Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

nama,
babban
nasu wanda yayi magana a baya wanda kuma ga
dukkan
alamu yasan Hasanu a baya, ya buɗe baki cikin
firgici,
jikinsa na rawa, yana cewa, ”kai… yaushe….. ka kai
matsayin Ótaki, Hasanu….yaushe??!?”
Bai gama rufe bakinsa ba, mutun biyun dake
bayansa suka
zube a ƙas, inda wanda keda taurari biyu ya zarce
kasa a
sume, fatarsa a rufe da wannan ƙanƙara ruwan toka,
shi
kuma mai taurari uku ya fara faɗuwa bisa gwiwarsa
fuska
cike da mamaki, kafin daga bisani shima yaje ƙas.
Waɗannan mutun-mutumi guda biyu na iska, dake
tsaye a
gefen Hasanu sukai ihu mara sauti, inda kafin Ƙilik
yayi
wani abu tuni sun cimmasa, inda suka ɗaga hannu
kawai
saiga wani dogon zare shima na iska, ya bayyana a
hannunsu.
Kan kace meye wannan sun gama naɗɗaɗe arnan
daji
Ƙilik dashi, sannan cikin tsananin sauri suka fito da
wata
jaka irin ta tsafi suka cillashi aciki.
Kai ko damar yin ihu bai samu ba, kafin sun cillashi
cikin
jakar, sannan kuma daga bisani suka dawo gefen
Hasanu
suka tsaya.
Dukkan abinda ya faru zai ɗau lokaci a wajen bayani,

amma a zahiri ya faru ne cikin ƙiftawar ido da
bismillah.
A dai-dai lokacin mamakin dasu Nostalgiya da Kiru
suke
ciki yakai matuƙa, inda tuni ma suka manta da
abinda ya
gaya musu na cewa su lura zai koya musu wani sirri
daga
cikin sirrikan Sihri.
”Ku lura sosai, yanzu ne zan nuna muku abinda na
faɗa!”
Muryar Hasanu ta cika kunnuwansu da wani ƙarfi
duk da
cewa maganar a hankali yayi ta.
Amma nan take suka dawo hayyacinsu suka kuma
ƙura
masa ido su na kallon wannan sirri da za’a saukar
musu.
Dukda cewa dukkaninsu sun san irin yadda ake ji da
ƙarfin na Hasanu, bama a iya Sisiya ba, har iyakacin
dukkanin Burja.
Ko ba komai shi ne kwamanda na biyar a dukkanin
jerin
kwamandun ƙungiyar Burja.
Amma duk da haka abinda suka gani yanzu ya firgita
su
saboda wannan bashi bane karo na farko ba da suka
taɓa
ganin faɗa da Ótakí ba, amma banbancin Izzar da
suka ji a
jikinsu yanzu tsakanin wancan da wannan tamkar
banbancin sama da ƙasa ne!
Hasanu ya ja numfashi matsakaici, kamar wanda
yake
zuƙar wani abu acikin sanyin iskar dake kewaye
dasu, nan
take idanunsa suka canja inda suka cika da tsananin
imani
da nutsuwa.
Duk da kasancewar har a wannan lokaci gabansa
yake
fuskanta, wato tun bayan wannan taku guda ɗaya da
yayi
na farko, amma duk da haka saida suka ji ajinkinsu
yanayin yadda fuskarsa ta canja.
Wanda hakan yasa nan take suka fuskanci tsananin
muhimmancin abinda zai gaya musu wanda yasa
suka
ƙara nutsuwa da tara hankalinsu.
Har a lokacin da Hasanu ya buɗe baki ya fara
magana bai
waiwayo ya kallesu ba, sannan kuma bai ɗaga

ƙafarsa
daga inda ya ɗora ta ba tun farko sannan kuma
dukkanin
abubuwan da suka faru, waɗannan mutun-mutumi
guda
biyu dake tsaye a gefen Hasanu kansu a rusune yake
tamkar waɗanda dukkan alamarinsu ya ta’allaƙa da
kareshi
komai wuya komai tsanani, ko kuma wasu bayi
waɗanda
suka kai maƙura wajen jin daɗi cikin bautar abin
bautarsu,
sannan kuma da wannan yanayi na sanyin-sihiri da
yake
kaɗawa acikin wannan jar iska, komai yana nan a
inda
yake bai motsa ba, bai kuma canja ba kamar yadda
shima
Hasanun bai motsa ba.
”Kuyi sani cewa duk wani Sihiri dake faɗin duniyar
kafin
ya zama kai ka zama shi, sai ka sadaukar da wani abu
daga
cikin sassan jikinka wanda yake motsi.” yaci gaba dai
musu bayani, muryarsa a nutse.
“Wannan abu da zaka sadaukar ya zama wajibi ya
zamanto kana da dukkan iko na sarrafa shi.
”Saboda wannan waje shi ne zai zama ma’ajiyar
dukkan
fasahohinka.
”Kuma yadda zaka iya sarrafa wannan ɓari na jikinka
haka zaka iya sarrafa dukkanin sihirinka, yadda zai
zamo
wata hanya da zaka rinƙa sarrafa sihiri irin yadda
kaga
dama.
”Yanzu ku ɗauki misali dani, dukkanin sihiri na yana
da
alaƙa da ƙafata, wato dai kamar wannan jar iska da
kuke
gani.
”Ku kula kugani!” Yana gama faɗar haka sai ya ɗaga
ƙafarsa ta dama wadda ya riga ya taka da ita tunda
farko,
ya dawo da ita baya.
Faruwar hakan keda wuya, kamar a mafarki dukkan
wannan jar Iska dake ta kaɗawa ta ɓace ɓat, sannan
babu
alamun waɗannan mutun-mutumi guda biyu babu
alamunsu, sannan kuma babu wannan sanyi na
babban
sihiri dake kaɗawa, komai ya ɗauke cak tamkar ba’a

taɓa
samar dashi ba.
Babu abinda ya rage banda, waɗannan Arnan daji
dake
kwance fululu a ƙasa a sume.
Hasanu yaja numfashi sannan ya juya yai duba izuwa
Zahra da Kiru waɗanda bakinsu yake a buɗe cike da
mamaki, ya ce, ”wannan shi ne mataki na gaba da
zaku
shiga yayinda kuka gama kwarewa akan wannan
mataki
da kuke kai.
”A yanzu kawai abinda nakeso shi ne ku buga
tambarin
dukkan abinda kuka gani da abinda kuka ji a wannan
rana
acikin ranku, domin cikin shekaru masu zuwa zaku
kai
matakin da zaku fara koyar amfani da irin wannan
sihiri, a
lokacin zaku ga amfanin abinda na nuna muku
yanzu.”
Yana gama faɗar haka ya ƙara ɗaukan taku ɗaya
wanda
ya isar dashi gabansu.
Yana isa cikin mamaki sai suka ga wata iska mai jan
launi
ta bayyana ta kuma zagaye su, inda kafin su buɗe
baki
suyi magana tuni wannan iska ta sure su tayi sama
dasu,
inda suka ɓace cikin samaniya suka kuma nausa
cikin
sauri izuwa garin Sisiya.
Su na cikin tafiya acikin wannan iska Kiru ya kasa
daurewa, inda ya haɗiyi yawu sannan idanunsa cike
da
ƙara ganin girman Hasanu ya tambaya, ”wato idan
na
fahimta, aljaninka na jar iska ne, sannan kuma
sihirinka a
ƙunshe yake acikin takun ƙafafunka. Tayadda idan
kai
niyya kawai ɗaga ƙafa kake da buƙata kawai kayi,
domin
ka bayyanar da aljaninka na jar iska?”
Hasanu yai ɗan murmushi gami da kyaɗa kai alamun
yadda da abinda Kiru ya faɗa.
Kiru ya ƙara jan numfashi ga dukkan alamu kuma
bai
gama tambayoyinsa ba, gami da cewa, ”Shin Yanzu
matakai nawa ne suka rage min na Izza kafin nakai

wannan mataki?”
Yayi tambayar ne fuskarsa da idanunsa cike da buri
da
kafiya na ranar da shima zata zo ya kira kansa
ma’abocin
irin wannan Izza.
Hasanu ya ɗau lokaci mai tsaho su na tafiya ba tare
ya
bashi amsa ba, inda har ya fara tunanin ko bazai
amsa
masa ba. Amma daga bisani Hasanu ya ɗaga kai ya
kalleshi gami da girgiza masa kai yana mai cewa,
”kada ka
zamo mai hanzari acikin al’amarin Izza da sihiri.
”Komai lokaci ne, kuma hasali ma a yanzu mafi
muhimmancin abu a gareku shi ne ku ƙure kuma ku
kai
matuƙa akan matakan da kuke.”
Yana magana yana dubansu biyun kamar dukansu su
ne
sukai tambayar, idanunsa cike da ma’ana.
”Kunga saura sati uku kawai a buɗe *Non-toch-teka*
dake
birnin Maikironomada, kuma tuni ƙungiyarmu ta
Burja, ta
biya farashi mai tsadar gaske wajen kama muku
babbar
ƙofa, kunga wannan shi ne lokaci mafi dacewa da
zaku
tabbatar da horonku.
Nidinne dai Shuraih Usman inkiya
99%
Daga taskar magajin wilbafos
MAGAJIN WILBAFOS
Marubuci: Dr Abdullahi Muhammad Ibrahim
Babi na 16: Ido da ido da Daikirin
Post by: Shuraih Usman
@shuraih 99%
www.facebook.com/hausaebooks
.
.
”S hekara uku!!” Armad yai ajiyar zuciya gami da
ƙurawa wannan budurwa ido cikin mamaki.
”Ba zan iya yin shekara uku anan ba, saboda akwai
abinda
nake so nayi sauri nayi, na koma gida. Dan ALLAH yi
min cikakke bayani naji abinda ke faruwa da wannan
waje.”
Kallonsa kawai tayi na ɗan lokaci, kafin daga bisani ta
girgiza sannan ta ja dogon numfashi gami da ɗaga
yatsanta na dama inda ta nuna masa filin dake gabas

dasu
tace, ”hanyar fita daga wannan waje tana can
ɓangaren.
”Daga nan kuma zuwa wajen baifi tafiyar awa ɗaya
ba.
”To amma kayi sani cewa gaba ɗaya wurin nan a
zagaye
yake da wani sinadari mai suna Negrinki.
”Wanda shi ne babban dalilin daya sa baka ga
kowacce
irin halitta anan duniyar ba.
”Kasancewar shi wannan Negrinki yana iya zuƙe ran
duk
wani abu mai rai.
”Kuma babban tashin hankalin shi ne iyakacin yadda
ka
kusance shi, iyakacin yadda zaka fuskanci ƙarfinsa.
”Mafi ƙanƙantar lokaci da aka ɗauka kafin wuce
wannan
mataki tsahon shekaru da dama, shi ne shekaru uku.
”Amma kaga yanzu acikin shekara ta ukun nan, a iya
lissafin da nayi har yanzu ban wuce kaso sittin ba na
wannan jarrawabar ba.” Ta kalleshi kallo mai ƙunshe
da
tambayar, ”ko ka fuskanci girman wahalar dake
gabanka?”
Armad ya gane meke ƙunshe acikin wannan kallo,
saboda
haka yayi mata murmushi a lokaci na farko tun
bayan
haɗuwarsu.
Shi kansa bai san dalili ba, amma kawai sai yake jin
cewa
hankalinsa a kwance yake da ita, wato dai baya jin
wata
barazana ko kuma mugun nufi a tattare da ita.
Ya buɗe baki yai kyaran murya sannan cikin
girmamawa
ya ce, ”baki gaya min sunanki ba, amma idan ba
matsala
zan iya kiranki yaya.”
Kallonsa kawai tayi ba tare da cewa komai ba, sai dai
kawai acikin idonta akwai alamu dake nuna lallai taji
daɗin wannan magana da Armad ya faɗa, tamkar
yana
tuna mata da wani abu daya faru da ita.
Maimakon ta bashi amsa, sai tace, ”naga alamun
kamar
baka fahimta ba sosai yanayin da kake ciki ba.
”Ina ga muje na nuna maka ka gani da idonka.”
Tana gama magana ta miƙe gami da yi masa inkiyar
ya

biyo ta.
Cikin ƙanƙanin lokaci tuni Armad ya saɓa takobinsa
ya na
murmushi yabi ta yana cewa, ”mai yasa kike kyautata
min
bayan baki taɓa gani na ba.
”Kuma da wuya inma ban zame miki wahala ba.”
To amma tambayar tasa bata samu wata amsa sa ba,
inda
tayi kamar ma bata ji shi ba, kawai ta ƙara sauri suka
ƙara
dosar gabas.
Da farko Armad yayi niyyar yayi mata shiru bayanda
ya
karanci cewa ba mai son magana bace sosai ba, to
amma
shi ɗin ya kasance mai nutsuwa da kamala, amma
kuma
hakan bai hanashi bin diddigi ba, kuma koda bai
jima da
sanin mutun ba, ya kan saki jiki suyi hira sosai dashi.
A taƙaice zaka iya cewa Armad mutun ne mai saurin
sabo
da mutane da kuma barkwanci.
Yanayin daya ke ji a ransa na cewa babu wata
mugunta a
ran wannan budurwa yasa ya ƙara sakar jikinsa ya ci
gaba
da janta da zance, ”hmm..” yai ajiyar zuciya, “kinsan
kuwa
kece mutun ta farko dana fara gani mai irin launin
fatata
tun bayan bari na garinmu?
”Kinsan shi ne dalilin da yasa nace in kin yarda, na
kiraki
yaya!
Haka dai Armad yayi ta ƙoƙarin janta da hira amma
ina
ko ƙala bata ce masa, har dai ya gaji shima yayi shiru
suka
ci gaba da tafiya.
Jim kaɗan bayan Armad yayi shiru, sai abinda tun
bayan
farkawarsa yake ta kai komo a zuciyarsa ya ƙara faɗo
masa, inda ya shiga tunani akan fasahar da yayi
amfani da
ita ya halaka wancan Dordor, wato ‘Wilbafosiyan
Siwod
Dans!’
”Har yanzu acikin ƙarnika goma dake ƙunshe acikin
wannan hari, na kasa kwarewa akan koda kaso goma
na

ƙarni guda ɗaya.
”Hasali ma aduk lokacin da nayi amfani da wannan
fasaha,
saina rasa inda kaina yake, sai dai kawai na buɗe ido
na
ganni a wata duniyar kawai.
”Gashi yanzu bama tare da Baba Zaikid, ban ma san
yadda
zan iya ci gaba da koyon wannan fasaha ba!
”Hmmm..” yai ajiyar zuciya shi kaɗai acikin duniyar
tunaninsa.
Can alƙawarin daya ɗauka na cewa lallai sai ya cika
burin
mahaifiyar sa na ganin cewa ya nemo wannan
mutun da
akewa laƙabi da Tirifil-fakta kuma ya gabatar dashi a
gareta, ya faɗo masa.
Nan take idanunsa suka kaɗa da kafiya da kuma
jajurcewa, wanda a wannan lokaci wani sabon
tunani ya
bayyana acikin kansa, ”na san cewa lallai duk da ban
daɗe
da zuwa wannan doron ƙasa ba, nasan cewa lallai a
yanzu
bana daga cikin jaruman gaske abin misali koda
kuwa
acikin sa’anni na, ina ji a jikina cewa da dama sun fini
kwarewa ta kusan kowanne fanni.
”Duk da cewa a yanzu bani da masaniyar yaya
wannan
tafiya tawa ta nemo wannan mutun zata kasance ba,
amma
lallai nasan abu ɗaya; cewa a yanda nake ɗin nan
bazan ko
iya kare kaina daga cutarwa ba, ballantana wani abu.
”Saboda haka abinda ya zama wajibi a gareni shi ne
na
zama jarumi, ya zama wajibi a kaina na koyi duk
wasu
hanyoyi na horo da suke akwai a wannan ƙasa.
”A yayinda nake karɓar horo na sai kuma na ci gaba
da
bincike akan yadda zan cimma manufa ta.
”Bari muga… a doron ƙasa ta uku kowanne yawancin
mutane koyarwar manyan gidaje suke bi a
makarantunsu,
hmm… ban sani ko nanma haka suke.
”Idan haka suke, to kawai sai na duba naga wanne
gida ne
yafi kama da nawa.
”Tunda ban tawo da wasu kuɗi ba, saina yi aikin ƙarfi
na

samu kuɗi na biya na shiga.
”Idan ma dai kuma ba wannan tsari suke bi ba, to
koma
dai yaya ne zanyi duk yadda zanyi, naga na cimma
buri
na shiga da kuma karɓar horon. Dama a gida ban
taɓa
samun damar shiga makarantar yaku-bayi ba,
saboda haka
ina ganin abu ne da zai bada ma’ana.”
Yana zuwa nan a zancen zucin da yake, wani ɗan
ƙaramin
murmushi ya bayyana a gefen bakinsa yana mai
ɗokin
wanne irin sabon tsari zaije ya tarar, a doron
wannan ƙasa.
Yana cikin wannan hali sai yaga wannan budurwa ta
tsaya
cak inda shima ya tsaya gami da ƙura mata ido yana
ƙoƙarin tambaya ko me yasa suka tsaya sai ta rigashi
magana da cewa, ”munzo!”
Armad ya ɗaga kai gami da ƙura ido amma a iya
hangensa
bai ga wani banbanci ba.
Ya kalli kudu ya kuma kalli arewa amma duk da haka
baiga komai ba.
Yana niyyar ƙara yin magana ta ƙara rigashi da cewa,
”a
ƙa’idar wannan waje babu wanda yake iya ganin
wani, shi
yasa duk da bani kaɗai na fara wannan jarrabawa ba,
kuma duk da cewa dukkanin masu jarabawar a waje
ɗaya
suke amma babu wanda zai iya ganin wani.
”Badan komai ba saboda, duk idan wani ya wuce
gaba
ɗaya hijabin dake rufe hanyar na sinadarin Negrinki
zai
ɗauke gaba ɗaya.
”Shi yasa kowa dole ne yayi jarabawar sa a wajensa
daban. Tana faɗar haka ta ɗaga hannu ta nuna masa
can
gabansu da ɗan yatsa, ta kuma fara tafiya gami da yi
masa
inkiya daya biyota.
Har sun kusa ƙarasawa sai ta ja wani dogon
numfashi,
sannan ta ce, ”koma daga ina kake, kuma koma taya
ya
kazo wannan waje bai shafe ni ba, amma kayi sani
cewa
fitarmu daga wannan waje nada matuƙar wahalar

gaske.
”Saboda ƙarfi da taurin hijabin sinadarin Negrinki,
dake
gaba lallai ni kaina yafi ƙarfin na iya wuceshi a
shekaru da
dama masu zuwa.
”Saboda haka ina gani wannan shi ne iyakacin
taimako da
zanyi maka.” A dai-dai sanda ta gama faɗar hakan
sun iso
wajanda suke iya hangen wani waje irin na
musamman a
gabansu, wanda gabaki ɗaya ya banbanta da dukkan
sauran wajen da Armad ya gani tun shigowarsa.
Kallon farko da Armad yayiwa wajen yaji zuciyarsa ta
buga da ƙarfin gaske wanda sai da yasa ya ɗan ja
baya.
Ba komai bane ya janyo haka ba illa wani mutun
mutumi
dake tsaye kimanin taku ɗaya bayan an shiga wajen.
Gaba ki ɗayan shashin dake gaban nasu a rine yake
da
launin shuɗi wanda yake garwaye da launin ja.
Kama daga ƙasar wajen zuwa sama zuwa komai dake
kewayen wannan launi ne dashi, face wannan
mutunmutumi shi kaɗai.
Wanda ke riƙe da doguwar takobi a hannunsa na
hagu,
wadda ke a ɗage tana nuni izuwa gabansa da ita, kai
kace
yana neman fafatawa ne da dukkan duniya baki
ɗaya.
Sanye yake da sulke sannan kuma akwai tambarin
Miyura
a goshinsa wanda ke ɗauke da wani yare da Armad
bai
sanshi.
Gashi dai mutun-mutumi ne kawai, amma irin
girman
izzar da Armad yake ji tana tashi daga jikinsa yasan
cewa
babu wani abu dazai iya kwatanta tata dashi, kai bai
ɗau
lokaci bama ya tabbatarwa da kansa cewa baima kai
matsayinda ko kuma kace baima cancanci ya ce zai
auna
buwayar wannan Izza dake tashi daga jikin wannan
Mutun-mutumi ba.
Amma a dai- dai wannan lokaci da Armad ya jada
baya
idanunsa suka kai kan idanun mutun-mutumin inda

nan
take mutun-mutumin ya buɗe idonsa ya kuma kalli
Armad.
Babu abinda Armad yake gani a ransa illa irin
wannan
kala data cika wajen dake gabansa cike acikin
wannan
idon.
Babu shiri yaji tsananin ruɗani da firgici acikin ransa
irin
wanda bai taɓa ji ba.
Kafin ƙiftawar ido da bismilla zuciyarsa ta tabbatar
masa
da cewa idan ya ci gaba da kallon idon wannan
mutunmutumi zuwa daƙiƙu biyu masu zuwa, to lallai
gabaki
ɗaya jikinsa sai ya tarwatse gabaki ɗayansa.
To amma tashin hankalin shi ne tuni yake ta ƙoƙarin
janye
idon nasa amma abin yaƙi yiwuwa tamkar ba’a
jikinsa
yake ba.
A dai-dai lokacin da ya fara ɗebe haso daga rayuwa
saboda tsananin firgici, a dai-dai lokacin ne wannan
mutun-mutumi ya rufe idonsa, wanda hakan yasa
Armad
ya dawo cikin hayyacinsa.
Amma kafin kace meye wannan ya jada baya
kimanin
taku biyar imda ya faɗi ƙasa gami da yin aman jini.
Can bayan wani lokaci ya farfaɗo, yana buɗe ido
yaga
wannan budurwa tana riƙe dashi duk fuskarta cike
da
damuwa.
Amma tana ganin ya farka saita sakeshi, gami
tambayarsa
mai ya faru.
Baima tsaya tunanin wani abu ba ya gaya mata duk
abinda
ya gani.
Yana ambatar cewa sun haɗa ido da wannan mutunmutumi, yaga fuskarta tayi matuƙar canjawa, wanda
nan
take ta cika da firgici gami da miƙewa tsaye tana
kallonsa.
Bayan ƴan daƙiƙu ta fara magana aciki, idanunta
cike da
hargitsi, ”waye kai!!!
”Kuma daga ina kake!!!”

Nidinne dai Shuraih Usman inkiya
99%
Daga taskar magajin wilbafos
MAGAJIN WILBAFOS
Marubuci: Dr Abdullahi Muhammad Ibrahim
Babi na 17: Sadaukarwan Nusi
Post by: Shuraih Usman
@shuraih 99%
www.facebook.com/hausaebooks
.
.
N an take abubuwa da dama, musamman hikayoyi
da
suka shafi wannan mutun-mutumi dake wannan
waje, suka fara kai-komo acikin ranta.
Cikin tsammani ta buɗe baki da niyyar fara yi masa
tambayoyi, to amma da yake shima kamar sunyi
anko ne,
domin babu abinda ke kai-komo a zuciyar ta, banda
tambayoyin nan guda biyu; wai shin wanene wannan
yaro
da har ya isa ya ga mutun mutumin Daikirin, kuma
daga
ina ya fito?
Hakan ne yasa duk su biyun sukai anko wajan buɗe
bakunan su da niyyar yiwa juna tambaya, amma a
dai-dai
wannan lokaci ne kwatsam babu tsammani idanun
Armad
suka rufe ruf, sannan babu alamar rai a tattare dashi,
ya
faɗi kasa da ƙarfi a sume.
Kallo ɗaya kacal zakai masa kasan yayi zazzafan suma
ne
irin wanda bashi da nisa sosai da mutuwa.
Cikin tsananin mamakin abinda ke faruwa da Armad
tayi
firgit ta matsa daga kusa dashi zuwa nesa, inda ta
zauna
tana haki.
Ta dubeshi cikin mamaki da firgici zuciyarta cike da
tunanin maike faruwa ne, kuma mai ya kamata tayi?
To amma bata ma gama tunanin nata ba, Armad ya
ɗan
farka, inda ta dubeshi fuskarta cike rashin sanin mai
ya
kamata tayi.
To amma a wannan lokaci yana farkawa nan take ba
tare
da ya cika cikakkiyar daƙiƙa ba, ya ƙara faɗawa cikin
suma. Sannan kuma jikinsa ya fara jijjiga.

Tana dubansa ta tabbatar da cewa lallai wannan shi
ne
lokaci na ƙarshe da zata yanke shawarar kota taimaki
wannan yaro da bata taɓa sani ba a rayuwarta, ko
kuma ta
bari ya halaka!
Badan komai ba sai dan cewa wannan suma na
ƙarshe da
Armad yayi, ya bayyana ƙarara a fuskarsa da jikinsa
cewa
ruhinsa gaba ɗaya bazai iya ɗaukan wahalar wani
suman
ba, kuma lallai idan haka ta faru to lallai zai halaka,
wato
dai dukkan alamunsa sun nuna ya kai iyakacin
ƙololuwar
juriyarsa.
Fuskarta ta yamutse cikin tunani, kai daka ganta
kasan
cewa tana cikin ruɗani ne da ruhinta, akan cewa ta
rasa
wanne mataki ya kamata ta ɗauka.
Bayan sama da daƙiƙa talatin ana cikin wannan hali,
a
wannan lokaci jikin Armad ya fara karkarwa irin
wadda
duk baiyi ba a baya.
Nan take fatar jikinsa ta fara tsufa tamkar wanda ya
wuce
shekaru aru-aru a ɗan wannan lokaci, kai daka
ganshi
kasan ya tashi daga wannan ɗan yaro mai yawan
murmushi da barkwanci, zuwa wani tsohon mutum
mai
yawan shekaru.
”Yanzu haka zan bar doron ƙasa ba tare da kammala
alƙawari na, na nemo Tirifil-fakta ba?” Wannan ita ce
tambaya ɗaya dake gilmawa acikin zuciyar Armad,
yayinda yake tsaka da wannan suma nasa.
To amma a dai-dai lokacin da rayuwarsa take cikin
tsananin hatsarin salwanta…
Sai kawai yaji wani abu ya shiga bakinsa.
Bama shida ƙarfin taunawa, amma jim kaɗan sai yaji
ya
narke a bakinsa, ya kuma wuce maƙogoronsa, inda
ya
zarce zuwa cikin cikinsa.
Haka na faruwa, cikin abinda bai wuce daƙiƙa ɗaya
ba,
Armad yaji wani mahaukacin ƙarfi ya bayyana acikin
kwakwalwarsa inda nan take yaji lurarsa ta ƙaru
matuƙa

sama ma da da kafin ya fara suman.
Nan take wannan haske ya daki idanunsa inda suka
buɗe
tarai.
Hasken ya wuce ya daki zuciyarsa da hannayensa da
ƙafafunsa da dukkan kayan jikinsa.
Kafin kace meye wannan dukkan tsufan da da jikinsa
ya
fara yi ya ɓace ɓat, inda fatarsa ta dawo kamar
yadda take
ada.
To, duba da irin halin faran-faran da barkwanci na
Armad, yana farkawa ya fara murna , inda yayi
dogon
numfashi gami da cewa, ”hmmmmm!”Yana faɗar
haka
yana miƙa hannunsa na dama yana share gumi a
goshinsa.
Duk da bashi da cikakkiyar masaniyar mai ya faru,
amma
zai iya cankar cewa wannan budurwa tana da sa
hannu
aciki, saboda koba komai irin wannan taimako a irin
wannan waje da wuya ya faɗo daga sama.
Nan take ya fara dudduba damansa da hagu yana
nemanta. Can idanunsa suka kai kanta daga
ɓangaren
arewa maso gabas tana zaune ta haɗa kai da gwiwa.
Dud da bai kalli fuskarta ba, amma wannan kallo
ɗaya ya
isa yasa yaji irin jimamin dake tashi daga zuciyarta.
Nan take sama da tunani goma sha, da wataƙila su
suka
faru har ya samu sauƙi, suka gifta ta cikin kansa.
Kafin kace meye wannan fuskarsa ta canja inda ya
nufi
inda take cikin zafin nama.
Yana isa ya durƙusa a gefenta inda daga bisani bayan
ya
kalli yanayin da take ciki ya yanke shawarar kada yayi
magana a lokacin, wato ya ɗan jinkirta.
Nanfa ya zauna a gefenta inda bayan wani ɗan lokaci
ya
juyarda kansa daga ita ya sunkuyi da kansa inda nan
take
juyayi na tunanin meke faruwa da kuma maiya
kamata
yayi, suka cika masa kai.
Tun rana tana tsakiya suke zaune babu wanda yace
uffan
acikinsu har saida rana ta kusa faɗuwa inda a
wannan

lokaci ne wannan budurwa ta ɗago kai ta dubeshi,
wanda
a wannan lokaci zuciyarsa tuni ta gama gano masa
mafi
yawaicin abinda ke faruwa.
Ta numfasa gami da fara jawabi, ”Suna na Núsi
Djinn.
”Mutane na na ƙabilarmu da muka rage a duk faɗin
doron
ƙasashe bakwai bamu da yawa.
”Kuma a wannan zamani bamu da ƙasa ta kanmu,
hasalima da dama daga jama’armu basu da
taƙamaiman
wajen zama, sannan kuma kamar muma da muka
samu
muhalli muna iya ƙoƙarin mu wajen ganin cewa
mun
ɓoye sunan Djinn ɗin dake nasabarmu.
”Kuma saboda wannan hali da muke ciki nema muka
samar da hanyoyi da dama, waɗanda indai ɗaya
daga
cikin mu yaga ɗan uwansa na ƙabila nan take yake
ganeshi!”
Tana faɗar haka ta ɗago ido ta kalli Armad, irin kallo
mai
cike da ma’anar cewa; ”nasan kai ba ɗan ƙabilar
Djinn ba
ne, (ba Armad Djinn sunanka ba)!”
Armad dama tunda farko yasan ba Djinn ɗin bane
shi,
amma kamar yadda tsarin danginsa yake, bazai
baƴyanawa kowa sunan gidansu ba.
Armad ya juya ya kalleta gami dayi mata yaƙe
idanunsa a
rufe, fuskarsa cike alamun bata haƙuri.
Bata ce masa komai ba, kawai sai ta ɗauke kai kuma
taci
gaba da bayani,
”Djinn ƙabila ce data bada gudunmawa ta
musamman a
babban yaƙi mafi girma daya faru a duniyar aljanu
shekaru aru-aru tun kafin al’umma su fara rayuwa
akan
ƙasashen ƙasa.
Koda tazo nan a zancanta sai ta ja numfashi gami
ajiyar
zuciya, sannan tayi murmushi mai ɗauke da alamun
zurfin
tunani.’
Ta rufe jawabinta da cewa ”Wannan shi ne wani abu
daga
cikin labari na, manufa ta da kuma ƙudiri na aban

ƙasa,
wannan wani abu ne wanda bazan iya gaya maka
ba!”
To haƙiƙa duk da cewa Armad yana da ƙarancin
shekaru,
amma ba dolo bane. Domin tun daga lokacin daya
farka
ya kuma ga yanayin data shiga da kuma yadda ta
fara
bashi labarin kanta kwatsam, yasan cewa akwai wani
abu
dake damunta.
Musamman yanayin yadda take bada labarin a wani
yanayi irin mai kama da bankwana, ko kuma ɗebe
haso.
Saboda haka duk da cewa labarin nata ya motsashi,
kuma
zaiso yaji menene manufarta da ƙudirinta, shin
itama
neman Tárifil-faktan take, ko kuma tana tare da
waɗancan
mutane su Gimbiya Nostalgiya, ko kuma nata
ɓangaren
daban yake. Amma zuciyarsa tana kan tambayar
dake
cikin zuciyarsa.
Inda ya numfasa idanunsa cike sanin ya kamata ya
ce,
”Yaya Núsi, me ya faru ne wai?”
Bayan ɗan lokaci sai tayi murmushi, sannan ta ɗaga
kai, ta
dubi wannan ƙasa mai launin ja haɗe da kore a
jikinta,
tace, ”bamu da wani tsammani na fita daga wajen
nan
yanzu.”
Sannan ta ƙara wani murmushin tana cewa, ”ALLAH
mai
iko, ban taɓa tunanin rayuwata anan zata ƙare ba!”
Idanun Armad suka kaɗa da ruɗanin rashin fahimtar
mai
take faɗa, inda cikin sauri yace, ”wai me kike nufi ne?
kiyimin bayani yadda zan gane!”
Nidinne dai Shuraih Usman inkiya
99%
Daga taskar magajin wilbafos
MAGAJIN WILBAFOS
Marubuci: Dr Abdullahi Muhammad Ibrahim
Babi na 18: Mutumin dayafi kowa yawan makiya a duniya (tirifil fakta)
Post by: Shuraih Usman

@shuraih 99%
www.facebook.com/hausaebooks
.
Daga:- Taskar Magajin Wilbafos
.
Núsí ta kalleshi kallo mai zurfi, wanda acikinsa akwai
alamun tausayi, tsahon daƙiƙa goma, kafin daga
bisani ta
fara wata dariya mai matsakaicin sauti, kai daka ji
kasan
akwai tsananin ciwon rai acikin wannan dariya.
Kana daga bisani ta numfasa tace, ”Mangwaron
Negrinki!
”Zaka sha wahala matuƙa, kuma abu nema mai kama
da
samun jaki mai ƙaho, kafin ka sami wani abu guda
ɗaya
dake da muhimmancin Mangwaron-Negrinki wajen
ƙarfafa ruhi da inganta Izza, kai hasali ma akwai
hikayoyi
da dama da suka rawaito cewa idan ka samu adadi
mai
kyau ka kuma yi amfani dasu ta yadda ya dace, to
zaka
iya tashin matacce daga kabari da ƙarfin sihirin
wannan
mangwaro.
”Hakan nema yasa mallakar wannan mangwaro abu
ne
mai tsananin wahalar.
”A misali; a sama da shekaru goma da nayi a birnin
Maikironomada nayi ayyuka na kwadago da dama
kuma
na samu dukiya dai-dai gwargwado.
”Amma a lokacin da zan fito wannan jarrabawa
wadda
nasan bazata taɓa yiwuwa ba idan mutun bashi da
wannan
Mangwaro ba.
”A saboda haka na tattare dukkan tari na, na tsahon
rayuwa ta dan na sayi wannan mangwaro, amma a
ƙarshe
ban iya mallakar sama da guda biyu ba.
”Bayan zuwa na nan wurin acikin shekaru uku da
nayi
anan, na ƙarar da guda ɗaya aciki.
”Saura guda ɗaya, wanda kuma shima yanzu babu.
”A duk lokacinda kake fafatawa wajen ƙoƙarin wuce
wannan hijabi idan ka samu rauni, to fa baka da
wata
hanya mafi sauƙi face kayi amfani wannan
mangwaro,

wajen warkar da ciwon naka.
”Babban sharrin sinadarin Negrinkin dake wajen
nan, shi
ne ciwon da yake yiwa jiki baya warkewa da wuri,
ɗan
ƙarami ma yakan ɗauki shekaru da dama.
”Amma da taimakon wannan mangwaro zaka iya
rageshi
zuwa kwanaki.
”Dukkan waɗannan dalilai ne suka sa babu ta yadda
wani
mahaluƙi, zai iya wuce waɗannan wannan mataki ba
tare
da wannan mangwaro ba.”
Tana zuwa nan a zancanta ta girgiza kai gami da cize
haƙora tana cewa, ”naso na fita daga wannan waje.
Armad ya ƙura mata ido yana sauraren ta cikin
mamaki.
Tun kafin tazo nan a zancenta Armad ya gama haɗa
lissafin duk abinda ke faruwa, kuma ya gane inda ta
dosa;
wato wannan abu daya ji a bakinsa ba komai bane
illa
mangwaron-negrinkin nata guda ɗaya daya rage.
Kuma wannan yanayi na ɗebe haso daya bayyana a
fuskarta ba komai ya jawoshi ba, illa rasa wannan
mangwaron sihiri da tayi.
Bayan ya gama fahimtar komai, sai nan da nan yaji
kyautayi da ƙaunar wannan budurwa ta shiga ransa.
Irin
ƙaunar dake zuwa rai ga wanda ya taimake ka a
lokacin da
kafi buƙatar taimako.
Armad yana wannan tunani ne hankalinsa a kwance,
babu
ko alamun ayar tashin hankali a tattare dashi.
Duk da kuwa duba da cewa babban abinda yafi
ɗagawa ita
Núsín hankali shi ne rashin hanyar da zasu fita daga
wajen.
Hakan nema yasa ta dago kai ta dubeshi idanu cike
da
mamaki, tayadda duk da bata ce komai ba ya
bayyana
ƙarara a idonta cewa mamaki take da hankalin
Armad bai
tashi ba duk da cewa kuwa ta gaya masa a fili cewa
basu
da hanyar fita daga wannan waje.
Armad yai murmushi gami da cewa, ”kamata yayi a
mayarda alkhairi da alkhairi, wato ina nufin baki
sanni ba

amma kin yarda dani kuma harkin sanar dani
labarinki.
”Nima ina ganin ya kamata na gaya miki dukkan
labari na
a zahiri, kuma ina baki haƙuri dana ɓoye miki a
baya.”
Nan fa Armad ya kwashe dukkan labarinsa tun daga
dalilin fitowarsa daga doron

Please Login or Register in order to submit comment