Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ƙasa ce ta fita ba, a'a toka ce
kawai. Nan take Armad ya tabbatarwa da kansa abinda
yake tunani.
Wato cewa wannan abu mai kama da toka daya gani tun
da farko, ba wani abu bane illa Iskar datai rashin sa'a ta
gifta ta cikin wannan ƙawanya, lamarinda yasa nan take

ƙonewa izuwa toka, ba tare dama tabi ta matakin kama
wa da wuta ba!
Daga cikin abubuwan da Armad yafi maida hankali akai,
tun bayan fara koyar dabarun yaƙi da Izza shi ne
banbance-banbance akan aljanu da kuma matakai
daban-daban da ake iya amfani dasu, misali; duk da cewa
zaka iya samun mutun biyu, dukkaninsu aljanunsu na
sarrafa abu iri ɗaya, amma kuma ƙarfin waɗannan
mutane su banbanta.
Ba kuma komai yake jawo haka ba illa banbancin Izza!
Saboda hatta ɗalasimai akwai waɗanda idan Izzar ka bata
kai wani mataki ba, to baza ka taɓa iya amfani dasu ba.
Armad ya daɗe da sanin irin wannan koriyar wuta, wadda
suke cewa 'Jukísa' da yaren Alderiya.
Ita dai Jukísa zaka iya cewa tana daga cikin manyan haraharen da masu bautar da aljanun da suke sarrafa wuta
suka ji dashi, kuma kusan duk wanda yakai matakin Izza
ta ɗari zuwa sama, zaka samu cewa Jukísa ita ce ƙure
adakar sa!
Domin abu ne sananne cewa indai ka riga ka bari ka shiga
ta cikin wannan ƙawanya, to lallai sai dai ka fice a
matsayin toka. Wato ka riga ka ƙone ƙurmus.
Tun daga kan masu Izza ɗari da hamsin har zuwa ƙasa,
babu wanda a tarihi ya taɓa shiga cikin wannan ƙawanyar
koriyar wuta mai suna Jukísa ba tare ya ƙone izuwa toka
ba!
Sannan kuma wani babban sharrinta shi ne yadda take da
tsananin sauri wajen faɗaɗa girmanta, domin tuni a
wannan lokaci faɗin ƙawanyar ya haura taku ɗari a dama
da hauni daga inda Armad yake, saboda haka yasan a
yadda yake, gujewa wannan ƙawanya ba abune mai
yiwuqa ba.
Duk waɗannan abubuwa su ne abbubuwan da suka sa
Armad ya shiga cikin firgicin da yake ciki.
Shi kuwa wannan dattijo kallo ɗaya zakai masa kasan
cewa yakai matuƙa wajen yadda da wannan fasaha da yai
amfani da ita mai suna Jukísa.
Wanda a ɗaya ɓangaren kuma Armad na tsaye cikin zufa
yana wasu-wasin mai ya kamata ya aiwatar!!!
***
Ku biyomu a ci gaban wannan babi domin jin yadda
Armad zasu ƙarke da wannan mutun wanda tunda aka
fara fafatawar bai bawa Armad ko dama ɗaya ta kai masa
hari ba!
Ina buƙatar comment ɗinku musamman akan abinda
kuke hasashen shi ne zai faru da Armad a babi na gaba.
A gaskiya comment ɗinku shi ne zai ƙara min ƙarfin
gwiwa wajen ci gaba da fassara muku wannan littafi nawa
dana rubuta da turanci! Thanks.
Copyright © 2017 A M IBRAHIM . All rights reserved

Nidinne dai Shuraih Usman inkiya
99%
Daga taskar magajin wilbafos
MAGAJIN WILBAFOS
Marubuci: Dr Abdullahi Muhammad Ibrahim
Babi na 4: wasi wasi part 2
Post by: Shuraih Usman
@shuraih 99%
www.facebook.com/hausaebooks
.
A dai-dai wannan lokaci tuni wannan ƙawanyar wuta
takai kimanin faɗin ƙafa maitan a kowanne ɓangare,
dama da hauni, sama da ƙasa, Armad kuma na tsakiya
babu ta inda zai iya guje mata.
Gashi kuma a dai-dai lokacin ƙawanyar ta matso dab
dashi, tsakaninsa da ita baifi taku ɗaya da rabi ba.
Sai dai kuma a dai-dai wannan lokaci na ɗimuwa
kwatsam fuskar Armad ta canja kamar wanda wani abu
ya shiga jikinsa; ƴan daƙiƙu da suka wuce idan ka kalli
idanunsa, alamun wasu-wasi zaka gani, amma kuma a
dai-dai wannan lokaci gaba ɗaya yanayin idanuwan nasa
suka canja zuwa alamun kafiya da ƙeƙashewa, kamar
wanda ya yanke wata shawara acikin zuciyarsa mai
wahalar gaske!
A wannan lokaci ne, Armad ya miƙa hannunsa na dama a
hankali, zuwa ƙeyarsa inda wannan wannan jan ƙyalle ke
ɗaure akai.
A hankali ya warware ɗaurin da hannayensa biyu sannan
daga bisani ya cire kyallen, tare da zira shi acikin rigarsa.
Abin mamaki ashe wannan ƙyalle bawai na ado bane
kawai. Hasalima bawai gama-garin ƙyalle bane, a'a anyi
shi ne da kayan sihiri da kuma audugar Jamsiƙa.
Ana dai amfani da audugar Jamsiƙa ne kurum wajen
ɓoye abubuwa mafiya ƙololuwar daraja, a suturcesu
daga idanun mutun da aljan, kasancewar irin baiwar da
ALLAH ya saka acikin wannan auduga.
To ko me yasa Armad yake amfani da irin wannan ƙyalle
domin ɗaure gaban goshinsa?
Amsar tana kan goshin nasa! Domin a dai-dai wannan
lokaci da Armad ya kwance wannan ƙyalle wani tambari
ne ya bayyana a ɗamfare a jikin goshin nasa.
Kallo ɗaya zakai wa tambarin kasan cewa ba zana shi akai
ba, domin a ɗamfare yake a jikin fatar Armad. Kai idan ka
matsa kusa ma zaka ga cewa, asali wannan tambari bama
a jikin fatar tasa yake ba, hasalima zaifi dacewa ace a jikin
ƙashin goshin Armad yake.
Wato dai a taƙaice akwai matuƙar yiwuwar cewa koda an
yanke wannan fata ta gaban goshin, wannan tambari
bazai ɓace ba.
Tsarin tambarin yana ɗauke da zanen mutun-mutumi
daga tsakiyarsa, wanda idan ka lura sosai zaka ga cewa
akwai wani al'amudi mai faɗi a hannunsa na dama. Irin

yanayin alamun da wannan mutun-mutumi yake ɗauke
da ita, idan ka ƙura masa ido, zaka ga tafi kama da ta
aljanu.
A kewaye da wannan mutun-mutumi kuwa akwai wasu
takubba guda uku, wanda sukai masa ƙawanya. Kowacce
acikinsu tana ɗauke da alamun yanayin iskar kabari.
Wato irin yanayin nan da mutumin da ya kashe dubban
bil'adama da aljanu yake bayarwa idan ya gifta. Kai idan
ka fiya kallon waɗannan takubba uku ma, zaka iya
rantsewa jini ne ke ɗisa daga jikinsu saboda tsabagen
alamun mutuwa dake tashi daga jikinsu.
To daga waɗannan takubba kuma sai wasu rubucerubuce, wanda suka kewaye gaba ɗayan tambarin.
Gabaki ɗaya rubutun a sarƙaƙe suke da juna sannan
kuma a kewaye. Tayadda koda kasan yaran da akai
rubutun dashi, iya karantawa zai maka wahala.
Ballantana ma shi kansa Armad bai san wane yare bane,
domin wannan yare baya daga cikin duk yaran da akeyi a
wannan zamani.
Kuma ya taɓa tambayar kakansa Zaikid, akan ya fassara
masa, amma ya ce masa ba yanzu ba.
Buɗe wannan tambari keda wuya, goshin Armad ya fara
haske, lamarinda yasa cikin sauri Armad yasa haƙorinsa
ya ciji babban ɗan yatsansa na dama har saida jini ya fito.
Sannan cikin sauri ya ɗora ɗan-yatsan akan wannan
tambari dake goshinsa.
Hakan na faruwa wannan tambari ya fara zuƙar jinin
dake fitowa daga inda Armad ɗin ya cija yana shigewa
cikin tambarin kamar wanda wani ƙaton baki yake
zuƙewa.
Kan kace meye wannan tuni wannan takubba guda uku
na cikin wannan tambari sun fara motsi suna kewaya
wannan mutun-mutumi.
Abu kamar wasa cikin ƙiftawar ido da bismillah, kamar
wanda aka sawa rai, wannan mutun-mutumi ya fara
motsi ta hanyar ɗaga hannunsa mai riƙe da wannan
al'amudi sama. Lamarinda yasa Armad yai wata
muguwar ƙara mai firgitarwa tamkar wanda ake zare wa
rai.
Kafin daga bisani gaba ki ɗayan jikinsa ya fara karkarwa,
sannan kuma daga baya ya fara tashin wata walƙiya
kamar yadda a baya takobinsa tayi.
Zaka iya cewa tun daga ƙololuwar kansa har zuwa tafin
ƙafarsa duk inda ka kalla walƙiya kawai zaka gani tana
tashi kamar wani wanda ake saukarwa da aradu.
A cikin wannan hali Armad na tsaye, idanunsa a rufe,
takobinsa riƙe a hannunsa na hagu, gaba ki ɗaya babu
abinda kake gani a jikin Armad inba wannan walƙiya ba.
Bisa mamaki ana cikin haka sai Izzar Armad ta fara yin
sama, kuma kan kace meye wannan cikin abinda bai
haura daƙiƙa ɗaya da rabi ba ta tashi daga hamsin da
ɗaya takai tamanin da uku.

A dai-dai wannan lokaci ne Armad ya ɓace ɓat daga inda
yake, inda ya bayyana a can sama kimanin taku ɗari biyu
da hamsin daga inda yake ada. A dai-dai wajenda hatta ita
kanta ƙawanyar wutar bata ƙarasa ba.
Yana bayyana a wajen wannan ƙawanyar wuta ta ƙara
ruruwa tayo kansa, tamkar ta kula da cewa ya fita daga
cikin zagayenta.
Sai dai kuma kash, Armad ɗin wanda idonsa har a lokacin
a rufe yake, a lokacin ne ya ƙara ɓacewa daga inda yake
ya kuma bayyana a bayan ƙawanyar sannan kuma a
gaban wannan mutun. A dai-dai lokacinda Izzarsa har
takai mataki na ɗari.
Dukkanin abubuwan da suka faru, tun daga lokacin da
Armad ya kwance wannan jan ƙyalle har ya zuwa sanda
ya bayyana a gaban wannan dattijo, a rubuce sun ɗauki
dogon lokaci wajen bayyana su, amma a zahiri komai
daya faru bai wuce cikin daƙiƙa biyu ba.
Dama wannan dattijo tunda yai amfani da wannan
koriyar wuta a fasahar nan mai suna Jukisu, ya nutsu da
cewa lallai ya gama da Armad, tunda tun a lokacin ya
maida takobinsa cikin kufenta.
Amma a lokacinda yaga wannan tambari na gaban goshin
Armad sai daya jada baya bakinsa a buɗe, sannan kuma a
lokaci guda ya kai hannunsa kan takobinsa da niyyar zare
ta, sai dai kuma ina kan ya zare tuni Armad ya bayyana a
gaban nasa.
Inda a lokacin ne Armad ya kaiwa wannan dattijo
mummunan sara a kafaɗarsa ta dama da niyyar nakasta
hannun da wannan dattijo yake riƙe takobi dashi a lokaci
guda.
Takobin Armad ɗin ta tafi da tsananin sauri, sannan kuma
da ƙarfin tsiya tayadda har iskar wajen saida ta fara ƙugi.
Sai dai kuma a dai-dai lokacinda takobin take gabda
haɗuwa da jikin dattijo wanda yake ta ƙoƙarin kaucewa,
sai kawai takobin ta ƙara wani mugun sauri wanda ya
wuce gaban hankali, wanda kuma za'a iya fasalta shi da
cewa ya ninninka saurin da take tafiya dashi a baya.
Lamarinda yasa ta ɓace ɓat ba'a ko ganinta, kuma abin
mamaki a lokacin data ƙara bayyana tana riƙe a hannun
Armad. Jikinta wanda da yake cike da walƙiya, yanzu
babu komai akai sai farin ƙarfe. Sannan kuma wani abin
mamaki kana gani zaka tabbatar da cewa ƙarfen yayi
duhu sosai ba kamar sanda Armad ya fito da ita ba.
A dai-dai wannan lokaci babu abinda Armad yai sai kawai
kai tsaye mayarda takobinsa da yai cikin kufenta, sannan
kuma a lokacin walƙiyar dake rawa a jikinsa ta ɓace ɓat,
sannan kuma ya buɗe idanunsa. Babu abinda yake sai
haki, kai kace shekara yai yana gudun fanfalaƙi.
Shi kuwa wannan dattijo yana tsaye a dai-dai inda yake
baki a buɗe yana kallon Armad wanda yake tsaye yana ta
haki.
Sai dai kuma babban abin mamakin shi ne, babu wani

alamun sara ko kuma ciwo a kafaɗar wannan dattijo ko
kuma a jikinsa.
Amma ga dukkan alamu shi kansa acikin mamaki yake.
Armad na tsaye ya ɗan dunƙufa yana fuskantar wannan
mutun wanda shima ke tsaye yana kallon Armad ɗin ba
tare da alamun wani ciwo a jikinsa ba.
"hmmm....." cikin mamaki wannan mutun ya fara kallon
jikinsa yana yamutse fuska.
Ba wani abu bane ba kuwa ya janyo haka ba illa wani abu
daya fara ji a jikinsa.
Wannan abu ba wani abu bane illa fuskanta da yayi cewa
Izzarsa akankanta ba tare yayi wani abu ba, ta fara
raguwa, daga mataki na ɗari daya barta zuwa ƙasa.
Amma bisa mamaki maimakon hankalin dattijon ya
ɗungunzuma, abu na gaba da wannan da yai shi ne
murmushi, gami da duban Armad tare da cewa, "nasan
wacce ƙabila ce suke da irin wannan MIYÚRA ta gaban
goshinka!"
***
Kalmar Miyura ba wani abu take nufi ba illa 'tambari',
kuma kalma ce daga yaren 'Aldurish', wanda kamar
yadda aka faɗa a baya shi ne yaren da yafi shahara a
wannan zamani.
***
Dattijon na gama faɗar haka ya zare takobinsa sannu a
hankali, sannan ya fara tafiya taku ɗai-ɗai yana dosar
inda Armad yake, a lokaci guda kuma yana bayani, "Ina
da tabbas cewa Miyura ce daga zuri'ar Wilbafos!
"Sannan kuma waccan fasaha dakai amfani da ita ɗazu ka
tsere daga ƙawanya ta....nasan mece ce!" yana zuwa nan
a zancensa ya ɗanyi shiru gami da duba izuwa ɓangaren
da wannan ƙawanyar wuta mai suna Jukisu daya harbi
Armad da ita ɗazu tayi, kuma har a wannan lokacin tana
nan tana dosar ɓangaren da Armad ya baro, duk abinda
ya shiga ta cikinta sai dai kaga ta juye izuwa toka. Wala
wannan manyan bishiyu wala tsuntsu wala koma meye,
hatta iskar dake kaɗawa a wajen bata ƙyale ba.
Ajiyar zuciya kawai yayi, gami da dawo da kallonsa izuwa
Armad, wanda a lokacin tuni hasken da wannan tambari
na goshinsa yake bayarwa ya fara dusashewa sannan
kuma Izzarsa ta sauka ta dawo yadda take a da wato
hamsin da ɗaya.
"Abu ɗaya dazan gayama, wanda kuma wataƙila ka riga
ka sani shi ne, wannan abu daka aikata zai ƙara maka
ƙarfi ta kowacce fuska na ɗan taƙi, amma a dalilin hakan
kuma adadin tsahon rayuwarka zai ragu!
"Ta hanyar kallonka kaɗai zan iya gaya maka cewa a ƴan
daƙiƙun daka ɗauka kana amfani da wannan tambari na
goshinka, kayi asarar sama da shekara biyar na ainihin
rayuwarka!"
A dai-dai lokacin da yazo nan a zancensa tuni yana dai-dai
gaban Armad, takobinsa na riƙe a hannunsa na dama.

Kana ganinsa kasan cewa a shirye yake daya afkawa
Armad a kowanne lokaci.
Sai dai kuma a lokacin ne Armad yai sauri ya ce, "dattijo,
kafin ka aika ni lahira kuwa, baza kaso kaji maiya biyo
dani wannan duniyar ba!"
Dattijon ya buɗe baki zaice wani abu, amma kamar
Armad yana jin tsoron kada ya ce baya son ji, nan take
yai firgigit ya ce, "TIRIFIL-FAKTA!
"Na fito ne neman Tirifil-fakta!"
"Hmmmmm..... eh.... Tirifil-fakta?" cike da mamaki kuma
cikin ƙinƙina, wannan tsaho ya furta sunan gami da jada
baya, jikinsa yana karkarwa, tamkar wanda akaiwa
albishir da al'amari mai tsananin firgici.
Sama da kimanin daƙiƙa goma wannan dattijo yana cikin
wannan hali na ɗimuwa daya tsinci kansa aciki.
Sai dai kuma amma yana cikin wannan hali ne, kamar a
mafarki yaji hannunsa na dama dake riƙe da takobinsa ya
fara karkarwa da ƙarfin gaske, lamarinda yasa hatta
takobin dake riƙe a hannunsa ta fara girgiza tana neman
faɗuwa ƙasa.
Mamaki ne rubuce akan fuskarsa asanda ya jada baya
gami da ƙurawa Armad ido cikin wani yanayi mai cike da
kokwanto da WASU-WASI.
Amma haƙiƙa da ace a iyakacin karkarwa komai ya tsaya,
to da ba wani abin tashin hankali bane, amma a dai-dai
lokacin ne daga dai-dai kan kafaɗarsa ta dama harya
zuwa ƙasan ƙirjinsa ya dare tayadda ana iya gano farin
ƙashinsa.
Nan take jini yai tsiri zuwa sama, tare da feshe gaba ɗaya
wajen. Kan kace meye wannan ƙasar wajen ta koma
jajawur.
A dai-dai lokacin ne wannan dattijo ya kasa riƙe takobin
tasa, inda ta faɗi ƙasa. Shi kuwa tsalle yai tare da matsawa
can nesa baya da Armad.
A jikin fuskarsa babu komai sai tarin Wasu-wasi. Wasuwasi akan cewa yaushe ne?
Yaushe ne har Armad yai masa wannan mahaukacin
saran bai kula ba. Duk da yana cikin wannan hali na rai a
hannun ALLAH, amma ƙoƙari yake kawai yake ya tsayar
da jinin dake feshi daga ƙirjinsa ya kuma tambayi Armad
yaushe ne?
Koya samu wasu-wasin dake dukan ruhinsa ya sassauta!
Sai dai kuma a dai-dai wannan lokaci ne ya ji muryar
Armad na cewa, "daƙiƙa ashirin da bakwai!
"Lallai na samu ci gaba, a wancan lokacin daƙiƙa ashirin
ashirin da uku kawai ya ɗauka, kaga an samu ƙarin
daƙiƙa huɗu kenan!"
Alamun nutsuwa da yadda dakai ya bayyana ƙarara a
fuskar Armad sanda yake waccan magana. Nan take ya
fara tafiya taku ɗai-ɗai izuwa wannan dattijo, a wani salo
mai kama da yadda shima dattijon ɗazu ya isa wajensa.
Yana zuwa ya ce, "dattijo, tunda nai maka kallon farko

nasan cewa babu yadda za'ai na taɓa samun nasara akan
ka, badan komai ba saboda yawan Izzarka, banma kai
matsayin da zan iya karanta ta ba saboda yawanta.
"Sai dai kuma saboda sanin cewa ba kullum bane wanda
yafi ƙarfi yake samun nasara a yaƙi ba. Saboda haka ban
fitar da rai ba.
"Amman ina jin kace zaka ƙayyade Izzarka izuwa mataki
na ɗari nasan cewa iskar sa'a ɓangare na take yowa!
"Domin nasan cewa duk da Izza ta a mataki na hamsin da
ɗaya take, lallai nasan cewa ina da waccan fasaha da zan
iya shammatarka da ita!
"Kaga dai kamar yadda kai hasashe lallai wannan fasaha
ina amfani da ita ne abisa hatsari. Domin ta ƙunshi aro
Izza daga iyaye da kakanni na ta hanyar wannan Miyura
dake goshi na, wanda hakan lallai zai rage min yawan
kwanaki na a duniya, amma kuma ni indai zan cimma
burina na nemowa mahaifiya ta wannan mutun mai suna
Tirifil-fakta, to ya ishe ni na mutu acikin murmushi!
"Kuma idan da ka kula tun daga lokacin dana kwance
ƙyallen dake goshina na kuma saka jini na akai, Izza ta ke
ƙaruwa, har saida takai matakin ɗari da sha ɗaya.
Lamarinda ya bani damar yin amfani da fasahar saran
takobin da ake cewa Wasu-wasi!
"Wadda fasaha ce ita kaɗai ce fasahar da tasha gaban
fasahar 'gayawa jini na wuce', domin ita 'gayawa jini na
wuce' bata ɗaukan sama da daƙiƙa ɗaya zuwa biyu, saran
daka aiwatar yake bayyana, amma a wannan fasaha akan
iya ɗaukar tsahon lokaci kafin mutun ya gane an sare shi,
badan komai ba saboda tsananin sauri.
"Wanda hakan ne yasa duk wanda aka sara yake tsintar
kansa acikin yanayi na WASU-WASI akan cewa yaushe ne?
Yaushe ne aka sare shi!" Armad ya girgiza yana duban
wannan dattijo wanda shima idanunsa suna kansa,
amma daga dukkan alamu hankalinsa wani abun yake
tunani.
Cikin yarda dakai Armad yaci gaba da cewa, "nasan zan
iya aiwatar da fasahar WASU-WASI koda ina kan mataki
na hamsin da ɗayan, to amma tunda fasaha ce wadda
take amfani tsananin sauri da zafin nama mai kama dana
walƙiya, saboda haka nasan baza ta taɓa yiwuwa ba, indai
Izza ta bata haura taka ba. Wanda shi ne dalilin da yasa na
buƙaci Izza ta ta haura ɗari.
"Saboda haka kai sani bama wannan ba, koma mai ya
kama a halin wannan tafiyar tawa, koma mene ne, koda
kuwa sama bakwai da ƙasa bakwai zasu haɗe, nayi
alƙawarin saina nemo wannan mutun." A lokacin da
Armad yake faɗar wannan magana idanunsa cike suke
ƙololuwar kafiya da ƙeƙashewa irin kafiyar nan da ita
kaɗai ka iya tarwatsa rundunar abokan gaba dubu da
ɗoriya!
"Hmmmmmm..." Ajiyar zuciya kawai wannan dattijo yai
sanda yaga kafiyar dake cikin idanun Armad, kafin daga

bisani ya ce, "a iyakacin mataki na Izza ɗari babu yadda
zanyi na iya shawo kan wannan raunin da kaimin ya
daina zubar da jini!" yana faɗar haka ya kalli wannan
wawakeken rami dake ƙirjinsa.
Sannan yaci gaba da cewa, "tunda kuma na riga nayi
alƙawarin faɗa dakai a iyakacin matakin Izza na ɗari,
bazan saɓa alƙawari ba.
"Saboda haka na yarje maka ka wuce ta wannan hanya!
"Amma kafin ka wuce, bari nayi maka kyautar-kashedi
saboda samun nasarar da kayi!!" Yana faɗar haka ya tafa
hannayensa guda biyu, lamarinda yasa cikin ƙiftawar ido
Izzarsa ta fara hawa sama.
Kan kace meye wannan tuni wannan ciwo da Armad ya ji
masa ya haɗe da kansa tamkar ma ba'a taɓa jinsa ba.
Sannan Izzarsa kuma hawa kawai take tayi da ƙarin
hamsin-hamsin babu alamun zata taɓa tsayawa.
Tun Armad yana iya lissafa ta har saida abin yazo ya wuce
gaban ikonsa. Lamarinda yasa Armad ya ƙame a waje
ɗaya tare da haɗiyar yawu gami da ajiyar zuciyar duk a
lokaci ɗaya, a ransa babu abinda yake tunani illa ratar
dake tsakaninsu da wannan mutun ta fannin Izza, da
kuma sa'ar da yaci da har ya yadda ya fafata dashi a
matakin Izza na ɗari. Domin a lokacin Armad ya fuskanci
cewa ko rabin-rabin Izzarsa baiyi amfani da ita ba wajen
fafatawar da sukai!
"Wannan kyautar-kashedi ba wani abu ba ce illa, labarin
abinda ya faru shekaru ɗaruruwa da suka gabata, akan
mutun mafi girman Izza daya taɓa wuce wa ta wannan
hanya!
"Wannan mutun sunansa AMRAIKUGYU!"
Armad najin wannan sunan ya haɗe gira gami da
bayyana alamun mamakinsa ƙarara a bayyane. Ba komai
bane ya janyo haka ba illa cewa wannan suna ba
ɓoyayyen suna bane, hasalima kowa kusan yasan shi,
kuma saboda daɗewar labarin mai wannan sunan, ba
kowa ne yake yadda dashi bama.
Ganin yadda Armad yayi sai wannan dattijo ya
tambayeshi, "mene ne?"
Armad ya kada baki ya fara da cewa, "Ai nasan labarin
Amraikugyu, na karanta shi ba so ɗaya ba, ba sau biyu,
domin duk da wasu suna cewa ba labarin ba gaskiya
bane, ni yana ƙayatar dani.
"Wai ko bashi ne wanda bama mutane ba, hatta aljanu
saida suka fara rusunawa a gaban Izzarsa ba?
"A zamaninsa kuma saida yayi abinda bai taɓa faruwa ba
a tarihi tun farkon duniya, wato tsayawa ƙafa da ƙafa a
gaban ma'abota baƙaƙen idanu (URURU).
"Kai daga ƙarshe, shi shi kaɗai ya ɗauki takobinsa mai
suna YURA-SHÍRA izuwa doron ƙasa ta biyu, ya yaƙi
sarkin wannan ƙasa wato Dul'Ururu, yaƙin da aka shafe
kwana ɗari ana yi, amma kuma daga ƙarshe har yau
babu wanda yasan wanda yai nasara tsakanin Dul'Ururu

da Amraikugyu!
"Amma daga ƙarshe, ance tunda wannan mutun ya shiga
ƙasar wasu mutane da ake cewa MATAFIYAN-ALWASHI
ba'a ƙara jin labarinsa ba har yau!
"Sai dai ance kanya tafi ya bar takobinsa Yura-shíra a
kwazazzaben Yúga, wadda tsahon shekaru ba'a samu
wanda ya samu nasarar ɗauko ta ba, saboda hatsarin
wajen."
Tunda Armad ya fara jawabi baiko haɗiyi yawu ba, kana
ganin yadda yake bada labarin kasan cewa jarumtar
wannan mutun mai suna Amraikugyu tana ƙayatar dashi.
Wannan dattijo yai murmushi bayan Armad ya gama
bada wannan labari, sannan ya ce, "lallai kasan ɗan wani
abu acikin tarihi.
"To amma kasan sunan wannan mutun na gaskiya?"
Armad yai kasaƙe dajin wannan tambaya, kafin daga
bisani ya ce, "sunansa na gaskiya kuma? Ai sunansa
Amraikugyu...."
"A'a ba haka bane!!" Wannan dattijo ya katse Armad cikin
zafin nama. Sannan cikin fushi ya ci faba da cewa,
"Matsalarku kenan yaran wannan zamani, ba wani yare
da kuka sani inba Aldurish ba, to bari kaji kalmar
'Amraikugyu' kalma ce daga cikin yaren WILBIWRISH.
"Wadda take nufin mafi girman sarki acikin daula, tunda
yawanci a wancan zamanin kusan zaka ga duk manyan
dauloli suna da sarakuna manya guda bakwai, wanda
acikinsu zaka samu mafi girma guda ɗaya, wanda shi ake
cewa AMRAIKUGYU da yaren Wilbiwrish!"
Baki a buɗe Armad ya ƙurawa wannan dattijo ido, wanda
ga dukkan alamu rashin sanin yaren Wilbiwrish da Armad
baiba yai matuƙar ɓata masa rai kamar wanda aka ce
ƙabilarsa bata da muhimmanci.
Wannan dattijo ya ci gaba da cewa, "to sunansa na asali
BAYAJIDDA! Daga baya ne bayan yaci galaba akan dukkan
abokan gabarsa na gida aka koma yi masa laƙabi da
Amraikugyu."
"BAYAJIDDA!" Idanun Armad suna neman fitowa saboda
mamakin jin sunan BAYAJIDDA. "Bayajidda ba shi ne
wanda ya kafa ƙabilar Bayajidda ba, a ƙarni na bakwai
bayan anyi yaƙin Yékashínu ba!"
Tsohon nan kawai kyaɗa masa kai yai, alamun maganar
daya faɗa haka take. Sannan ba tare da ya bashi damar
farfaɗowa daga halin da yake ciki na ɗimuwa ba ya ɗora
da cewa, "ba komai bane yasa na kawo maka maganarsa
ba illa abu ɗaya, wanda kuwa shi ne, shi kansa shugaba
AMRAIKUGYU, gabaki ɗayan rayuwarsa da fafatawar da
yayi, yayi tane akan neman wannan mutun mai suna
TIRIFIL-FAKTA!!!"
"Ehhhhhhhhh!!!" Mamaki ya fara sa Armad matsawa baya
daga inda yake, yana neman faɗuwa.
Wanda dattijo baiko lura da halin da Armad yake ciki ba
ya ɗora da cewa, "Amma a ƙarshe baiyi nasara ba!" Yana

zuwa nan a zancensa yai shiru gami da kallon Armad
cikin yanayin tausayi, kafin daga bisani ya ci gaba da
cewa, "zan iya tunawa a wancan zamanin, shima saida ya
faɗamin kusan sak irin abinda ka faɗa yanzu!
Yake cewa, " 'Ni BAYAJIDDA, ina rantsuwa da mahaliccin
sarki WILBERIYA, saina nemo TIRIFIL-FAKTA, koda kuwa
zan kashe dukkan mutun da aljani dake ban ƙasa akan
yin hakan. Wannan alƙawari ne tsakani na da ma'abocin
wannan raƙumi!!!' "
Wannan dattijo ya ƙara yin ajiyar zuciya tare da girgiza
kai, sannan ya ce, "Yadda kaji haka ya faɗa a wancan
lokacin kalma da kalma bazan taɓa mantawa ba.
"Kawai sai bayan shekaru casa'in da biyu naji cewa shima
ya salwanta a hannun MATAFIYAN ALWASHI.
***
Idan mai karatu bai manta ba sunan littafin nan gabaki
ɗaya TAFIYAR ALWASHI, domin sunan MAGAJIN
WILBAFOS sunan littafi na ɗaya ne daga cikin jerin
littattafan TAFIYAR ALWASHI.
***
Dattijon yai wani kwauron ajiyar zuciya tare da tambayar
Armad acikin wani yanayi na hangen nesa, "Duk da
wannan labarin dana gaya maka kana ji har yanzu baza
ka canja shawara ba?"
Armad na jin wannan tambaya kamar wanda aka
watsawa ruwan sanyi da hunturu, yai firgigit ya farka
daga ɗimuwar daya shiga tare da cewa, "bazan taɓa janye
magana taba koda zan rasa raina!" Sannan a wani salo na
alamun nuna ƙaguwa da sauri kamar wanda ke tsoron
kada wani ya rigashi yaci gaba da cewa;
"Na gode, sosai da wannan tsohon tarihi daka bani, baka
san yadda zai ƙaramin kwarin gwiwa ba, domin har na
ƙara jin ina da buƙatar nayi sauri na tafi domin na fara
neman wannan mutun, kona dawo na haɗu da mahaifiya
ta da wuri!"
Bakinsa abuɗe, wannan dattijo yama rasa abinda zaice
saboda ganin irin kafiya ta Armad tare da rashin tsoro,
ƙura masa ido kawai yai yana kallonsa, wanda shi kuwa
tuni ya maida takobinsa cikin kufenta yana jira yaga
wacce hanya dattijon zai nuna masa.
Can bayan wani ɗan lokaci, kamar wani abu ya shiga
jikinsa, dattijon ya numfasa ya ce, "suna na HánDiyuza,
kada ka manta suna na, domin zai ma ka amfani
wataran!"
Armad na jin haka ya buɗe baki zai faɗa masa sunansa,
amma cikin sauri dattijon ya ɗaga masa hannu, yana mai
cewa,
"bashi da amfani ka gaya min sunanka, domin bana riƙe
suna ye, amma kai sani duk inda muka ƙara haɗuwa zan
tuno kamannin ruhinka, domin bana taɓa manta
kamanni ruhi!"
Nan take dattijo HánDiyuza ya zira hannu cikin rigarsa

gami da fito da wani ɗan littafi, inda ya buɗe shafin farko
acikinsa. Sannan bayan ya gama karanta wani rubutu mai
motsi aciki ya ɗago kai ya dubi Armad tare da cewa, "a
halin yanzu ƙasa ta huɗu ita kaɗai ce a buɗe!
"Amma zuwa nan da ƴan awanni ƙasa ta biyu zata buɗe
ita ma.
"Ƙasa ta biyar sai nan da kamar sati, sai kuma ƙasa ta
shida wadda zata ɗau lokaci mai tsaho gaskiya, amma
ƙasa ta bakwai babu rana tunda ba'a daɗe da kammala
yaƙi akanta ba!"
Cikin sauri kamar wanda yake son yai sauri ya rabuda
Armad, dattijon yaci gaba da cewa, "Wacce kake son
zuwa?"
A wani yanayi mai nuna ƙaguwar da Armad yayi, ya amsa
da cewa, "ƙasar da tafi kowacce sauri mana, wato ta
huɗu kenan!!"
Dattijo HánDiyúza yana jin haka bai tsaya yiwa Armad
wata magana, ya bubbuɗa cikin wannan littafi, gami fito
da wata takarda mai cike da rubutun ɗalasimai aciki gami
da miƙawa Armad ita, sannan ya rufe maganarsa da
cewa, "shekaru sha takwas da suka wuce wani mutun mai
suna BIHANZIN ya wuce ta wannan hanyar, kuma yana
ɗauke da takobin Shugaba Amraikugyu Bayajidda! Ban
san ya akai ya mallaketa ba, amma lallai ita ce!
"Ka kula sosai idan ka haɗu da wannan mutun mai suna
BIHANZIN, domin a halin yanzu yafi kowa

Please Login or Register in order to submit comment