*""* *""

Insha Allah bazata kuma samun damar da kuba Ahmad,Ahankalima zata daina bibiyar rayuwarku ,Kunsan jinnu irin wa innan wuyar sha'ani ne dasu Sabida suma musulmaine saidai masu mugunta,Sannan dole saika tsananta hakuri musamman tunda tagayamaka cewa zata dinga shiga tsakaninku har sai kun sami sabanin da zaku rabu ko? To kaikuma matakin da zaka d'auka shine duk abinda yataso daga zuciyarka ka danneshi ka hanashi tasiri Sannan Duk abinda matarka zataimaka kai hakuri,Dan itace haskenka ce Farincikinka ce nutsuwarkace,Karka yarda laifinta ya tunzuraka har kai wani abu kaji ko?

Ahankali yakuma d'aga kanshi.


"Yauwa Allah yashige mana gaba kadai dage da addua insha komai yazo k'arshe zaka sami nutsuwa da kwanciyar hankali kamar kowane magidanci,Kuma tsoron ma zata dainaji insha Allah.


garin habba yqbasu domin turarenta Sai wanda Dr. zai dinga sha.



Cikin mota.
nima na yarda Salim aysha haskece gareni ka duba kaga yanda abubuwa keta warwarewa duk sanadiyyar ta shiyasa nakejinta can k'aeshen zuciyata.


"Hakane Ahmad Allah ya k'ara warware komai to.


Ahankali ya zaro wayarshi daketa ringing dan d'azuma yaji kiran Amma ya kyale sai yanzu dayasami nutsuwa.


"Abba"

"To ganinan zuwa, Nabar asbt ne Amma ganinan zuwa kace tsohon gida Abba lafiya ko?

"To shikenan Sainazo.

"Wai Abba ke nemana yana gidansu Allah dai yasa bawata fitinar bace dan wallahi nagaji da jarabar mutanen nan Salim Sam basu kaunar Abba amma yaki ya gane balle yaja musu layi Amma insha Allah daga wannan lokacin komai zaizo k'arshe zan fito musu a kalar da basu taba ganina da itaba.


"Karma kai tunanin wai Abba be saniba Wallahi yana sane kawai dai yanada farar zuciyane Sabanin tasu Sannan kuma yasan 'yan uwanshine duk wuya nashi ne kuma babu yanda zaiyi dasu,Cewar Salim yana kallon Hanya.



**""**


Ahankali take Sauke numfashi gami da ajiyar amma kuma barci takeyi,Gaba dayanmu Saman kanta muke Har lokacin mama batabar fada ba"Kana tunanin wai tausayine ko gata kaimata dan kawai tana kuka shine ka barta ta kwana haka Alhalin kasan abinda kaimata? Sakarai duk ku kenan baku iya tattalin mace ba Amma saiku dinga fadin kun iya soyayya.


"Kiyi hakuri mama zan kiyaye insha Allah.

harararshi tai tare da ficewa.

Ajiyar zuciya na sauke yayinda shima ya sauke tashi,,Murmushi mukai atare kamin yadawo kusada zainab din ya zauna yana taba yanayin zafin jikinta.

fitar da yai niyya dole yafasata Sabida yanda yaga tana bukatar me kula da ita sosai.

niko ficewa nai nabiyo bayan mama sabida girkin rana.




***

Saida ya hade girar Sama data k'asa sannan ya k'arasa cikin gidan.

ba laifi matasan gidan daya tadda sungaisa dashi ba kamar da ba da idan zasu bangaji juna da daya daga cikinsuba babu wanda zai tankama wani,Kawai sabida tsabar hassada Allah ya d'agashi susuna nan zaune.




maman khadija.
12/10/20, 9:49 PM - Naffy Aliyu Umar: 69




"Jira kakeyi in gaisheka ne Amadu?

. Wani kuma bata fuska yai kamin ya nufi yayan mahaifin nashi ya mik'amishi hannu.

tsananin mamaki yasashi kasa d'ago nashi hannun Sai idanu daya zubamishi bakinshi na motsi.

Shi kanshi Abban mamaki ne ya kamashi.


Komawa yai can gefe ya zauna batare daya kalli wajan da Abban yakeba dan yasan saiyayi mishi magana koda ta idone akan abinda yayi.

"Ah lallai Aini Sam banyi tunanin iskancinka yakawo wannan matakin ba sai yanzu danagani da idona,To ka kyauta kuma hakan bazai hanani aiwatar da abinda nai niyyaba.

"Kanaji ko? To ummi ameerana uwar masu gida tace babu wanda takeso ta aura Sai kai Nikuma nace tasamu kamar yadda dama bata taba neman wani abu ta rasaba.Danhaka yanzu shawara dai ta rage naka danni nariga nagama magana.


Kallon cikin idanunshi yai kamin yai wani mugun murmushi"Ka gama magana amatsayinka na wa wajane?

"Idan ka manta in tunamaka da bakinka kace bakasan waye Mekudi ba balle 'ya'yanshi ko? To muma tuni muka cireka daga cikin dangin mahaifinmu,Kacemin maye kacemin meshan jini kacemin d'an fashi kace dukiyata da luwadice Niba mutumin arziki bane duk ahakanne zaka aurawa diyarka ni?
To bari ingayamaka gaskiya Wallahi wallahi wallahi koda ace banda mata bazan taba auren diyar d'aya daga cikinkuba koda zan mutu babu aure kuwa balle yanzu da nakeda mace guda d'aya tilo tamkar da dubu,Danhaka ku canza tunani daga kai zuwa sauran wallahi saidai yaranku su mutu dason aurena Amma wallahi ko sharar gidaba bazasu samuba balle.

waima wace kalar zuciyane daku dan Allah? yanzu nan nufinka duk abinda kaimin da mahaifina ka manta? Ka manta lokacinda yazo nan yana hawaye akan kabani auran daya daga cikin yaranka? Ka tuno abinda ka gayamishi lokacin? To komai yana nan akai na kuma cikin kwa kwalwata danhaka Babu abinda ya hadani dakai balle kai tunanin zakai iko dani,Shidai Abban da yake kallonku mutune kuma 'yan uwanshi har yanzu to gashi gaku Ammani wallahi bani da dangin mahaifima kuma nasan yayu nama hakan take garesu,Nabarku lafiya.


Wani irin shiru d'akin ya d'auka kamar babu wani me rai cikinshi kamin Abban ya mike shima Har cikin ranshi beji dadin abinda Ahmad din yaiba to Ammafa koshi bazai taba yarda Ahmad din ya auri wata yarinya cikin dangin suba.,Sabida shi kanshi beson tuno abinda 'yan uwanshi keyimai da iyalinshi.Sailace wands yake 'yan uba cikinsu.

Yai tunanin zai dakatar dashi Amma saiyaga har yabar harabar gidan beji wani kiraba, Ajiyar zuciya ya sauke lokacinda ya hangi motar ahmad din afake kenan be bar wajenba har yanzu.


Kwankwasa kofar yai tare da kanga idanunshi jikin gilas din.

Ahankali ya bude motar ya zubama Abban yai tunanin zai ganshi cikin damuwa shiyasa yakasa tafiya saidai ga mamakinshi Saiyaga Abban qalau dashi.


Shiga yai gefenshi ya zauna"Muje ka maidani gida tunda kagama cimana mutunci.



***


"Baby pls yaufa kwana biyar dan Allah ki kwantar da hankalinki bazan cutar dake ba kinji?

Kai ta kauda tare da cewa babu wani baby wallahi ku da kuntashi cin zalin mutun sai ace baby toni ban warkeba.


Jiyake kamar ya tausheta yaimata dole Amma yana tuna irin kashedin da maman taimishi.

"To kiyi hakuri kiji tausayina mana,Na yarda idan kinji wani abu Allah ki rufe abinki.

Dariya tasaki kamin tace ta amince.

tare sukai wankansu kamin ya lallabata da wayau da dibara ya hillaceta suka lula Duniyar raya sunna.



***

Tunda yafara shafar man jikinshi nake aikin kallonshi anatse yake komai,Ammadai Sam fuskarshi babu walwala tausayinshi nakeji yanzu dan sosai yake bukace da son kasancewa dani Amma kuma tsoron da nakeji yana hanashi kaiwa gareni gashi kullun abun gaba yake,Sainaga shirina da shan alwashin daya zo zanbashi aamma wani abun takaici daya fara tabani jikina zai fara kyarma ina neman sikewa wanda kan dole yake kyaleni.

Ganin yanda nazuba mishi ido yasashi sakarmin murmishi"Babyna inzo ne?

Boye kaina nai cikin bargo ina dariya.

turare kawai yashafa ya hawo gadon.

Bansan me yasaba Amma saina samu kaina dayimishi magana cikin kunnenshi"Nasan kayi hakuri da yawa tunda baka da wajan da zaka sauke buk'atarka dole sai gareni,Dan Allah yau kome zanyi kayi abunka kawai nasan dai bazan mutuba kaji?


...
Hakane bazaki mutuba baby Amma bansan damuwarki ai.


babu kalar rawa da tashin hankalin da banshiba lokacin,Amma ahaka yacigaba da biyan bukatarshi dan daga karshema dena tunawa da wani hali nake ciki yai,To dama ga uban gyaran danasha wajan mama.

tun ina gane abinda yakeyi har na daina ji da ganin komai.


Shi kanshi besan iyakar lokacinda ya d'aukaba dan so biyu yana Samin nutsuwa batare daya bariba.

Saida yagama hutunshi,Sannan ya debo ruwa ya yayyafamin kamin ya shigar dani jikinshi.

"Dr.Ruwa zansha"

Ahankali yatashi tare da jawo tawul ya d'aure k'ugunshi,Shi kanshi saida yasha ruwan Sosai Sannan ya tasheni yabani,Gaba daya nawani firgice kitsona daya fara tsifarshi d'azu ko rabi ba ai ba duk yagama tashi.

wata dariya naji yasaki wadda banyi zaton jintaba.

watakil ganin yanda nake kamar mahaukaciya yasashi dariya,Saidai cikin dariyar tashi naji yana fadin "Baby sumafa kikayi wallahi ko ranar farko baki sumaba tashi inga zaki iya!!!

Wata harara nasakar mishi tare da bare baki nakama kuka dama me neman kukan ne sai aka jefeshi da kashin awaki.


Rungumeni yai jikinshi yana murmushi"Yi hakuri dan Allah ba dake nakeba sannu yi hakuri.


Wani irin mugun tsaki mukaji Daga wajan taga,Aiko da gudu ya dilliko kaina duk muka zubama tagar ido muna hangen wata doguwar inuwa.

Nannadewa nai cikin kirjinshi yayinda shima yakuma rufeni kamar me boyeni.



"Baby inuwar mecece can wai?a

Cikin duhun na harareshi Dan tuni yakashe hasken dake cikin d'akin.

"Kaimana addua mana Amma ji kawani boye saikace ba namiji ba!!

kirjina ya matse da k'arfinshi har saida nai wani marayan ihu kamin yace"Dan ina namiji sai akace miki babu tsoro a zuciyata? To nima nan tsoron nakeji yarinya kumamafa nayi adduar wallahi.

Shiru mukai kowanne da tunanin da yakeyi,Yayinda bunu bunu zamu fiddo kawunanmu dan ganin ko Inuwar ta bar jikin window din.

"Baby bude idanunki muyi wanka ta wuce.

"Dan Allah kabarni inyi barci nifa sanyima nakeji nagaji zazzabi zanyi.

Dani yatashi jikinshi kan dole na bude idanuna nabishi toilet din.


Kwanciyata nai inajin jikina kamar ba nawaba.Yayinda shikuma ya kalli gabas yafara nafilfili,Nikam barcina nai.

Shima beyi tunanin yace Inyiba ganin yanda ya taramin gajiya.




***

"Babu abinda yafi k'arfin Allah shine ya haliccemu kuma shine ya jarabcemu da abinda yasan zamu iya d'auka,Danhaka zamu cigaba da rok'onshi sauki da sassauci har zuwa lokacinda zai amsa,Ayanzu banda matsalar Ahmad wallahi banda damuwar komai,Ina tausayawa yaron daga wannan sai wannan kinji yanzu kuma? Dama tunda naji kince wai mamanta ta gayamiki tacemata wai mafarki tayi nasan dama akwai wani lauje cikin nadi,Danhaka dole mu jajirce mu dage da addua har zuwa lokqcinda zamuga komai ya daidaita da izinin Allah,Kuma kinga bayanin da salim yai shima ya nuna matsalar daga Ahmad dinne har yanzu.

Kimmasan ko duk menene sanadiyyar wa innan abubuwan kuwa?

Hijab dinta ta gyara tana kallonshi Amma takasa magana.


"Ina tunanin kamar mune mukaja ma Ahmad duk wa'innan matsalolin,Domin mune Masu adduar Allah yabamu namiji magaji kota wani haline idan ma baki manta har cemin kikai kwana kike rokon Allah akan yabaki namiji,To ko ni inayin wannan Adduar Saigashi Allah yabamu Amma kuma ya kasance damuwa da tashin hankali garemu,Tabbas gara mu dinga neman zabin Allah akan dukkan abinda mukeso domin zai iya yiwuwa abinda mukeso ba alkhairi bane garemu shiyasa idan muka samu saiya wahalar damu,Amma idan mukabawa Allah zabi shine yasan daidai damu,Tun watannin baya nake tunanin nan mun roki Allah yabamu namiji yabamu gashi kuma ta bangarenshi mun gaza samun kwanciyar hankali,Shiyasa idan kaga Allah be baka abuba to hakika kila ba alkhairi bane gareka,Danhaka kitashi muci gaba da kai kukanmu ga Allah mun tuba mungane kuren mu dan wannan laifinmu ne, Ya shafeshi.

Share hawayenta tai"Tabbas sai yanzu nagane kuskurenmu Alhaji kuma insha Allah zamu gyara.

yana gaba tana bayanshi yayinda suka dukufa wajan kaima Allah kukansu domin sai yanzune suka fahimci kuskurensu akan rayuwar tilon d'ansu namiji.

Hakika abubuwa da yawa ba alkhairi bane garemu Amma saimu like aita rokon Allah,Shikuma idan yabamu sai ya hanamu jin dadin abun kodan mu hankalta,Saidai wa'inda ke hankaltuwa din basu da yawa.




** **

Cikin walwala da farinciki mukatashi musamman oga wanda murmushin dake fuskarshi yaki gushewa,Duk da natashi da d'an nauyin jiki Amma haka na gyara bangaren tas dayake yanadan kama min.


Dama tun farkon zuwan zainab maman tace ta d'auke mana Abincin safe ita zata dingayi duk ta yafe muji da dawainiyar mazajenmu.Zata barmu dana rana dana dare Amma nasafe ta yafe.


Yau sai wajan goma nasafe muka fita hannuna cikin nashi babu ruwanshi dawata kunya ko kawaici duk irin yanda naso kwace hannuna kin sakinshi yai Saida ya zaunar dani wajan da zamu karya Sannan yasakeni yana murmushi.

Akunyace na gaida abubakar wanda ke zaune yanacin abinci shima banga zainab ba wajan,Shiyasa bayan gaisuwar na d'ora da tambayar ina zainab fa?

"Yanzu tabar nan mama tai kiranta.


Tare muka gaido mama da abba sannan suka fice nikuma nakoma wajan mama wadda har lokacin takema zainab din fada,Saidai narasa gane akan mene Saida ga baya na fahimci Abubakar dinne yakawo k'ararta wai taki sakar mai jiki yai yanda yakeso.

kunyama hanani motsin kirki tai lokacinda naji zainab din na fadin"Wallahi mama yayi da zai kumane nace nagaji.

"Ke ar can dallah dan zai kuma sai me ? so kikeyi ya nema waje?
Karki bari yakuma kawomin k'ararki wallahi idan kikasaki jikinki ai ahankali zaki saba ko?


gyaramata d'akin mukai kamin mukoma falo, Mukaci gaba da hira hadda maman.




BAYAN WATA BIYAR.




haske writers asso.
12/10/20, 9:49 PM - Naffy Aliyu Umar: 70.




Kwance nake nai filo da damtsen hannunshi idanuna rufe Amma ba barci nakeba,Hannunshi na Saman kaina ahankali yake shafawa hade damin Susa"Baby narasa meke damunki kwana biyunnan Duk jikinki yai Sanyi ko akwai matsala ne?


"Nifa wallahi bansan abinda ke damunaba Amma gaskiya banda lafiya Kaga har bakina banjin dadinshi.


"Ok to ko asbt zamuje sai na ganki acan?

Da sauri na na girgiza mishi kai,Nidai a a babu inda zanje.


D'an jim yayi kamin yatashi da sauri ya d'aukomin hijab da zani dan wandone da k'aramar riga jikina.

Narkemai idanu nai Amma saiya kawar dakai yacigaba da samin hijab din"Muje babyna yanzu zamu dawo kuma zan siyamiki abun dadi ahanya.


Babu yanda na iya dole nabishi,Babban falon babu kowa,Dayake maraicene to dayake ma zainab bata zama sosai yanzu dan laulayi ya tasota duk da yake yanzu Akwai dan sauki da, ya wuce wata hudu ma cikin.


office dinshi ya budemin nashiga Sannan shikuma yafita be jimaba saigashi shida wata mata da fararen kaya jikinta daga gani dai nan take aiki.

Duk irin harararshi da nakeyi besa ya kyaleniba saida ya dibarmin jini Sannan yabata ita kuma ta fice.

Sumbatar goshina yai yana dariya,Baby kin san me?

Kallonshi nai da alamar a a.

"Kilamafa karatunki tsayawa zaiyi"

"Banganeba sabida me ? Menai maka kuma?

"Oh kwantar da hankalinki mana,Babu abinda yafaru Amma dai ina tunanin kamar Ah bari dai ta kawomin ingani tukunnah.


Muna nan zaune Saigata tazo bakinnan awashe"Is positive fa.

Amsar takar dar yai yana mata godiya.Bayan ya kwashi kudin aljihunshi yabata.


Rungumeni yai tare da rufeni da wata irin zazzafar sumba ta ko ina.

Rikeshi nai har Saida ya sassautamin dan kanshi kamin ince"Lafiya?


Sumbatar bakina yai"Baby cikine dake fa!!

Sulalewa nai daga jikinshi na dora hannuwa na aka tare da bude bakina da niyyar sakamishi ihu,kamar yasani kuwa yai gaggawar.rufemin baki "Ke bansan hauka lafiyanki?


K'afata nacigaba da dirzawa ina kukan gaske,Wallahi banso ni ba yanzuba kai har ka manta irin wahalar danasha wancan karan shine kake murna to wallahi banso.

Rungumeni yai yana dariya"Bazakisha wahalaba baby babu abinda zai faru wannan ba irin wancan bane pls karki batamin farinciki na baby wannan shine burina kullin adduar nemanshi ke hanani barci.

Tuttureshi nakeyi yana kuma matseni jikinshi yayinda yaketa sauke ajiyar zuciya me hade da farinciki da godiya ga Allah a bayyane.

"Nagode Aysha Allah yaimiki Albarka ubangiji Allah yasakamiki da mafificin Alkhairi ya rabaki dashi lafiya,Sorry baby Kinji?

Tun inayin kukan da sauti har na koma yinshi saidai hawaye da gaske nake tuno wahalar danasha wancan karon yasani ko sha'awar cikin banyi Balle yanda naga zainab nata amaye Amaye itama dan har yanzu idan taci abinda bemataba saitayi amanshi.

Tureshi nai daga jikina ina share hawaye,Haba koda naji shiyasa cikin kwanakinnan kullun banjin dadin jikina gawata masifar sha'awarshi danakeji Saidai ban yarda yagane,Amma daya nema nakebashi hadin kai duk da inajin nagaji wani lokacin,Domin tunda muka dage magani da Addua shikenan,Allah ya temakemu inuwa bata kuma waiwayarmu wajan wata biyu kenan domin tabbas babu abinda zai gagari Allah saidai idan mutun gajen hakuri yayi yace bega daidai ba.


Zubamin ido yayi ganin nakoma gefe na takure ni wallahi ma Sainaji zazzabi na neman sakkomin tsabar yanda maganar ta bugeni,Sam bankawo ma raina hakan ba.

"Zonan ki kwanta inyi miki scaining inga yakai sati nawa?

makale kafada nai ina murzar ido.


d'aukata yai gaba daya ya d'ora saman d'an gadon dake d'akin"Ni bansan lokacin da zaki girma ki daina wannan rigimar ba wallahi koda yake dakin fara aje iyali zaki fara rage wasu abubuwan nikuma inta kallonki yaranki na maki dariya.

make mishi hannu nai wanda keta latsar kirjina amemakon hoton da yai niyyar yi.

Saida ya mula dan kanshi Sannan ya dubani.

gabadaya 7weeks bema k'arasa ba.


Rungumeni yai tsam jikinshi yana sumbatata"Nagode baby.




**
Har muka kawo gida bansaki fuskataba danni gani nake kamar shikenan wahala ta ganni kuma.

Saidai

Please Login or Register in order to submit comment