Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

haka zata tashi da wannan ciwon jikin fadan da kukayi.

Tabbas idan wadda aysha ta kashe cikin family dinmu take to na tabbata daga yau zuwa gobe zamuji labari.

"Kai Innalillahi wa inna ilaihirraji'un,Oh kaji abu saikace cikin labarin hikaya?
To Allah ya kyauta insha Allah zamu tsananta addua Allah zai warware komai,Lallai aysha JARUMA ce kuma fitilar Ahmad tunda gashi Sanadiyyar aurenta abubuwa nata bayyana.


" Hakane saimu tayasu da addua Allah ubangiji yasa k'arshen damuwarmu kenan,Dan d'azu yaya Audi hadda yimin habaici wai Ashe surukata nakan hanya? Wallahi abubuwan da sukemin yana damuna dandai kawai bani da yanda zanyi da sune.


"Haba alhaji ka kwantar da hankalinka inda sabo ai munsaba da halinsu dan Allah ka daina sa damuwarsu cikin ranka,Balle yanzu da bawata lafiyar kirkine dakai ba koma menene ai Allah yana gani kuma shine zaimana magani.

Kiran wayarta yasata yin shiru tana kallon lambar wayar.

" Assalamu alaikum,innarsu halima anyini lafiya?

"Lafiya lau,Alhamdulillah naga lambar inna gambo lafiya ko?

" Gaskiya ba lafiyaba,Dan saidai aka balle gidanta yau Allah yaimata rasuwa bakuma mutuwarce damuwaba a a wani irin baki k'irin da gawar tata yayine yatashi hankalin mutane dan har yanzu ba ai mata wankaba balle agyarata ai mata abinda yadace.


"Innalillahi wa inna ilaihirraji'un, Nabani,Tuni ta yarda wayar tana sakin kuka,Innalillahi,Innalillahi,Innalillahi wa inna ilaihirraji'un meyaja ma inna haka meyai mata zafi har haka lahaula wala kuwwata illa billah.

Tana kuka tanayima Abban bayani wanda shima nan take hankalinshi yai mugun tashi.

Sam basu zaci hakanba basu kawo hakan aransuba,Musamman maman wanda kullun take ganin ana zargin innan tasune kawai sabida iskancin mutane,Gara Abba wanda zai iya yadda Sabida yanda mutane da yawa suke magana akanta.


Shiru falon yai sai sheshshekar kukan maman dayagama karade falon.

" Kinga ki daina wannan kukan ki tashi muje mu wuce aga yanda za ai da gawarta.

Wani kallo taimishi me kama da harara kamin ta share kwallar idanunta"Kasan Allah? Babu inda zani saidai ta rube cikin d'akin nata,Ko wannan kukan dakaga inayi wallahi kukan bakin cikin abinda taima Ahmad ke damuna Amma bawai na mutuwartaba danhaka babu inda zani indai ba umarni zaka bani ba.

Fuuuu ta shige kitchen taci gaba da girkinta Amma har lokacin batabar sharar kwallah ba jitake kamar ta hadiye zuciya ta mutu tukunna ko zata ji saukin d'acin da zuciyarta keyi mata.


Da kanshi yasa wayarshi ya kira babbar diyarshi halima yace ta gayama sauran 'yan uwanta idan akwai sarari kuma mazajensu sun bari to duk yanason ganinsu agida kamin la'asar.



**

Tun yana tunani da sake sake har shima barcin yai awon gaba dashi dan dama barcinne cikin idanunshi.

Amma ahakan ko numfashi me k'arfi na sauke saiya jijjigani,Kunsan idan tausayi ya had'u da soyayya to abun yakan ninka yanda duk aka zata.






Haske writer's association.
12/10/20, 2:49 PM - Naffy Aliyu Umar: 52




Lokacinda la'asar tai gaba d'aya sungama hallara kuma abban na dawowa masallaci yaimusu bayanin duk abinda ke faruwa tare da d'orawa da fad'in "Bekamata ace ba za a danhaka ko wacce ta tambayi me gidanta aje aimata addua karku manta kowane bawa da kalar jarabtar da Allah ke mishi,Ahmad jarabawowinshi duk masu nauyi ne kuma manayimishi adduar Allah yabashi ikon cinyesu to kuma me yai saura? Ai ko gano mutun kai yana cutar dakai to ka nunamishi kasan duk abinda yake aikatawa amma kadda kai yunkurin d'aukar wani mataki barshi da Allah kana zaune saikaga sakayya tazo wanda Allah zai iya yimishi abinda kai bazaka iyaba,Dan haka inaba mai umartar ku da Lallai ku kintsa insha Allah kamin magriba mundawo,Ke Hannah jeki lek'o k'aninki lafiya kuwa ko masallaci be fitaba Sannan basu nemi abinciba.




Kasan cewar umarni ne Abban yabada Shiyasa kowa ya daure Ammafa babu wanda ranshi yaso Cikinsu balle mama da har lokacin take hawayenta.


Abban da kanshi ya kira 'yan uwan maman duk ya gayamusu rasuwar shiyasa nan da nan kowa yaji.



Tajima tsaye tana kwankwasawa taji shiru shinefa hankalinta yatashi,ta turo k'ofar ta shiga kai tsaye ta wuce bedroom din bakinta da Sallama.


Zaune yake har lokacin amma ya jingina da fuskar gadon barcinshi yake sosai yayida nake kwance akan kafarshi barci muke sosai irin wanda dama ya dameka dinnan.

Share kwallar idanunta tai sabida tausayin k'anin nata,Wai Ahmad din da yake d'an gayu meji da kyau da kwalliya shine ya fige haka cikin kwanakinnan? Tunda ita duka yaushene bata ganshiba.

Duk ya fad'a sai wani dogon hanci afuskar.

Matsawa tai jikin gadon tafara shafaar kanshi tana kiran sunanshi,Ahankali ya bude idanunshi yana kallon inda take tsaye.
"Ah aunty sannu da zuwa.

"Yauwa Ahmad yame jiki?

" Alhamdulillah taji Sauki sosai barci tasamu Ashe nima ya kwasheni ban saniba,Nagaji ne aunty abubuwa sunyimin yawa wallahi banso wani abu ya sameta ita ka'adaice farincikina aunty.


Hannunshi ta dumtse cikin nata"Karka damu Ahmad insha Allah zaka rayu da Aysha komai yazo k'arshe,Aysha tayi jaruntar kashe abinda abinda ke kawomata hari kuma ba kowa bace face baba gambo kakarmu kenan yanzu haka shirin tafiya gaisuwa mukeyi Abba yace inzo in tasheka ko Sallah bakuyiba.


Jiyai kamar beji daidaiba tsabar yanda maganar ta dokeshi.

Sama sama taimishi bayanin duk abinda abban ya gayamusu sannan ta d'ora da fad'in "Katashi ku shirya kuma ai yakamata taci abinci Itama tun safe kunata barci.

" tsaya aunty wai nufinki bacin duk abinda ya faru haddani za aje gaisuwarta?


"Eh mana haka Abba yace

Katashi kuyi wanka yanzu zan kawomuku abinci.


Fuskata ya zubama ido,Yana kallon yanda fuskar takuma wani haske gawani dogon hanci girar nan me tsayi da bak'i sudul sai shining take,dai dai kan k'aramin bakina ya tsaida ganinshi,Besan ya fara tsotsarshi ba Saida yaji ina k'okarin tureshi.

Murmushi ya sakarmin kamin ya sumbaci goshina yana mike gabobin jikinshi wa inda yakeji kamar rirrikewa sukayi sabida zaman da yajima batare daya motsa ba.

Tausayinshi naji ya kamani kenan gadi na ya tsaya yi,Nikuma inata barci.

Cikin sanyin murya yace" Baby zamuyi wanka tare?

Girgiza kai nayi ina d'an shafar wuyana daya mak'ale,Hannunshi yakai wajan yana tausamin kamin yace Sannu nima barci ne ya kwasheni shiyasa ban juyakiba,Amma yanzu jikinki ina ke miki ciwo?

Hannunshi na rik'o daga yuwana da yake shafa"Babu inda kemin ciwo sai abuna har yanzu banjin dadinshi Allah.,Na idasa maganar cikin yanayin shagwaba.

Cikin mamaki ya fiddo idanunshi waje"Sorry kodai zaki bari in dubaki ne? Ko ruwan Sanyi kikasama wajan?

Tabe bakina nai kamar zanyi kuka"Ni babu wani ruwan sanyi,Ba kaine kaimin me zafiba sosai.


" To yi hakuri bazan kuma ba insha Allah zan dinga lallabawa bari in zuba ruwan zafi.



***

Da mamaki nake kallon falon maman duk su aunty sunzo,Sannu da zuwa naimusu mukacigaba da gaisawa dan cikinsu babu wacce naje gidanta duk hanawa yai.

Duk sannu sukaimin kamin akuma jajantama juna,Anan nakejin labarin abinda ya faru wanda ya tsoratani hankalina kuma yatashi.

Ammadai nai shiru musamman danaga su hankalinsu kwance sunata harkokinsu.

Saida Abba yai maganar zuwa gaisuwa Sannan Dr. Yace shidai bazai jeba aikima zashi.

"Kai bansan shirme da hauka wani irin aiki zakaje haka da yamma idan kaje gaisuwar akwai abinda zai ragu daga jikinka ne? Komai ai ya Riga ya wuce ko kanaso kuma sai kowa Yasan wannan maganar? Komai ya wuce Ahmad saidai mu dage da addua insha Allah hakan bazai kuma tasowaba nidai fatana ku yafemata abarta da abinda ta shuka,sai yanda Allah yayi da ita kuma.



Bacin rai besa Dr. Yakuma maganaba Haka akai tafiyar ranshi amatukar bace dan beyi niyyar zuwaba balle kuma ai maganar Wai yafiya, Lallai ma.



Gidan babu mutane sosai Dan ana kaita duk mutane suka watse musamman da wata mata ta bada fatawar wai maitar ta zata iya shigar wani😂kamin wani lokaci gidan ya koma saidai tsirarun mutane.


Ba a wani jimaba Saiga abban ya turo wai muzo mu wuce gida kadda dare yayi.

Nariga kowa mikewa dan dama kamar akan k'aya haka nakeji na.


Saida muka d'auki hanyar gida Sannan Dr. Yafara walwala har yanasa baki cikin maganar da akeyi.






Haske writer's association.
12/10/20, 2:49 PM - Naffy Aliyu Umar: 53




Sai magriba muka shiga gida,Kai tsaye wajanmu na shige dan watsa ruwa,Yayinda Abba ya tsare Dr yanamishi fad'a akan halin da yake nunawa.

"Duk abinda yafaru dakai da sanin Allah Ahmad sannan ka kasance me yafiya dan nuna godiyarka ga Allah bawai nuna fishi ba,Kumama ko babu komai ai kakar kace kowa Yasan bata kyautaba yanzu kuma babu ita kaga Allah ya gwadamata iyakarta kenan ko?

Dan Allah kai hakuri ka yafe mata insha Allah zakai farinciki ko kana tunanin wannan nasarar da akasamu kai kasa aka sameta?

Girgiza kai yai yana kuma Sadda kai.
To kagani danhaka kai hakuri dan Allah komai ya wuce Allah ya shige mana gaba,Kuma jiya d'azu mahaifin ayshan ya kirani Amma akan maganar abubakar danhaka ka shirya ranar asabar baka da aiki ka kaini sai inji yanda za ai.


***

" wai me kikeyi tun d'azu nake kiranki?

Dariya nayi jin yanda take kunbura baki" Sorry zainabu abu na shiga wanka ne ya akaine me zaki bani?

"Dallah labari zanbaki wai jiya Abbaa yaima mamanmu maganar Wai wannan tubabben yanasona kuma da aure kiji fa?

Bakina na rufe da hannuna ina zare ido" Dan Allah da gaske duk yaushe akai hakan?

"Wallahi kuwa to shine nakeso muyi shawara,Danni dai gaskiya bamma sanshiba balle kinga bawani wayarshi nai ba sosai ko kamanninshi ba bazan iya k'ararwa ba,Gashi kuma sabon shiga a addini.

" uhum kinjiki da wata magana gaskiya sanin da naimishi yanzu beda matsala,Kuma ma ai jahadi zakiyi zainab zai sami addini daga wajanki zai ga kimarki da darajarki Sannan kuma kyakkyawa ne ga dukiya duk da dai naji Dr. Na fad'in an rabar da dukiyarshi Amma duka kwana nawa zai maida wata tunda ga aikinshi hannunshi kuma babban abin farinciki ma shine zamu kasance gari d'aya kuma nasan hatta makaranta d'aya zasu nema mana Allah babu matsala anyimishi wankan tsarki.Na idasa maganar ina sakin dariya dan har na hango yanda zataci ubanta hannunshi.


"Ke dallah sai ana maganar arziki saiki wani kawo ta tsiya,Dan Allah me zancema Abbaa din wallahi cewa yai anjima da dare zai dawo yaji abinda na yanke sabida yanaso yaba shi abubakar din damar zuwa wajena.

" Dan Allah ki amince kinga nima nasami 'yar uwa kusa wallahi beda matsala musamman yanda naji Dr. Na fad'in k'okarin shi na Neman ilmi na tabbata zai rikeki amana tunda yasan anyimishi halacci kedai kawai ki amince.

Batace komaiba ta yanke wayar.


Shiru nai da wayar hannuna ina zare ido wato abinda ake shiryawa kenan? Allah na gode maka,Nasan ko banza nasami abokiya kusu kuma duk wannan mugun kullen nashi dole ya dinga barina ina zuwa wajanta idan ma Abba bece ya zauna nan gidan ba tunda akwai inda zai ishesu indai zamane.

Asanyaye yashigo cikin d'akin tare da zama Saman gadon.

Samun kaina nayi da yimishi Sannu da zuwa.


Kamo hannuna yayi ya d'ora saman kirjinshi yana kallon Saman idanuna.

"Ina sonki babyna,Cikin Wata siririyar murya yai maganar shiyasa naji gaba d'aya tsigar jikina tatashi bansan lokacinda nakuma lafewa jikinshi ba.

Sumbatar goshina yai akaro na uku bayan shigowarshi cikin d'akin" Inyi?

Da Sauri natashi daga jikinshi ina turo bakina gaba Dan tuni na hararo inda ya dosa niko inaji bazan iya da wannan kwatirar tashi ba,Ballema jikina bawani dadinshi nakejiba.

Rikoni yai k'asa yana dariya"Haba baby be kamata ace kinajin tsoroba bayan yanzu ai yaci acema kin saba.

Kauda kaina nai daga kallonshi,Bansan meyasa bejin kunyataba.

Murmushi yasaki "Ke dallah Wata bakauyace sai ana maganar love Amma saiki wani fara dojewa yanzu me kike nufi da wannan sunne kan da kikeyi uhum?

Natsuwa nai cikin jikinshi ina shak'ar k'amshin da yake Tashi jikinshi,Shima shiru yai Sai kitson kaina da yake wasa dashi.Tsawon lokaci kamar bazaice komai,Sannan yakuma sumbatar hannuna,Da alama yasaba da hakan kuma yanajin dadi dan kusan duk wani motsina saiya sumbaci wani waje jikina,Saina godema Allah Dana kasance me son k'amshi kuma nake amfani da shi koda yaushe.

" nawa ga Wata abunki ke zuwa? Yai maganar yana kauda shirun da falon ya d'auka.


Miyau na hadiye da k'arfi kamin in d'an zakuda"25.

Jelar kitsona yaja har Saida naji zafi kamin yace"Wannan watan bazakiyiba insha Allah inafatan na ajiye muhimmiyar ajiyata cikin mahaifarki.

Cikin zuciya ta nake adduar ba Aminba Allah yasa ba Yanzu ba.

"Meyasa bakiso ki sami ciki yanzu?

Manyan idanuna na fiddo kamin in rufe bakina da hannuna tunanina kodai bakina yai subutar fadin abinda na fad'i cikin zuciya ta ne.
Kaina na girgiza mishi inajin idanuna na cikowa da hawaye.

Lakucemin hanci yai yana murmushi" Karki damu babu matsala insha Allah kuma duk lokacinda yabamu muna so inaso ki huta da ciwon maran ne dannasan idan kinada ciki to bazakiyi ba,Kunyi waya da zainab kuwa?

Gyara zama nai ina kallonshi"Ashe abubakar ke sonta yanzu muka gama waya da ita Amma kai kana ganin babu matsala kuwa?


"Ah karki damu babu Wata matsala wallahi,Mutumin kirkine dama rashin imani da Allah yasa shi aikata wasu abubuwan Amma yanzu Alhamdulillah ya fahimci komai kuma Allah ya wankeshi,Abin da yasa nakeganin ya auri zainab din kinga tanada ilmin addini sosai zata dinga nunamishi wasu abubuwan da suka dace cikin kwanciyar hankali ba kamar yadda yanzu yake walagigiba bamu can bashi can danhaka kibata shawarar data dace dan Allah.


" To insha Allah.


"Yauwa Allah yaimiki albarka,Ya maganar d'azu dan Allah ahankali zanyi wallahi ni bammasan abinda yasa har yanzu kikejin ciwo ba,Bayan nasan tuni nasami hanya ta d'odar.

Kauda kaina nai ina d'an turo bakina gaba.


Azafafe ya dinga nunamin soyayyarshi har bansan na mik'a wuyaba Saida naji zai shiga jikina Sannan nafara tureshi,Aiko yaki yadda dan yariga yai nisa.

Kukan shagwaba na Sakarmishi,Ashe kuma kunnoshi nai batare Dana Saniba.



Yajima kwance akaina yana fitar da numfashi da gudu gudu kamin ya zanzare gefe,Yana rungumoni jikinshi" Sorry babyna.

Note.
Saina tuna Wata k'awata,Tace babu abinda ke k'onamata rai da mijinta irin kwanciyar da yakeyi ajikinta idan ya biya buk'atar shi wanda Akwai randa ta hantsaloshi ya antayo k'asa har yai targade,Sabida basusan dama abakin gadon sukeba.
To irin haka hakuri yakamata mu dingayi domin kowane namiji akwai yanayin da yake gwadawa idan yasami biyan buk'ata wanda kuma dolene Sai sunyi din danhaka gara ki tsaya Ki fahimceshi dan ki jure da kyau.

Kadda wataran garin turewa a karya megida,Dan komai zai iya faruwa lokacin dan babu wani kwarin jiki Tare dasu,Saisun huta Sannan suke dawowa daidai.




Matseni yai gam jikinshi yana sakin numfashi niko lamo nai jikinshi dan Yanzu bawata wahala yaban ba Saidai gajiya wadda har yanzu nakasa sabawa da ita.







Haske writer's association.
12/10/20, 2:50 PM - Naffy Aliyu Umar: 54




Da asuba ma da fitinarshi ya tasheni dan ko Sallar asuba be samuba.

Naje yin tsarki naga abun yazo hadda tsallen murna dannasan duk tsiya yanzu dr saidai ya kalleni Amma nai mamakin da banyi wannan masifaffen ciwon maran kamin zuwanshi ba.


Gyara jikina nai Sannan na fito fuskata fes.
Babu wannan kunburin fishin Dana shiga dashi.

" zo kiyi Sallar mana kikai tsaye!!

Hannuna nacigaba da murza batare Dana kalleshiba.

Tasowa yai yazo gabana tare da riko hannuwana,Zonan mana bazakiyi Sallar ba?


Ahankali na d'aga mishi kaina dan Wata kunya naji na tasomin.


"Ah kamar ya? Oh ko abinne yazo?

Shirun da nayi yasashi dafe goshin ya yana shafar fatar wajan,duk tunaninshi na sami ciki musamman dayaga nakuma canzawa sosai.

Numfashi ya sauke kamin ya riko hannuwana" OK Sannu ammadai marar bata ciwo sosai ko?

Kad'an na d'aga mishi kaina.

"Sannu jeki shirya to Saiki kwanta ki huta.

Duk cikin rashin walwala yai maganar har nafara mamakin hakan wato shi tsammaninshi ciki nasamu daga zuwa,To ashe kenan yanason yara Amma ko alama bantaba ganiba dan yarinyarshi datake raye bantabajin yai maganar taba tun zuwana gidan,Shiyasa nai tunanin ko yana cikin maza wa inda basu damu da yara bane,Ashe abin ba haka bane,Daga yanayin daya nuna yanzu to tabbas yanason haihuwa.

Cikin Sanyin jiki na kimtsa Sannan na koma gefen gado na kwanta.

Tashi yai zaune ya jawoni jikinshi Sannan muka kwanta ya d'ora kaina saman kirjinshi yana shafar gashin kaina.

Can nafara jin barci ma naji Sautin muryarshi cikin kunnena" Babyna zan k'ara kaimi wajan addua da kuma kan shimfida dan gaskiya da alama taurin kai zakiyi ko?

"Wane irin taurin kai kuma?


" Eh mana taurin kai tunda gashinan ina k'okarin baki Amma baki amsa da alama maidomin abuna kikeyi nifa nakosa inga kinfara d'an zazzabin dare haka da zubda yawu.

Wata uwar harara na wurgamishi tare da sunne kaina k'asa.




*****


"Wai kai dan Allah meyasa kake da bak'in nacin tsiya ne ka kira kaji mutun be d'aukaba ba saikai hakuri ba Idan an jima ka kuma kira ba?

" Dallah ni kyaleni banza mayen mace kawai ni ka fito ganinan falon mama tun d'azu nake faman jiranka bamazaka aiki bane? Abubakar yai maganar k'asa k'asa sabida kadda maman ta fito ta taddashi yana maganar.


Idonshi d'aya ya bude ya hango agogo aiko da Sauri yatashi zaune Tara nasafe yake fita office amma gashi yanzu Saura mintina yaushe ya shirya kuma ya karya.

"Baby tashi yi Sauri ki hadomin break fast wajan mama na makara yi Sauri.


Da azama nima na mik'e dan ya kamata ace na taya maman girkin Amma barcin nan yaimin nisa.


Dogon hijab nasaka na nufi falon maman bayan nad'an shafa turare,Shikuma yashiga wanka.


Cikin nutsuwa na gaida maman tare da abubakar wanda ya amsa cike da zumudi na juya zan wuce ne naji yana fad'in" Ya zainab?

Kunya nitafara kamawa dan tuni mama tabimu da kallo Saida yaga alamun naji kunya Sannan ya kalli mama shima saiya kauda kai yana shafar kanshi wanda yaji askin gayu.


Duk abinda nasan zai buk'ata Saida na had'a mishi,Koda nashiga yana fesa turare,Dan ya gama kintsawa.

Saida na had'a mishi Sannan ya amsa idanunshi na kaina,Nikuma kaina na k'asa,Dan sosai nakejin nauyin idanunshi.


"Zan wuce baby idan kinji wani abu to kimin waya ga waccan can ki dinga amfani da ita dama sabuwa ce nasan zakiji dadinta sosai.


Wayoyinshi da key din motar na d'auka nabi bayanshi.

Saida ya duk'a Sannan ya gaida mama Abba ko tuni ya fice,tare da abubakar suka fita Amma duk da haka saida narakashi har k'ofar falo Sannan na mik'a mishi wayoyin" Adawo lafiya Allah ya tsare yabada sa'a.

"Ameen ya Allah thank you baby.




""**""

"Baka da mutunci man tun safe nake jiranka fa!!!

" Kajika to dallah ni nace ka jirani ko na nemeka ne waima ina ka kwana jiya?

Murmushi yai kamin yace"barcine ya kwasheni cikin masallaci shine na kwana can Ammafa na cizu wlh jikina Duk yayi ja Sainasha magani.

"OK to Neman me kakemin,Cewar Dr. Yana karya kwanar da zata shigar dasu cikin get din asbt da yake aiki,Danshi abubakar din har yanzu transfer din daya nema bata fitoba tukunna balle Yasan inda zai fara nashi aikin.



" Yauwa dama salim ne yaimin waya wai Abba yace mu shirya muje ko da kai ko dashi wajan zainab anbamu izni to kaikuma inata nemanka inji yanda za ai Amma ka boye bayan baby.

"D'an harararshi yai yanakwaso tarkaenshi" To yanzu nufinka kanon zamuje?

"Eh mana,Ni fa ko yau shirye nake.


" Kabari anjima kad'an salim zaizo sai mu shirya yanda zakuje tare dashi kaga ni babu halin inje kwanakinnan ina wasa da aikinnan wlh Amma insha Allah nasan babu matsala da Salim da ni Duk d'aya ne dan garama salim zai iya tsayawa yai maka kanfe sosai ba kamar niba,Kace nan kusa zamu angonce,Ya idasa maganar yana mai dariyar shakiyanci..




"""""



"Lafiyarki lau kuwa aysha? Cewar mama idanunta na kaina.


Kamar jira nakeyi na bude bakina gaba d'aya nasaki kuka INA zamewa K'asa daga kan kujerar danake zaune.

Da Sauri ta dawo kusa dani" Subhanillahi lafiya meya faru?


Hannuna na yarfe INA matsar kwallah"Ciwo mama wayyo marata.


Agago ta kallah biyu saura to kuma k'arfe biyu yake Tashi aiki,Sannu yi hakuri ya dawo Saiya dubaki lokacinki yayi ne?

Kaina kawai na d'aga mata Sabida ya mutsar da nakeji marata namin.

Ina kwance k'asa akan kafet ya shigo gidan,Barcine ya kwasheni wajan bayan naci kukana na k'oashi.
Fuskata yafara lek'awa dan ni kad'aice falon.

Gabanshi yaji ya fadi dayaga fuskar duk tai ja ga busassun hawaye.




Please Login or Register in order to submit comment