Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ƙasa ta uku har ya zuwa
sanda suka haɗu dasu Zahra da kuma yadda ya ƙare
a
wannan waje.
Sai dai kuma abu ɗaya; duk da haka bai gaya mata
tsakaninsu da Masanin-ƙasa ba dangane da sunansa
na
gaskiya ba.
Ya kula sosai wajen labarinsa, tayadda shidai bai ƙara
yi
ƙaryar sunansa ba, amma kuma bai gaya mata
sunansa
Wilbafos ba! Kawai yai shiru yabar wajen a haka.
Ita ma kuma, tunda ta fuskanci baya son maganar,
sai
kawai ta share.
Wani abu da Armad ya kula dashi shi ne, tunda farko
daya
ambaci sunan Tirifil-fakta fuskarta ta canja sosai, sai
dai
tunda batai magana ba shima bai ce mata komai ba,
kawai
ya ci gaba da zayyana labarinsa.
Bayanda ya gama sai yai shiru inda ya kalli gabansa
daidai wajen wannan hijabi.
Ya dubi Núsí da niyyar ya tambaye ta me ake buƙata
mutun yayi kafin ace ya wuce wannan waje, amma
kafin
yayi magana yaji muryarta tana cewa, ”Tirifilfakta……!!!
”Lallai kana da ƙarfin aniya…. amma shin kasan
meka
ɗaukowa kanka kuwa!” Tayi shiru gami da ajiyar
zuciya
tana kallon Armad cikin mamaki.
Can bayan daƙiƙu ta ƙara numfasawa tace ”Bazan
kashe
maka gwiwa ba, amma abu ɗaya daya kamata ka
fara sani
akan wannan alamari shi ne; babu wani mahaluƙi,
rayayye
ko matacce, tun daga kan doron ƙasa ta farko harya
zuwa
doron ƙasa ta bakwai daya kai mai wannan suna

yawan
masu so su cimmasa.
”Wasu maƙiya wasu masoya. Babu wanda yasan
daɗewar
wannan suna a doron ƙasa babu kuma wanda yasan
wanene ko kuma ya yake. Kai hikayoyi da dama ma
sun
rawaito cewa daɗewar sunan tamkar daɗewar
ƙasashe
bakwai ne.
”An rawaito a mas’alolin farkon lokaci, cewa shi shi
kaɗai
ne mutumin da Ma’abota Ururu suka taɓa saka
kyauta ga
duk wanda ya kamo ko kuma ya bayarda wani
bayani
daya kai aka kamashi.
”Kimanin shekaru ashrin da suka wuce Dul’ururu ya
saka
hannu kan dokar kyauta akansa.
”Kayi sani cewa a halin yanzu zaka iya cewa duk
duniya
babu wani mahaluƙi kai tsaye ko kuma ba kai tsaye
ba,
yana sane ko kuma baya sane, da baya neman mai
wannan
suna.
”Da dama su na nemansa ne saboda kyautar da za’a
Bawa
duk wanda ya kawo shi, ko kuma kawai ya bada wani
bayani daya taimaka aka iya cimmasa.
”To, zata iya yiwuwa wasu su na da tsohuwar
ƙiyayya,
wasu kuma akasin haka, amma dai a zahirin gaskiya
zaka
iya cewa mutanen da suka san Tirifil-fakta ko kuma
wani
abu muhimmi akansa ƙalilan ne, domin har sunfi
adadin
jaki mai ƙaho yawa.”
”Shin yanzu ka fahimci wa kake nema?” Ta rufe
jawabinta
da tambaya.
To a wannan lokaci bayan ta gama duk wannan
jawabi
Armad na tsaye yana kallonta, wanda a sannan ne ya
bata
amsar da bata taɓa tsammani ba.
Inda yayi murmushi gami da cewa, ”ba matsala,
kawai
yana nuna ina da buƙatar na fi ƙarfin duk ragowar
masu

neman nasa ko?”
Fuskarsa cike da murmushi ya ci gaba da cewa, ”ta
yaya
ake wuce matakin wannan jarabawa?” Ya tambaya ya
na
nufat gurin wannan hijabi cikin sauri da kwanciyar
hankali tamkar wanda zai shiga cikin ɗakinsa.
Sai dai kuma a wannan lokaci ne Núsí wadda tun
amsar
daya bata bakinta ke buɗe cike da mamaki, ta taso
da sauri
inda ba tare da cewa komai ba ta riƙo hannunsa da
sauri a
dai-dai lokacinda yake ƙoƙarin miƙa hannu cikin
wannan
waje.
Ta janyoshi da ƙarfin tsiya inda har saida yayi tagataga
gami da yowa baya kamar zai faɗi.
Tun kafin Armad ya gama nutsuwa ya fara magana
cikin
mamaki, ”aargh.. Yaya?”
Nan take ta rufeshi da masifa, ”kasha giya ne!
hannuka
yana taɓa wancan waje zaka ƙara shiga yanayin daka
shiga ɗazu.
”Dama gashi bawai gama farfaɗowa kai ba.
”Kuma nidai bani da wani abu daya rage dazan iya
ceto ka
idan haka ta faru.
”Saboda haka ya kamata ka nutsu, mu zauna muyi
tunani
akan mai ya kamata muyi.”
Har a lokacin da take magana Armad idonsa na kafe
akan
wannan waje.
Shi dai waje ne wanda babu wani abu ban tsoro a
tattare
dashi ko kaɗan.
Kai hasali ma babu komai face dai kawai tamkar
wani layi
ne aka sa aka raba tsandaurin ƙasar zuwa gida biyu;
ɗaya,
inda su Armad ke tsaye, ƙasar nada launin ruwa ƙasa
kamar a ko’ina, sai kuma ɗan rairayi daya rufe ta,
ɗaya
kuma wanda ke gabansu shi ma fili ne kawai kamar
na
farkon, sai dai kawai ƙasar wajen launinta na
musamman
ne, imda take da launin ja mai gauraye da shuɗi.
Wannan kala ta ja-da-shuɗi ta ɗau haske sosai, inda

har
kyalli take tana zubarda haske inda ya maida iskar
dake
yawo a saman ƙasar irin kalar.
Aƙa’ida duk wani tsarar Armad daya kalli wannan
waje ya
kamata yaji nauyi yana tashi acikin zuciyarsa, kamar
yadda ita ma Núsí take ji.
Amma abinda bata sani ba shi ne Armad baya jin
komai
ko kaɗan daga kallon wannan waje, kuma hasalima ji
harga ALLAH shi ji yake acikin ran nasa tamkar ɗakin
nasa zai shiga.
Bayan Armad ya gama kallon wannan waje, bai bata
amsar duk maganganun da tai masa ba, sai kawai ya
dubeta, gami yi mata murmushi, wanda ke ƙunshe
da
godiya na kula da take nuna masa.
Amma gama murmushi keda wuya, shi kansa bai san
mai
yasa ba, kawai yaji tsananin soyayyar ya tashi ya
shiga
wannan wuri, tamkar wanda wani abu acikin wajen
yake
kiransa.
Armad ya ƙara juyawa ya kalleta gami da cewa, ”bari
na
gwada, sau ɗaya kurum, idam baiba, saimu canja
wata
shawarar!”
Tayi niyya, kuma harta buɗe baki domin gaya masa
wani
abun, duk don ta gaya masa cewa bazai yiwuba,
amma ina
kafin ma tayi wani abu tunu Arnad ya kwace ya nufi
wannan guri gadan-gadan, tamkar wanda ake jansa.
Nan take ta miƙe ta kuma bishi, amma kafin ta
cimmasa
tuni ya afka da ƙafafunsa biyu cikin wannan waje!
Nidinne dai Shuraih Usman inkiya
99%
Daga taskar magajin wilbafos
MAGAJIN WILBAFOS
Marubuci: Dr Abdullahi Muhammad Ibrahim
Babi na 19: sa hannun sarki dul ururu
Post by: Shuraih Usman
@shuraih 99%
www.facebook.com/hausaebooks
.
Daga:- Taskar Magajin Wilbafos
.

.
Saboda saurin da Nusi ta taso dashi, duk dan ta riƙo
Armad cikin ƙoƙarinta na ta hanashi sanya ƙafa
acikin
wannan waje, tana ganin ya riga ya faɗa sai taci birki
da
ƙarfin tsiya domin kada ita ma ta faɗa ayi biyu babu.
Amma ina, dama a lokacin bai wuce sauran kamu
uku ba
tsakaninsu da Armad ba, saboda haka duk da cijewar
da
tayi saida ta ita ma ta afka.
Duk da cewar ba dukkan jikinta bane ya faɗa ba,
amma
ƙafarta ta dama tuni ta shiga wajen.
Nan take ta rufe ido cikin takaici, babu abunda take
tambayar kanta face, ”mai yasa…mai yasa… duk
akan
wannan yaro da bai ma san banbancin fari da baƙi
ba,
nake neman halaka kaina….”
Wannan shi ne tunaninda yake ta juyawa a ranta, a
lokacin
da ta gano cewa ta rasa komai data daɗe tana tanadi,
duk
acikin ƙanƙanin lokaci, sannan kuma ga rayuwarta
nan ma
tana kusantar halaka.
Amma wani abun mamaki ga ita kanta shi ne, gashi
dai
lallai ya kamata tayi baƙin ciki gameda yadda
abubuwa
suka juya mata, kuma babu wanda ya kamata ta
zarga face
Armad, amma ko kaɗan bata jin dana sani acikin
zuciyarta.
Hasalima ji take tamkar tayi wani babban abu mai
matuƙar
muhimmanci a gareta, tamkar sauke wajibi daga
cikin
wajibai.
Saboda irin wannan tunani da take, kawai saita rufe
idanunta cikin ɗimuwa a wani yanayi na bankwana
da
duniya.
Ƙafarta tata tana shiga cikin wata iska mai tsananin
ƙarfin
gaske ta finciko dukkan jikinta daga inda yake izuwa
cikin wannan waje.
Nan take ta buɗe ido, sanda taji ta a sama tana lilo
tana
nufar ƙasa, ƙiris ta faɗo.

Abu ne sananne cewa acikin waje da suke kira da
Hijabi,
tsananin hawa-hawa ne, kuma yana mafi ƙarfi akan
ƙasar
wajen.
Saboda haka ta fara ƙoƙarin yin wata dabarar,
domin kada
ta taɓa ƙasa, amma ina kafin tayi wani abu tuni baifi
saura
kamu biyu ba a tsakaninsu da ƙasa ba.
Idanunta a rufe tana jira ta fuskanci irin wannan
uƙuba
data riga ta sani aduk lokacinda tayi arba da wannan
guri,
kwatsam kawai sai jitayi komai ya tsaya tsak aduniya
babu
abinda ke motsi.
Kai a yadda taji ma, hatta zuciyarta saida ta tsaya da
bugawa na taƙi ɗaya kafin ta ci gaba.
Nan take ta buɗe ido gami da duba izuwa muhallinta
domin ganin mai yake faruwa.
Nan kuwa idanunta sukai arba da Armad wanda ke
riƙe da
ita akan iska.
Bata san lokacinda tsananin mamaki ya kamata ba, a
sanda
ta juya ta kuma tabbatar da cewa ƙafafun Armad ɗin
a
tsaye suke cak akan wannan waje babu kuma ko
alamun
girgiza a tattare dashi.
Kai hasalima babu wani alamun yana kan wani waje
na
musamman ko kuma mai sharri.
Armad yayi murmushi mai ɗan ɗauke da yarinta ta
dai-dai
shekarunsa, inda baice komai ba, bai kuma tsaya ba,
nan
take ya ci gaba da tafiyarsa a wannan waje.
Duk inda Armad ya taka saiya ƙara yin tsananin ja
sosai,
tayadda har sai kore-koren dake gauraye da launin
jan ya
ɓace ɓat, amma hakan ko kaɗan baya ko alamun
cutar
dashi, hasalima tamkar sauri yake ƙara masa.
Tuni mamakin daya haɗiye Núsí ya rikiɗe ya koma
firgici,
inda idanunta suka fara karkarwa saboda firgici.
Ba komai bane ya jawo haka ba illa abinda take
tunani
acikin ranta, ”mai ke faruwa, hatta sinadarin

Negrinkin
cikin wannan waje ma baya masa komai, maimakon
su
rinƙa tureshi, shi kuma yana ƙoƙari akan su
karɓeshi,
amma wannnan yaro tamkar nemansa suke, tamkar
sune
suke buƙatarsa bashi bane yake buƙatarsu ba….
“Wai haƙiƙanin wane ne wannan yaro, kuma maike
faruwa…kuma dai na tabbatar ba mafarki nake ba!!!”
To abinda bata sani ba shi ne Armad yana shiga
wajen,
yaji wannan mutun-mutumi da suka haɗa ido dashi
a baya
ya ƙara motsawa, inda wani abu ya faru cikin
tsananin
sauri, wanda lallai da Armad ɗin ya ƙifta ido sau ɗaya
kacal to da lallai bazai gani ba.
Abinda kuwa ya faru shi ne; Armad na sanya ƙafa
cikin
wannan guri yaji tamkar ya faɗa cikin garwashi.
Tsananin raɗaɗi ya gauraye jikinsa, tayadda kafin
yayi
wani abu tuni ƙafafunsa sun kasa ɗaukarsa kuma
sun fara
neman durƙushewa.
To amma a wannan lokaci ne wannan mutunmutumi ya
motsa cikin tsananin sauri tayadda inka ƙifta ido sai
ɗaya
kaɗai bazaka lura da faruwar abin ba.
Amma wannan motsawa da yayi ita ce tasa iskar
dake
kewaye dashi ta motsa, inda wata ƴar ƙaramar
guguwa ta
kaɗa inda kafin kace meye wannan tuni ta gauraye
wajen.
Armad bazai taɓa iya bayanin maiya faru ba, ko
kuma
taya ya abinda ya faru ya faru ba, amma zai iya
rantsewa
cewa acikin wannan iska data giftashi wadda ta fita
daga
jikin wannan mutun-mutumi, akwai wani ‘umarni’,
irin
umarnin da babu wata halitta mai rai ko mara rai
data isa
ta saɓashi.
Armad baisan haƙiƙanin meke cikin wannan umarni
ba,
amma lallai zai iya rantsewa cewa an bada wannan
umarni.

Wanda kuma faruwar hakan keda wuya yaji duk
abinda
yake ji a jikinsa ya kau, babu ko alamun ciwo ko zafi.
Kuma hakan na gama faruwa hankalinsa ya dawo
jikinsa
inda yaga Núsí tana ƙoƙarin faɗuwa, shi kuma yayi
sauri
wajan tallafo ta.
Su na tafiya tana riƙe a hannun nasa, inda shi kuma
yake
nufar ɗaya ɓangaren domin fita daga wajen.
Kuma koda yaga irin yanayi na mamaki da firgici
data
shiga, sai kawai ya fara mata bayanin dukkanin
abinda ya
faru, daga sanda ya taka ƙafarsa har ya zuwa wannan
lokacin.
To dama dukkanin wajan da zasu wuce ɗin wanda
ake
kira da Hijabin, baifi taku ashirin ba, saboda haka a
daidai kusan lokacin da suke niyyar ficewa ya hattama
zayyana mata abinda ya faru.
Haka dai suka ƙarasa takunsu na ashirin da ɗaya
wanda ya
ƙarasa fitar dasu daga wannan waje gaba ɗaya.
Inda ya ajiye ta gami da kyara musu waje dominsu
zauna.
Ƙasar dake bayan wannan waje tana da banbanci da
wadda suka baro; tayadda duk inda ka duba zaka ga
alamun rayuwa.
Kamarsu tsirrrai da namun daji, kuma gaba kaɗan
garesu
daji ne katafare.
Núsí ta ɓoye mamakin ta kuma ta haɗiye
tambayoyinta
game da Armad, domin a ɗan iya lokacinda suka yi
dashi
da kuma abubuwan daya gaya mata, ta fahimci cewa
lallai
akwai abubuwa na ban al’ajabi a tattare da wannan
yaro.
Kuma babban abin mamakin shi ne, shi kansa ga
dukkan
alamu bashi da masaniya akan wannan abubuwa.
Saboda haka taji a ranta bata san ta matsa masa da
tambaya.
Amma wani abu guda ɗaya wanda dole ne shi da ita
su
warware shi ne, a wanne matsayi suke a yanzu.
Nanfa ta buɗe baki, fuskarta cike da murmushi mai
alamun godiya tace, ”nagode Armad, daka wutar

dani
wannan jarabawa, domin kuwa ban taɓa tsammanin
wucewa da wuri haka ba.
”Amma wani hanzari ba gudu ba, naji labarinka
kuma naji
aniyarka ta neman Tarifil-fakta.
”Sannan kuma na gaya maka kaɗan daga cikin irin
hatsarinda wannan aniya taka ke ciki. Amma daga
alamun
daka nuna min naga baka da niyyar canja ra’ayi.
”To amma naga lallai bakai kama da wawa ba,
saboda
haka nasan daga ɗan abinda na gaya maka da kuma
wanda ka sani, ya isheka ka gane cewa a yadda kake
ɗinnan babu abinda zaka iya. A taƙaice dai ina ganin
baka da ƘARFIN DA ZAKA IYA NEMO SHI A
YANZU!”
Data zo nan a zancenta, sai ta ɗan tsaya, saboda
ganin da
tayi ya ɗago kai yana kallonta.
Duk da ba tayi mamaki ba sosai, kuma bata daɗe ba
ta ci
gaba da bayani ba, amma abinda bata sani ba shi ne,
dalilin da yasa ya ɗago kai shi ne, ta taɓa dai-dai inda
yake
masa ƙaiƙayi.
”Kamar yadda kaji a labari na ina daga cikin manyan
ɗalibai a mazhabar Maikironomada, saboda haka
idan
kana so zan iya zuwa dakai na samar maka wajen
fara
horo!”
To daya ke faɗuwa ce tazo dai-dai da zama, Armad
bai
tsaya ɓata lokaci ba ya amince ɗa wannan shawara.
Inda suka zauna a wannan waje tsahon kwanaki biyu
suna
hutawa.
Suka kafa ɗan ƙaramin tanti, inda suka zauna aciki.
Duk da cewa bata kulashi sosai, amma hakan baisa
ya rage
bata labarai ba wanda mafiya yawansu na doron
ƙasa ta
uku ne, da kuma yi mata tambayoyi akan yaya ƙasar
Maikironomada take, kuma yaya irin horonsu yake.
A rana ta uku suka ɗaura siddi akan wata alfadara da
suka
kama a ranar farko, kuma suka nufi gabas ta cikin
wannnan daji dake gabansu.
Duk da cewa sun ɗauki sama da sati ɗaya suna tafiya
acikin wannan daji, amma babu wani abu muhimmi
daya

faru a yayin tafiyarsu.
A kwana na tara suka iso wani ɗan ƙauye mai yawan
bukkoki.
Duk da akwai ƙofar gari amma babu wani caje da
ake
kafin shiga wannan ƙauye, kuma babu wata doka ta
musamman.
Saboda haka basu sha wata wahala ba suka shiga
kuma kai
tsaye Núsí ta jasu wani ɗan waje da aka gina da
rumbu.
Daga saman ƙofar shigar an rubuta, ‘wajan shan
furar
matafiya’.
Har sun kusa zuwa sai ta buɗe baki ta ce, ”shekaru
uku da
suka wuce kafin na fara wannan jarabawa, anan
nasha
fura da zan wuce.
”Musha fura anan, kafin mu nemi wajan kwana a
wannan
gari saboda…….”
Dai-dai sanda tazo nan a zancenta tana gabda shiga
ƙofar
wannan waje, amma saita tsaya cak ta kuma yi sauri
ta
juya.
Ba komai bane ya jawo haka ba face Armad wanda
ya
tsaya cak, fuskarsa a kafe akan bangon wannan wuri
na
ɓangaren kudu.
Kana ganinsa kasan acikin firgici yake, jikinsa kaf
karkarwa yake amma kuma wani babban abin
mamaki shi
ne idanunsa a rufe suke ruf.
Kuma ƙarara ƙoƙari yake tayi ya buɗe su harda
hannayensa biyu amma ya kasa.
Bata tsaya ɓata lokaci ba ko kaɗan, ta juyo ta kuma
nufoshi da sauri, sannan kuma a lokaci guda,
idanunta
suka bi dai-dai fuskar ta Armad take kafe a jikin
bangon.
Ba komai ta gani ba, illa takardar da kusan kowa a
wannan
doron ƙasa ta huɗu ya sani.
Wadda kuwa ita ce takardar da Sarki Dul’Ururu ya
saka
hannu akai.
Wadda ita ce ke ƙunshe da Kyaututtukan da za’a
bawa duk
wanda ya kawo ko kuma ya bada wani bayani daya

taimaka aka kama Tarifil-Fakta.
Sannan kuma da wasu hanyoyi da za’a iya ganeshi.
Sai kuma sa hannun sarki bisa doron ƙasa ta biyu,
wato
Dul’Ururu, wanda ke jaddada ingancin wannan
takarda!
Nidinne dai Shuraih Usman inkiya
99%
Daga taskar magajin wilbafos
MAGAJIN WILBAFOS
Marubuci: Dr Abdullahi Muhammad Ibrahim
Babi na 20: magajin wilbafos
Post by: Shuraih Usman
@shuraih 99%
www.facebook.com/hausaebooks
.
Daga:- Taskar Magajin Wilbafos
Minti ɗaya da daƙiƙa ashirin kafin rufewar idon Armad.
Tafiya yake yana dube-dube hagu da dama, badan komai
ba sai dan irin kyawun muhalli da yaga wannan ƙauye
nada shi.
Duk da cewa wannan ƙauye bashi da girma, amma duk
inda ka duba akan hanyoyinsu sunyi shuka ta korayen
tsirrai masu sanyaya ido.
Sannan kuma ga filawowi masu launi daban-daban ko ina
ka kalla.
Armad bai san mai yasa ba, amma yana shiga wannan
ƙauye yaji hankalinsa yayi matuƙar kwanciya tamkar
tsumma a randa.
Wani farin ciki da baisan daga ina yake ba ya fara
lulluɓeshi.
To yana cikin wannan hali ne idanunsa suka kai ga kan
wata ƴar takarda mai launin ja, kuma tana da
matsakaicin faɗi.
Acikin wannan takarda akwai ɓangarori guda uku; na
farko yana magana kamar hakaTarifil-fakta mutun ne mai tsananin hatsari ga zaman
lafiyar al'umma.
Saboda haka maɗaukakiyar masarauta take tabbatarwa
da jama'a su kwantar da hankulansu domin zatai duk
wata mai yiwuwa wajen ganin cewa an kama shi.
Ɓangare na biyu kuma yana magana ne akan
kyaututtukan da aka tanada ga duk wanda ya kawoshi ko
kuma ya samarda jawabi daya taimaka aka cimmasa,
kamar hakaDuk wanda ya kamoshi ko kuma ya bayarda wani bayani
daya taimaka aka cimmasa, to yana da waɗannan
kyatuttuka;
1-Za'a ɗaga darajarsa data ƙabilarsa zuwa doron ƙasa ta
farko!
2-Za kuma a bashi mafificin muƙami a wannan ƙabila

kowacce ce!
3-Za'a ƙarfafa ruhinsa dana zuriyarsa da ɗaya daga cikin
huɗu na Izzan dake Maɗaukakiyar masarauta!
Ɓangare na uku kuma yana bayani ne akan alamonin
yadda za'a gane shi;
Yana da tambarin Miyura a goshinsa madauwami, wanda
baya taɓa ɓacewa.
A kewaye da wannan tambarin akwai hoton wata guda
uku; ɗaya daren tara, na biyun daren sha takwas sai
kuma na ƙarshe daren ashirin da bakwai!
Waɗannan watannin guda uku su na motsawa tamkar
masu rai, inda suke kewaye wannan Miyura!
Ga hoton wannan Miyura!
Sai kuma daga ƙasa aka bayarda hoton Miyurar da ake
magana akai!
Ɓangare na ƙarshe kuma yana ƙunshe da sa hannu na
sarki bisa doron ƙasa ta biyu, wato Dul'Ururu.
A gabansa kuma kaɗan akwai alamun fuska, wadda ba
abinda ake gani acikinta face ɓaƙaƙen idanuwa guda
biyu.
Waɗanda idan ka kula sosai zaka ga wasu lokutan idan
wani yazo yana karanta wannan takarda suna motsawa
su kalleshi.
Sai dai kuma ba kowa ba, domin wani ko mai duban da
zaiyi ba zasu taɓa nuna alamun motsi ba, tamkar ma
babu wanda ke wajan.
Sai kuma wani lokaci da idanun suke motsi shi ne, idan
wani yazo yai magana a gabansu cewa yana da bayani
akan Tirifil-fakta, to su na motsawa su kuma kalli cikin
idanun mutun.
Kuma kamar yadda kowa ya sani, a gaban waɗannan
idanu baka da buƙatar ka mayarda bayaninka zuwa
kalmomi, domin kallo ɗaya kacal suke da buƙatar suyi
maka su zaƙulo wannan bayani daga cikin kwakwalka ba
tare ma ka sani ba.
Abu na ƙarshe a jikin wannan takarda shi ne tambari mai
ɗauke zanen ƙasa bakwai wanda a samansa yake da
hoton fada.
Wannan ba wani tambari ba ne, illa na maɗaukakiyar
masarauta.
To ko mai yasa idanun Armad suka rufe ruf, kuma duk da
ya sa hannu amma ya kasa buɗe su.
Abinda ya faru shi ne, Armad na zuwa ƙarshen wannan
takarda bayan ya gama karanta jawaban saman, kuma
tuni ya ƙara fahimtar abinda Núsí ta gaya masa akan
girman al'amarin daya ɗauko da kuma kaɗan daga cikin
wane ne Tarifil-fakta. Sai idanunsa suka nufi kan ɓangare
na ƙarshe a jikin wannan takarda, wanda ke ƙunshe da
alamun wannan fuska da kuma waɗannan baƙaƙen
idanu guda biyu.
Amma a wannan lokaci ne, ya ji kawai idanunsa da kansu
sun fara rufewa da kansu, kuma kafin yayi wani abu yaji

suna ƙoƙarin rufewa su kaɗai.
Nan take ya fara ƙoƙarin rufe su, amma ina.
A wannan lokaci ne yaji tamkar wata Izza mara iyaka ta
taso daga jikin wannan mutun-mutumi dake cikin
tambarin Miyura dake goshinsa,ta ƙarawa idanun nasa
sauri, inda cikin ƙiftawar ido suka rufe ruf.
Sannan kuma wannan Izza ta kewaye su, gami da
tabbatar da cewa sun zauna a rufe.
Armad bai yadda da abinda ke faruwa ba, saboda haka
nan take ya fara ƙoƙarin buɗe idon nasa.
Amma ina ko motsi basuyi ba.
Sai dai kuma amma a wannan lokaci ne iskar dake
kewaye da wannan baƙaƙen idanu a jikin wannan
takarda ta kaɗa. Wanda nan take duk da cewa idanun
Armad a rufe suke ya fara jin wata irin Izza wadda tunda
yake a rayuwarsa bai taɓa jin irinta ba ko da a mafarki
kuwa, ta fara tashi daga wannan idanu.
Kuma inda idanunsa a buɗe suke da yaga abinda Núsí
take gani baki a buɗe a wannan lokaci.
Domin kuwa wannan idanu sun fara fitarda wani baƙi
hayaƙi, wanda kafin kace meye wannan ya cika wannnan
waje ta yadda da kyar kake ganin waye a gabanka.
Kafin kace meye wannan kusan dukkanin mutanen
wannan ƙauye sun firfito daga gidajensu cikin firgici,
kasancewar sun san cewa indai wannan idanu suka fara
fitar da hayaƙi to yana nuna cewa kenan akwai sanarwa
ta musamman daga maɗaukakiyar masarauta.
Tuni wannan baƙaƙen idanu suka fara sheƙi, suna ƙara
baƙi.
Kafin kace meye wannan tuni wannan ƙauye ya fara
duhu duk kuwa da cewa rana ce tsaka.
Tamkar baƙaƙen idanuwan suna zuƙe haske gaba ɗayan
ƙauyen ne!
Bayan kimanin daƙiƙa talatin, sai kawai suka ga wannan
hayaƙi ya fara tattaruwa yana dunƙulewa a waje ɗaya.
Kafin kace waye wannan ya haɗe a waje ɗaya ya dunƙule,
inda nan take ya fara juyawa da ƙarfin gaske, ta yadda
idan ka fiya ƙura masa ido kaima sai kaji kanka ya fara
juyawa.
Cikin daƙiƙa bakwai wannan hayaƙi ya rikiɗe ya koma
siffar ƙararrawa.
Baƙar ƙatuwar ƙararrawa, wadda idan ka ɗaga kai, sai
kaga tamkar ta rufe dukkanin sararin samaniya.
A dai-dai wannan lokaci tuni Núsí ta isa kan Armad
wanda tuni abinda ke faruwa a cikin kwakwalwar sa yasa
yama daina ƙoƙari buɗe idon nasa, ya tsaya kawai jikinsa
yana karkarwa.
Dukkanin abubuwan dake faruwa, idanun Armad a rufe
suke, saboda haka bai san da dama daga abubuwan dake
faruwa ba.
Sai dai kuma shima acikin ruhinsa yana ganin abinda
babu wanda yake gani saishi.

Acikin kwakwalwar tasa yana ganin wata duniya ce ta
musamman, inda yake tsaye kamar matacce, wannan
hayaƙi dake tashi daga wannan baƙaƙen idanu guda biyu
yazo ya fara ƙoƙarin buɗe idon nasa ta ƙarfin tsiya,
tamkar wanda rayuwarsa da samuwar sa ya wanzu akan
wani abu dake cikin idanun na Armad.
To amma kuma a wannan lokaci ne wannan mutunmutumi da hotonsa ya bayyana acikin kwakwalwar
Armad wanda ke ƙoƙarin hanashi buɗe idon nasa ya
ɗaga hannunsa inda wata doguwar takobi, wadda takai
tsayinsa ta bayyana aciki.
Wanda kuma nan take yayi kan wannan hayaƙi da sara.
To sai dai kuma a dai-dai lokacin ne wannan baƙin hayaƙi
ya juye izuwa halitta mai kai tara.
A jikin kowanne kai akwai baƙaƙen idanu guda biyu,
wanda hakan ya sa baƙaƙen idanu guda gima sha takwas
suka bayyana.
Armad dai na tsaye acikin wannan duniya kamar ɗan
kallo, mahaukacin azababben yaƙi ya kaure.
Dukkaninsu daga ita wannan halittar, har shi mutunmutumin babu wanda hotonsa ya fita sosai yadda Armad
zai gane kamanni sosai, amma duk da haka yana jin irin
ƙarfin tsananin tsana da azabar yaƙi ta har abada dake
tsakanin sifofin guda biyu.
A waje kuma acikin duniyar mutane, Núsí tana tsaye tana
ta ƙoƙarin farkar da Armad, amma ina, baya ko alamun
jinta, kuma har wannan lokaci idanunsa a rufe suke.
Nusi na tsaye inda a dai-dai lokacinda wannan ƙararrawa
ta gama haɗuwa ta ɗaga kai sama, kuma ta samu cewa
bisa mamaki ƙararrawar tana dai-dai samanta.
A saboda haka nema dukkan mutanen wannan ƙauye da
suka firfito, idan suka ɗaga kansu sama suka kalli wannan
ƙararrawa sai kuma su saukar da kai kuma su dubi su
Armad domin ganin mai ke faruwa.
Wanda kuma, abinka da ƙauye kowa yasan kowa, saboda
haka nan take maganganu suka fara tashi ana nunosu ana
cewa baƙi ne suka shigo.
Wannan abu dake faruwa bai ɗau hankalin mafi yawa
daga cikin jama'ar ƙauyen ba, domin da dama har a
lokacin kansu yana kan wannan ƙararrawa kuma su na
jira su ji wane bayani ne zai sauka daga maɗaukakiyar
masarauta a wannan lokaci.
To kowa dai yana tsaye yayi kasake, wasu kuma
hankalinsu nakan Armad wanda suke tunanin mai yasa ya
rufe idonsa.
Wasu ma tuni sun fara tunanin ai makaho ne, amma
daga bisani daga bisani suka ƙara ƙura masa ido suka ga
kwata-kwata baiyi kama da makahon ba.
Sannan kuma akwai wasu jijiyoyi a zagayen idanun nasa
dake ƙara kumbura wanda ke nuna alamun cewa idanun
nasa da ƙarfi aka rufesu, wato bashi ya rufe su ba.
Ana cikin wannan hali ne, ƙararrawar nan tai ƙara sau

ɗaya, wanda hakan yasa duk mutanenda ke wajen suka
zube akan gwiwowinsu.
Hatta Núsí sai da ta zube ba tare da ta sani ba, tamkar
wadda bata da iko da jikinta.
To amma wani abu wanda yasa dukkanin mutanen wajen
suka maida hankalinsu kan Armad cikin mamaki, shi ne
ko kaɗan Armad bai durƙusa ba.
Hasalima hatta Nusi da taga mutane nata kallonsa, saida
ta fara ƙoƙari fizgarsa dan shima ya durƙusa amma ina,
tamkar wanda take jan bishiyar kuka.
Wannan ƙararrawa ta ƙara kaɗawa ta biyu, inda wata
murya mai ɗauke da wata irin irin Izza wadda ke
tursasawa kunne sauraro kuma ta tursasawa kwakwalwa
fahimta ta fara jawabi, ''sanarwa zuwa ga dukkan
ma'abota dukkan ma'abota ƙasashen ƙasa.
''Wani Magajin Wilbafos ɗin ya sake bayyana.
''Yana da tambarin Miyura mai tsarin dauwama a
goshinsa.
''Mai irin wannan tsari'' Wannan murya na furta haka, sai
hoton wannan Miyura da take nufi ya bayyana acikin
ruhin dukkan wani mutun da yaje sauraron wannan
magana.
''Wannan wata dama ce ga dukkan wani mai so ya cimma
Tarifil-fakta, ku kamashi kuyi amfani da jininsa.''
Tana faɗar haka sai tayi shiru, sannan bayan ƴan daƙiƙu
ta ƙara kaɗawa inda dukkanin al'ummar dake wajen
hankalinsu ya dawo jikinsu.
Nan take suka mimmiƙe, idanunsu cike da mamakin
abinda suka ji.
''Magajin Wilbafos........
''Magajin Wilbafos.... maike faruwa...
''Wane ne wannan...ai koma wane ne dai an kamashi an
gama." Nan take mutanen wannan gari suka fara
tattaunawa a tsakakninsu.
A can gefe wasu dattijai guda uku suka numfasa tare da
fara fara jawabi, ''Yanzu bayanin shi ne wane ne zai fara
cimmasa...domin kuwa duk wanda ya kama wannan
magajin Wilbafos ɗin, lallai ya samu wata dama
musamman ta kama Tirifil-fakta.
''To amma kuke tunanin shi wannan magajin bashi da
ƙarfin Izza, domin kuwa na tabbata indai tarihin da yazo
a littattafai akan zuriyar Wilbafos haka ne, to fa lallai
jarumin gaske ne kaɗai zai iya zama magajin wannan
gida.
''A'a, ai ni ina gani cewa komai ƙarfinsa, to fa lallai kamar
an kamashi ne an gama, domin ko waye shi babu tayadda
za iya da dukkanin miliyoyin al'ummar jaruman dake son
kama Tirifil-fakta, dan ni idan ni ne shima, kawai zan
miƙa kaina ne kawai.''
To waɗannan dai sune kalamanda al'ummar wannan
ƙauye suka fara tattauna hankulansu na dawowa jikinsu.
Sai dai kuma a dai-dai wannan lokaci ne wannan

ƙararrawa bayanda ta baje, ta ƙara komawa wannan
hayaƙi, shi kuma ya dunƙule waje ɗaya inda ya rikiɗe
izuwa siffar wani hannu mai girman gaske, wanda ke a
rufe da baƙin gashi.
Wannan hannu yana bayyana ya nufo Armad da saurin
gaske a buɗe, tamkar wanda ke ƙoƙarin ƙwaƙule masa
ido.
Kafin wani yayi wani abu tuni wannan hannu ya isa gabda
idanun Armad, kuma yana gabda taɓa su.
Amma a dai-dai wannan lokaci ne wata iska ta bayyana ta
daki wannan hannu, inda yayi sama izuwa goshinsa.
Kafin kace meye wannan yayi sama inda ƙarfin wucewar
tasa ta cire jan kyalle da Armad yake amfani dashi wajen
ɗaure goshinsa.
Nan take tambarin

Please Login or Register in order to submit comment