Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

haka ya yiwo
kan Ikenga ta ɓangaren dama.
A gabansa kuwa tuni wannan sara ya haɗu da wannan
ƙanƙara da wuta da walƙiya. Haɗuwar tasu keda wuya
gaba ki ɗayan abubuwan nan guda uku suka tarwatse
suka ɓace, tamkar ba'a taɓa yinsu ba. Sannan saran yaci
gaba da tafiya yayi kan wannan mutun-mutumi gadangadan. Amma suma basu yi ƙasa a gwiwa ba wajen ci
gaba da aikowa da wannan sara saƙon bala'i. A haka suka
samu suka tsayar dashi kafin ya isa gare su. Ai kuwa saran
na tsayawa duk su ukun sukai kan Armad suka hanashi
ƙarasawa kan Ikenga wanda ke tsaye a gefe na ganin
maike faruwa.
Suka saka Armad a tsakiya, sannan suka fara aika masa da
saƙon ruwan zafi, walƙiya da dusar ƙanƙara. Suna niyyar
halaka shi ta kowanne ɓangare. Amma ina, Armad a tafe
ya kwana. Domin kuwa a dai-dai wannan lokaci ne ya

fusata ya juya takobinsa da karfin tsiya, sannan ya kaiwa
waɗannan mutun-mutumi uku sara, inda ya tsinke musu
kai nan take. Wata iska mai zafi ta fice daga jikin takobin
tasa sannan ta daki jikin mutun-mutumin suka juye
izuwa toka. Cikin ƙiftawar ido Armad ya bayyana a gaban
Ikenga ya kuma kai masa wawan sara.
A dai-dai wannan lokaci babu wata kalma da zaka iya yin
bayanin Armas da ita illa kace yayi kama da matashin
bajimin aljani ɗan fari. Babu alamun tausayi ko yafiya a
tattare da idanunsa, lallai a kowanne lokaci Ikenga zai iya
ziyartar lahira.
Sai dai ana cikin haka ne Ikenga yaga babu sarki sai
ALLAH yai zafin nama ya tafa hannayensa tare da kiran
ɗalasimin Takun-sarki, "Shaibal-shísu."
Acikin wani yanayi na ban al'ajabi gaba ki ɗaya lokaci ya
tsaya cak, ya kuma bawa Ikenga damar yin taku bakwai
da ƙafafunsa kafin saran Armad ya cimmasa. Yana ajiye
ƙafa a takun ƙarshe wani duhu irin na farkon ketowar
alfijir ya bayyana ya maye gurbin hasken da da ke cikin
filin kallon. Hatta ƴan kallon dake cikin filin basu samu
damar ganin abinda ke faruwa ba a dai-dai wannan
lokaci.
Bayan kimanin daƙiƙa biyar wannan duhun ya sarara,
sannan haske ya dawo. Ai kuwa sukai arba da Ikenga
sanye da wata rigar tsafi ruwan dinare, sannan kuma riƙe
da wata takobi mai kyalli ita ma ruwan Dinare.
Armad kuwa na can gefe a tsaye shima riƙe da takobinsa
ruwan ɗorawa. Babu alamun ciwo ko rauni ko gajiya a
jikin kowannensu, amma ga dukkan alamu iskar dake
kaɗawa a tsakaninsu ta canja, kuma lallai yanzu ne za'ai
faɗan ƙarshe. Kana gani kasan kowa acikinsu yai
rantsuwa daya faɗi ƙasa a wannan wasa a gaban idon
duniya kwara ya mutu.
"Fasahar Ɗorawa ko?" Ikenga ya kalli takobin Armad
cikin nazari sannan yaci gaba da cewa, "lallai babbar
fasaha ce. Kuma idan da ba dani ka haɗu ba, to da lallai
zaka iya yin nasara akan kowa. Amma kayi sani cewa
ƙarfin dake cikin ruhi da jini na ya wuce gaban lisaafin ka,
kuma yanzu zan nuna maka dukkan ƙarfina. Zan nuna
maka fasahar takobi dana sakawa suna Lokacin Alfijir. Ina
mai baka shawara idan har kana da wani shiri a ɓoye, to
ka fito dashi."
Yana rufe bakinsa yai kan Armad cikin zafin nama tare da
kaɗa wannan takobi ruwan dinare dake hannunsa. Ai
kuwa nan take wani duhu irin na alfijir ya fito daga jikin
ƙarfen takobin ya kuma yiwo kan Armad.
Duk inda wannan duhu ya gifta sai kaga wajen ya tsufa
nan take kuma ya murmushe tamkar wanda yayi shekara
dubu a ajiye. Kan kace meye wannan tuni filin da suke
fafatawa akai ya tashi daga sabo mai kyalkyali ya koma
izuwa tsoho tamkar wanda akai shekara dubu da sarrafa
shi.

Armad na ganin haka ya ja da baya da sauri ya tafa
hannayensa ya sa tsinin takobinsa ya caki hannunsa,
sannan ya shafa jinin akan takobin. Kafin wannan sara na
Ikenga ya ƙaraso tauraruwa ɗaya dake saman takobin
Armad ta fara ƙoƙarin rabewa izuwa biyu. Amma ina, kan
ta ƙarasa rabewa wannan sara ya iso, inda ya daki jikin
takobin Armad da ƙarfin tsiya sannan ya ɓace. Yana
ɓacewa Armad ya kalli hannunsa yaga yayi furfura ya
tsofe ya yamushe tamkar wanda yayi shekara dubu a
raye. Cikin ɓacin rai ya maida takobin hannun dama, inda
lokacin tauraruwar ta koma biyu. Dukkan wani ƙarfi dake
jikin Armad da takobinsa ya koma izuwa biyu. Nan take
wani tsananin nauyi mai ban tsoro ya fara fita daga jikin
Armad yana yiwo wa kan Ikenga.
Kan kace meye wannan wajen da suke tsaye ya fara
lotsawa cikin ƙasa, tamkar wanda aka dunƙule nauyin
dala da kwauron dutse aka ɗora masa. Ikenga yaji
ƙafafuwansa sun fara ƙara suna neman karyewa saboda
wannan nauyi. Amma a lokacin ya ƙara kaɗa takobinsa
ruwan dinare, lamarinda yasa wannan nauyi ya tsofe nan
take, tamkar yayi shekara dubu. Lallai ba nauyi ba koma
mene ne zai ƙare idan yayi shekara dubu.
Ana cikin haka ana kallon kallo aka ji muryar Ikenga,
"Hmmm.... wato kana da takobin da take sarrafa nauyi.
Ta ƙarashi ko kuma ta rage shi. Lallai kaima ma'aboci Izza
ne, amma duk da haka baza ka iya tsayawa a gaban
fasaha ta Lokacin alfijir ba. Takobi ta ta duhun alfijir tana
sarrafa lokaci. Kuma duk abinda na sara da ita a lokacin
take yake tsufa na shekara ɗari. Ko yaro ne anan take zai
tsofe tamkar yayi shekara ɗari. Lallai saina mulki duniya
da fasaha ta takun sarki. Kayi sani cewa indai na sare ka
koda sau ɗaya ne, kuma komai ƙanƙantar saran sai ka
tsufa na kimanin shekara ɗari nan take."
Yana rufe baki yai kan Armad da takobinsa gadan-gadan,
shima Armad kawai fusata yaƙara yi ya kuma yiwowa
kansa. Duk inda Armad ya gifta sai wajen ya nutse a
ƙarƙashin ƙasa tamkar an haƙeshi da kimanin ƙafa ɗari.
Shi kuma Ikenga duk inda yayi sai kaga wajen ya tsufa.
Suna haɗuwa suka kaure da azababben yaƙi, ƙura ta
turnuƙe, iska ta tsofe, haske ya ɗauke. Ƴan kallon basa jin
komai sai ƙarar takubba. Cikin daƙiƙa ashirin kawai su
biyun sun isarwa da juna sara sama da hamsin. Duk
sanda saran Ikenga ya yiwo kan Armad, Armad zaiyi
amfani da nauyi ya danne shi izuwa ƙas ya hanashi zuwa
wajensa. Shi kuma Ikenga kawai tsofantar da saran
Armad yake kafin ya isa gareshi.
Haka wannan yaƙi yaci gaba tsahon kimanin mintuna
bakwai, kafin daga bisani a daina jin komai. Kowa acikin
ƴan kallo yayi tsit acikin filin wasan. Jira kawai ake aga
ƙurar ta lafa domin aga maike bayan wannan ƙura.
Bayan minti ɗaya ƙurar ta lafa, akai arba da Ikenga da
Armad a kwance cikin jinin shane-shane, babu wanda

yake iya motsi acikinsu. Lallai duk su biyun sunkai ƙarshe
wajen ƙarar da ƙarfin jikinsu. Kai hatta ɗan yatsa basa iya
motaswa. Amma duk da haka basu daina yiwa juna kallin
tsana da azabar yaƙi ba. Kansu na tsaye suna kallon juna,
kuma da da yadda zasu yi da tuni sun ƙara tashi sun
afkawa juna.
Ana cikin haka alƙali ya rasa wa zai bawa nasara, kawai sai
Armad yaga wani dattijo mai yawan farin gashi bayyana
akan Ikenga ya dafa shi. Haka na faruwa dukkan Izzar
Ikenga ta dawo tamkar yanzu aka fara faɗan.
Yana ji Ikenga ya ce, "Bayajidda, karfa wani ya ganka."
Sannan kuma yana ji dattijon da aka kira da Bayajidda ya
amsa, "Ai ko Uznu Ururu dake cikin can bai isa ya ganni
ba. Saboda dalili guda biyu, na farko dai ƙarfin Izzarsa bai
kai ya ganni ba, sannan kuma koda ƙarfinsa yakai babu
wanda zai iya gani na sai jinin Bayajidda."
Armad ya buɗe baki zai gayawa alƙali da ƴan kallon cewa
Ikenga zaiyi fasha, amma hatta bakinsa ma yaƙi motsawa
saboda tsananin gajiya da ƙarewar ƙarfin Izzarsa baki
ɗaya. Kai hatta idonsa ma ya kasa ƙiftawa.
Tunani kaɗai yake iya yi acikin ransa, 'wai mai wannan
tsohon yake nufi da babu wanda zai iya ganinsa sai jinin
Bayajidda, gashi ina ganinsa. Kuma yana nufi Uznu Ururu
ma bai kai ƙarfinsa ba. Koma dai meye lallai bazan yadda
ba, wannan ai fasha ce!'
___
Nauyin dake fita daga takobin Armad shi ake kira da
GRAVITY da English. Amma nayi ta bincike ban samu
fassararsa da hausa ba, saboda haka nayi fani da kalmar
NAUYI.
Nidinne dai Shuraih Usman inkiya
99%
Daga taskar magajin wilbafos
MAGAJIN WILBAFOS
Marubuci: Dr Abdullahi Muhammad Ibrahim
Babi na 47: Hidaya Wilbafos
Post by: Shuraih Usman
@shuraih 99%
www.facebook.com/hausaebooks
.
Daga:- Taskar Magajin Wilbafos
Armad na ganin wannan ruhi mai girman Izza daya
bayyana ya taimaki Ikenga babu abinda ya faɗo masa
acikin rai sai ƴar uwarsa mai suna Hidáya Wilbafos.
___
1847 Bayan Amri
Kaɗan daga cikin tarihin Armad da ƴar uwarsa.
"Armad wallahi zan dake ka! Wai baza ka maida hankali
ba!" Wata budurwa mai matuƙar kama da Armad tayi
masa tsawa a yayinda suke tsaye a filin horo.
A wannan shekara ta 1847 Armad yana ɗan shekara

takwas, kuma tun a wannan lokaci aka fara koyar dashi
al'amuran Izza.
Wannan budurwa na tsaye sanye cikin jar alkyabba irin ta
mutanen farko. Kimanin shekarunta zai kai ashirin da
biyar koma fiye da hakan. A rataye da kafaɗarta ta dama
akwai doguwar takobi mai zanen taurari ruwan ɗorawa.
Budurwar doguwa ce wadda a ƙalla zata yi zira'i uku a
tsaye. Kamanninta akwai kamala da nutsuwa da jarumta
aciki, lallai akwai ƙarfin Izza a tattare da ita.
Sunan wannan budurwa Hidaya Wilbafos. Kuma yayar
Armad ce ta jini duk da kuwa ratar shekarun da ke
tsakaninsu.
Armad na sanye cikin farar ƴar shara ɗaure da jan kyalle
a goshinsa. Daga ganin yadda yake ɓata rai kasan dole
tayi masa, amma lallai da zata kyaleshi da bazai yi
wannan horo ba.
"Shikenan, idan baza ka dage ka koyi al'muran Izza ba to
ba ruwa na da kai. Idan bana nan wa zai kare ka?
"Ehmmm..." Hidaya ta ja dogon numfashi tare da girgiza
kai. "gaka da tsokana amma baka san dagewa ka koyi
al'muran Izza, sai muga idan bana nan wazai ringa hana
yaran da kake tsokana suyi maka duka. Zo mu tafi gida,
kuma gobe ma sai mun dawo ka ci gaba. Ai ko kana so ko
baka so saika zama ma'aboci Izza."
Hidaya ta juya zata tafi amma Armad ya tsaya yaƙi binta,
fuskarsa cike da shagwaɓa irin ta ƙananun yara.
"Ka taho mana...." Hidaya ta waiwayo tai masa magana.
"Ni.....ni fa ƙafa ta ciwo take!" Armad ya haɗe fuska
kamar zai fashe da kuka.
"Hmmm....." Hidáya taja numfashi gami da gyaɗa kai.
Domin tuni ta gano abinda Armad yake nufi. Sau da
dama idan suka fita tare yakan ce bazai iya tafiya ba saita
goyashi shi a bayanta. Kuma a wannan lokacin ma abinda
yake nufi kenan.
"Indai baka dage ba ai daina ɗaukan ka zanyi." Cikin
sanyin zuciya da tausayi irin na ƴan uwa ta juyo izuwa
Armad. Inda ta durƙusa ta goya shi sannan suka kama
hanya.
Ba jimawa suka fara fita daga cikin duhun manyan
bishiyun goriba da suka kewaye wajen. Hidaya ta
numfasa tare da ci gaba da nunawa Armad
muhimmancin ya dage da horonsa. Ga dukkan alamu
baza ta haƙura ba indai Armad bai maida hankali yayi ba.
"Kaga ina so na koya maka duk wasu fasahohi na sarrafa
aljanu da suka shafi zuri'ar gidan wilbafos kafin lokaci ya
ƙure. Amma kaƙi maida hankali, towai mai kake so ka
zama ne, gayamin naji?"
Armad na kwance a bayanta cikin shagaɓa irin wadda
yayar tasa ita kaɗai yake yiwa, ya fara da cewa, "kinsan
me yaya, ni dai abinda nake so a rayuwa shi ne zaman
lafiya ya wanzu. Ko wa ya zamanto acikin kwanciyar
hankali. Idan na girma na zama kamar ke nayi aure, idan

na kara girma saina haifi ƴaƴa guda uku duk masu kama
dake, sannan idan na tsufa saina mutu akan gado na akan
cinyarki tare da mama da Abba da ƴaƴa na duk sun
kewaye gadon da zan mutu. Shikenan inna mutu sai kuyi
kuka sannan kuma ku ringa tunani na...." Koda yazo nan a
zancensa sai yai shiru tamkar wani abu ya gilma acikin
ransa, inda cikin tsoro irin na yara ya ɗaga kai ya dubu
yayar tasa Hidaya. Idanunsa a wangale ya ce, "Ai zaki
ringa tunani inna mutu ko Yaya?"
Maimakon ta bashi amsa sai kawai ta juyo da kanta ta
ƙura masa ido tana mai mamakin wannan abu daya faɗa.
Badan komai ba sai dan cewa ita ma kanta shekaru da
dama da suka wuce burinta kenan. Tamkar ƙanin nata
Armad ya shiga ranta ya gani, duk da kuwa cewa bata
taɓa gayawa wani mahaluƙi wannan buri nata na yarinta
ba har zuwa wannan lokaci.
Saboda haka sai kawai tayi murmushi tare da cewa, "eeh,
zan tuna ka."
Amma ga dukkan alamu wannan magana kaɗai ta faranta
wa Armad rai, inda ya ƙara maƙalewa a bayanta tamkar
yana tsoron wani abu zaizo ya raba su da ita.
Murmushi kawai tayi taci gaba da tafiya tana yin tunanetunanen ya zatayi ta kare wannan ƙani nata wanda baya
son koyon al'amuran Izza ko kaɗan.
Tana cikin tunani ne taji muryar sa yana cewa,
"ehmmm... Kinsan me? Mu ɗaura alkawari cewa duk
wanda ya riga mutuwa ɗayan zai ringa tuna shi."
Tun kafin ya rufe bakinsa ya ziro ɗan ƙaramin ɗan
yatsansa ta gefen kunneta da niyyar su ɗaura. Babu
abinda tayi face ajiyar zuciya sannan kuma ta kama
hannun nasa da niyyar ta yarda.
Kamar zaiyi shiru, amma abu na gaba daya faɗa shi ne,
"to indai da gaske kin yarda toki ɗakko min ɗaya daga
cikin filawar dake wancan lambun." Armad yai nuni da
wani katafaren lambu kimanin taku dubu daga inda suke
tsaye.
Babu abinda kake gani daga nesa sai baƙin duhuwar
wannan daji da wasu manya-manyan baƙaƙen bishiyu
waɗanda lallai koda basu yi shekaru dubu a raye ba to
kaɗan ne babu. Tsayin kowacce bishiya yakai zira'i maitan
da ɗoriya. Kai lallai har sai hular mai kallo ta faɗi ƙasa
saboda ɗaga kai amma bai gano ƙarshen wasu daga cikin
bishiyun ba.
Lambun daban yake da wanda su Armad ke ciki, kuma an
kewaye shi sannna kuma ansa shedar sarki Hanibal Sarkin
ƙasa ta uku akai. Sarki Hanibal shi ne sarki mai mulkin
doron ƙasa ta uku, sannna kuma yana ɗaya daga cikin
sarakunan Jinzidal biyar.
Koda jin wannan magana sai Hidaya ta canja fuska,
"Armad ka fasan cewa duk abinda ke cikin can wajen na
Hanibal ne kuma ya hana shiga."
"Eh na sani, amma fa ta sama zamu bi kawai mu ɗauki

guda ɗaya ai ba wanda zai sani fa. Kinji Yaya, kinji... Kinji
daga wannan fa shikenan."
Tai murmushi tare da ajiƴar zuciya, "To muje amma
karka taɓa komai kaji."
Armad ya kyaɗa kai.
A dai-dai wannan lokacin Hidaya ta tafa hannayenta ta
kuma kira wani ɗalasimi a zuci, sannan tai tsalle ta tashi
sama tamkar tsuntsu mai fuka-fuki. Abu ne sananne cewa
duk wanda ya haura shekaru dubu na Izza to zai iya tashi
yayi tafiya a sama ba tare da matsala ba. Kuma hasalima
Armad bawai filawar ce ta dame shi ba, sai dai kawai yana
so ƴar uwar tasa ta tashi sama dashi, saboda yasan lallai
indai zasu shiga dajin to saisun tashi saman.
Ai kuwa suna tashi sama Armad ya ƙara saƙale hannunsa
ta ƙirjinta tamau, sannan ya saki ɗayan akan iska yana
ihun farin ciki. Duniya tayi masa daɗi domin a wannan
lokaci babu abinda yake so face tashi sama a bayan yayar
tasa.
"Wuuuuuu...." Tun daga nesa zaka iya jiwo ihun Armad a
saman.
"Dama nasan abinda kake so kenan. Ka riƙe ni dai sosai
karka faɗo." Tana cikin magana suka dira acikin tsakiyar
wannan daji. Inda ta ajiye Armad ta kuma juya tana
hangen imda filawar take.
"To ka tsaya anan, ga wata can bari na ɗauko maka." Nan
take ta ƙara tashi sama ta nufi wani surƙuƙi a ɓangaren
arewa.
Bayan daƙiƙa ashirin ta dawo da wata filawa yaluwa mai
kyawun gaske.
Amma tana sauka a gaban Armad taga hannunsa na ɗisa
da jini.
"Waye ya ji maka ciwo?" Shi ne kawai abinda ta tambaya.
Tun kafin Armad ya bata amsa siffarta ta canja baki ɗaya.
Wani yalon haske ya fara fita daga jikin takobin dake
rataye a kafaɗarta. Wata baƙar wuta ta fara ci acikin
idanunta. Nan take iskar wajen ma ta canja ta ƙara nauyi,
sannan kuma wani sauti ya fara tashi daga cikin wannan
daji. Lallai inda akwai mai fassara maganar tsirrai da yaji
cewa haƙuri waɗannan bishiƴoyi ke bawa Hidaya. Amma
ina, tuni ta toshe kunnenta tsahon lokaci. Kai hatta
alkyabbar dake jikinta ta canja launi izuwa baƙa, lallai a
wannan lokaci Hidaya tayi kama da siffar mutuwa kanta.
Amma a wannan lokaci shi kamsa Armad karkarwa yake
yana matsawa baya ganin yadda yayar tasa ta canja
kama. Yana ji tamkar wutar dake cikin idanunta zata soya
naman jikinsa nan take.
Bai san lokacinda bakinsa da kansa ya fara magana ba ba
tare da ya bashi umarni ba. "Wancan ƙayar dake jikin
wancan bishiyar ce." Ya nuna wata bishiyar ƙaya a kusa
dashi yana karkarwa.
"Wato har akwai wanda ya isa ya jiwa ƙanina ciwo ina
wajen! Lallai yau ba Hanibal ba, koda wannan dajin na

sarkin Ururu ne a bisa doron ƙasa ta farko saina rusa ku."
Tanan rufe baki ta zare takobinta, inda nan take wasu
taurari guda uku suka bayyana a kewaye da takobin.
Ai tunma kafin ta juya takobin dukkanin wannan lambu
ya kama da wuta. Wanda idan da zaka kula zaka ga irin
wutar dake ci acikin idonta ce.
A dai-dai wannan lokaci Armad ya sume a wajen. Babu
abinda yake iya tunowa sai tashi dayayi washe gari ya
ganshi akan gadonsa Hidaya na gefensa tana shafa kansa.
To a wannan shekara ne da kakan Armad mai suna Zaikid
da yayar tasa Hidaya suka tafi wani aiki wanda Armad
yayi-yayi amma suka ƙi bayyana masa ina zasu. Daga
ƙarshe ya haƙura.
Bayan wata biyu da wannan tafiya tasu, dattijo Zaikid ya
dawo shi kaɗai. Babu Hidaya amma akwai takobin ta mai
taurari ruwan ɗorawa a hannunsa.
Armad ya taho da gudu yana tambaya ina take, amma
kakan nasa baice komai ba sai kawai takobin daya miƙa
masa. Armad na karɓa ya fashe da kuka ganin alamun jini
a jiki.
Tun daga wannan lamari Armad ya ɗau takobi ya kuma
shiga koyon horo da alamuran Izza.
____
To ko ina Hidaya Wilbafos?
Nidinne dai Shuraih Usman inkiya
99%
Daga taskar magajin wilbafos
MAGAJIN WILBAFOS
Marubuci: Dr Abdullahi Muhammad Ibrahim
Babi na 48: Uznu Ururu 1
Post by: Shuraih Usman
@shuraih 99%
www.facebook.com/hausaebooks
.
Daga:- Taskar Magajin WilbafosRundunar mayaƙan sarki Ururu, sarki bisa doron ƙasa ta
farko, sun rabu ne izuwa kaso kimanin biyu, kaso na
farko masu kare Rukunin gasar Jinzidal, kaso na biyu
kuma masu kula da doron ƙasa ta farko da babbar fadar
sarki Ururu.
Idan muka ɗauki runduna mai kare rukunin Jinzidal
zamu ga a can ƙololuwar sama akwai manyan
kwamandoji biyar, a ƙasansu kuma akwai muƙamin
kyaftin-kyaftin guda biyar-biyar, wanda kowannensu
nada iko akan miliyoyi mayaƙa dake ƙarƙashinsa.
Kowanne kwamanda acikin biyar ɗinnan nada Kyaftin
guda biyar a ƙasansa. Kowanne kyaftin kuwa nada a ƙalla
girman Izza da yakai shekaru dubu da ɗoriya, kuma
kowannensu mutun ne shahararre a fagen Izza a ƙasa
bakwai.
Su kuwa kwamandojin nan guda biyar kowannensu nada
a ƙalla girman Izzar da takai shekaru ɗai-ɗai har dubu
biyar da ɗoriya. Sannan kuma a ƙalla sai ya mallaki

Ururu. Wato dai sai yana da baƙaƙen idanu. Kowannensu
anyi ittifaƙi yana da ƙarfin da zai iya juya daula duk
girmanta izuwa toka cikin ƴan daƙiƙu.
Aikin wannan mayaƙa shi ne kawai kula da rukunin
Jinzidal. Da tabbatar da cewa lallai kowa yana biyayya
akansa.
Uznu Ururu ɗaya ne daga cikin wannan kwamandoji
biyar na mayaƙan Ururu.
____
A wannan lokaci Armad ya tattaro dukkan ƙarfinsa, inda
ya miƙa hannu ya daki Littafin-takobin dake cikin rigarsa.
A iya saninsa wannan littafi daya samu a sakamakon rasa
Miyurarsa ya taka rawa ta musamman a faɗansa na baya,
amma baisan mai yasa a wannan hali da yake buƙatar
taimako yaƙi yi masa komai ba. Hakan nema yasa ya
yanke shawarar ya zungureshi yaji ko zai iya tashinsa.
Ai kuwa hannunsa na taɓa littafin, littafin ya fara ɗaukan
zafi yana bada koren haske. Tun daga nesa zaka iya hango
wannan haske.
Shima Ikenga wanda ya daɗe da tashi tsaye yaga wannan
haske, kuma nan take ya zare takobinsa ya yiwo kan
Armad da niyyar hanashi koma mai yake son aiwatarwa.
Domin zuwa wannan lokaci Ikenga yasan Armad ba
kanwar lasa bane, saboda haka bashi da wata hanya face
yai sauri ya ƙarasa Armad kan ƴayi wani abu.
A ɓangaren Armad kuwa wannan haske yasa yana jin zafi
tamkar ana soya shi a raye. Amma duk da haka ya daure
ya cije, kasancewar yasan a ƙarshen wannan haske
babbar Izza na nan tafe. Kuma da sannu zai ci galaba
akan Ikenga zarar wannan Izza ta bayyana a gareshi.
Shekaru 10,20,.........
A dai-dai lokacin da Izzar Armad ta fara yin sama a
wannan lokaci Ikenga ya ƙaraso kansa. Yana zuwa ya
ɗaga takobinsa sama ya kuma nufi wuyan Armad da
niyyar sare masa kai baki ɗaya.
___
A dai-dai wannan lokaci da Ikenga ya ɗaga takobinsa
Uznu Ururu ne ya canja fuska ya kuma haɗe tare da
yanke shawara nan take.
Acikin ransa yana mai cewa, 'Idan na bari ya kashe
wannan yaro Armad to lallai Littafin-takobi ƙara ɓacewa
zaiyi. Kuma ba lalle na ƙara ganinsa ba sai bayan wasu
ɗaruruwan shekarun.' Yana gama wannan tunanin acikin
ransa ya ɓace daga kan kujerarsa dake cikin wajen
manyan baƙi.
Yana ƙara bayyana sai gashi a tsakanin Armad da Ikenga.
Nusi na ganin haka ta zare takobin ta, ta caki hannunta na
dama, sannan ta shafa jini akan takobin. Wani sanannen
farin haske wanda ke fita a duk lokacin da mutun yake
ƙona ruhinsa domin ya samu ƙarin ƙarfin Izza ya fara
tashi daga jikinta.
Nan take Izzarta ta juye izuwa shekaru ɗari uku da

saba'in da huɗu. Ta bace daga inda take ta bayyana a
gaban Armad. Kana ganinta kasan tayi shirin ko a mutu.
A dai-dai lokacin ne shima Armad Izzarsa takai ɗari da
uku. Lamarinda ya bashi damar miƙewa cikin kwanciyar
hankali ya kuma ɗauki takobinsa ya ja da baya tare da
Nusi yana mai kallon wannan baƙon mutun daya
bayyana.
Shima dai Ikenga yana ganin dirar Uznu Ururu yai tsalle
zuwa baya. Ya kuma ƙurawa wannan ma'aboci Ururu ido.
Tunda Uznu ya dira a filin idanunsa a rufe suke kuma
babu wanda yai motsi. Amma a wannan lokaci ya buɗe
baki ya fara magana cikin wani sauti mai tsananin tsufa
da firgici, "Suna na Uznu Ururu. Gasar Jinzidal ta wannan
shekara tazo ƙarshe, kuma ina mai sanar daku cewa
kowa zai iya tafiya amma banda wannan." Yai nuni da
ɗan yatsansa izuwa Armad.
Tun kafin ya rufe bakinsa Nusi ta fara magana, "Armad
gudu...kada ka tsaya kuma kada ka waiwayo. Zan riƙe shi
anan tsahon lokacin da zaka iya guduwa."
Armad ya tsaya baki a buɗe cike da mamaki yana ƙoƙarin
gane maike faruwa. Amma kan yace komai Ikenga ya tafa
hannayensa ya kuma ɓace daga filin. Ga dukkan alamu
Ikenga yasan wane ne Uznu Ururu.
Armad na nufin tambayar Nusi maike faruwa ya ƙara jin
muryar Ururu, "Indai aka rubutawa bawa adadin
kwanaki, lallai bazai iya shallakewa ba. Tunda dai
halakarku tazo a wannan rana lallai babu wanda ya isa ya
hana hakan a ban ƙasa."
Tun kafin Armad ya gama gane abinda yace, Uznu Ururu
ya buɗe idanunsa a hankalinsa. Faruwar hakan keda
wuya Armad yaga dukkan duniya ta koma baƙa-ƙirin,
tamkar wanda aka rufewa ido ko kuma wanda aka saka
acikin surƙuƙin baƙar duniya. Babu abinda yake gani sai
duhu da kuma wasu ɗugonguna kamar na tawada manya
guda biyu a gabansa. Lallai bada ban zafi da nauyi da yake
ji a jikinsa ba da tuni ya yarda da cewa mafarki kawai
yake.
Wata Izza mai ruɗarwa da rikitarwa ta fara shiga cikin
jikinsa. Babu shiri ya fara ji tamkar ana soke shi da
baƙaƙen wuƙaƙe ta ko'ina. Tamkar dukkan duniya so
take ya mutu, tamkar saiya mutu sannan za'a samu sauƙi.
Lallai babu makawa Armad bai taɓa jin ƙarfin Izza mai
rushe ruhi irin wannan ba. Kai ko ta cikin wannan littafi
bata kaita ba. Lokaci ɗaya kaɗai da Armad ya taɓa jin irin
wannan Izza shi ne sanda yake tare da yayarsa Hidaya
acikin wannan daji.
'Wato wannan Izza ita ce Ururu!' Wannan shi ne kawai
abinda yace acikin ransa kafin yaji numfashinsa ya fara
ɗaukewa.
Nidinne dai Shuraih Usman inkiya
99%

Daga taskar magajin wilbafos
MAGAJIN WILBAFOS
Marubuci: Dr Abdullahi Muhammad Ibrahim
Babi na 49: Uznu Ururu 2
Post by: Shuraih Usman
@shuraih 99%
www.facebook.com/hausaebooks
.
Daga:- Taskar Magajin Wilbafos
A cikin filin nan kuwa tuni ƴan kallo da kowa da kowa
suka ƙame cak, babu mai motsi kuma babu wanda yasan
inda kansa yake ballantana susan mai ake ciki.
Amma bisa mamaki wannan abu da Armad ke gani baiyi
aiki akan Nusi ba. Domin kuwa bawai motsi ƙaɗai take yi
ba, tuni ta zare takobinta ta yo kan Uznu Urúrú da niyyar
ta sare kansa.
Tana ƙarasowa, ta ɗaga takobin ta ta da niyyar saransa,
amma Uznu Ururu ko motsi baiyi ba har saida takobin ta
kusa taɓa jikinsa da kimanin ɗan taƙi, inda a wannan
lokaci ya ƙifta idonsa sau ɗaya kawai. Haka na faruwa
wani baƙin haske mai tsananin duhu tamkar na kabari ya
fice daga cikin idonsa.
Wannan haske na fitowa ya juye izuwa siffar baƙin miciji
mai kimanin tsayi zira'i hamsin. Wanda nan take ya fasa
kai ya buɗe baki ya haɗiye wannan takobi tata. Ai kuwa
haka na faruwa takobin ta fara murmushewa tana
juyawa izuwa toka.
Kan kace meye wannan, wannan miciji ya fara tunkarar
jikin Nusi yana nema ya haɗiye ta. Nusi tayi tsalle ta
koma baya. Amma Nusi na dira a ƙasa wannan miciji ya
juye izuwa ƙatoton al'amudi na baƙin ƙarfe ya kuma yi
kanta.
Nusi ta zare wani allon tsafi ta kuma fara karanto
ɗalasimai wanda suka sa wasu manyan ƙarafa na jan
ƙarfe suka bayyana a tsakanin ta da wannan al'amudi.
Tun kafin ma al'amudin ya ƙaraso Nusi tayi tsalle cikin
fasaha da kwarewa izuwa gefe inda ta ƙara kiran sunan
wani ɗalasimin. Wanda nan take ya saka wani tsiro ya
fara bayyana a gefen Uznu Ururu, kuma kafin Uznu yayi
wani abu tuni wannan tsiro ya zama bishiya ya kuma
ɗaure shi a cikin jajayen rassansa.
Nusi ta tafa hannu wata ƴar ƙaramar tukunya ta koren
dutse ta bayyana a hannunta. Nan take ta fara daka wani
sinadari acikin tukunyar a dai-dai lokacin da wata ƴar
ƙaramar wuta ta kama a ƙasan tukunyar ta kuma fara
soya abinda ke cikin ƙaramar tukunyar.
Nan take wani sauti da wani irin ƙanshi mai kama dana
ƙasan tekun maliya ya fara ɓulɓula yana mamaye ko'ina.
Ba jimawa wani koren ruwa mai danƙo ya bayyana acikin
tukunyar, sannan Nusi bata jira komai ba ta watsawa
Ururu wannan ruwan tsafi.

Dukkanin abubuwan nan sun ɗau lokaci wajen bayani
amma a zahiri baifi daƙiƙa biyu zuwa uku suka ɗauka ba.
Ruwan na taɓa bishiyar

Please Login or Register in order to submit comment