Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Shiru sukai tsawon lokaci kamin wanda yake gefen hagu yafara maganar me suna muntari"To tunda abun hakane yaya kawai kabashi auren saimuga zata mutun kokuwa sannan kaga zata dinga kawomana dukiyarshi muna zaune.


"Mitsw wawaye kawai kawai sai ind'auki diyata inkai inda zata mutu bata shiryaba ko? To kuma daina wannan maganar wallahi cikinku babu wanda beda diya zaku iya bashi Amma bandani.

Mesunan kamal dinne ya yamutse fuska kamin ya mike tsaye" Nidai na gayamuku kadda wanda yakuma sakani cikin maganar data shafi yaya wallahi balle Ahmad abarsu da masifar data damesu ni saima yanzu nake mamakin wane irin rashin tunanine ya samemu na gallazawa d'an uwanmu wannan shirmene kuma nidai nagamashi.

Duk da kallo sukabishi bayan barinshi d'akin.



***

Tana rungume jikinshi yana shafarta idanunshi alumshe yanajin yanda jikinta yake da wani irin taushi har mamaki yakeyi yanda take canzawa akai akai" Fatima ya akai ne?

"Babu komai amma nidai banso katai ka barni kaga yanzu kullun firgita nakeyi wallahi tsoro nakeji.

" To Fatima ya zanyi dake kinga bazai yiwu intai da keba iyakata abuja Aiki kawai zanyima wani mutun indawo bazan wuce two days ba ki kwantar da hankalinki inkuma zaki koma wajan maka kamin na dawo to?


"Kuma shigewa jikinshi tai kamin tace eh na yadda sai inkoma can din Amma bazan iya kwana nan gidan na kadaiba.




Bayan kwanaki biyu.
Takardu yake hadewa yana shiryasu cikin jakarshi so yakeyi daya kuma duba mutumin ya wuce gida Dan hankalinshi naga matarshi.

Jin ana kwankwasa kofar yasashi furta yes',Da sallama yashigo kamin Dr.din ya mike yabashi hannu suka gaisa.
" Bashir kwana biyu ka boye?

Dariya bashir din yayi kamin yace wallahi kuwa kaidai bari kawai aikine ke hanamu sukuni Yanzuma zuwa nai iyimaka tsiya wai najib ke cemin kai aure!!

Ajiye wayar hannunshi yai dayagama turama fatiman sakon lallashi Dan yanzu tagama mitar har yanzu be tasoba,Kaga wallahi matsala aka samu kagadai yanda auran nawa yake kasancewa to shiyasa wannan ban gayawa kowama musamman wa inda ke nesa Ammadai ayi hakuri idan ta haihu sai kowa yaje barka amadadin d'aurin auren.


Duk dariya suka saki ataren sannan yaimishi Allah sanya alkhairi har lokacin yana mamaki balle dayaji bikin yama wace watanni biyu.

Bashir shima abokin Dr.ne duk tare sukai karatu saidai dayake wajan aikin ba d'ayaba shiyasa wani lokacin sai haduwarsu tai wahala.



***
"Aysha kina kina?

" Ya fati inajinki yaushe da yaushe kikai mafarkin?

Inajin lokacinda ta sauke numfashi kamin tace"Yanzu kwana biyunnan ne banyi sabida benan Amma kullun sainayi indai zai kwanta dani narasa kalar tunanin da zanyi kuma kinga yanzu duk wanda nagayamawa sai hankalinshi yatashi shiyasa duk nashiga damuwa.

"To ya fati ki kwantar da hankalinki kuma ki dage da addua idan har ajalinki gidan Dr.yake to babu makawa sai hakan ya kasance duk yanda mukakai ga rashin so kuwa kema kinsani haka kuma idan zakuyi doguwar rayuwa tare to babu makawa duk wuya zaku kasance tare kamar yadda Abba yace wataran sai labari to hakanne kadda ki yadda wani tunani ya tsaya miki balle ya tauye imaninki kedai kawai ki dage da addua.


" Hakane k'anwata kuma nagode da kwarin guiwar da kikebani koda yaushe Saidai ni ba mutuwa nake tunaniba wallahi ina tausayin Dr.ina tunanin halin da zai kuma shiga kuma da wuya yakuma samun wanda zaibashi aure shikuma gashi mabukacin auren.


"Hummm yaya kenan to Ki cire wannan tunanin cikin ranki Allah Wanda ya halicceshi kuma ya halicceki yafiki jin tausayinshi haka kuma shiyasan yanda zai kasance,Kuma kamar yadda Abba yabashi auranki to haka zaikuma bashi wanda zai bashi diyarshi ya aura koda yasan zata mutun pls ki kauda wa innan tunanikan aranki zasu iya hanaki sukuni.

" shikenan nagode idan kinji gidan yaya uwani kice nace mata jiya inata kiran wayarta batayi wai ta kirani,Ki gaishemin dasu mama yanzu muka gama waya anjima kadan zai dawo sai anjima.



Rasa inda zan tsoma raina naji sabida tashin hankali, Dan duk maganar da naimata to wallahi k'arfin hali nayi wayyo Allah kadda ka kashemin yayata mafi soyuwa daga cikin yayuna.,Innalillahi wa inna ilaiharraji'un meke faruwane ni kaina kwana biyu mafarkinta nakeyi cikin kyakkyawar shiga nishadi da farinciki Amma narasa me hakan ke nufi.






Haske writers association.
12/10/20, 7:51 AM - Naffy Aliyu Umar: 🇯 🇦 🇷 🇺 🇲 🇦 .
17
Na maman khadija.





Cikin kwana biyu na yamutse Dan ban tunanin ko ita takaini shiga tashin hankali.

"Wai aysha meke damunki ne duk kika yamutse cikin kwanakinnan kodai duk jarabawarce? Ammadai asanin da naimiki dacan nasan cewa baki barin damuwa cikin ranki balle harta bayyana danhaka gayamin meya faru?

Mama ni kaina bansan abinda ke damunaba wallahi ammadai inajina wata kala kamar dai bani cikin walwala balle farinciki.

" ashsha Allah ya kyauta Ammadai in hakane to saiki dage da Addua Allah yasa koma menene ya zama alkhairi tsakani,Tashi ki shirya ga dalhat nan zuwa zai wuce dake yayarki na asbt inaga haihuwa zatayi.

Da murna na mike ina dariya wayyo dadi nakusa samu wasu yaran kennan Allah ya rabasu lafiya bari in shirya.



Ya dalha mijin ya maryam ne daga ita sai ya ya Fatima saini.

Dayake dama tsohon cikine da ita to d'azu ya kira mama wai ya kaita asbt yana tunanin haihuwace.

Kamar kullun haka yauma nai shirina kusan akofar gida yasameni shiyasa beshigo cikin gidanba muka wuce.

"Wancan satin naita kiranki kizo ki taya maryam zama Amma kika kiya ko?

Dariya nayi tare da sadda kaina k'asa lallai ma kaji yaya ni shikenan kun maidani sarkin yawo bani nan bani nan shiyasa naki zuwa kumama banace ka kawo min su sadiq ba idan sune suka dameta Amma kace wai a a.

Hararata yayi kamin yasha kwanar shiga asbt" To naji sarkin hujja yanzu idan ta haihun ai dole kizo ki zauna ko?

Murmushi kawai nayi Amma nasan dama ai tana haihuwa zan tare can Dan haka Allah yayini da son yara.



***


"Tashi ki shiryani Fatima zan makara fa!!
Yamutse fuska tayi cikin shagwaba tace Dan Allah ka shirya Dr.wallahi banjin dadin jikina.

Dariya yasaki yana matsarta cikin jikinshi" Yo dama ya za ai kiji dadin jikinki tunda kin d'auki magana daga zuwanki?

Kallon mamaki taimishi kamin tace banganeba?


Eh nasan yanzu haka akwai ciki jikinki waima ke baki tunawa da tunda kikazo gidannan bakiyi fashin Salla ba gashi munshiga wata na uku kinga kenan baby yafara kwari ma.

Dafe kanta tayi da sauri tana boyewa cikin jikinshi Dan sai lokacin tunanin hakan ya dawo mata.

Dariya yaita mata kamin yace yo nidai atashi atayani shiri kokuma insa mutun barcin dole yanzu.


Da sauri ta mike tana harararshi dantasan kadan daga aikinshi shine yakuma tausheta Dan bawai wahalar hakan yake gani ba.

Sai bayan yabar gidan sannan ta zauna tanata murna cike take da farinciki.


**""**

Munjima zaune muna sauraren abinda zamuji,Sannan saiga Dr.din tafito.
Kiranshi office dinta tai tabashi magungunan da zai siyo Saigashi ya fito.

"Aysha ashema ba hauhuwar bace Ammadai duk da haka sunce zata huta zuwa hudu na yamma saimu koma gida.

Ajiyar zuciya na sauke tare da mata fatan sauka lafiya tunda cikin yariga ya shiga Tara dole lokacin ya kusa,Imma ba yanzu ba.

Zama nai har ya dawo siyen maganin sannan mukashiga wajanta,Barci takeyi hankalinta kwance,Wannan itace haihuwa ta uku da zatai kuma yaranta duk mazane duk da dai ba aga wannan ba amma shima da akaimata scanning abinda sukace kenan.

" Bari inje gida indawo aysha idan tatashi lokacin Sai mu koma gida zanbiya ta gida in d'auko miki kaya Dan Allah ki zauna damu zuwa lokacinda zata haihu nasan Abba bazai hanaba bansan barinta ita kadai wallahi kindaisan yanda take haihuwa awahale kinji?

To ai yaya islamiyya fa tunda kaga bamu fara neco ba.

"Zan dinga kaiki Amma Dan Allah ki zauna damu OK?

To saika dawo .



Zaune take ita kadai tana gyaran farcenta kawai saitaji wani dummm kamar dai irin an tsaya akan ka din nan shiyasa saita d'ago kanta tare da kallon inuwar dake tsaye saman kanta saidai koda ta duba babu wani Abu cikin harabar wajan saidai ihuwar Wanda bata isa tace ta mececeba sabida yanda inuwar take babu fasali balle ka misalta Amma tabbas inuwar wani Abu ce.


Tsigar jikinta ce tatashi gaba daya kamin taji sarawar kai,Matsawa tayi daga gaban inuwar ta canza waje,Saidai ga mamakinta itama inuwar kuma matsowa tai takuma shigewa jikinta.
Miyau ta hadiye kwatt kamin ta mike tsam tana karanta ayatul kursiyyu tabar wajan.
Wani dogon tsaki taji ya dira cikin kunnenta Dan haka da kusan gudu ta idasa shigewa cikin falon,Falaki da nas da ayatul kursiyyu take karantawa abayyane kamin ta jawo hijab gamida makullin gidan ko sisi bata d'aukaba sai wayarta.
Tana rufe gidan ta tari me adaidaita sai gidansu Dr. Din.

Allah yasa saitaci karo da usman Dan haka saitace yabashi kudin itakuma tashige.


Zazzafan zazzabine ya rufeta Dan ta bala'in tsorota dauriya kawai tayi,Cikin kujera tashige tare da nannade jikinta tana sauke numfashi.

" Ah innalillahi subhanillahi Fatima daga ina haka lafiya ko? Cewar maman cikin damuwa.

"Hawayen idanunta ta share kamin tace mama zazzabi nakeji kuma benan.


" Subhanillahi sannu ina zuwa,Maman tace tare da wucewa da sauri ta jawo wayanta, Saidai taimishi kira uku ganin be d'aukaba yasata tunanin aiki yake Kobe kusa.

Tea ta hadomata me kauri tabata tasha,Sannan ta bata magani saitace ta kwanta ta huta kamin Ahmad din ya dawo.



**
Data na bude nafara hira sainaga ya fatin taimin magana minti ashirin da suka wuce danhaka saina kira wayarta lokacin.
Muryarta ashake alamun batajin dadi ta furta hello aysha ya kk?

Lafiya lau ya Fatima naga kina nemana ya jikin naki? Dayake kwana biyu tanacemin batajin dadin jikinta.

"Da sauki aysha Ashe cikine dani shiyasa banda lafiya Ammafa akwai matsala.

Maida murnar datazomin nayi kamin ince bangane akwai matsalaba meya faru?

" Ina gidansu yanzu Amma ki bude datar ki saimuyi magana ta WhatsApp kinji.


Ganinta online yasa na tsaya sauraren typing din danagana tanayi.

"Aysha ina cikin damuwa yau tsoro aka bani gidan Dr. Shine nataho gidansu shikuma benan wallahi aljanune cikin gidan.


Dariya nayi azahiri kamin in fara rubutamata,Lallai yaya fati da bakinki kike fadin saikika tafi memakon ki tsaya ku goge raini da kowane shege ko shigeyace shine saiki gudu? Lallai za ai miki raini bana wasaba Wallahi keda gidanki!!!

" uhumm bazaki ganeba banza ina miki bayani kina d'auka wasa inuwace fa taita bina gidan uwabanwa zan ganta harna kara da ita? Kemeyasa baki da hankaline?

Turo bakina gaba nai kamin ince to Allah yabaki hakuri Amma wallahi inda nice babu inda zani sainaga k'aryar iskanci yo nida gidana ai babu wani shege dama karatu kika kunna kikai zamanki kowane shaidanine saiya kama gabanshi.

Alamun harara ta turomin,Amma batai maganaba.

Murmushi nasaki nasan tanacan tacika,Kamin na rubutamata ina nan asbt da yaya maryam Amma sunce ba haihuwa bace Dan haka anjima kadan zamu koma gida.


Murmushi ta turomin kamin tace Allah ya rabasu lafiya nakosa ta haihu wallahi kodan inzo gida Amma yanzu danaimishi maganar zuwa gida saiyace wai me akeyi,Sai anjima zamuyi waya kaina ke ciwo.


Tunani nafara bayan na rufe data na,Shin kodai Dr.ne keda aljanu suke mai wannan ta'asar kokuwadai sihiri ne? Anya ba matsafi bane Dr.?




Haske writer's association.
12/10/20, 7:51 AM - Naffy Aliyu Umar: 🇯 🇦 🇷 🇺 🇲 🇦 .
18
Na maman khadija.




Kayanmu na hade sabida drip din da aka samata ya k'are muka wuce gidan ta dan hadda kayana ya kwaso saikace wadda zatai musu shekara.

Bansha wahalar gyaran gidan ba dan inaga duk cikin d'akinmu babu wanda yakai yaya maryam tsafta dan idan tanayin yawama to tata tayi shiyasa da wuya kashiga gidanta kace ma ba amarya bace kullun bata gajiya da gyara yaranta dakuma gidanta kai shi kanshi mijinta idan taga abinda bemataba ajikinshi gyarashi takeyi.

Yaran yaje ya d'auko daga gidansu saigashi hadda mahaifiyarshi tazo dubata dayake matar ta manyanta sosai dan shine auta tana fama da ciwon k'afafu.

Gaisheta nai sannan ta wuce cikin bedroom din yaya maryam din dan dubata nikuma na wuce da yaran d'akinsu dan canza musu kaya duk da umman tace anyimusu wanka.


Mama ta kirani akan suna nan wutowa ita da inna hassatu yayarta dan sunje asbtn aka an sallamemu,Nikuma na manta ban gayamataba.



**
"Tashi muje gida Fatima nagaji wallahi ina buk'atar hutu,Cewar Dr.ganin tai mirsisi abinta bata niyyar binshi.

Cikin shagwaba tace waikai Banace kaje ni nan zaunaba?

Hannuwanta ya riko cikin nashi yana tunanin ta inda zai fara Sam beyi tunanin da gaske takeba datace ita bazata komaba,Haba Fatima ya zakimin haka dan Allah mukoma gida.

Marairaicewa tai kamar tasa kuka Shikuma saiya kauda kanshi dan Bejin zai iya barinta, Shi bemaso maman tafito ta fahimci me ake ciki.

" kinga taso kiji babyna,Tarairayota jikinshi yayi tare da sumbatar lebenta yauwa d'auko hijab dinki anjima idan anyi sallar isha'i saina maidoki idan nan kikeso Amma kadda ki hanani jin dumin jikinki yanzu kinji pls Fatima.

Ranta besoba Haka ta mike tana tutturo baki dan Sam batai niyyar komawa gidan ba.

"Ah Fatima kinfasa kwanan kenan? Cewar maman tana kallon Dr.Wanda ya kauda kanshi.

" Kai bansan shakiyanci ina magana kana kallon kofa Kaine ka hanata kwanan ko?

Shagwabe fuska yayi kamin yace Mama ni babu ruwana kumamafa anjima zamu dawo dan Allah kibari mutafi.

"To Allah ya tsare saikun dawo.


Hannunta ya rike yana murzawa ahankali kamin yace haba Fatima dan kinga ina wahala da kewarki shiyasa kikeso saikin wahalar dani ko? Nasan babu wani Abu cikin gidannan inagadai kadaicine yaimiki yawa shiyasa kikejin tsoro.

Itadai bata tankaba har suka isa gidan yafito ya bude sannan suka shiga,Duk da haka cikin ranshi akwai tsoro gamida fargaba sabida yanda yaga babu walwala atare da ita Sannan bata taba yimishi hakaba.


Be tsaya jiran tafiyartaba ya d'auketa saikuma sukafara dariya.



***

Juyi kawai nake kan gado Sabida tsabar yanda na jigata Sam mafarkin bame dadi bane.

" Aysha ke Aysha"
Azabure natashi ina zare ido yayinda wata irin zufa tacigaba da karyomin innalillahi nake nanatawa gami da salati kamin inji idanuna suncika da wata irin kwalla.

"Lafiya kk kuwa inata tashinki kiyi sallah yau kin makara ko abin be d'aukeba?

Ina mikewa naji biyowarshi jikin cinyoyina kenan dawowa yayi dan jiya har Sallar isha'i nayi,Toilet na wuce dan gyaro jikina babu maganar sallah Amma anya ba mafarkin danayi yasashi dawowaba?



Komawa nai na kwanta ina addua dan sosai jikina ya mutu harwani ciwon kai naji yana nema ya lullubeni, sadiq naima shirin makaranta da misalin bakwai da kwata nasafe da kaina nabashi abin kari tunda yaya maryam din har yanzu ta kanta takeyi musamman ma yau naga tatashi bata da lafiya gaskiya.

Abun haushi wai,Tsawon lokaci ina jiran fitowar yayan ya mika sadiq din makaranta Amma shiru dole saidai nafice dashi tunda babu nisa sosai kuma na rikema Abbas hannu danshi ba asakashi makarantarba.

Saida naga yashiga ajinsu Sannan na juyo ina mamakin meya zaunar da ita d'akin tunda shima nasan aiki zashi.

Rufe idanun Abbas nayi ina dariya,Tsaye suke afalo yana rungume da ita yana aikin lasar bakinta saikace tsohon maye,Ni wannan Abu yanaban mamaki waifa damma k'aton cikinta ya tokareshi.

Sakinta yai yana share bakinta da yatsanshi kamin yace Zan wuce zamuyi waya anjima nagode sosai Amma duk abinda kikaji ki gayamin kinji ko?


Da kyar ta zauna bayan barinshi gidan,Gefenta na zauna ina kallonta"Wai yaya maryam kina fama da kanki Amma kin like jifa abinda kukeyi!!


Hararata tai kamin tace bansan shirme kinji ko idan ban kyautatamishiba wayake da ita wacce zataimishi anya zaki iya sauke hakkokin aure kuwa?

Turo bakina nai gaba ina kauda kaina,Cikin kunkunai nace ni wallahi bazai yadda namiji ya dingamin hakaba Saikace bansan ciwon jikina ba.

Kallo tabini dashi tare da girgiza kai tana jin haukar da nakeyi acewarta.



"*"*"

Saida yasami nutsuwa sosai Sannan ya sararamata ya rungumeta yana shafar bayanta alamun lallashi yanajin yanda take sauke numfashi akai akai.

Cikin kirjinshi ya kuma shigar da ita kamin yace"Kidaina jin tsoro Fatima nan gidankine babu Wanda ya isa ya hanaki walwala cikinshi danhaka ki dage da addua kinji insha Allah komai zai wuce yazama labari OK?

Itadai jinshi kawai take Amma batajin dadin jikinta kwanakinnan.

"Tashi muje muyi wanka saikisha magani naji zazzabi jikinki dan Allah ki kwantar da hankalinki bansan damuwarki kinji ko?

Saida ya temaketa Sannan ta mike dan sosai jikinta yasaki tsabar murzar datasha duk yai gaba da dan kuzarinta.



Bayan kwana hudu.

Kwance nake ina barci Amma kuma sama sama nakejin nishi kamar ina mafarki,Da kyar nasamu na yakice barcin dake kaina na bude idanuna saidai d'akin ni kadaice Amma kuma inajin nishin daga toilet saima lokacin naji sautin yaya maryam na kwalamin kira.

Wata irin hantsalowa nayi har ina bige Abbas dake gefena yana barci.

Durkushe take akan guyawunta tana salati.

Wata rawa jikina ya d'auka kamin infita da gudu na jawo wayata dama dazai fita yasamin kati sabida lalura koda wani abu zai faru irin haka.

Da saurinshi ya d'aga kamin ma inyi magana naji ya furta ganinan zuwa.

Yana tafe yana mita cikin ranshi dan dama tun asuba tacemishi taga alamun haihuwar Amma tsabar gaddama ta ki yadda ya kaita asbt.


Duk wani abun buk'ata nagama hadashi kamin ma yashigo,Saida ya kaita cikin mota Sannan ya dawo ya d'auki Abbas nikuma na kwashi kayan.

Koda mukaje haihuwar tariga tazo shiyasa cikin babu me motsin kirki saida wata ta leko take gayamana cewa ta haihu lafiya amma ana gyarasu yanzu.

Hamdala mukai kamin ya kalleni bakinshi har keya"Aysha zauna ki huta Allah ya nufa tasauka lafiya bari na kikkira.
Zama nai gefen Abbas inajin yanda guiwoyina duk sukai sanyi Saidai cikin zuciyata hamdala nakeyi da fatan Allah ya raya itakuma Allah yabata lafiya.

Atsaye yaketa kira yana fadin haihuwar batare dayasan abinda ta haifaba danshima bawai sanin yayiba.



Zuwa dare muka koma gida da k'aton baby jajir dashi tazama uwar maza itakam,Saidai har dinki akai mata dan yaron girmanshi ya kusa wuce misali.

"Ya fati albishirinki?

"Goro fari tar,Tai maganar tana dariya.

" hahhhhha to wallahi ki tahomin da goron albishr dina ina binki bashi yaya maryam ta haihu dazu baby boy ki bude data na turamiki hotonshi.


Ihu ta buga da tsalle lokaci guda.
Da gudu ya fito daga bayin jikinshi duk kumfa yana kokarin d'aure tawul din dake Neman sancewa.

Turus yaja yai tsaye ganin yanda take tikar rawa.
Da gudunta ta idasa jikinshi ta rungumeshi tare da mannamishi kiss kirjinshi kamin takuma juyawa tana wata girgiza gami da murza mazaunanta.

Murmushi yake saki kamin ya nufeta ya rungume dan sosai ta motsamishi da sha'awarta,Riketa yai sukacigaba da jujjuyawa cikin d'akin Saikace wasu turawa beso ya katsemata wannan farincikin shiyasa yake tayata.

Kwace jikinta tai ta jawo wayarta ta bude data,Saiga hotunan baby har kala biyu.

Makalkalshi tai tana sakin ihu balle dataga babyn rusheshe dashi"Wayyo Allah dadi yaya mero ta haihu kalli babyn kaga,Wayyo sai zuwa gida zan bar wani yaimin gadin gida.

Dariya yayi Ashe murnar da biyu ake yinta,Janta yayi cikin bayin ya kwalemata kayan jikinta dansuyi wankan tare.





Haske writer's Association.
12/10/20, 7:51 AM - Naffy Aliyu Umar: 🇯 🇦 🇷 🇺 🇲 🇦 .
19
Na maman khadija.





Cikin kwana biyu nazama busy tsabar yanda aiki kemin yawa damma akwai yayuna,Kullun karbar 'yan barka mukeyi daga danginmu dakuma nashi.

Hafiz ya kirani yaimana barka,Kuma gaskiya naji dadi lokacin dan da ina tunanin tsabar girman kanshi bazata bari ya kirani ba domin ya kwana biyu bamuyi wayaba saidai kullun massage dinshi ke fara shigowa.

Yaya dalha yaimin dinkuna har kala biyu na suna dan yau kwana hudu kenan har mun fara shirye shiryen yanda sunan zai kasance.


***

Idanunta sunyi ja sosai sai ajiyar zuciya take saukewa, Shikuma har lokacin yana aikin jijjigarta banda hauka irin nata yaushe zaibarta ta tafi gida tun yau kwana hudu da haihuwa ya tabbata saita kusa yin sati idan yai wasa.
"Nace kiyi hakuri Fatima insha Allah jibi da kaina zan kaiki kinji

Please Login or Register in order to submit comment