Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

fasaharka,
amma kafin lokacin zan fara da koya maka dabarun
amfani da takobi da kuma fasahar aljanu.
"Kaga dai amfani da aljanu yana buƙatar shekarun izza.
Kuma iyakacin yawan shekarun izzarka iyakacin ƙarfin
fasahar da zaka iya amfani da ita. Da shekarun izza
hamsin da ɗaya da kake dasu baza ka iya wuce mataki na
farko ba daga cikin matakai shida na amfani da aljanu.
Kuma indai...."
Armad na cikin bayani yaji wani yanayin-izza mai
tsananin ƙarfi da buwaya ya tunkaro shi ta baya. Tunda
Armad yake bai taɓa jin irin wannan yanayin izza ba. Idan
a misali zai iya kwatanta girman yanayin-izzar duk daya
taɓa ji a matsayin kofin ruwa ɗaya to wannan izzar takai
girman tekun maliya.
Bawai kuma girman izzar ne yasa Armad ya fara gumi ba,
tsananin zafi da muni da azabar dake cikin izzar ne yasa
Armad yaji tamkar ruhinsa zai fashe.
Kafin Armad yai wani motsi Inara ya faɗi ƙasa sumamme.
Yana juyawa bayansa wani ƙatoton hankaka baƙi-ƙirin
mai ido kwaya ɗaya tak ya kawo masa wafta. Armad ya
manta da cewa zai iya juyewa izuwa walƙiya ya baje a
ƙasa wannan hankaka ya wuce.
Kafin ya miƙe hankakan yayiwo kwana. Cikin sauri Armad
ya kirawo Hannun-Aradu ya fuskanci wannan hankaka.
To amma bisa mamaki sai hankakan ya tsaya cak yana
kallon Armad sama da ƙasa tsahon lokaci kafin daga
bisani ya juya ya ɓace.
Abu na farko daya fara zuwa ran Armad shi ne wani
labari da mahaifiyarsa ta taɓa bashi akan wata ƙabila
wadda aka manta da sunansu. Wannan ƙabila sune asalin
tsafin Sanyin-Babban-Sihiri. Dukkan tsafinsu suna yinsa
da baƙin aljanin-hankaka wanda ake kira da HANKAKAN-
MUTUWA. Acewar wannan labari hatta sarki Eyriyon
Wilbafos da sarki Kuyurussa'ayi Ururu baza su iya sawa
wannan hankaka ya durƙusa musu ba. Shi yasa suka haɗa
ƙarfi da ƙarfe suka halaka wannan ƙabila. Kuma tun daga
wannan rana babu wanda ya ƙara ganin Hankakan-
mutuwa a doron ƙasa. Amma indai Armad ba mafarki
yake ba lallai yau yaga hankakan-mutuwa da idonsa.
**MAGAJIN WILBAFOS
Marubuci: Dr Abdullahi Muhammad Ibrahim
Babi na 96: Shiga Fada
Post by: Shuraih Usman
@shuraih 99%
www.facebook.com/hausaebooks
.
Daga:- Taskar Magajin Wilbafos
**
Koda Armad yaga wannan baƙin hankaka na neman ɓace
masa saiya buɗe ƙofar zobensa na sihiri ya cilla Inara
aciki. Sannan yayi amfani da fasahar Kaban'shísu ya ɓace
daga inda yake tare da bayyana acan nesa dai-dai ƙasan
inda hankakan ke tafiya a sama.
Hankakan na ganin haka ya sha kwana tare da ƙara
azama wajen iyo akan iska yana ƙoƙarin gujewa Armad.
Amma murmushi kawai Armad yayi tare da barin
hankakan yayi nisa kafin ya ƙara yin amfani da ɗalasimin
Kaban'shísu ya bayyana a ƙasansa. Sannu a hankali
Armad yana bin wannan baƙin hankaka sai kawai ganinsa
yayi a kusa da fadar sarki Bihanzin mai dauwamammen
sara. Abin mamaki sai wannan hankaka ya ƙara shan
kwana yabi jikin katangar wannan fada ya nufi yamma.
Armad nada ragowar ɗalasimai biyu kacal saboda haka
ya fara tunanin hanyar da zaibi ya kama wannan hankaka
idan bai tsaya ba. Yana cikin tunani ya hangi hankakan ya
tsaya a ƙarshen katangar ta ɓangaren yamma. Har wani
waiwayo wa yake yana kallon Armad tamkar yana jiransa.
A fusace Armad ya yanke shawarar yadda zaiyi ya kama
wannan hankaka. Ya buɗe baki ya kira ɗalasimin
Kaban'shìsu amma a wannan lokaci saiya canja
maimakon ya bayyana a ƙasa saiya bayyana akan
katangar wannan fadar dai-dai gefen wannan hankaka.
Yana bayyana ya miƙa hannu ya damƙe jelar hankakan
tare da finciko shi da niyyar jefashi cikin zobensa na
sihiri.
To amma bisa mamaki sai Armad yaji tamkar ya finciki
dutsen uhudu. Ko motsi wannan baƙin hankaka baiyi ba.
Hasalima kaɗa jelarsa kawai yake ba tare da ya waiwayo
ya kalli Armad ba.
A fusace Armad ya sanya ƙarfin shekarun izza dubu a
hannunsa ya finciko hankakan dashi. Amma bisa mamaki
ko motsi baƙin hankakan baiyiba. Armad ya haɗe gira
yana tunanin maiya kamata yayi domin dai bazai iya
amfani da hannun-aradu ba a wannan hali. Koba komai
duk wanda yaji ƙarar saukar aradu wajen zai taho yaga
ganshi, wanda hakan zai tona masa asiri.
Armad na cikin tunani yaji jelar hankakan dake hannunsa
ta motsa ta fincike shi. Kafin yayi wani abu hankakan ya
jashi ƙasa daga saman wannan katanga sun faɗa cikin
babban gidan sarautar daular Sisiya.
Saida suka kwashe daƙiƙu suna faɗawa sannan suka isa
ƙas, badan Armad yayi sauri ya juyarda jikinsa izuwa
walƙiya ba da tuni ya karairaye. Kafin ya miƙe hankakan
ya tashi ya gudu. Armad ya tsaya yana nazarin wannan
katanga. Kaurinta yakai ƙafa goma, kuma dukkaninta da
duwatsu aka sarrafa ta. A tsaye kuwa takai zira'i casa'in.
Lallai koda kuɗi ɓarawo bazaiyi ƙoƙarin haura wannan
katanga ba.
Yana cikin haka yaji motsin tafiya daga nesa haɗe da
maganganu wanda sukai kama dana masu tsaron fadar.
Nan take ya rufe ido domin jin yanayin izzarsu da kuma
adadinsu da kuma ta inda suke tahowa. Amma bisa
mamaki abu na farko da Armad ya fara ji wata sanyayyar
izza ce mai ni'ima da faranta rai daga can gefensa
ɓangaren arewa.
Ya waiwaya ɓangaren tare da buɗe ido. To amma wajen
cike da yake da bishiyun goba dana inubi wanda sukai
masa duhuwa tayadda baza'a iya ganin wanda ke ciki ba
daga nesa.
Amma bisa mamaki Armad ya gane waye aciki.
Murmushi kawai yayi tare da nufar wannan waje kai
tsaye. Ƙanshi ne ya fara yi masa sallama, ƙanshin da
yasha banban dana turare. Wannan ƙanshi mutun ɗaya
ne kacal yake da irinsa a duk faɗin duniya.
Armad ya tsaya kimanin taku uku kafin ya ƙarasa. Nan fa
zuciyarsa ta fara bugawa kamar zata fasa ƙirjinsa. Bashi
da cikakkiyar masaniyar maike faruwa amma yaji gumi
na ƙoƙarin kwace masa.
Sanyayyar murya wadda Armad ƴasanta sarai ita ce tayi
masa sallama. "Mai yasa ka tsaya?"
Armad ya fashe da murmushi ba tare da yasan dalili ba,
ya amsa da cewa, "Mai yasa kike tsaye a duhu?"
Muryar ta amsa masa da cewa, "ka bani kunya daka kasa
kama hankaka guda ɗaya tak."
Armad ya fashe da dariya yana cewa, "dama ke kika
turoshi. Nasan zaki aikata. Amma meye alaƙar ƙabilarku
da Hankakan-mutuwa?"
Muryar taja dogon numfashi tare da yin ƴar ƙaramar
dariya sannan ta fito daga cikin duhun. Kyakkyawar sura
wadda babu kamarta ce ta bayyana. Wato gimbiya Zahra
wadda aka fi sani da Nostaljiya Nára.
"Baka yarda zoben dana baka ba kenan."
Armad ya kalli zoben dake hannunsa sannan ya ɗago kai
ya dube ta ya ce, "kona mutu dashi za'a binne ni."
Nostaljiya na sanye da doguwar riga mai kwalliya da
bezar gashin farin aku. Jikinta kamar lokaci na ƙarshe da
Armad ya ganta acikin wancan kogo haske kawai yake
yana bada ƙawa da armashi. Gashinta na kwance har
gadon bayanta babu abinda yake sai sheƙi da ƙanshi.
Babu kalmar da tafi dacewa da wannan gashi illa mudubi
domin tsaf zakai kwalliya kana kallon kanka acikinsa.
Armad ya buɗe baki zaiyi magana sai yaji masu gadin
fadar sun matso kusa saboda haka ya fara lisaafin neman
wajen ɓuya.
Koda Nostaljiya ta fuskanci haka saita jashi izuwa cikin
duhuwar wannan bishiyu. Da farko Armad yayi tunanin
ɓuya zasu yi har sai ma'aikatan sun wuce amma sai kawai
yaga sun wuce izuwa wata siriyar hanya wadda ta ɓulle
izuwa wani shinge mai kama da lambu. Baki a buɗe
Armad yaci gaba da kallon ikon ALLAH a yayinda
Nostaljiya take jansa izuwa tsakiyar wannan fada.
Abin mamaki ko mutun ɗaya basu gani ba a hanyarsu.
Amma idan akai duba da cewa wannan fada gidan
Nostaljiya ce kuma anan ta taso to ba abin mamaki bane.
Ba daɗewa Armad ya tsinci kansa a wani kewayayyan
sashi mai dogayen ɗakuna wanda aka gina bangwayensu
da gilasai da yaƙutu. Dukkan wajajenda suka wuce babu
wanda yakai wannan waje kyau da armashi. Hatta ƙasar
wajen da lu'u-lu'u aka shimfiɗe ta. Nostaljiƴa taja Armad
ɗaya daga cikin manyan ɗakunan dake kewaye da wajen.
Suna shiga Armad ya tsinci kansa akan wani farin gilas da
ruwa garai-garai yana gudana a ƙasansa. Kifaye masu
haske kyawawa suna ta wasa acikin ruwa. Daga can gefe
kuma wani ƙasaitaccen ƙaton gado ne wanda zai iya
ɗaukan mutun aƙalla hamsin. Armad yai duba izuwa
manyan gilasan da suka kewaye ɗakin inda ya hango wani
ƙasaitaccen lambu a bayan ɗakin. Wata iska mai armashi
na ƙarawa yanayin ni'ima. Nan take Armad ya
tabbatarwa kansa bai taɓa tsintar kansa a waje mai
kyawu da armashi irin wannan ba a rayuwarsa ta duniya.

MAGAJIN WILBAFOS
Marubuci: Dr Abdullahi Muhammad Ibrahim
Babi na 97: Sammaci
Post by: Shuraih Usman
@shuraih 99%
www.facebook.com/hausaebooks
.
Daga:- Taskar Magajin Wilbafos
**
**
Nostaljiya ce fara magana. "Ka jira ni anan ina zuwa."
Sannan ta fice cikin sauri, tun yana hangen jar doguwar
rigar data saka har ya daina. Ajiyar zuciya kawai yayi
sannan ya faɗa kan wannan hamshaƙin gado wanda
tunda yake bai taɓa yin arba da kamarsa ba a tsahon
rayuwarsa.
Abu kamar wasa jikinsa na dira akai ya nutse cikin laushi
ai kuwa sai bacci ya ɗauke Armad. Yayi ta sharar bacci
tsahon lokaci har saida rana ta faɗi. A lokacinda yaji
muryar Nostaljiya na tashinsa. Da kyar ya buɗe ido yana
gani hazo-hazo har dai ya wartsake.
Bayan Nostaljiya Armad ya kula cewa akwai wasu kuyangi
guda bakwai duk sanye da kaya ruwan kasa iri ɗaya sunyi
sahu suna ta shigo da kayan ci da sha. Ƙanshi ne kawai
yake tashi a ɗakin.
"Ka tashi kayi wanka kaci abinci. Mahaifina yana so zaiyi
magana dakai."
Da akwai ragowar bacci a idon Armad amma koda yaji
abinda Nostaljiya tace saiya miƙe zumbur gami da fara
gumi. Ko sirikinka yawon bola yake akace zaku gaisa
dashi sai kaji zufa ballantana ɗaya daga cikin mafi girman
sarakuna a duniya.
Cikin sauri Armad ya tambaye ta. "Da gaske kike koda
wasa?"
Nostaljiya ta fashe da ƴar ƙaramar dariya wadda ta dace
da karfin ikonta. Bangon ɗakin na ɗaukan sautin
kyakkyawar muryar ta. Nan take Armad yaji tamkar
sarewa ake kaɗa masa. Lamarinda yasa ya faɗa cikin
tunani ya manta da cewa shugaba mai dauwamammen
sara yana jiransa.
"Ka tashi yana jiranka?"
Koda Armad yaga ga dukkan alamu da gaske take saiya
miƙe cikin damuwa ya ce, "lafiya dai ko?"
Nostaljiya ta haɗe rai cike da shagwaɓa. "Nima ban sani
ba."
Armad yai ajiyar zuciya a karo na uku sannan ya fara
tunanin mai Bihanzin zai ce masa. Lallai da matsala.
"A ina zanyi wankan? Kuma ni gaskiya..."
Nostaljiya tayi wa Armad wani kallo mai cike da tsokana
tana cewa, "Kai gaskiya me? Ga ƙoramar wanka can ta
musamman nasa an haɗa maka." Tayi nuni izuwa wani
ƙasaitaccen tafki mai ɗauke da filawowi a samansa. Wani
tiriri ne mai alamun ni'ima ke tashi daga saman ruwan.
Kana gani kasan an shirya shi ne domin wankan manya
ƴaƴan sarauta.
Armad ya juya ya nufi ƙofa yana ta zulumi. Har ya kusa
kaiwa ƙofar sai yaji muryarta. "Idan ka fita kasan ta ina
zaka zagaya?"
Armad ya juyo fuska a murtuke yana cewa, "to kizo ki
rakani mana."
Nostaljiya na ganin yadda yake magana ta ƙara fashewa
da dariya tana cewa, "kaci gaba da ɓata rai saina kirawo
maka yaya Kiru da yaya Hasanu yanzu-yanzu."
Armad ya buɗe baki zaiyi magana amma ya kasa ganin
Nostaljiya ta taho tana rangwaɗa irin ta ƴaƴan
sarakunan farko. Kwata-kwata ya manta dasu Kiru da
Hasanu. Amma a wannan lokaci ya tuno da fafatawarsu
da Kiru shekaru da dama da suka wuce a sanda ya fara
fitowa nemawa mahaifiyarsa lafiya.
Can bayan Nostaljiya ta fara jan hannusa izuwa waje ya
samu ya tattaro kwarin gwiwarsa ya ce, "Kiru da Hasanu?
Da fatan suna nan lafiya? Na daɗe bamu haɗu ba."
Nostaljiya ta amsa da cewa, "ba wani nan. Da yaushe
rabon da ka tambayesu? Kai dai kawai tsoron yaya Kiru
kake ji. Dan kasan yanzu ya ƙara kwarewa matuƙa a
fannin takobi."
Armad na niyyar cewa shima ya ƙara ƙarfin takobinsa
Nostaljiya ta fara jansa da gudu suna sassarfa. Duk
kwanar da suka sha sai sun haɗu da kuyangi suna hidima,
kuma duk wanda duka gansu sai sun zube a ƙasa suna
gaisuwa. Nostaljiya ko a jikinta, Armad kuma tun yana
amsawa harya gaji. Ga dukkan alamu zuwansa shi ne yasa
aka kawo wannan kuyangi da yawa haka domin sanda
yazo babu kowa a wajen.
Suna cikin tafiya Armad yai ciki da wata tukunyar filawa
garin ya kauce mata. Nan take ya fara jan hannun
Nostaljiya yana cewa, "ki daina gudu. Wai wajen wankan
nan tashi zaiyi ne? Kinga ban san hanya ba ina yi muku
ɓarna."
Amma Armad na magana Nostaljiya kawai ƙara jansa
take tana dariya. "Komai ka fasa zan biya kar ka damu."
Tun yana zuƙewa har ya saki jiki suka ringa zagayawa
suna gudu acikin fadar nan suna shewa kamar wasu yara
ƴan shekara goma. Bayan kimanin rabin sa'a suka iso
wajen. Arnad ya waiwaya ya hango ɗakin da suka fito
daga ciki sannan yaga hanyar da suka biyo, nan take ya
gane cewa Nostaljiya na sane ta ringa zagaye dasu ba
gaira ba dalili.
Kamar ta gane mai yake tunani ta ce, "Eh mana. Ina sane
na kewaya damu kaga yanzu kasan hanya baza ka ɓata
ba. Kayi sauri ka shiga kai wanka tun kafin abba ya turo a
ɗaukeka a tafi dakai."
Armad najin wannan kalma ya fara azamar cire kaya zai
faɗa cikin ruwan, amma a lokacin ya tuna tana wajen ya
juya ya kalleta. "Anan zaki tsaya?"
Nostaljiya ta haɗe rai. "Ko baka faɗa ba tafiya zanyi.
Kawai dai kada ka nutse ka mutu ka barni."
Armad ya fashe da dariya a karo na farko yana cewa,
"kamar wata ke. Ɗan wannan ruwan ne zai kashe ni,
mutuwa ta sai anyi shiri."
"Nidai kayi sauri idan ba haka ba zan dawo na fito dakai."
Nostaljiya ta juya ta fice.
Armad ya jira yana murmushi har saida ta ɓace sannan
ya ƙarasa cire kayansa ya afka cikin tafkin ya fara iyo.
Ruwan ya kasance mai ɗumi dai-dai wanka. Sannan yana
bada wani ƙanshi mai inganci. Filawowin kai kuwa na
bada wani sinadari mai kama da sabulu wanda nan take
ya wanke jikin Armad tas. Idan ta shawarar Armad ne
kada ya futo daga cikin wannan daddaɗan ruwa har sai
ya nutsu amma sarki na jiransa.
Ba shiri ya fito ya maida rigarsa. Akan hanyarsa ta
dawowa ya fara tunanin wanne kaya zaisa yaje dasu.
Tambayoyi sama da ɗari suna ta yawo akansa akan
menene dalilin da yasa Bihanzin ke nemansa. Kowanne
dalili ya tuna sai yaji zuciyarsa ta buga. A lissafin Armad
wannan ba wani abu bane illa sammaci.
Cikin ƙanƙanin lokaci ya dawo ƙofar ɗakin daya kwanta
aciki ɗazu. Yana shiga yai arba da Nostaljiya zaune tana
jiransa zagaye da abinci.
"Na baka minti goma ka shirya. Idan ka dawo kaci
abincin."
Armad ya zare ido cikin sauri yana cewa, "Yunwa nake ji
fa."
Nostaljiya ta canja fuska sannan ta fara magana cikin
shagawaɓa. "Yana jiranka fa."
Armad bai san sanda ya sanya kaya cikin ƴan daƙiƙu ba
ya bita suka nufi nufi cikin fadar. Ranar da zaiyi arba da
mai dauwamammen sara tazo.
_______
Yekuwa Manazartar littafin Magajin Wilbafos
Sarki Kurussa'ayi Ururu Sarki Bisa Doron Kasa na daya 1
yana Gaisheku ya kuma ya gaisheku
Sannan yace a sanar daku cewa kwamitin Rubutun
magajin wilbafos karkashin jagorancin Shuraih 99% sun
canja tsarin Posting,
A yanzu za'a runga posting Kullum sabanin zamanin baya
da sai sati sati,
A kowane Rana za'a runga yi maku post Daya,
.
Sako daga shalkwatar Ururu ta doron kasa na Uku,
Sa hannun sarki Kurussa'ayi Ururu, Dhul ururu,Yarima
Dumakisu Ururu,Uznu Ururu, Haruta Ururu,Maruta
Ururu,deniz ururu
______
dafatan za ku bamu hadin kai
99%

Babi na 98: Armad da Bihanzin
**
Haka Armad da Nostaljiya suka yita keta cikin wannan
fada suna wuce manyan gine-gine masu fasali daban-
daban. Nostaljiya na ƙoƙarin yiwa Armad hira amma
hankalinsa baya wajen harta gaji tayi shiru. Bayan wani
ɗan lokaci suka iso harabar wani ƙaton ɗakin taro da aka
kewaye da mutun-mutumin mutane kala-kala.
Nostaljiya ta nuna ƙofar ɗakin tana cewa, "shiga ka jira
aciki ina zuwa."
Armad ya nufi ƙofar ɗakin ita kuma ta kewaya tabi
hanyar da tabi ta bayan ɗakin.
Ɗakin nada madaidaicin girma amma abubuwan dake
cikinsa basu da yawa. Wani ƙaton teburi ne kewaye da
kujeru a tsakiyar ɗakin. Ga dukkan alamu wannan ɗaki
kullum acikin kula yake domin ko ƙura ɗaya babu. Komai
kyalli kawai yake, shi kansa teburin na gilashi ne. Armad
ya ja kujera ɗaya ya zauna yana jiran shigowar mai
dauwamammen sara.
Ba jimawa saiga Hasanu Sisiyu, yayan Noltaljiya, ya shigo.
Fuskarsa babu murna kuma babu ɓacin rai. Ya dubi
Armad ya ce, "kwana da yawa. Da fatan kana lafiya."
Muryar Hasanu na nan ɗauke da ƙarfi da girma irin na
sarakuna. Fuskarsa ta ƙara cika da kamala, kana ganinsa
kasan ba'a zaune yake ba.
Armad ya amsa da cewa, "ina nan lafiya. Da fatan na
same ku lafiya?"
Hasanu ya nemi waje ya zauna sannan ya dubi Armad ya
ce, "bari na baka shawara a matsayi na na abokinka. Kada
kayiwa mahaifinmu ƙarya domin duk abinda zaka faɗa
zai san gaskiya kake faɗa ko ƙarya."
Armad yai murmushi. "Ai dama bana shirin yin ƙarya."
Hasanu ya girgiza kai kafin daga bisani yai murmushi
sannan su koma hirar takobi. Hasanu yayi ta yiwa Armad
tambayoyi akan fasahar takobinsa shima Armad yana
masa har dai suka ji an buɗe ƙofar ɗakin. Wani babban
mutun sanye da doguwar riga ƴar shara ya shigo cikin
ɗakin. Nostaljiya na tafe a bayansa. Yana shigowa Hasanu
ya miƙe tsaye tare da durƙusawa, shima Armad ya miƙe
ya bashi girmansa.
Mutumin na tafiya kamar ba tafiya yake ba, ƙafafunsa na
motsawa cikin isa da iko irinta sarakunan aljanu.
Idanunsa tsaye suke kan Armad yana nazarinsa. A tsaye
zaka iya cewa wannan mutun ragowar samudawa ne
domin aƙalla yakai zira'i ashirin. Wanda hakan ya ninka
tsayin Armad sau wajen takwas.
Yana shigowa ya nufi kujerar da aka tanada domin sa
wacce ke gaba da dukkan sauran kujerun.
Yana zama Hasanu da Nostaljiya suka fice suka barshi da
Armad. Wannan mutun dai ba wani bane illa Bihanzin
mai dauwamammen sara, ɗaya daga cikin sarakuna biyar
na Jinzidal. Mutuminda akai ittifaƙi takobinsa tafi
kowacce takobi ƙarfi a duniya.
A wannan lokaci Armad ya nutsu tare da tsayawa yayi wa
Bihanzin kallo na tsanaki. Bihanzin dai ya kasance mutun
ne wanda kana kallonsa zaka san yayi matuƙar daɗewa a
duniya. Idan kana kallonsa zaka ga tamkar shekarun
ƙarni-ƙarni ne ke wucewa ta ruhinsa. Idanunsa a kafe
suke kuma suna bada wani haske mai ɗauke da firgici da
saka jimami. Fuskarsa nada tsayi da faɗi kamar dukkan
jikinsa, sannan kuma cike take da farin gemu. Gashin
kansa ma fari ne dogo mai tsayin gaske wanda har
bayansa yake taɓawa. Hatta shi kansa gashin girar
Bihanzin a lanƙwashe yake zubin takobinsa.
Rigar dake jikinsa doguwar ƴar shara ce wadda ta bashi
damar saƙale takobinsa a sauƙaƙe. Armad na ganin
takobin nan yaji hankalinsa ya ɗugunzuma, tsigar jikinsa
na tashi. Yanayin-izzar dake kewaye da takobin iri ɗaya ne
sak dana Hankakan-mutuwan da Armad ya gani. Nan take
Armad ya miƙa hannunsa kan takobinsa ba tare da ya
sani ba. Tuni Armad ya manta da inda yake, babu abinda
yake tunawa sai labarin da mahaifiyarsa ta gaya masa
akan waccan ƙabila wadda aka manta da sunanta.
Ƙabilar da tarihi ya nuna cewa saida ƙabilar Wilbafos da
ƙabilar Ururu suka haɗa hannu da ƙarfe sannan suka ga
bayanta.
"Kada ka damu da takobi na. Ita wannan takobin tawa
babu wanda take yadda dashi idanba ƴaƴa na ba."
Muryar Bihanzin ce ta farfaɗo da Armad daga tunanin
daya shiga. Amma duk da haka bai ɗauke idonsa daga
kan takobin ba.
Takobin dai bata da faɗi da yawa amma tafi tsayin zira'i
uku. Lallai ba daban Bihanzi basamude bane da bazai iya
ɗaukanta ba. Abin mamakin shi ne takobin har wani huci
take tana kallon Armad tamkar tana jin mai ake cewa.
Koda Bihanzin yaga Armad bai daina kallon takobin ba sai
yaja rigarsa ya rufe ta yana cewa, "sunan wannan takobi
tawa Bankái. Indai ka biya ta Bankái haka zatai ta
tsokanarka har sai ta jaka izuwa faɗa."
Mamaki ya ƙara rufe Armad yadda yaji Bihanzin yana
maganar takobinsa yana bata suna kamar wata mai rai.
Nan take Armad ya tuna yadda yayarsa Hidaya take yiwa
takobinta magana. A sau da dama Armad yana yaro
yakanyi tunanin ko Hidaya tsokanarsa kawai take amma
takan ce masa takobin ta tana da ruhi nata na kanta
kuma tana ji idan akai mata magana.
Armad yai murmushi na girmamawa sannan ya ce,
"barka da warhaka. Ina fatan ban ɓata maka ƙa'idarka ba
dana shigo fadarka ba tare da izini ba."
Bihanzin yai gyara murya haɗe da girgiza kai, lamarinda
yasa muryar tayi kama da ana goga busasshen ƙashi a
jikin bango. Dama dai muryar Bihanzin kaushi ne da ita,
amma gyaran muryar da yayi shi ne yasa abin ya ƙara
fitowa fili. A wannan lokaci Armad yayi ƙoƙarin jin
yanayin-izzar Bihanzin amma bisa mamaki baiji komai ba
sai wani sanyi mai ratsa ƙashi wanda ya banbanta da
sanyin-babban-sihiri kuma ya banbanta da sanyin
hunturu ko na ƙanƙara. Wannan sanyin da Armad yake ji
yafi dana tsohon kabari. Nan take Armad ya daina
ƙoƙarin jin yanayin-izzar Bihanzin amma duk da haka
saida yaji ya fara rawar ɗari.
Muryar Bihanzin ce ta ƙara farfaɗo dashi. "Kada ka damu,
Magajin Wilbafos, tunda har ka shigo ba tare an kama ka
ba ai gayyato ka akai."
Armad ya zare ido cikin mamakin wannan magana,
domin hakan na nuna Bihanzin na sane da shigowarsa.
Nan take Armad ya buɗe baki zai tambayi Bihanzin amma
sai Bihanzin ya riga shi magana.
"Nakan ji yanayin-izzar abokan gaba tsahon tafiyar
shekara guda tun ina ɗan shekara bakwai. A lokacin da na
cika shekara takwas ina iya banbance mutane na gane ko
su waye ta hanyar yanayin-izzarsu koda nisansu da inda
nake yakai tafiyar shekara guda. Kaga bazai zama abin
mamaki ba dan naji shigowar ka daula ta a lokacin da ka
sauka daga jirgin Fataken-dare."
Armad ya zare ido cikin tsananin al'ajabin ƙarfin izzar
wannan halitta dake gabansa. Lallai ba'a zama sarkin
Jinzidal a banza. Koda yake dama wannan shi ne karo na
farko da Armad yai arba da ɗaya daga cikinsu.
Idan dai har Bihanzin zaiji yanayin-izzar mutun kimanin
nisan tafiyar shekara guda kuma ya gane waye, lallai babu
wanda ya isa ya shigo wannan daula ba tare da saninsa
ba. Kuma lallai ba abin mamaki bane dan Bihanzin yasan
Armad shi ne Magajin Wilbafos.
Kai tsaye Armad ya bugi ƙirji ya tambayi Bihanzin. "Mai
kake buƙata daga gareni daka bari na shigo?"

Chapter 99 & 100
MAGAJIN WILBAFOS
Marubuci: Dr Abdullahi Muhammad Ibrahim
Babi na 99: Armad da Bihanzin part 2
Post by: Shuraih Usman
@shuraih 99%
www.facebook.com/hausaebooks
.
Daga:- Taskar Magajin Wilbafos
"Hmm... " Bihanzin yaja dogon numfashi sannan yaci
gaba da bayani. "Wilbafos kai kake neman wani abu a
waje na ba ni nake nema a wajenka ba. Zaka sauƙaƙa
mana wannan tattaunawa idan ka gayamin hakikanin mai
ya kawo ka daula ta."
Armad ya sunkui dakai yana tuno asalin abinda ya
kawoshi wannan daula. Koma meye a bayan samarwa
mahaifiyarsa lafiya yake kuma lallai abinda kawai ya kawo
shi kenan. "Nazo neman shekarun izza domin yiwa
mahaifiyata wadda take fama da cutar izza magani."
Bihanzin ya danyi shiru kafin daga bisani ya ce, "Naji
labarin cewa abinda ya fito dakai daga gida kenan
shekaru uku da suka wuce. Indai wannan ne kaɗai
buƙatarka to babu matsala, a yanzu zan warkarda
mahaifiyarka. Koba komai bai wuce biyan bashi ba,
domin har yanzu bamu biyaka fassarar dakai mana ba a
waccan shekara."
Armad ya zare ido tare da miƙewa tsaye cikin murna
yana cewa, "da gaske kake? Lallai idan ka samarwa
mahaifyata lafiya bani da yadda zanyi na iya sakamaka.
Nagode."
Bihanzin ya ɗaga hannu yana dakatar da Armad alamun
bai gama magana ba. "Nasan akwai soyayya tsakanin ka
da ƴata Nostaljiya, kuma bazan ce maka ka haƙura ba
indai kana sonta, amma akwai abu guda ɗaya da nake so
ka sani." Koda Bihanzin yazo nan a zancensa sai ya dubi
Armad a nutse domin ya tabbatar yana tare dashi sannan
yaci gaba.
"Shi CIKAKKEN MUTUN shi ne wanda yake ɗaukan alhakin
abu idan yasan shi ya jawo shi. Nostaljiya ta ɗau alhakin
abinda ta aikata a wajen cinikin bayi kuma taƙi yadda a
ɗora maka laifi. Idan za'a wanke ta a idon duniya to sai
dai ta yadda ta auri Deniz Bizaya wanda a zahiri ba shi
take so ba. To amma idan bata aure shi ba, hukumar
Jinzidal zata yanke mata hukunci. Hatta ni kaina a matsayi
na na babanta bazan iya kare ta daga sauran sarakunan
Jinzidal ba, kuma idan na hana ayi mata hukunci, yaƙi ne
zai afku. Idan kace kana sonta, shin zaka iya zama
cikakken mutun ka ɗauki alhakin komai a kafaɗunka ka
kare ta, kuma ka shiga yaƙi saboda ita? Idan dai har zaka
iya wannan to ka cancanci ƴata, amma idan baza ka iya
ba to ka manta kawai. Biyo ni." Bihanzin ya miƙe ya nufi
ɗaya daga cikin ƙofofin dake kewaye da wannan ɗaki,
Armad na biye dashi.
Bihanzin na tunkarar ƙofar ta buɗe, Armad ya tsinci
kansa a wani ƙaton fili mai yawan rairayi. Abin mamaki
iskar dake kaɗawa acikin wajen ta banbanta data cikin
dakin daya baro, tamkar wata duniya ta daban suka
shiga. Take saboda sanyi Armad ya tuna da cewa yana da
kayan sanyi a ajiye acikin zobensa. Amma kafin ya fito
dasu sai kwatsam yaji yanayin ya fara canjawa, rairayin
ya fara ɗaukan zafi kamar ana kunna masa wuta. Kafin
kace meye wannan gumi ya fara gudu a fuskar Armad.
Suka ci gaba da tafiya Bihanzin bai ce masa komai shi
kuma bai tambaya ba. Amma abu kamar wasa taku
bakwai bayan an fara zafin kawai sai ruwa ya ɓarke
kamar da bakin kwarya.
Armad ya tsaya ido a zare yana mamaki. Lallai akwai abin
al'ajabi a tattare da wannan waje. Kuma tashin hankalin
shi ne bai san inda Bihanzin yake ƙoƙarin kaishi ba. Yana
cikin tunane-tunane yaji murya Bihanzin, "A cikin
wannan waje duk bayan minti ɗaya yanayi yake canjawa.
Kaga maimakon zafi da sanyi da damina da rani kowanne
yazo a shekara sau ɗaya, kowannensu a wannan waje
yana zuwa a kowacce rana sau dubu uku da ɗari shida.
Acikin wannan waje nake ajiye wani kaso daga cikin
shekarun izza ta na kwangila ta. Ban san shekara nawa
mahaifiyarka take buƙata ba amma nayi maka alƙawarin
bata shekarun izza dubu goma zuwa ashrin. Fito da ita ka
ajiye ta anan."
Bihanzin ya nunawa Armad tsakiyar yashi inda ruwa ya
ɗan taru. Da farko Armad ya fara mamakin yadda akai
Bihanzin yasan mahaifiyarsa na cikin zoben dake
hannunsa amma kuma ya tuna komai ma zai iya faruwa
indai ana maganar sarki Bihanzin sabida haka babu wani
abin mamaki. Nan take Armad ya futo da mahaifiyarsa
sanye cikin fararen kaya kamar tana bacci. Amma yaƙi
yadda ya ajiƴe ta a ƙasa har saida Bihanzin ya tafa
hannunsa wani gado ya bayyana.
Bayan wasu ɗalasimai da Bihanzin ya kira a zuci sai kawai
wani ƙatoton shaiɗanin aljani ya bayyana. A tsakiyar kan
aljanin akwai ƙahunhuna guda

Please Login or Register in order to submit comment