Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

bayani
kaɗan akan darajar Ayrid. Shi dai Ayrid kamar yadda aka
labarta a baya kwaya ce ƴar ƙarama kamar masara ko
kuma dawa. Wasu su na zuwa manyan wasu ƙanana.
Kowanne yana da launinsa na daban. Amma abu mafi
muhimmanci shi ne, akwai busasshen Ayrid, akwai kuma
ɗanye. Dukkaninsu daga irin bishiya (zangarniya) ɗaya
suke. Shi busasshe, shi ake sarrafawa izuwa sisi da
kwandala domin kashewa. Akwai ma'aikatu na
musamman dake shalkwatar Ururu wanda ke sarrafa irin
wannan Ayrid. Shi kuwa ɗanyen Ayrid shi ne wanda keda
mataki-mataki kamar yadda aka gani a baya.
Kamar wanda Nusi tayi amfani dashi (mai keken doki).
Akwai wasu da dama irinsa. Ana iya amfani dasu wajen
ajiya na kayan abinci ga matafiya ko kuma kayan yaƙi.

Akwai na magani, akwai na sihiri, akwai masu ƙara ƙarfin
Izza. Kai dama dai sauransu. Kuma iya matakin Ayrid ɗin,
iya darajar abubuwan da zai iya yi.
Idan ka duba zaka ga sama da kaso casa'in da tara na
al'umma iyakacin wanda suke iya mallaka, shi ne mai
daraja ta uku, wanda dashi zaka ga suna tura saƙo komai
nisan waje, kuma su karɓa. Sannan kuma su iya ajiye
kayansu a yayin tafiya.
Amma Ayrid masu daraja sama da uku amfaninsu bazai
lisaafu ba anan, domin kuwa idan muka fara za'aci
shafuka da dama anayi, saboda haka ku biyu mu a gaba
zakuga irin al'ajabin dake ƙunshe cikin wannan ɗan iri da
akewa laƙabi da Ayrid!
Bayan kimanin mintuna sha biyar, alƙalin wasa ya bada
umarnin su Armad su shiga cikin filin su uku.
Inda bayan sun shiga suka tararda wannan abu da ake
cewa Alkadar!
Wannan dai ba wani abu bane illa wani mutun-mutumi
da akai da jan dutse. Komai kamar na jikin mutun ne,
amma a wajenda ya kamata ace fuska ce, sai ya zamana
kamar gilas ne kawai, daya rufe kaf wajen.
Aciki akwai hoton lambobi guda uku a jere, wanda ba
wani abu bane illa sikelin wannan abu mai suna Alkadar.
Kuma kamar yadda Nusi ta bayyanawa Armad cewa
abinda kawai yake da buƙata yayi shi ne, yayi amfani da
sak irin Izza da yai amfani da ita ya wuce mataki na farko,
ya tattare ta ya kuma daki cikin wannan mutumi da ita.
Ta kuma gaya masa cewa wannan sikeli ɗaya zuwa ɗari
ne, kuma duk wanda ya fi kowa lamba shi ne zai wuce
zagayen gaba!
Saboda haka a lokacin Niyashi shi ne a gaba, Kiru na biyu,
sannan kuma Armad na ƙarshe.
Cikin sauri, fuska a murtuke, Niyashi ya isa kusa da
wannan mutun-mutumi, inda ya ɗaga hannu ya daki
cikin wannan mutun-mutumi.
Hakan na faruwa lambobin dake fuskarsa suka fara bada
haske, sannan suka fara motsi.
Kan kace meye wannan tuni sun wuce hamsin...
sittin..saba'in, inda suka fara rage sauri.
Amma dukda haka saida suka kai tamanin da tara,
sannan suka tsaya.
Kan kace meye wannan shewa ta ɓarke, tuni har an fara
taya ƴan Infiriya murna.
Kasancewar dama abinda su Armad basu sani ba, shi ne,
mafi girman makin da aka taɓa samu a gasar Jinzidal
ƙarama shi ne casa'in da ɗaya, saboda haka samun
tamanin da tara a wajen Niyashi lallai abin yabo ne.
Ana cikin haka ne Kiru ya isa gaban Alkadar, inda ya ɗaga
takobinsa da niyyar ya caki cikin Alkadar ɗin dashi, amma
a wani salo mai ban mamaki wata murya ta fara magana
acikin kunnensa, wadda kuma shi kaɗai ke iya jinta, duk
da kuwa ba'a hankali take maganar ba!!

Nan take hannunsa ya tsaya cak a sama, abinda yasa ƴan
kallon buɗe baki.
Wannan murya cike da wata irin Izza mai ban mamaki ta
ci gaba da raɗa masa, ''kada kayi amfani da sama da kaso
tamanin na Izzarka!''
Wannan murya na gama faɗa ta ɗauke, inda takobin Kiru
ta ci gaba da tafiya daga inda ta tsaya.
Ta kuma ƙarasa ta daki cikin Alkadar ɗin, lamarinda yasa
wata ƙara tayi sama sannan lambobin suka motsa kuma
basu tsaya ba har saida suka je sittin!!
Shiru kamar mutuwa ta gifta, haka mutane suka kwalalo
masa ido yayinda ya juyo kansa a sunkuye cikin ƴan
tawagarsa.
Kai hatta alƙalin bai iya cewa komai ba har Armad ya
tashi ya isa gaban Alkadar ɗin! Domin babu wanda zaiyi
tunanin ɗan Behanzin guda zai tsaya a sittin kawai.
Armad na isa yasa hannu ya zare takobinsa dake rataye a
kafaɗarsa ta hagu, wato takobin mahaifiyar tasa wadda
tun a farkon fitowarsa daga gida yake tare da ita.
Ya kuma ɗagata sama, inda iya ƙarfinsa ya sari Alkadar
ɗin a ciki!
Wanda hakan na faruwa lambobin nan suka fara
motsawa cikin sauri.
Basu fara rage gudu ba, har saida suka kai sittin da biyar,
inda suka fara juyawa a hankali a hankali har suka isa
tamanin da takwas dai-dai!!!
Inda suka tsaya cak!
Armad ya tsaya kurum yana kallon waɗannan lambobi,
kamar wanda bai yadda da abinda yake gani ba.
"Lamba ta bata kai ta Niyashi da ɗaya ba kenan?" cikin
mamaki Armad ya girgiza kai. Domin ya fuskanci mai
hakan yake nufi. Wato dai dashi da Kiru sun fita kenan,
shi kuma Niyashi yayi nasara.
____
To ko waye yayi wa kiru magana ta kunnensa?
Ko mai zai faru bayanda Armad baiyi nasara ba?
Nidinne dai Shuraih Usman inkiya
99%
Daga taskar magajin wilbafos
MAGAJIN WILBAFOS
Marubuci: Dr Abdullahi Muhammad Ibrahim
Babi na 33: Bayyanar Ururu
Post by: Shuraih Usman
@shuraih 99%
www.facebook.com/hausaebooks
.
Daga:- Taskar Magajin Wilbafos
.
Armad saida ya ware dukkan ƙarfin dake dantsensa
sannan ya afkawa wannan Alkadar da sara. Amma bisa

mamaki gashi akan idonsa yana gani cewa ƙarfin wannan
fasaha bata kai ƙarfin fasahar da Niyashi ma'abocin
mashi yayi amfani da ita ba!
Koda yake Armad kusan yayi tunanin hakan zai iya
faruwa, tunda dukkanin waɗannan samari da yake
karawa dasu yara ne waɗanda suke karɓar kulawa ta
musamman daga manyam ƙabilu.
Wanda ma zaka iya cewa acikin ƙabilunsu anai musu
kallon waɗanda zasu jagoranci ƙabilun ne a gobe.
Saboda haka Armad yayi tunani cewa lallai dukkaninsu
baza suyi amfani da ƙananun fasahohi ba ko kaɗan,
kuma su ɗin ba ababen da Armad zaiyi wasa da su bane!
Musamman duba ga cewa ya rasa Miyurarsa.
Kuma hakan ya ƙara tabbata acikin ransa, a lokacin da
yaga makin da Niyashi ya samu.
Kamar yadda ta gaya masa, amfanin Alkadar ɗin shi ne, a
tantance tsakanin waɗanda suka samu maki ɗaya, wane
ne Izzar da yayi amfani da ita tafi ƙarfi.
Hakan zai iya kawo adalci, domin tunanin cewa wani
lokacin Izzar ka zata fi ƙarfi, amma ka gamu da abokan
gabar da zasu fi na ɗan uwanka.
Saboda haka shi Alkadar abu ne da zai banbance tsakanin
dukkan Izzan da akai amfani dasu domin fitarda wanda
yake gwani na gaskiya acikin wanda suka sami maki iri
ɗaya.
Saboda duk waɗannan abubuwa, duk da tunanin dake
ran Armad ya daure bai ƙara ko kuma canja Izzar tasa ba,
amma kuma bisa takaici gashi makinsa bai kai ba.
Abu na farko daya fara zuwa ransa shi ne, irin imanin da
Nusi tayi cewa shi zai ci, amma gashi ya faɗi. Saboda haka
da wace fuska zai kalle ta ma!! Shi ne kawai tambayar da
yakewa zuciyarsa.
Acikin wannan waje na manyan baƙi kuwa, tun kusan
sanda Uznu ya gayawa sarki Deniz abinda ke tafe dashi,
sarkin ya shiga wani yanayi, bai kuma ƙara cewa komai
ba sai a wannan lokaci, inda ya motsa domin bada
umarnin a kaɗa wasa domin zuwa zagaye na gaba.
Sai dai kuma a wannan lokaci ne, mutumin dake zaune a
gefensa, wato Uznu'Ururu, wanda tunda yazo bai buɗe
idanunsa ba, kai kace dama can a haka aka yisu, ba'a taɓa
buɗe suba. Amma a wannan lokaci ya buɗe idanun nasa!!
Yana buɗewa sarki Deniz duk da ba kallonsa yake ba, yaji
wani gumi ya keto masa, gami da rawar ɗari.
Nan take ya gane maike faruwa!!!
Saboda haka ya fasa abinda yake niyyar yi na bada
umarnin a fara zagaye na gaba. Kawai ya tsaya cak, a inda
yake.
Duk da cewa sarki Deniz shi ya tsayar da kansa yana sane,
amma al'amarin ba haka yake ba, ga ragowar sauran duk
mutanen dake wajen, idan ka ɗauke Asifu, wanda shi ma
ya nutsu, kuma kamar wata ibada ya daina motsi kwatakwata gami da kallon gabansa kamar yadda Deniz Iluru

yayi!
Amma kama daga kan wanda suke hira da Asifu, zuwa
kan dukkanin ragowar mutanen da ke cikin wajen
manyan baƙin, zuwa kan waɗannan samari guda shida da
masu kula dasu, harda su Armad da Nusi.
Zuwa ga dukkanin ƴan kallon dake wajen da dukkanin
waɗanda ke bibiyar abubuwan dake faruwa acikin
wannan fili saida suka shiga cikin wani yanayi mai ban
mamaki.
Abinda kuwa ya faru shi ne, kowa daga cikinsu ya tsaya
cak a dai-dai inda yake, kuma acikin abinda yake yi.
Misali idan ka kalli Armad zaka ganshi a tsaye a gaban
Alkadar ɗin, kuma yana ƙoƙarin juyawa, amma daga
ganin cikin idanunsa kasan akwai wani dalili da yasa baya
son juyawa.
Idan kuma ka kalli Nusi zaka ganta a tsaye cak, hannunta
yana rufe da fuskarta kamar wadda ke ɓoye wani abu.
Wani daga gefenta kuwa magana yake mata a kunnenta
na dama.
Haka dai kowa ka kalla zaka ganshi a ƙame cak baya ko
motsi.
Dukkanin abubuwan dake faruwa, ba wani abu bane ya
jawo su ba, illa buɗe wasu idanu guda biyu rak.
Idan da waɗannan mutanen na cikin hankalinsu da sun
lura da cewa wajen da suke kwatsam ba dalili ya fara yin
duhu. Duk da kuwa ba yamma bace, ba kuma dare bane!
Rana ce tsaka, sannan kuma ga futulu ko'ina a wajen!
Tamkar kawai wani abu ne yake zuƙe dukkanin hasken
wajen baki ɗaya.
Sai dai kash! Da ace wani daga cikin mutanen nan dake
wajen yana cikin wajen manyan baƙin nan, kuma
hankalinsa na jikinsa kamar Deniz Iluru da Asifu, da yaga
cewa haka abin yake!
Wato waɗansu idanu ne guda biyu, dukkanin cikinsu
gaba ɗaya baƙi ne kurum.
Baƙi-ƙirin, babu zancen wani farin ido, babu komai sai
baƙi. Irin baƙin nan da idan ka kalla zakaji tamkar ana jan
ka ciki saboda tsabagen duhu.
To idan da iyakacin abubuwan da suke faruwa kenan to
da da sauƙi, amma ina!
Idan ka kalli waɗannan idanu zaka ga cewa a zahiri
dukkanin hasken wannan waje cikinsu yake shigewa,
tamkar dai wani abu ne acikin idon wanda yake zuƙe
hasken. Ko kuma shi kansa hasken ne da kansa yake ji
cewa bai kamace shiba ya kasance a waje ɗaya da
waɗannan idanuwa guda biyu a waje ɗaya ba, wato yana
ji cewa yayi rashin kyautawa!
Kafin kace meye wannan komai dake wannan waje ya
koma duhu, duhu dun ɗum!
Amma abin mamakin a dai-dai lokacin kuma kowa ya
dawo hayyacinsa, kowa ya ci gaba da abinda da yake yi,
tamkar wani abu bai faru ba.

Amma a wannan lokaci ne kowa ya kula da duhun dake
wajen, wanda da ba haka yake ba!
Kafin kace meye wannan idanun kowa sun koma kan abu
guda ɗaya rak dake da ragowar haske a wajen.
Wannan abu ba komai bane ba illa wannan Alkadar dake
gaban Armad, saboda haka kan kace meye wannan
hankalin kowa ya dawo kansa.
Wani abin mamakin shi ne, akan idon kowa lambar da da
take kan tamanin da takwas ta juya ta dawo tamanin da
tara, wato dai-dai da Niyashi.
Hakan na faruwa waɗannan idanu wanda idan ka kula
zaka ga ba na kowa bane illa, Uznu'Ururu suka rufe ruf.
Wanda tamkar an kawo wuta dukkanin wannan duhun ya
ɗauke ɗif, wajen ya dawo kamar yadda yake a da.
Kuma komai ya ci gaba da yadda yake. Tamkar babu
abinda ya faru.
Amma banda abu ɗaya; wannan kuwa shi ne makin
Armad, wanda ya ƙaru da ɗaya.
Kuma babban abin mamakin shi ne, abinda kowa kawai
yake iya tunawa shi ne Armad ya samu maki ɗaya da
Niyashi.
Hasalima idan ka matsa kusa da jama'a, zaka ji maganar
abinda zai faru a gaba kawai suke; wanda kowa ya riga ya
sani, cewa fafatawa ce gaba da gaba taakanin Armad da
Niyashi, wanda yaci nasara kuma shi ne zaije kewaye na
gaba!
Babu wani abu da zai iya yin bayanin haƙiƙanin abinda ya
afku, wanda yasa dukkanin mutanen dake wajen duk da
sun gani da idanunsu cewa makin nan ƙaruwa yayi da
baya, amma kowa acikinsu, hatta Armad ɗin abinda ke
ransa shi ne ya sami maki iri ɗaya da Niyashi, kuma bisa
ƙa'idar gasar kamar yadda Nusi ta gaya masa abu na
gaba shi ne su biyu su kece raini!
Saboda haka abinda ke ransa kenan kawai. Wato dai a
taƙaice kowa ya manta duk abinda ya faru.
Amma kuma wata tambaya da Deniz Iluru yayiwa
Uznu'Ururu ita ce ta nuna cewa shi ɗin lallai yasan mai ke
faruwa a wajen ba kamar sauran mutanen wajen ba,
''Uznu, mai yasa ka taimake shi?''
Uznu Ururu ya amsa masa da cewa, ''Wancan yaron mai
suna Armad ya nada abinda nake buƙata, amma ina so
na tabbatar kafin nayi wani abu. Kuma lallai indai ya fita
daga gasar a wannan mataki, tabbatarwar zata yi wuya.!
''Saboda haka ina son naga fafatawarsa, domin na
tabbatar da abinda nake tunani!
Shi kuwa Asifu na gefe sun ci gaba da tattaunawa akan
Izza da wannan Badenize, wanda yai matuƙar nutsuwa,
kai a sunkuye yana sauraron wani bayani daga Asifu,
''Deniz Kalhari, girma da faɗin al'amuran Izza sun wuce
yadda kake faɗa!
''kasan kuwa hatta kwakwalwa tana riƙe abubuwan da
suke faruwa na yau da gobe, a mataki-mataki ne kuwa.

''Wanda kuma gaba ɗayan waɗannan matakai sun
ta'allaƙa da Izza ne!
''Misali, zaka iya raba abubuwa zuwa gida uku; na farko
abinda kwakwalwarka zata iya riƙewa, wanda kamar kace
Izzar ka zata iya kusantar wannan abu ne harta iya riƙeshi
acikin kwakwalwarka.
''Na biyu abinda baza ka iya riƙewa ba, wanda wannan
kuma shi yake nuna cewa Izzarka baza ta iya kusantar
wannan abu ba, wanda kuma idan tayi to tarwatsewa
zatai, shi yasa kawai saita haƙura, tayadda kai kuma
bazaka iya taɓa tuna wannan abin ba, har sai sanda
Izzarka takai wannan mataki!!
''Sai kuma mataki na ƙarshe wanda ke tsakatsakiya, wato
zaka tunowa amma rabi da rabi!!''
Asifu yai shiru kamar wanda yake tunani, sai daga ƙarshe
ya ɗago kai ya ƙara duban Deniz Kalhari, ya ce, ''Deniz,
kasan a wanne mataki kake idan aka kwatanta ka da
wancan mutumin dake zaune idonsa a rufe?''
Cikin sauri Deniz Kalhari ya miƙa ido ya hangi
Uznu'Ururu, sannan ya dawo da kansa izuwa Asifu, gami
da cewa, ''nasan yafi ni ƙarfin Izza, amma dole ma a
mataki na farko nake dashi.
''Domin a irin ƙarfin Izza ta, dole komai ƙarfinsa bazai
yimin nisan da zan shiga kashi na uku dashi ba, idan aka
dubi wannan labari naka. Wato dai ina nufin duk abinda
Izzarsa zatai, to inada ƙarfin Izzar da kwakwalwata zata
iya riƙewa!!''
"Hmmm!!!" Asifu yaja wani kwauron numfashi. "Hakane!"
Wannan kawai shi ne abinda Asifu ya bashi amsa dashi
gami da murmushi, sannan ya bayyana masa cewa
tattaunawar su akan Izza tazo ƙarshe a wannan lokaci, sai
dai ko wataranar.
Domin yana so ya kalli ragowar wasannin da zasu
kasance!
Haka Asifu yace, amma a zahiri abu ɗaya ne kawai a
ransa. Yana tunanin cewa wannan Badenize mai suna
Deniz Kalhari bai masan matsayinsa ba a harkar Izza.
Saboda haka babu amfanin yaci gaba da bayani akan Izza
dashi.
Sannan kuma ya maida idanunsa izuwa cikin filin da ake
shirye-shiryen fafatawa tsakanin Armad da Niyashi. Idan
ka lura sosai zaka idanunsa na kan Armad Wilbafos!!!
Babu abinda yake kewayawa acikin ransa sai tunanin mai
yasa Uznu Ururu ya taimaki wannan yaro. Sannan kuma
menene tsakaninsu. Lallai zaiso yaji tsakaninsu da kuma
dalilin da yasa Ururu yake taimakon wani mahaluƙi
wanda ba Ururu ba
Nidinne dai Shuraih Usman inkiya
99%
Daga taskar magajin wilbafos
MAGAJIN WILBAFOS

Marubuci: Dr Abdullahi Muhammad Ibrahim
Babi na 34: Karan Battar Armad da Niyashi
Post by: Shuraih Usman
@shuraih 99%
www.facebook.com/hausaebooks
.
Daga:- Taskar Magajin Wilbafos
.
Note : wannan chapter tayi Kadan sosai, nayi niyyar kada
nasa. Na bari saina Karasa ta. Amma bisa ganin cewa
tadan bada ma'ana a hakan, da kuma cewa karashen
chapter zai iya daukan Dan lokaci.
____
Acikin wannan filin gasa kuwa, tuni aka kammala duk
wasu shirye-shirye da ake buƙata domin fafatawa
tsakanin Armad da Niyashi, a wani salo na tantance
tsakanin aya da tsakuwa.
A kuma ga wanne acikin su zai isa zagaye na kusa dana
ƙarshe.
Dukkanin ƴan kallo, tuni suka fara murna da nishaɗin
ganin mai zai faru, da kuma wa zaiyi nasara.
Kusan kowa, sama da mutun dubu ɗari zaka iya cewa
idonsu akansu yake, a dai-dai wannan lokaci da alƙalin
wasa ya bada umarnin a fara.
Armad na ɓarin arewa, rataye da takobinsa, Shi kuma
Niyashi na tsaye a ɓarin kudu, mashinsa na maƙale acikin
wani abu mai kama da aljihu da aka ɗinka masa na
musamman domin ajiye mashin.
Gashi dai an busa ƙaho, kuma an basu dama su fara
fafatawa, amma har zuwa tsahon daƙiƙa talatin babu
wanda ya motsa acikinsu, kuma babu wanda yace uffan!
Can daga bisani Niyashi yai ajiyar zuciya a wani yanayi
mai kama da tausayawa Armad, ya ce, ''naga kaima kana
daga cikin ƙalilan da a zagaye na farko baka kashe kowa
ba, saboda haka zan baka dama ɗaya ka fita daga cikin
filin nan. Domin kuwa hakan ne kaɗai zaisa ka tsira da
ranka. Na baka daƙiƙa biyar.
Bayan ya gama magana sai kawai yai shiru yana kallon
Armad. Idanunsa cike da mamakin ko mai yasa Armad
bazai yi amfani da wannan dama ba, ya fice daga cikin
wajen.
Kasancewar a dukkanin tunaninsa shi ne, Armad bazai
taɓa iya jure koda ɗaya tak daga cikin azabar hare-haren
jan mashin saba.
Amma ganin Armad yai masa shiru, kuma bashi da niyyar
fita daga filin, yasa ransa ya ɓaci. Nan take ya ce, "bana
son masu girman kai, saboda haka kada ka zargi kowa sai
kanka akan abinda zai biyo bayan girman kanka."
Yana ambata haka ya tafa hannayensa guda biyu inda ya
kira sunan ɗalasimin da yake so yai amfani dashi,
''Sayanósis!!"
Koda wannan ɗalasimi ya fita daga bakin Niyashi sai ya

dunƙule hannunsa na dama ya fara dukan iskar dake
gabansa. A duka na uku ne wata iska mai zafin gaske
tamkar wuta, ta kaɗa a dukkanin ilahirin wannan fili.
Wannan iska tayi kan Armad ganga-ganga tamkar zata
haɗiye shi. Ya ɗaga hannunsa ya ɗan kare fuskarsa,
amma ina, wannan iska ta fara ƙoƙarin kaishi ƙas.
Wani mummunan jiri ya fara ɗibansa yana neman kaishi
ƙas.
Yai taga-taga ya nufi ƙasa, amma a lokacin ne ya dage ya
dasa takobinsa a ƙasa tayadda gwiwowinsa basu je ƙas
ba.
Can daga nesa ya ci gaba da jin Niyashi yana bayani cikin
girman kai da yadda da kai, "kamar yadda kaji, wannan
ɗalasimi sunansa Sayanósis, kuma na ƙabila ta ne kaɗai a
duk faɗin duniya.
"Muna amfani da faɗan hannu da akewa laƙabi da 'fiƙar
zaki' wajen canja iskar da mutun ke shaƙa!
"Mu tsame kason da jiki ke buƙata, tayadda inma ka
shaƙi iskar baza tayi amfani a jikinka ba.
"Ta haka idan babu iskar da jikinka ke buƙata acikin
jininka, fatar jikinka zata fara canjawa izuwa koriya ko
kuma baƙa, kafin daga bisani ka fara jin jiri, kafin ka
suma."
Yana faɗar haka ya juya da niyyar tafiya, yana cewa, "ban
san iyakacin lokacinda zaka iya jurewa ba kafin ka faɗi.
Amma an riga an kammala wannan faɗan, sai dai ka tara
a gaba!!!"
Nidinne dai Shuraih Usman inkiya
99%
Daga taskar magajin wilbafos
Tsakanin kowanne mutun da aljaninsa akwai wata ƴar
rata wadda bata wuce taƙi uku ba. Bayan an haifi
kowanne mutun kafin ya girman baya iya ganin aljaninsa
sai dai kawai wannan ɗan taƙin dake tsakani.
Acikin wannan ɗan taƙin ake ganin fasahar da aljaninka
ke da ita. Yawanci ana fara gani daga shekara biyar zuwa
sama. Sannan kuma bayan mutun ya girma ya mallaki
hankalin kansa, sai kuma ayi ƙoƙarin haɗa shi da wannan
aljani nasa a wani salo mai kama da bautarda wannan
aljani. Tayadda wannan mutun zai iya sarrafa sirrin
wannan aljanin. Wato dai idan aljanin mai sarrafa wuta
ne, shima zai zamo yana iya sarrafa wutar.
Armad tun yana yaro ɗan shekara sha uku, ya fara iya
ganin wannan ɗan taƙi dake tsakanin ruhinsa da
aljaninsa. Kuma yakanga wajen acike da walƙiya da tsawa
da aradu, tamkar ana maka tsawa daga sama. Yana ɗan
shekara tara, kakansa da babarsa da Shugaban
makarantar da yake koyon harkar Izza aciki, suka haɗa
ƙarfi da ƙarfe domin haɗa shi da wannan aljani nasa.
Akai sa'a aljanin ya amince, kuma Armad ya mallake shi.
Tun daga wannan rana Armad ya fara sarrafa tsawa da
walƙiya tamkar shima walƙiyar ce. Idan ka hangi Armad

walƙiya tana rawa a jikinsa da hannunsa kai kace ɗan
aiken mutuwa ne. Lallai mallakar ƙarfin aljanu da sarrafa
fasaharsu abu ne wanda yake ƙara daraja da ƙarfi na
ma'aboci Izza. Kuma abu ne wanda yake sawa sauran
mutane su tsorace shi.
Abinda kawai Armad yake buƙata shi ne yayi duba izuwa
wannan ɗan taƙi dake tsakaninsa da aljaninsa, ya kuma
ɗebo walƙiyar dake wajen wadda aljanin nasa ya tara
masa. Sannan ya aiwatar da fasaharsa.
Armad yakan yi amfani da walƙiyar sa wajen ƙarawa
kansa gudu kamar yadda aka gani a harinsa mai suna
'WASU-WASI', ko kuma yayi amfani da ita kanta walƙiyar
domin kaiwa abokin gabarsa harin Aradu.
____
Armad najin duk abinda Niyashi yake faɗa, kuma
hasalima duk waɗannan bayanai ALLAH ya taimakeshi ba
sababbi bane a wajensa!
Ba dan komai ba, sai dan cewa daga cikin littattafan daya
koya yana yaro akwai mai suna "jiki da Izza" na dafta
Hauwas al-kamaini. Wanda babu abinda babu acikin
abubuwan da ya faɗa, kai harma da ƙari. Sai dai kuma
Armad ba komai yake iya tunowa ba. Amma dai cikin sa'a
ya iya tuno abinda zai iya cetarsa daga cikin wannan hali
da yake.
Armad ya dage yai ƙaraji gami da buɗe idanunsa, inda yai
taga ya dawo ya tsaya cak da ƙafarsa gami da kafa ido
yana kallon Niyashi, wanda ya juyo cikin sauri, fuska cike
da mamaki.
"Eehhhh...." shi ne kawai abinda ya fito daga bakin
Niyashi, sannan ya ƙurawa Armad ido yana kallonsa ciki
da bai, kamar wanda ke ƙoƙarin karanta wani abu acikin
jikin Armad.
Can bayan wasu ƴan daƙiƙu yayi wani murmushi mai
cike da mugunta, gami da cewa, "lallai yaro ba laifi!
"Watohar zaka iya amfani da Izzar dake jikinka, kana rage
yawan iskar da jikinka ke amfani da ita, tayadda duk da
baka shaƙar dai-dai adadin iskar da jikin naka ke buƙata,
zaka iya jurewa tsahon wani lokaci."
Ya girgiza kai gami da cewa, "ban taɓa tunanin kamar kai
zai samu irin wannan ilmi ba, wanda ko a ƙabila ta abu ne
daba kowa ya sani ba.
"Amma duk da haka ina sane cewa wannan hanyace
kawai da zata ƙara maka lokaci, amma a hankali cikin
awanni masu zuwa baza ka iya jurewa ba." Ya ƙara girgiza
kai yana yatsine fuska.
"Sai dai kash, bani da wannan lokaci. Saboda hakan bazan
iya jiranka ba."
Yana faɗar haka ya ja baya gami da canja tsayuwa.
Lamarinda yasa shima Armad wanda ya riga ya dawo daidai, ya canja tsayuwarsa.
Daga can gefe kuma, wannan alƙalin wasa yana kan
wajen gabatarwarsa babu abinda yake sai zuzuta abinda

ke faruwa tsakanin Armad da Niyashi.
Amma yana ganin dukkaninsu sun canja tsayuwa ya saki
baki gami da cewa, "ga dukkan alamu kowa acikinsu ya
maida hankali, bari mu zuba ido, shin yarima Niyashi
daga Infiriya ne zai samu nasara, ko kuma wannan
saurayi da ba'a san ko wanene ba, mai suna Armad Djinn
daga Maikironomada."
Kafin ma ya ƙarasa rufe baki Niyashi ya nufi Armad da
sassarfa.
Idan ka lura da hannunsa na dama zaka ga cewa wani
baƙin haske ne ya bayyana kuma ya keta zagaye hannun.
Yana isa ga Armad wanda har yanzu bai motsa daga inda
yake ba, ya ƙara sauri inda cikin ƙiftawar ido ya kaiwa
Armad Sara da hannunsa mai zagaye da wannan baƙin
haske ta gefen Armad na hagun. Yana mai kiran sunan
wani ɗalasimi, "Kulo-han-Difómiti!"
Sai dai amma a dai-dai wannan lokacin ne Armad ya ɗaga
hannunsa sama, inda wani haske ya fara bayyana yana
kewaye hannun. Nan take wannan hasken ya juye izuwa
walƙiya mai kama da kama da Aradu. Wannan walƙiya ta
rikiɗe izuwa dauƙule-dunƙule har guda uku.
Dukkanin dunƙule ukun juyawa kawai suke akan hannun
saman hannun Armad. Su na ƙaraji suna ƙuwa irin
wadda kake ji yayinda ake ruwan sama. Kai kace zasu ci
babu.
Armad ya cillo ɗaya daga cikin wannan dunƙulallun
walƙiya uku wadda ta taho tana gunji, ta kuma daki baƙin
hasken dake zagaye hannun Niyashi. Wata ƙara mai
kashe kunne ta tashi. Dukkanin ƴan kallon dake wajen
saida suka rufe kunnensu. Kai harda ma idanunsu, domin
kuwa hasken daya tashi saida ya kashe wa kowa ido.
Ƙarfin daya tashi daga wannan walƙiya yai cilli da Niyashi
gefe. Tamkar an cicciɓeshi sama an watsar. Toda yake
shima ba ƙaramin ma'aboci Izza bane, tun kafin ya je
ƙasa yasa jan mashinsa ya tare. Inda ya cake shi akan filin
wasan, lamarinda ya bashi damar miƙewa ba tare da yaje
ƙasa ba. Yai wata katantawa a wani salo na nuna
kwarewa, sannan ya kuma ƙara fuskantar Armad yana
mai nuna shi da mashinsa. Kai da kaga Niyashi zaka san
cewa lallai duk wani wasa ya kau daga idonsa. Kuma lallai
yanzu ne za'a fara fafatawar da gaske.A gefe guda kuwa
shima Armad tasa takobin ya zare a hannunsa na hagu.
Sannan a hannunsa na dama kuma yana riƙe da balabalan walƙiya guda. Waɗanda suke ta kewaya hannun
nasa a wani salo mai ban tsoro.
MAGAJIN WILBAFOS
Marubuci: Dr Abdullahi Muhammad Ibrahim
Babi na 36: karan battar Armad da niyashi part 3
Post by: Shuraih Usman
@shuraih 99%
www.facebook.com/hausaebooks
.

Daga:- Taskar Magajin Wilbafos
.
.
"Ehmm..." Armad yai ajiyar numfashi gami da haɗe rai,
sannan yaci gaba da cewa, "bani da lokacin dazan tsaya
ina wasa dakai anan. Watanni kaɗan ne suka rage min
nayi abinda duk duniya ta kasa, saboda haka ina baka
shawara daka haƙura, ka fitar da kanka daga wannan
gasa."
Tun kafin Armad ya rufe bakinsa wani abu yazo wuyan
Niyashi ya tsaya saboda tsananin baƙin ciki dake dukan
ransa. Lallai babu wanda ya taɓa gaya masa baƙaƙen
maganganu irin waɗannan. A matsayinsa na ɗan sarki,
jikan sarki. Sannan kuma babban abin takaicin ma shi ne,
wanda ke gaya masa wannan baƙaƙen maganganu na
raini Izzarsa bata fi hamsin ba. Bayan shi Niyashi yana da
kusan ɗari.
"Da sannu zaka gane kuskurenka!" Wannan shi ne kawai
abinda ya fito daga bakin yarima Niyashi yayinda
idanuwansa suka kaɗa sukai ja. Baƙin ciki ya cika ruhinsa,
sannan kuma yaji babu abinda zaisa ya ƙara yin dariya a
ban ƙasa idan bai turmuza hancin Armad a ƙas ba. Nan
take yai ƙaraji da ƙuwa, tare da tafa hannayensa a wani
salo na kiran ƙarfin dake cikin Izzarsa.
Nan da nan wata ankwa mai launin ja, wadda akayi ta da
zallar azurfa irin ta mutanen farko ta bayyana a saman
kansa tana lilo akan iska. Wannan doguwar ankwa ta
lanƙwashe izuwa ƙawanya ta kuma kewaye kan Niyashi.
Idan da zaka matsa kusa ka kuma

Please Login or Register in order to submit comment