Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

sake shi ta tsira, kodai taci gaba
da riƙeshi su halaka tare.
Amma ga dukkan alamu bata da niyyar sakarsa, koda
kuwa wannan halitta zata cimmusu!!
''Hmmmm,'' yayi ajiyar zuciya, sannan kuma ya kalli
idanun wannan budurwa wadda ke ta ƙoƙari iyakacin
ƙarfin ta wajen zaroshi amma ina saurin wannan halitta
yafi gaban misali tuni ta cimmusu.
Tana kuma dab da taɓa jikin Armad!
***
Shin kuna ganin zai yiwu, baka taɓa ganin mutun ba,
amma kaji kamar ka taɓa ganinsa, harma kana tuno wasu
abubuwa da suka faru a tsakaninku kamar a gaske???

Copyright © 2017 A M IBRAHIM . All rights reserved.
Nidinne dai Shuraih Usman inkiya
99%
Daga taskar magajin wilbafos
Dordor!! Wannan suna ne wanda jama'ar wannan zamani
suka laƙabawa waɗansu halittu, waɗanda ba mutane
bane, hasalima a zahiri fatalwowi ne. Sai dai kuma amma
su na da irin sura ta mutane sak, in banda waɗansu
banbance-banbance da suka raba.
Girmansu ya haura na mafi yawancin mutane misali,
tsaka-tsakinsu sune waɗanda girmansu yakai kimanin
girman ƙarti biyu na mutane a haɗe.
Kalar fatar jikinsu zata iya ɗaukar kowacce irin kala, kama
daga kan baƙi, fari, ja, kore, shuɗi kai dama dukkan
sauran launuka.
To ɗaya dai daga cikin irin waɗannan fatalwowi ne, ya
nufo Armad ta baya, da tsananin muguwar niyya taya
halaka shi. Kuma shi ne wanda Hasanu ya gano yana
tahowa tunda farko, kuma shi ne dai wanda Zahra/
Nostalgiya ta gani, lamarinda yasa take ta ƙoƙarin janyo
Armad waje.
A dai-dai lokacin da Armad ya waiwaya, sukai ido biyu da
wannan fatalwa, mai suna Dordor, kamanninta suka
shiga kwakwalwarsa. Nan take yasan cewa lallai a
kowanne lokaci, mutuwa zata iyai masa sallama idan
baiyi wani abu ba.
Wannan Dordor dai daya Shuɗi ne gabaki ɗayansa; tun
daga kan dogon gashin kansa wanda ke taɓo har tafin
ƙafarsa, harya zuwa tafin ƙafar tasa komai shuɗi ne.
Idan ka cire launin fatar jikinsu, wani banbanci da
waɗannan fatalwowi suke dashi, idan ka haɗasu da
mutane shi ne, adadin kawunan kowanne ɗaya a cikinsu.
Duk da kasancewar yawanci waɗanda jama'a suke arba
dasu, adadin kayikansu bai wuce ɗaya zuwa biyu ba, to
amma akan gamu da masu kai uku a lokuta ƙalilan. Misali
wannan shuɗin dake biye da Armad kansa ɗaya ne
kurum, wanda hakan yasa yayi kama da ɗan-adam sosai,
idan banda mahaukacin dogon gashin kansa da kuma
shuɗiyar fatar jikinsa!
Amma a zahiri da yawa daga cikin mutane sun san akan
iya samun Dordor masu kai ɗai-ɗai har guda bakwai.
Abin mamakin shi ne, watanni shidan ƙarshen kowacce
shekara duk wata ƙasa dama duk wasu matafiya dake da
burin yin tafiya akan Bangwayen ruwa guda biyu sai sun
yi rijista, a wajen ma'abota Ururu, domin tafiya akan
wannan ruwan.
Hakan zaisa abasu shedar kariya daga waɗannan halittu
masu laƙabin Dordor, wanda ta hakane kaɗai ake iya yin
tafiya akan wannan bangwayen ruwa cikin kwanciyar
hankali.
A cikin littafin ''Halittun farko a duniya,'' da B. Zinariya ya
wallafa, ya rawaito cewa, A farkon lokaci, al'ummar fulani

mazauna yamma, sun yanke shawarar yin hijira zuwa
gabas.
Amma bisa ƙaddara akan hanyarsu ta tafiya, sun gamu
da halittu masu firgici da dama, sai dai kuma mafi muni
aciki, su ne waɗansu halittu da suka kira da suna Dódo.
Karawar waɗannan fulani da waɗannan halittu shi ne ya
zamo mafi munin abu da fulanin suka taɓa fuskanta.
Domin abisa alƙaluma kafin su isa inda zasu je, sai da
sama da biyu cikin uku, na jama'arsu suka salwanta.
Bayan shekaru masu yawa, suka isa gabas. Amma sai suka
ɗauki wata sabuwar al'ada ta rashin magana tsahon
kimanin wata ɗaya, domin jimanta waɗanda suka rasa
rayuwarsu a yayin wannan hijira.
Bayan shekaru masu tsaho, zafin rashin da suka fuskanta
yaɗan fara raguwa, ma'abota kwarewa ta fannin magana
da salo wajen bada hikaya acikinsu, sai suka fara rubuta
labarai domin fito da jarumtar mutanen nasu da suka
fafata da waɗannan halittu, masu suna Dódo.
A saboda haka kafin jimawa sunan Dódo ya bazu a sassa
da yawa na duniya. Harma ya zamanto abin bawa yara
firgici da tsoro;
''Wato idan yaro yayi abu sai kaji ance ya bari ko kuma a
haɗa shi da Dodo."
***
To wannan dai shi ne abinda yazo acikin wancan littafi.
To da yake a gaba kaɗan acikin littafin anyi bayani akan
su waɗannan halittu masu suna 'Dódo' da kuma siffofin
su, waɗanda idan ka duba za kaga sunyi kama sosai dana
waɗannan halittu da a wannan zamani, jama'a sukewa
laƙabi da Dordor, to da dama daga cikin mutane su na
tunani cewa akwai yiwuwar waɗannan halittun iri ɗaya
ne ko kuma ƴan'uwan juna ne da waɗancan da suka
fafata da fulanin a wancan zamani.
***
Armad ya kalli idanun wannan budurwa ya kuma kalli irin
yanayin yadda take ta ƙoƙarin kuɓutar dashi.
Tuni har makarin fuskarta ya faɗi, amma duk da hasken
dake tashi daga fuskarta ta bai hana ganin kwalla dake
haɗowa acikin idanun nata ba.
Armad bayan yayi ajiyar zuciya ya ɗaga ido ya ƙara
kallonta, suka haɗa ido.
Baice komai ba, ita ma kuma bata bashi amsa da komai
ba, amma bayan wannan kallo guda ɗaya tak da sukai wa
juna, Armad ya yanke shawarar cewa lallai bai kamata ya
bari wannan budurwa ta halaka a wajen nan ba.
Koba komai yana da buƙata ya tambaye ta yaji baki da
baki, mai yasa yake jin cewa kamar ya taɓa ganinta,
harma yana ganin waɗansu mu'amaloli da suka gudana a
tsakaninsu. Waɗanda suke matuƙar kama da zahiri,
amma kuma shi yasan a iya tunaninsa basu faru ba.
To a dai-dai wannan lokaci tuni wannan shuɗin Dordor
ya ɗaga hannunsa ya kuma kawowa Armad wafta.

Wanda kuma a lokacin ne su Hasanu suka ƙaraso dab
dasu.
Idanunsu acike da rashin sanin yadda zasuyi, suka tsaya
cirko-cirko akan Zahra.
Kasancewar su na da cikakkiyar masaniyar cewa taɓa
wanda Dordor ya taɓa tamkar taɓa Dordor ɗinne da
kanka, wanda kuma hakan tamkar cakawa kanka wuƙa
ne. Domin duk wanda ya taɓa Dordor, a take gaba ɗayan
ruwan jikinsa ke ƙonewa!
Saboda yana daga cikin sanannen ilmi a wannan zamani
cewa ba'a taɓa Dordor da fata, saboda haka basu da
damar taɓa wannan budurwa, a dai-dai wannan lokaci da
take riƙe da Armad shi kuma Armad ɗin bai rage saura
ɗan taƙi ba, tsakaninsa da shuɗin hannun wannan
Dordor ɗin nan ba.
To a wannan lokaci da kusan kowa acikinsu ya ɗebe haso
a sannan ne abinda ko a mafarki basu taɓa kawowa zai
faru ba ya faru ba.
Wannan Dordor yana gab da taɓa Armad, a yayinda
Armad ya fizge hannunsa daga hannun Zahra, ya guma
zare takobinsa, sannan yana lilo akan iska ya juya ya kai
sara ga hannun wannan Dordor da sauran ƙiris ya kama
wuyansa.
Koda ganin abinda ya faru, sai jikin Zahra ya fara
karkarwa, ba tare da ta sani ba ma ta yunƙura da ƙarfin
tsiya tare da miƙewa da niyyar riƙo Armad.
Amma a dai-dai lokacin da take gab da faɗawa cikin
ramin ne, su Hasanu da Kiru suka isa gareta, a inda Kiru
yakai hannu ya riƙo ta, sannan kuma kafin kace meye
wannan ya dawo da ita baya kuma a lokaci ɗaya duk su
ukun suka yi tsalle sukai baya da sauri.
Cikin daƙiƙa ɗaya tuni sun bada kimanin taku biyar
tsakaninsu da Armad.
To a sannan ne suka tsaya, sannan baki a buɗe cike da
mamaki suka ƙurawa Armad ido.
A baya basu samu lokacin mamaki ba, amma yanzu da
suka ga sun ceto ƙanwar tasu wadda keta ƙoƙarin
kwacewa daga riƙon da su biyun sukai mata, sai suka ɗan
nutsu. A inda hatta Kiru da dakakkiyar zuciyarsa, saida ya
sarawa Armad da irin jarumtar daya nuna wajan
fuskantar wannan Dordor, gaba da gaba.
Idanun Kiru suka ƙara kaɗawa da marmarin yaƙi babu
abinda yake faɗa a zuciyarsa sai, ''kash! badan
mutuwarsa tazo da wuri ba, ai daya taimaka wajan fiƙe
takobi ta, domin ko badan komai ba ina son fafatawa da
marasa tsoro irinsa.''
Shi kuwa Hasanu wanda ke riƙe da hannun hagun Zahra
ƙam-ƙam magana yake aciki, ''hanzari ya kamata nayi na
koma gida, na tabbatar da abinda nake kokwanto!''
Da yake tunda aka fara wannan fafatawar baice uffan ba,
sai kawai nazari da kuma bibiyar abubuwa da yakeyi.
Daga gefe kuma acikin abinda bai wuce daƙiƙa biyar ba,

har Armad da wannan shuɗin Dordor, sunyi musayar
sama da sara ashirin, a fafatawarsu a saman wannan
rami.
Duk da tsananin kyau kamar na ƴaƴan sarakunan
manyan fararen aljanun farko, da kuma girman kai da
ƙasaita da mulki irin ma'aboa maɗaukakiyar Izza, da
Zahra take dashi, amma hakan baisa ta buɗe baki ba,
idanunta cike da kwalla ta dubi Armad,kamar wani
wadda take so ta bawa wanda zai mutu cikin ƴan daƙiƙu
wasiya, amma ina takasa cewa komai.
Nan take Kiru ya riƙe baki, yana mamaki; shi dai yasan
irin buwaya da ƙanwarsa take dashi a fannin kyau da
sarautaa dukkan faɗin ƙasa bakwai. Hasalima kusan ta
kori sama da ƴaƴan manyan sarakuna goma, masu
neman aurenta. Kuma tunda yake bai taɓa ganin ta nuna
wani yanayi irin wannan ga wani ɗa namiji ba, komai
kyansa, komai buwayarsa, kuma komai mulkinsa.
Ballantana Armad, wanda yasan cewa koda ma wani ɗan
babban sarkin ne, to yasan cewa bazai taɓa kama ƙafar
manyan ƴaƴan sarakunan da suke neman auren ƙanwar
tasa ba.
Hasalima da dama zasu iya bayarda duk abinda suka
mallaka, domin kawai rana ɗaya, sau ɗaya tak, ta riƙe
hannunsu. Amma basu samu ba.
Yana gama wannan tunanin, kawai abu ɗaya ya yanke
acikin zuciyarsa, cewa LALLAI WANI ABU YA TAƁA
AFKUWA TSAKANINSU; BANDA GAYA MANA DA TAYI TA
CETO SHI DAGA CIKIN WANNAN GARI, LALLAI AKWAI
WANI ABU, WANDA BAMU SANI BA!
Can bayan wani lokaci kalmar kawai data fita daga
bakinta ita ce, ''Ar...mad...''
A dai-dai wannan lokaci ne wannan Dordor ya buɗe
bakinsa ya fesowa su Hasanu wani ruwa baƙi-ƙirin a
dunƙule kamar ƙawanya daga bakinsa.
Wanda kan kace meye wannan, tuni ya bayyana a gaban
su Zahra, inda ya fara buɗewa yana ƙara girma tamkar
wanda yake so ya haɗiye su gaba ɗaya. Kan kace meye
wannan tuni wannan baƙin ruwa ya canja daga kimanin
kamu ɗaya zuwa kimanin ɗaya.
Bayanin yadda abubuwan suka faru zai ɗauki lokaci,
amma yanayin yadda komai ya faru a zahiri baifi ƙiftawar
ido da bismillah ba.
Lallai duk wani mutum a wannan zamani yasan me
wannan baƙin ruwa yake ƙunshe dashi, lallai yasan cewa
ko mai za'ai kuma ko a bakin ransa to bai kamata ya bari
wannan ruwa ya taɓa shi ba.
Armad duk da bai taɓa arba da Dordor ba, amma yasan
haka daga ilmin da yayi a rayuwarsa, su kuma waɗannan
mutane uku dake wajen dukkansu ƴaƴan sarakuna ne,
saboda haka sun san sarai mai hakan yake nufi.
Armad bai san mai yasa ba, amma kawai yaji a ransa
cewa bai kamata ya bari wannan budurwa ta halaka a

wajen. Sannan kuma ya san cewa idan ya bari ta halakan,
to lallai baya jin zai samu wanda zai iya bashi amsar
abubuwan da yake so ya tambayeta.
Kan kowa ya farga tuni Armad ya ɗaga takobinsa sama,
ya numfasa a wani yanayi mai cike da yanke shawara,
sannan ya saukarda saran takobin tasa da ƙarfin gaske
gami da ambatar, ''Wilbafosiyan-Siwod-Dans!!''
Rufe bakinsa keda wuya wani haske ya fara feshi daga
jikin takobin tasa, nan take komai ya tsaya cak; kama
daga kan wannan baƙin ruwa dake gab da haɗiye su
Zahran da kuma wannan Dordor dake biye da Armad
zuwa ga dukkan ƙasar data rududduge.
Wannan haske nan take cikin ƙiftawar ido yai matuƙar
ƙaruwa ta yadda ya kashewa kowa ido, ko tafin hannu
ba'a iya gani.
Bayan kimanin daƙiƙa biyu hasken ya fara raguwa, kafin
daga bisani ya ɗauke gaba ɗaya.
Su Hasanu na tsaye inda suke, idonsu a gaba na ƙoƙarin
karanta maiya faru.
Abinda kuwa sukai arba dashi shi ne, babu alamun
wannan baƙin ruwa, babu alamun shuɗin Dordor ɗin,
sannan kuma bisa mamaki dukkan ƙasar da suke kai
wadda da duk ta rududduge kuma su na gab da ruftawa
ta dawo ta haɗe tamkar wani abu bai taɓa faruwa da ita
ba.
Dukkanin wannan abin mamakai ne da ban al'ajabi a
garesu musamman ganin ƙasar da da ta riga ta
rududduge ta kuma zaizaye, amma yanzu kuma ta dawo
ta haɗe tamkar babu abinda ya taɓa samunta.
To amma wani abu guda ɗaya daya fi ɗugunzuma
hankalinsu sama da komai shi ne rashin ganin Armad ko
sama ko ƙasa!
Bayan ganin wannan fasaha da Armad yai amfani da ita,
Hasanu ya ƙara samun nutsuwa kan abinda yake
kokwanto, lamarinda ya ƙara sawa yaji akwai buƙatar ya
koma da Armad garinsu maimakon kashe shi, duk da
kuwa Armad ɗin yaji sirrin su, SIRRIN DAZAI IYA RIKITA
DUNIYA BAKI ƊAYA.
Shi kuwa Kiru, marmarin yaƙi ne kawai ya ci gaba da
kaɗawa a idonsa, yana jin cewa lallai Armad ya isa su kara
dashi.
Ita kuwa wannan budurwa kana ganinta zaka san tana
cikin jimami da ɓacin rai, saboda badan hannun Hasanu
dake riƙe da ita ba, da tuni ta faɗi ƙas!!
***
Wai me Hasanu yake kokwanto akan Armad, harda yasa
ya fara ƙoƙarin fasa kashe shi?
Anya kuwa babu wani abu daya faru tsakanin Armad da
Nostalgiya, wanda bamu sani ba, wanda kuma shima bai
sani ba, wanda kuma ga dukkan alamu ita kaɗai ta sani?
Copyright © 2017 A M IBRAHIM . All rights reserved
MAGAJIN WILBAFOS

Marubuci: Dr Abdullahi Muhammad Ibrahim
Babi na 12: Ururu
Post by: Shuraih Usman
@shuraih 99%
www.facebook.com/hausaebooks
.
.
K wanaki huɗu bayan ɓacewar Armad bayanda yayi
amfani da wannan hatasabibiyar hanya ya ceto su
Zahra daga wannan baƙin ruwa da shuɗin Dordor
ya harba musu. Zahra tayi shiru su na tafiya bata
kuma
yiwa kowa magana ba tun bayan tahowar tasu, duk
da
kuwa ƙoƙarin kwantar mata da hankali da Hasanu
yayi
tayi, kai hatta Kiru ma da ya nuna aniyarsa a fili ta so
ya
halaka Armad a baya, sai da ya sauko ya kuma fara
lallamar Zahran yana gaya mata cewa shi dai bai
gane
mene ne a tsakaninsu ba, amma koma mene ne ta
gane
cewa, Armad ba irin mutanen da zasu mutu cikin
sauƙi ba
ne, ya kuma gaya mata da Armad ɗin zai iya mutu da
wuri
aida tuni ya rigaya ya halaka shi da farar takobinsa.
Ya gaya mata hakan ne da wasa duk da niyyar ko zata
ɗan
saki fuska, amma ina ko kaɗan bata ma nuna ta jishi
ba,
idanunta kawai na nuna nutsawa acikin tsananin
tunanin
wani abu ne kawai.
Tun da farko bata yarda sun baro wajan ba sai da
suka
kwashe awa ashirin da huɗu cir, tana kallon wajan
da
Armad ya ɓace.
Babu yadda Kiru bai ba akan ta gaya masa menene
tsakanin ta Armad ɗin ba amma bata ce komai ba,
”ba
kamar ke ba, bai dace dake ba, ki faɗa cikin wannan
yanayi ba, duk ina taƙamar ki da ji da isa ta tafi kuma
yau.
”Ca nake gab da zamu taho kika ƙara korar ɗan
sarkin
Liha ba, wanda kuma shi ne na bakwai a layin ƴaƴan
sarakunan da kika ƙi.
”Ji nake ke inba Yarima Deniz Bizaya ba sai rijiya!!”
To haka irin waɗannan maganganu suka ringa fita

daga
bakin Kiru duk dan ya saussauta mata ƙuncin da
yaga ta
shiga. Wanda a gari banza ko mai zata bashi ba lallai
ma
taga dariya a fuskarsa ba, ballantana ma ya tsaya
yana yi
mata irin waɗannan maganganu.
Amma saboda ganin halin da take ciki ya yanke
shawarar
hakan.
To! Haka dai ya ci gaba amma ko a jikinta, inda daga
ƙarshe ya gaji ya rabu da ita kurum, ya koma wajan
Hasanu wanda ke kan dokinsa samfurin Kili, shima
ga
dukkan alamu akwai abinda ke damun zuciyar sa,
domin
ya natsa matuƙa a cikin tunani.
To haka dai suka tashi suka nufi hanyar Sisiya akan
dawakansu, inda suka shafe kwanaki uku su na
tafiya.
Kuma a wannan lokaci tafiyar data rage tsakaninsu
da
garinsu mai suna Sisiya, bata fi ta sati biyu ba.
Kiru wanda ke tafiya a dama da Zahra, Hasanu kuma
a
hagu, inda saka ta a tsakiya, yai firgit ya ɗaga kai,
kana ya
dubi Hasanu idanunsa cike da kokwanto.
Shima Hasanun kamar yasan abinda yake tunani ya
ɗaga
kai ya dubeshi.
Su na haɗa ido Hasanu bai jira wani abu ba ya fara
tambayar Kiru, ”dame-dame ka lura dasu a tattare da
wancan yaro waɗanda baka fahimta ba?”
Kiru yaɗan ƙifta ido kasancewar tambayar ta
tabbatar
masa da abinda yake zato na cewa lallai Hasanun
yasan
wani abu a tattare da Armad.
Saboda haka bai tsaya ɓata lokaci ba, kawai ya
numfasa ya
fara bayani, ”na kula da abu biyu!” Ya ɗaga ɗanyatsansa
na hagu guda ɗaya yana nuni da ɗaya.
”Na farko na lura ya iya tsaiwa akan iska,” ya ɗan
dubi
Zahra kamar wanda yake jira tace wani abu, kafin
daga
bisani ya ƙara ɗaga yatsunsa guda biyu sama sannan
ya ci
gaba da bayani, ”Na biyu shi kansa bai san cewa yana

da
wannan Izza ba ta iya tsayawa akan iska ba, badan
komai
ba sai dan cewa da fari yayi ƙoƙarin miƙa hannu
domin ya
riƙe tsandauri dan ya kuɓuta daga faɗawa ramin
kamar
yadda nima nayi, inda ba daban Zahra ta riƙoshi ba
to da
akwai yiwuwar ya faɗa ya mutu batare da ya taɓa
gano
cewa yana da wannan Izza ba.”
Koda Kiru yazo nan a zancensa sai yai shiru ya kuma
kalli
ƙasa kamar mai jimanta wani abu, kafin can daga
bisani
ya ɗago kai ya ƙara fuskantar Hasanu, wanda ya
taddashi
yana kallonsa shima.
Bayan ɗan jira da bai wuce na daƙiƙa biyar ba,
Hasanu ya
numfasa ya tambaye shi, ”wannan su ne abubuwan
da kafi
lura dasu?” Kiru ya kyaɗa kai alamun eh.
”Eh to! Ba komai ina ga kayi ƙoƙari, amma kamar
kullum
yadda nake ƙara gaya maka, yadda kake maida
hankali
akan horonka na takobi haka ya kamata ka ƙara
maida
hankali akan karatu ma, badan komai ba sai dan ka
ƙarawa ƙwaƙwalka ƙarfi ita ma.”
A dai-dai wannan lokaci fuskar Hasanu ta nuna
alamun
muhimmancin maganar da yake yiwa Kiru da kuma
sonsa
da ace Kirun ya ƙara maida hankali wajan karatun da
yake
gaya masa.
Bayan ya kalli farar takobin Kiru na lokaci sai ya
ɗauke
idonsa daga kan Kirun ya kuma fuskanci gabansa
inda ya
fara jawabi, ”tunda farko da naga wasu abubuwa
hankali
na ya fara ɗugunzuma, lamarinda yasa na sa masa
ido.
”Amma bani da wasu cikakkun hujjoji, wanda hakan
ne
yasa na ci gaba da bin abubuwan da suke faruwa
tsakaninku ba tare da na shiga ba, abisa tsammanin
hakan

zai kaini ga gano abinda nake tunani.
”Kaga dai abu na farko… shi ne wannan jan ƙyalle
dake
ɗaure a gaban goshinsa na musamman ne. Haske
baya
shugewa ta cikinsa, saboda haka indai baka fasaha ta
musamman ko kuma ido na musamman baza ka iya
ganin
mene ne a bayansa ba.”
Kiru wanda ke sauraro ya ɗaga kai cikin mamaki ya
kalli
Hasanu, ”kyalle kuma??”
Hasanu ya ƙara numfasa wa sannan ya ce, ”ba
kyallen
bane abin daya ja hankali na sosai bama!
”Abunda kyallen ke rufe dashi. Domin ina kyautata
zato,
indai ba rafkanwa na samu ba, to lallai akwai irin
wannan
Miyura da akewa laƙabi da ‘Miyura Yinfinita’ ko kuma
‘Miyura Madauwamiya’, wadda bata taɓa ɓacewa tun
daga
sanda aka haifi mutum har mutuwarsa, maimakon
kwana
bakwai data kowa take ta ɓace.
”Kamar yadda ka sani abu ne mai tsananin wahala ka
samu
irin waɗannan mutane, kai harma yafi wahala ka
samu
raƙumi acikin kuratandu da ka samu irin waɗannan
mutane musamman ma a wannan zamani.
”Wanda har yakai kawai mutane da dama suna
tunanin
kawai dai labaru ne irin na hikayun gizo da ƙoƙi
kurum.
”To amma mu da muka fito daga Burja, munsan
cewa
yana daga cikin ɗaukakar shugaba Ibasi Burja, Jinnnafarko irin wannan Miyura.
”Abu na uku wanda shi ne mafi muhimmanci, shi ne
wannan fasaha da yayi amfani da ita ta ƙarshe!!
”Har yanzu dai bazan iya cewa ina da kaso ɗari na
tabbashi ba, amma lallai nafi kaso saba’in.
”Cewa na taɓa ganinta acikin wannan littafi na Jána
Sisiyu.”
Tuni Kiru ya shiga cikin ruɗani da zuciyarsa saboda
abubuwan duk daya ke ji, abubuwa ne da duk da
baya
son bincike da karatu amma yasan tarihin Ibasi
Burja
wanda shi ne ma ya kafa kusan gaba ɗayan daular

Banfiriya, mutumin da akewa laƙabi da Jinn-nafarko,
inda daga baya ma aka kafa sabuwar ƙungiya da
suka
sakawa sunansa.
Kuma sannan yasan littafin Jana Sisiyu!
Kuma yana da cikakkiyar masaniyar manufar
maganar da
Hasanu yake yi!!
Saboda haka ya shiga wannan ruɗani.
Hasanu yai kyaran murya sannan ya ƙarasa zancensa
da
cewa, ”to koma dai meye, yanzu abu biyu ne suka
rage
mana; na farko dole ne muyi sauri mu ISA Sisiya,
domin
mu isarda wannan babba sirri da muka gano ga
Shugaba!”
Ya na faɗar haka ya waiwaya gefe ya kalli Zahra,
domin
yasan cewa wannan sirri, yana cikin kanta, tun bayan
da ta
karanta zuciyar Armad ta zaƙulo shi!
“na biyu kuma,” ya juyo izuwa Kiru gami da ci gaba
da
bayani, “zarar muka isa Sisiya, DOLE NE ASAKA
MANYA-MANYAN MA’ABOTA IZZA SU BAZAMA SU
NEMO WANNAN YARO MAI SUNA ARMAD, duk inda
yake a duniya, ko shi ko gawarsa!!”
To a dai-dai lokacin da suka kammala tattaunawar
tasu
kuma suka dubi gabas, Zahra wadda kwanaki huɗu
kenan
cir bata ce komai ba tun bayan sanda ta kira sunan
Armad,
ta buɗi baki, kanta a sunkuye tayadda baza a iya
tantancewa ko hawaye take ko kuma ba hawaye take
ba, ta
furta wata kalma guda ɗaya.
”Shi ne!!”
Cikin mamaki duk su biyun sukai saurin juyawa
izuwa
gareta bakinsu a buɗe, kai daka gani kasan cewa
magana
ce mai yawa a bakinsu.
Amma duk su biyun babu wanda ya iya furta wani
abu
bayanda suka ga yanayin ɗimuwa dake fuskar
Zahran,
lallai sun san cewa yi mata magana a dai-dai wannan
lokaci bashi ba ne mafi kyawun abinda zasuyi ba.
Saboda haka suka haɗiye abinda ke ransu suka ci

gaba da
tafiya ba tareda kowa yace ƙala ba.
A haka su na tafiya su na yada zango, saffa-saffa har
suka
ƙara cinye wata tafiyar ta kwana uku.
To a wannan rana su na tafiya suka iso cikin wasu
manyan
duwatsu masu yawan gaske, sannan kuma ga girma
ta
yadda kana gani kasan cikinsu zaiyi daɗin fakewa
akai
harin sunƙuru.
Koda zuwansu nan, sai Hasanu ya bada umarnin su
kwana
anan in yaso da sanyin asuba, saisu shiga cikin
duwatsun
ido na ganin ido.
Haka kuwa sukai, inda suka kafa tanti sannan suka
kwana,
asubahin fari suka ɗaura ɗamara suka shiga cikin
wannan
duwatsu.
Abu na farko da suka fara arba dashi shi ne sauyin
yanayi,
inda su na taka ƙafa ciki ɗan hasken daya fara fitowa
na
asuba suka ga ya dusashe nan take, wani duhu na
musamman ya maye gurbinsa.
Sannan kuma suka fara jin wata iska mai sanyin
gaske
tana dukan fuskarsu.
Kafin zuƙatansu su gama ankarewa da wannan
sabon
muhalli suka fuskanci wani sabon firgici.
Inda suka fara jin wata kakkausar murya daga cikin
dajin
duwatsun na tasowa, ”kwamanda na biyar na
rundunar
tsakiya daga Burja, Hasanu!
”Ance yiwa ɓarawo sata bashi ce.
”Ba komai nake magana ba illa AYRID mai mataki na
shida dake hannunka!!
”Ku bamu ku tsira da ranku, ku hanamu, mu kasheku
sannan kuma mu ɗauka da ƙarfin tsiya.”
***
Ururu
A tsohon yaren Aldúrish, kalmar Urú tana da ma’ana
biyu;
ta farko tana nufin baƙin abu, yawanci ana amfani
da ita
ne, a abinda yake da alaƙa da jikin ɗan adam, sai
kuma

ma’ana ta biyu, wato adalin shugaba (yawanci mara
dukiya da yawa.)
Shekaru aru-aru da suka gabata (Before Amri, B.A),
al’ummar wata tsohuwar ƙabila wadda babu wanda
yasan
asalinta a dukkan wannan zamani suka bayyana da
wani
abu sabo.
Wanda ba’a saba gani ba; wato gabaki ɗayan
idanuwansu
baƙaƙe ne, baƙi ƙirin, babu ko alamar fari acikinsa.
Saboda haka, sai mutanen wannan zamani suka fara
kiransu da suna Uru.
To amma, ga dukkan alamu wannan suna baiyi musu
daɗi
ba, saboda a cewarsu, lallai akwai ƙololuwar rashin
kyautawa a ringa kiransu da kalmar da zata iya
ɗaukan
ma’anar sarki adali mara dukiya. Acewarsu wannan
zagi
ne ga buwayarsu da ƙarfin mulkinsu aban ƙasa.
Saboda haka, ba jimawa aka maida wannan suna ya
koma
Urúrú, wato aka ƙara ‘rú’ a ƙarshe. Wanda ma’anar
sunan
ta baƙaƙen idanu amma na manyan sarakunan
aljanu
masu ƙololuwar girman kai waɗanda suka taɓa
mulkar
duniya, waɗanda kuma aka ce saboda tsananin
girman
kansu aka shafesu daga ban ƙasa. Domin kalmar ‘Rú’,
indai anyi amfani da ita, to ana nuni da waɗancan
aljanu
ne.
Wannan ƙabila sun daɗe suna mulkar bil-adama,
babu
zamani da yazo da bai tafi dasu ba, hasalima a
dukkan
littafan tarihi saika gansu, wanda hakan yasa
mutanen
wannan zamani da dama suke tunani kodai dama
wannan
duniyar tasu ce su kaɗai.
Sunga jiya, sunga yau, kuma ga dukkan alamu babu
abinda ya isa ya hana suga gobe.
Su suka ƙirƙiro da Amri, kuma su suke da yaren
Aldurish,
sannan kuma su suke tsarawa dukkan mazauna ƙasa
bakwai tsarin rayuwarsu, a wata hanya da suke cewa
Rukunan Urúrú!
Sudai waɗannan Rukunai, guda uku ne asali, amma

daga
baya saboda wani dalili da ba’asan ko menene ba,
suka
goge Rukuni na uku, ya dawo saura rukunai biyu
kawai.
Rukuni na farko, shi suke kira da Jinzidal! Yana
magana
ne akan yadda mutane zasu yi rayuwarsu, cewa
dukkan
mutane sai sun zama iri biyu.
Kaso na farko sai sun zama Bayi, wato su aikinsu
bauta
kawai!
Na biyu kuma su ake kira da Béligi, waɗanda su
kuma
aikinsu yaƙi.
A ƙarƙashin wannan tsari, duk shekarar duniya sai
anci
gagarumar kasuwar cinikin bayi, wadda akeyinta a
bisa
tsarin da ake kira da suna Jinzidal.
***
Jinzidal shashi ne mai zaman kansa acikin wannan
littafi,
wamda za’a zo kansa na bada daɗewa ba. Inda zaku
ji
yadda Ururu suka ɗaurewa cinikin bayi gindi.
***
Shi kuwa rukuni na biyu, shi ake kira da Izza
Ristirikta!
A ƙarƙashin wannan tsari, dukkan wani ɗan adam
dake
rayuwa abisa doron ƙasa bakwai, idan ka cire ƴan
ƙabilar
Ururu, saiya karbi jarrabawar daga Ururu, idan dai
yana
so ya haura daga matakin Izza na ɗari zuwa sama.
Haka daga na ɗari biyu zuwa sama, haka haka, wato
duk
bayan shekaru ɗari na Izza, sai ka karɓi wannan
jarrabawar kafin ka wuce gaba.
Wannan jarrabawar ba wani abu bane illa, Ruwan
wuta da
za’a saukar maka daga doron ƙasa ta farko kai kaɗai.
Idan ka wuce shi ka rayu, to kaci wannan jarrabawa,
amma idan ka mutu shikenan.
Kuma duk bayan mataki ɗaya, wahalar daɗa ƙaruwa
take.
Wanda hakan nema yasa kaɗan ne suke iya ci gaba
da
ƙarawa Izzarsu yawa zuwa wani mataki, indai kai
baɗan

ƙabilar Ururu bane.
A ƙarƙashin wannan Rukuni akwai abubuwa da
dama,
waɗanda Ururu ke amfani dasu wajen tabbatarda
cewa
babu wani mahaluƙi daya kuɓucewa wannan
jarrabawa.
Wannan abubuwa za’aji su anan gaba kaɗan.
***
Wannan shi ne kaɗan daga cikin girman iko da Ururu
ke
dashi a ban ƙasa a wannan zamani.
To wannan sirrin dai da Armad yaji a wajen su
gimbiya
Nostalgiya, yana da alaƙa da rukuni na farko, wato
Rukunin Jinzidal (cinikin bayi), dama kuma wani
ɓangare
na Rukunin Izza Ristirikta.
Sabida haka, ko’a wannan lokaci da iska tayi cilli
dashi
zuwa wata duniyar, kafin hankalinsa ya gushe abinda
ya
fara faɗo masa kenan.
Lallai yasan cewa akwai babban tashin hankali, koma
kuma mummunan yaƙi dake gabatowa indai aka
aiwatar
abinda yaji.
To amma mai ya kamata yayi? Wannan ita ce
tambayar
daya kasa bawa kansa amsa.
Nidinne dai Shuraih Usman inkiya
99%
Daga taskar magajin wilbafos
MAGAJIN WILBAFOS
Marubuci: Dr Abdullahi Muhammad Ibrahim
Babi na 13: Wacce shekara muke
Post by: Shuraih Usman
@shuraih 99%
www.facebook.com/hausaebooks
.
Magajin Wilbafos
Babi na sha Uku 13: a Wacce shekara muke wannan
Marubuci:- Dr Abdullahi Muhammad
Posts by Shuraih Usman
Daga:- Taskar Magajin Wilbafos
.
T un bayan ɓacewar Armad daga wannan waje,
hankalinsa ya dusashe ta yadda shi kansa bayan
farkawarsa bai san a inda yake ba, bai san kuma
tayadda yaje wajen daya farka ya tsinci kansa ba,
sannan

kuma bai san kwana nawa yai ba, tun bayan
dusashewar
hankalinsa ba.
Amm abu ɗaya da yake iya tunawa

Please Login or Register in order to submit comment