Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Miyurar dake goshin Armad ya
bayyana ƙarara.
Kafin kace meye wannan jama'ar wannan ƙauye sun fara
ajiyar zuciya, babu abinda kake ji illa, ''wannan Miyura
dake goshiɓ wannan yaro... kai..... Ai.... Ita ce...
''wannan Miyura.....ai...ita yanzu aka nuna mana a
jawabin nan....
''Kar dai ace......wannan yaro.....shi.....ne...
"shi....ne!!!"
***
To fa, shi ne wa?? Waye zai canka
Nidinne dai Shuraih Usman inkiya
99%
Daga taskar magajin wilbafos
Nan take kace-nace ya ɓarke tsakanin al'ummar wannan
ƙauye, ''hmmm... wannan yaron.. Ƙardai ace shi ne
Magajin Wilbafos ɗin?" Inji wani ɗan saurayi daga cikin
mutanen garin.
Sai dai kuma amma wani dattijo daga gefe najin haka ya
waiwayo a fusace ya dubi wannan saurayi tare da cewa,
''Ah haba dai, kai kasan matsayi da ƙarfin Izzar waɗanda
suka taɓa hawa kan wannan muƙami kuwa, ku dubeshi
fa.... Izzarsa fa bata fi hamsin ba, haba dai."
Nan take saurayin yai ajiyar zuciya, ''Hmmm.... hakane,
to amma kuma ai wannan Miyurar dake goshinsa ita ce
sak irin wadda aka nuna mana yanzu."
Dagacin wannan gari najin wannan magana da suke
tattaunawa ya tari numfashinsu tare da cewa, ''To koma
dai menene wannan shi ake cewa tsuntsu daga sama
gashasshe.
''Wannan ƙauye namu Kanwa, lallai kyauta ce daga
ALLAH, saboda haka ni ina ganin kawai mu kamashi, mu
siyarwa da ɗaya daga cikin manyan ƙasashen nan na
arewa. Nasan ko shi ne, koma bashi bane, lallai zamu
samu kyauta mabayyaniya.
''Sannan kuma koda ya zama bashi bane ba aiba komai.
Ko ba komai baza muyi dana sani ba, idan ya zama shi ne

kuma muka bari ya suɓuce mana.''
Wannan sune maganganun da waɗannan mutane acikin
wannan ƙauye suke tayi, idanunsu cike da buri da
haɗama.
Kafin kace meye wannan tuni da dama daga cikinsu sun
cimma wannan matsaya, inda kafin kace meye wannan
tuni sun fara matsowa kusa dasu Núsí da Armad wanda
yake tsaye cak ko motsi bayayi, idanu a rufe.
A wannan lokaci, duk abinda ke faruwa Nusi na kallo,
kuma babu abinda yake juyawa acikin kanta banda
lissafin yaya zata fitar dasu daga wannan hali.
Domin komai a fili yake a gareta cewa kowanne mataki ta
ɗauka, to shi ne zai zama ƙaddarar wannan yaro, saboda
baima san inda kansa yake ba a halin da ake ciki.
Tai tunani cewa lallai wannan yaro duk da ta gama gaya
masa labarinta dalla-dalla, yadda bata taɓa gayawa wani
ba, amma duk da haka bai yadda da ita ba.
Hasalima bama a rashin yadda abin ya tsaya ba, a'a sai
ƙarya da ɓoye-ɓoye kawai yake mata, wata bayan wata;
misali tabbas ta gamsu zuwa wannan lokaci cewa
sunansa ba Djinn bane, amma yaƙi gaya mata na
gaskiyar, yama share shancen.
Sannan kuma ga al'amarin tambarin goshinsa wanda
shima bai gaya mata ba!!
Saboda haka tayi tunanin cewa abu mafi dacewa da
zatayi shi ne ta rabu da wannan yaro tayi hanyarta.
Ta haka kaga bata janyo kanta cikin wannan husuma data
shafe shi ba.
To amma duk da wannan tunani, zuciyarta taƙi
amincewa da hakan. Kuma abinda take gaya mata shi ne
lallai ya kamata ta taimaki wannan yaron duk da kuwa
zuciyar tata tana da yaƙinin cewa babu wani alkhairi da
zai fito daga wannan mataki.
To komai dai ɗan lokaci ne, domin tasan lallai tana da
buƙatar ta yanke shawara cikin zafin nama kafin
waɗannan mutane su cimmusu, in ba haka ba kuwa
dukkansu lallai halakarsu tazo, domin babu tayadda zata
iya da dukkan mutanen ƙauye guda ita kaɗai.
Bata san mai yasa ba, sannan kuma bata da wani dalili
mai ma'ana acikin ranta, amma kawai cikin tsananin zafin
nama ta miƙa hannu inda ta cafe wannan jan kyalle
wanda tunda ya fizge daga kan Armad yai sama kuma sai
a wannan lokaci yake faɗowa.
Tana fizgarsa kawai kanta tsaye taja hannu Armad da
ƙarfin tsiya da niyyar su ɓace daga wajen.
Amma ina, ko motsi baiyi tamkar an kafeshi a wajan
saboda haka ita ma ja birki.
A dai-dai wannan lokaci, suma waɗannan mutanen garin
da suka ga tana ƙoƙarin guduwa sai suka ƙara sauri, inda
suka fara gudu domin su cimmusu.
Kai hatta waɗanda da basu motsa bama, saida suka
nufosu, wasu da makami wasu babu. Kafin kace meye

wannan tuni baifi saura taku biyu ba a tsakaninsu ba.
Nan take wani tunani ya ƙara gilmawa ta zuciyar Nusi,
cewa idan har mutun yayi niyyar yin abu, toai kwanda
yayi shi da cikakkiyar niyya, ko kuma kawai a haƙura.
Wannan tunani yana gilmawa a zuciyarta, kawai ta zira
hannu cikin mayafinta, inda ta zaro irin Ayrid daga ciki,
wanda ya kasance yana da kala ruwan ƙasa, sannan kuma
girmansa yakai kimanin rabin babban ɗan-yatsa. Kallo
ɗaya kacal zaka san cewa na musamman ne.
Tana fito dashi ba tare da ɓata lokaci ba, ta sakeshi ya
nufi ƙasa.
Yana taɓa ƙasa ya nutse, wanda hakan na faruwa wani
ɗan ƙaramin keken doki ya bayyana a dai-dai inda Ayrid
ɗin ya nutse.
Yana bayyana ya fara ƙara girma, kuma kafin ƙiftawar ido
da bismilla ya kai taku ɗaya, inda ya maye gurbin ƙasar
da su Nusi ke kai, wato suka zamanto tamkar acikinsa
suke.
Nan take Nusi ta haɗa hannayenta guda biyu, inda ta
furta wasu ɗalasimai.
A lokacinda mutanen garin nan suka ga wannan keken
doki na faɗaɗa sai suka fuskanci lallai idan basuyi da
gaske ba, to fa lallai tsuntsunsu daga sama gasasshe zai
guje musu.
Saboda haka sai suka fara jefa makaman dake hannunsu
domin raunata su, a ƙoƙarinsu na su hanasu guje musu.
A dai-dai lokacinda wasu masu suka kusa cimmusu, ita
kuma Nusi take ƙoƙarin karesu, sai kawai wannan keken
doki ya fara haske.
Kaɗan da kaɗan ya fara, amma kafin kace meye wannan
tuni ya cika wajen, tayadda wannan mutane basa ko iya
ganinsu Armad.
Wanda hakan yasa dole suka ci birki, gami da kewaye
dukkan wajen da niyyar hasken na ɗaukewa suyi taron
dangi, wajen cafke su Nusi.
Amma haƙarsu bata cimma ruwa ba, domin kuwa bayan
daƙiƙa uku hasken ya fara raguwa, kafin daga bisani ya
ɗauke baki ɗaya.
Inda sukai arba da fili kawai, babu su Armad babu
dalilinsu.
***
Shi dama Armad bai san inda kansa yake ba, saboda har
yanzu bai san abinda ke faruwa ba.
Amma ita kuwa Nusi tunda hankalinta nanan,
kasancewar kuma wannan lokaci shi ne na farko data
taɓa yin amfani da irin wannan fasaha, saboda haka tasan
menene amfaninta amma bata san menene hatsarin
amfani da ita ba.
Shi dai wannan Ayrid ɗin data fito dashi, malaminta tane
ya bata shi saboda da ɓacin rana, kuma kamar yadda taji
ana amfani da shi ne wajan yin tafiya mai nisan gaske a
lokaci ɗaya, a lokacin da mutun yake fuskantar hatsari.

Saboda haka ta ajiye da niyyar yin amfani dashi wataran
idan ta shiga babban hatsari a rayuwarta da baza ta iya
guduwa ba.
Amma bisa mamaki gashi tayi amfani dashi a wani yanayi
da ba wannan ba.
Abu ɗaya data ayyana a ranta lokacin da take lazimta
wannan ɗalasimai shi ne garin Maikironomada.
Saboda haka wannan Ayrid mai sifar keken doki ya
ɗaukesu zuwa can, inda ya watsar dasu a ƙarshen wani
daji wanda daga nan baifi tafiyar wuni bace tsakaninsu da
garin na Maikironomada ba.
To amma sai dai kamar yadda aka bata da cikakkiyar
masaniya akan hatsarin amfani da wannan fasaha.
Saboda haka suna dira kanta ya fara juyawa, inda kafin
kace meye wannan ta faɗi ƙasa sumammiya.
Shi kuwa Armad yana tsaye ido a rufe, har a wannan
lokaci baisan meke faruwa.
Abinda kuwa yasa ta suma shi ne, shi wannan Ayrid,
fasahar sa tana zuƙe Negrinkin jikin mai amfani da ita ne.
A saboda hakane bayan Negrinkin jikin nata yaje ƙarshe
ta yadda ana ci gaba da zuƙa, to sai dai ta kuma ta mutu.
Sai wannan fasaha ta tsaya cak, wanda kuma hakan ne
ma yasa basu isa cikin garin na Maikironomada ba,
hasalima a dokar daji ya watsar dasu.
***
Acan wannan ƙauye kuwa tuni mai garin, ya tara dukka
ƴan majalisarsa kuma suka yanke shawarar cewa bazasu
bari wannan yaro da suka samu ya tafi a banza ba.
Saboda haka suka samo ma'abota zane, waɗannan suka
zana siffar Armad komai da komai, sannan kuma da
bayanansa.
Cikin kwanaki uku suka tashi ƴan aike inda suka aikesu
wasu garuruwa dake bawa wannan ƙauye tsaro, da
wannan zanuka, da niyyar inganta dangantakarsu da
kuma siyarwa da duk wani maɓuƙaci wannan hoto na
Armad.
***
A kwana na biyar bayan wannan keken doki ya watsar
dasu acikin dokar daji, Nusi ta farka, ta kuma tararda da
kanta acikin tanti, Armad kuma a gefenta ya rufe ta
kayayyaki, sannan kuma ya haɗa wasu yayi mata
matashin-kai dashi.
Bayan farkawar ta ya kawo mata abinci taci tasha, sannan
kuma ta samu nutsuwa.
Kallo ɗaya kacal tayiwa Armad ya gane cewa ranta a ɓace
yake a game dashi, kuma dama a kwana biyar ɗin da suka
wuce tun bayan sanda hankalinsa ya dawo jikinsa, ya
tabbatar da cewa lallai wani babban abu ya faru wanda
yasa bai gansu acikin wannan ƙauye ba, amma kuma
gasu a tsakiyar daji.
Saboda abu na ƙarshe da yake iya tunowa shi ne wannan
ƙauye da kuma wannan takarda dake ɗauke da sunan

Tirifil-fakta.
Saboda hakan nema ya riga ya yanke shawarar cewa
lokaci yayi daya kamata ya amince da wani a doron
wannan ƙasa da bai san kowa ba.
Kuma yasan cewa indai har yana da buƙatar ya amince
da wani to Nusi ita tafi dacewa.
Kuma babu aminta idan akwai ƙarya! Saboda haka ya
yanke shawarar gaya mata sunansa na gaskiya a duk
sanda ta farka.
Tana kuwa yi masa wannan kallo ya ce, ''ehmmmm...
yaya, suna na er... Armad Wilbafos!''
Fuskarsa cike da murmushin ban haƙuri ya kwashe
dukkanin abubuwan da suka shafi Miyurarsa da kuma
sunansa da ma yadda sukayi da antinsa Jushaya ya gaya
mata.
Bayan ya gama gaya mata, sai tayi shiru kawai tsahon
lokaci.
Kai har saida tunane-tunane suka fara yawo acikin
zuciyar Armad akan ko mai yasa tayi shiru bata ce komai
ba.
Amma bayan kimanin rabin rabin sa'a, saita ɗago kai,
fuskarta babu alamun fushi ko kaɗan kuma ta dubi
Armad gami dayin kyaran murya sannan ta fara kawabi,
''To amma yanzu meye abinyi.
"Domin a halin yanzu, bawai neman Tirifil-fakta bane
mafi muhimmanci a gabanka ba, a'a, kare kanka shi ne
mafi muhimanci!
"Domin kuwa kaima yanzu kaine abin neman! Domin zan
iya ce maka yadda duniya take nemansa, kaima haka za'a
fara farautarka, banbancin kaɗan ne!!!"
MAGAJIN WILBAFOS
Marubuci: Dr Abdullahi Muhammad Ibrahim
Babi na 22: shiga garin maikironomada
Post by: Shuraih Usman
@shuraih 99%
www.facebook.com/hausaebooks
.
Daga:- Taskar Magajin Wilbafos
Armad na zaune jingine a gindin wata bishiyar darbejiya,
kansa yana kallon wata daren goma sha bakwai a sararin
samaniya.
Irin iskar daren nan mai ɗan sanyi tana kaɗa rigar jikinsa
da kuma maɗaurin kansa.
Babu abinda kake ji face kukan tsuntsaye da namun dawa
a kusa da nesa. Amma ga dukkan alamu, dukkanin
waɗannan abubuwa basu isa su katsewa Armad tunanin
da yake ba, domin kuwa kallo ɗaya kacal zakai masa
kasan cewa ya tsunduma cikin kogon tunani.
Can bayan wani lokaci mai tsaho, ƙarar bushasshen
ganyen bishiya da ake takawa ta bayansa yasa ya farka
inda ya waiwaya domin yaga wake kusato shi.
Nan kuwa yayi arba da Nusi, ita ma ta fito daga cikin

tantin da suke, idanunta sun ɗanyi ja kaɗan, daga dukkan
alamu ta ɗan gimtsa kuma bata daɗe da tashi ba.
Tun kafin ta ƙaraso, suna haɗa ido tayi masa murmushi.
Sannan kuma tayi kyaran murya gami da cewa, ''Armad
ƙanina!''
Tana faɗar haka, a karon farko run bayan haɗuwarsu
wata ƴar ƙaramar dariya ta kwace mata, kafin daga
bisani taci gaba, ''hmmm... kasan ko, ko a iya nan ka
tsaya ka koma gida, na tabbata mahaifiyar ka zatai
matuƙar farin ciki da jarumtar daka nuna....'' Nan take
lafazinta ya ƙara taushi ya kuma juya mai kama da
lallashi, ''basai ka matsawa kanka ba, idan muka mu
ƙarasa cikin gari,'' ta ɗaga ɗanyatsan gami da yi masa
nuni da wani waje daga can nesa ɓangaren arewa inda
wani haske yake tashi.
''Akwai kuɗi na da zan karɓa na cin wannan jarabawa,
nasan zai isa ka hau Ecigan har zuwa doron ƙasa ta uku.
''Hmmmm....karka damu, kyauta na baka, ba kace ni
yayar ka bace!'' Ta ƙarasa maganar ta da wani lafazi,
kamar tana jin tsoron kada yaƙi amince da biya masa da
tace zatai.
Shima Armad murmushi kawai yayi sannan barta ta
ƙaraso inda ya fara nasa jawabin, ''na yanke shawara,
saboda dalilai guda uku;
''Na farko, lallai haƙiƙa ina so na koma gida wajen
dangina, musamman yadda na fara ji a jikina cewa lallai
na daɗe bamu haɗu dasu ba.
''To amma a yadda nake ɗinnan, ko na koma bana
tunanin idan ma wani rikici ne ko kuma yaƙi ya taso zan
iya taɓuka wani abu.
''Sai dai ma wataƙila na kawo musu cikas kawai, saboda
kamar yadda nake gaya miki har yanzu na kasa kammala
koyon ko ƙarni na farko na 'Wilbafosiyan siwod dans'.
''Saboda haka lallai bana jin zan ƙara musu wani abu.
''Sannan kuma na biyu, ina ganin na fara fahimtar kaɗan
daga cikin dalilin da yasa dangina suke ɓoye wannan
sunan.
''Saboda ina ganin suna na yana alaƙa da neman wannan
mutun mai suna Tirifil-fakta. Ina tunanin ma shi ne yasa a
duk cikin manyan kwamandojin Troika suka zaɓi
mahaifiya ta domin ta jagoranci nemansa a wancan
lokaci.
''Saboda haka, indai akwai dama, ko yaya take, na cewa
zan cika burin mahaifiya ta na nemo wannan mutun
koma wanene, to bazan jada baya ba, ko kaɗan har sai
ranar da na cika buri na!!!
''Kuma ina ganin haɗuwa ta dake ƙaddara ce daga ALLAH,
kamar yadda kike ta taimako na baji ba gani.
''Ina ƙara gode miki yaya, kuma ina fatan nima ALLAH ya
bani damar dazan rama miki wannan alkhari. Saboda
haka inaga wannan ita ce shawara t........."
Kwatsan ya katse zancensa, bai san mai ya faru ba, shi dai

kawai yaji an jefo masa wani abu a fuskarsa, kafin ya
ɗago kai daga bisani ya kuma yi arba da Nusi tana huci
akansa.
''kada ka ƙara cewa idan nayi maka abu zaka biyani!!!
''Darasi na farko; babu irin wannan godiyar tsakanin ya
da ƙani!''
Nan fa bayan ya gama saurararta ya dage abin da kyar, ya
ƙaƙalo wani ɗan murmushi mai kama da yaƙe, amma
acikin ransa kawai cewa yake, lallai tana da zafin nama,
ko motsin tahowar abin nan banji ba!
Abu na gaba daya gani shi ne Núsí ta gama haɗa musu
kayansu, kuma harta fito, inda ta cilla masa jakarsa ita
ma ta rataye tata, gami da cewa, ''yafi kamata mu shiga
cikin garin yanzu da daddare, saboda wasu dalilai.
Nan take suka fara tafiya su na gudu-gudu sauri-sauri a
ƙasa inda suka nufi wajan hasken nan data nuna ɗazu,
wanda shi ne ya kasance ɓangaren garin da zasu je.
''Garin da zamu shiga sunansa khan, kuma yana ɗauke da
sama da mutane dubu ɗaruruwa. Amma kuma duk da
haka shi ne mafi ƙanƙanta acikin garuruwa huɗu dake
wannan ɓangare.
''Kuma sama da kaso casa'in na mutanen garin baƙi ne,
wato dai ba ƴan ƙabilar Maikironomada bane.
''Amma kuma dukkanin wanda ya shiga garin amintacce
ne a ma'aunin Maikironomada. Idan mun ƙarasa bakin
ƙofar garin zaka fuskanci abinda nake nufi da hakan.
''Kasaka a ranka cewa amfanin shigarka garin nan shi ne,
ka reni irin Izzarka, ta yadda kaima a hankali zaka zama
ma'aboci Izza.
''Kaga a wannan lokaci, koda tsautsayi yasa wani ya gano
kasancewarka magaji, zaka iya ɗaukar matakin daya
dace, sannan kuma zai zamo ba kowa bane zaiyi mafarki
gabato kaba da sharri.
''Ba kamar yanzu ba da ba wanda zaiji tsoronka ba.'' Ta
kalleshi sama da ƙasa tamkar wacca take mamakin ya
akai har yanzu yake raye.
Amma Armad ko a jikinsa, kawai kallonta yayi kuma yai
dariya, domin ya riga ya gane cewa ƙoƙari kawai take,
nata saka shi ya ƙara himma, da kuma kada ya sa ran
mataki Izzarsa ta ishe shi a haka.
''Zanyi duk wata mai yiwuwa domin ganin ka samu duk
wata dama data dace domin ƙarfafa maka gwiwa,
ragowar kuma ya rage ya naka.
''A sanda kake bacci, tuni na tura saƙo ta Ayrid zuwa ga
mutane na, kuma tuni sun kama maka layi na shiga Nontoch-teka! Saboda haka ka zama cikin shiri.''
To duk da yake wannan bashi bane karo na farko ba,
daya ji kalmar Nin-toch-teka ba, amma jin cewa koma
mene ne , wannan lokaci ya shafe kai tsaye, yasa yayi
hanzarin yin tambayar, ''wai yaya, menene wannan
abinne, waishi Non-toch-teka?''
Ta kalleshi kawai fuska cike da mamaki, sannan tace,

''hmmm.. bani da masaniyar meke wakana a doron ƙasa
ta uku, amma a iya sani na duk wani mai Miyura yana da
buƙatar Non-toch-teka.
''Amma karka damu, yanzu dai ka gane cewa wata
hanyace da zata taimaka maka wajen sarrafa Negrinkin
ka da kuma Fotenshiyal-sifes ɗinka, ragowar kuma saika
gani da idonka.''
A dai-dai lokacin da tazo nan a zancenta suka fara hango
katangar gari ta tashi sama, sannan kuma ga ƙatun ƙatun
ɗin ƙofofin gari nan guda biyu suna kallonsu daga nesa.
Ɗaya baƙa ɗaya kuma yaluwa!
Tun daga nesa mutun zai iya hango ƙatun-ƙatun ɗin
mutun mutumi nan guda shida manya-manya a bakin
yaluwar ƙofar, sannan kuma guda ɗaya a bakin baƙar
ƙofar.
Suna ƙara kusanta wannan ƙofofi suna ƙara girma da
waɗannan mutun mutumi. Sannan kuma suka ga mutane
a kan layi a bakin wannan baƙar ƙofar.
Sai dai kuma babu mai gadi, amma duk da haka
waɗannan mutane dake bin layi a nutse suke babu ko
ɗaya mai nuna alamun son yin rige ko kuma turereniya
ko kuma hayaniya.
Kai duk da tsakiyar dare ne saika nutsu sosai zaka iya
tsuntar magana ɗaya biyu.
Kafin ma su ƙarasa waɗansu mutane sanye da fararen
kaya suka bayyana a gabansu.
Ɗaya fari mara jiki, mai kama da ɗan fulani, ɗaya kuma
wankan tarwaɗa sannan kuma murɗaɗɗe.
Duk da fuskokinsu a sunkuye suke, amma zaka iya
fahimtar cewa wankan tarwaɗar bazai yi barkwaci ba ko
kaɗan ba kamar mai kamar ƴan fulanin ba, sannan
bazaiyi magana sosai ba.
Mai kamar ƴan fulanin ya fara magana cikin ladabi,
''barka da zuwa yaya Núsí, da fatan kin iso lafiya.''
Fuskarta cike da murmushi ta amsa da cewa, ''Basharu,
Kamálu, ba sai kun sunkuyar da kawunanku ba.'' Amma
duk da haka bai sa sun ɗago kawunan nasu ba.
A saboda haka kawai ta girgiza kai tayi murmushi, gami
da ajiyar zuciya, ''toh, da fatan na sameku lafiya.''
A wannan lokaci ne wani abu ya fara gayawa Armad cewa
lallai Nusi babbar mutun ce acikin wannan gari. Nan fa ya
fara tunanin wacece harda ake mata irin wannan ladabi??
Nan take su biyun suka juya gami da cewa, ''mun gama
shirya komai, mu ƙarasa zuwa ciki.''
Nan take suka juya suka nufi wannan ƙofofi.
Tunda suka bayyana ƴan tsirarun mutanen dake tsaye a
bakin baƙar ƙofar nan, suka waiwayo suke kallonsu.
Amma a ciki babu wanda ya gane su, da dama ma ɗauke
kai sukai.
Amma can bayan wani lokaci sun ƙara kusantar katangar,
sai kuwa ɗaya daga cikin waɗannan mutun-mutumi guda
shida suka ya buɗe idonsa inda wani haske ya feso daga

ciki ya nufo su.
Kafin kace meye wannan tuni, wajen da da yake shiru tsit,
ya hargitse da hayaniya, ana nunosu da hannu.
Wannan haske bai tsaya ko ina ba, sai akan fuskar Nusi.
Yana taɓa fuskarta ya shuge ciki kuma ya ɓace ɓat.
Tamkar babu abinda ya faru, sai dai kuma a wannan
lokaci idanun ta a rufe suke ruf.
Nan take suka nufi wannan yaluwar ƙofa gadan-gadan,
inda suna isa Armad ya fara ƙoƙarin tsayawa domin a iya
kallonsa babu hanyar wucewa, saboda waɗannan mutunmutumi, amma bisa mamaki sai yaga sun wuce ta cikinsu
tamkar ma babu su a wajan.
Saboda haka shima kawai yabi bayansu da niyyar
wucewa.
Amma abu na gaba daya gani shi ne jini yana tsiyaya ta
goshinsa, sannan kuma yana zaune a ƙasa zaman
dirshen.
Ba komai ya jawo haka ba kuwa illa karo da yayi, da ɗaya
daga cikin mutun-mutumin nan guda shida. Inda ya daki
kansa, kuma kafin kace meye wannan ya fasa kai jini ya
fara zuba, gami da faɗuwa ƙasa dirshen.
Ɗaya daga cikin abubuwan mamakai na wannan ƙabila
ta Maikironomada shi ne, a tsahon shekaru da dama da
suka gabata a bakin ƙofar kowanne gari, abu ne sananne
cewa akwai manya-manyan mutun-mutumi, waɗanda
yawansu ya banbanta tsakanin kowacce ƙofa daga cikin
ƙofofin shiga garuruwan nan guda huɗu.
Misali a garin Khan, yaluwar ƙofa nada shida sannan baƙa
kuma nada ɗaya.
Kuma duk da matuƙar kama da na gaske da waɗannan
mutun-mutumi sukai musamman idan ka hangesu daga
nesa, amma kowa yasan cewa ba na gaske bane, kamar
hoto suke na magiji, tayadda zaka iya wucewa ta cikinsu
kai tsaye ba tare kaji komai ba.
Waɗannan mutun-mutumi bawai dasu aka ƙirƙiri ƙofofin
nan ba, a'a a hankali a hankali shekaru su na wucewa aka
samesu.
Ta wata hanya wadda kusan duk wani ɗan ƙabilar
Maikironomada ya sani, kuma yake burin shima ya isa
wannan mataki.
Kai har amintattun baƙi ma daga cikin garin Khan suma
su na burin kaiwa wannan mataki, duk da kuwa sanin
cewa, kusan abu ne da bazai taɓa yiwuwa ba, amma
bazasu iya daina burin hakan ba har sai sun jisu a kabari!!
Alƙaluman da kowa ya sani su ne na mutumin ƙarshe
daya saka mutun-mutumi ɗaya ya ƙaru daga na garin
khan, wanda hakan yai matuƙar ɗaga darajar gabaki ɗaya
garin har ya zuwa wannan lokaci.
Wannan ba kowa bane illa wani da ake kira da Bihanzin!
Kuma wanda ya ƙaru shi ne wannan guda ɗayan dake
baƙin baƙar ƙofar, kasancewar a lokacin da zai fara shiga
garin, ta wannan ƙofa ya shiga.

Abinda aka sani shi ne duk wanda ya samu damar fito da
ɗaya daga cikin waɗannan mutun-mutumi alamu ne na
cewa tauraruwar sa zata haskaka a duniya, saboda haka
aka saka musu sunan Al'yaya.
Kalmar da a Aldurish( yaren Alderiya) take nufin
maɗaukakin jarumi.
A dai-dai lokacin da Armad yaje ƙasa wani haske mai
tsananin kashe ido, ya tashi sama gami da haskaka
sararin samaniya.
Sannan kuma tamkar wanda yake son ya tabbatar kowa
acikin garin ya tabbatar da meke faruwa, ya nausa bayan
gatangar ya kuma shiga cikin garin, inda kafin kace meye
wannan tuni ya haskaka kowannna loko da saƙo na cikin
garin.
Kafin kace meye wannan tuni hayaniya da ruɗani ta fara
tasowa daga cikin wannan gari.
A dai-dai wannan lokacin su Nusi suka ƙarasa juyowa
wajen Armad wanda ke zaune a ƙas, jini na ɗisa ta cikin
jan ƙyallen daya ɗaure goshinsa.
Nan take ba tare da wani jawabi suka fara ƙoƙarin
rufewa Armad fuska, kasancewar tuni ƴan tsirarun
mutanen da ke tsaye a bakin baƙar ƙofar nan suka fara
azama wajan isowa wajan domin su ganewa idonsu
wanene ya zama ƙara zama Al'yaya.
Acikin garin kuwa a wata fada wasu mutun uku ne suka
bayyana, dukkaninsu daga ka kallesu zaka ga cewa
fuskokinsu a ɓace suke.
Suna sanye da alkyabba iri ɗaya mai ruwan baƙi da yalo,
tamkar ƙofofin wannan gari.
Kai idan kallesu sosai ma zaka iya hasashen cewa
muƙaminsu ɗaya ma.
Nan take ɗaya daga cikinsu ya ce, ''wannan ƙabila.....''ya
ƙara cije haƙora sannan ya kwalla, ''Djinn!!
''Kamar bai isheta ba dawowar da tayi ba, amma saita
taho wani, kuma waninma irin wancan wancan
mutumin.... Bihanzin!''
Ɗayan ya ce, ''yanzu dai meye abinyi, domin idan
bamuyi da gaske ba, to abinda ya faru da Bihanzin Djinn
shekaru ashirin da biyar da suka wuce, zai ƙara faruwa da
wannan yarinyar, Núsí Djinn''
***
Nidinne dai Shuraih Usman inkiya
99%
Daga taskar magajin wilbafos
MAGAJIN WILBAFOS
Marubuci: Dr Abdullahi Muhammad Ibrahim
Babi na 23: Matafiyan Alwashi
Post by: Shuraih Usman
@shuraih 99%
www.facebook.com/hausaebooks

.
Daga:- Taskar Magajin Wilbafos
Tuni labari ya bazu kusan ko'ina acikin garin Khan, cewa
ga abinda ke faruwa, kasancewar da dama sunada
masaniyar me wannan hasken yake nufi.
Saboda haka tuni mutanen garin suka fara tattauna
abubuwa da dama, wasu suna farin ciki wasu baƙin ciki
wasu kuma mamaki, kai wasu ma tuni sun fara azama
domin isa bakin wannan ƙofa domin ganewa idanunsu.
Amma ina haƙarsu bai cimma ruwa ba domin kafin ma
su kansu ƴan tsirarun mutanen da ke wajen su ƙarasa
suga fuskar Armad, sun nausa cikin garin.
Sannan kuma wata sa'a data faru, shi ne da dama na
mutanen baƙi ne, saboda haka suna da buƙatar subi ta
cikin wannan ƙofa a hankali, domin yana daga cikin
amfanin waɗannan mutun-mutumi duba zuƙatan masu
shiga garin, domin tabbatar da cewa basu zowa garin da
sharri ba.
Kuma hakan nema yasa a daular Maikironomada ake
auna girman gari da kuma falalar na cikinsa, da adadin
waɗannan mutun-mutumi da suke dasu.
Haka dai suka ci gaba hango su Armad har suka ƙule a
nesa.
Kafin daga bisani su juyo da dubansu kan waɗannan
mutun-mutumi guda shida.
Inda suka ga wannan haske da da ya tashi ya bazu ko'ina,
ya fara dawowa yana haɗuwa a tsakiyar waɗannan
mutun-mutumi shida.
To amma saboda bada sauri yake dawowa ba, kafin kace
meye wannan tuni haske asubahi ya fara kawo kai.
A lokacin kuma da dama na mutanen cikin garin sun fara
iso wa wajan, tayadda kafin rana ta ɗaga tuni sama da
mutun dubu sun hallara a wajen.
Wajen gaba ɗaya ya canja, daga shiru tsit a yadda Armad
ya ganshi zuwa mai kasuwa.
Mafiya yawa kuma abinda suke tattaunawa shi ne,
''wannan karan kuma bari muga wanne irin mutunmutumi ne zai fito.
A lokacin dake rana ta ɗaga, idan ka lura zaka ga banda
banbancin fuska da waɗannan mutun-mutumi ke da shi,
yanayin kayan jikinsu ma da banbanci.
Misali; uku daga ciki kawai ƴar shara ce da ɗan bante a
jikinsu, kuma babu makami ko ɗaya a hannunsu.
Biyu suna da alkyabba a jikinsu mai kyau duk da babu
makami a hannunsu.
Na ƙarshe kuma yana da wani dogon mashi a hannunsa,
amma babu alkyabba, kawai alamun doguwar riga ce a
jikinsa.
A cikin garin Khan kuwa, a shashin kudu maso gabashin
ƙasar, akwai wani ƙato gida mai tsayin gaske. A tsakiyar
wani lambu mai yawan bishiyun giginya.
A can ƙololuwar saman gidan acikin wani babban ɗaki,

zaune akan kujeru su Armad ne da Nusi da kuma
waɗannan mutane guda biyu.
Tuni sun gama yi masa maganin ciwon da yaji a goshinsa,
sannan kuma aka gabatar da ƴaƴan itatu da soyayyen
nama gami da fura da nono a gabansa.
Nusi ta dubeshi gami da yin ajiyar zuciya, sannan tayi
murmushi gami da cewa, ''ban taɓa tunanin irin abinda
ya faru da Bihanzin zai faru yau ba, shi yasa ban yi maka
bayanin waɗannan abubuwa ba.
''Amma ba komai, yanzu ka huta, ka ɗan samu bacci ko
yaya ne, da safe zan shigo na labarta maka duk abinda ke
faruwa.''
Tana faɗar haka Armad ya ɗaga kai da niyyar faɗa mata
wani uzurin da zai nuna mata cewa shi a yanzu yake son
yaji labarin. Kasancewar tuni zuciyar sa take masa sakesaƙen abubuwa da dama, a game da abubuwan da suke
faruwa.
Amma ina, tuni Nusi ta juya cikin sauri ta kuma fara fita
daga cikin ɗakin, kana ganinta kasan akwai abinda yake
ranta, saboda haka bai matsa ba, ya bari kawai saida safe.
A wannan dare shi kansa Armad yayi mamaki, sabida irin
baccin daya

Please Login or Register in order to submit comment