Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kace meye wannan wata
ƴar ƙofa ta bayyana a jikin bangon.
Cikin sauri wannan dattijuwa ta juyo ta dubi wannan
budurwa tare da cewa, "gimbiya ta lokaci yayi, wannan
ne gwaji na talatin da ɗaya, wanda kuma kamar yadda
muka yanke shawara yanzu shi ne kwaji na ƙarshe, indai
ba'a samu nasara a wannan karanba, to dole mu bi
umarnin shugaba Bihanzin mu koma gida!"
Kafin ta gama rufe bakinta tunu wannan budurwa wadda
ba'a iya tantance launin kayan jikinta da kamanninta
kwata-kwata, badan komai ba saboda tsananin haske mai
kashe ido dake tashi daga jikinta, ta tashi tsaye gami da
duban wannan dattijuwa tare da kyaɗa kai. Kafin daga
bisani ta shige cikin wannan ƙofa. Tana shiga ƙofar ta
ɓace ɓat, a lokacinda ita kuma wannan dattijuwa tai
ajiyar zuciya tare da cewa, "sa'a tana tare dake gimbiya
Nostalgiya Nára!"
***
Bayan kwana huɗu da shigar wannnan budurwa cikin
wannan ƙofa, a zaune a bakin wani kogi mai ɗauke da
baƙin ruwa, ita ce. Inda take zaune cikin nutsuwa,
ƙafafunta a tankwashe, kanta a kafe akan wannan
ƙatoton kogi tana nazari, wannan ruwa wanda gaba
ɗayansa baƙi ne, baƙi-ƙirin!
Abin al'ajabi a kefenta kuma wani saurayi ne kwance a
sume dukkan kayan jikinsa sunyi daga-daga, tayadda
sama da rabin jikinsa a fili yake a bayyane.
Fatarsa ta ƙoƙƙone, sannan kuma duk jikinsa ƙasa ce da
kuma datti ko'ina ka kalla.

Sannan kuma bisa mamaki akwai wani farin haske mai
siffar miciji yana ta kewaya jikin wannan saurayi dake
kwance a gefe bai san inda kansa yake ba.
Sai dai kuma duk da wannan hali da wannan saurayi yake
ciki, akwai wani jan kyalle a ɗaure a goshinsa, wanda
babu alamun ƙonewa a tattare dashi ko kaɗan. Hasalima
ko datti babu a jikinsa tamkar daga baya aka ɗaura masa
shi.
Idan ka lura da wannan saurayi sosai zaka ga ba wani
bane illa Armad Wilbafos!
A kwana a tashi Armad na kwance a sume a gefen
wannan budurwa, har tsahon kwana uku, ita ma tana
zaune tana nazarin wannan baƙin ruwa ko motsi batai ba
tsahon wannan kwanaki.
Sai a ƙarshen wannan rana ne, wannan budurwa ta
ɗauke idonta daga kan wannan baƙin ruwa, ta kuma juyo
ta kalli Armad da dara-daran kyawawan idanuwanta.
Wannan budurwa ta kasance nada matuƙar kyawun
gaske, tayadda a lokaci ɗaya zata sa duk wanda ya kalleta
cikin zulumi da tunanin anya kuwa ya taɓa ganin mai
kyanta akaf tsahon rayuwarsa da mafarke-mafarkensa da
labaran daya taɓa karantawa. Da kuma kokwanto ko anya
ma kuwa mutun yake gani!
To kamar dai ƙirar jikinta tsayin fuskarta ya dace matuƙa
da faɗinta, lamarinda ke bayarda fasalin tsananin cikar
kyawun diri.
Idanuwanta dara-dara ne, wanda farin cikinsu fari ne fat,
kuma baƙin cikinsu baƙi ne wuluk. Sannan kuma ga
hanci wanda tsahonsa ya dace da girman fuskar tata.
Tana da yawan gira, wadda take a saice dai-dai da dai-dai
a saman idanunta.
Duk da cewa tsahon baƙin gashinta ya kai har gadon
bayanta, amma wannan ba abu bane da Armad bai saba
gani a ƙasar daya baro ba, amma babban abinda zai
bashi mamaki dazai farka shi ne, wannan yadda wannan
gashi yake kyalli yana sheƙi, tayadda idan ka ƙura masa
ido zaka iya faɗawa wasu tunane-tunane basu dace ba.
Tun kafin tai murmushi akwai alamun dimful dake
bayyane akan madaidaicin kuncinta.
Idan ka haɗa cikakken kyawun diri da ƙololuwar kyawun
fuska da wannan budurwa ke dashi, sannan kuma ga
yanayin yarinta dake tashi daga ilahirin jikinta, sai kaga
cewa lallai samun wadda takai ta kyau abu ne da zaiyi
matuƙar wahalar gaske koda tsakanin mafi kyawun
fararen aljanu da mutane farko.
Kai lallai babu wata tantama idan kace kasancewar
wannan budurwa a wajen da take yayi matuƙar ƙarawa
wajen kyau, tamkar kyawun surar ta yana shafar shi
kansa muhallin da take musamman duba ga irin hasken
da jikinta yake bayarwa yana ƙarawa bakin wannan kogi
ƙawa.
Bayan ta juya ga Armad ta ɗaga hannunta na dama, inda

ta ɗorashi a ƙirjinsa.
Abin mamaki hakan na faruwa nan take gaba ki ɗayan
ciwukan dake jikin Armad suka fara warkewa. Kan kace
meye wannan tuni sun gama haɗewa, jikinsa ya koma
kamar ba'a taɓa jin rauni ba akansa.
Sai dai kuma abin mamaki a lokacin gaba ɗaya hasken
dake jikin wannan budurwa a lokaci guda ya zuƙe ya ragu
sosai, tayadda kallo ɗaya zakai mata kasan cewa warkar
da ciwukan Armad da tayi Armad yana da farashi mai
tsauri.
***
Tana ɗauke hannunta ta fara haki tana nishi irin wanda ya
dace da ma'abota ƙololuwar kyawun sura da ruhi, na ɗan
tsahon lokaci, kafin daga bisani ta dawo hayyacinta, inda
ta fiddo da wata takarda daga cikin rigarta, ta kuma
sakawa Armad acikin ragowar fatattakakkun kayansa.
Haka na faruwa ta miƙe, inda tayiwa wannan baƙin ruwa
kallon ƙarshe, sannan ta juya tabar Armad a kwance a
inda yake. Kuma kan kace meye wannan, wannan
kyakkyawar sura ta ɓace daga wannan waje.
To a ƙarshen wannan ranar ne shima ya farka a wani
yanayi na kasala.
Abinda ya fara bashi mamaki shi ne ya tabbatar da cewa
acikin wannan gari ya faɗi ya suma, bayan yaji wannan
murya, amma kuma yanzu gashi nan a kwance a gefen
wani kogi.
Sannan kuma ga kayansa nan a ƙoƙƙone, alamun tabbas
wuta ce ta ƙona su, amma kuma shi babu ko rauni ɗaya a
jikinsa.
Yana ganin haka abu na farko daya fara faɗo masa shi ne
wannan takarda wadda yasan cewa ita ce manuniyar
hanya a wajensa, indai yana so ya fita daga cikin wannan
duniya lafiya.
Saboda haka cikin sauri ya miƙa hannunsa cikin aljihun
wandonsa duk da yasan ba'anan ya saka ta ba, to amma
kamar yadda ya gani shishi kaɗai ne aljihun daya rage a
jikinsa.
Sai dai kuma bisa mamaki sai yaji takarda aciki. Yana fito
da ita mamaki ya ƙara kamashi, bayanda ya fara ganin
canje-canje a jikinta, lamarinda ya tabbatar masa cewa
ba wancan takardar bace.
Domin a ƙasan wannan takardar hadda rubutu, ansa
'Gimbiya Nostalgiya Nára' an kuma saka hannu daga can
ƙasa. Abubuwan da duk babu su a wancan takarda da
Armad ya sani.
Cikin mamaki ya fara tunanin me ya faru bayan ya suma,
amma ina duk yadda yai ƙoƙari baya iya tuna no komai.
Sai dai kawai abu ɗaya da yake iya hasashe shi ne cewa,
lallai cetarsa akai daga cikin wancan gari daya suma aciki,
kuma ga dukkan alamu waɗanda suka ceto shi sun san
muhimmancin wancan takarda. Wanda hakan yasa da
suka ga tasa ta ƙone suka canja masa wata.

"To amma su wane ne suka cece ni?" Wannan ita ce
tambayar da yake ta yiwa kansa kuma bashi da amsa illa
abu ɗaya, wato sunan 'Gimbiya Nostalgiya Nára', wanda
ya gani a jikin takardar. Sunan da bashi da masaniyar ko
na waye!!!
Armad bashi da masaniyar cewa ga wadda ta ceto shi,
sannan kuma a wannan lokacin za'a iya cewa kusan duk
su biyun basu da masaniyar cewa wannan shi ne abu na
farko da zai haɗa tsakaninsu a wani irin tarihi da baza a
taɓa mantawa dashi ba!!!
***
Sai dai kuma ba jimawa Armad ya yanke shawarar lokaci
yayi da ya kamata ya fita daga cikin wannan duniya izuwa
doron ƙasa ta huɗu. Inda ya yanke shawarar zai fara
neman Tirifil-fakta daga nan.
Saboda haka nan take ya ajiye tunanin gimbiya
Nostalgiya Nára a gefe ya kuma dubi takardar dake
hannunsa inda ya fara karanto wasu ɗalasimai daga ciki.
Yana gama ambatarsu, ba daɗewa ya fara hango wani
ɗan ƙaramin kwale-kwale yana isowa inda yake.
Yana zuwa baiyi wata-wata va ya ɗare akai, sannan ya
ƙara karanta wasu ɗalasiman ƙamarinda yasa wannan
jirgi ya fara tafiya izuwa gabas masi kudu akan wannan
baƙin kogi!!
Armad ya fuskanci gaban kwale-kwalen nan, yana ta miƙa
ido ko zai hango gaba, amma ina. Har gari ya waye, rana
taje tsakiya bai ga komai ba.
Lamarinda yasa ya yanke shawarar ya ɗan rintsa kaɗan
kafin ya isa, inda ya nemi waje ya kwanta, hannunsa akan
takobinsa.
A lokaci daya tashi baiga rana a sama ba, hasalima yana
kallon gabas yaga alamun ɗagowar rana, lamarinda yasa
yasan lallai safiya ce, abinda ke nuna cewa ya kwana ya
kuma wayi gari yana bacci.
Yayi mamakin yadda yai bacci da yawa haka, lamarinda
yasa ya fara ƙoƙarin tuno lokaci na ƙarshe daya kwanta
yai bacci haka, ya kuma tuno cewa ai tun sanda aka
ƙwanƙwasa masa ƙofa aka ce ga mahaifiyarsa ta dawo
daga yaƙi amma bata san inda kanta yake ba.
"Hmmmm!!" Ajiyar zuciya kawai yai, ya kuma ƙara ji a
ransa cewa lallai yana so yai sauri ya nemo wannan
mutun mai suna Tirifil-fakta, koya koma gida yaga
mahaifiyarsa.
Amma yana cikin wannan tunani ne yaga wani abun;
wannan kuwa ba komai bane, illa sararin samaniyar
wannan waje.
A iya saninsa, a kullum idan rana ta fito, akwai rana ɗaya
wadda take tasowa daga gabas ta faɗi a yamma, sannan
sai kuma ɗayar wadda bata motsawa tana tsaye a tsakiyar
sama cak.
To amma banda a wannan waje, inda duk yadda ya duba
guda ɗaya tak yake iya gani, wadda ke tasowa daga gabas.

Bai san mai ya janwo hakan ba, amman babban abinda
yake gabansa shi ne yaushe zai isa bakin gaɓa.
A zuciyar sa tun daga sanda ya taka ƙafa ya shiga wannan
ƙofa da Abul-Babara ya buɗe masa, yake ta tunanin dame
zai fara wannan alƙadari nasa na neman TF, idan ya isa
doron ƙasa ta huɗu.
Armad nata tafiya acikin wannan jirgi, babu abinda ke
ransa sai son ya isa bakin gaɓa.
A rana ta biyar yana cikin tafiya yunwa ta tayar masa,
inda ya rasa yadda zaiyi, kawai saiya rufe ido ya fara rera
wakar da mahaifiyarsa take masa sanda bai kai shekara
goma ba, idan tana so yai bacci.
Ai kuwa haka akai, ba jimawa bacci ya ƙara ɗauke shi,
yana kwance yana bacci, kwatsam girgizar jirgin da yake
ciki tasa ya farka.
Yana buɗe ido, yayi arba da abinda ya daɗe yana jira,
wato bakin gaɓa.
Sai dai kuma ba a yadda yai tsammani ba. Domin kuwa
abinda ya hango daga nesa shi ne bango ruwa, wanda
kallo ɗaya kawai yai masa yasan cewa lallai wannan yana
kama da bangon duniya.
To amma ba wannan ne abinda ya firgita shi ba, illa wani
ƙatoton waje mai kama da wawakeken rami dake
tsakanin wannan bangon da kuma wannan baƙin ruwa
da jirginsa yake kai, wanda lallai idan da za'a auna zai kai
kimanin faɗin taku dubu da ɗoriya.
Kuma daga yanayin tafiyar jirgin, ya fuskanci cewa bashi
da niyyar tsayawa ko kaɗan, hasalima yana ƙara kusanto
wannan rami yana ƙara sauri, tamkar dama aikinsa ya
jefa Armad cikin wannan rami.
A lokacin da Armad ya farka tuni wanki hula ya kaishi
dare, saboda baifi saura taku biyar ba tsakaninsa da
wannan rami ba, amma a wannan lokaci saura taku uku
kacal.
Tuni Armad yake ta tunanin wacce hanya zaibi ya
tsayarda wannan jirgi, amma ina babu wata hanya mai
ɓullewa data zo kansa.
Duk tunanin da yayi sai yaga bamai ɓullewa bane, saboda
babu wani abu mai kama da alamun Armad zai iya
riƙewa ko kuma ɗanewa wanda zai iya sawa wannan
kwale-kwale ya ƙi faɗawa wannan rami.
Yana cikin wannan tunani ne, ba shiri wannan jirgi nasa
yaje bakin wannan rami, inda bisa mamaki kawai ya tsaya
cak, sannan kuma kafin Armad ya ƙarasa ajiye ajiyar
zuciyar da yayi tuni wannan kwale-kwale ya ɗaga shi
sama, inda cikin sauri ya cilla Armad cikin wannan
wawakeken rami, shi kuma ya juya ya koma inda ya fito!!!
Copyright © 2017 A M IBRAHIM . All rights reserved
Nidinne dai Shuraih Usman inkiya
99%
Daga taskar magajin wilbafos

MAGAJIN WILBAFOS
Marubuci: Dr Abdullahi Muhammad Ibrahim
Babi na 8: Sirrin da zai rikita Duniya
Post by: Shuraih Usman
@shuraih 99%
www.facebook.com/hausaebooks
.
Abu ɗaya da Armad yake iya tunawa a lokacin da yake
tsaka da faɗawa cikin wannan wawakeken rami shi ne
riƙe takobinsa da yayi, ya ɗaure ta a jikinsa.
Amma bayan wannan, gaba ɗaya hankalinsa dusashewa
yayi, kafin daga bisani ya sume gaba ɗaya.
To koma dai mai ya faru bayan wannan, wanda bazai iya
tunawa ba, to yana ganin bai halaka shi ba tunda a dai-dai
wannan lokaci ya tsinci kansa a kwance a kan tantagaryar
ƙasa da kuma ragowar numfashi a jikinsa, ga kuma
waɗansu abubuwa daya kasa tantancewa a tsaye a
kansa...
"Hmmmm...." Cikin firgici Armad yai ajiyar zuciya, acikin
ransa bayanda kwatsam abin ya faɗo masa a rai cewa ko
mutuwa yayi.
A hankali a hankali, ganinsa yana ƙara dawowa,
waɗannan halittun dake bisa kansa su na ƙara
bayyanuwa, sai ya gano cewa ashe mutane ne!
Ba daɗewa ya gano cewa ashe maza ne guda biyu da
mace ɗaya.
wadda ke tsaye a bayansu.
Mamaki ya cika zuciyar Armad kuma hankalinsa ya ɗan
kwanta, lokacin da yaga macen dake cikinsu ta cillo masa
bututun ruwa.
Amma kafin ma ta ƙaraso wajensa ɗaya daga cikinsu
wanda ke tsaye a daman Armad yasa ƙafa ya doke
bututun, yana mai cewa, ''meye amfanin shayar dashi!''
Babu wanda ya ce uffan acikinsu akan wannan abu daya
afku, kuma akan idon Armad wannan mutun ya gabato
gareshi da farar ankwa ya ɗaureshi gaba da baya.
Sannan suka ɗaureshi shi akan wani doki ƙarami
samfurin ak-wali, sannan suka hau nasu dawakan suka
nufi gabas.
Lokaci bayan lokaci Armad zai farka ya ji basu daina
sukuwar da suke ba kafin ya ƙara komawa.
Bai san tsahon lokacin da sukai su na tafiya ba, abu na
gaba daya gani shi ne, farkawa acikin wani ɗan tanti
ɗaure acikin ankwa.
Bayan ya nuts, abinda ya fara lura dashi shi ne, kwatakwata jikinsa babu alamun ciwo ko kaɗan, lamarinda ya
bashi mamaki sosai, saboda sanda ya fara buɗe idonsa
bayan faɗowarsa daga wannan waje, baya ko iya motsa
jikinsa saboda ciwo.
Yana ɗaga ido yai arba da waɗannan mutane ne uku da
suka ɗakko shi, zaune akan kujerun alfarma da akaiwa
ado da jan dinare, inda ya bisu da kallo ɗaya bayan ɗaya.

Yana kwance, baya iya motsa komai a jikinsa face
idanunsa, wanda yayi amfani dasu wajen ƙurawa suturar
dake jikin wannan mutane kallo.
Dukkaninsu a sanye suke da kayan yaƙi, wanda kallo ɗaya
ya isa mutun yasan cewa masu tsadar gaske ne, kuma na
sarauta.
Mafi tsayi acikinsu namiji ne, yana tsaye bisa saitin kan
Armad, sai kuma mai biye masa, wanda ke tsaye a
gwiɓinsa, sai kuma macen, Babban cikinsu magidanci ne
wanda tabbas zaifi shekaru talatin.
Yana da ƙira cikakkiya abar dacewa da sadaukai. Domin
tun daga inda Armad yake yana iya hangen murɗaɗɗen
zubin jikinsa. Da kafaɗunsa masu faɗin gaske duk da
cewa bashi da tsayi sosai.
Fuskarsa tana da ɗan tsayi, amma saboda faɗin ta ba
sosai mutun zai iya kula da tsayin ba.
Babu gashi da yawa a fuskar tasa, face wani ɗan gemu
mara tsayi sosai.
Sai kuma mai biye masa, wanda a karon farko da Armad
ya kalleshi ya yanke shawarar cewa ƙanin wancan
zabgegen ne.
Badan komai ba saboda kama da suke da juna, duk da
kuwa cewa babban ya fishi girma sosai da sosai, amma
kana ganinsu zaka ga kama.
Dukkanin su, su na sanye da ƴar shara ta jan alharini,
wadda akaiwa ado da zinare daga wuya zuwa ƙasa.
A wannan lokaci ne kuma idanunsa suka kai ga macen
dake gefensu.
Yana ɗora idonsa akanta ya ce, "kai!!!" Cikin mamaki ya
ƙara wara idanuwansa saboda wani abu dake faruwa a
dai-dai wannan lokacin.
Ba komai bane yake faruwa illa kasancewar Armad acikin
waniyanayi da yake ji a ransa cewa lallai ya taɓa ganin
wannan budurwa, sai dai kuma a lokaci guda hankalinsa
na tambayarsa a ina!
Bakinsa a buɗe, mamaki kawai yake akan abinda ke
faruwa, sannan kuma yana ƙara tambayar kansa akan
wace ce taƙamaimai wannan budurwar!
Duk da ƙarancin shekaru na Armad amma bai daɗe yana
kallonta ba, ya tabbatarwa da kansa cewa lallai bai taɓa
gani ko jin halitta mai kyawunta ba, kai koda a zane ko
kuma a labarai da tarihin fararen aljanu!
Tuni Armad ya ƙurawa wannan budurwa, wadda bata fi
sa'ar sa ba ido, bama tare da ya sani ba. Badan komai ba
saboda kwatsam yaji a ransa cewa lallai akwai yiwuwar
idan ya fiya kallon fatar jikin wannan budurwa, zai iya
samun damar ganin wucewar jini da idonsa, kamar
yadda ya ji ya faru a 'Hikayar Lasína Naitingel', macen da
aka ce ba'a taɓa haifar wata data kaita haske ba!
Sai dai amma Armad bai samu damar cimma burinsa na
ganin hakan ba, domin a dai-dai lokacin ne ya fuskanci
cewa ashe a ɗaure yake tamau acikin ankoki!!!

Ba shiri ya dawo hayyacinsa, tare da canja fuska gami da
cewa, "wai su waye ku, kuma me nayi muku da zaku
ɗaure ni acikin ankoki haka!"
Bai ƙarasa rufe baki ba, saurayin dake ɓangaren dama ya
dubeshi a fusace gami da cewa, "mu zamuyi maka
tambaya, bakai zakai mana ba.
"Saboda haka abu na farko daya kamata ka sani shi ne,
muna so kayi mana wani abu guda ɗaya, idan kayi shi,
zamu sake ka ka tafi, idan kuma baka yishi ba to...!"
Saurayin na zuwa nan a zancensa sai ya ja numfashi tare
da kallon doguwar takobinsa yana kuma yiwa Armad
inkiya da ita.
Mamaki ne kawai ya cika zuciyar Armad, ya kuma rasa
mai zaice, lamarinda yasa nan take ransa ya ɓaci. Amma
koda ya duba ya ganshi ɗaure acikin ankoki sannan kuma
ga takobinsa can a ajiye a gabansu, sai yasan babu abinda
zai iya a wannan lokaci, banda sauraronsu yaji mai suke
tafe dashi.
Ba tare da ɓata lokaci ba, ɗaya namijin ya taso daga inda
yake, ya gabato gaban Armad a hankali. Inda yana zuwa
ya zaro wani ɗan allo daga cikin ƙasaitacciyar
alkyabbarsa ya nunawa Armad.
Sannan kuma a lokaci guda da ɗanyatsansa na dama ya
nunawa Armad wasu rubuce-rubuce a gaban allon
wanda aka yisu tayadda suka kewaye izuwa fasalin
ƙawanya, gami da cewa, "abinda kawai muke buƙata da
kai shi ne ka ɗisa jininka acikin wannan ƙawanya."
Muryarsa a nutse take, tamkar babu wani tashin hankali
aciki ko kuma damuwa aciki, amma kana kallon idanunsa
zaka ga wani abu mai kama da buri, wanda zai tabbatar
maka da cewa ko ma mai suke nema a game da Armad,
lallai babban abu ne.
Wannan allo ya kasance yana da matsakaicin girma,
kuma fari ne mai ɗan duhu. Sinadarinsa kuwa yana kama
da sinadarin haƙorin bakin ɗan adam.
Sheƙi kawai yake da ɗaukar ido duk da rana bata haska
shi ba.
A tsaye baifi kamu biyu ba, sannan bashi da kauri
kwatakwata.
Ƙurawa wannan rubutu ido kawai Armad yayi tsahon
lokaci yana nazari, kafin daga bisani ya gane anyi shi ne
da tsohon yaren Aldurish! Yaren da kusan zaka iya cewa
an manta dashi kwata-kwata a wannan lokaci.
Saboda sama da shekara dubu aka maye gurbinsa da
sabon yaren Aldurish, wanda akewa laƙabi da AldurishAmri saboda alaƙarsa da Amri. Kuma kusan kowa ya iya
Aldurish-Amri, amma samun mutun ɗaya daya iya
Aldurish-tsoho, dai-dai yake da samun raƙumi acikin
kuratandu.
Armad na ganin wannan yare yasan cewa lallai waɗannan
mutane dake gabansa kodai ƴaƴan manyan sarakuna ko
kuma sun fito daga cikin manya-manyan ƙungiyoyi,

domin a iya tunaninsa indai ba haka ba to babu yadda
za'ai su samu wata alaƙa da wannan yare.
Armad ya iya wannan yare sosai da sosai, duk da cewar
sai da ya ɗauki lokaci mai tsahon gaske yana koyonsa a
wajen mahaifiyarsa.
Saboda haka yana gani wannan rubutu, ya karance shi. Ya
kuma ƙara tabbatar da cewa abinda suke nema lallai
babban abu ne. Saboda haka sai ya fara tunanin mafita.
Badan komai ba, sai dan cewa daga cikin ƴan dabarun
daya ilmantu dasu a iyakacin ƴan shekarunsa, yasan
cewa abu ne mai sauƙi bayan yayi musu abinda suke so,
su halaka shi.
Ƙurawa wannan rubutu ido kawai Armad yayi tsahon
lokaci yana nazari, kafin daga bisani ya gane anyi shi ne
da tsohon yaren Aldurish! Yaren da kusan zaka iya cewa
an manta dashi kwata-kwata a wannan lokaci.
Saboda sama da shekara dubu aka maye gurbinsa da
sabon yaren Aldurish, wanda akewa laƙabi da AldurishAmri saboda alaƙarsa da Amri. Kuma kusan kowa ya iya
Aldurish-Amri, amma samun mutun ɗaya daya iya
Aldurish-tsoho, dai-dai yake da samun raƙumi acikin
kuratandu.
Armad na ganin wannan yare yasan cewa lallai waɗannan
mutane dake gabansa kodai ƴaƴan manyan sarakuna ko
kuma sun fito daga cikin manya-manyan ƙungiyoyi,
domin a iya tunaninsa indai ba haka ba to babu yadda
za'ai su samu wata alaƙa da wannan yare.
Armad ya iya wannan yare sosai da sosai, duk da cewar
sai da ya ɗauki lokaci mai tsahon gaske yana koyonsa a
wajen mahaifiyarsa.
Saboda haka yana gani wannan rubutu, ya karance shi. Ya
kuma ƙara tabbatar da cewa abinda suke nema lallai
babban abu ne. Saboda haka sai ya fara tunanin mafita.
Badan komai ba, sai dan cewa daga cikin ƴan dabarun
daya ilmantu dasu a iyakacin ƴan shekarunsa, yasan
cewa abu ne mai sauƙi bayan yayi musu abinda suke so,
su halaka shi.
Amma kuma bayan ɗan lokaci kaɗan, yana kallonsu suna
kallonsa. Gashi acikin ankwa, gashi shi kaɗai su uku, sai
kawai ya yanke shawara duk abinda zai aiwatar zai
ta'allaƙa ne da mai ya faru a gaba bayan ya ɗisa jinin
nasa.
Badan komai ba, saboda baiga wata hanya dazai ƙi saka
jinin nasa kuma su ƙyaleshi ba. Kuma idan suka samu
matsala tun daga ɗisa jinin, ya tabbatar da cewa yiwuwar
kuɓutarsa a gaba ta ƙara raguwa.
Saboda haka ya yanke shawara ya nuna musu ya amince
zai aikata hakan.
Lamarinda yasa wannan saurayi daya taso ya zare farar
doguwar takobinsa tare da nunawa Armad kakkaifan
tsininta, yana mai cewa, "ina kake so na fasa?" Babu
alamun tausayi ko kaɗan a tattare dashi, sai dai kuma

shima Armad babu tsoro a tattare dashi. Domin tuni yayi
masa nuni da tafin hannunsa na dama.
Haka kuwa akai ba jimawa jinin Armad ya ɗisa akan
wannan allo acikin wannan ƙawanya.
Hakan na faruwa ragiwar mutun biyun dake zaune, suma
suka taso suka tsaya akan Armad, inda macen tai wani
ɗan ƙaramin murmushi wanda bai ƙunshi alamun
komai, tare da cewa, "Nan bada jimawa, sak irin muryar
da kaji acikin wancan gari zatai magana daga cikin
wannan allo.
"Abinda kawai muke so shi ne ka gaya mana abinda
tace!!"
Duk da ƙarancin shekaru irin na Armad, amma a dai-dai
wannan lokaci abu ɗaya ne kawai yake ta kai-komo a
zuciyar sa, wanda shi ne kawai yanayin yadda maganar
wannan budurwa take shafar hatta iskar dake ilahirin
wajen; kasancewar Armad zai iya rantsewa indai ba
mafarki yake ba, to lallai yaga iskar cikin wannan tanti
tana ƙara kyau.
Bai gushe ba yana cikin wannan hali ba, har sai da yaga
takobin ɗaya daga cikin samarin nan biyu a wuyansa
tukun. To sai a wannan lokaci ne ya fara tuno abinda yaji
ta faɗa na game da wancan murya.
Sannan kuma ya fara mamakin yadda akai ta san
al'amarin shigarsa wancan gari.
Sai dai kuma tunda dama Armad ya kasance mutun ne
mai saurin gane abubuwa, ba jimawa ya biɗe baki cikin
mamaki yana kallon wannan budurwa tare da cewa,
"Gimbiya Nostalgiya Nára?"
Tsahon daƙiƙu bata ce masa komai ba, kafin daga bisani
ta kalli Armad ido cikin ido sannan a yanayi daya kamace
ta ce, "to kaga na cece ka a baya, to kaima yanzu ya
kamata indai kaji wannan murya kada ka ɓoye mana
domin tana da muhimmanci a garemu."
Armad shima baice komai ba sama da daƙiƙa sittin
tamkar ma bazai ƙara magana ba, kafin can daga bisani
ya ja dogon numfashi ya fara bayani da godiya, "na gode
Gimbiya, lallai kin ceci raina a baya, kuma nima yanzu
zan saka miki da alkhairi!
"Ina mai tabbatar muku da cewa koda kun kwance bazan
je ko'ina har sai wannan murya tayi magana! Wannan shi
ne aƙƙawari na a gareki gimbiya!"
Armad bai sani ba, amma tuni ya fara kallon wannan
mace a matsayi na musamman!!
Suna jin haka suka kalli juna, sannan bayan sun ja gefe,
sun kuma gama yin ƙus-ƙus, sai suka dawo suka kwance
Armad.
Ba jimawa tuni har Armad ya fara jansu da hira,
musamman ma gimbiya Nostalgiya, inda yake
tambayarta tayi masa bayanin yadda akai ta same shi
acikin wannan gari da kuma yadda ta ceto shi ta kaishi
bakin wannan ruwa da kuma yadda har tasan takardarsa

ta ƙone kuma ta canja masa wata.
Sai dai kuma kash, duk tambayoyinsa babu wadda ta
samu amsa. Domin kuwa ga dukkan alamu daga kan
gimbiyar har samarin guda biyu basu da saurin sabo, ba
kamar shi Armad ɗinba; wanda yake da saurin sabo da
kuma son raha.
Amma dai duk da haka daga ƙarshe saida yaji cewa
dukkansu ƴan uwa ne, kuma babban sunan sa Hasanu
Sísiyu Nára, ƙaramin kuma Kíru Sísiyu Nára, sai kuma ita
gimbiyar wadda tace masa sunanta na asali Zahra Sísiyu,
amma saboda wasu dalilai kowa yanzu Nostalgiya Nára
Sísiyu yake kiranta.
Duk da a lokacin Armad ya lura da cewa ƴan uwan nata
biyu basu ji daɗin wannan sirri data gaya masa ba!!
Amma kawai dai suka ɗauke, duk da daga baya saida
babban ya gaya masa cewa wannan sunan nata kada ya
gayawa kowa, domin ba'a faɗa yanzu!
Armad baice komai ba kawai ya amsa da "eh!"
Haka Armad yai ta ƙoƙarin jansu da hira amma bai samu
nasara sosai ba, duk da kuwa kusan ya gama ɗebe
labarinsa kaf ya gaya musu in banda sunan sa na gaskiya
dabai faɗa ba; inda ya ce sunansa Armad Djinn!
Suna cikin haka kwatsam sai ji sukai Armad yai shiru yana
cikin magana! Lamarinda ya tabbatar musu da cewa
wannan allo dake hannunsa ya fara maganar.
Nan take suka tattaso daga inda suke, suka tsaya akansa.
Inda a lokacin tuni hankalinsa ya fara gushewa, baima
san inda kansa yake ba.
Sai dai kuma ba kamar a cikin wancan gari ba, a wannan
lokaci cikin abinda bai wuce daƙiƙa ɗari biyu ba ya
farfaɗo!
Inda bayan ya farka ya dawo hayyacinsa ya ɗaga kai ya
kalle su, fuskarsa cike tsananin mamaki da firgici, saboda
yaji abinda bai taɓa zato ba bai kuma taɓa tsammani ba.
Amma kafin ya fara magana, bisa ƙarin mamakinsa kawai
sai yaga duk su biyun sun juya sun kalli gimbiyar. Inda ita
kuma ta kyaɗa musu. A dai-dai lokacin da Armad yaji
kamar wani abu ya shiga cikin kansa ya karanta wannan
murya da yaji sannan kuma ya fice.
Duk su biyun suna ganin haka sukai wata dariya mai cike
da murna da annushuwa da nuna cikar buri.
Kafin daga bisani babban nasu ya dube su cikin murna
tare da cewa, "ta wacce hanya kuke ganin yafi kamata mu
kashe wannan yaro, mu ƙarasa aikinmu!!"
Magana ce mai kama da tambaya, amma kana gani kasan
ba amsar kowa yake nema ba, illa tasa. Domin kuwa
kawai Armad yake kallo yana murmushi.
A dai-dai wannan lokaci Armad ƙoƙari yake ya gane meke
faruwa, saboda acikin ƴan daƙiƙun da suka wuce, lallai
yaji gilmawar wani abu a kwakwalwarsa, amma yaƙi
amincewa ya yadda da cewa kwakwalwarsa suka duba,
sai dai kuma cewa lallai yasan cewa hakan ne ya faru

daga abinda yaji babban nasu ya faɗa,

Please Login or Register in order to submit comment