Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ƙarfin Izza a
doron ƙasa ta huɗu, idan son samu ne kada ka taɓa yin
faɗa dashi!"
Yana gama faɗar haka ya juyawa Armad baya ya fara
tafiya, a lokacin ne shi kuma Armad ya buɗe baki da
niyyar tambayarsa mai ya kamata yayi, sai dai kafin yai
magana yaji gaba ɗayan kansa ya fara juyawa, inda daga
bisani ƙasar da yake tsaye akanta yaji ta fara narkewa
tana komawa kamar ruwa.
"Aaarrrghh" muryar Armad kenan bayan da yaji kwatsam
ya rufta ƙasa. Wanda a lokacin ya tsinci kansa a wani
yanayi mai kamada mutun yana faɗawa wawakeken rami
mara ƙarshe, sai dai abinda Armad yake fuskanta a
lokacin yama fi haka.
Nidinne dai Shuraih Usman inkiya
99%
Daga taskar magajin wilbafos
MAGAJIN WILBAFOS
Marubuci: Dr Abdullahi Muhammad Ibrahim
Babi na 5: Koriyar Duniya
Post by: Shuraih Usman
@shuraih 99%
www.facebook.com/hausaebooks
.
A babi na hudu mun tsaya a inda Armad ya tsinci kansa

yana faɗawa cikin rami ba tare da shiri ba, yanzu zamu ci
gaba.
***
Hankalin Armad tuni ya gushe, a lokacinda yake cikin
halin ruftawa wannan waje, zuciyarsa cike da jimamin
ina zai faɗa, kuma a wanne hali zai faɗa.
Abu na gaba da Armad ya gani bayan hankalinsa ya dawo
jikinsa shi ne tsintar kansa da yayi a wata duniya ta
musamman.
Tun kafin idanunsa su ƙarasa buɗewa wani haske wanda
gaba ɗayansa kore ne babu ko garwaye, ya fara yi masa
sallama ta hanyar haske masa ido. Kafin daga bisani ya
ƙarasa buɗe idanunsa ya kuma ga zahirin wannan duniya
daya tsinci kansa aciki.
Bayan buɗe idon nasa ne ya kuma ɗaga kansa sama, inda
ya fahimci cewa dukkan abinda ke wannan wajen kore ne
shar. Kama daga kan sararin samaniyar wannan duniya
har zuwa kan tantagargar doron ƙasar. Ba shiri ya
durƙusa gami da dantsi ƙasar dake kusa dashi domin ya
ƙara ganewa idonsa launinta.
Wani abu daya ƙara bashi mamaki shi ke babu wani
alamun rauni a jikinsa, duk da kuwa cewar bai san yadda
akai yazo wajen ba, amma kuma abu na ƙarshe da yake
tunawa shi ne faɗawa cikin wannan rami wanda a iya
lissafinsa, a tayi masa da kyau ya sha da karaya biyu zuwa
biyar.
Yana tsaye cikin mamaki da talazzuzin yanayin daya samu
kansa a wannan duniya sai kawai jin alamun motsi yai a
samansa.
Ai kuwa yana ɗaga kai yai arba da wani ƙatoton shaho
kore shar, wanda yakai kimanin ƙafa uku a kwance, yana
ƙoƙarin kawo masa wata muguwar wafta da niyyar tsinke
masa kai.
Bakin shahon yana da tsayi da tsini matuƙa, sannan kuma
ga kyalli da sheƙi da yake yi. Daga can ƙarshen bakin
kuma akwai wani koren abu mai kama da yawu da yake
ɗisa daga cikin bakin shahon.
Wani abun mamaki shi ne, wannan koren abu, babu
abinda yake sai tiriri, tamkar daga cikin wuta yake
futowa!!
Ba shiri Armad yai sauri ya sunkuya ƙasa, lamarinda yasa
ya kubuta da ɗan taƙi kaɗan daga tsinin bakin wannan
shaho.
Sai dai kuma kafin Armad ya ƙarasa ɗagowa tuni wannan
shaho ya juyo a fusace, tamkar wanda aka hana abincin
daya halatta a gareshi ko kuma wanda aka hana
haƙƙinsa, ya kuma ƙara nufo Armad ta baya.
Kan kace meye wannan tuni yayi ƙasa-ƙasa ya kuma
ɗaura azamar ƙara kawowa Armad wata suka mai cike da
mugun nufi irin wanda shi kaɗai zai iya karayar da
rundunar abokin gaba hamsin da ɗoriya.
Ba shiri Armad ya wartsake daga halin da yake ciki, gami

da miƙa hannu ya kuma zare takobinsa.
Wata muguwar ƙara ce ta tashi, irin wadda ke tashi idan
ƙarfe ya haɗu da ƙarfe, a lokacinda tsinin bakin wannan
shaho ya haɗu da kaifin takobin Armad.
Wani abun mamaki daya firgita Armad shi ne bayan
haɗuwar takobinsa da bakin wannan shaho, kawai sai
allankatafur suka ƙi rabuwa da juna tamkar ansa wani
abu an ɗaure su a tare; a dai-dai lokacin Armad fincikar
takobinsa kawai yake amma ina, ko motsi bata yi.
Shi kuwa wannan shaho ya caka bakinsa akai shima baya
ko motsi. Lamarinda ya ƙara bawa Armad mamaki.
Abu na gaba da Armad yai shi ne dunƙule hannunsa na
dama, inda ya dubi wuyan wannan shaho, cikin zafin
nama ya kai masa wani mugun duka ya kuma ci sa'a ya
sameshi.
Amma bisa mamaki shahon ko gezau baiyi ba da niyyar
kaucewa hannun na Armad, haka ya barshi yaje ya haɗu
da wuyan nasa, lamarinda yasa wata ƙara ta tashi sama
mai kama da ana dukan dutse.
Idanunsa cike da mamaki Armad ya janye hannunsa cikin
mamaki da ɗimuwa, hannunsa yana karkarwa kamar
ba'a jikinsa yake ba.
Ba komai bane ya jawo haka ba illa abinda Armad yaji
bayanda ya daki wuyan wannan shaho. Wanda duk da
cewa gashi a ido wuya ne mai ɗauke da nama da jini,
amma a zahiri taurinsa yafi na jan dutse.
To amma da ace lamuran da Armad yake fuskanta anan
suka tsaya, toda da sauƙi matuƙa, to amma a dai-dai
wannan lokaci ne hannunsa dake riƙe da takobinsa ya
fara fuskantar wani abu.
Wannan kuwa ba wani abu bane illa ji da yayi takobinsa
ta fara rage nauyi, lamarinda yasa ya ƙurawa takobin tasa
ido domin tabbatarda ko abinda yake ji a hannunsa
gaskiya ne!
Sai dai kuma amma a lokacin ne akan idonsa ya fara
ganin takobin tasa ta fara rage tsayi da faɗi.
Duk da wannan abubuwa da suke faruwa, mamakin
Armad bai kai ƙololuwa ba, saida idonsa yakai kan
wannan shaho ya kuma ganshi acikin halin limshe ido,
bakinsa a kafe ajikin ƙarfen takobin.
Nan take Armad ya lissafa abubuwan dasuke faruwa ya
kuma gano cewa lallai wannan shaho mayarda takobinsa
abinci yai kurum, abinda ke faruwa kuwa shi ne shahon
yana zuƙe ƙarfen takobin ta Armad ne kawai ta wata
hanya da Armad bai taɓa jinta koda a karance-karancen
littattafan tarihi da yaƙi da yai a iyakacin tsahon
rayuwarsa.
Mamaki da ɗimuwa su ne abubuwan da suka cika masa
zuciya a wannan lokaci.
Sai dai kuma a lokacin ne ya fuskanci cewa wannan ba
lokacin ya tsaya yana mamaki bane, kasancewar wani
mummunan ƙaraji da yaji mai tsoratarwa ta bayansa,

wanda yasa nan take Armad ya juya izuwa ɓangaren da
yaji wannan ƙaraji.
Sannan kuma a lokaci guda wani abu ne yake faruwa
wanda Armad bai sani ba, wannan kuwa ba wani abu
bane illa haske da wannan takarda da wannan dattijo mai
suna HanDiyúza ya bashi, take tayi acikin aljihun
wandonsa!

Nidinne dai Shuraih Usman inkiya
99%
Daga taskar magajin wilbafos
MAGAJIN WILBAFOS
Marubuci: Dr Abdullahi Muhammad Ibrahim
Babi na 6: Kuskuren armad
Post by: Shuraih Usman
@shuraih 99%
www.facebook.com/hausaebooks
.
Armad na tsaye yana cikin yanayin tunanin maiya kamata
yayi har tsahon kimanin daƙiƙu biyu zuwa uku.
Kafin daga bisani ya ƙara jin irin wannan ƙaraji da yaji a
baya, lamarinda yasa ba shiri ya waiwaya ɓangaren da
ihun ya taso.
Inda idanuwansa sukai arba da wani ƙatoton miciji kore,
wanda a tsaye kaɗai yakai tsayin Armad wato taku huɗu,
a kwance kuwa yakai kamu sittin da ɗoriya.
Idanun micijin suma koraye ne kaf, kuma a buɗe suke
tar-tar, domin tun daga nesa Armad ya hangesu suna
bada sheƙin kore.
Sai dai kuma wani babban abin mamaki shi ne kana ganin
wannan miciji zaka fuskanci cewa ba'a cikin hayyacinsa
yake ba, domin gumi kawai yake sannan yana cikin halin
gudu mai tsanani tamkar wanda yaga mutuwa ido da ido.
Armad na tsaye baima gama karantar abinda ke faruwa
ya ƙara hango wata koriyar ƙura ta turnuƙe a can bayan
wannan miciji, kafin kuma daga bisani ya fuskanci cewa
ashe wata tawagar korayen namun dawa ce, irinsu su zaki
da damisa da kuma manya-manyan kuraye, dukkaninsu
koraye, sai dai kuma bisa mamaki dukkaninsu suma
gudun suke kamar ransu zai fita.
Yana cikin haka sai kawai yaji wannan wannan shaho
dake manne a jikin takobinsa ya fara karkarwa kamar
wanda ke cikin farfaɗiya.
Ba shiri Armad ya juyo da niyyar ganin meke faruwa,
inda yai arba da wannan shaho acikin wani yanayi na
firgici kamar irin wanda yaga wancan miciji na ciki.
Ba shiri Armad yaga wannan shaho ya fizge bakinsa daga
jikin takobin, inda cikin tsananin sauri da zafin nama ya
fara kaɗa manyan fuka-fukansa, tare da kuma yin sama

da juyawa ya doshi gabas.
Nan take Armad ya tabbatarwa da kansa cewa lallai akwai
wani abin tsoratarwa da yake saka waɗannan manyan
halittu wannan gudu. Saboda haka nan take shima
Armad, a irin girman rashin tsoronsa, ya yanke shawarar
maiya kamata yai.
Wanda ba komai bane illa ya tsaya yaga abinda yasa suke
gudun kafin shima yasan maiya kamata yayi.
Ko cikakkun daƙiƙu bakwai ba'ai ba, wannan halittu dake
ta gudun fanfalaƙi suka zo suka wuce inda Armad yake
tsaye, ko kallonsa babu wanda yai acikin su, lamarinda ya
ƙara bashi mamaki sosai. Domin a sannan ne ya tabbatar
lallai ko menene yasa waɗannan namun dawa gudu, ba
ƙaramin abin firgici da tashin hankali bane, kuma koma
menene ba abu bane da Armad ya kamata yai gangancin
tara ba, saboda nan take Armad ya fara tunanin yanke
sabuwar shawarar shima ya kamata ya ranta a na kare, in
yaso daga baya yaga mene ne!
Har Armad ya juya zai bi bayan waɗannan halittu, kawai
sai yaji ƙarar gudun ruwa, lamarinda yasa ala dole ya
juyo da niyyar ganin mai ya kawo ruwa wajen.
Tun kafin ya ƙarasa juyawa idanunsa suka fara karkarwa,
fuskarsa cike da mamaki, gashin jikinsa ya mimmiƙe,
sannan kuma a lokaci guda gumi ya fara keto masa.
Duk ba wani abu bane ya janyo haka ba illa abinda
idanun Armad suka gane masa da kuma abinda zuciyarsa
take ɗarsa masa.
Wannan abu ba wani abu bane illa wata ƙatotuwar igiyar
ruwa wadda girmanta yafi gaban misali, sannan kuma
launinta baƙi ne, baƙi ƙirin. Kuma wannan shi ne karon
fari da Armad yaga wani abu ba kore ba, tun bayan
shigowarsa wannan koriyar duniya.
Armad ne tsaye cak, kamar an riƙe masa agara, ya kasa
ko motsi. Babu abinda yake mamaki sai launin wannan
ruwa.
Kasancewar tunda yake bai taɓa gani ruwa mai launin
baƙi, baƙi-ƙirin irin wannan ba!
Sannan kuma wani abin mamaki ruwan ya tokare sararin
samaniya, ta inda baka iya gano ƙarshensa duk yadda ka
ɗaga kai.
Nan take Armad ya juya cikin tsananin sauri da niyyar da
fara gudun-tsira da rai, inda ya ɗaga ƙafarsa ta dama
gami da yin tsalle da niyyar fara gudu.
To amma rashin sani yafi dare duhu, juyawarsa keda
wuya sai kawai bisa mamaki yaji wani abu mai santsi
yana ƙoƙarin haɗiye shi, abu na gaba sai kawai yaga
ganinsa ya fara yin dishi-dishi, kafin daga bisani ya fara
jinsa akan iska wani mugun jiri yana ɗaukansa, inda ba
zato ba tsammani sai kawai tsintar kansa yayi a sume.
Bayan adadin wani lokaci da Armad bai iya tantancewa
ba, sai kawai farkawa yayi ya kuma tsinci kansa acikin
wani ɗaki.

Ya na buɗe ido jikinsa ya fara bashi cewa lallai akwai wani
kuskure daya aikata, duk da kuwa cewa bashi cikakkiyar
masaniyar menene, amma yana da yaƙinin cewa lallai
yayi kuskure a wani waje!
To babban abinda Armad bai sani ba shi ne, duk wani abu
da zakai a wannan duniya yana da sakamako, kama daga
kan motsi, numfashi, magana da dai sauransu. Kuma shi
ne babban amfanin wannan takarda mai ƙunshe da
bayanai da ɗalasimai da wancan mutun mai suna
HanDiyúza ya bashi.
Daga inda da Armad yake tsaye acikin wannan koriyar
duniya zuwa cikin wannan ɗaki tafiya ce ta sama da
shekara goma akan ingarman doki, wadda gabaki ɗaya
Armad yayi ta ba tare da ya sani ba.
Sai dai babban abin tambayar shi ne, a ina ya bayyana,
kuma ina ne cikin wannan ɗaki.
Ɗaki ne mara girma sosai, kuma samansa a buɗe yake
hanhai, sannan yana da bangwaye guda huɗu; gabas da
yamma, kudu da arewa.
Babban abin mamakin shi ne, kowanne bango launinsa
daban ne; bangon arewa shuɗi ne na kudu kuma kore ne
sai kuma na gabas da yamma waɗanda farare ne.
Babu ƙofa ko taga acikin wannan ɗaki.
A tsakiyar ɗakin akwai wata ƴar ƙaramar shirwa ta
zinare.
Wannan shirwa ta kasance an gina ta akan wani gadan
aba'i wanda sai mutum yabi takansa sannan zai iya kaiwa
gareta.
Bayan tsahon lokaci Armad na tsaye yana mamakin
bayyanarsa a wannan waje, sai kawai ya yanke shawara
ya gwada zuwa wajen wannan shirwa ya duba ko zai
tadda wani abu.
Yana isa matattakalar gadon aba'in nan ya tsaya, ya fara
dube-dube yana tunanin maiya kamata yayi, amma bisa
mamaki kan ya yanke wata shawara yaga bakin wannan
shirwa ya fara buɗewa da kansa ba tare ya taɓa komai ba.
Kan kace meye wannan ya buɗe hanhai.
Wanda sai a dai-dai lokacin ne Armad ya kula da hasken
da takardar dake aljihunsa take yi. Inda nan take ya zira
hannu ya fito da ita.
Nan take ya fara karantawa, tunda daman karatu da
rubutu a wajensa ba matsala ba ne, musamman yanayin
yadda mahaifiyarsa ta matsa masa tun yana yaro akan
karance-karancen abubuwa da dama, wanda har a
wannan lokaci Armad bai san amfanin da dama daga
cikinsu ba, ko kaɗan.
Ba komai ake bayani acikin wannan takarda ba sai
umarni da ƙaidojin yadda za'a fita daga cikin wannan
duniya, wanda ganin hakan ne yasa Armad ya fara
fuskantar abinda ya faru dashi a baya acikin wancan
koriyar duniya daya bayyana. Sai dai kuma Armad bashi
da lokacin tsayawa tunani a lokacin.

Nan take cikin sauri ya karanta wasu ɗalasimai daga cikin
takardar sannan ya tofa acikin bakin shirwar nan data
buɗe. Sannan ba tare da ɓata lokaci ba ya dawo tsakiyar
wannan ɗaki, wato kusan daidai inda ya fara bayana a
karan fari kenan.
Daga nan ya dubi kudu, inda kai tsaye yayi taku biyar,
idonsa a buɗe, kafin daga bisani ya rufe ido ya ƙara wasu
taku biyar ɗin.
Sannan ya tsaya cak yana duban wannan bango, kamar
wanda ke tsammanin wani abu ya afku.
Yana tsaye a haka ba jimawa sai wannan bango ya fara
ƙara kamar ana buɗe ƙofa, kuma kafin a jima, gaba
ɗayan bangon ya fara girigiza, inda daga bisani ya karkace
ɓari ɗaya ya bada hanya kamar an buɗe ƙofa.
Yana ganin haka, ya ɗanyi tunani kaɗan, kafin daga bisani
ya faɗa cikin ƙofar.
Shigarsa keda wuya wani haske ya kashe masa ido tsahon
daƙiƙu, inda bayan ya washe ya tsinci kansa a wani fili na
daban.
Babu alamun rayuwa a wajen ko ɗaya, ko'ina ka kalla
babu abinda yake tashi sai yanayin kaɗaici.
Daga can nesa ɓangaren gabas akwai wasu manyamanyan tsaunuka guda biyu, wanda baya iya hango
ƙarshensu daga inda yake.
A tsakiyarsu kuma abin mamaki wani ƙasaitaccen gari ne,
amma babban abin mamakin shi ne tun daga inda yake
yana iya hangen yana ta rufe garin ruf, tayadda daga
yawan yanar kaɗai zaka iya ƙiyasta cewa anyi shekara
sama da dubu babu wanda ya shiga wannan gari.
Bisa mamaki sai Armad yaji tsananin son ya shiga cikin
wannan garin duk da bai san mai yasa ba, kuma yana da
cikakkiyar masaniyar cewa kafin yai wani abu akwai
abinda ya kamata ya karanta acikin wannan takarda.
Amma kuma duk da haka yana ji tamkar rayuwarsa ta
ta'allaƙa da shiga cikin wannan gari.
Saboda haka bai san lokacin da ya ɗaga ƙafa da niyyar isa
gun waɗannan tsaunika ba, da niyyar ya ɗan leƙa ciki
kawai yaga meye aciki.
Haka kuwa akai, cikin rashin tsoro, Armad ya nufi ƙofar
garin, inda yana zuwa yasa hannunsa ya fara cire ƙoƙarin
cire yanar data lulluɓe ƙofar.
Haka kuwa akai, ba jimawa ya gama cire ta, lamarinda
yasa ƙofar garin ta bayyana a sarari yadda yake iya
ganinta.
Sai dai kuma wani abu daya bawa Armad mamaki shi ne,
ba kamar yadda yayi tunani ba da fari, ƙofar garin a buɗe
take maimakon a rufe. Domin yana ɗan tura ta kaɗan ta
tafi ta fara biɗe kanta hanhai.
Lamarinda saida yasa Armad ya ɗan jada baya kaɗan,
kafin daga bisani ya yanke shawara ya kuma shiga cikin
wannan gari.
Shigarsa keda wuya, takunsa na farko ya tsaya cak a inda

yake,abu na gaba kuwa daya gani saida yasa nan take duk
da ɗimbin rashin tsoro na Armad saida jikinsa ya fara
karkarwa. Kuma kan kace meye wannan tuni ya fara
ƙoƙarin jada baya cikin sauri da niyyar ficewa daga cikin
garin kasancewar tuni ya daɗe da yin nadamar saka ƙafa
aciki, da kuma tabbatar da cewa yayi kuskure!
Sai dai kuma amma ina a dai-dai wannan lokaci ne yaji
ƙasar wajen da yake tsaye ta haɗiye shi zuwa idan sahu.
Ala dole haka ya tsaya cak a inda yake, bashi da ko niyyar
juyawa baya, ya kuma ƙurawa abinda ke gabansa ido,
abisa dole.
Ba komai Armad yake gani ba illa wasu mutane manyamanya mutane samfurin adawa. Kowannensu cikin kayan
yaƙi irin na al'ummar farko, sannan kuma a jere suke a
layi; kowanne layi yakai mutun casa'in zuwa ɗari, sannan
kuma akwai layika kusan guda goma a jere.
Babban abin tsoron daya firgita Armad shi ne babu
alamun canji na tsufa ko kuma gajiya ko kaɗan a jikin
waɗannan mutane, wato dai kamar fitowarsu kenan zasu
fita yaƙi, kawai motsi ne da basa yi. Domin idan badan
wata kakkaurar yana data rufesu ba to da babu ta yadda
Armad zai iya gane cewa wannan mutane sunyi shekaru
aru-aru a tsaye basu motsa ba.
Sannan kuma babban abin mamakin shi ne dukkansu
idanunsu a buɗe yake, kuma acike da tsananin tsana da
baƙin ciki. Sun kasance acikin yanayi na ɗaga kai suna
kallon sama kamar wanda suke kallon abokin gaba a kan
ƙasar dake samansu.
Irin tsananin faɗuwar gaban da Armad yake fuskanta
idan ya kalli waɗannan mutane irin wadda bai taɓa ji
bace.
Sai dai kuma duk wannan ba shi ne abinda ya razana
Armad ba, kuma yasa yake ƙoƙarin ficewa daga cikin
duniyar ba.
Wannan abu kuwa ba wani abu bane illa wata murya da
Armad yake ji a kunnensa, wadda tafi kama da muryar
manya-manyan sarakunan aljanu ma'abota Izza
maɗaukakiya, irin Izzar nan wadda ita kaɗai zata sa kaji
dole saika durƙusa akan gwiwowinka ka kai gaisuwa idan
kai arba da ita.
Abinda kuwa da wannnan murya take cewa shi ne;
"NI BAYAJIDDA ƊAN ALMA'ATA ƊAN DJINN ƊAN
ODUDUWA ƊAN IKENGA DA HÁRÚNU ƊAN
MASARAYÚLÚ, INA MAI RANTSUWA DA MAHALICCIN
SARKI WILBERIYA, BAZAN TAƁA DENA YAƘAR KUBA, KU
MA'ABOTA BAƘAƘEN IDANUWA (URÚRU).
"KODA KUNYI AMFANI DA WANNNAN LA'ANANNIYAR
IZZAR DA KUKA GADA ACIKIN WAƊANNAN BAƘAƘEN
IDANUWA NAKU, KUN HANANI TAKA DORON ƘASA, TO
NI KUMA ZAN YAƘE KU A TSAYE A INDA NAKE.
"IDAN MA KUMA KUKA YI AMFANI DA WANNAN
TSINANNIYAR IZZA DAKE CIKIN BAƘAƘEN IDANUWAN

KU, KU KA HANANI MOTSI, TO NI KUMA ZANYI AMFANI
DA BAKI NA NA YAƘE KU.
"KAI KODA KUNYI AMFANI DA WANNNAN KORARRIYAR
IZZAR DAKE CIKIN BAƘAƘEN IDANUWAN KU, KUN
HANANI MAGANA, TO NI KUMA ZANYI AMFANI DA
ZUCIYA TA NACI GABA DA YAƘARKU.
"KAI KODA KUNYI AMFANI DA BAƘAƘEN IDANUWAN KU,
KUN KASHE RUHI NA, BAZAN DAINA YAƘARKU BA, BAYAN
NA MUTU!!!" Bayanda muryar tazo nan a zancenta saita
ɗanyu shiru, kafin daga ƙarshe ta rufe da jimla guda
ɗaya!
"URURUUUUUU, DUK MASIFAR DA AL'UMMA KE CIKI KU
NE SANADI!!!"
A dai-dai lokacin da Armad ya gama jin waɗannan
maganganu wanda yake jinsu suna tasowa daga can cikin
garin nan, tuni ya faɗi ƙasa akan gwiwowinsa, jini ne
kawai yake feshi daga idanunsa da bakinsa da hancinsa.
Hankalinsa kuwa tuni ya gushe. Sai dai kuma abu na
ƙarshe da Armad yai tunani a ransa kafin ya ƙarasa suma
shi ne, "wannan ba wani abu bane illa kawai muryar
wannan mutun mai suna BAYAJIDDA, wadda take neman
halaka ni, kawai saboda na saurare ta!
"To mai zai faru idan da shi wannan mutumin na ainihin
ne ya tsaya a gabana!!" Armad ya ciji yatsa gami da girgiza
kai, sannna ya rufe da cewa;
"Lallai bani da ƙarfin Izza, lallai ya kamata na ƙara zage
dantse, dan idan ba haka ba babu inda zanje acikin
duniyar da mutane irinsu BAYAJIDDA suka rayu!!!"
Waɗannan sune kalaman da Armad yake ta faɗa acikin
zuciyarsa a yayinda ya suma a bakin ƙofar wannnan gari
mai ban al'ajabi!!!
Copyright © 2017 A M IBRAHIM . All rights reserved
Nidinne dai Shuraih Usman inkiya
99%
Daga taskar magajin wilbafos
MAGAJIN WILBAFOS
Marubuci: Dr Abdullahi Muhammad Ibrahim
Babi na 7: Gimbiya Nostoljiya Nara
Post by: Shuraih Usman
@shuraih 99%
www.facebook.com/hausaebooks
.
A babi na shida mun tsaya a inda Armad ya faɗi a sume
cikin wannan gari, bayan jin wannan murya. Yanzu zamu
ɗora;
***
Babban abinda Armad bai sani ba shi ne, wannan murya
da yaji ta kasance kullum saita maimaita sak irin abinda
yaji tana faɗa sau casa'in da tara.
Bata taɓa fashin yin hakan ba, sannan kuma babu wani
mahaluƙi daya taɓa shiga cikin wannan garin tun bayan

da muryar ta fara maganar, sama da shekaru dubu
kenan, sai Armad.
A dai-dai wannan lokaci, Armad yana kwance a sume
baisan inda kansa yake ba, sannan kuma bashi da
masaniyar cewa duk sanda wannan murya ta gama
maganarta, gaba ki ɗayan iskar wannan gari kamawa take
da wuta, badan komai ba sai dan tsananin ƙarfin Izzar
dake ƙunshe cikin muryar.
Kuma hatta a wannan lokaci, abinda ya afku kenan;
ɗaukewar muryar keda wuya, gabaki ɗayan ilahirin iskar
dake cikin garin ta fara ɗaukan zafi.
Sai dai kuma a dai-dai wannan lokaci ne wasu tafkatafkan jajayen kunami masu kafafu Irin na mutane,
wanda a tsaye sunkai girman ƙananun giwaye, suka
bayyana a dai-dai inda Armad yake.
Kana ganinsu zaka tabbatar da cewa a matuƙar fusace
suke, saboda yanayin yadda suke kallon Armad, wanda ke
kwance a sume baima san abinda ke faruwa ba.
Waɗannan kunami guda biyu ba wasu bane illa masu
tsaron wannan gari.
Kasancewar a dai-dai lokacin da Armad ya shigo garin
suka ji shigowarsa, to amma saboda wasu dalilai basu
bayyana ba saida ya suma. A wannan lokaci ne suka
rikiɗe izuwa siffar mutane sanye da tufafi irin na can-can
mutan da, launin ja da rotsi-rotsi, sannan kuma da irin
hular nan mai lankwasa da tsoffin da suke sawa.
Na hannun daman ya dubi na hagun tsahon ƴan daƙiƙu,
kafin daga bisani ya fara magana a nutse da cewa, "zuri'ar
Wilbafos ne, kuma ko badan komai ba, saboda alaƙar
dake tsakanin shugaba Amraikugyu da Wilbafos-na-shida,
bai kamata mu halaka shi ba."
Yana zuwa nan a zancensa yai shiru tare da ci gaba da
duban ɗan'uwan nasa, kamar yana jira yaji mai zaice. Shi
kuwa babu abinda yai illa sunkuyawa, ya kuma dangwali
jinin dake malale a gaban farar rigar Armad.
Wanda ya ƙura masa ido tsahon daƙiƙa kusan talatin
kamar wanda yake karanta wani haɗaɗɗen littafin da
baya son ɗauke ido. Can daga bisani ya ɗago kai ya dubi
wannan ɗan'uwa nasa da yai magana da fari tare da
cewa, "abinda ka faɗa gaskiya ne, to amma kuma bai
kamace mu ba, mu tseratar dashi."
Yana gama faɗar haka ya miƙe, inda dukkaninsu suka
kyaɗa kai alamun amincewa, kafin daga bisani su ɓace
ɓat, babu su babu alamunsu.
Sai dai kuma a dai-dai wannan lokacin tuni wuta ta fara
tashi acikin wannan gari. Kuma duk wani abu da zaka iya
gani wutar nan bata barinsa.
Ba jimawa kayan jikin Armad suka fara ci da wuta, kan
kace meye wannan tuni fatar jikinsa ma ta fara kamawa.
Ana cikin haka sai kawai wannan takarda dake cikin
aljihun Armad ta bada wata ƴar ƙaramar ƙara, mai kama
da an fasa tulu. Inda ita ma ta fara cida wuta, kuma kan

kace meye wannan tuni ta ƙone.
Armad na kwance a sume, sannan kuma ga jikinsa ya fara
cida wuta, sannan kuma ga takardar da ke ƙunshe da
ɗalasiman da zasu fitar dashi daga cikin wannan duniya
su kaishi zuwa doron ƙasa ta huɗu inda yake sa ran fara
neman Tirifil-fakta, ta ƙone.
Lallai da idonsa biyu da ana tamabayarsa zai yadda da
cewa yana cikin mafi munin halin da zai iya samun kansa
a ciki a wannan lokaci!!!
***
Sai dai kuma a dai-dai wannan lokaci ne da Armad ke
kwance a sume, a can wani ɓangare na duniya, wani
ƙatoton lambu ne, wanda idan ka ƙiyasta girmansa sai
kaga shi kaɗai yakai kimani girman wasu ƙauyukan.
Wasu irin dogayen bishiyu ne na ƙasaita da isa da
alfarma, masu fala-falan ganyayyaki, yawanci masu
launin kore, yalo da ja suka kewaye dukkan wannan
lambu. Daga cikinsa kuma ƙananun bishiyu ne a jejjere a
layi-layi sahu-sahu. Babu komai akan waɗannan bishiyu
banda ƴaƴan itatuwa kala-kala masu yawan gaske,
waɗanda tsabagen yawansu da dama daga cikinsu ma
idon bil'adama bai taɓa gani ba.
Sannan kuma a tsakankanin waɗannan bishiyu dake jere
akwai wasu ƙoramu suna kwaranya, masu ɗauke da wani
tataccen ruwa garai-garai, wanda saboda kyawunsa, kai
kace ba daga duniyar nan yake ba.
Dukkanin waɗannan abubuwa sune suka sa tun daga
nisan sama da tafiyar kwana ɗaya da wuni mutun zai iya
fara jin ƙanshi mai sanyaya rai, na tashi daga cikin
wannan lambu.
Sai dai kuma a zahirin gaskiya duk wannan bashi ne
abinda yasa wannan lambu ya zama na musamman ba.
Abun kuwa da yasa hakan ba wani abu bane illa wani ɗan
ƙaramin gida dake a tsakiyar wannan lambu, wanda yake
ta bada wani irin haske mai tsananin ƙawa da kyawun
tsari, wanda bazai taɓa misaltuwa dai-dai da dai-dai ba.
Kuma wani babban abin mamakin shi ne babu alamun
wata fitila wadda za'a ce ita ke bada wannan haske, a'a sai
dai kawai hasken na ɓullowa ne daga cikin wannan gidan.
Acikin wannna gida kuwa akwai wani ɗaki wanda shima a
tsakiyar gidan yake. Kuma abin mamaki dukkan wannan
haske da wannan gida yake bayarwa asalinsa daga
wannan ɗaki yake fitowa.
A dai-dai wannan lokaci wasu mutun biyu ne a tsakiyar
wannan ɗaki akan wani gadon alfarma da aka yiwa ado
da fatar fararen aljanu.
Waɗannan mutun biyu ba wasu bane illa wata budurwa
da kuma wata dattijuwa wanda ba daban kayan dake
jikinsu sun banbanta suba, da idan ka kalle su ta baya sai
saika ce ma ƴa da uwa ne, saboda dukkanin jikinsu haske
yake.
Amma ina, kallo ɗaya kacal zakai ka tabbatar da cewa

lallai ratar dake tsakaninsu irin wadda ke tsakanin
sarauniya da kuyangarta ce.
Domin kuwa bisa ƙololuwar mamaki, duk wannan haske
dake tashi wanda ya mamaye mutanen biyu da kuma
gidan baki ɗaya, sannan kuma har yake fita waje yana
haskaka wannan lambu baki ɗayansa, daga jikin wannan
budurwa yake tashi.
Tun daga baya idan ka dubi wannan budurwa zaka ji wani
tsananin gwarjini irin na manyan sarakunan farko na
tashi daga jikinta, wanda shi kaɗai zai iya saka maka
tsananin firgici da tunanin wace ce wannan budurwa.
Amma kuma wani ƙarin abin mamakin shi ne hatta
wannan dattijuwar dake kama da kuyangar wannan
budurwa, Izzar ta takai mataki na ɗari uku da arba'in da
biyu, wanda hakan zai ƙara nuna ma girma da falalar
wannan budurwar.
A dai-dai wannan lokaci wannan dattijuwa ta kyaɗa kai
alamun amincewa. Kai daka gani kasan cewa basu daɗe
da gama tattauna wani abu mai matuƙar muhimmanci
ba. Sannan kuma ta tashi daga inda take ta nufi jikin
bangon ɗakin da wannan budurwa take fuskanta, inda ta
tsaya ta kira sunan wani ɗalasimi, "Hai-há-ka!"
Faɗar wannan ɗalasimi keda wuya kawai sai wannan
bango ya fara haske, inda kan

Please Login or Register in order to submit comment