Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

duk wata fasaha da suke da ita. Amma babban
abin mamakin shi ne a ina wannan yaro ya samo wannan
laya? Ta yaya ɗan ƙaramin yaro zai mallaki Farar-laya."
Haka dai Ghalee ya ci gaba da bayyana alajabinsa a fili
ƙarara da yadda akai Armad ya mallaiki Farar-laya.
Domin dai ko ba'a faɗa ba ansan ya riga yaci nasara akan
Amuru, wanda tuni ya faɗi ƙasa ko motsi baya iya yi.
Domin bawai kaɗai ɗaure aljanu wannan Farar-laya take
yiba, hatta ma'aboci aljanin sai yaji muguwar kasalar da
bazai iya komai ba.
Babu daɗewa abinda ya faru ya girgiza kowa a wajen,
kuma tuni mahangar da dama daga cikin ƴan kallon akan
Armad ta canja nan take.
Kusan sama da kaso arba'in sun fara yi masa kyakkyawan
zato.
Likitoci suka garzayo cikin filin-dagar suka ɗauki Armad,
domin abin mamaki shi ne, Armad shi ne yayi nasara
amma kuma shi yake ta aman jini. Saboda ko ciwo ɗaya
babu a jikin Han Amuru in banda kasancewar dai ko tashi
bazai iya yi ba saboda aikin wannan Farar-laya. Inda dai
ALLAH ya taimaki Armad shi ne akwai wata fafatawar
kafin ayi wasan ƙarshe. Saboda haka yana da lokacin da
zai huta ya ɗan farfaɗo.
____
Ba daɗewa aka buga wani ƙugen yaƙin, dake sanarda
cewa lokaci yayi da za'a fafata tsakanin Deniz Bizaya ɗan
sarki Deniz Iluru mai masaukin baƙi, da kuma Ikenga O.
Bayajidda wanda shi ne sanadiyyar rabewar ruhin Armad
gida biyu da kuma ɓacewar Miyurar sa!
A can gefe ɗaya kuma Armad ya fito matakin ƙarshe na
wannan gasa!
Nidinne dai Shuraih Usman inkiya
99%
Daga taskar magajin wilbafos
Alƙalin wasa Ghalee ya kira wasa na gaba. Deniz Bizáya
ɗan sarki Deniz Iluru ya fito kan filin wasa tare da abokin
karawarsa wato Ikenga O Bayajidda.
Kai daga ganin tsaiwar waɗannan jarumai biyu kasan sun
banbanta da sauran.
Sa'ilin nan kuma tsayuwa ce wadda ake gani a jikin
jaruman farko waɗanda ƙafafunsu suka ginu a fagen

daga.
Fuskokinsu babu tsana ko kallon raini a game da junansu,
lamarinda ke nuna cewa kowa acikinsu ya yarda da
matsayin Izzar abokin fafatawarsa, amma fa kana ganin
idanunsu zaka ga kafiya, irin ta ƙololuwa. Irin wadda lallai
idan mutun ya sa abu a gaba, to saiya cimmasa.
Tunda farko dai babban dalilin da yasa Ikenga ya riga
kowa zuwa shi ne goron gayyata da Deniz Bizáya ya aika
masa na cewa yana jiransa yazo su motsa jini kafin a fara
gasar!
Haka kuma akai, Ikenga yazo, shi kuma Bizáya yasa aka
buɗe masa ƙofa tun ma kafin lokacin fara gasar yayi.
Kwanansu goma sha uku su na fafatawa a gaban
waɗannan giwaye, lamarinda yasa daga ƙarshe suka
haƙura aka tashi kunnen doki, dan kowa ya kasa samun
nasara.
Kuma a ƙarshen wannan doguwar fafatawa da sukai,
kowa acikinsu ya tafi da abu guda ɗaya acikin ransa; cewa
indai yana so ya zamo na ɗaya a wannan gasa to saiya
ƙara ƙarfin Izzarsa fiye da ɗan'uwansa domin inba haka
ba kuwa, sai dai koda sun haɗu a zagayen ƙarshe, a
ƙarayin kunnen doki. Dan haka kyautar ma sai dai a raba
musu. Wanda kuma wannan abu ne da babu wanda
acikinsu ya yarda dashi.
Hakan nema yasa kowa acikinsu yayi amfani da ragowar
kwanakin wajen ƙara samun horo. Kuma yanzu gashinan
sun haɗu tunma kan aje zagayen ƙarshen.
Deniz Bizáya ne ya fara magana da cewa, "inaga babu
buƙatar mu ɓata lokaci a wannan faɗan, dani dakai kowa
yasan kowa! Kar tasan kar!
"Kuma jan faɗa a tsakaninmu a wannan mataki, ba abu
ne mai amfani gare mu ba. Domin zamu iya gajiya ko
kuma mu jiwa juna rauni, kuma ba lalle a bada hutu mai
yawa a tsakanin wannan zagaye dana gaba ba.
"Shin mai zai hana muyi wani abu a gaban kowa!"
Yana zuwa nan a zancensa ya rufe idanunsa, bayan
kimanin daƙiƙa biyar ya buɗe; yana buɗewa baƙar
kwayar idonsa ta ɓangaren dama ta ɓace gaba ɗaya,
kuma a wajenta na da babu komai sai hoton wani zane
guda ɗaya mai kama da ƙatuwar ƙusa irin wadda ake
ginin gidajen aljanu da ita!
Wanda idan ka ɗaga idonka, ka kalli goshinsa dai dai
wajenda ya kamata ace Miyura ce, zakai arba da sak irin
wannan hoton ƙusa na cikin idonsa, sai dai kawai ya fishi
girma.
To idan da a haka abin ya tsaya, to da da sauƙi, amma
buɗe idanun Bizaya keda wuya gaba ki ɗayan ilahirin
cikin wajen filin ya fara girgiza kamar zai kife.
Can bayan kamar daƙiƙa goma sai komai ya tsaya cak,
amma kuma kowa ya samu kansa cikin sakin baki dan
mamakin abinda suke gani tsaye cak a bayan Bizaya.
Ba komai bane illa wata ƙatotuwar ƙusa mai malafa ta

jan dinare. Tsaye take cak tamkar bata taɓa faɗuwa ba
tunda aka shimfiɗa duniya, tamkar kuma baza ta taɓa
faɗuwa ba koda duniyar ta ƙare.
Saboda girman ƙusar idan ka ɗaga kai baka iya gano
ƙarshenta, sai dai kawai ka hangi malafar ƙusar kawai ta
nutse a cikin gajimare.
Ƙasanta kuwa wanda a fiƙe yake, kuma a tsaye a bayan
Bizaya, yana cake akan iska.
Kai ta kowanne ɓangare, kuma komai duban mai duba
bazai iya gane cewa wannan ƙusa ba'a zahirin gaske take
ba. Indai ba zuwa kai ka taɓa ba, sai dai amma idan ka
taɓa zaka fuskanci cewa wannan ƙusa hoto ne bawai a
zahiri take ba.
Ana cikin haka ne wannan ƙusa a gaban mutane, ta fara
rabewa gida biyu! Kan kace meye wannan ta rabe zuwa
gida biyu, wanda kuma kowanne rabi ya rabe zuwa gida
biyu, inda kowacce ta ƙara rabewa, kai cikin ƙiftawar ido
tuni wannan ƙusa ta rabe zuwa gida takwas.
Hakan na faruwa ta daina rabuwa, amma kuma ɓariɓarin nata, wanda da kowanne wani ɓangare ne kawai na
jikin ƙusar farko, suka fara mulmulewa su na haɗewa,
kan kace meye wannan kowacce acikinsu ta zama ƙusa
akan kanta. Kuma duk manya, wanda duk da basu kama
ƙafar ta farkon ba, amma kowacce tafi zira'i ƙafa sittin!
Duk wanda ya taɓa ziyartar daular Denizawa yasan sunan
wannan hoton ƙusa daya bayyana a bayan Bizaya, wanda
shi suke kira 'Márakána'.
Bizaya yai wani murmushi mai cike da yadda dakai, gami
da ci gaba da cewa, "zan saka dukkan ƙarfin Izza ta acikin
wannan Marakana da kake gani, zan kuma sa su kewaye
ka.
"Abu ɗaya kacal kawai nake so kayi, ka iya fita daga
cikinsu acikin daƙiƙa sittin!
"Indai har kai haka, to ni Deniz Bizáya na yarda kayi
nasara akaina!
"Idan kuma ka kasa, to nima kayarda nayi nasara!"
Cikin ƙasa da daƙiƙa ashirin duk wanda ke wajen yaji
wannan gasa da Bizaya ya sakawa Ikenga, duk da kuwa ba
da ƙarfi ya faɗa ba, amma ya faɗa yadda alƙali Gali zai iya
ji, wanda daka ganshi a fili kasan Bizaya yake goyon baya.
Ai kuwa yana ji ya fara yayatawa, tayadda kowa saida yaji
meke faruwa, a wani yanayi na tabbatar da cewa Ikenga
bazai iya cewa a'a ba!
Abin mamakin shi ne, kana kallon Ikenga kasan kai komo
yake da zuciyarsa, akan ko ya yarda ko a'a.
Wanda a gaskiya, kowa zaiyi mamakin hakan,
musamman duba ga yanayin tsananin buwayar ƙarfi da
kowa yasan Ikenga da shi, shi-shi kaɗaine a iyakacin tarihi
tsahon lokaci wanda aka taɓa samu ya fafata da Yarima
Deniz Bizaya acikin filin horonsa kuma baije ƙas ba.
Amma ganin cewa yana kokwanton amsawa Bizaya
wannan abu, sai ya fara bawa mutane mamaki, kuma kan

kace meye wannan tuni ƙus-ƙus ya fara tashi akan cewa
ko dama Ikengan da ake faɗa da labaran faɗansa da
Deniz duk ba gaskiya ne.
Amma acikin wajen manyan baƙi kuwa, tun ɗazu da
wannan ƙusa ta jan dinare ta bayyana, a karon fari Asifu
yayi wa Sarki Deniz Iluru magana, "lallai Deniz Iluru zanso
naga yadda Bizaya zai taso.
"Wataƙila ma yazo ya fika!!"
Maganar da wasa ya faɗe ta, amma acikin idanunsa idan
ka kula zaka ga nufaƙa a can ƙasa, kuma da yake shima
Deniz ba na yau bane, tuni ya gane hakan, inda kawai ya
bashi ɗan ƙaramin murmushi mai ƙunshe bayanai kalakala.
Amma abinda mutane basu sani ba shi ne duk wanda bai
taɓa shiga cikin Marakana ba, to bazai taɓa sanin maike
faruwa aciki ba.
A faɗansu na kwanaki da suka wuce, Bizaya ya samu
damar saka Ikenga acikin Marakana, lamarinda saida
yasha matuƙar wahala aciki kafin ya iya fitowa.
Amma kuma yanzu ga abinda Bizaya ya zo dashi.
Tunda jimawa Ikenga ya rantse da mahaliccin Bayajiddan
farko, wadda ita ce mafi girman rantsuwarsa, cewa saiya
zo na ɗaya a wannan gasa.
Wanda wannan wani mataki ne na farko acikin tsaretsaren daya shirya zaibi wajen ɗaukar fansar abinda ya
faru da ƙasarsa da danginsa!
To amma kuma ko ma a wanne yanayi ake ciki, yana daga
cikin halayen Ikenga shi ne, baya son abinda zai ɓata
masa suna ko kaɗan.
Saboda haka yana kallon dariyar dake kan fuskar Bizaya,
ya kuma ji abubuwan da ƴan kallo ke faɗa, da kuma
yadda alƙali Gali yake ta ƙara zuzuta maganar, cikin isa ya
amsa cewa ya yarda.
Lamarinda yasa wajen yai tsit, ana jira aga mai zai faru a
gaba.
MAGAJIN WILBAFOS
Marubuci: Dr Abdullahi Muhammad Ibrahim
Babi na 41: Shaibal shisu Takun Sarki
Post by: Shuraih Usman
@shuraih 99%
www.facebook.com/hausaebooks
.
Daga:- Taskar Magajin Wilbafos
.
Deniz Bizaya dariya kawai yayi, gami da ƙara taku ɗaya
gaba, lamarinda yasa waɗannan ƙososhi guda takwas
dake bayansa ɓacewa ɓat daga inda suke a sama kansa.
Kafin daga bisani su bayyana a gaban Ikenga, inda suka
kewaye shi, kuma suka ci gaba da matsawa suna rufe shi,
har saida ya zamo ba'a iya ganin ko da rigar Ikenga, sun
rufeshi ruf.
A dai-dai wannan lokaci ne Bizaya yayi wata ƴar ƙaramar

dariya gami da cewa, "daƙiƙar ka ta farko ta fara, Ikenga!
"Saura daƙiƙa hamsin da tara!"
ƴan kallo najin wannan batu suka fara shewa su na ihu
su na kiran sunan Bizaya.
Acikin zuciyar Deniz Bizaya yana da cikakkiyar amannar
cewa indai mutun Izzarsa bata haura shekaru dubu ba, to
lallai bazai iya fita daga cikin wannan kurkuru ta ƙusar
tsafi ba. Kuma yasan Izzar Ikenga bata haura shekara ɗari
ba, saboda haka yana da nutsuwa acikin ransa cewa
tabbas yayi nasara. Idan kuma Ikenga ya iya fita daga ciki
to lallai abinda mahaifinsa sarki Deniz Iluru ya labarta
masa akan tsakanin Ikenga da ƙabilar Ururu gaskiya ne.
Daga waje babu abinda ake gani sai rumfar waɗannan
samudawan ƙusoshi. Acikin wannan ƙusoshi kuwa,
Ikenga ne ya tsinci kansa acikin wani ɗaki, wanda yake a
kewaye da katangu iyakacin ganinsa. Kowacce katanga
anyi tane da irin wannan jan dinare na wannan ƙusoshi.
Kuma idan da zaka lissafa, zaka ga a kewaye da wannan
ɗaki adadin waɗannan katangu guda dubu takwas ne daidai da dai-dai!
Kowacce idan ka ɗaga kai baka gano ƙarshenta!
Kuma babu komai a wajen sai duhu!
Sannna shi kuma gashi acikin ɗaki a ƙulle sannan kuma a
sarƙafe da ankoki, waɗanda suma da zai lissafa su da
yaga cewa guda dubu takwas ne dai-dai.
Ikenga ya taɓa shigowa irin wajen sak, sai dai a wancan
lokacin ankokin daya tarar guda dubu huɗu ne kawai,
sannan suma katangun dubu huɗu ne kawai.
Kuma yasan cewa idan yana so ya fita daga wajen saiya
sare gaba ɗayan waɗannan katangu, waɗanda tsananin
taurinsu bazai misaltu ba!
Amma abin mamakin shi ne, tuni daƙiƙa talatin da uku
sun wuce, amma Ikenga na kwance ko motsi baiyi ba!
Idanunsa a buɗe, babu abinda yake sai kallon cikin
duhun ɗakin nan, zuciyarsa na tunani.
"Hmmm... yayi kyau da ban nuna masa dukkan fasata a
karawarmu dashi a baya ba! Yayi kyau da ban nuna masa
fasahar TAKUN-SARKI ba!"
Ikeng ya ci gaba da magana a nutse tamkar babu wani
lokaci dake jiransa, cikin ƙasaita tamkar duk duniya shi
kaɗai ne sarki, "Lallai dana nuna masa bazai taɓa yarda
da wannan gangancin gasar daya saka min ba. Domin
kuwa lallai yayi kuskure. Kash... amma koma na nuna
masa koma ban nuna masa ba, babu abinda zai canja.
"Gaskiyar kawai ita ce indai baka kai matakin Izza shekara
dubu ɗaya ba, to fa lallai baza ka iya tsayawa a gabana ba
kai maganar Izza ba. Ballantana ma kace zaka fafata
dani."
To ko mai wannan saurayi mai suna Ikenga ya taka da
yake wannan cika-baki haka. Bari dai muga gudun
ruwansa....
Ikenga ya kira wani ɗalasimi, "Shaibal-shísu!" Wanda idan

da mutun yana jin yaren Aldurish to da zai gane cewa
fassarar wannan ɗalasimi yana nufin TAKUN-SARKI.
Yana rufe bakinsa, takobin dake bayansa a saƙale ta fara
haske, inda ɗakin ya fito fili ya bayyana cewa shima anyi
shi ne da jan dinare iri ɗaya da sauran.
Wannan takobi ta fara motsi da kanta, inda ta fice daga
cikin ankokin nan tamkar basa wajen. Tana fitowa ta sari
ankokin dake hannunsa na dama, inda nan take suka
zube ƙas.
Ya ɗaga hannunsa izuwa cikin bakinsa, ya cizi babban ɗan
yatsansa, inda jini ya fara ɗiga.
Nan take ya kai hannun goshinsa, inda ya fara zana wani
tambari mai kama da Miyura da jinin.
Yana gamawa a dai-dai wajen wata Miyura ta musamman
ta bayyana.
Babu komai acikinta sai wasu zanen idanu guda uku,
kowanne a kusurwa daban, haɗe da wani jan layi a
tsakaninsu!
Wannan Miyura na bayyana yai wata dariya, sannan kai
tsaye ya miƙe, ya kuma miƙa hannu ya damƙi takobinsa
dake kan iska!
Ya ja dogon numfashi, ya ɗaga ƙafarsa ta dama yai taku
ɗaya da ita.
A dai-dai lokacin da yai wannan taku, dukkanin
waɗannan ankoki dake ɗaure ajikin sa suka juye suka
koma takubba.
Idan ka hango daga nesa, babu abinda zaka gani face
wani waje mai ban tsoro, wanda babu komai acikinsa
face takubba marasa adadi na jan dinare.
To idan da shikenan, lallai da da sauƙi, amma Ikenga na
ƙarasa dire ƙafarsa daga wannan taku na farko,
waɗannan takubba suka ɓace ɓat, suna bayyana kowacce
na cake a jikin wannan katangu guda dubu takwas da
suka zagaye wannan ɗaki.
Abu na gaba kuma daya faru shi ne, fashewa da wannan
katangu sukai dukkaninsu a lokaci guda, lamarinda ya
bada ƙara mai kashe kunne, da kuma ƙura wadda ta tashi
sama, kuma tasa baka ganin komai.
Tana lafawa babu wannan ɗaki da waɗannan katangu ko
sama ko ƙasa, kaf sun ɓace ɓat!
A dai-dai wannan lokaci daƙiƙa ta hamsin da ɗaya tayi!
Sai dai kuma da yake na wajen wannan duniya basa ganin
abinda ke faruwa, basu ga komai ba sai a daƙiƙa ta
hamsin da shida inda suka ga waɗannan ƙososhi dake
zagaye da Ikenga sun tarwatse ɗaya bayan ɗaya, har gaba
ɗayansu suka ƙare.
A tsaye, idanunsa a rufe, Ikenga ne riƙe da takobinsa
tsirara a hannun hagu.
Baiyi magana ba, kuma bashi da niyyar cewa komai, daga
ganin yadda ya tsaya! Kai dukkan kamannin sa ma sun
canja. Lallai a wannan lokaci idan da zaka kwatanta
Ikenga, to zaka ce yafi kama da jan jarumin zaki irin na

mutanen farko.
Sai dai kuma a dai-dai wannan lokaci ne, Bizaya ya tafa
hannu gami da cewa, "ahhhh...ka samu nasara!" Fuskar
Bizaya babu damuwa aciki.
Yana tafa hannu ya fara matsowa kusa da Ikenga, ko
kaɗan a fuskarsa babu alamun baƙin cikin rashin zuwa
zagaye na karshe, lamarin da hatta Gali saida yayi
mamaki.
Amma ina kowa idonsa na kansa, babban abinda ya ƙara
jan hankalin kowa shi ne yadda suka ga Bizaya na dosar
Ikenga, saboda su ga mai zaiyi yayinda yaje kusa da
Ikenga.
Amma bisa mamaki babu abinda ya faru, yana zuwa ya
ƙarasa kunnen Ikenga yai masa magana acikin raɗa,
"dama nayi tunanin akwai abinda kake ɓoyewa a
fafatawarmu dakai a baya!Amma.... kana tunanin kai
kaɗai ne mai shiri a ɓoye? Hmmm... Bari dai kawai da
sannu wataran zamu ƙarasa wannan faɗan!"
Yana gama faɗin haka yai tsalle ya fice daga cikin wajen,
mutane kuwa suka bishi da kallo, cikin rashin gane mai ke
faruwa, amma ina taku kaɗan yai suka nemeshi suka
rasa.
Tuni wajan ya rikice da ƙananan maganganu, akan
abubuwan dake faruwa.
Kowa dai ya gani da idonsa Ikenga shi ne yaci wancan
gasa data gabata, amma abin mamakin shi ne, yadda
Bizaya bai damu ba kwata-kwata, hasalima wasu tuni sun
fara raɗe-raɗen yana sane ya bari aka cinye shi.
Toh! Koma dai meye gaskiyar al'amarin bari mu koma
kimanin kwana ɗaya kafin fara wannan gasa.
____
KWANA ƊAYA KAFIN A FARA JINZIDAL.
A cikin ƙatoton ɗakin-karatu dake cikin tsakiyar fadar
daular Denizawa, sarki Deniz Iluru ne sanye da ƴar shara
yana yiwa ɗansa Deniz Bizaya karatun ƙarshe akan gasar
da zata gudana a washe garin ranar.
Sarkin ya kasance masoyin tarihi ne matuƙa, domin zaiyi
wuya a samu wanda ya kaishi son tarihi da bincikarsa.
Hakan nema yasa aka gina masa ƙaton ɗakin-karatun da
babu irinsa a ƙasa-bakwai, domin kawai ya ringa tara
al'amuran tarihi aciki.
"Bizaya kana ji ko," sarkin yaci gaba da yiwa ɗan nasa
bayani, "wannan yaro Ikenga da ka gayyato kuka fafata
dashi, na gano acikin tarihi cewa abunda muka daɗe
muna nema domin samun damar rayuwa akan doron
ƙasa yana da alaƙa da shi. Ko kuma nace yana da alaƙa
da abinda ya faru shekaru dubu biyu da suka wuce
tsakanin kakanninsa da ƙabilar Ururu.
"Labari ne mai tsayi, amma zan gaya maka kaɗan daga
ciki. Abinda kawai nake so dakai shi ne ka gano mana
cewa shin wannan Ikenga da gaske shi ɗinne wanda yake
da wannan sirri ko kuwa. Indai ka gano haka to yama fi

ace kai nasara. Domin lallai zan baka kyautar da baka
taɓa zato."
Koda jin kalmar ƙarshe dake magana akan kyauta sai tasa
Bizaya ya daina ɓata rai. Domin yasan lallai kyautar
mahaifin nasa aba ce maɗaukakiya. Da fari baiji daɗin
maganar ba, domin yana so ya samu nasara a wannan
gasa ya nuna kansa a duniya. Amma da yaji zancen
kyautar baban nasa nan da nan ya amince.
Yazo dai a tarihi cewa asali dole ce tasa daular Denizawa
suka koma ƙarƙashin ƙasa saboda wani yaƙi daya afku
shekaru aru-aru da suka wuce. Kuma sirrin dalilin
wannan yaƙi babu wanda ya sani inba sarki Deniz Iluru
ba. Shima saida ya zama sarki ya sani, saboda haka hatta
Deniz Bizaya bai sani ba. A ƙa'idar daular Denizawa sai ka
zama sarki zaka san wannan sirri. Amma abu ɗaya da duk
manyan wannan ƙabila suka sani shi ne su na da buƙatar
su dawo rayuwa a saman ƙasa koma ta halin ƙaƙa.
"Saurara kaji kaɗan daga cikin tarihi." Deniz Iluru ya fara
labartawa ɗansa kaɗan daga cikin tarihin duniya.
___
Hasashen waɗanda suka ce Ikenga zaiyi nasara ya dace da
gaskiya. Armad Wilbafos yana gaisheku!
Nidinne dai Shuraih Usman inkiya
99%
Daga taskar magajin wilbafos
MAGAJIN WILBAFOS
Marubuci: Dr Abdullahi Muhammad Ibrahim
Babi na 42: Takun Sarki part 2
Post by: Shuraih Usman
@shuraih 99%
www.facebook.com/hausaebooks
.
Daga:- Taskar Magajin Wilbafos
.TARIHIN ƘASA BAKWAI.
Shekara ta 352 Kafin Amri.
Sarki Deniz Iluru ya zaro wani ƙaton littafi daga cikin wata
kantar littattafai dake gefensa. Kai daka ganin yadda
shekaru sukai sheda akan takardun wannan littafi kasan
yayi shekaru aru-aru a duniya.
Sarkin yai duba izuwa ɗansa dake durƙushe a gabansa,
kana ya fara karanto tarihi daga wannan littafi.
____
Kimanin shekaru dubu biyu da suka wuce, a wata ƙabila
da akewa laƙabi da Jidda, anyi wani zamani na wani sarki
mai suna Báya Azába.
Asali shima sunan mutun na farko daya kafa ƙabilar aka
sakamasa, wato dai bashi ne Azába na farkon da ƴan
ƙabilar ke rantsuwa dashi ba.
Wani tarihi babba a game da wannan sarki, wanda baza a
taɓa mantawa dashi ba shi ne abinda ya faru a wannan
shekara ta 352 Kafin Amri. Kuma wannan al'amari shi
yasa aka sakawa wannan sarki suna Báya. Hasalima shi ne

asalin dalilin da yasa aka canja sunan wannan ƙabila daga
Jidda ta koma Baya+Jidda, wato Bayajidda.
An rawaito cewa a lokacin da aka haifi wannan sarki, a
dai-dai lokacinda ya faɗo duniya bai faɗi ƙasa ba, kuma
bai faɗo a kwance ba; hasalima da ƙafafunsa ya dira ƙasa,
inda akan idon kowa yai taku ɗaya, biyu, har zuwa taku
bakwai yana fuskantar gabas, sannan ya faɗi!
A lokacin waɗanda suka halacci wannan haihuwa suka
rankaya zuwa ga sarki baban wannan yaro, suka labarta
masa. Amma bai yarda dasu ba, hasalima sawa yai a
daina zancen, wai acewarsa baya son a ringa yiwa ɗansa
kallon wani mai aljanu ko kuma wani mai rauhanai.
Haka wannan magana ta mutu a bisa umarnin sarki.
Amma kuma wani abin mamaki shi ne, sai ya sawa yaron
suna Báya, ma'ana bakwai kenan da yaran wannan gari
da ake kira da Wilburish.
A kwana a tashi saida wannan yaro mai suna Baya ya
girma ya zama hamshaƙin sadauki, ya kuma ɗaga
martabar ƙabilar zuwa ƙololuwa aduniya, hasalima ance
har gogayya ya yi da mutane irinsu Haruta Ururu da
Maruta Ururu, dama irinsu Tarifil-fakta da kansa, da dai
sauransu!
Ana nan ana nan, watarana ya auri ɗaya daga cikin
ƴaƴan manya-manyan ƙabilar Ururu. Wadda ake kira
Dáya Ururu.
Lallai kowa zaiyi mamaki ace ƴan wata ƙabila sun samu
auren maɗaukaka ƴan ƙabilar Ururu. Wanda abu ne da
ba'a taɓa yi ba a tarihi hasalima sarki ɓisa doron ƙasa ta
farko, wato Sarki Ururu da kansa ya haramta yin hakan. A
cewarsa za'a lalata masa jini idan aka sirka shi da wani.
Amma a wannan lokaci shida kansa ya amince da
wannan aure.
Kowa daga cikin manyan sarakuna sunyi mamaki sosai,
hasalima da dana daga cikinsu sun nemi aure daga Ururu
tun iyayensu da kakanninsu sama da shekaru dubu
amma an hana su. Yau gashi an bawa wannan yaro mai
suna Baya ɗan gidan sarki Azába.
Saboda haka hankalin duniya ya tashi, duniya ta girgiza.
Babu yadda ba'ai ba a hana wannan biki ba, amma saida
ya afku. A ranar wannan biki duk wani wanda ya isa a
duniya saida yaje domin ganewa kansa wannan al'amarin
mamaki.
Dáya Ururu sanye da baƙaƙen idanuwan ta da kuma
farar fata mai walƙiya samfurin jarirai irin wadda bata
taɓa ganin ƙura ba. Ta fito sanye baƙar rigar ta kalar
idanunta. Lallai ko acikin Ururu, Dáya na daga cikin
kyawawa ababen misali. Labaranta na daga cikin
waɗanda ake labartawa acikin littattafan mata kyawawa a
wannan zamani.
Bayan biki, babban sarki Ururu yasa aka bawa Baya Azaba
sarauta kuma aka naɗashi sarki daga cikin daulolin dake
ban ƙasa ta farko.

Bayan shekaru uku, Daya Ururu ta haifi ƴan biyu; ɗaya
yaro santalele ɗaya kuma mace, ALLAH yasa yana wajen,
kuma ɗaya daga cikin waɗanda suka karɓi haihuwarsa,
wata ƴar tsohuwa mai yawan farin gashi ita ma na wajen,
duk da ta tsufa da yawa a lokacin.
Yaron farko daya fito, babu wani abu na musamman
daya faru, amma na biyun yana fitowa ya tsaya cak da
ƙafarsa kuma ya fara tafiya, bai tsaya ba saida yayi taku
ɗai-ɗai har bakwai.
Wannan sarki na ganin haka, abubuwan da aka gaya
masa a lokacin haihuwarsa suka fara dawo masa.
Tun daga lokacin ya sawa wannan ɗa nasa ido, har ya
girma, kuma cikin mamaki shima yaron ya girma ya
zama shahararre kamar babansa.
Kuma a lokacin wannan ɗa nasa ne aka canja sunan
ƙabilar ya koma Báya-Jidda, daga asalinta na Jidda. Wato
ya ƙara sunan kakansa wato Báya a farkon sunan ƙabilar.
A haka a haka aka ringa samun ire-iren waɗannan
mutane acikin ƙabilar Jidda (Bayajidda), wanda
dukkaninsu suke zama shahararru, kuma a ƙarshe su
suke zama katangar ƙabilar a zamaninsu.
Ana nan ana nan, abin ya fara yawaita har kusan kowa a
ƙabilar yasan da zancen, duk da basu bari maganar ta fita
waje ba, amma duk da haka sai suka sawa abin suna
'HAIHUWAR-SARKI', wanda daga nan aka samu sunan
'TAKUN-SARKI!'
Kwatsam sai wani abu ya faru wanda har a wannan rana
da Armad zasu kara da Ikenga ba'asan maiya jawoshi ba.
Wani haske ya ringa tashi daga saman wannan ƙabila har
tsahon kwana uku. Wanda daga baya ya ɗauke.
Tun daga wannan al'amari aka daina samun waɗannan
ƴan baiwa. Aka wayi gari an daina samun irin waɗannan
yara kwata-kwata a wannan ƙabila. Har saida akai sama
da shekaru dubunnai. Wanda hakan ya jawo cima baya
wajen ƙarfi da Izzar ita ƙabilar a tsakanin tsaranta. Harma
daga ƙarshe Ururu suka cire su daga layin sirakansa.
Zamanin daya zo daga baya har saida aka manta da
wannan al'amari na Takun-Sarki a ban ƙasa.
___
Koda sarkin yazo nan a zancensa saiya rufe littafin, ya
kuma matso kusa da ɗan nasa yana cewa, "Inada labari
cewa shekaru goma sha an haifi wani yaro, wanda yazo
da wannan baiwa ta ban al'ajabi da ake cewa Takun-sarki.
"Kuma an sakawa wannan yaro suna Ikenga! Abinda ban
sani ba shi ne ko wannan yaro Ikenga shi ne dai wancan
Ikengan da aka haifa da wannan baiwa. Saboda haka nake
so ka gano min a yayin faɗanka dashi."
Wannan shi ne abinda ya faru tsakanin sarki Deniz Iluru
da ɗansa Bizaya kwana ɗaya kafin a fara wannan gasa.
___
To kunji tarihin Ikenga wanda acikin jininsa akwai sirri na
shekara sama da dubu biyu, sirrin da har zaisa Ururu da

kansu su haɗa zuri'a da zuri'arsa. Lallai akwai tarihi mai
yawa a tattare da Ikenga. Shin meye haƙiƙanin tsakanin
Ururu da ƙabilar Ikenga. Shin mai yasa sarki Deniz Iluru
yake so ya gano tarihin Ikenga.
Nidinne dai Shuraih Usman inkiya
99%
Daga taskar magajin wilbafos
Marubuci: Dr Abdullahi Muhammad Ibrahim
Babi na 43: Karan batta
Post by: Shuraih Usman
@shuraih 99%
www.facebook.com/hausaebooks
.
Daga:- Taskar Magajin Wilbafos
A wannan lokaci, alƙali Gali, cikin ɓacin rai ya sanar cewa
Ikenga ne yaje zagaye na ƙarshe, inda zasu kara da
Armad.
Da dama dai abin bai musu daɗi ba, musamman tunda
yawancin su Denizawa ne, kuma su na so suga nasu yaje
zagayen ƙarshe. Amma tunda babu yadda zasuyi, kuma
musamman bayanda suka ga shi kansa Bizaya bai damu
ba, sai kawai suka ajiye abin a gefe, kuma suka fara
zancen zagayen ƙarshe, wanda shi ya kamata ace yafi
kowanne ƙayatarwa.
A wannan lokaci ne, alƙali Gali ya sanar da cewa abisa
doka, indai babu mai mummunan ciwo acikin waɗanda
zasu buga wasan ƙarshe, to cikin awa shida masu zuwa
za'a fara wasan ƙarshe.
Da aka tambayi Ikenga ko yana da wani rauni da yake
neman a ɗaga lokaci, sai yace shi bazai bar cikin filin
bama. Yana nan a inda yake tsaye, lamarinda ya ƙara
ɗaga ƙimarsa a tsakanin ƴan kallon nan.
Shi ma Armad da aka tambayeshi, amincewa yayi da
lokacin awanni shidan.
Kamar ƙifta ido awa shida ta doso kai!
Acikin wannan awa shida Nusi ta gabatowa Armad da
wani labari mai daɗi.
"Armad."
"Na'am yaya Nusi, na shirya fa, ki daina damuwa sosai,
kinji." Armad ya amsa mata cikin tsokana, a zatonsa
maganar data saba zatai masa. Amma baisan wani abu ne
daban ba.
"Kasan mai zance maka ne a'a! Kuma nace maka ka daina
cemin yaya." Nusi ta canja fuska haɗe da ɗan murmushi.
Ga dukkan alamu su biyun sun fara sabawa sosai. "Indai
kaci nasara a wannan fafatawar to lallai muna da damar
zuwa garin Shadeniz. Domin kuwa munyi magana da ƴan
uwana da muke so mu buɗe garin tare.
"Kai koda bamu samu damar buɗe ƙofar garin ba, lallai
zan samo maka labari akan Tarifil-fakta. Kai dai kawai ka
dage kayi nasara, kaji!"

Please Login or Register in order to submit comment