Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

halartar Deniziyya Kurónikil.
Wasu sune zasu shiga da kansu, wasu kuma ƴan rakiya
ne, wasu kuma manyan baƙi ne.
Tuni mutane suka fara bin layi, suna biyan kuɗin shiga
inda za'a haɗa su da wani Badenize dake wajen ya faɗa
dasu cikin ɗaya cikin ramikan dake kewaye dasu.
Kowa ka gani sanye yake da kaya daban-daban, kai kasan
daga ƙasashe daban-daban suke.
Kafin jimawa da dama daga cikin waɗannan jama'a sun
shige cikin waɗannan ramika, izuwa cikin wannan gari.
Daular Denizawa zaka iyai mata kallon kamar wani
ƙatoton gari ne mai tsananin girman ƙasa.
Wanda acikinsa akwai birane manya guda biyar.
Birane huɗu sune a zagaye da wannan gari guda ɗaya,
wanda ya kasance a tsakiya, kuma ya ɗan haurasu girma.
Sun tsara ginin kowanne gari ne, yadda zai zamo, a
kewayen kowanne gari, akwai ƙaiyadaddun adadin
ramika dake kewaye dashi, wanda kuma ta ciki ne,

mutane ke ɓullowa bayan sun shiga ta waɗannan dajika
na waje.
A kewaye da waɗannan birane huɗu, dazuka ne kala-kala,
iri-iri, wanda girman ƙasar da suka ci, shi kaɗai ya haura
girman gaba ɗaya garuruwan nan guda biyar.
Sannan kuma a kewaye da waɗannan dazuka kuma
katanga ce, wadda akayi da wani sinadari na musamman,
shidai ba ƙasa ba kuma dutse ba, ba kuma ƙarfe ba!
Katangar nada girma sosai, tayadda baka iya gano
ƙarshenta dama da hauni, sama da ƙasa.
Acikin wannan gari dake tsakiyar garuruwan nan, akwai
wani ƙaton fili wanda ya kasance a kewaye.
Idan ka shiga cikinsa zaka ga cewa yama fi yadda kake
tunani girma.
Daga farkonsa a zagaye yake da kujerun zama na alfarma
waɗanda yawansu bazai lissafu. Idan kai musu kallon
farko abinda zaizo ranka shi ne, komai yawan mutane
zasu iya ɗebe su.
Daga cikin filin kuwa wasu ƴan ginannun wajaje ne ƴan
ƙananu waɗanda suma suna da ɗan yawa kuma suna
gaban waɗannan kujeru na farko.
Daga tsakiyar filin kuma wani ƙatoton fili ne wanda akai
masa tsarin filin danbe, kuma aka kewaye shi.
Kai daka gani kasan wannan fili yaga fafatawar Mazan
jiya.
Domin duk da sabon mashimfiɗi aka lulluɓeshi dashi ta
kowanne ɓangare, hakan bai hana kaji yanayi mutuwa na
tashi daga jikinsa ba.
Akwai fitilu na musamman dake kewaye da wannan filin
na tsakiya suna bada haske mai ba sha'awa da sawa kaji
marmarin yaƙi na tashi acikin ranka.
Duk da cewa babu kowa acikin filin tsakiyar, daga cikin
waɗannan ƴan ƙananun wajaje kuwa waɗanda basu da
nisa sosai daga filin tsakiyar akwai mutane kusan acikin
guda shida daga ciki.
Kana gani zuciyarka zata baka cewa waɗannan sune
mutanen da suka zo daga sauran manyan kabilun nan da
sauran ƙasashe.
Wani abu mafi ban mamaki da ba'a ambata shi ne, wani
ƙaton gini daya tashi ta ɓangaren gudu maso yammacin
wannan fili na tsakiya. Wanda ya kasance shi ne waje
mafi kusanci da filin tsakiyar. Gilashi ne ke kewaye da
wurin baki ɗaya, tayadda ana iya ganin komai dake ciki.
Kuma a wannan lokaci zaka iya hangen kujeru na alfarma
waɗanda yawansu bai wuce goma sha ba aciki.
Akan waɗannan kujeru kuma dake zagaye da duk filin,
mutane ne da dama, ana ta mayar da labari akan ire-iren
waɗannan gasanni da suka gabata.
Amma duk wannan kaɗan ne idan ka kwatanta da yawan
mutanen dake tsattsaye a bakin ƙofar shigowa wannan
waje.
Babu abinda kake ji sai hayaniya akan suna yen taurarin

da ake saran zasu buga wannan gasa.
Kuma ga dukkan alamu waɗanna mutane sun san
taurarin nasu basa wajen, wanda hakan nema ya sasu
fitowa bakin ƙofar domin kallon sanda zasu shiga.
A dai-dai wannan lokaci saura ƙasa da awa ɗaya a fara
wannan gasa, a yadda aka ƙayyade lokacin farawar.
Ana cikin hakan ne wani saurayi ya bayyana, mutun
bakwai na bayansa, dukkansu sanye da kaya mai fari da
yalo.
Tun daga nesa wasu daga cikin waɗannan mutanen daje
jira suka fara nunashi.
Koda jama'a suka kyalla ido suka ganshi, sai kuwa
hayaniya ta ƙara tashi. Babu abinda kake ji sai, ''kai.......
aikuwa da gaske ne!!!
''Kai..ka...kai....., wannan karan hardasu, lallai za'a sha
fama.
''Wallahi shi ne!!!'' Can daga cikin taron waɗannan
mutane, wani yaro mai ƙarancin shekaru, yana tsaye a
ɓangaren arewa, babu abinda yake sai jan rigar wani
dattijo Badenize, ya na tambayarsa, ''baba wanene? Baba
wanene?''
Baban ya waiwaya, gami da cewa, ''ƴan ƙabilar Hán, daga
doron ƙasa ta uku!
''Kuma ina kyautata zaton wancan yaron na gaba shi ne
Hán-na-bakwai, wato Hán-Amuru, ko kuma sunansa
cikakke Hanamúru Zulkiflu!!''
Kafin wannan dattijo ya gama bayani muryarsa ta fara
rawa, kamar wanda yake tuno wata azaba.
Kamar yaron ya fuskanci maike faruwa da sauri ya ce,
''shikenan baba na gane!''
A dai-dai wannan lokacin wannan tawaga suka zo suka
wuce, suka shiga cikin wajen.
To kamar yadda tsohon ya faɗa dai haka ne, wannan
tawaga data wuce daga ƙasa ta uku suke, kuma wannan
yaron shi ne, Hánamuru, wanda akewa laƙabi da Hán-nabakwai.
Shima yazo wannan gasa, kuma tuni suka gabatarda
adadin bayi dubu goma ga Jinzidal kamar dai yadda
sauran ma daga sauran ƙasashe suka kawo.
Ana cikin hakane waɗannan mutane suka ƙara ruɗewa
zaka hango kusan tawaga har guda uku tana tafe.
Kan kace meye wannan tuni shewa da ihu mai cike da
murnar gani gwanayensu ta cika wajen.
Kusan zaka iya cewa duk cikin garin nan ana jin wannan
ihun.
Nan take maganganu suka fara tashi, ''Shugaba yarima
Bizaya!!
''Ah! ga Ikenga O. Bayajidda can ma!!
''Ga kuma hmmmm....Maikironomada!!''
Tawaga ta farko mai ɗauke kusan mutum sha biyar,
dukkaninsu sanye da fararen kaya, ita mutanen keta
nunawa

suna murna gami da kiran sunan 'Bizaya'!
Ya biyun kuma wadda ita ce mafi ƙanƙanta, mutane uku
ne kawai, dukkaninsu sanye da kaya masu baƙi da
ɗorawa. Kuma ita ake nunawa ana kiran sunan Ikenga.
Sai kuma ta ukun wadda ke ƙunshe da kusan mutun
goma, waɗanda mafiya yawansu kaya daban-daban suka
sa.
Kuma wani abin mamaki duk da irin girman wannan
ƙabila ta Maikironomada, waɗannan mutane dake wajen
basa nuna wani buri akansu.
Hasalima tuni sun ɗauke kansu daga garesu, suna ta
ɗagawa Bizaya da Ikenga hannu sunai musu fatan
alkhairi.
Bayanda aka gama sallamar tawagar Bizaya da Ikenga,
kuma aka basu shedar shiga da kuma wajen da zasu tsaya
idan sun shiga, sai da dama daga cikin mutanen nan dake
tsaye suma suka juya baya suka rufa musu baya, ba tare
da ko damuwa da ƙarasa kallon tawagar Maikironomada
ba!
Tundai abin baya damun ƴar tawagar, har takai wasu sun
fara tsaki.
To amma a dai-dai wannan lokacin ne wata tawaga guda
biyu suka doso wajen, kuma duk da nisan da suke dashi
kafin su ƙaraso, tuni ƴan tsirarun da suka rage sun fara
nunasu da hannu suna kwalawa, ''Kaiiiiii......kai wannan
shekarar Infiriya Yarima Niyashi suka turo, lallai, wataƙila
za'ai Deniziyya Kurónikil ɗin da ba'a taɓa yi ba!
''Wallahi shi ne!! Yarima Niyashi, mashin mutuwa!!!
''Kaiiii! Ku duba gefe ga tawagar Banfiriya can ma!!
''Dama su a duk shekara yarima suke turowa!!!!
''Kaga wannan shekara yarima Kiru suka turo!!
''Shi ne yayan gimbiya Nostalgia!!
''Oh...Zahra Kyau!! Kana tunanin kuwa tana cikin
waɗancan Babysawan uku dake cikin tawagar tasa!!''
Kan kace kwabo, tuni irin waɗannan maganganu sun cika
wajen.
Kuma waɗannan mutane da da suka juya baya suka fara
tafiya, yanzu sun dawo, wasu ma har gudu suke suna
tunkuɗe mutanen dake shiryen-shiryen shiga ƴan
tawagar ƙasar Maikironomada!!! Lallai mutanen wajen
basu da wani gwani Maikironomada, ko mai yasa?
Nidinne dai Shuraih Usman inkiya
99%
Daga taskar magajin wilbafos
MAGAJIN WILBAFOS
Marubuci: Dr Abdullahi Muhammad Ibrahim
Babi na 31: Na daya dana karshe
Post by: Shuraih Usman
@shuraih 99%

www.facebook.com/hausaebooks
.
Koda waɗannan ma'abota Izza guda shida suka tsaya, sai
kowa acikinsu ya buɗe baki tare da furta waɗansu
ɗalasimai waɗanda suka shafi al'amarin Izzarsa.
Dukkaninsu nada cikakkiyar amanna cewa lallai
waɗannan ɗalasimai nasu sunfi ƙarfin kowa dake cikin
zagayen karawarsu. Badan komai ba saidan cewa a
wannan gasa zance ne na waye ya riga gamawa. Domin
suna da cikakkiyar masaniyar cewa acikin waɗanda sukai
nasara guda shida daga kowanne zagaye, guda huɗu
kaɗai za'a ɗauka suje zagaye na gaba. Waɗannan kuma
sune wanda suka riga sauran gamawa.
Musamman duba ga cewa da dama daga cikin waɗanda
suke kwabzawa dasu a rukunin nasu basu kaisu ƙarfin
Izzarsu ba. Saboda haka mutun shidan nan suna da
amanna sai sunyi nasara a rukuninsu, kawai dai kowa
yana ƙoƙari ne ya riga sauran ƴan uwansa gamawa.
Saboda ƙarar karan batta dake faruwa da ihun mazaje
suna fafatawa a cikin dukkanin wajajen shida, babu
wanda ya kula da abinda suke aiwatarwa, kusan kowa ya
takansa yake. Kowa so yake ya samu nasara ko ya samu
ya tseratsarda ƙannensa da ƴaƴansa da abokansa da
iyayensa daga zama bayi. Domin rashin yin nasararsu
tana nuna kason mutanen da suka kawo sun zama bayi
kenan a wajen wanda yayi nasara.
A dai-dai lokacin da waɗanann samari shida ke ƙoƙarin
aiwatar da munanan hare-hare akan ƴan uwan
fafatawarsu, kowa ka gani idonsa a rufe yake. Babu
abinda nakan filin dagar nan suke sai saran junansu, jini
na malala, kayika na tsalle sama. Amma tamkar ba ɗan
adam ake kashewa ba, ma'abota kallon fafatawar nan
kawai sai ihu da jin daɗi da shewa suke daga kan
kujerunsu da suka zagaye filin wasan. Kai daka gani kasan
sun saba gani kuma wannan ba wani sabon abu bane.
Ana cikin haka saurayin dake rukunin E, wanda babu
makami a hannunsa, ya tafa hannayensa guda biyu!
Suma sauran samarin kawai sai wani shuɗin haske ya fara
tashi daga jikinsu, lamarinda ta fara jan hankalin wasu
daga cikin masu fafatawar da kuma da yawa daga cikin
ƴan kallo.
Abu na gaba kuwa da aka gani a kowanne rukuni ya bada
matuƙar mamaki, wanda saida yasa dukkanin wanda ke
kallon wannan gasa acikin wajen ko kuma a waje ta
hanyar Ayrid mai nuna hoton bidiyo, buɗe baki da shiga
mamaki mai haɗe da firgici.
Bayanin dalla-dalla abinda ya faru ba abu bane mai
yiwuwa ba, domin komai ya faru ne cikin rabin ƙiftawar
ido kuma a tare. Sannan kuma ga wannan shuɗin haske
ya ƙaru matuƙa tayadda ya haskewa mutane da dama
idanu.
Ga kuma wani wuta jajawur datai ƙuwa tare da tsalle

sama ta kuma haske ilahirin filayen fafatawar nan guda
shida. Lallai akwai ma'abocin aljanin wuta a ɗaya daga
cikin waɗananan filaye.
Bayanda wannan wuta da wannan shuɗin hasken suka
gauraye suka bada wata irin kala mai ban tsoro, suka lafa,
sai mutane sukai arba da filaye guda shida. Kowanne
babu kowa a tsaye sai mutun ɗaya; A rukunin A, wani
saurayi ne riƙe da wata doguwar takobi da tama fishi
tsayi. Yana sanye da kaya masu zanen ɗorawa da baƙi.
Fari ne mai yawan baƙin gashi. Idanunsa a tsaye suke,
sannan kuma idan kayi duba cikinsu babu abinda zaka
gani sai azabar tsana da kafiya, kai kace duk wata tsana da
fushi da baƙin cikin duniya daga cikin waɗannan idanu
suka samo asali.
Fatar fuskarsa kuwa a ɗame take, kana gani kasan yayi
shekaru da dama baiyi dariya ba.
Kallon ɗaya zakai masa ka gane cewa a lokacin yana yaro
kyakkyawa ne, kuma kuma har a wannan lokacin idan ka
kalli yanayin zubin hancinsa da fuskarsa kasan irin kyan
nan ne da baƙin ciki da ɓacin rai yake lalatawa.
Kaf tsokar jikin wannan saurayi a murɗe take, kai kace
basu taɓa motsi ba.
Irin waɗannan mutananne da idan aka ce kayi bayaninsu
a kalma ɗaya zuwa biyu, zaka ce, 'rashin imani', kawai ka
rufe baki!
Idan kuma ka kalli mutanen dake kwance a ƙasa acikin
rukunin zaka tabbatar da haka.
Domin kuwa dukkaninsu ƙirjinsu a cake yake da
makamai, kuma abin mamakin shi ne, makamansu ne
kuma hannayensu ne suka daɓa musu su a ƙirji.
Kaf ɗinsu sama da mutun talatin gasu nan a kwance a
ƙasa matattu!
Wannan saurayi ba wani bane illa Ikenga O. Bayajidda!
Ba jimawa ƙasar filin rukunin na A ya fara haske, kafin
daga ƙarshe ya nuna alamun daƙiƙa ashirin da tara.
Wato alamun cewa Ikenga ya gama a tsahon daƙiƙa
ashirin da tara kenan. Koda wannan haske ya ɗauke sai
Ikenga ya ɗaga ya ɗanyi wani murmushi mai cike da
nufaƙa. Ɗaga kan nasa kuma ya ƙara bayyanarda wani
ƙaton tabo a wuyansa.
A rukunin B kuwa wannan saurayi mai riƙe da takobi
wadda bata fi tsayin hannunsa ba, da kyalle a goshinsa
shi-shi kaɗai ne a tsaye.
Kuma idan ka kalleshi sosai zaka ga ba wani bane illa
Armad Wilbafos. Wanda bai samu hankalinsa ya kwanta
ba saida yasa kyalle ya rufe goshinsa duk da kuwa
Miyurar tasa ta ɓace kuma baisan inda tayi ba. Amma
kasancewar kyallen a goshinsa yana ɗan sawa yaɗan
manta na ɗan lokaci. Tuni Armad ya yanke acikin ransa
cewa duk ma inda wannan Miyura ta tafi lallai saiya nemo
ta. Domin yafi kowa sanin amfanin ta. Koba komai tana
ƙara masa ƙarfin Izzza, kuma da dama daga cikin fasahar

walƙiyarsa suna buƙatar babbar Izza, wadda kuma bashi
da ita. Amma ta dalilin wannnan Miyura bashi da matsala.
A kwance a ƙasansa ragowar ƴan rukuninsa ne suke ta
murƙususu amma babu wanda ke iya tashi, saboda haka
bayan ƴan daƙiƙu shi ma wannan haske ya bayyana,
wanda ya sa masa alamun daƙiƙa talatin da biyu, wato
ƙarin daƙiƙa uku kenan akan na Ikenga.
A rukunin C kuwa babu kowa akan gaba ki ɗayan filin.
Dukkansu kamar ansa tsintsiya an sharesu zuwa ƙasa.
Babu kowa sai wani saurayi mai yawan gashin fuska, riƙe
da fafalo mai lanƙwasa.
Sannan hasken dake tashi na nuna daƙiƙa talatin dai-dai.
Saurayin nada faɗi da yawan gaske, hakan nema yasa duk
da cewa bawai gajere bane kuma ba dogo bane, amma
da dama sai a ringa yi masa kallon gajere. Lamarinda bai
masa dadi Ko Kadan!
Amma kuma wani abu dashi shi ne, fuskarsa bata da faɗi
sosai, sannan kuma baka buƙatar a gaya maka cewa
tsatson wannan saurayi ma'abota sarauta ne.
Domin a duk cikin waɗannan samari, da wuya ka samu
mai yawan kyawunsa da kuma fitarda kamalar sarauta.
Wani ƙarin abu ga fuskarsa shi ne, saboda yawan gashin
dake fuskarsa sa, gashin girarsa ma a haɗe suke, wanda
hakan ya bashi kamanni na daban, kuma da dama suna
ganin abinda ke rage masa kyau kenan!
Amma duk da wannan, babban abinda zaisa idan ka kalli
wannan saurayi baza ka taɓa mantawa dashi ba shi ne
idanunsa.
Babu komai acikinsu face tsananin azabar masifar
marmarin yaƙi!! Irin soyayyar nan da baza ka iya rabuwa
da abu ba, irin ta sak zaka gani acikin idonsa, amma ba
soyayyar komai bace ba illa yaƙi.
Wannan saurayi ba wani bane illa Deniz Bizaya! Ɗan sarki
Deniz Iluru.
Saboda tsananin sansa da yaƙi, ance kullum yana cikin
gwabzawa, har nemo abokan fafatawa yake a kullum
ƙasa zuwa ƙasa, kuma hakan nema yasa suka saba da
Ikenga! Idan mai Karatu bai mantaba an gano su suna
fafatawa kwanaki kaɗan kafin a fara wannan gasa. Koya
waɗannan giwaye suka ji, domin dai ga dukkan alamu
basu samu damar haɗiye su ba. Tunda gasu acikin filin
daga.
A rukunin D kuwa, saurayi ne riƙe da mashi a hannunsa,
kuma kana ganinsa, zaka san cewa ransa ɓace yake kuma
acikin zuciyarsa akwai ɓacin rai na rashi!
Amma kuma idan ka lura zaka ga wannan ɓacin ran
baishiga cikin ƙashinsa ba kuma baikai irin ƙiyayyar dake
zuciyar Ikenga ba!
Fuskarsa babu gashi ko guda, kuma kyakkyawa ne, fari fat
dashi kamar fulanin farko!
Idan ka duba ƙasansa zakai arba da yuyar mutane
kwance fululu!

Amma abin mamakin da wannan rukuni shi ne, dukkanin
waɗannan mutane dake kwance, idan ka lura zaka ga
cewa da dama daga cikin waɗannan mutane waɗanda da
suka kasance farare, amma a wannan lokaci suna ƙasa
fatar jikinsu ta sauwa izuwa shuɗiya!!
Sannan ragowar kuma waɗanda suke baƙaƙe, su kuma
sun ƙara baƙi sosai matuƙa, tayadda kana ganinsu zaka
gane cewa sun canja.
Amma bisa mamaki, duk wannan abin hasken dake tashi
daƙiƙa talatin da biyu shima yake nunawa, wato kamar
na Armad.
Babban wajan al'ajabin shi ne rukunin E, inda babu
abinda kake ji sai ihun mutane waɗanda rashin sa'a ya
tadda su, domin kuwa a wannan lokaci idan ka kallesu
zakai arba da cewa acikin wata jar wuta suke muraran
suna soyuwa!!
Duk inda ka kalla sai kaga wannan wuta ce a jikin
mutanen, sannan kuma sun kasa motsawa a wani yanayi
na kamar ta ɗaure su da ƙasar wajen, ta yadda ko motsi
basa iyayi.
Kuma abin mamaki shi ne, hasken dake tashi yana nuna
masa daƙiƙa ashirin da takwas ne, wato ƙasa dana Ikenga
ma.
Kuma duk da abinda ke faruwa, murmushi ne kawai a
fuskar wannan yaro.
Sai kuma wani abin al'ajabi idan ka kalli idanun wannan
yaro mai suna Han Amuru wanda bai wuce shekaru sha
shida ba, zaka alamun aljanin wuta yana balbali da wuta.
Kai kace idanun sun ƙone gaba ɗaya. Sai dai kuma amma
saboda wannan aljani nasa ma'aboci wuta, shi baya jin
zafin wutar ko kaɗan. Ko kuma ace shi bata aiki a kansa.
Wannan saurayi shi ne yazo daga ƙasa ta uku. Wato
mahaifar Armad kenan. Kuma daga ƙabilar Han, wato
ƙabilar babban sarkin ƙasa ta uku kenan.
A rukunin F kuwa wani saurayi ne tsaye da takobi mai
hasken gaske, kai kace walƙiya ce saboda yadda take
haskawa.
Yana tsaye, kuma duk inda ka duba, idan banda wajen da
yake tsaye akai, zaka ga ya rududduge ya zama gari, duk
sauran abokan karawar tasa na ƙas.
Wato dai a taƙaice shi kaɗai ne akan wajen da aka
ƙaiyaje!
Ya riga ya gama fashe ko'ina, kuma sauran abokan
fafatawar tasa suna tsaye a zagaye dashi a ƙasa, amma
haka zasu haƙura, babu abinda suka iya saidai kallo.
Domin an riga an cire su saboda sun fita daga kan
kewayen.
Idan ka dubi wannan saurayi sosai zaka ga ashe ba wani
bane illa Kiru Sisiyu, yayan Zahra! Kuma duk yadda akai
yayi amfani da farar takobi. Wadda idan mai karatu bai
manta ba ta kusa halaka Armad a baya.
Amma fuskar Kiru bata nuna alamun komai, ko kaɗan.

Wato dai bata nuna farin ciki, ba kuma ta nuna baƙin ciki,
tamkar babu wani abu da yake tunani acikin zuciyarsa!
Idan da Armad zai ganshi a wannan lokaci kuma ya tuna
da yadda ya sanshi, to da lallai saiya sha mamaki.
Hasken dake tashi daga ƙasansa na nuna daƙiƙa talatin da
biyar.
Bakin ƴan kallo a buɗe yaƙi rufuwa. Kai hatta shi kansa
alƙalin wasan bakinsa a buɗe yake, idanunsa na cike
firgici.
Can bayan wasu ƴan daƙiƙu ya dawo hayyacinsa inda ya
bayyana cewa, da Ikenga mai ashirin da tara, da HánAmuru mai ashirin da takwas, da kuma Deniz Bizaya mai
talatin da ɗaya duk sun wuce zuwa zagayen kusa dana
ƙarshe.
Amma Armad da Kiru da Niyashi duk sun sami maki iri
ɗaya wato talatin da biyar, saboda haka, abisa dokar
Deniziyya za'a kawo musu Alkadar domin fitar da gwani.
To a wannan lokaci ne aka tafi hutun lokaci, kafin a dawo
a fitarda gwani a tsakaninsu Armad, sannan kuma a wuce
izuwa gasar kusa dana ƙarshe.
Kuma a lokacin aka bawa sauran manyan baƙi damar
zasu iya zuwa su tattauna da waɗanda suka zo dasu.
Kuma a wani lamari mai ban mamaki kawai saiga tawagar
Banfiriya nan sun danno kai!!!
Nidinne dai Shuraih Usman inkiya
99%
Daga taskar magajin wilbafos
MAGAJIN WILBAFOS
Marubuci: Dr Abdullahi Muhammad Ibrahim
Babi na 32:
Post by: Shuraih Usman
@shuraih 99%
www.facebook.com/hausaebooks
.
Daga:- Taskar Magajin Wilbafos
.
Wani abin mamaki, wannan tawaga ta Banfiriya suna
zuwa suka nufi inda Kiru yake, kuma suka jashi gefe suna
ƙus-ƙus. Babu wanda yasan mai suka tattauna, amma dai
daga baya sun nemi waje sun tsaya a kewayen wajen da
ake fafatawar, wato dai basu shiga wajen manyan baƙi
ba.
Ragowar sauran manyan baƙin kuwa irin su Asifu (wanda
akafi sani da RUWAN BALA'IN), baima nuna alamun yaga
shigowarsu ba, kawai hira yake. Suna tattaunawa akan
Izza da ɗaya daga cikin mutanen da suka rako sarki Deniz.
Wani Badenize da ake kira da Deniz Kalhari.
To da yake idan ka duba gefen Armad zaka ga Nusi a
gefensa. Kuma tunda ta fito daga cikin wajan manyan
baƙi take yi masa bayani akan Alkadar.

Ji take kamar wani babban jafa'i na dab da saukarwa
Armad, saboda haka kwata-kwata bata saki jiki ba.
Kuma tunda daman su Maikironomada gaba ɗaya basu
fiya damuwa da tura wani babba zuwa wannan gasar ba,
shi yasa da tace zata zo, da wuri ta zama shugabar tafiyar,
tunda babu wanda yakaita matsayi acikin tawagar.
Hasalima wannan shi ne babban dalilin da yasa Denizawa
basu kula dasu ba a baya, saboda a matsayinsu na babbar
daular tsohuwa, bai kamata ace basa taɓa turo wani
babba ba, kai koda matsayin ɗan majalisa kawai. Wanda
hakan yasa Denizawa suke ganin raini ne yasa.
Nusi ta gama yiwa Armad bayani kenan tana niyyar
komawa wajen manyan baƙin, kawai taga ƴan Banfiriya
sun tsaya saboda haka ita ma ta tsaya.
Acikin wajen manyan baƙin nan kuwa tuni sarki yasa aka
wadatashi da kayan ci da sha, sannan bayan wani lokaci
ya ƙara komawa gefen Uznu'Ururu, wanda har wannan
lokaci idanunsa a rufe suke, yana isa ya dubi Uznu tare da
cewa, ''ina fatan yaran suna ƙayatar dakai!
''Kaga yanzu duk wanda suka futo matakin zagayen kusa
da ƙarshe kyautar da zan basu ita ce Ayrid mai mataki na
ɗaya guda hamsin hamsin sannan kuma da ƙusar yaƙi
guda ɗaya ga kowannensu.
"Wanda yazo na biyu kuwa, Ayrid guda ɗari da kuma
ƙusar yaƙi guda biyar.
"Amma ga wanda yazo na ɗaya kuwa kyautarsa ita Ƙusar
yaƙi guda goma da kuma Ayrid mai mataki na goma."
"Wato ni da kaina zan basu wannan kyauta, saboda haka
ya zamo zai iya yin nutso a wannan fage na Izza kamar
yadda kowanne Badenize zaiyi. Duk wannan kyauta kawai
zan bada ita ne a matsayin nuna jin daɗi ga ƙasashen da
suka taka rawa a wannan gasa acikin ƙasa ta. Kaga idan
aka haɗa da kyautar bayi ga waɗanda sukai nasara ɗin, to
kaga gobe kowacce ƙaramar ƙasa babba ko ƙarama zata
so ta taka rawa a Jinzidal idan za'ai a gari na na Seerisha."
Sarki Deniz Iluru ya ƙarasa bayanin sa da kurɓar wani
ƙayataccen fari lemo dake hannunsa.
Sai dai kuma Uznu Ururu shiru kawai yai masa baice
masa komai ba, sai can wani lokaci, tuni Armad da
Niyashi da Kiru sun hau kan ɗaya daga cikin sababbin
filayen da akasa domin gudanar gasar mutun-mutumin
Alkadar, sannan acikin wata murya ƙasa-ƙasa ya ce,
"Abubuwa masu muhimmanci sun taso, na farko
bayyanar Magajin Wilbafos, wanda kasan ba batu bane
da Ururu take ɗauka da wasa ba.
"Na biyu, muna da isassun hujjoji dake nuna mana cewa
akwai masu san tada ƙayar baya akan Rukunin Jinzidal,
nan bada daɗewa ba!!"
"Na uku, akwai ƴan ƙabilar Djinn, waɗanda suma suke
ƙoƙarin komawa garin Shaedníza da kuma ƙara yaɗa
abubuwan da suka afku a wannan shekara, domin
mutane suji. Kaga ta haka, tunda abin ya haɗa da Tirifil-

fakta, mutane zasuyi ca akai, kaga tashin hankali zai afku."
Wannan mutun mai suna Uznu'Ururu yaci gaba da
bayani cikin mulki da isa da ƙarfin Izza. "Amma mafi
muhimmanci akwai abinda nayi shekaru sama da ɗari
tara ina nema. Kuma nayi duba izuwa taurari bakwai
dake saman ƙasa ta farko. Wanda suka tabbarmin da
cewa wannan abu da nake nemo zai bayyana a wajen
wani yaro dazai taka rawa a wannnan gasa.
"Duk waɗannan dalilai, su ne suka taso ni nazo wannan
gasa. Da fatan kuma Denizawa zaku bamu haɗin kai
domin kautarda asarar rayukan da ba dole ba."
Yana gama jawabinsa, bai jira wata amsa daga sarki Deniz
Iluru ba, kawai ya juya kai, idanunsa a rufe, ya kuma ci
gaba da fuskantar filin fafatawar nan. Wato dai zaka iya
cewa, koma sarkin ya yarda koma bai yarda ba, wannan
shi ta shafa, domin a iya saninsa, su ma'abota Ururu, su
na da ikon aikata duk abinda suka ga dama, kuma a duk
lokacin da suka ga dama.
Dama dai taƙarƙashin ƙasa, shima sarki Deniz yaji
waɗannan abubuwa, cewa wani daga cikin manyanmanyan ƙusoshin duniyar ƙasa bakwai, yana so ya tada
zaune tsaye akan Rukunin Jinzidal (wato cinikin bayi da
ake.)
Sannan kuma bayyanar Magajin Wilbafos, abu ne da
kowa ya sani, amma ba'asan ko waye ba, duk da kuwa
kusan kowa farautarsa yake.
Sai kuma batun ƴan ƙabilar Djinn, wanda shi ne kaɗai
sabon abu, a abubuwan da yaji.
Sai dai kuma babban abinda ya ɗagawa wannan sarki
hankali shi ne, da abu na ƙarshe da Uznu Ururu ya faɗa
akan abinda yake nema. Wanda nan take Deniz Iluru ya
shuga tunani akan ko menene.
Hakan nema yasa tunda Sarki Deniz yaji wannan batu,
ilahirin annurin dake fuskarsa ya ɗauke, kuma bai ƙara
cewa komai ba.
Hasalima daka ganshi zaka san idanunsa ne kawai acikin
filin gasar, amma tunaninsa yana wata duniyar. Lallai
yasan wani bala'I yana kan hanya. Badan komai ba sai
dan girman ikon Uznu Ururu da ya sani. Koda kuwa
acikin ma'abota Ururu yasan shi ɗin mutun ne mai
darajar gaske.
Tun bayan sanda ya zamanto mutun ɗaya daya dawo
daga wancan fafatawa data faru a shekaru da dama da
suka wuce. Wadda tayi sanadiyyar samun shi kansa
Littafin-Takobin.
Saboda haka zai iya turo wasu ma'abota Ururun ma dake
ƙarƙashin ikonsa.
To amma mai yasa yazo da kansa??
Kusan tunda manyan baƙi daga Banfiriya suka tsaya a
kusa da Kiru, kuma suka ƙi tafiya, itama Nusi ta dawo,
dukkanin ragowar waɗanda ke tafe da waɗannan mazaje
ma'abota Izza guda huɗu suma sun sauko ƙasan.

Wato idan ka duba zaka ga mutanen Maikironomada tare
da Armad, mutanen Banfiriya da Kiru, Mutanen Infiriya
da Niyashi, mutanen Hán, daga ƙasa ta uku tare da HánAmuru, sai kuma Denizawa waɗanda suka fi kowa yawa,
dan sunkai kusan su goma sha biyu, a tattare da Deniz
Bizaya.
Saurayi ɗaya wanda babu kowa a tare dashi shi ne
Ikenga!
Kuma idan ka dube zaka san cewa kwata-kwata hakan bai
dame shiba, hasalima ko a jikinsa, kawai kansa ne a ɗage
yana kallon sama acikin matuƙar nutsuwa, tamkar wanda
yake kallo wani abu da baya so ya wuceshi, ko kuma
wanda yake karanta tafiyar taurari!!
Ana cikin wannan yanayi ne, wanda kowa ke ƙoƙarin
gayawa nasa abinda ya kamata yayi da kuma ƙara nuna
musu muhimancin samun nasara, kawai alƙalin wasa ya
sanar cewa, sarki Deniz Iluru ya bada damar a sanar da
kowa kyaututtukan wannan shekara, abinda ya ƙara rikita
wajen! Domin kowa yayi tunanin kawai kyautar bayi za'a
samu kawai kamar yadda aka saba. To amma ga dukkan
alamu gashi sarki Deniz Iluru ya ƙara wasu kyaututtukan.
Amma wannan alƙalin wasa bai tsaya ɓata lokaci ba ya
zayyana dukkanin kyaututtukan da suke akwai, kamar
yadda sarki Deniz ya gayawa Uznu'Ururu.
Jin waɗannan kyaututtuka yayi matuƙar hargitsa ƴan
kallon gaba ɗayansu, kai bama su ba kaɗai, hatta
waɗannan manyan baƙi dake tare da waɗannan samari
shida saida alamun mamaki suka bayyana ƙarara a
fuskarsu.
Kai hatta Asifu dake cikin wannan waje yana tattauna
al'amuran Izza da wannan Badenize, saida ya juya ya kalli
Sarki Deniz cikin mamaki.
Kai gaba ɗaya wannan taro, wanda idan ka lissafa, sama
mutun dubu ɗari suna cikin wajen, amma saida aka shiga
shiru na ƴan daƙiƙu kamar mutuwa ta gifta.
Kai hatta masu kallo wannan gasa a sauran garuruwan
Denizawa, suma saida suka shiga mamaki!
Wataƙila mai karatu yana buƙatar ɗan ƙarin

Please Login or Register in order to submit comment