Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

dake ɗaure da Uznu Ururu,
rassan ta suka fara tamkewa suna ƙara girma da yawa.
Kai kan kace meye wannan tuni kowanne reshe ɗaya ya
koma dubu, sannan kuma dukkaninsu suka ɗaure Uznu
tamau ko jikinsa ba'a gani.
Haka na faruwa Nusi ta rame nan take, fuskarta ta fara
tsufa, wani farin gashi guda ɗaya ya bayyana a goshinta.
Babu abinda take sai haki, ko tsaiwa bata iyayi sai ta ɗan
rankwafa. Lallai wannan fasaha ta janye ƙarfinta da yawa.
Uznu Ururu kuwa na tsaye ɗaure cikin wannan bishiyar
tsafi baya ko motsi.
A dai-dai wannan lokaci ne sarki Deniz Iluru ya miƙe cikin
firgici, idanunsa na karkarwa. Ya juya ya dubi jaruman da
suka rako shi yana mai cewa, "Kuyi maza ku saka hijabi
tsakanin ƴan kallo da filin can!" Ya nuna inda Ururu ke
tsaye a ɗaure, "Waɗannan yaran sun jawo masifa. Yau
duniya zata kara yin arba da abinda ake kira da Ururu."
Yana magana yanayin fuskarsa na nuna girman halin da
ake ciki, "Domin mutane da dama basu san mai ake cewa
Ururu ba."
Ai kuwa bai rufe bakinsa ba Uznu Ururu ya yaye hijabin
dake rufe da idonsa, lamarinda yasa baƙaƙen idanun
nasa suka bayyana a fili. Kallo ɗaya zakai musu kasan
cewa duk abinda da ake gani bawai shi ne haƙiƙanin
idanun Uznu ba, domin kuwa asalin idanun nasa na
bayan hijabi.
Wasu manyan abubuwane suka bayyana masu kama da
wata da rana, baƙaƙe ne masu firgitarwa.
Bayyanarsu keda wuya Uznu ya ƙifta idonsa sau ɗaya
lamarinda yasa nan take wannan bishiyar tsafi da Nusi ta
ɗaure shi da ita ta narke. Sannan a lokaci guda yai duba
izuwa Nusi da Armad.
Armad tuni dama yake ganin duhu tunda farko da sukai
arba da Uznu, wanda hakan ne yasa ya kasa komai.
Amma a wannan lokaci kawai ji yayi wannan manyan
baƙaƙen abubuwa masu kama da rana da wata sun daki
ruhinsa, sannan suka fara karya shekarun Izzarsa suna
tarwatsa su.
Nan take ya faɗi ƙasa sumamme.
Ita kuwa Nusi kawai karkarwa take cikin tsoro da firgici.
Domin kuwa tuni ta ƙarar da ƙarfinta a harin da tayi na
farko, kuma bata taɓa tunanin ƙarfin Uznu yakai haka ba.
Domin acikin wannan bishiyar tsafin data ɗaureshi da ita
akwai sama da shekaru dubu na Izza.
Tana cikin wannan tunani taji wani abu mai kama da
nauyin dukkan duniya ya dake ta aciki, nan take ta jita
anyi cilli da ita can sama ta fice daga cikin gaba ɗayan
filin. Abu na ƙarshe da
ta sani shi ne aman jini da take kafin ta sume. Amma duk
da ta suma bata daina gudu a sama ba saboda wannan

duka da Ururu yayi mata. Taci gaba da tafiya inda taje ta
daki ƙarƙashin ƙasa sannan ta fice daga duniyar
ƙarƙashin ƙasa izuwa wata duniya ta musamman. Lallai
tasan rayuwarta na cikin hatsari a wannan lokaci domin
kuwa dukkan ƙasusuwan jikinta sun ruguje kuma kayan
cikinta sun farfashe.
--Shi kuwa Armad kamar a mafarki, yaji hannu yana shiga
rigarsa zai ɗauki littafin takobi, amma kuma sai yaji
Littafin ya narke nan take sannan kuma yaji shi ya shige
jikinsa baki ɗaya.
A wannan lokaci Uznu Ururu ya kira ɗaya daga cikin
Sadaukai biyar dake ƙasansa ya bashi umarnin ya ɗaukan
masa Armad izuwa babbar shalkwatar Ururu dake doron
ƙasa ta huɗu da niyyar aje a zaƙulo littafin daga jininsa.
***
A dai-dai wannan lokaci da ake shirin ɗaukar Armad a tafi
dashi fadar Ururu, Armad ya tsinci kansa a wani hali mai
ban mamaki.
Ya tsinci kansa a tsaye a wata duniya ta musamman. A
gabansa a ɗaure cikin ankwa wata ƙatotuwar halitta ce
wanda girmanta yakai zira'i dubu.
Yana ganin wannan duniya abinda ya fara zuwar masa kai
shi ne kodai mutuwa yayi ko kuma mafarki yake, saboda
haka tun bayan samun kansa a wajen Armad ya mari
kansa domin ya tabbatar shi ɗin ne ba wani ba. Inda ya
tabbatar lallai shi ne a tsaye a wajen ba kuma mafarki
yake ba.
Dukkan duniyar launin fara ce fat, babu wata kala banda
fari. Kuma shi Armad ɗin abu na ƙarshe daya ke iya
tunawa shi ne ganin idon Uznu Ururu da yayi da kuma
suma da yayi amma gashi a wannan waje.
Armad ya ƙurawa wannan halitta ido kamar yadda ita ma
take kallonsa.
A ƙololuwar kanta akwai ƙahonhuna guda uku, sannan
kuma idanunta koraye ne masu ratsin toka. Sannan kuma
fatar ta fara ce fat babu ko kwayar gashi.
Girman wannan halitta yakai yadda zaka iya cewa
ƙaramin ɗan yatsanta shi ne dukkan girman jikin Armad.
Bayan ɗan lokaci Armad ya numfasa ya dubi wannan
halitta tare da cewa, "Kaiko waye kai, kuma mai yasa aka
ɗaure ka, kuma sannan ina ne nan wajen?"
Wannan halitta ta dubi Armad cikin ɓacin rai tare da
ɗauke kai. Kallo ɗaya kacal zakai mata kasan cewa koma
mece ce, kuma koma ya ake ciki bata farin cikin ganin
Armad a wajen.
____
Ko wacce halitta ce wannan?
Nidinne dai Shuraih Usman inkiya
99%
Daga taskar magajin wilbafos
MAGAJIN WILBAFOS

Marubuci: Dr Abdullahi Muhammad Ibrahim
Babi na 50: Tsarin Ruhi
Post by: Shuraih Usman
@shuraih 99%
www.facebook.com/hausaebooks
.
Daga:- Taskar Magajin Wilbafos
Bayan wasu ƴan daƙiƙu na kallon-kallo tsakanin Armad
da wannan halitta, sai halittar ta buɗe baki ta fara da
cewa, "Idan da ka tsaya ka koyi al'amuran Izza a lokacin
da Hidaya take koya maka da baka tsinci kanka a wannan
hali na baƙin ciki da rasa yadda zakai ba."
"Ehmmmm!" Armad ya ja numfashi tare da haɗe gira,
"Nai maka tambaya baka bani amsa ba, waye kai?"
Halittar ta ƙara buɗe baki cikin ɓacin rai, inda wani farin
hayaƙi ya fito daga bakin, "Ni ne aljaninka JIDAIME! Baka
ma san aljaninka ba, baka san koda ma'anar Izza ba, baka
san tarihin Izza ba, baka san tsarin ruhinka ba, to tayaya
zaka iya gwada kafaɗa da manyan ma'abota Izza."
Armad bakinsa a buɗe yake ya kasa magana, babu abinda
yake kai-komo acikin ransa sai abubuwan da wannan
halitta ke faɗa. Da farko dai halittar tace ita aljaninsa. Ta
kuma ce baisan ma'anar Izza ba, bai san tarihin Izza ba,
sannan kuma bai san tsarin ruhinsa ba.
Lallai Armad bai yadda da waɗannan abubuwa ba,
hasalima yana ji cewa ai zancen banza ne ace baisan
ma'anar Izza ba, ko kuma ace baisan tarihin Izza ba,
tunda yayi karance-karance masu yawa akan al'amuran
Izza tun yana yaro. Sai dai kuma abu na biyu da aljanin ya
faɗa lallai Armad bai gane mai suke nufi ba.
Na farko zancen cewa shi ne aljaninsa Jidaime, domin
Armad bai taɓa ganin aljaninsa ba. Kullum abinda kawai
yake gani shi ne ɗan taƙin dake tsakanin ruhinsa da
aljanin nasa. Na biyu kuma Armad bai gane mai aljanin
nasa yake nufi da baisan Tsarin-ruhinsa ba.
Amma duk da haka Armad ya yanke shawara bari yabi
wannan aljani a hankali koya ci ribar zancen, "Jidaime?
Sunanka kenan. Da farko dai a sani na mutun baya iya
ganin aljaninsa sai yakai shekaru ɗari bakwai da ɗoriya na
Izza. To ta yaya nake iya ganinka bayan Izza ta bata kaiba?
Na biyu kuma na yarda bansan tsarin ruhi na ba, kuma
bansan tarihin Izza ba, saboda haka ka ganar dani. Amma
duk da haka, kada ka manta baka amsa min tambayata
ba: mai yasa kake a ɗaure idan kai aljani na ne, ko kuma
dukkan aljanu irinka a ɗaure suke, sannan kuma nan a
ina muke?"
Aljani Jidaime najin hakan wani ɗan murmushi ya gilma
ta gefen korayen idanunsa masu ratsin toka. Domin a
ɗabi'ar aljanu suna so a basu girma, kuma a yarda ba'a
sani ba sune suka sani. Saboda haka yana ji Armad ya
yarda bai sani ba ya juyo izuwa gareshi tare da buɗe

haƙoransa masu kama da farar kasa, "Bari na sanar dakai
ilmi.
"Kowanne bil-adama ana haifarsa da abinda ake kira da
Tsarin-Ruhi. Duk wani Tsarin-Ruhi yana ƙunshe da
abubuwa guda uku: Na farko aljani, na biyu takobi na
uku Izza.
"Kamar yadda ka riga ka sani kowanne mutun yana iya
sarrafa fasahohi daban-daban kamar na Wuta ko Ruwa
ko Ƙanƙara kwatankwacin aljaninsa. Kamar yadda ka
sami fasahar walƙiya daga gare ni. To wannan gabatarwa
ce kawai akan harkar tsakanin mutun da aljaninsa, kuma
da dama manyan ma'abota Izza sun ƙarar da rayuwarsu
gaba ɗaya akan gano wannan alaƙa amma basu gama ba.
Lallai mutun kamar ka wanda baima taɓa ganin aljaninsa
ba bashi da tacewa.
"Takobi ita ce abu na biyu a ɓangaren Tsarin-Ruhi. Kuma
anci sa'a bayanda ka rasa ƴar uwarka Hidaya ka farkarda
fasahar takobinka, kuma yanzu kana iya amfani da
fasahar takobi mataki na farko. Amma kayi sani cewa
baka san komai ba a wannan fage.
"Na uku a Tsarin-Ruhi shi ne Izza. Kamar yadda ka sani
Izza wani tsarin shekaru ne na musamman tsakanin
sadaukai ma'abota Izza, wanda yake basu damar ƙarin
tsahon rayuwa.
"To amma duk abubuwan nan guda uku daka ji baka san
komai ba akansu. Hasalima kai baka iya amfani da kaso
goma cikin ɗari na aljaninka domin ko kwance ni baka
yiba. Sannan kuma har yanzu baka iya haƙiƙanin amfani
da takobinka ba, daɗin daɗawa kuma Izzarka tayi kaɗan
da yawa. Kai hasalima kai baka ma san matsayi na a
tsakanin rundunar aljanu ba a matsayi ni aljaninka.
Saboda haka baka san komai ba a duniyar Izza, idan kana
so ka zamanto daga cikin manyan ma'abota Izza to
kwance ni, ni kuma na koyar dakai abinda kake buƙata ka
zama ma'aboci Izza.
"Kuma ban manta da tambayoyinka guda biyu ba: na
farko dai nan kana cikin duniyar aljanu ne, nine na janyo
ka nan domin na gaji da ganinka a wulaƙance kana jawo
min cin mutunci a tsakanin ƴan uwana sarakunan aljanu.
Amma ka sani har yanzu jikinka yana hannun Uznu Ururu
kuma bani da ikon kuɓutar dakai daga hannunsa, domin
bazan iya shiga duniyar mutane ba. Wannan kawai
ruhinka na janwo.
"Na biyu kuma ina ɗaure ne saboda yayarka Hidaya ta
ɗaure ni. Kada ma ka tambaye ni nima bansan mai yasa
ba, amma wannan yaya taka ita kaɗai ce wadda aka haifa
da ƙarfin ruhin da tun tana ƙarama take iya yin safa da
marwa a tsakanin duniyar aljanu da mutane ta shiga inda
take so. Lallai ƙarfin Izzarta abun tsoro ne har a tsakanin
manyan aljanu. Ta haka ne ma ta shammace ni ta
yaudare ni ta ɗaure ni." Koda aljani Jidaime ya faɗi
jimlarsa ta ƙarshe sai ya canja fuska izuwa kalar fuskar

wanda budurwarsa ta yaudare shi, tare da jan irin
numfashin nan na dana sani, sannan yaci gaba da cewa,
"Saboda haka zaɓin ka ne, kodai ka kwance ni ka koyi
al'amuran Izza ko kuma ka bari Uznu Ururu ya kashe ka,
kaga babu zancen samarwa mahaifiyarka lafiya.
"Duk biyun zaɓinka ne!" Aljani Jidaime na zuwa nan a
zancensa ya kautar dakai ya rufe ido ya fara kyankyaɗi."
___
Ina godiya ga dukkan waɗanda sukai min addu'a ta
Komawata makaranta ngd, sai gobe zamu cigaba
Nidinne dai Shuraih Usman inkiya
99%
Daga taskar magajin wilbafos
Anan muka kawo karshen fita na daya
Wanda muka tsakuro maku littafin magajin wilbafos daga part 1 zuwa part 50 in Allah ya yarda
zamu cigaba,
Daga http://hausaebooks.cf

MAGAJIN WILBAFOS
Fita na biyu 2
Marubucin littafin
Dr Abdullahi Muhammad Ibrahim
Ebook creat by Shuraih Usman
Ebook publish by www.hausaebooks.cf
Ebook din nan yazo maku ne daga shafin www.hausaebooks.cf
Kuna ziyartar shafinmu don samun sababbin littatafai
Ga duk wanda ke bukatar ebooks nashi ya samu shiga cikin wepsite namu sai ya turo mana da littafin ta Email namu hausaebooks@gmail.com
MAGAJIN WILBAFOS
Marubuci: Dr Abdullahi Muhammad Ibrahim
Babi na 51: Umarnin Ururu
Post by: Shuraih Usman
@shuraih 99%
www.facebook.com/hausaebooks
.
Daga:- Taskar Magajin Wilbafos
___
SHEKARU DA SUKA GABATA (ALAƘA TSAKANIN HIDAYA
DA ALJANI JIDAIME)
___
Hidaya ta ɓata rai tana duban aljani Jidaime wanda ke
tsaye yana lilo akan iska, "Kasan mai yasa Ururu suka fi
kowacce ƙabila ƙarfi a wannan zamani, ba komai bane
saboda su basu dogara da aljanu ba. Saboda haka babu
wata farar-laya da zata iya aiki a kansu. Sun dogare ne
kachokam da ƙarfin Izzar dake cikin baƙaƙen
idanuwansu. Haka nake so Armad shima ya dogara da
ƙarfin jininsa na Wilbafos. Bana son ya dogare dakai a
matsayinka na aljaninsa, domin hakan bazai kaishi ko'ina
ba."
Aljanin najin haka ya murtuke fuska, "Kina nufin kin raina
ƙarfina ne. Kuma kema ai kina amfani da aljaninki,
danme yasa kike so ki hana shi amfani da nasa."
Hidaya ta ɗanyi murmushi sannan ta amsa da cewa
,"Bawai ina cewa ban yadda da ƙarfin ka bane, Jidaime.
Kawai dai nasan akwai ƙarfin Izza irin wadda ni kaina ban
san iyakacin ta ba acikin ruhin ƙani na, saboda haka ina
so yayi amfani da ita maimakon ya dogara da ƙarfin
aljaninsa. Saboda haka kayi haƙuri zan ɗaure ka ta yadda
babu yadda Armad zai iya amfani da haƙiƙanin ƙarfinka.
Kuma ina mai yi maka gargaɗi na ƙarsge da kada wani
tsautsayi yasa ka ƙara haɗa kanka da aljani na domin yin
hakan zai jawo maka hukunci. Aljani na bai taɓa biyayya
ga Ururu ba kuma Ururu basu isa su baahi umarni ba. Kai
kasan mai nake nufi."
Tana rufe baki Aljani Jidaime ya fara jada baya yana
neman guduwa, amma ina tuni Hidaya ta saukarda
al'amudan Farar-laya akansa.
Tun daga wannan rana yake a ɗaure, kuma basu samu
wata damar ganawa da Armad ba sai a wannan lokaci.
Hasalima Armad baisan cewa aljaninsa a matsayi ɗaya
suke dana Ikenga ba. Kuma bawai kaɗai Walƙiya aljanin
nasa yake sarrafawa ba. Kai a taƙaice ma wannan walƙiya
ba daga aljanin nasa take fitowa ba. Tana fitowa ne daga
ainahin cikin ƙarfin ruhin Armad wanda aka haifeshi
dashi. Irin ƙarfin da yayarsa Hidaya take so yayi amfani
dashi.
_____
Acikin filin Jinzidal kuwa, har wannan sadauki mai
muƙamin kyaftin ya ɗauki Armad a sume da niyyar tafiya
dashi sai Uznu Ururu ya dakatar dashi.
Uznu na tafiya taku ɗai-ɗai ya iso ga jikin Armad ya kuma
saka hannunsa akan zuciyar Armad. Haka na faruwa wani
haske ya fara fita daga jikin hannunsa yana shiga jikin
Armad.
____
Acikin duniyar aljanun nan kuwa Armad yana tsaye yana
tunani wacce shawara ya kamata ya yanke kawai sai yaga
duniyar ta fara cika da wani baƙin haske. Lamarinda yasa
shi ajiyar zuciya. Amma tun kafin ya gama gane maike
faruwa yaga fuskar aljaninsa Jidaime ta canja.
"Armad ko ka kwance ni yanzu ko kuma baza ka iya ƙara
amfani da fasahar walƙiya ba." Aljanin ya faɗa cikin sauri
da alamun tsoro.
Idanun Armad suka cika da mamaki a lokacin da yaga
canjin yanayin da aljanin ya samu kansa aciki. Nan take
ya buɗe baki ya tambayi aljanin, "Mai yake faruwa?"
"Uznu Ururu ne yake neman ƙara ƙarfin ankwar dake
ɗaure dani. Ban san tayaya ba, amma da ƙarfin baƙaƙen
idanun sa yana iya gani har cikin ruhinka. Wato dai a
taƙaice yana ganinmu a halin yanzu. Kana da ƙasa da
daƙiƙa biyar ka yanke shawara akan abinda zakai."
Aljanin na rufe baki ya fara karkarwa lamarinda ya ƙara
ruɗa Armad, domin har a wannan lokaci ya kasa yanke
shawara.
Abu ɗaya dai da Armad ya sani shi ne ba dukkan
maganganun da aljanin ya faɗa zai yadda dasu ba, yasan
cewa lallai ba'a raba aljanu da ƴan ƙarairayi nan da can.
Amma a halin da yake ciki bashi da wani zaɓi face ya
bawa wannan aljani dama yaga kozai iya kuɓutar dashi
daga halin da yake ciki.
Saboda haka Armad yayi tsalle izuwa wannan aljani, ya
kuma ja ankwar da ƙarfin tsiya. Abun mamaki bai taɓa
tsammani ba, amma kawai sai yaga ankwar tana
murmushewa tana sakar wannan aljani. Wanda a iya
lissafinsa cire ankwar zai ɗau lokaci kuma yana buƙatar
makami kafin ya faru. Amma koda Armad ya tuna cewa
ai ankwar ta tsafi ce, sai kuma ya gane yadda abin yake.
Aljani Jidaime yai ƙaraji tare da miƙe hannayensa sama
bayanda yaji shi a sake. Ranar daya daɗe yana jira tazo.
Amma kafin ya fara komai yana buƙata ya kashe Uznu
Ururu dake waje, wanda idan baiyi saurin yin hakan ba
wannan baƙin hayaƙi zai iya ƙara ɗaure shi ya maida shi
gidan jiya.
Nan take ya finciko ruhin Armad daga wannan duniya ya
dawo dashi izuwa jikinsa a wannan fili. Shi kuma ya
bayyana a gaban Uznu Ururu yana mai riƙe da farin
al'amudin aljanu a hannunsa na dama.
Koda bayyanarsa sai dukkanin kyaftin guda biyar ɗinnan
dake biye da Uznu sukai tsalle suka dira a gabansa domin
su kare shi. Amma suna dira aljani Jidaime ya kawo wata
muguwar wafta da al'amudinsa inda ya share su baki
ɗayansu a lokaci guda. Sannan kuma yayi kan Uznu
gadan-gadan. Lallai ƙarfin aljanu da bil-adama da
banbanci.
Nan da nan fuskar Uznu ta canja, yanayin firgici ya
bayyana akanta. Amma a wannan lokaci ne ya ciji
ɗanyatsansa na dama, inda jini ya fara ɗisa. Uznu baiyi
wata-wata ba wajen saka wannan jini acikin idanunsa
baƙaƙe guda biyu. Ai kuwa haka na faruwa wani baƙin
haske ya fara ɓulɓula daga ciki, sannan Uznu ya fara
magana, "Ina mai umartarka da ƙarfin Ururu dake jini
na, da ƙarfin Ururu dake bisa ƙasa ta farko daka tsaya a
inda kake."
Abin mamaki yana rufe baki wani irin ƙarfin izza marar
misaltuwa mai cike da buwayar Ururu ya fara ambaliya
acikin filin. Kan kace meye wannan aljani Jidaime ya tsaya
a inda yake cak ya kasa motsi. Sannan kuma Izzar Uznu ta
fara hawa tana ambaliyar har saida takai Shekaru dubu
huɗu da ɗari tara da casa'in da tara. Uznu ya cafi
takobinsa yayi kan aljani Jidaime.
Tun kafin ya ƙarasa akaji muryar aljanin na cewa, "Idan
ka kashe ni kasan ƙabila ta baza suyi shiru ba. Kuma
babban sarki Ururu Kuyurussa'ayi yayi mana katanga
daku..." Yana magana yana karkarwa, kuma ganin cewa
Uznu baya saurarensa kawai sauri yake ƙarawa yasa tsaya
ya kasa ƙarasa abinda yake faɗa tare da fara karkarwa.
Uznu na ƙarasowa yasa takobinsa ruwan toka ya tsarge
aljani Jidaime gida biyu. Aljanin yai wata ƙara mai
firgitarwa, inda daga bisa ya fara narkewa izuwa toka
yana murmushewa.
"Da kasan da tsakanin da akai mana da baka tunkare ni
ba. Ko ba komai ina da hujja idan aka je gaban babban
sarki Ururu Kuyurussa'ayi." Uznu na magana yana goge
takobinsa.
Sannan nan take ya ɗau Armad ya ɓace daga wannan filin
gasa.
___
A can gefe guda kuwa sarki Deniz Iluru da dakarunsa
suna tsaye suna kare duk wani hari da yayo kan ƴan kallo
a lokacin da ake wannan fafatwa tsakanin Uznu da su
Armad.
Duk da kuwa cewa tunda Uznu ya buɗe idonsa dukkan
ƴan kallon suka sume, amma bayan da aka gama komai
hankali ya dawo jikinsu saida hukumar yaƙin garin tayi
amfani da rahoton ƙarya na cewa girgizar ƙasa ce tasa
aka tsayar da gasar wannan shekara. Amma ta ƙarƙashin
ƙasa sarki Deniz Iluru ya rubuta ƙara izuwa fadar Ururu
dake ƙasa ta biyu mai kula harkokin Jinzidal akan su
hukunta Uznu Ururu saboda cikas ɗin daya kawo a gasar
Jinzidal ɗin. Cewa kuma suna fata ai musu adalci.
To haka dai aka kawo ƙarshen wannan gasa ta Jinzidal ta
wannan shekara.
____
To ALLAH ya kawo mu ƙarshen Jinzidal. Yanzu zamu shiga
wani sabon sashi na wannan littafi. Duk mai tambaya ko
kuma wani abu da bai gane ba a babika 50 da suka wuce
ya rubuto a comment.
Nidinne dai Shuraih Usman inkiya
99%
Daga taskar magajin wilbafos
MAGAJIN WILBAFOS
Marubuci: Dr Abdullahi Muhammad Ibrahim
Babi na 52: Dordor mai waka
Post by: Shuraih Usman
@shuraih 99%
www.facebook.com/hausaebooks
.
Daga:- Taskar Magajin Wilbafos
Doron ƙasa na huɗu
Shalkwatar Mayaƙan Ururu
____
Sahu-sahu ne na mutane ɗai-ɗai har sahu ɗari, kowanne
ɗaya daga cikin wannan sahu yana ɗauke da mutane
guda ɗari. A taƙaice dai mutanen dake cikin wannan sahu
su dubu goma ne. Dukkaninsu na sanye da baƙaƙen kaya.
Babu mai ko magana acikinsu. Kai ko tari babu maiyi.
Dukkanin wannan mutane ba kowa suke jira ba illa
kwamanda Uznu Ururu. Uznu Ururu dai yaje ƙaro ilmi a
jami'a mafi girma a duniya dake bisa doron ƙasa ta farko.
Jami'ar da ake kira da Namibiya da yaren Aldurish na
Ururu. Saboda daɗewar da yayi nema baya nan suka
shirya masa wannan gagarumar tarya.
Amma bisa mamaki Uznu yana bayyana kawai tsayawa
yayi kimanin daƙiƙa ɗaya, inda ya kyaɗa musu kai
alamun jinjina sannan yai ɓangaren inda ofishinsa yake.
Koda yake baza a iya kiran wajen na Iznu Ururu da ofishi
ba kaɗai, tunda iya girman wajen kaɗai yakai wani ɗan
ƙaramin gari. Sannan kuma ga shirye-shirye na
musamman na al'amura da suka shafi Izza da ake
gudanarwa a wajen. Kusan zaka iya cewa duk wani
sinadari da za'a iya samu a ƙasa bakwai akwai a wannan
ɓangare na Uznu Ururu, kasancewar shi ɗin yawanci
kayansa daga doron ƙasa ta farko yake tahowa dasu.
Amma dukkanin wannan abubuwa basu suka dami Uznu
ba, a yayin da cikin sauri ya shige wani ƙaton ɗaki na
bincike-bincike inda yana shiga ya turo ƙofa ya rufe,
tunda dama babu kowa acikin ɗakin. Sannan ya zaro
wani ɗan irin Ayrid na musamman daga aljihunsa ya
karanta wasu ɗalasimai, wanda nan take wannan Ayrid ya
fara ƙara girma yana girma har saida ya kai girman ƴar
ƙaramar ƙofa, inda nan take wannan irin Ayrid yai aman
Armad ta cikin wannan ƙofa.
Uznu ya fizgi Armad ya kwantar dashi akan wani ƙaton
taburi na aiki. Sannan kuma ya fara karanta wasu
ɗalasimai wanda suka saka wani farin haske ya fara cika
ɗakin.
Nan take wasu Rauhanan aljanu guda biyu, ɗaya mai
ƙaho ɗaya mara ƙaho, suka bayyana, suna bayyana suka
zube a gaban Uznu, kana gani kasan alaƙar dake
tsakaninsu bata wuce ta bawa da ubangidansa ba.
Uznu ya amsa sannan ya fito da wasu fararen takardu
daga aljihunsa guda biyu ya miƙa musu. Sannan ya fara
jawabi da cewa, "Kunga wannan shi ne karo na biyu da
muka shigo da Littafin takobi wannan ɗaki acikin shekaru
ɗari da suka wuce, saboda haka haka ina fata zamu
kiyaye duk abubuwanda suka sa a wancan lokaci bamuyi
nasara ba."
Ya kalli aljanin mai ƙaho daga cikin guda biyun yace,
"Kalkutu kasan mai zakai."
Sannan ya juya izuwa mara ƙahon, "Kaima Netti kasan
meye aikinka."
Uznu ya ci gaba da bayani a yayinda wannan aljanu biyu
suka nutsu suna saurare, "A bisa bincike na na gano cewa
Littafin-takobi yana da rai yana kuma da hankali nasa na
kansa. Kawai dai ba irin yadda mutane da aljanu suke ba.
Kuma ta hakan nema na gano cewa indai akwai ma'aboci
Ururu a waje to Littafin-takobi bazai taɓa baƴyana kansa
ba. Kuma hakan ba abin mamaki bane tunda shi wanda
ya samarda Littafin takobin ɗan adawar gidan mune na
Ururu.
"Saboda haka a lokacin da za'ai wannan aiki dole ne ya
zamanto bana kusa da wannan yaro, in ba haka ba
wannan Littafi bazai taɓa bayyana kansa ba.
"Sannan kuma a wani binciken da muka gudanar a
jami'ar Nimibiya mun gano cewa wannan Littafin ya zaɓi
ƴan zuri'ar Wilbafos har a karo biyar daga cikin karo
bakwai da ya taɓa zaɓar wani. Kuma shima wannan
yaron daya zaba ɗan zuri'ar wilbafos ɗinne. Amma
babban abinda zaku riƙe ku kiyaye shi ne, Littafin-takobi
yana bayyana ya taimaki waɗanda ya zaɓa. Saboda haka
hanya ɗaya da zamu tabbatar ya bayyana shi ne mu
tabbatar da cewa mun azabtar da wannan yaro ta
kowacce hanya ƙololuwar azabatarwa tayadda Littafin zai
fito da kansa ya taimakeshi. Da zarar ya fito kunsan
abinda zaku yi na gaba, saboda haka ku fara aiki.
"Zan shiga shalkwata na fara shirye-shiryen sarrafa
wannan Littafi tayadda kuna zaƙulo shi kawai aiki zamu
fara akansa. A tafiya ta zuwa doron ƙasa ta farko na samu
dama na tattautana da Babban ɗan sarki Kuyurussa'ayi,
yarima mai jiran gado Níwajítu Dúmaƙísu Kuyurussa'ayi.
Kuma ya bada koyon bayansa ɗari bisa ɗari akan abinda
muke niyyar yi da wannan Littafi. Saboda haka lallai sai
mun tabbata munyi nasara a wannan karan."
Bayan Uznu ya tabbatar da cewa aljani kalkutu da Netti
sun fuskanci halinda ake ciki sai ya fita ya barsu domin su
fara aiki akan Armad.
________
A can wani sashin duniya dake ɓangaren Ikwatora na
doron ƙasa ta shida kuwa wata mace ce kwatsam ta
bayyana cikin jini kuma a sume. Lallai kana ganinta zaka
san gab take da mutuwa, kuma lallai idan ba'ai wani abu
akanta ba, to babu makawa mutuwa zatai. A tsakiyar inda
wannan mace ta bayyana kamar wata daula ce ta Dordor
launi-launi. Domin kuwa duk inda ka duba su zaka gani.
Babu gida gaba babu gida baya a wannan daji da take,
babu kuma abinda kake ji sai kukan tsuntsaye da
maganganun jinsin halittar nan da ake kira da Dordor.
To kamar masifar da wannan mata take ciki bata isa ba,
sai kurum wasu daga cikin Dordor dake wajen suka
hange ta. Ai kuwa nan take manyansu suka fara isa wajen.
Amma bisa mamaki kowanne Dordor idan yazo ya
shanshana wannan mace sai kawai yai tsaki ya juya kai ya
tafi. Kuma dukkanin waɗannan dordor da suke zuwa
kanta suna da kai sama da biyar. Kuma kowannensu fatar
jikinsa nada launi na daban. Babu kuma wanda keda Izza
ƙasa da ɗari biyar acikinsu. Lallai koda wannan mace na
cikin hayyacinta bata ishe su kallo ba.
To abu ne dai sananne a duniya cewa Dordor mai kai
biyar zuwa sama shi ake cewa Babban Dordor, sannan
kuma babban Dordor baya cin naman halittar da Izzarta
bata kai ɗari biyar ba. Saboda haka dai ga dukkan alamu
wannan mace ta taki sa'a.
Sai dai kuma ana haka bayan waɗannan manyan Dordor
masu kayika da yawa sun bar kanta sai ga wani Dordor
nan mai kai biyu ya gabato, yana tafiya a hankali kana
ganinsa kasan a yunwace yake. Tun daga nesa ya hangi
wannan mace ya kuma fara murmushi da kansa na
dama, sannan kuma yana dariya da waƙa da kansa na
ɓangaren hagu.
*Abinci ya samu
Yau yau abinci ya samu
Abinci har da kalace
Abinci ya samu
Abinci ya samu*
Haka dai wannan aljani ya wanzu yana gudu-gudu sauri-
sauri yana waƙa har ya isa inda wannan mace ke kwance.
Abune sananne ansan cewa jinsin fararen Dordor sha'irai
ne ma'abota waƙa, kuma sukan rera waƙa musamman a
lokacin da suka samu abinci.
Hakan nema yasa waƙa taƙi ƙarewa a bakin wannan Farin
Dordor wanda kaf komai a jikinsa fari ne fat tun daga
gashin kansa har zuwa fatar tafin ƙafarsa.
Dordon ya miƙa farin hannunsa wanda yafi farar-ƙasa
fari ya juyo da fuskar wannan mace. Sannan ya zaro wata
ƴar ƙaramar wuƙa daga aljihunsa da niyyar ya fara
yankar naman wannan mace yana kaiwa bakinsa-na-
waƙa. Amma kafin ya fara komai ya ɗaga hannu ya fara
da addu'a, "Godiya ga ubangijin daya jefowa da farin
Dordor naman bil-adama. Muna fata gobe ma a bamu!
Ameen!" Wannan Dordor ya shafa wannan addu'a
sannan yai azama wajen fara yankan naman jikin wannan
mace.
Idan ka kalli fuskar wannan mace zaka ga ba wata bace
illa Nusi ƙawar Armad wilbafos, wadda kwamanda Uznu
Ururu yai cilli da ita aka nemeta aka rasa tsahon lokaci.
Nidinne dai Shuraih Usman inkiya
99%
Daga taskar magajin wilbafos
MAGAJIN WILBAFOS
Marubuci: Dr Abdullahi Muhammad Ibrahim
Babi na 53:

Please Login or Register in order to submit comment