Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

irin
ta acikin wannan daji ba. Idan zai iya tunawa da kyau shi
kansa Babara saboda an kore shi daga cikin gari ƴasa ya
tsinci kansa a wannan waje.
Bayan da tai gaba sai Armad ya fara binta a baya. Bai san
inda zata je ba amma koba komai zata iya sanin inda
Babara yake. Ba jimawa suka isa bakin wani ƙaton tanti
wanda Armad bai san dashi ba a lokacin daya ziyarci
Babara. Nan take ya laɓe a bayan wani farin dutse
tayadda zai iya hangen abinda ke faruwa a gaban wannan
tanti. Ana haka wannan budurwa daya biyo ta fito daga
cikin tantin amma tare da wata budurwa ita ma sanye da
kaya irin na ma'aikatan asibiti. A hannunsu suna ɗauke da
wata mata sanye doguwar riga. Nan take sukai shimfiɗa
sannan suka kwantar da wannan mata suka farai mata
fifita.
Kallo ɗaya zakai wa matar da suka kwantar kasan tana
cikin ƙoshin lafiya. Abu ɗaya kacal da zai nuna ba'a cikin
hayyacinta take ba shi ne idanunta, wanda suke a rufe
ruf. Amma fatar ta sheƙi kawai take sannan kuma babu
rama a tattare da ita.
Wata ƙwalla ce mai zafi ta fito daga idanun Armad a
lokacin da yaga wannan mace, domin kuwa ba kowa
bace illa mahaifiyarsa. Ba tare da wani tunani ba Armad
ya fito daga bayan wannan dutse ya nufi inda wannan
mata suke. Koda ganinsa sai suka miƙe suka jada baya.
Amma bai kula dasu ba, kurum yaje ya durƙusa a gaban
mahaifiyarsa yana mai kuka da muradin ina ma zatai
masa magana.
Abu na farko daya fara fuskanta shi ne babu alamun
wuya a tattare da ita. Amma kuma dai kamar ƴadda ya
rabu da ita har yanzu tana cikin suma. Yanzu abinda ya
rage masa shi ne ya tursasawa Babara ya bata magani ta
dole. Saboda haka ya juyo ga waɗannan mata guda biyu.
Amma kafin yayi magana ɗaya daga cikin su ta fara
karkarwa tana cewa, "Ma'aikatan asibiti ne mu, babu
abinda ya kawo mu face mu kula da ita. B......babara ne
ya ɗakko mu."
Armad najin sunan Babara hannunsa yakai kan
takobinsa, "Ina Babaran?"
Amma duk su biyun babu wadda ta iya amsa masa.
Karkarwa kawai suke. Ana cikin wannan hali Armad yaji
muryar Babara kamar yadda yasan ta a shekarun baya da
suka gabata.
"Armad Wilbafos! Barka da dawowa, ina fata ka dawo
min da abinda mukai alƙawari?"
Armad yai duba izuwa ƙofar tantin nan inda wani wada
mai yawan farin gashi ya fito. Wannan wada ba wani
bane illa sarkin duba Abul-Babara. Mutumin da shekarun
da suka gabata yayi wa Armad alƙawari zai samarwa
mahaifiyarsa lafiya zarar ya nemo Tarifil-fakta. Sai dai
kuma gashi Armad ya dawo bayan tsahon lokaci amma
ba tare da Tarifl-fakta ba. Koda yake duk da cewa Babara
bai yiwa mahaifiyarsa tasa magani ba yadda Armad yaga
Babaran ya ɗakko ma'aikatan lafiya suna kula da ita yasa
ya ɗan rage zargi dake cikin ransa. Amma hakan bai hana
Armad zare takobi ba tare da tunkarar Babara.
"Zan baka dama ɗaya tak kayi wa mahaifiya ta magani ko
kuma takobi ta tasha jininka."
Babara yai murmushi gami da girgiza kai, "Idan ka kashe
ni waye zaiyi maka bayanin ciwon dake damun
mahaifiyarka kuma waye zai gaya maka labarin ƴar
uwarka Hidaya. Samu waje ka zauna."
Babara ya tafa hannayensa inda wasu kujeru suka
bayyana. Babara ya zauna a ɗaya amma Armad ya tsaya
da takobinsa a hannu, domin ba komai Babara ya gaya
masa zai yadda ba.
"Hidaya kuma?" Armad ya haɗe gira cikin mamaki. Shi
dai dama yana ji a jikinsa yayar tasa na nan da rai. Amma
da kakansa da babarsa sunƙi gaya masa wani abu akanta.
Babara yayi kyaran murya tare da fara jawabi, "Sama da
shekaru dubu da suka wuce ƙungiyar ƴan-duba ta
duniya ta daɗe tana rikici da jinsi daban-daban na aljanu.
Asalin rigimar aljanu ne suka fara zargin ƴan duba da
keta musu haddi su kuma ƴan duba suna zargin aljanu
dayi musu ƙarya. Rigima ce data fara ƙarama amma daga
baya ta zama hamshaƙiya wadda ta halaka dubban ƴan-
duba da aljanu. Shekaru sittin da huɗu da suka wuce
Hidaya ta shiga tsakani ta raba wannan rigima, lamarinda
ya kawo zaman lafiyar da ake dashi a yanzu. A sakamakon
haka a matsayina na shugaban yan duba nayi alƙawari
zan saka mata da sak irin alkhairin datai mana komai
daren daɗewa.
"A wancan lokaci bazan manta ba Hidaya ta bugi ƙirji
tana cewa bata buƙatar komai daga waje na. Amma sai
gashi ko shekara ɗari ba'ai ba yaƙi ya haɗa da ita a
tsakanin aljanu masu biyayya ga Ururu da kuma sauran
sarakunan aljanu. Yaƙi mai tsananin gaske wanda babu
yadda zatai ta iya barin filin daga duk da kuwa
mahifiyarta bata da lafiya, kuma ƙaninta yana buƙatar
taimako.
"Ciwon dake damun mahaifiyarka ana kiransa da Cutar-
Izza. Ciwo ne wanda ake samu a yayinda ma'aboci Izza
yake ƙoƙarin ƙara yawan Izzarsa. Duk wata hanya da ake
amfani da ita wajen ƙara Izza zata iya jawo wannan cuta
amma bansan taƙamaimai wacce hanya ce ta jawo wa
mahaifiyarka wannan cuta ba. Kai sani cewa wannan
ciwo ciwon ajali ne. Duk wanda ya sameshi ƙarshensa
kabari. Kuma wannan ciwo shi ne yasa zaka ga sama da
kaso casa'in da tara na mutane sun gwammace su
haƙura da izzarsu a iya shekarunta, domin ko yaya aka
samu matsala a lokacin da mutun yake ƙoƙarin ƙara
yawan Izzarsa to lallai ƙarshensa kabari. Abu guda ɗaya
tak dake maganin wannan ciwo shi ne idan mutun ya
karɓi shekarun Izza daga wani. Wato a misali ka ɗiba daga
cikin shekarunka na Izza ka ƙarawa wannan mutumi.
"Kai sani cewa kamar yadda ake haifar ƙabilar Ururu da
baiwar Baƙaƙen idanuwa haka ake haifar iyalan Wilbafos
da baiwa ta musamman. Wannan baiwa ita kaɗai ce
abarda zata iya maganin wannan ciwo."
"Wannan baiwa kuwa ba wata bace illa fasahar dake cikin
idanunku. Idanu ruwan ƙasa masu ratsin toka. Duk
wanda yake da irin wannan idanu yana da wannna baiwa,
kuma iyalan wilbafos su kaɗai keda wannan idanu.
"Da wannan idanu zaku iya bayarda izza, za kuma ku iya
karɓa tamkar yadda ake saka kaya a cire. Wannan ita ce
baiwar ka a matsayinka na ɗan ƙabilar wilbafos. Kayi sani
cewa turaka da nayi ka nemo Tarifil-fakta bashi da alaƙa
da ciwon mahaifiyarka. Sai dai kawai na jefi tsuntsu biyu
ne da tsakuwa ɗaya. Kaga tafiyar ka keda wuya na ɗakko
waɗannan ma'aikata da kake gani na sasu su ringa kula
da mahaifiyarka, ni kuma na tafi duniyar aljanu domin
sanarda Hidaya abinda ke faruwa. Nasan duk duniya
babu wanda zai iya yi mata magani sai ita, domin kuwa
kai baka ma san komai ba acikin alamuran Izza a lokacin.
To amma bansan halin da zan tarar da Hidaya ba,
wataƙila ma bata raye, saboda haka kaima na tura ka
duniya domin kaga yadda duniya take, kayi ƙarfi ka zama
ma'aboci Izza tayadda koda ban samu Hidaya ba kaima
zaka iya taimakon mahaifiyarka. Amma nasan baza ka iya
nemo Tarifil-fakta ba. Kada ka manta hatta Ururu sun
kasa nemo shi.
"Sai da na ɗauki shekaru biyu ina bilayin yadda zan shiga
filin yaƙin da Hidaya ke ciki amma ban samu damar shiga
ba, domin kuwa naji aljanu suna cewa hatta mutuwa tayi
hijira daga wannan fili. Wasu aljanun ma suna cewa shi
yasa yaƙin yaƙi ƙarewa saboda babu mutuwar da zata ci
gaba da ɗaukar rai a wajen. Kai daga ƙarshe dakyar na
samu wani tsohon aljani ya shigar dani filin yaƙin. Amma
muna shiga wannan aljani ya rasa ransa. Nima ALLAH ne
ya taimake ni na tsira dakyar amma duk da haka saida
nayi asarar shekarun Izza ɗari biyar kafin na fito daga
wannan fagen-daga. Tun daga nan nasan cewa ganin
Hidaya ba abu ne mai yiwuwa ba. Kuma lallai babu
wanda ƴa rage dazai ceto mahaifiyarka sai dai kai.
Saboda haka na dawo na aiko maka da saƙon daka gani
na wata bakwai.
"Naso na gaya maka haƙiƙanin mai ake ciki acikin saƙon
amma na ƙara baka lokaci naga ko zaka iya farkar da
jininka na wilbafos. Kai sani cewa nayi farin ciki kwanakin
baya da naga hasken farin-wata ya canja kala. Domin
nasan cewa lokaci yayi dazan biya Hidaya bashin da take
bin ƙungiyar ƴan-duba ta duniya.
"Amma fa kai sani wani hanzari ba gudu ba...."
Armad ya katse Babara ta hanyar yin ƙaraji ya zare
takobinsa yana huci, "Wai kana nufin duk wahalar dana
sha ta nemo Tarifil-fakta a banza!!"
Armad bai san lokacin daya kaiwa Babara wani sara ba
cikin ɓacin rai. Babara yai tsalle gefe guda yana
murmushi, "To yanzu da ban tura kaba zaka farkar da
jininka? Kasha wahala, amma yanzu zaka ga amfaninta.
Sannan kuma indai hanyar Izza zaka bi wannan baka ga
komai ba a fannin wahala. Yanzu duniya tasan dakai,
idanun kowa zai dawo kanka. Idan bakai da wuri ba ka
farka lallai yanzu ne zaka san wahala."
Babara yana magana amma Armad kawai huci yake yana
kallonsa a fusace. Bayan ɗan lokaci Babara yaci gaba da
jawabi, "Sai ansha wuya ake samu Izza. Kuma lallai indai
kana so ka zama ma'aboci Izza yanzu ka fara. Saboda
yayarka Hidaya nayi alƙawari zan koya maka yadda zakai
amfani da idanuwanka wanda ita kaɗai ce hanyar da zaka
zama ma'aboci Izza na gaskiya ka iya tsayawa a gaban
Ururu sannan kuma ka ceto mahaifiyarka ta hanyar bata
shekarun Izza. Amma kai sani cewa hatta yayarka Hidaya
wadda hatta a duniyar aljanu ana labarin ƙarfin
kwakwalwarta da gane abubuwanta saida tayi shekaru
uku tana koyar yadda zatai amfani da idanuwanta. Lallai
zaka iya yin shekaru goma kana koya wanda kuma
mahaifiyarka baza takai wannan lokaci ba.
"Naji daɗin ganinka da wannan zoben domin zai taimaka
mana wajen ajiye mahaiyarka aciki." Babara yai nuni da
zoben da Nostaljiya ta bawa Armad.
Babara ya tafa hannunsa tantin dake bayansa ya ɓace,
babu abinda ya rage sai wata ƴar jaka a hannunsa. Ya zira
hannu a jakar ya ɗakko wata leda mai cike da Ayrid ya
jefawa matan nan guda biyu ladan aikinsu. Sannan ya
juyo wajen Armad yana mai cewa, "Zan koya maka yadda
zakai amfani da idanunka dama kuma duk wani abu dana
sani a shekaru na dubu ɗaya da ɗari uku a duniya.
Saboda Hidaya."
Armad yama rasa mai zaice. Kansa yana nema yai tsawa
saboda tsabar caji. Ya za'ai ace abinda yai shekaru yana
nema wai dama duk gwada shi kawai ake. Sannan kuma
babban abin haushin ma shi Babara yana nunawa ba
wani abu bane. Hasalima har ya gama yanke shawara zai
koya wa Armad al'amuran Izza kamar ma babu abinda ya
faru.
Armad ya kasa daurewa, "Zan bika sabida mahaifiyata,
amma idan wannan ma ya zama wani kwajin to lallai sai
na sare kanka." Armad ya buɗe ƙofar wannan zobe ya
killata mahaifiyarsa aciki sannan yabi Babara.
Babara yai dariya, "Kai sani cewa idan na bari
mahaifiyarka ta rasu kona mutu sai Hidaya ta ƙara kashe
ni."
A wannan lokaci hankalin Armad ya dawo kan Hidaya,
inda ya buɗe baki ya tambayi Babara, "Wai kana da
tabbas yayata tana raye? Kakana ya kawo min takobin ta
shekarun baya da suka gabata."
Babara ya kyalkyala dariya yana mai kallon sama tare da
cewa, "Kasan mai suke cewa yayarka a doron ƙasa ta
farko? Hmmm.... Koda yake wasu suna cewa sunan ya
samo asali ne daga jinsin Dordor wasu kuma suna cewa
daga aljanun farko. Amma dai yayarka hatsabibiya ce ta
rubutawa a jarida! Lallai baza ta mutu ta sauƙi ba, kuma
idan ta mutu sai labari ya cika duniya."
Armad ya haɗe gira, "Wanne suna suke gaya mata?"
Babara yai murmushi gami girgiza kai, "Bari ta gaya maka
da kanta idan kun haɗu."
________
Alhamdullh rabbil alamin. Dukkan godiya ta tabbata ga
ALLAH madaukakin sarki daya bani ikon kammala littafin
farko na jerin littattafan Magajin wilbafos. Ina rokon
ALLAH ya ci gaba da bani lafiya da ikon rubuta wannan
littafi har zuwa karshensa.
Godiya ta musamman ga dukkan makaranta Wanda suka
kasance tare dani tun daga farko har zuwa karshe.
Nidinne dai Shuraih Usman inkiya
99%
Daga taskar magajin wilbafos
MAGAJIN WILBAFOS
Marubuci: Dr Abdullahi Muhammad Ibrahim
Babi na 63: Eyriyon
Post by: Shuraih Usman
@shuraih 99%
www.facebook.com/hausaebooks
.
Daga:- Taskar Magajin Wilbafos
_____
***
Shekarar 1841 Bayan Amri, acikin garin Kanyu, Armad ne
ke zaune shida kakansa Zaikid Wilbafos da Mahaifiyarsa
da kuma yayarsa Hidaya a kewaye da teburin cin abinci
suna cin abincin dare. Zaikid dai mutun mai yawan farin
gashi da manyan gaɓɓai, kana ganinsa zaka san duk da
shekaru sunja amma yana nan da jarumtarsa. Hidaya
kuwa tana kama da Armad sosai sai dai cewa ita fara
kamar mahaifiyarsu.
Hidaya ta leƙa ta tagar dake dai-dai saitin ta sannan ta
juyo ta dubi Armad tana cewa, "Kaga kai sauri ka cinye
abincinka ka kwanta dare ya fara yi. Kalli kwanon kowa ya
gama amma banda kai."
Tundai fara cin wannan abincin Armad yake ta cakwala
kuma yaƙi tsayawa yaci abincin. Hasalima da Hidaya tayi
masa magana baima nuna yaji ba, kawai yaci gaba da
abinda yake. Zaikid ya kalli Hidaya, Hidaya ta zare ido da
sauri tana cewa, "Dattijo, bafa ninai girkin nan ba kake
kallo na, abincin Mama ne baiyi daɗi ba shi yasa ƙani na
yaƙi ci."
"Hahaha..." Zaikid ya kyalkyala dariya yana ƙifta ido tare
da satar kallon gefe. "Ƴata Fatima kinji dai me ƴaƴanki
suke cewa! Wai abincinki baiyi daɗi ba!"
Fatima dai irin matan nan ne fara re kyakyawa masu
girman jiki. Sau da dama Zaikid yakan ce shi ta gado a
girman jiki da kuma fari domin kuwa yana bada labari
cewa matarsa, wato babarta, bata da girman jiki kuma
baka ce wankan tarwaɗa kamar Armad. Fatima nada
idanu dara-dara masu cike da ƙaunar ƴaƴanta guda
biyu.
Zaikid na kyalkyala dariya irin ta manyan mutane, Fatima
na ɓata rai tana cewa, "Sa'a ta biyu cir ina wannan kirkin
sannan ace baiyi daɗi ba. Ɗana Armad gayamin maiya
hana ka ci."
Armad yai shiru baice komai ba. Wasa kawai yake da
cokalinsa yana kallon kasa. Hidaya taja kujerarta kusa
dashi ta caka cokalinta akan naman dake kan kwanonsa
sannan ta haɗa da wainar dake kan kwanon ta buɗe
bakin Armad ta danna masa.
"Cinye kaji ƙanina." Hidaya ta shafa tambarin Miyurar
dake ɗamfare a goshin Armad tana mai cewa, "Indai
kacinye gobe kafin na fita zan tashi dakai sama."
"Nhi....fa bha tasshi nakeh so ba....." Armad ya furta
bakinsa cike da abinci.
"To mai kake so?"
Armad ya ɗau lokaci ya haɗiye abincin a hankalin sannan
yace, "Ina Abba?"
Tambaya ce mai sauƙi amma duk ɗakin saida yayi tsit.
Armad bai san mai yasa ba amma mahaifiyarsa da
kakansa basa san zancen baban nasa. Nan take sukai
kyaran murya suka fice daga cikin ɗakin suka bar Armad
da Hidaya.
"Indai ka cinye abincin nayi maka alƙawari yau zan gaya
maka abu biyu ko uku a game da babanmu. Amma sai
kayimin alƙawari baza ka ƙara yin maganarsa a gaban
mama ba."
Tana rufe baki Armad yai tsalle, fuskarsa cike da
murmushi ya amsa wannan alƙawari. Cikin daƙiƙa kaɗan
ya gama cin abincin. Hidaya taja shi suka fita ta bayan
gidan suka zauna a gaban wasu tagwayen bishiyu suna
suna kallon farin wata.
Hidaya taja numfashi ta dubi Armad, wanda ke kallonta,
ta fara da cewa, "Da tuni sunanka Eyriyon, Eyriyon
Wilbafos. Ina tuno sanda Abba yace shi ne sunan da yake
so a sa maka. Amma mama tace sunan baiyi ba, Armad
Wilbafos take so."
"Eyriyon??" Armad ya karkata kai, domin kuwa bai taɓa
jin sunan ba. Hasalima sunan yafi kama dana mutanan
da.
Hidaya tace, "Eh... Amma dai abinda nake so ka riƙe shi
ne Abbanmu yana sonmu sama da komai a duniya. Yama
fi sonka akaina. Sannan kuma yana da rai kuma zaka
ganshi indai muna raye. Armad...." Hidaya ta ɗan ja
numfashi kamar tana kokwanton ta faɗi abinda ke ranta
ko kuwa. Amma dai daga ƙarshe ta yanke shawarar ta
faɗa, "Armad kasan mai ake cewa Zaɓi?"
Armad ya kyaɗa kai, "Eh.. Shi ne kowa a bashi dama yayi
abinda yake so?" Daga jin sautin Armad bashi da tabbas
domin kuwa sautin yafi kama da tambaya a maimakon
amsa. Amma yaci sa'a Hidaya ta kyada kai.
"To mahaifinmu zaiso ace idan ka girma ka zama jarumi
ko kuma wani jagora ko kuma mai yin doka, kada ka
takurawa mutane akan abinda yake ba dole ba, ko kuma
abinda yake ra'ayinka ne kawai. Zaiso ace kowa ka bashi
zaɓi. Ka gane mai nake nufi?"
Armad yai shiru idanunsa cike kokwanto. Lallai kallo ɗaya
zakai masa kasan bai gane mai take nufi ba.
"Hmmmm..." Hidaya taja dogon numfashi, "Ba sai ka
gane yanzu ba, kawai ka riƙe kalmomin kuma ka tuno su
anan gaba koda na mutu. Kaji ƙanina."
Armad ya kyaɗa kai, sannan a lokaci guda fuskarsa ta
canja domin kuwa baya so ko kaɗan yaji yayar tasa tana
zancen mutuwarta, wanda kuma abu ne data saba.
***
Shekarar 1854BA
____
Babara ya ja dogon numfashi gami da tafa hannunsa
akan iska, lamarinda yasa iskar dake wajen ta kaɗa tare
da yin ƙuwwa. Sannan ya juyo ya dubi Armad wanda ke
tafe a gefensa, "Daga yau zaka iya kirana da Bóka, Boka
Babara."
Armad ya haɗe fuska cikin mamaki, "Bóka kuma?"
Babara ya kyaɗa kai, "Boka shi ne sunan da ake kiran duk
wanda yakai muƙamin sarkin duba."
"Ohoo.."
"Kakanka Zaikid yazo watanni kadan bayan ka tafi. Nayi
mamaki da baka tambayeshi ba."
Armad ya cake ƙafa a ƙas tare da tsayawa. "Ina sane
dashi."
Lallai bawai mantawa yayi da Zaikid ba sai dai kawai
daman bai taɓa tsammanin zai dawo ya tarar da kakan
nasa a gida ba. Abu ɗaya daya sani bayan sunyi magana
dashi ta hanyar Ayrid a shekarun baya shi ne lallai Babara
bai isa ya cutar da mahaifiyarsa ba, tunda kakan nasa
zaije ya same shi.
Armad ya ɗanyi shiru an ci gaba da tafiya sai kwatsam yai
zumbur kamar ya tuno da wani abu, "To mai yasa shi ɗan
tsohon baiyi mata maganin da kansa ba. Ai shima
Wilbafos ne, kuma indai ni ko Hidaya zamu iya shima ya
kamata ace ya iya."
Babara yaja dogon numfashi, "To kai a tunaninka waye ya
koyamin yadda zaka iya sarrafa idanunka. Nima ban san
mai yasa yaƙi yi mata maganin ba, amma dai ya bar saƙo
na baka sannan kuma ya ce na tambaye ka mai kake so
ka cimma a rayuwarka bayan samarwa mahaifiyarka
lafiya?"
Armad yai shiru yana tunani naɗan lokaci kafin daga
bisani ya kyaɗai yayi magana ƙasa-ƙasa, "Daman nasan
ɗan tsohon nan zaiyi abinda yafi haka ma."
"Me kace?" Babara baiji mai Armad yace ba.
Armad ya kyaɗa kai, "Ba komai!Babban abinda nasa a
gaba bayan samarwa mahaifiyata lafiya shi ne hana
cinikin bayi. Kuma ina mai rantsuwa da mahaliccin ƙasa
bakwai, saina hana cinikin bayi a doron ƙasa kafin na
daina numfashi."
"Hmmmm....." Boka Babara yaja dogon numfashi gami
da kyaɗa kai. "Ruwa baya tsami banza. Jini kuma baya
ƙarya. Da bakai haka ba da ba'ace kai jikan Wilbafos
bane. Bari na tambaye ka, shin ka taɓa tunanin mai yasa
mahaifiyarka ta hanaka gayawa mutane sunanka na
wilbafos?"
Armad ya girgiza, "Na sha yin tunani akai amma har
yanzu bansan mai yasa ba."
Babara yayi murmushi, "Ga dukkan alamu ƴan uwanka
basa son gaya maka tarihinka. Amma kada ka damu yau
zan gaya maka mai yasa akan hanyar mu kafin mu ƙarasa
wajen da zaka fara karɓar horo."
______
Ku saurari chapter gobe. Sannan kuma ina buƙatar wasu
daga cikinku su rinƙa yin comment a ɗaya group da nake
sharing littafin domin sauran mutane sufi gani.

Nidinne dai Shuraih Usman inkiya
99%
Daga taskar magajin wilbafos
MAGAJIN WILBAFOS
Marubuci: Dr Abdullahi Muhammad Ibrahim
Babi na 64: Magajin wilbafos na farko
Post by: Shuraih Usman
@shuraih 99%
www.facebook.com/hausaebooks
.
Daga:- Taskar Magajin Wilbafos
____
Babara yai kyaran murya ya fara bawa Armad kaɗan daga
cikin tsohon tarihin ƙasa bakwai, "Yau muna shekarar
1854 Bayan Amri(BA), kamar yadda ka sani Amri kalmar
yaren Aldurish ce wadda take nufin saukar da mutane
zuwa ƙasashen ƙasa. Al'ummar ƙasa bakwai suna da ilmi
akan abubuwan da suka afku acikin wannan shekaru
dubu ɗaya da tamanin na bayan Amri, amma kaɗan ne
daga cikinsu suke da masaniya akan al'amuran da suka
afku kafin Amri. Ni Boka Babara ina daga cikin waɗanda
suka san kaɗan daga abubuwan da suka faru a wancan
zamani domin kuwa an haifeni a shekarar 27 kafin Amri
(KA). Wanda idan ka haɗa zaka ga shekaru na a yanzu sun
kama 1881 da haihuwa.
"Lokacin da aka haifeni lokaci ne mafi tsanani a tarihin
ɗan adam. Lokaci ne na yaƙi, lokaci ne wanda ba'a taɓa
samun irinsa ba a tarihi. Mahaifiya ta tana haifata aka
biyo ta za'a kashe ta, kuma saboda ta ceci ni ta salwantar
da rayuwarta ta hanyar bani dukkan ragowar shekarunta
na Izza. Babana dama ya daɗe da mutuwa a filin daga.
Babu kowa babu wanda na sani haka na rayu saboda
shekarun Izza da mahaifiya ta barmin. Shin kasan
menene ya jawo wannan yaƙi?"
Armad ya girgiza kai, "A'a."
Boka Babara yaci gaba da bayani, "Doron ƙasa ta farko ya
kasanse bashi da sashin Ikwatora, amma a maimakonsa
wani katafaren ruwa ne wanda ya raba ƙasar gida biyu.
Wannan ruwa shi ake kira da Ruwan maliya. A shekarar
9541KA anyi wani sarki mai suna Aldaima Wilbafos
wanda akafi sani da Wilbafos na farko. Aldaima shi ne
mutun na farko daya taɓa mulkar dukkan doron ƙasa ta
farko ɓangaren gabas da ruwan maliya, kuma ya haɗa
kan dukkan ƙabilu a tafarki ɗaya. Aldaima ya rayu tsahon
shekaru dubu shida zuwa shekarar 4033KA, inda bayan
ya mutu ƙaninsa mai suna Eyriyon Wilbafos ya haye
karaga kasancewar Aldaima bashi da ɗa. Eyriyon Wilbafos
ya zama Wilbafos na biyu. Nima ba'a haifeni ba a lokacin
kuma lallai bansan haƙiƙanin taƙamaimai mai ya faru ba,
amma nasan cewa Ururu ƙabila ce wadda tafi kowacce
girma a ɓangaren yamma da ruwan maliya. Kuma
sarkinsu, Kuyurussa'ayi Ururu da ɗansa Dumaƙisu
Dul'ururu Kuyurussa'ayi sune halitta ta farko da suka
taɓa haye ruwan maliya suka shigo sashin gabas da
ruwan maliya a shekarar 945KA. Wanda idan ka lissafa
zaka ga bayan Eyriyon Wilbafos yayi shekaru sama da
dubu uku kenan yana mulki. Kuma abin mamaki shima
Eyriyon bai sami haihuwa ba har zuwa wannan lokaci.
"Naji labari mutanen gabas da ruwan maliya basu karɓi
Ururu ba, musamman saboda baƙaƙen idanuwansu,
amma daga baya sarki Eyriyon yai magana aka daina
kyamarsu. Shekaru ɗari biyar bayan Sarki Ururu ya
bayyana a ƙasar gabas saiya fara kira izuwa tafarkin
rukunai biyu. Wanda sune dai rukunan daka sani wanda
ɗaya shi ne na Jinzidal, ɗaya kuma na Amri. A wancan
lokaci ana kiransu da 'Amri da Jinzidal'. Bansan maiya
biyo baya ba, amma dai nasan sarki Eyriyon ya nemi
Ururu da su daina wannan tafarki ko kuma su koma inda
suka fito.
"Ururu sukai kunnen uwar shegu da wannan kashedi na
sarki Eyriyon Wilbafos. Shekaru kaɗan bayan sunƙi sai
Eyriyon ya kira kwamandojinsa guda ɗari dake ban ƙasa
izuwa yaƙi da Ururu. Yaƙin da aka shafe shekaru ɗari uku
ana yinsa. Yaƙin da yai sanadiyyar asarar sama da rayuka
miliyan dubu a ban ƙasa. Bazan taɓa mantawa ba ina ɗan
shekara ashirin da biyar saida takai duk wata ƙasa ta juye
izuwa launin ja launin jini saboda tsabagen jini dake
kwaranya.
"Sarki Eyriyon kafin fara wannan yaƙi ya bar wasiyya a
cikin wani sihirtacce littafi wanda akace ya juye izuwa
takobi. Sannan ya aiki ɗaya daga cikin kwamandunsa da
wannan littafi/takobi.
"Wannan yaƙi dai kamar yadda ka sani Ururu ne sukai
nasara kuma a sakamakon haka rukunai biyu wato Amri
da Jinzidal suka kasance. Ina tunano lokacinda sarki
Ururu ya kira wani ɗalasimi wanda yasa dukkan wani
biladama wanda bashi da baƙin ido bacci. Wanda bayan
mun tashi daga wannan bacci muka tsinci kanmu acikin
duniyoyi shida na ƙasa. Shekaru kaɗan bayan munzo
sarki Ururu ya aike da ruduna wanda suka zo suna
binciken wannan kwamanda da sarki Eyriyon ya aiko.
Naji daga baya cewa suna neman wani abu ne da Eyriyon
ya bari mai suna Littafin-takobi. Amma dai ga dukkan
alamu har yanzu basu samu wannan abu ba, domin kuwa
har yanzu akwai tsofaffin ƙungiyoyi dake neman wannan
abu mai suna Littafin-takobi. Wannan shi ne kaɗan daga
cikin tarihin duniyar ƙasa bakwai."
Boka Babara ya daki ƙasa da sandarsa inda ƙoƙon ruwan
ya bayyana. Ya kwankwaɗi ruwan sannan ya juyo ya dubi
Armad wanda ke tsaye yana mamakin wannan tsohon
tarihi da yaji. Ko a mafarki bai taɓa tunanin ƙabilarsa ta
Wilbafos takai haka tsufa ba. Sannan kuma ga zancen
Littafin-takobi, sai a yanzu ya gane dalilin da yasa Uznu
Ururu yake matuƙar neman wannan littafi. Kuma Armad
ya gano cewa indai har da gaske littafin ya narke a cikin
jininsa to kuwa lalle bazai taɓa bawa kowa shi ba har sai
yasan meye aciki. Armad ya tuna da zancen ɓacewar
Miyurarsa wanda abu ne wanda har a wannan lokaci bai
daina damunsa ba. Lallai ko a iya haka Littafin-takobi ya
janyo masa masifu da dama kuma babu yadda za'ai ya
rabu dashi ba tare da yaga abinda ke ciki ba.
Muryar Boka Babara ita ce ta katse masa tunaninsa inda
ya juyo ya kwashe duk labarin daya faru dashi akan
Littafin-takobi ya gayawa Babara. Lalabarin da yasa
Babara ya daɗe yana tunani wanda har suka iso inda zasu
fara horon baice komai.
Daga bisani Babara ya juyo izuwa Armad da murmushi
yana mai cewa, "Ga dukkan alamu jininka na Wilbafos ba
ƙarami bane. Amma lokaci ne kawai zai nuna, domin
kuwa ba kai kaɗai ne jinin Wilbafos ba. Idan baka da wata
tambaya zamu fara bayanin horo."
Armad ya dubi Babara fuskarsa ɗauke da murmushin
fahimta yana cewa, "wato idan na fuskanta a shekarun
baya daka tambaye ni suna na tuni dama ka riga ka sani
saboda kasan yayata Hidaya. To amma mai yasa ka turani
nemo Tarifil-fakta indai burinka kawai na koyi horo ne? Ai
akwai hanyoyi da dama wanda zan samu horo wanda
basu kai wannan hatsari ba. Mai yasa?"
Babara ya ƙara yin murmushi, "lallai kana da zurfin
tunani. Wannan haka yake, akwai hanyoyi da dama
wanda da naso da ban tura ka nemo Tarifil-fakta ba, to
amma kada ka manta nasan cewa da Hidaya da
Mahaifiyarka Fatima da kakanka Zaikid suna daga cikin
wanda suka yadda Tarifil-fakta shi ne kaɗai mutumin da
yasan yadda za'a sarrafa Littafin-takobi. Na tabbata wani
daga cikinsu ya taɓa yi maka zancen neman Tarifil-fakta."
Nan take Armad ya tuno da abinda mahaifiyarsa ta gaya
masa akan neman Tarifil-fakta. Komai yanzu ya fara yi wa
Armad ma'ana. Babara yasan iyalan gidan Armad sosai:
yasan Fatima Wilbafos tana neman Tarifil-fakta kuma
yasan neman da take masa yana alaƙa da Littafin-takobi,
sannan kuma yasan Hidaya. Hakan nema yasa ya tura
Armad nemo Tarifil-fakta.
Babara ya daga ɗan-yatsa,
"Amma dai duk da haka kada ka gayawa Hidaya halin
daka shiga a yayin neman Tarifil-fakta, koba komai kaga
ai yayi maka amfani ka samo Littafin-takobi. Ina roƙonka
da koda na mutu kada ka gaya mata."
Armad ya gwale ido cikin mamaki, "Koda ka mutu?"
Babara ya girgiza kai,

Please Login or Register in order to submit comment