Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

daga wannan kwanuka
suka kalleta, "Idan kun gama akwai tafki na wanka mai
cike da ruwan zafi. Kuyangi suna ciki suna jira suyi muku
wanka."
Cokali ne ya ƙara yin magana da ƴar kumburarriyar
fuskarsa cike miya caɓo-caɓo. Lallai kallo ɗaya zakai
masa ka fashe da dariya. "Wanka???!!! Iliyasis yaushe
rabonka da wanka."
Iliyasis ya harari Cokali, "Kai yaushe rabonka? Nusi ce
kaɗai tayi a wannan satin, har gwanda nima nayi wancan
satin. Kaifa?"
Duk su ukun suka fashe da dariya. Ko a mafarki basu taɓa
tunanin samun irin wannan daula ba, kuma lallai basu da
niyyar yin tunanin daga ina wannan daula take har sai
sunyi hani'an. Haka kuwa akai, kwata-kwata basu fara
tunanin matsaloli ba sai washegari bayan sun tashi daga
baccin awa ashirin da sukai akan wani katafaren gado na
alfarma. Duk su uku acikin fararen kaya irin na bacci.
Iliyasis ne ya fara tashi, sannan Nusi.
Su biyun suka kalli ƙasaita ta cikin wannan ɗaki sannan
suka kalli junansu cikin damuwa. Iliyasis ya numfasa ya
ce, "ba dai abinda nake tunani kike tunani ba?"
Nusi ta kyaɗa kai, lallai duk abu ɗaya suke tunani. Waye
ya kawo su nan? Kuma maiya faru dasu Ɗan-darbejiya?
Ina ne wannan gida da suka tsinci kansu?
Ba jimawa suka tashi Cokali, fuskarsa cike da yawun bacci
suka labarta masa cewa akwai matsala. Abu kamar wasa
Cokali ya buɗe baki ya ce, "amma dai ba'a gidan yankan
kai muke ba ko? Ba siyar damu akai ba? Ina ne nan?"
Ba jimawa tsoro ya cika su duk su ukun, inda kafin kace
meye wannan tuni sun cure a ƙarshen gadon suna leƙe-
leƙe. Kafin wani lokaci tuni sun fara lissafe-lissafen yadda
zasu tsere daga wannan gida. Suna cikin haka sai suka ji
an buɗe ƙofar ɗakin. Suna tsammanin suga wannan farar
kuyanga sai suka ga wani farin saurayi mai yawan gashi.
Lallai tsayin gashinsa ya haura na mata da yawa a wannan
zamani, domin kuwa yakai har gadon bayansa. Sai dai
abin mamakin gashin nasa launin ja ne, jajawur. Yana
sanye da baƙar alkyabba. Yana shigowa ya nemi waje ya
zauna, sannan yayi murmushi a garesu.
Duk su ukun suka ƙame a waje ɗaya, ko numfashi basa
iya yi sosai ballantana magana.
Saurayin ya fara magana cikin lafazi mai ɗauke da
tsantsar Izza da kamala, "suna na Yarima Niyashi. Ni ne
na ceto ku daga waɗancan mutane dake neman halaka
ku. Sannan kuma ni ne na kawo ku wannan gida."
"Y....yarima Niyashi?? Kai.... ne Yarima Niyashi?" Iliyasis ya
fara magana cikin ƙinƙina, domin kuwa indai abinda yake
tunani haka ne to kuwa lallai suna ganawa da ɗaya daga
cikin waɗanda ake yiwa kallon su zasu iya mulkar duniya
anan gaba. A duk faɗin ƙasa bakwai mutun ɗaya ne mai
suna Yarima Niyashi wanda keda irin wannan jan gashin,
saboda haka Iliyasis bai ɓata lokaci ba ya dubi wannan
saurayi ya ce, "Yarima Niyashi, ɗan sarkin Jinzidal, Rafiya,
na daular Infiriya?"
Saurayin yayi murmushi, tare da kyaɗa kai. Alamun haka
ne.
Cokali ya ja rigar Iliyasis cikin tsoro, "Wane ne? Kasan
shi?"
Iliyasis bai kula da Cokali ba ya ci gaba da magana, "to
amma mai kake yi a daular Maikironomada? Na tabbatar
duk wanda ya ganka anan cewa zaiyi leken asiri kazo."
Wannan saurayi ya ɗan numfasa tare da juyawa ya kalli
Nusi wadda tai shiru tana tunane-tunane, ga dukkan
alamu ita ma ta gane wane ne wanna saurayin.
Kafin daga bisani saurayin yayi mata magana, "Tsahon
lokaci ina nemanki, Nusi Djinn."
***
2)Yaku ma'abota karatun littattafan Hausa ga wata dama
ta samu. Wepsite din Hausaebooks
wanda zai ringa kawo maku littatafan hausa a cikin apk
na ebook ya kuma baku daman downloading zuwa kan
wayoyinku kyauta batare da sisin ku ba Zaku samu
sabbin littafai wanda babu su a kasuwa. Muna muku
barka da zuwa.
Yi hanzari ku ziyacemu
A shafin mu na facebook akan
www.facebook.com/hausaebooks
Nidinne dai Shuraih Usman inkiya
99%
Daga taskar magajin wilbafos
MAGAJIN WILBAFOS
Marubuci: Dr Abdullahi Muhammad Ibrahim
Babi na 70 & 71: Cokali da ilyasis sun shiga Duniya
Post by: Shuraih Usman
@shuraih 99%
www.facebook.com/hausaebooks
.
Daga:- Taskar Magajin Wilbafos
-------
Nusi ta ƙara jada baya cikin tsoro, inda ta ɓoye a bayan
ƙibar Cokali. A wannan rana ta gane cewa hatta ƙibar
Cokali nada ranarta. A ranta tama kasa gane maike
faruwa. Ta yaya za'ace wai ɗan sarkin babbar daular
Infiriya yana nemanta? Wai tayaya ma akai ya santa?
Dududu shekarunta shida kacal a duniya, kuma acikin
waɗannan shekaru bata taɓa yin inda hanyar daular
Infiriya take ba, ballantana ace ta gamu da ɗan sarkin
dake mulkin wannan daula, harma ace wai yana
nemanta. Lallai koma wanne laifi ta aikata yana da
girman gaske, tunda har za'ace ɗan ɗaya daga cikin
sarakuna biyar na Jinzidal ya taso ƙafa-da-ƙafa yana
nemanta.
"Kada kiji tsoro." Muryar yarima Niyashi ta shiga
kunnenta tamkar ana busa algaita. "Banzo danna cuce
kiba. Nazo ne danna taimake ki. Amma kiyi sani cewa a
halin yanzu bani da ikon gaya miki tayadda akai na sanki
ko kuma mai yasa nake nemanki, duk da kuwa nasan
wannan tambayoyi sune suke yawo akanki. A halin yanzu
wannan gida da muke ciki naki ne halak-malak. Bama
gidan ba kaɗai, tare da duk abinda ke cikinsa. Sannan
kuma akwai kuɗin Ayrid kimanin miliyan ɗaya dana bari
wanda zaku yi amfani dashi zuwa sanda zan dawo. Na bar
umarni mutanen cikin wannan gida zasu yi muku shaidar
zama cikakkun ƴan garin nan kuma zasu saka ku a
makarantar koyon Izza. Akwai mutanen mu wanda zasu
kula dake har zuwa sanda zan dawo."
Koda yarima Niyashi yazo nan a zancensa sai ya miƙe ya
gabato izuwa gaban wannan gado dai-dai inda Nusi
maƙale a bayan Cokali tayi kalar tausayi. Koda ganin haka
sai Iliyasis yai tsalle ya dira a gabanta, wato ya shiga
tsakaninta dashi.
Iliyasis yai ta maza ya buɗe baki ya ce, "Bazan bari kayiwa
ƙanwata wani abu ba indai inada rai."
Abin mamaki saiga Cokali shima yai tsalle ya dira a gefen
Iliyasis, inda gadon yai wata ƙara ƴana neman ɓallewa
saboda nauyi. Hannun Cokali na karkarwa, ƙaton cikinsa
na sama da ƙasa saboda tsabagen nishi, yana ƙinƙina
yana cewa, "ni....ma... b...bazan bari k...ka taɓa taba.
Kwandama ka tafi ko kuma ka tafi." Koda Cokali yazo nan
a zancensa amma Niyashi bai tsaya, sai nan take
haƙoransa suka fara karkarwa tamkar wanda aka tsoma
acikin dusar ƙanƙara.
"Baza ka tsaya!!!" Cokali ya kwala ƙara mai kama da kuka.
Amma Niyashi yai kamar baiji shi ba yaci gaba da tafiya.
Yana ƙarasowa saitin Cokali ya tsaya, inda ya juyo da
kansa ya kalli Cokali. Abun mamaki suna yin ido-da-ido
Cokali ya faɗi ƙasa sumamme saboda tsananin tsoro.
Sannan ya tafi gadan-gadan zai faɗa ƙasan gadon. Haka
na faruwa Niyashi yai sauri ya taroshi tare da fashewa da
dariya. Yana cewa, "Haha... lallai Nusi kina da wanda zasu
kare ki ba saina damuba." Yana rufe baki ya shafa fuskar
Cokali ya farfaɗo dashi ta hanyar ɗalasimai. Sannan ya
juya ya fice daga ɗakin yana dariya.
---------
Tun daga wannan rana basu ƙara ganin Niyashi ba, tun
suna tsoron wannan ƙaton gida har suka saki jiki. Duk
abinda suke buƙata akwai aciki, sannan idan zasu fita
akwai bayi jarumai dake kula dasu. Ba daɗewa suka zama
tamkar wasu ƴaƴan attajirai a wannan gari na Khan.
Suka shiga babbar makarantar Izza dake wannan gari na
Khan.
Abu kamar wasa suna jira Niyashi yazo amma baizo,
bashi ba alamunsa. Rani yazo, kaka tazo, bazara tazo, akai
hunturu sannan damuna ta kewayo. Sannu a hankali har
sunyi shekara ɗaya a wannan gida. Abin mamaki duk su
uku tamkar an haɗa baki suka zamanto masu matuƙar
ƙoƙari a makaranta. Sannu a hankali a kwana a tashi wata
shekarar ta wuce. Iliyasis ya zaɓi ɓangaren takobi a
makaranta, shi kuma Cokali ya zaɓi ɓangaren aljanu da
zanunnuka. Nusi kuwa ta zaɓi ɓangaren Izza da dabarun
yaƙi na daular Maikironomada.
Sannu a hankali a wannan hali saida sukai shekaru tara
cif, harma sun fara mantawa da labarin Niyashi. Ranar
nan kwatsam sun dawo daga makaranta su uku sai
babbar hadima mai yi musu hidima a gidan tace musu
suna da baƙo idan sun shirya.
Dukkaninsu sukai tunanin bazai wuce ɗaya daga cikin
masu zuwa gida yanai musu karatu ba, saboda haka ko a
jikinsu. Suka shige izuwa sashinsu sukai wanka suka
kimtsa a hankali sannan can yamma suka bayyana a falon
gidan.
Nusi na sanye da doguwar riga samfurin daular
Maikironomada mai ɗauke da bezar gashin zaki. Babu
abinda take sai sheƙi. Kyawunta ya bayyana matuƙa a
wannan lokaci, domin kuwa tuni Nusi ta cika ƴar shekara
sha biyar da haihuwa a duniya. Ga dogon gashinta yana
kwanciya akan kyakkyawar fuskarta mai ɗan duhu.
Cokali ya ɗan rage ƙiba, amma duk da haka yana da
tumbi da kuma da manyan gaɓɓai. Shi kuwa Iliyasis
kamalarsa da nutsuwa ta ƙaru. Yana rataye da takobinsa
launin ja.
Abinda suka gani basu yi tsammani ba, domin kuwa ba
kowa bane a zaune acikin wannan falo ba illa yarima
Niyashi. Hannunsa ɗauke da jaridar kamfanin Maikiro ta
wannan sati.
Dukkaninsu suka gabato izuwa gareshi fuskokinsu cike da
damuwa, duk da kuwa babu sauran tsoro a tattare dasu.
Abu ɗaya da suka sani shi ne idan da Niyashi yaso halaka
su da tuni hakan ya ɗaru tun shekaru tara da suka wuce.
Yana ganinsu ya miƙe fuska cike da murmushi yana
cewa, "Ahh.. duk kun girma. Nusi... dube ki har kin kamo
ni tsayi. Cokali kaima....."
Amma a dai-dai wannan lokaci da Niyashi ya ajiye jaridar
data rufe masa fuska suka ga fuskarsa sosai sukai tiris
suka cake a inda suke, baki a buɗe. Niyashi yana nan dai-
dai da dai-dai yadda suka ganshi shekaru tara da suka
wuce. Da daida girma ko kuma canji na kwayar zarra
babu a fuskarsa. Hasalima sai kace sa'ansu ne koma sun
girme shi. Musamman ma Iliyasis da yake da kamannin
manya lallai zaka ce ya girmi Niyashi.
"W...ane ne kai? Maike faruwa?"
Wannan kawai shi ne abinda duk su ukun suka buɗe baki
suka cewa Niyashi cikin mamaki da ɗimuwa.
Amma Niyashi yai murmushi tamkar ba wani abu ya ce,
"kada ku damu, sannu a hankali zan baku labari na.
Amma ba yanzu ba. Kamar dai yadda kuka gani bana
tsufa kuma shekaruna sun tsaya cak tun daga ranar da na
cika shekara sha shida a duniya. Babu wanda yasan
wannan labari daga ƴan gida na saiku. Kuma abinda ya
kawo ni nan a wannan lokaci shi ne ina so kuyimin
alƙawari cewa baza ku gayawa kowa ba. Baza ku gayawa
kowa kun sanni ba, sannan kuma baza ku gayawa kowa
wannan labari nawa na rashin tsufa ba. Idan kukai min
wannan alƙawari to ni kuma zanyi muku alƙawarin
taimakon ku a duk lokacin da kuke buƙatar taimako,
sannan kuma zanyi muku bayanin komai akan dalilin da
yasa nake neman Nusi da kuma dalilin da yasa bana tsufa
idan lokaci yayi."
Duk su ukun suka kalli juna suna mamaki wannan abu.
Iliyasis ne ya fara magana, "To mai yasa bazaka gaya
mana yanzu ba?"
Niyashi ya amsa yana murmushi, "Saboda bazan iya ba."
Nusi ta tari numfashinsa tace, "Zanyi alƙawari, amma
idan kayadda cewa zaka amsa min tambaya ɗaya."
Niyashi ya ce, "Wacce tambaya ce?"
Nusi tace, "Ka gayamin, shin kasan mahaifina?"
Niyashi yaja dogon nimfashi tare da sunkuyar dakai, baya
so ya amsa wannan tambaya, amma ga dukkan alamu
Nusi ta daɗe tana so tayi masa wannan tambaya, kuma
baza ta amince da wannan alƙawari nasa ba idan bai
amsa mata ba, saboda haka a ƙarshe ya buɗe baki yace,
"Nasan shi. Amma bazan gaya miki komai akansa ba
yanzu."
-------
To daga wannan rana Nusi da Cokali da Iliyasis da Niyashi
suka ɗaura wannan alƙawari. Niyashi ya daɗe acikin
wannan gida suna tare a wannan karan, amma bayan ɗan
ƙokaci ya ƙara tafiya ya koma daular Infiriya. Kuma tun
daga wannan rana har zuwa sanda Nusi ta zama ɗaya
daga cikin manyan ɗalibai masu hazaƙa a daular
Maikironomada basu ƙara haɗuwa da Niyashi.
Nusi tana ƴar shekaru sha tara ta shiga takarar jarabawar
da zata bata dama ta zamo ɗaya daga cikin waɗanda za'a
ɗaukaka matsayinsu a daular Maikironomada. Jarabawar
da ta kaita inda suka haɗu da Armad a shekarun baya.
Jarabawar da ta canja rayuwarta har abada.
Nusi bata ƙara ganin yarima Niyashi ba sai a gasar
Jinzidal. Tayi mamaki sanda ta ganshi yana nan dai-dai
yadda ta sanshi shekaru goma sha da duka wuce. Kuma
taso su gana dashi amma Niyashin bai amince ba. A
cewarsa akwai kunnuwa a binne a ƙarƙashin ƙasa, da
kuma idanu a kafe a sararin samaniya wanda baya so suji
ko kuma su ganshi tare da ita.
---------
Iliyasis na tsaye rataye da takobinsa yana kallon ƙaton
mutun-mutumi na Al-yaya a bakin ƙofar garin Khan. A
gefensa Cokali ne tsaye shima yana kallon wannan
mutun-mutumin. Abin mamaki basu kaɗai ne tsaye suna
kallon wannan mutun-mutumi ba. Mutane sama da ɗari
biyar kallonsa kawai suke suna kuma kallon jaridun dake
hannunsu. Babu abinda kake ji sai hayaniya. Wataƙila ace
ba abin mamaki bane aga mutane suna kallon wannan
mutun-mutumi ba, tunda sama da shekara ɗari mutun-
mitumin gida shida ne a ƙofar garin na Khan, amma ƴan
watannin baya kaɗan na bakwai ya ƙaru. Lallai maza da
mata zasu so suje suga wannan sabon mutun-mutumi da
ake cewa na wani kyakkyawan saurayi ne.
Sai dai kuma abin aljabin shi ne wannan sabon mutun-
mutumi yana tsaye ɗaure a kansa da ɗan kyalle. A saman
hannunsa na dama walƙiƴa ce take ta ci tana balbali. A
hannunsa na hagu kuwa takobi ce tsirara. Idanun
wannan saurayi sunyi kama dana jakadun mutuwar ƙarni
na farko. Gashin kansa baƙi ne, wani a kwance wani a
tsaye. Idan ka matsa kusa zaka gane cewa wannan yaro
ba wani bane illa Armad Wilbafos. Kuma shi ne acikin
shafin wannan jarida da mutane suke ta kallo suna
hayaniya. A saman wannan hoto nasa ga kuɗi nan ansa
har Ayrid sama da miliyan.
Iliyasis ya dubi Cokali ya ce, "Lallai Ururu sunji labarin
wannan mutun-mutumi shi yasa suka zabga wannan kuɗi
akan Armad. Amma dai a halin yanzu ya zama dole mu
nemeshi a duk inda yake, domin kuwa shi kaɗai ne zai iya
gaya mana taƙamaimai inda ƴar uwarmu Nusi take.
Amma na yarda da shawararka, mu fara zuwa daular
Infiriya mu tuntuɓi yarima Niyashi muji ko yasan inda
take."
Cokali ya kyaɗa kai, "To mai muke jira, mu ɗau hanya
kawai. Mu da dawowa wannan gari sai sanda muka ganta,
ko kuma mu mutu muma nema, domin kuwa ita ma
haka zatai mana idan mune muka ɓata."
A wannan shekara Cokali da Iliyasis suka shiga duniya
neman ƴar uwarsu Nusi Djinn.
_____________________
Yarima Niyashi shi ne wanda Armad yaci galaba akansa a
gasar Jinzidal, nayi tunani da nasa labarinsa a babi na
baya zaku ce ya akai yake saurayi tun lokacinda su Nusi
suke ƴan shekara shida, sannan kuma yake saurayi bayan
sun girma har a sanda suka fafata da Armad. To ga amsar
nan dai na faɗa, yarima Niyashi yana da sirrin Izza a
jininsa tayadda baya tsufa. Yanzu tambayar ita ce mene
ne alaƙarsa da Nusi?
2)Yaku ma'abota karatun littattafan Hausa ga wata dama
ta samu. Wepsite din Hausaebooks
wanda zai ringa kawo maku littatafan hausa a cikin apk
na ebook ya kuma baku daman downloading zuwa kan
wayoyinku kyauta batare da sisin ku ba Zaku samu
sabbin littafai wanda babu su a kasuwa. Muna muku
barka da zuwa.
Yi hanzari ku ziyacemu
A shafin mu na facebook akan
www.facebook.com/hausaebooks
Nidinne dai Shuraih Usman inkiya
99%
Daga taskar magajin wilbafos
MAGAJIN WILBAFOS
Marubuci: Dr Abdullahi Muhammad Ibrahim
Babi na 73: Ikenga
Post by: Shuraih Usman
@shuraih 99%
www.facebook.com/hausaebooks
.
Daga:- Taskar Magajin Wilbafos
______
Kwana biyu kun jini shiru
Bani da lafiya ne shi yasa jiya na fara samun sauki,
.
---------
Ran Nusi a ɓace haka suka rankaya tare da Waziri, Saiza,
da Galadima, Náru, da Sarkin Bai, Rayaya, izuwa garin
Dula. Akan hanyarsu ne Nusi ta waiwayo izuwa waziri
tana mai cewa, "amma nasan dole akwai mutanen da
suke da damar keta wannan bango a sashin Ikwatora, ko
kasan su?"
Waziri Saiza ya ja dogon numfashi tare da kyaɗa kai yana
cewa, "Eh, lallai akwai mutun ɗaya, babban sarkin
Ikwatora, sarki Rainay Guguwa. Shi ne kaɗai sarki a
ikwatora wanda tun shekarar da aka saukarda al'ummar
biladama izuwa ƙasashen ƙasa yake mulki a sashin
Ikwatora. Duk shekara tsibirin guguwa shi yake zaɓa a
sashin Ikwatora dake doron ƙasa ta biyu. Ko a wannan
shekara ma shi aka zaɓa. Wasu daga cikin mutane suna
ganin cewa acikin baƙar guguwa aka haifeshi. To koma
dai menene shi ne sarkin da yafi kowanne ƙarfin iko a
sashin Ikwatora, kuma shi ne ya saka hannu a dokar hana
ratsa wannan bango shekaru dubu da suka wuce, kuma
shi kaɗai yake da ikon sauya wannan doka."
Nusi taji daɗin wannan labari na waziri, inda ta juyo
izuwa gareshi cikin jin iko da ƙarfin mulki tana cewa,
"mene ne matakin da ake bi wajen zama babban sarkin
Ikwatora? Ko zaɓe ake yi? Domin koma me akeyi saina
hau wannan kujera na kuma karya wannan doka. Babu
ruwana da a ina aka haifi sarki Rainay Guguwa, ko kuma
ƙarfinsa ko kuma alaƙarsa da Ururu. Abinda na sani
kawai shi ne saina nemo abokina Armad da ƴan uwana
Iliyasis da Cokali.
Koda jin wanann magana sai duk su ukun suka ja linzami
cikin firgici suna duban Nusi wadda ko a jikinta. Baki a
buɗe sun kasa cewa komai, haka suka rankaya har zuwa
fada ba tare da kowa yace uffan ba.
***
A shekarar da aka gama Jinzidal abubuwa da dama sun
afku. An siyarda Armad a matsayin bawa, Nusi ta ɓata
sannan kuma Ikenga ya gudu bayanda yayi arba da Uznu
Ururu.
Armad ya rayu a hannun Ururu duk da kuwa uƙubar da
suka gana masa, sannan ya farkar da babbar Izza a
jininsa.
Nusi ta rayu duk da raunin da Uznu yaji mata, sannan
kuma ta tsinci kanta a sashin Ikwatora ba tare da tasan
yadda akai taje ba.
Shi kuwa Ikenga yana ɓacewa daga wannan fili ya
bayyana a tsakiyar saharar dajin Ƙairus dake doron ƙasa
ta biyar. Babu gida gaba babu gida baya, hasalima Ikenga
shi kaɗai ne a tsakiyar wannan dokar dajin. Ƙuwwar iska
da zafin rana da yashi yasa gumi ya fara karyo masa.
Gashi tuni ya ƙarar da ƙarfin Izzarsa a fafatawarsa da
Armad. Saboda haka dakyar yake tafiya. Sai dai kuma ana
cikin haka yaji wata ƙara a bayansa. Yana waiwayawa yai
arba da wasu manyan-manyan sadaukai guda biyu.
Wanda kana ganinsu zaka tuna da tarihin daular
samudawa. Saboda nauyinsu ƙafafunsu sun nutse acikin
ƙasar da suka dira. Suna sanye da baƙaƙen kaya masu
ratsin ɗorawa daga sama. Kowanne ɗaya acikinsu Izzarsa
ta haura dubu ɗaya.
Ikenga yana ganinsu ya gane su. Ba wasu bane illa biyu
daga cikin kwamandu biyar dake aiki a ƙarƙashin Uznu
Ururu. Ikenga yayi murmushi yana mai cewa, "dama
nasan baza ku kyale ni haka ba."
Ɗaya daga cikin kwamandun guda biyu ya miƙa
hannunsa kan takobinsa yana mai cewa, "ka miƙa kanka
salin-alin babu gardama. Dukkanmu izzarmu ta haura
dubu, kana da ɗari kacal. Mai zaka iya yi face miƙa wuya."
Ɗaya kwamandan wanda keda baƙar fuska da manyan
ƙasusuwa masu kama da duwatsu ya ƙara da cewa, "kada
ka zargi kowa ka zargi rauninka da lalacinka dana zuri'ar
ka."
"Hmmm....." Ikenga yaja dogon numfashi tare da
murmushi yana cewa, "Idan zaku iya kama ni to ku
gwada." Yana rufe baki ya tafa hannayensa guda biyu
yana kiran waɗansu ɗalasimai da harshen Wilburish.
Lamarinda yasa wani shinge na koren haske ya bayyana
ya kewaye shi. Abin mamaki daga cikin wannan haske
saiga wasu mutane uku sun bayyana. Babban abin
mamakin shi ne biyu daga cikinsu kamarsu ɗaya sak da
Ikenga, kai hasalima Ikenga ne kawai. Babu maraba koda
kuwa ta kwayar zarra. Ɗaya mutumin kuwa wannan
tsohon ne mai suna Kána, wanda aka gansu tare da
Ikenga watanni kaɗan kafin Jinzidal, a lokacin da Ikenga
ya jawo salwantar ruhin Armad.
Waɗannan mutane biyu masu kama da Ikenga suka
rikiɗe izuwa iska sannan suka shige jikin Ikenga. Haka na
faruwa wannan da'irar haske ta ɗauke, amma Izzar
Ikenga nan take ta canja daga ɗari zuwa duba ɗaya,
sannan ta ƙara rikiɗewa daga dubu ɗaya zuwa dubu
goma. Gashin kan Ikenga ya rikiɗe izuwa fari fat, sannan
kuma ya ƙara tsayi har zuwa gadon bayansa. Fatarsa
jikinsa tai fari fat tamkar an zuƙe jinin dake jikinsa. Wata
sabuwar nutsuwa ta bayyana a tattare dashi. A wannan
lokaci idan baka sanshi sosai ba baza ka gane shi ba.
Ana haka saiga aljani Gal-iyyu ya bayyana ya fito daga
jikin Ikenga ya zube a ƙas cikin biyayya. Shima wannan
tsoho Kána a ƙas ya zube yana mai cewa, "barka da dawo
wa, sarkin duniya."
Su kuwa waɗannan kwamandu guda biyu buɗe baki sukai
cikin firgici suka fara jada baya, amma ina tuni sanyin
babban sihiri ya sauka a garesu. Wannan ƙanƙara ruwan
toka mai ɗauke da ƙarfin Izzar Ikenga ta ratsa ƙashinsu,
sannan ta rusa ruhinsu. Kan kace meye wannan
waɗannan kwamandu masu Izza sama da dubu sunyi
bindiga sun faɗi ƙasa matattu.
Ikenga ya juyo izuwa Aljani Gal-iyyu da tsoho Kana yana
magana a nutse tamkar ba shi ne ya halaka ma'abota Izza
sama da dubu ba. "Kunga yanzu duniya zatai tunanin
ƙarfinmu bai wuce na Izza ɗari ba. Za suyi tunanin cewa
ƙarfin Izzarmu bai wuce na mu kara da wannan yaro ɗan
zuri'ar Wilbafos ba. Hakan zaisa baza a saka mana ido ba
a lokacin da muke gudanar shirye-shiryenmu ba."
Ɗan tsoho Kána ya amsa da cewa, "wannan haka yake ya
shugaban mu. Zanso naga fuskar yaron nan Armad a
sanda zai gane cewa da ɗaya bisa ukun ka ya fafata amma
ya kasa samun nasara. Hasalima saida ka raba izzarka
gida ɗari sannan kai amfani da kaso ɗaya."
"Armad?" Ikenga ya tambaya cikin girman kai da jin Izza
tamkar bai taɓa jin sunan Armad ba, sannan ya ɗora da
cewa, "Ah... sunan sa kenan."


2)Yaku ma'abota karatun littattafan Hausa ga wata dama
ta samu. Wepsite din Hausaebooks
wanda zai ringa kawo maku littatafan hausa a cikin apk na ebook ya kuma baku daman downloading zuwa kan wayoyinku kyauta batare da sisin ku ba Zaku samu
sabbin littafai wanda babu su a kasuwa. Muna muku
barka da zuwa.
Yi hanzari ku ziyacemu
A shafin mu na facebook akan
www.facebook.com/hausaebooks


Nidinne dai Shuraih Usman inkiya
99%
Daga taskar magajin wilbafosMAGAJIN WILBAFOS
Marubuci: Dr Abdullahi Muhammad Ibrahim
Babi na 74: Miyura (1)
Post by: Shuraih Usman
@shuraih 99%
www.facebook.com/hausaebooks
.
Daga:- Taskar Magajin Wilbafos
--------
A wani gari nisan kimanin shekaru hamsin daga inda
Armad tsaye, a wani tsiburi dake tsakanin doron ƙasa ta
farko data biyu, wasu yara ne ƴammata guda biyu ke
wasa a gefen wani kogi. Kana ganin ƙirar yaran da kayan
jikinsu zaka san cewa lallai ƴaƴan sarauta ne. Dukkan
idanunsu farare ne fat babu ko kwayar baƙin dake cikin
ido. Kai ka rantse makafi ne.
Amma zaka gane cewa suna gani tar-tar kamar kowanne
ɗan adam a yayinda ɗaya daga cikinsu wadda ta kasance
fara mai gashi roɗi-roɗi ta ga wani mutun a kwance a
gabanta ruwa ya koroshi. Ba shiri taja rigarta sama, ta
kuma fara kiran ƴar uwar ta, "Suwee! Suwee!! Suwee!!!"
Ƴar-uwar tata ta juyo izuwa gareta. Asalin sunan ƴar
uwar shi ne Suwainah, amma ƙanwar tata mai suna Zeera
ta fiso ta ringa kiranta da Suwee.
Zeera ta nuna mutunin dake gabanta tana cewa, "Kizo
kinga wani ma, ina ragowar ukun?"
Suwee ta zare ido cikin firgici tana cewa, "Wani ne ya
ƙara bayyana? Waɗancan baba ya tafi dasu wajen sarki."
Zeera ta buɗe baki cikin mamaki,"Baba kuma? kina nufin
baba da kansa! To gaskiya ne kenan abinda ake faɗa cewa
daga wata duniyar aka jefosu!"
Tun kafin ta rufe baki yayar tata mai kimanin shekaru sha
shida wadda kuma ta bata shekaru uku, ta taho wajen da
take da gudu domin taga wannan mutun da ƙanwarta
take nuna mata. Tana zuwa ta rufe ƙanwar tata da faɗa,
"ba baba yace mu daina faɗa ba, so kice wasu suji. Yana
ina?"
Zeera ta nuna mata wani yaro kwance a gefen kogin, duk
taɓo ya shafe masa jiki da fuska. Amma duk da haka idan
kalura sosai zaka ga cewa akwai ɗaurin jan kyalle a gaban
goshinsa. Kuma lallai idan kasan Armad Wilbafos
mamallakin tambarin Miyura zaka gane cewa shi ne ba
wani.
Suna tsaye suna tunanin ya zasu yi kawai sai suka ji
hayaniyar sauran ƴan matan daga nesa suma suna
kusanto wannan kogi.
Zeera ta dubi ƴar uwar tata cikin sauri tana cewa, "Yaya
to ya zamuyi dashi, ga mutane nan!"
Nan take Suwainah ta fito da wata ƴar ƙaramar jakar
tsafi a cikin rigarta ruwan hoda, inda ta bawa ƴar uwarta
ta. Suka kuma fara tala wannan jaka har saida takai dai-
dai tsayin yadda zasu iya zira Armad aciki.
Ƙanwar ta miƙa hannunta domin ta fara saka kan Armad
aciki, amma a lokacin al'amari ya canja.
Domin kuwa tana taɓa jikin Armad hannunta ya shige
cikin kansa tamkar babu komai a wajen. Cikin sauri ta
zaro hannunta ta kuma ƙara taɓawa dan ta tabbatar,
amma hakan dai ta ƙara faruwa a karo na biyu.
Nan da nan ita ma Suwainah ta miƙa nata hannun ta taɓa
ƙafarsa, amma taga itama hannunta ya shige tamkar
babu komai a wajen. Cikin tsananin mamaki suka fara
tunanin ko mafarki suke. Amma maganar ƴan uwansu
matan dake ƙara matsowa ita ce ta tabbatar musu cewa
ba mafarki suke ba. Nan take suka fara bin duk wata
hanya domin zira jikin Armad acikin wannan jaka, amma
ina.
Kuma suna cikin haka ne ɗaya daga cikin matannan masu
ƙarasowa ta hango su, ai kuwa nan take ta fara kwala
musu kira, tare da tahowa inda suke.
Nan take Suwainah ta yanke hukunci tana mai cewa,
"Zeera jeki ki gano inda baba yake. Idan da dama ki gaya
masa abinda ke faruwa a ɓoye ba'a cikin mutane ba.
Zanyi maganin abubuwa anan."
Tana faɗar haka ƴar uwar tata Zeera ta rankaya a guje ta
nufi gabas.
Suwainah tayi duk wata dabara da zatai ta ɓoye ruhin
Armad amma abin ya gagara. Tana cikin wannan hali
wannan ƴammata huɗu suka iso wajenda take tsaye. Tai
kasaƙe tana jira su tambaye ta wane ne wannan mutun
dake kwance a bayanta amma ba suce komai ba.
Hasalima tamkar basa ganinsa. Wanda hakan yasa
Suwainah waiwayawa cikin zafin nama tayi duba izuwa
inda tabar Armad amma babu shi babu alamunsa.
Tana cikin diri-diri taji muryar ɗaya daga cikin wannan
mata dake gabanta. "Suwainah me kike anan ke kaɗai?
Saura kwanaki bakwai a rantsar da ma'abota Ururu na
wannan shekarar, kije ki rubuta sunanki ki hau layi."
Suwainah ta kyaɗa kai tana cewa, "Eh hakane. Dama nazo
wanka ne kuma bansan an fara rubuta suna ba. Yaya
tsarin yake?"
Ɗaya daga cikin ƴan matan taja dogon numfashi kafin
daga bisani ta kyaɗa kai tana cewa, "fafatawa za'ai kawai.
Duk wanda ya farkar da Ururun dake idanunsa zai shiga
cikin ma'abota Ururu. Ragowar kuma zasu ci gaba da
zama anan sai wata shekarar. Sannan kuma acikin
waɗanda

Please Login or Register in order to submit comment