Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

wanda ke nunawa
Armad, kamar basa buƙatar suji abinda yaji.
Ba jimawa Armad ya haɗa ɗaya biyu, ya kuma gane cewa
lallai akwai yiwuwa wani daga cikin wannan mutun uku
nada Izzar da take iya duba abinda ke cikin kan mutane.
Kuma akwai yiwuwar anyi amfani da ita akansa, a
wannan lokacin.
Wannan tunani na shiga kansa ya ɗaga ido ya bisu da
kallo ɗaya bayan ɗaya. Yana zuwa kan wannan budurwa
ya tsaya.
Ba dan komai ba, saboda wani abu a jikinsa na gaya masa
cewa tabbas, koma mai ya faru ita ce, musamman idan
ya tuno da yadda yaga samarin biyu sun kalle da farko.
Armad ya gayawa kansa cewa koma dai mai ya faru, lallai
a wannan lokaci basa buƙatar ya gaya musu wani abu,
domin kuwa gashinan a gabansa ana tattauna ta wacce
hanya yafi kamata a kashe shi, wanda hakan ya bashi
dukkan tabbashin da yake nema.
Abin al'ajabi mutanen da basu daɗe hira dasu ba amma
gashi suna tattauna ya zasu halaka shi a gaban idonsa
kamar ma baya wajen; babban nasu ya ce kawai su
ɗaureshi su cillashi acikin ruwa, ƙaramin ya ce kawai su
sare masa kai da takobi a wajen, macen kuma bata ce
komai ba da farko.
Sai da taga sun rasa wacce zasu zaɓa aciki, har suna
neman jefa ƙuri'a, sannan ta dubi babban nasu tace,
"ahhh, mai zai hana, a haɗashi da yaya Kiru su fafata, in
yaso idan suka gama faɗan sai ku san mai zaku yi dashi
daga baya." Kamar wadda take tsoron kada suƙi yadda da
shawararta, sai tayi sauri taci gaba da cewa;
"Badan komai ba, saboda inason naga faɗan Yaya Kiru, da
kuma sabuwar fasahar da kace ka koya masa!"
Tana rufe baki babban nasu yai murmushi gami da
girgiza kai, ya ce, "a'ah, ki bari idan munje gida....."
Amma ina tun kan ya rufe baki ƙaramin da ta kira da
Yaya Kiru ya miƙe tsaye gami da duban babban nasu ya
ce, "Yaya Hasanu, kullum kana gaya mana wataran mu
zamu kare Burja, kuma wataran mu zamu tsaya a gaban
filin daga mu jagoranci yaƙi ko, to ina roƙonka daka bani
wannan dama na nuna maka Izza ta!"
Yana gama faɗa ya sunkuyar da kansa ƙasa, amma tun
daga nesa zaka iya jin yanayin marmarin yaƙi na tashi
daga jikinsa. Babu abinda yake jin tsoro face Yayan nasa
ya ce a'a.
Amma yana cikin wannan hali yaji yayan nasa ya ce,
"tohhh!
"Nuna min na gani! Kai sani ina sa ran ganin abinda zai
faranta min rai!!"
Amma yana cikin wannan hali yaji yayan nasa ya ce,
"tohhh!
"Nuna min na gani! Kai sani ina sa ran ganin abinda zai
faranta min rai!!"

Nidinne dai Shuraih Usman inkiya
99%
Daga taskar magajin wilbafos
MAGAJIN WILBAFOS
Marubuci: Dr Abdullahi Muhammad Ibrahim
Babi na 9: Farar Takobi
Post by: Shuraih Usman
@shuraih 99%
www.facebook.com/hausaebooks
.
Armad ne da Kiru a tsaye su na fuskantar juna, kowa da
tasa takobin a zare!
Tun dai ƴan mintuna da suka gabata, Hasanu wanda shi
ne babban wannan tawaga ya kwance Armad ya kuma
bashi takobinsa. Abinda kawai ya rage shi ne Kiru ya
nunawa Hasanu da wannan budurwa, wadda ta kasance
ƙanwarsa, irin sabuwar fasaha, da ya koyo.
Fuskar Armad bata canja ba ko kaɗan, tamkar babu
abinda ke faruwa, yana riƙe da ƙotar takobinsa.
A wannan lokaci ne Kiru yayo kan Armad, yana zuwa ya
ɗaga takobinsa ya kawo masa wani wawan sara.
Wata ƙara mai kashe kunne ta tashi sama yayinda
waɗannan takubba nasu suka haɗu a sama, lamarinda
yasa dukkan tsuntsaye da sauran dabbobi dake kewayen
fara guje-guje.
Kan kace meye wata iska ta tashi daga kewayen su, inda
ta bazu ko'ina, har saida ta kaɗa bangon ruwan dake
arewa, wanda bashi da nisa da inda ake fafatawar.
Kiru ya kalli takobin Armad idanunsa cike da mamaki,
wanda a wannan lokaci fuskarsa taɗan canja, kana gani
kasan haɗa takobin da sukai yasa ya rage kallon rainin da
yake wa Armad.
Duk da cewa yasan baiyi amfani da sama da kaso sittin,
na ƙarfin Izzar sa ba, a yayin wancan sara, amma yanayin
yadda Armad ya murza takobin tasa sannan kuma ya
kare saran ba tare da wata damuwa ba, shi ne abinda ya
bashi mamaki.
Bama shi ba, hatta Hasanu sai da idonsa ya ɗan ƙifta.
Armad ya ɗaga kai ya kalli Kiru ido cikin ido, lamarinda
yasa Kiru yai tsaki, a lokaci guda kuma ya afkawa Armad
da sara ta ko'ina.
Cikin abinda baifi ƙiftawar ido ba, tuni sun kaiwa juna
sama da sara ashirin.
Aduk lokacin da takubbansu suka haɗu sai kaji ƙara mai
kashe kunne ta tashi sama, sannan ƙura ta ƙara
turnuƙewa, babu abinda suke sai kai-komo.
Baya kimanin daƙiƙa sittin, dukkaninsu suka tsaya da
kaiwa juna sara, gami da ja baya, kowa na kallon kowa,
su na haki.
Suma su Hasanu da Zahra kallonsu kawai suke, kuma

harya zuwa wannan lokaci, Armad ya kula, babu alamar
su biyun zasu shiga cikin faɗan.
Wannan saurayi mai suna Kiru da suke fafatawa da
Armad, zaɓaɓɓe ne daga daular Banfiriya, kuma ɗan
sarkin garin Sisiya ne.
Kuma yana daga cikin waɗanda mutane da dama suke
yiwa kallon shugabannin gobe.
Kuma saboda tarin kayan aiki na horo da zai iya samu
aduk lokacin daya buƙata, da kuma manya-manyan
malamai a garinsu, da duk suke so karɓe shi a matsayin
ɗalibi na musamman, sannan kuma ga dangi na
musamman da yake dasu, kai dama sauransu...
Hakane ma yasa, a tsahon tarihin Kiru, tun daya taso,
harya zuwa shekaru goma sha bakwai da yake a wannan
lokaci, babu wani sa'ansa daya taɓa cin galaba a kansa a
fagen fama.
Saboda haka daga kansa har zuwa yayansa Hasanu,
wanda shi ne Kwamanda na huɗu a ƙarƙashin wannan
ƙungiya da akewa laƙabi da Burja, babu wanda ke da
kokwanton Kiru zai samu nasara akan Armad ba.
Kuma su na gani cewa, wannan kai-komo dake faruwa a
tsakanin Armad da Kiru bata wuce motsa jini ba a wajen
Kiru.
Shi kuwa Armad duk da shi, ba zaɓaɓɓe bane daga
kowacce masarauta ba, amma a dai-dai wannan lokaci da
yake tsaye yana fuskantar Kiru, babu abinda yake gayawa
kansa sai cewa, yanzu ya fara wannan tafiya tasa ta
neman Tirifil Fakta, kuma lallai shima jarumi ne, kuma
wannan faɗa kamar wata dama ce ALLAH ya bashi da zai
fita daga cikin halin da yake ciki.
Saboda haka babu abinda yake tunani face hanyar da zai
kuɓuta daga waɗannan mutane koma su waye.
Armad ba dolo bane, kuma yasan iyakacin ƙarfinsa,
saboda haka nema tunda farko Armad ya gama lissafa
cewa, a iyakacin ƙarfinsa a wannan lokaci babu yadda
zaiyi da waɗannan mutane uku. Amma yana jin cewa da
mutun ɗaya, zasu kara sai yaji daɗi, domin yasan akwai
yiwuwar mafita.
A dai-dai lokacin da yake wannan tunani kwayar idonsa ta
motsa daga kan Kiru izuwa kan Hasanu.
A lokacin ne yaji nan take tsigar jikinsa ta tashi da wani
irin tsoro, irin wanda rai ke fuskanta a dai-dai lokacin
mutuwarsa.
Ba komai bane ya janyo haka ba illa ratar ƙarfin Izza daya
ji a jikinsa wadda ke tsakaninsa da Hasanu!
Lallai yasan Hasanu ba sa'an sa bane.
To amma a dai-dai lokacinda zuciyarsa take ɗarsa masa
cewa, Kiru ba komai bane ba, Hasanu shi ne abin ji!
Shima Kiru yaga kallon da Armad yayi wa Hasanu da
kuma yadda ya tsorata dashi, saboda haka bai ɗau lokaci
ba ya gano abinda Armad ke tunani a ransa.
Wanda hakan yai matuƙar ƙona masa rai, ya ɗaga kai

sama yai ƙaraji, idanunsa ja-jawur.
Ba komai bane ya jawo haka ba, illa ji da yayi acikin ransa
cewa Armad ya raina shi, yana gabansa amma bata tasa
yake ba.
Nan take ya maida takobin dake hannusa cikin kufenta,
sannan ya fito da wata daga cikin kufen.
Sai dai ita wannan ta biyun fara fat ce, babu abinda take
sai matuƙar kyalli, idan rana ta haska ta sai kaga tana
haske ido, haske na tashi kamar walƙiya.
Ba tare da ɓata lokaci ba, cikin matuƙar fushi, ya afkawa
Armad.
Da farko Armad baiyi ko gezau ba, amma a lokacinda
idon sa yakai kan wannan takobi, kyallin da take, ya daki
idonsa, nan take yaji wata rawar-ɗari ta gifta ta jikinsa.
Abinda yasa dukkan tsigar jikinsa ta tashi. Babu abinda
zuciyarsa take ɗarsa masa sai alamun hatsari a tattare da
wannan takobi.
Bai ko ɓata lokaci ba yaja da baya, ya kuma zare
takobinsa gami da karanta wasu ɗalasimai daya koya a
wajen kakansa, waɗanda babban abinda suke shi ne
ƙarawa takobi ƙarfi.
Amma duk da haka Kiru yana ƙara matsoshi alamun
hatsarin da zuciyarsa ke nuna masa a tattare da wannan
farar takobin bai daina ƙaruwa ba.
Baima ko gama karanta wannan ɗalasimai ba, alamun
hatsarin da yake fuskanta daga takobin nan yakai
ƙololuwa, bayanda ya fuskanci cewa wani farin haske mai
kashe ido ya fara taruwa a gefen wannan farar takobin
dake hannun Kiru!
Kan kace meye wannan, hasken ya ƙaru matuƙa inda
yake bada alamun walƙiya-walƙiya, wanda kuma a daidai lokacin ne ya iso gaban Armad, inda ya kawo masa
wawan sara da takobin.
Da kyar Armad ya iya kai tasa takobi ya tare saran.
Wannan takubba na haɗuwa wata gagarumar ƙara ta
tashi sama.
Ƙarfin saran na Armad, ya daki takobin ta Kiru, inda
wannan ɗalasiman daya karanta suka fara fita daga jikin
takobinsa, kamar kibiya su na bi ta cikin takobin Kiru
sannan su shige jikinsa.
Wani mummunan zafi mai cike da gunji ya cika jikin Kiru,
wanda acikin lokaci ƙanƙani yasa ya fara gani dishi-dishi.
Wani tari na dole yazo wuyansa, wanda yayi iya
ƙoƙarinsa kada yayishi amma ina
Tarin na fitowa kuwa saiga alamun jini a jiki, wanda
hakan ke nuna cewa lallai wannan ɗalasimai, sun jiwa
wasu daga cikin kayan cikinsa ciwo.
To amma a dai-dai wannan lokacin shima Armad ƙarfin
saran takobin Kirun ya cimmasa, wanda yabi ta jikin
takobinsa sannan ya shige jikinsa a kimanin abinda bai
wuce rabin daƙiƙa.
Abu na farko da yayi arba dashi shi ne, wani haske mai

tsananin haskake ido, wanda yayi kama da hasken daya
gani a farko wanda ke kewaye da takobin ta Kiru tun
lokacin daya fara isoshi. Sai dai kuma amma wannan
hasken da yake gani, yafi wancan ƙarfi sau da dama,
domin yama fi kama da hasken WALKIYA.
Bayan wani ɗan lokaci da bazai iya ƙayyade shi ba sai
yaga hasken ya ɓace ɓat. To amma kuma kafin ma yayi
wani tunani dangane da yanayin daya samu kansa aciki,
sai kawai ya fara fuskantar wata uƙuba irin ta
musamman.
Shi dai yasan lallai abinda yake fuskanta yafi gaban ace
masa zafi, to amma bashi da taƙamaiman kalmar da zai
kira shi, saboda haka ya gayawa kansa cewa wannan lallai
uƙuba-ce-irin-ta-musamman.
Babu abinda yake ji a dukkanin sashikan jikansa illa irin
wannan uƙuba, wadda tasa yake ji tamkar kowanne
ɓangare na jikinsa gab yake daya farfashe, ya kuma
tarwatse.
Baima san lokacin daya rufe idonsa ba, saboda tsanani
zafin da yake fuskanta, wanda yasa yama manta cewa a
tsakiyar faɗa yake.
Can bayan wani lokaci da bazai iya ƙayyadewa ba, sai
kawai yaji tamkar ruhinsa ya fara marmashewa tamkar
busasshen yashi.
Yana bin iska da ƙarfin gaske, wanda hakan yasa ƙura ta
fara tashi.
Dukkanin wannan abu da Armad yake fuskanta, yasan a
mafarki yake jinsa, amma kuma lallai uƙubar da yake
fuskanta yasan cewa a zahiri take.
Babu abinda yake juyawa acikin idonsa banda wannan
abubuwa uku; WALKIYA da FASHE-FASHE da kuma ƘURA.
Yayi taga-taga, ya jada baya kamar zai faɗi, sannan bayan
kimanin taku uku ya tafi ya nufi ƙas tamkar zai durƙushe
akan gwiwowinsa guda biyu!
Da kyar ya samu ya ɗan iya buɗe idonsa, inda ya cake
takobinsa a ƙas, ya tallafi kansa da ita, lamarinda ya
taimake shi bai je ƙas ba.
Amma babu abinda ke fita daga bakinsa sai jini! Kallo
ɗaya zakai masa, kasan yafi Kiru jin jiki a waccan karawar
da sukai.
Da kyar ya miƙe akan ƙafafuwansa ya kuma zare
takobinsa daga ƙas.
Ya ɗaga ido ya ƙara fuskantar Kiru, wanda tuni shima ya
jada baya ya kuma tsaya daga ɗan nesa yana karanta
abubuwan dake faruwa cikin haki, a zuciyarsa kawai yana
auna ƙarfin abokin fafatawarsa ne, daga wannan haɗuwa
da sukai guda ɗaya, musamman tunda gashi har tasa yayi
tarin jini guda ɗaya.
To a dai-dai wannan lokaci ne, Armad ya fuskanci cewa
gaba ki ɗaya wajan da yake tsaye acike yake da ƙura
matuƙa, domin da ƙyar ma yake hango abokin karawarsa
daga nesa.

Yana cikin tunani akan mai ya jawo wannan turnuƙewar
ƙurar, wadda a iya tunawowarsa baya hango lokacin da
sukai bata kashin da har wannan ƙura zata tashi haka.
To amma a dai-dai wannan lokaci da yake wannan tunani
ne yaji muryar Kiru, ''kayi ƙoƙari daka iya kuɓuta daga
farar takobina.
''Kayi sani cewa ka shiga cikin kaɗan waɗanda suka
cancanci suji bayani akan sirrin wannan takobi tawa!
''Sunan wannan takobi; Walƙiya-Tarwatsi-Ƙura!
''Da abinda kaji da kuma abinda kake gani na game da
ƙura yanzu da idonka, duk zahiri ne bawai mafarki ba
ne!'' Yana zuwa nan a zancansa ya ƙara taku ɗaya izuwa
Armad, sannan yaci gaba da bayani, ''Duk sara guda daga
jikin wannan takobi, yana tafiya ne da farin haske wanda
waɗanda abin ya shafa sukan kwatanta a matsayin
Walƙiya.
''Sannan kuma abinda zai biyo baya shi ne tarwatsewar
abinda saran ya shafa, wanda hakan shi ne yake yin
bayani ga kalmar tarwatsi dake cikin sunan.'' A dai-dai
wannan lokaci ne Kiru ya ƙara ɗaukan taku ɗaya izuwa ga
Armad, sannan yayi shiru, ya kuma kalli gefen Armad
daga ƙasa, wanda a dai-dai lokacin ƙurar ta ɗan fara
lafawa.
Armad wanda ke gabansa, zare da takobi yana karantar
abokin fafatawar tasa, yana kuma sauraran mai yake
cewa, shima idon nasa ya motsa inda ya kalli gefen nasa
daga ƙasa.
Cikin tsananin mamaki ya jada baya, bama tare da ya sani
ba, saboda abinda idonsa ya gani.
Gaba ki ɗayan shatalen gefen nasa ya rarake yayi wani
mummunan rami, tamkar wanda aka haƙe da ƙarfin
gaske.
To a sannan nan ne ya fuskanci cewa ƙurar na dake tashi
daga wannan rarakakken rami take fitowa.
Bai ɗau lokaci ba ya gane duk abinda ke faruwa kuma ya
gane abinda kalmar ƙarshe ta sunan takobin take nufi,
''wato kalmar Ƙura wadda ke nufin ƙurar dake
turnuƙewa bayan abinda aka sara ya tarwatse!''
Yana cikin tunani ya ƙara jin muryar Kiru wanda a daidai
lokacin ne yayi taku na uku inda ya ƙara kusantar Armad,
yadda ya rage baifi kamu biyu bane a tsakaninsu ba
''nasan zuwa yanzu ka riga kasan ma'anar kalmar ƙarshe
dake cikin sunan takobi na.
''Kuma kasan irin sa'ar daka taka yadda ka tsira da jikinka
a haɗe.'' Yayi wata dariya ta mugunta da gefen bakinsa
sannan ya cike da cewa, ''amma nasan kasan cewa sa'a
bata zuwa sau biyu a lokaci ɗaya a kuma cikin tsakiyar
fafatawa ɗaya!''
Armad ya kalli gefensa yaga cewa babu inda ba'a
rarakeba, inba ɓangaren da Kiru yake ba, kai hatta
bayansa.
Nan take yasan cewa babu wata hanya, ta guduwa ko

kuma canja waje, abu ɗaya kawai daya rage shi ne su
afkawa junansu.
Yana cike da masaniyar cewa idan ya bari wannan farar
takobin, ta ƙara cimmasa a irin lokacin haka, to ba lallai
ya tsira da ransa ba!
Copyright © 2017 A M IBRAHIM . All rights reserved
Nidinne dai Shuraih Usman inkiya
99%
Daga taskar magajin wilbafos
MAGAJIN WILBAFOS
Marubuci: Dr Abdullahi Muhammad Ibrahim
Babi na 10: Gimbiya Zahra
Post by: Shuraih Usman
@shuraih 99%
www.facebook.com/hausaebooks
.
Daga gefe, idanun Hasanu da wannan budurwa acike
suke da mamaki, kuma zuwa wannan lokaci su na da
cikakkiyar masaniyar cewa shima Armad, koma daga ina
yake, lallai ya sami horo na musamman.
Dukkaninsu sun san irin ƙarfin da farar takobin Kiru ke
dashi, amma bisa mamakinsu Armad ya iya tare sara
daga gareta kuma ba tare da yaje ƙasa ba.
Hasanu ya ja numfashi sannan ya ƙara matsawa gaba,
gami da ƙara ƙurawa Armad ido.
Ya kalleshi sama da ƙas, sannan bayan wani ɗan lokaci sai
kawai idanunsa suka canja, kamar wanda yake so yaga
wani abu a tattare da Armad, amma kuma ya kasa.
Yana shirin ɗauke ido daga kan Armad, sai idonsa yakai
kan wannan jan ƙyalle dake ɗaure a gaban goshin Armad.
Nan take ya ƙura masa ido tsahon daƙiƙu, kafin kwatsam
idonsa ya cika da firgici sannan jikinsa ya fara karkarwa.
Cikin ɗimuwa ya fara magana aciki, "madauwamiyar
Miyura... ina ba abu bane mai yiwuwa... to amma...
''Hmmm.... ko madai ba ita bace a goshinsa ba, kashe shi
a yanzu ganganci ne, ya zama wajibi na koma dashi
Sisiya, in yaso na ƙara duba littafin 'Matsayin-Izza' na
shugaba Jána Sisiyu, kafin na kaiwa sarki wannan babban
labarin!''
Yana zuwa nan a zancansa ya ɗaga kai domin kawo
ƙarshen wannan fafatawa dake faruwa, tsakanin Armad
da Kiru da niyyar tafiya da Armad ɗin can garin Sisiya,
wajan sarki.
To amma a dai-dai wannan lokaci ne Kiru ya ƙara kawo
wa Armad wani wawan saran.
Amma abinda Kiru bai sani ba shi ne tuni ya bayyana ga
Armad cewa lallai, idan ya bari suka ƙara haɗuwa da
wannan farar takobin ta Kiru, a irin karo na farko, tofa
lallai sakamakon bazai masa kyau ba. Saboda haka tuni ya
riga yayi wata sabuwar shawara acikin ransa.
Yayi shawara cewa zaiyi amfani da wani hari na

musamman shima, ya kuma afkar da wani gagarumin
ɗauki akan Kiru wanda zai bashi dama ya ci nasara cikin
sauri ba tare da bawa abokin karawar tasa dama ba.
Saboda haka tuni ya gama shiri, a lokacin da Kiru yake
ƙoƙarin afka masa da wannan farar takobi.
A dai-dai wannan lokaci takobin Armad ta fara fitar da
wani irin hayaƙi.
Kan kace meye wannan gaba ki ɗaya kewayen Armad ya
cika da irin hayaƙin, ta yadda da kyar ake iya hangoshi a
tsaye cak a tsakiya.
Dukka wannan baisa ko kaɗan Kiru ya dakata ba, illa
kawai ƙara azaba da yai wajan afkawa Armad ɗin.
Kamar ana ziga wannan farar takobi dake hannun Kiru,
wani farin haske mai tsananin haske ido ya fara ambaliya
daga jikin ƙarfenta.
Sannan kuma idan ka lura ma zakaga kamar ta ƙara tsayi
da kimanin kamu ɗaya To a dai-dai lokacin ne, su biyun
suka haɗu kuma suka afkawa juna da sara, takubbansu
suka haɗu a sama, ga mi da fitarda wata ƙara mai
rikitarwa, wadda tasa saida Zahra ta rufe kunnuwanta da
hannayenta.
Iska mai ƙarfin gaske ta kaɗa, wadda tayi ƙoƙarin cilli
dasu daga wajan da suke tsaye. Iskar ta ƙarasa ta daki
bishiyun dake kewayen wajen wanda hakan yasa nan take
reshinansu suka fara girgiza, kamar zasu cire.
Kan kace meye wannan ƙura ta turnuƙe, har takai basa
iya ganin koda tafin hannayen su. Babu abinda suke ji illa
girgizar ƙasar da suke kai kurum.
''Dukkanin abinnan dake faruwa sara ɗaya ne kurum ya
janyo, daga jikin takubbansu!!!''
''Eh...'' Hasanu ya ja dogon numfashi, yayinda baki a
buɗe, fuska a yamutse cike da mamaki ya bar ƴar uwar
tasa, acikin ƙurar nan ya nufi cikin wajen da su Kiru suke
fafatawa da gudun gaske.
Ba wani abu bane ya jawo haka ba illa wata halitta da yaji
a jikinsa ta fito daga cikin Bangon Arewa tana kuma
gabato wajen da suke.
Wannan halitta ba wata aba bace, illa ɗaya daga cikin
fatalwowi na musamman dake cikin wannan waje.
Kasancewar dama tunda farko wajan da suka kafa tantin
nasu bashi da nisa da Bangon-arewar ta yadda zaka iya
hangensa daga nesa.
Akwai wani karin magana da kusan kowa ya sani a
wannan zamani, wanda indai kaji shi, to kawai kasan ana
magana ne akan waɗannan bangwayen ruwa biyu.
Wannnan karin magana kuwa shi ne, ''Mafakar mutuwa!''
Wanda ya samo asali ne tun da daɗewa, saboda wani
dalili guda ɗaya.
Wannan dalili kuwa shi ne, da dama daga cikin
al'ummatai na wannan zamani su na da fahimtar cewa,
dukkan mutumin daya mutu anan ruhinsa yake fara yada
zango kafin wani lokaci.

Hakan kuma ya samo asali ne daga yawan fatalwowi da
suke zaune akan wannan ruwa.
Kuma babban abun mamakin shi ne, da dama mutane
sukan ga fatalwar wani wanda suka taɓa sani a lokacin
yana raye a wannan waje musamman a wasu lokuta na
shekara.
Babban tashin hankali ga al'amarin waɗannan fatalwi shi
ne yadda suke cin naman mutun ɗanye wanda har takai
sukan kifarda jirage, sannan su halaka fasinjoji.
To amma a dai-dai lokacin da Hasanu ke ƙoƙarin isa
wajen wannan fafatawa dake faruwa,
Wannan haɗuwa da farar takobin Kiru sukai da takobin
Armad mai fitarda hayaƙi, ya haddasa wata mummunar
girgizar ƙasa, wadda cikin ɗan ƙanƙani lokaci ta fara
zagwanyar da dukkan ƙasar da suke kai.
Abin ya fara ne a iyakacin kewayen ƙasar dasu Armad
kekai, amma cikin daƙiƙa kaɗan ya fara bazuwa ko'ina.
Kan kace meye wannan dukkaninsu sunyi tsalle sama
izuwa kan ƙasar dake gabansu, domin kaucewa faɗawa
rami, sai dai kuma bisa rashin sa'a, ƙafafunsu na dira kan
ƙasar ita ma ta fara rududduge wa.
Kuma kan kace meye wannan ƙasar da Zahra ke kai, ta
rabe gida biyu kuma tana neman afkawa ciki. Lamarin da
yasa cikin tsananin zafin nama Hasanu ya juyo da niyyar
riƙota, amma tun kafin ya ƙarasa ya ji a jikinsa cewa
wannan fatalwa data fito daga cikin wannan ruwa ta kusa
cimma su Kiru.
Nan take Hasanu ya ƙara azama, inda yai maza ya riƙo
Zahra, ya hanata faɗawa wannan rami.
Sannan kuma cikin sauri ya ajiye ta acan gefe guda, ya
kuma juyo da niyyar ceto Kiru daga harin sumame da
wancan fatalwa take neman yi musu.
To amma abinda bai sani ba shi ne, tuni Kiru yasan
abinda ke faruwa kuma ya yanke shawarar me zaiyi.
Kan kace meye wannan, sunyi hannun riga, Kiru yayi
yamma Armad yayi gabas, shi Kiru yana ƙoƙarin gujewa
fatalwar, shi kuma Armad yana ƙoƙarin gujewa wannan
ramika.
Kan kace meye wannan, ratar dake tsakaninsu takai
kimanin taku bakwai. Hakan kuma ya faru ne ba tare da
saninsu ba, domin su kawai gudu suke suna tsallake rigiya
da baya daga wannan waje zuwa wannan a tsakanin
wannan girgizar ƙasa.
Wani abu da duk su biyun suka fuskanta shi ne, lallai
bawai kaɗai harin da sukai amfani dashi bane ya janyo
wannan girgizar ƙasa ba, dole akwai wani abu a ƙas.
Duk inda suka taka kafin ma su ajiye ɗaya ƙafar, shima ya
fara zaizayewa, to amma daya ke dukkanin su biyu ba
mutane bane wanda suka daɗe acikin duniyar horo ba,
kawai yara ne waɗanda aka haifa da baiwa, wanda kuma
hakan lallai bai kai a wannan lokaci yasa su tsere daga
mahaukacin saurin da zaizayar ƙasar ke faruwa dashi ba.

Hakan ne yasa bayan kimanin daƙiƙu shida ta cimmusu,
ta yadda takai ƙafafunsu suka dira a dai-dai lokacinda
itama ƙasar take cinyewa, saboda haka suka rufta ƙas ba
shiri.
To amma ga dukkan alamu sa'a tana tare dasu a wannan
lokaci, inda wannan girgizar ƙasa ta tsaya a dai-dai
lokacin da sukai amfani da hannayen su wajen riƙe
ƙarashen ƙasar da bata ƙarasa rushewa ba.
Hakan na faruwa suka miƙa hannayensu, suka kuma riƙe
waɗansu tubalin ƙasa waɗanda suma sauran ƙiris su cire.
Kasancewar kuma duk su biyu a gine suke da jiki
murɗaɗɗu, kuma wajajen da suka riƙe basu da kwari
sosai, bai ɗau lokaci ba kafin wajan da suka riƙe ya
fizgine, su ƙara nufar faɗawa.
Sai dai kuma a dai-dai wannan lokaci ne Hasanu ya isa
wajen, inda ya riƙo hannun Kiru, ya kuma fara janyoshi
waje.
To amma a dai-dai lokacin ne idanunsa suka cika da
mamaki saboda abinda yai arba dashi.
Zahra, wadda bai daɗe da ajiyeta a can gefe ba, ita ce a
kwance a rigingine, dai-dai wajen da Armad ke ƙoƙarin
faɗawa inda hannunta na hagu ke miƙe a gabanta riƙe da
hannunsa.
Shima Kiru wanda yake jira a janyoshi waiwayawa kawai
yayi, yayinda ya fuskanci inda Hasanu ke kallo.
Armad ya dubeta idanunsa cike da yanayi na rashin
fahimta.
Nan take ya shiga wani yanayi mai tsananin ban mamaki
da alajabi. Irin wanda bai taɓa fuskanta ba a rayuwarsa.
Hannunta na taɓa nasa, yaji wani a jikinsa cewa lallai ya
taɓa ganin wannan budurwa, kai bama iya haka ba, har
wasu hotuna yake gani acikin kansa wanda suke nuna
masa wasu mu'amaloli da suka faru tsakaninsa da
wannan budurwa a baya, lamarinda yai matuƙar ɗimauta
hankalinsa.
Ya cika da mamaki, domin kuwa yasan lallai duk
waɗannan abubuwa basu taɓa faruwa ba. Hasalima bai
taɓa ganinta ba, sai a wannan lokaci.
To amma bisa mamaki, abubuwan da yake ji, sunfi gaban
ace mafarki yake. Domin kuwa a zahiri yake ganin abin,
kamar ma bai daɗe da faruwa.
Dukkan abin daya gani, bai haura daƙiƙa biyar ba, amma
shi yana jin kamar ya kai daƙiƙa dubu a jikinsa.
Ya buɗe baki zaiyi magana, to amma duk da cewa akwai
samada tambayoyi dubu da zaiso ta bashi amsa, amma
bisa ya kasa cewa komai!
Kafin ya iya rufe bakinsa kawai sai wata kwayar hawaye ta
fito daga idanun Zahra ta kuma nufo idanunsa.
Kuma saboda yanayin yadda suke a lokacin, kai tsaye
hawayen ya ɗisa acikin idonsa.
Lamarinda baiyi wani abu naya hanashi faruwa ba.
Babu abinda yake ta kai-komo a ransa sai tunanin a ina ya

taɓa ganin wannan kyakkyawa??
Zahra ta buɗe baki kenan zatai masa magana, fuskarta
acike da murmushi, sai kawai yaga murmushin fuskarta
ta ya dusashe a lokaci ɗaya, sannan kuma an maye
gurbinsa da tsananin tsoro da firgici.
Kafin yayi wani abu tuni Zahra ta saka dukkan ƙarfinta
wajan ƙoƙarin janyoshi waje.
Idanunta nakan wani abu dake doso wajan da suke ta
baya.
Bai ɗauki lokaci ba ya fahimci cewa akwai wani abu mai
hatsari dake kusanto shi ta baya.
Kafin ma ya ƙarasa juyawa muryar Kiru wanda tuni
Hasanu ya fito dashi, suke kuma nufosu da gudu, ta isa
cikin kunnensa, yana kwala ƙara kamar maƙokwaransa
zai fashe, ''Kinsan cewa idan fatalwa ta taɓa shi kina riƙe
dashi har kema abin zai shafa, KI CIKASHI!!!''
To a dai-dai wannan lokacin ne Armad ɗin ya juya ya
hango wata siffa mai tsananin firgitarwa tana nufoshi
daga nesa da wani mugun sauri mai kamar walƙiya.
''So kike yi ki mutu, saboda wannan yaron da ba kowan
kowa ba!!'' Inji Kiru wanda ya ƙara azama a ƙoƙarinsa na
isa wajanda suke.
Shima Hasanu wanda fuskarsa ke cike da rashin-fahimta
da mamaki, da kuma ɗimuwa, musamman ma yasan shi
alhakin kula da ita ke kansa, ya fara roƙonta, ''kinsan
muhimmancinki a gurin mahaifinki, dama dukkan
al'ummar ƙasar Sisiya, kada kiyi haka, koma me kike
tunani akansa, kuma ko meye dalilinki!!''
A dai-dai wannan lokaci saboda tsananin saurin da
wannan halitta ke tafiya dashi tuni ta iso inda Armad
yake, wanda har a sannan Zahra bata ƙarasa janyo shiba.
Nan take ya gane mai maganganun su Hasanu suke nufi,
ya kuma fuskanci dukkan abinda ke faruwa, kasancewar
duk da bai taɓa ganin irin waɗannan fatalwowi a gaske
ba, amma ya taɓa karanta su a littafi;
Ya fahimci cewa saurin da wannan fatalwa take yi, yafi
wanda su Hasanu keyi, kuma tabbas kan su ƙaraso wajen
da suke, wannan fatalwa zata rigasu.
Saboda haka komai yana hannunsa da wannan budurwa,
mai suna Zahra, kodai ta

Please Login or Register in order to submit comment