Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

bakwai, sannan yana
sanye da wata baƙar hula da aka sarrafa da fatar aljanu
zalla. Abin mamaki ɗauke a kafaɗun wannan aljani
hankakan mutuwa ne baƙaƙe har guda biyu. Yana
bayyana ya faɗi yai gaisuwa ga Bihanzin yana cewa, "Ya
shugaba na. Mai kake buƙata?"
Bihanzin ya amsa da cewa, "mahaifiyar wannan yaro na
fama da cutar izza, ina so ka bata shekarun izza daga ɗaya
zuwa dubu ashirin. Iyakacin yadda zai ishe ta ta warke."
Aljanin ya ware samudawan hannayensa guda biyu yana
cewa, "An gama ya shugabana."
Nan take wani jan haske mai ɗaukar ido ya fara taruwa a
hannayen wannan aljani kafin daga bisani ya karkatar da
hasken izuwa gare ta. Hasken na taɓa ta jikinta ta fara
girgiza kamar mai farfaɗiya. Armad yai wuf zai riƙe ta
amma Bihanzin ya riƙe shi yana cewa, "Kada ka damu,
shekarun Izza ne ke shiga jikinta."
Haka Armad ya haƙura yana kallon mahaifyarsa wannan
jan hasken na shiga jikinta tsahon lokaci. Saida akai sa'a
guda acikin wannan hali sannan hasken ya ɗauke, aljanin
ya dubi Bihanzin ya ce, "An gama ya shugaba na. Na bata
shekarun izza dubu goma sha huɗu da dari biyu da sha
uku, kuma a lissafi na zata farka nan da wata tara."
Cikin sauri Armad ya durƙusa a gefenta yana share mata
gumi. Yana cikin haka kawai sai yaga a karo na farko
acikin shekaru uku mahaifiyarsa tayi motsi. Cikin murna
yai ihu yana niyyar yin tsalle yai shewa kawai sai yaga ta
buɗe ido. Ta kalli Armad, Armad ya kalleta. Nan take
hawaye ya fara zuba daga idanunsa. Ta buɗe baki zatai
magana amma kafin tayi magana saita ƙara komawa ta
suma. Amma duk da haka murnar Armad bata ragu ba.
Yana cikin haka yaji muryar Bihanzin a kunnensa. "idan
ka daɗe da yawa acikin wannan waje komawa duniyar
daka fito zaiyi maka wahala."
Armad najin haka ya maida mahaifyarsa cikin zoben
sannan cikin murna da annushuwa irin wadda ba'a taɓa
ganinsa aciki ba ya biyo bayan Bihanzin suka nufo waje.
Koda suka dawo cikin wannan ɗaki sai suka tarar da
Nostaljiya na tsaye tana jiransu. Tana ganin murnar dake
fuskar Armad ta fashe da murmushi, lallai tasan an samu
abinda ake nema. Koda Bihanzin yaga haka saiya dubi
Armad ya ce, "Ni zan barku anan. Ka tuna da abinda na
gaya maka. Ka zama CIKAKKEN MUTUN."
Babi na 100: Shawarar Armad
**
Armad da Nostaljiya suka nufi hanya izuwa ɗakin da aka
saukeshi. Akan hanyarsu kowa yayi shiru bai ce komai ba.
Nostaljiya tana jira Armad ya gaya mata abinda suka
tattauna da mahaifinta amma Armad yayi shiru. Ita kuma
bata tambaya ba.
Koda isarsu ƙofar ɗakin sai Armad ya shige ɗakin ba tare
da yace uffan ba sannan ya turo ƙofa. Nostaljiya ta buɗe
baki zatai magana amma ta fasa. Cikin ɓacin rai ta juya ta
tafi. Har ta kusa ƙulewa ta juyo ta dubi kuyangar dake
ƙofar ɗakin ta ce, "Ku bashi duk abinda yake buƙata, idan
ya nemi ku nuna masa hanyar fita daga fada ku nuna
masa." Tana rufe baki ta juya ta tafi.
Armad ya faɗa kan gado yana jinta harta ƙule. Yai shiru
yana tunanin maganarda Bihanzin ya gaya masa. Abu ne
mai sauƙi tunda mahaifiƴarsa ta sami sauƙi ya fice daga
wannan daula kada ya ƙara waiwayarta. Yaje can wani
waje ya tsara sabuwar rayuwarsa cikin kwanciyar hankali.
To amma Armad yasan cewa tun daga ranar da yayi
rantsuwa zai tarwatsa cinikin bayi rayuwarsa baza ta ƙara
kasancewa cikin kwanciyar hankali ba. Irin wannan
rayuwa wadda za'ai aure a haihu a sami ƴaƴa biyar ko
goma, sannan a zauna cikin kwanciyar rai har a tsufa a
mutu ba tasa bace.
Dama dai tuntuni abinda yasa Armad bai maida hankali
ba akan shirinsa na tarwatsa cinikin bayi shi ne halinda
mahaifiyarsa ke ciki. Amma ga dukkan alamu wannan ya
kau. A yanzu ne lokaci mafi dacewa daya kamata ya fara
aiwatar da shirinsa.
Auren Nostaljiya lallai zai ɗaukaka martabarsa a idon
duniya kuma zai saka rundunar sarki Bihanzin ta zama
kamar tasa. Daɗin daɗawa daga abinda Nostaljiya ta gaya
masa a wancan lokaci da suka haɗu, akwai rigima
tsakanin sarakunan Jinzidal tayadda kowannensu zaiso
yaga bayan ɗan'uwansa. Duk da cewa manufar Bihanzin
ta yaƙi da sauran sarakunan Jinzidal ba lalle bane ta zama
ɗaya data Armad ba, amma dukkaninsu suna da abokan
gaba iri ɗaya.
Matsala ɗaya ita ce; shin Bihanzin akan kansa yana so ya
tarwatsa cinikin bayi ko kuma kawai yana so ya tarwatsa
sarakunan Jinzidal ne? Domin zata iya yiwuwa Bihanzin
yana goyon bayan cinikin bayi amma yana rigima da
sarakunan Jinzidal.
Armad na zuwa nan a tunaninsa ya yanke shawara, Idan
har Bihanzin ya amince ce zai taimake shi ya rusa gasar
Jinzidal to shima zai taimaka masa ya karya sarakunan
Jinzidal.
Bayan Armad ya cimma wannan matsaya saiya fito da
Maikiro Inara daga cikin zobensa. Har izuwa wannan
lokaci Inara bai farfaɗo ba, amma ga dukkan alamu ruwa
kawai yake buƙata.
Ai kuwa Armad yana yayyafa masa ruwa ya farka, inda
Armad ya kwashe dukkanin labarin daya afku bayan ya
suma ya gaya masa. Inara ya taya Armad murnar samun
lafiyar mahaifƴarsa sannan yayi masa fatan alkhairi.
---------
Armad da Inara suka kwana acikin wannan ɗaki, washe
gari da safe Armad ya kaisu wannan tafki sukai wanka
sannan suka ci suka sha. Bayan sun dawo ɗaki Armad ya
fara jira ko zaiga Nostaljiya amma shiru har yamma ta
kawo kai rana ta faɗi ba labari. Da magariba Armad ya
tura ɗaya daga kuyangin dake kawo musu abinci ta kira
masa Nostaljiya amma bisa mamaki hakan bata samu,
Nostaljiya ta amsa amma bata zo ba. Haka ya gaji da jira
har dare yayi gari ya waye.
Washe gari Armad ya ƙara tura wata kuyangar, Noltaljiya
tace taji amma har dare yayi bata zo. Nan take Armad ya
fara shiga damuwa saboda yasan haƙiƙanin dalilin da
yasa Nostaljiya bata amsa kiransa ba.
Washe gari Armad ya yanke shawara ya taka yaje wajenta
da kansa. Koda ya fito bakin ƙofa saiya tarar da ɗalibinsa
Inara na tsaye yana gadin ƙofar. Murmushi kawai Armad
yayi ya bashi umarnin yazo ya rakashi.
Armad ya dubi ɗaya daga cikin kuyangin dake wajen ya
ce, "Muje ki rakamu wajen gimbiya."
Amma wannan kuyanga ta kada baki ta ce, "Ai ba'a shiga
wannan ɓangare daga mu kuyanginta sai ita kanta,
gimbiya."
Maganar bata yiwa Armad daɗi ba, ya tsaya yana ta
tunani kafin daga bisani ya juya ya koma ɗaki. Har ya isa
bakin ƙofa sai wata dabara ta faɗo masa, yaci birki ya
tsaya tare da juyowa izuwa wannan kuyanga ya ce, "muje
naga wajen saboda tsaro."
Kuyangar fara ce mai tsaho sanye da farar doguwar riga.
Tana jin abinda Armad ya ce ta zare ido tana mamaki.
Abinda bata gane ba shi ne mai Armad yake nufi da
'saboda tsaro'. To amma ba muhallinta bane a
matsayinta na kuyanga ta tsaya tana yiwa Armad
tambaya, saboda haka ta shige gaba ta fara tafiya, su
Armad suka bi bayanta.
Abin mamaki sai Armad yaga sun ɓulle ta wata ƙofa
wadda ta shigar dasu wani ƙaton fili. Duk kewayen da
Armad yayi na kwana biyu bai san da wannan filin ba.
Haka suka ci gaba da bin kuyangar har suka ƙarar da
wannan fili suka nufi ɓangaren arewa, sannan daga bisani
suka iso wata farfajiya mai yawan bishiyun dabino.
Wannan bishiyun dabino sun kekkewaye wannan sashi ta
yadda ba'a iya gano cikinsa sosai. Suna ƙara matsowa sai
Armad ya fuskanci cewa wannan ɓangare an raba shi ne
izuwa gida uku manya-manya. Abin mamaki shi ne hatta
katangar da aka kewaye wannan waje da zinare aka yaɓe
ta. Komai kawai walwali yake. Nan take Armad ya fara
tunani yana mamakin irin dukiyar dake cikin wannan
fada.
Suna isowa gindin wannan bishiyu sai wannan kuyanga ta
tsaya tana nuni da ginin dake tsakiyar gine-ginen guda
uku. "Wancan ne na tsakiyar. Na ɓangaren dama kuma
na ƴarima Kiru ne, na ɓangaren hagu kuma na yarima
Hasanu me. Amma daga nan babu wanda yake da damar
haurawa sai su ƴaƴan sarkin uku."
Tuni Armad ya gama lissafa yadda zai biyo dare ya haura
wannan katanga sai kawai wani haske mai kashe ido ya
haske masa ido. A zuciyar Armad ya gane wannan haske
amma yana ji a ransa wataƙila kawai dai idonsa ne.
Amma ba jimawa wanda ke ɗauke da hasken ya bayyana
daga bayan wannan bishiyun dabino.
Lallai Armad yayi gaskiya, domin kuwa ba idonsa bane.
Wannan haske hasken Farar-takobi ce, wato takobin
yarima Kiru Sisiyu ɗan sarki Bihanzin wanda suka fafata
da Armad shekaru da dama da suka gabata.
Kiru ya fashe da dariya tun kafin ya iso. "Ko baka zo nema
na ba zan neme ka. Domin kuwa bamu idar da
fafatawarmu dakai ba a wancan zamani. Da sannu zaka
gane ƙarfin Farar-takobi na."
A zahiri Armad ba wajen Kiru yazo ba, amma babu yadda
zaiyi. Wannan fafatawa kamar anyi ta ne an gama.
Armad ya fara magana yana leƙen saman benen ko zai
hango Nostaljiya, "K....kiru, lallai naji daɗin ganinka,
domin kuwa ina neman wanda zan wasa takobi na dashi."
......
Allah cikin ikonsa a yau mun riski posting na Dari 100 wanda ya kusan kai mu wajen watanni Hudu,
A lokacin da Dr Abdullahi ya fara post na littafin nan sai da yayi shekaru Biyu 2 kafin ya kawo chapter 100,
,
In bazan manta ba tun a shekarar 2016 Dr ya fara rubuta littafin Magajin Wilbafos wanda har yanzu yana kan aikin rubutawa bai idar ba
.
Cikin watanni mu gashi mun kada chapter 100 har mun kusan mu riski Dr,
.........
Toh jama'a zan dan Huta na Sati Daya kafin na cigaba da kawo maku littafin, amma kafin nan in baku manta ba lokacin da muka idar da chapter 1-50 mun hada su gaba daya a matsayin document inda na saka su a wepsite dina,
Haka wannan karon ma zamu hada tun daga chapter 51-100 a waje guda cikin manhajar document mu sake shi a wepsite namu na Ebook
.
Ebook din zai fito daga nan zuwa JIBI sai a ankare
---------
Na barku lafiya its Shuraih Usman
Inkiya 99%
MAGAJIN WILBAFOS
Fita na biyu 2
Marubucin littafin
Dr Abdullahi Muhammad Ibrahim
Ebook creat by Shuraih Usman
Ebook publish by www.hausaebooks.cf
Ebook din nan yazo maku ne daga shafin www.hausaebooks.cf
Kuna ziyartar shafinmu don samun sababbin littatafai
Ga duk wanda ke bukatar ebooks nashi ya samu shiga cikin wepsite namu sai ya turo mana da littafin ta Email namu [email protected]

An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels


Please Login or Register in order to submit comment