Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Bakar guguwa
Post by: Shuraih Usman
@shuraih 99%
www.facebook.com/hausaebooks
.
Daga:- Taskar Magajin Wilbafos
___
A kowanne yanki na Ikwatora dake kowacce ɗaya daga
cikin ƙasashe bakwai na duniya, akwai wani tsibiri wanda
shi ne waje da ma'abota wannan yankin suke gani a
matsayin tsarkakakken waje. Wannan tsibiri shi ake cewa
Tsibirin-guguwa.
A duk bayan kowacce shekara sittin wata guguwa mai
ƙarfin gaske na tasowa daga Tsibiri. Wannan guguwa ita
ake kira da Baƙar guguwa. Duk lokacin da aka fara ta
akanyi watanni kamar biyar ana yinta, kuma anyi ittafaƙi
wannan iska tana da ƙarfin da zata iya tarwatsa duwatsu
da ƙarafa da al'amudai komai girmansu.
Amma acikin wannan guguwa ake fitarda shugaban da
zaiyi mulki a kowanne shashi na ikwatora a shekaru sittin
masu zuwa. Hanyar kuwa mai sauƙi ce, duk wanda yake
so ya tsaya takarar wannan kujera saiya fito ya kuma
tsaya a tsakiyar wannan guguwa har tsahon wannan
watanni biyar, indai aka kammala iskar duk wanda yai
ragowa shi ne zai zama shugaba a wannan sashi na
Ikwatora har tsahon wasu shekaru sittin masu zuwa.
To amma mulki dai bashi kaɗai ne abinda ake muradi ba
a shiga cikin wannan guguwa ba. Babban abinda ake
muradi shi ne sadakar baiwa da ake acikin wannan iska.
Babu wata irin baiwa a duniya ko kuma wani sihiri ko
kuma wata fasaha wadda baza a iya tsinta ba acikin
wannan iska ba. Sabida haka nema wasu sukan siyar da
ransu su shiga duk da kuwa sunsan cewa ƙarfin Izzarsu
bai kaiba, amma saboda kwaɗayin wannan baiwa da ake
samu.
To wannan dai shi ne kaɗan daga cikin Tarihin wannan
sashi na Ikwatora inda a dai-dai wannan lokaci Nusi take
kwance rai a hannun ALLAH tana jira Dordor mai kai biyu
yayi layya da namanta.
Sai dai kuma kash, lallai naman Nusi yafi ƙarfin wannan
Dordor, domin kuwa a dai-dai wannan lokaci ne aka fara
busa wata sarewa wadda duk wanda ya rayu a sashin
Ikwatora yasanta. Sarewar da take nuni da cewa lokaci
yayi. Wato shekaru sittin sun kewayo kenan.
Ai kuwa wannan busa tana isa kunnen wannan Dordor
yai tsalle gami da cilli da wuƙar dake hannunsa, sannan
ya taka a guje. Bawai shi kaɗai bama, duk wani Dordor
dake wajen babu abinda yake face gudu izuwa maɓoya.
Tunda dama a wannan lokaci tuni lissafi ya cika, kuma a
kowanne lokaci ana jira ne kawai aga baiyanar wannan
guguwa. Hakan nema yasa a lokacinda Nusi ta bayyana ta
iske manyan Dordor suna tsaye cirko-cirko a wannan
waje.
Ba jimawa da fara wannan busa sarkin dake mulki a
wannan lokaci wanda ya kasance Dordor ne mai kai tara
ya bayyana sanye cikin kayan yaƙi. Kowanne ɗaya daga
cikin kayikansa tara yasha kwalliya ta kayan yaƙi. Lallai
kana ganinsa kasan ya shirya saiya koma kan wannan
mulki. Izzaraa kaɗai shekaru dubu bakwai da tamanin ce.
Sannan kuma fatar jikinsa da komai na jikinsa Ja ne.
Sai dai kuma amma bawai shi kaɗai bane, akwai sauran
zaratan tsofaffin Dordor da mutane ma'abota Izza wanda
suma suke neman wannan muƙami da kuma baiwa da
za'a raba a cikin wannan baƙar guguwa.
Babu wanda yake cikin filin nan wanda Izzarsa bata kai
dubu biyar ba acikinsu, sannan kuma babu wanda baiyi
shekaru samada da hamsin yana shirin wannan rana ba
sai mutun ɗaya. Wato Nusi kenan.
Ba jimawa gari yai duhu, ko tafin hannu ba'a gani, sannan
kuma daga bisani Baƙar guguwa ta fara sauka. Sadaukai
suka fara fitowa da shirye-shiryensu da suka tanada.
_______
Babu wanda yasan taƙamaimai maike faruwa acikin
wannan baƙar guguwa, domin a duk bayan shekaru sittin
mutun ɗaya ne kaɗai yake samun nasara, shi kuma tarihi
yazo cewa indai ya bayyana abubuwan da suka faru aciki
to duk wata baiwa daya samu zai nemeta ya rasa.
Hakan yasa sai dai kawai ka samu shaɗi faɗi, amma
taƙamaimai babu wanda yasan maike faruwa.
To haka dai wannan iska taci gaba da wanzuwa tsahon
lokaci, wata ɗai-ɗai har wata biyar. Sannan daga bisani ta
fara lafawa. Inda alƙalan kowanne yanki suka fara fitowa
domin suga wane ne sabon sarkinsu.
Saida aka ɗauki wasu kwananki ukun cir, sannan komai
ya lafa gari yai haske. Alƙalai suka gabato cikin filin da aka
gudanar da wannan gasa. Amma bisa mamaki maimakon
su tararda sarki sai suka tararda da sarauniya.
Wata mace ce mai kyawun sura baƙar fata. Tsaye take
riƙe da kambun nasara wanda duk wanda yaci nasara
yake samu. Babu alamun ciwo ko rauni a tattare da ita.
Kana ganinta kasan ta cika jaruma irin ta mutanen farko.
Idanunta suna fitarda farin hasken mai ɗauke da Izza
abar girmamawa. Abin aljabi wata ƴar ƙaramar tukunyar
dinare ce a hannunta na dama, sannan kuma a hannunta
na hagu wata ƴar ƙaramar bishiya ce mai yawan koren
ganye.
Amma da dama zasu fi yadda dani idan nace babban abin
mamakin shi ne wannan sarauniya ba wata bace illa Nusi.
Wannan alƙalai suna ganinta suka zube a ƙasa cikin
gaisuwa da biyayya.
To wannan dai shi ne abinda ya kasance da Nusi bayan
rabuwarsu da abokinta Armad wilbafos.
____
A can cikin fadar Ururu kuwa yau ankai wata biyar kenan
aljani Kalkuta da aljani Netti suna azabtar da Armad duk
domin Littafin takobi, amma babu labari. Tuni hankalin
Arnad ya gushe yafi sau ɗari yana dawowa. Amma a
kowanne lokaci sai dai aljanun su ƙara ƙarfin azabar da
suke yi masa.
Tuni Armad yaci alwashin kashe wannan aljanu guda biyu
da danginsu da kuma Uznu Ururu. Yayi kuma alƙawarin
lallai bazai mutu ba saiya ɗau fansar abinda sukai masa.
Idan kuwa a sakamakon tsare shi da sukai anan babarsa
ta mutu, to lallai saiya kashe duk wani ma'aboci Ururu
sannan zai huce.
Ana cikin haka ne Armad yaga watarana wannan aljanu
guda biyu sun shigo wannan ɗaki. Suna zuwa suka ɗaure
shi, sannan suka rufe masa fuska suka fice dashi daga
cikin wannan ɗaki sannan suka ɓace sukai yamma.
___
To ko ina suka tafi da Armad?
Nidinne dai Shuraih Usman inkiya
99%
Daga taskar magajin wilbafos
MAGAJIN WILBAFOS
Marubuci: Dr Abdullahi Muhammad Ibrahim
Babi na 54: Cinikin Bayi
Post by: Shuraih Usman
@shuraih 99%
www.facebook.com/hausaebooks
.
Daga:- Taskar Magajin Wilbafos
Aljani Kalkútu da aljani Netti na keta hazo suna tattauna
al'amuran da suka shafi wannan yaro mai suna Armad da
suke azabtarwa.
Aljani Netti dai shi yake magana a wannan lokaci, "Babu
abinda ba muyiwa wannan yaro ba amma littafin takobi
yaƙi fitowa. Yau wata biyar kenan, indai abu sunansa
azaba a duniya to munyi masa shi, amma babu labari. Ni
ina ganin shawarar da shugaba Uznu ya bayar tayi dai-dai
amma kai naga hankalinka bai kwanta ba."
Kalkutu yai kyaran murya gami da kallon Armad wanda
ke ɗaure a bayansa ya ce, "Eh.... Haka ne, amma kana
ganin siyar dashi a matsayin bawa shi ne zaisa Littafin-
takobi ya fito. Kada ka manta da irin azabar da muka
gana masa. Ai ina ganin azabar da mukai masa tafi azabar
siyarwa a matsayin bawa."
Netti ya gurgiza kai tare da cewa, "Eh da wannan dan
wannan, amma koma dai mene ne yadda aka umarce mu
haka zamu yi. Zamu je mu siyar dashi a matsayin bawa ga
ɗaya daga cikin sarakunan Jinzidal ɗinnan. Sannan kuma
zamu ci gaba saka ido a kansa har illa mashaALLAH, har
sai sanda Littafin ya fito. Wataƙila idan yaji azabar bauta
Littafin ya bayyana."
Haka dai suka ci gaba da tattauna yadda suke shirin
siyarda Armad a matsayin bawa.
____
Ranar sha tara ga watan goma na kowacce shekara, ita ce
ranar da aka tana da domin yin gagarumin taron da za'a
gabatar da dukkan bayin da aka samo ta hanyar gasar
Jinzidal. Duk wani mai iko yazo ya siyi abinda yake so.
To kamar dai yadda aka sani sarakunan Jinzidal guda
biyar sune suke gudanar da wannan ciniki, kuma sukan
rarraba wajen gudanarda wannan gasa a kowacce
shekara a tsakaninsu. Idan wannan shekara a ƙasar
wannan sarkin akai, wata shekarar sai aje ƙasar wani
sarkin. To a wannan shekara a ƙasar sarki Rafiya ake
wannan taro.
Sarki Rafiya ɗaya ne daga cikin sarakuna biyar na Jinzidal,
kuma yana da iko akan miliyoyin mutane da kuma
ɗaruruwan ƙasashe.
Wajen da aka tanada domin yin cinikin bayin dai wani
ƙatoton ɗakin taro ne mai hawa-hawa har guda uku.
A hawa na farko akwai mutane gama gari na zaune, a
hawa na biyu kuma ƙananun sarakuna ne, a hawa na uku
kuwa anan sarakunan Jinzidal da muƙarrabansu suke.
Daga gaban filin akwai dandamali mai ɗan tudu. Akansa
akwai wani ɗan akwati da akayi da gilashi. Ba sai ma ka
tamabaƴa ba, kana gani kasan acikin akwatin gilashin ake
saka wannan bayi domin gabatar dasu ga maiso.
Taro yayi taro kuma babu wanda bai hallara ba, saboda
haka ba jimawa aka fara shigo da bayi kala-kala ana
gabatar dasu acikin wannan gilashi ga mai buƙata.
Mai gabatarwar wani ɗan dogon mutun ne mai yawan
ƙasumba. Muryarsa tuni ta dusashe, koda yake dai dama
ba zaƙi ne da ita ba.
Bayan an gabatarda sama da bayi ashirin saiga wani
saurayi nan an fito dashi. Yana tafiya dakyar cikin ankoki
na baƙin ƙarfe. Duk jikinsa jini ne, sannan kuma rigarsa
ta yayyage.
Aka shiga da wannan saurayi cikin wajen nan, sannan
alƙalin ya saka masa kuɗi kimanin kuɗin Ayrid dubu sittin
kacal. Wannan saurayi ba wani bane illa Armad Wilbafos.
Ga dukkan alamu aljani Netti da aljani Kalkutu saida suka
saka wasu ɗalasimai a jikin Armad tayadda babu wanda
zai iya gane shi. Domin lallai da mamaki ace jaruminda
yai suna a gasar Jinzidal ta wannan shekara amma duk
taron dubunnan jama'un nan dake wajen cinikin bayin
babu wanda ya gane Armad.
Sai dai kuma wani abin Alajabi ana shirin siyarda Armad
ga wani attajirin birni kawai sai aka ji murya daga cikin
wajen hawa na uku, wato wajen da sarakunan Jinzidal ke
zaune.
Wannan murya ba wata bace illa muryar gimbiya
Nostalgiya. To koma dai ya ake ciki idanun Nostalgiya sun
gano wannan saurayi, kuma ga dukkan alamu babu
yadda za'ai aƙi siyar mata dashi.
Ana jin muryar daga inda take duk wani mai so yai
jayayya akan cinikin Armad ya fasa. Lallai babu wanda zai
iya jada sarakunan Jinzidal koshi wane ne.
Armad na cikin wannan gilashi yana rantsuwa da dukkan
abinda ya taɓa isa ai rantsuwa dashi cewa lallai tunda aka
saka shi acikin wannan gilashi to kuwa sai yaga bayan
Jinzidal. Kuma lallai ya maida shi dalilin rayuwarsa cewa
sai ya kawo ƙarshen ranar da za'a ringa saka mutane
acikin keji kamar wasu kaji ana siyar dasu. Armad dama
can ya tsani harkar cinikin bayi, to amma bai taɓa sanin
haka waɗanda ake siyarwa a matsayin bayi suke ji ba sai a
wannan lokacin. Ai kuwa nan take Armad yai rantsuwa ya
ƙara rantsewa cewa sai yaga bayan dukkan sarakunan
Jinzidal da dukkan Ururu waɗanda suka kafa harkar
cinikin bayi. Sai yaga ranar da zai kawo ƙarshen komai.
Sai ya hana dukkan cinikin bayi kafin ya daina numfashi.
A wannan lokaci Armad yaji jinin jikinsa ya fara balbalin
wuta yana soyuwa saboda baƙin cikin rashin ƙarfin
Izzarsa. Domin babu wanda Armad yafi zarga a
abubuwan dake faruwa dashi irin kansa. Armad yana
zargin kansa da rashin ƙarfin Izza, da rashin tsayawa ya
koyi abubuwa a lokacinda yayarsa taso ta koya masa.
Amma yanzu komai yazo ƙarshe. Yana da ragowar wata
ɗaya daya rage masa ya nemo Tarifil-fakta sannan kuma
ya fara shirye-shiryen ruguza dukkan sarakunan Jinzidal
da Ururu. A taƙaice dai a wannan rana ta sha tara ga
watan goma na shekarar 1853 bayan Amri Armad yai
alƙawarin yin faɗa da dukkan duniya ya kawo sabon tsari
wanda bai yadda da cinikin bayi ba.
Ai kuwa abin alajabi, tamkar wani sirri acikin jinin Armad
dama jira yake Armad ɗin yayi wannan rantsuwa, sai nan
take ya fara juyawa. Armad yaji idanunsa suna zafi
tamkar ana tsire su. Gashin jikinsa tamkar anan tsitstsige
geshi saboda zafi. Bada ban bashi da ƙarfin yin ihu bama
da tuni ya kwalla ƙara. Nan take ya fara zubarda gumi ta
ko'ina. Idan ka ganshi fassarar kawai da zakai ita ce yana
tsoron mai zaije ya tarar a wajen waɗanda suka siyeshi.
Sai dai kuma abinda shi Armad da dukkan ƴan kallo basu
sani ba shi ne a wannan lokaci ƙarfin da Armad ya gada
na zuri'ar Wilbafos a jininsa yake farkawa.
____
Ƙarfin Izzar jarumin jarumai Armad Wilbafos zai
bayyana a babi na gaba, ko wacce irin Izza ce?
Nidinne dai Shuraih Usman inkiya
99%
Daga taskar magajin wilbafos
MAGAJIN WILBAFOS
Marubuci: Dr Abdullahi Muhammad Ibrahim
Babi na 55: Sabon Farin wata
Post by: Shuraih Usman
@shuraih 99%
www.facebook.com/hausaebooks
.
Daga:- Taskar Magajin Wilbafos
_____
***
Idan ka/kin manta abubuwan da suka faru a babi na
takwas zuwa na sha biyu to ya kamata ku duba, domin
kuwa abubuwan zasu fara dawowa yanzu.
***
Wata ne daren sha bakwai a sararin samaniya, hasken
wannan wata ya cika ko'ina a sararin samaniya da sauran
ƙasashen duniyar ƙasa bakwai.
Kwatsam sai aka wayi gari hasken wannan wata ya fara
dusashewa yana duhu. Idanun duk wani abu mai rai ya
koma sama da kallo. Ba jimawa dukkan hasken wannan
wata ya ɗauke ɗif tamkar an ɗauke wuta.
Da dama mutane sun fara tunanin zazzaɓin wata ke
faruwa kuma tuni an fara shiga zulumi, malaman addinai
da dama suma sun fara nasu aikin. Kwatsam sai aka ga
wannan wata ya dawo ya fara yin haske, sai dai kuma
hasken nasa ba irin hasken da aka saba gani bane.
Wannan hasken ruwan ƙasa ne mai launin toka.
Ba jimawa mutane gama-gari suka fara shiga tashin
hankali ana raɗe-raɗen cewa masifa ce zata sauka. Amma
tsofaffin ma'abota Izza wanda suka ga jiya suka ga yau
sun san sarai maike faruwa.
A daular sarkin Jinzidal sarki Bihanzin mai
dauwamammen ciwo wani tsohon mutun ne ya farka
daga cikin wani akwatin gawa, yana buɗe idonsa wata
Izza wadda girmanta ya haura shekaru dubu goma ya
cika wannan ɗakin.
Wannan mutun dukkan jikinsa a bushe yake, fatar jikinsa
tayi ɓawo-ɓawo, bashi da maraba da gawa. Amma duk da
haka sai gashi ya buɗe bakinsa yana magana, "Jinin gidan
Wilbafos ya bayyana."
Yana gama magana ya koma ya rufe idonsa ya ci gaba da
bacci. Wannan magana daya faɗa babu inda ta isa sai
kunnen sarki Bihanzin mai dauwamammen sara.
Haka dai irin wannan mutun mai kama da gawa ya ƙara
tashi a daular Denizawa dake ƙarƙashin ƙasa ya kuma
ƙara faɗar irin abinda na farkon ya faɗa.
A can wani sashi kuwa na duniya dake kan wani siririn
tsibiri, wani mutun ne riƙe da AL'ƘURANI mai girma a
hannunsa. Idanun wannan mutun daɗe a rufe kuma
babu wamda zai iya kwatanta shekarunsa a duniya. Yana
buɗe idanunsa saiga irin hasken wannan wata aciki.
Murmushi kawai yayi irin na mutanen Sannan ya ƙara
rufe idanunsa.
Haka ire-iren wannan abubuwan al'ajabi suka ci gaba da
faruwa a dukkan dauloli na faɗin duniya.
Wannan sabon hasken farin wata kuwa ruwan ƙasa ko
ajikinsa, haka ya ci gaba da ƙaruwa yana game duniya.
A tsakiyar wannan ɗakin cinikin bayi kuwa wani saurayi
ne acikin gilashin da ake tallan bayin nan dashi. Saurayin
ya miƙe ya tsaya a tsaye yana kallon dukkan mutanen
dake wajen. Duk wanda ya ganshi zai iya tunanin tsoron
siyarwa ne yake damunsa.
Amma ba jimawa dukkan hasken wannan farin wata mai
ruwan ƙasa da ratsin toka ya fara raguwa a dukkan sassa
na duniya yana curewa a waje ɗaya.
Kan kace meye wannan dukkan hasken ya gama curewa a
waje ɗaya sannan ya fara sakkowa ƙasa a hankali a
hankali har saida yazo dai-dai idon wannan yaro dake
cikin wannan gilashi, sannan dukkaninsa ya shige cikin
idon wannan saurayi.
Wannan saurayi dai ba wani bane illa Armad Wilbafos.
Nan da nan idanunsa suka fara haske suna bada launin
hasken wannan wata wato ruwan ƙasa mai ratsin toka.
Komai da yake faruwa a idon kowa ya faru, saboda haka
a dai-dai wannan lokaci wannan mutumi dake bada
rahoton akan bayin da aka saka acikin gilashin ya fara
karkarwa yana matsawa baya.
Armad ya kalli wannan ankoki dake jikinsa, nan take
dukkan ankokin suka zube ƙasa, sannan dukkanin
ciwukan jikinsa suka warke nan take. Sannan ya ɗaga
idonsa ya kalli jikin wannan gilashi, ai kuwa hasken nan
ruwan ƙasa na dukan gilas ɗin ya tarwatse.
Armad ya bayyana a waje kamar wani ɗan ƙaramin
bajimin aljani. Inda ya haska idonsa akan dukkan
mutanen dake cikin wannan waje, nan take da dama
daga cikinsu suka fara jin karkarwa suna rawar ɗari
tamkar wanda akace mutuwa ce tsaye ke kallonsu. Koda
yake a wannan lokaci Armad bashi banbanci da mutuwar
kanta.
Idanunsa kawai haske suke suna fitarda tsananin azabar
yaƙi da ƙarfin Izza. Armad ya miƙa hannunsa sama, nan
take wata taga ta buɗe akam iska inda ya miƙa hannu ya
zaro takobinsa ta Wilbafos. Abin mamaki sai ga taurari
guda biyar a saman takobin. Armad yai murmushin
girma bayan da yaga adadin taurarin dake kan takobin
kuma ya tuna wanda suke kai a lokacin da yayi faɗa
Ikenga. Lallai Armad ya samu gagarumin canji a jikinsa
wanda keda ban al'ajabi.
Tun daga kan hawa na farko har zuwa na uku kowa yayi
shiru ba'a cewa komai. Ana haka kawai sai aka ga Armad
ya ɗaga takobinsa ya nufi kan waɗannan bayin da aka
riga aka siyar. Ko ba'a tambaya ba kasan nufin Armad ya
kwance su ya kuma ƴantar dasu a gaban dukkan duniya.
Wanda zarar Armad ya aiwatar da wannan abu, to dai-dai
yake da fito na fito da dukkan ƙabilar Ururu da kuma
Sarakunan Jinzidal biyar. Kuma lallai a wannan lokaci
zaka ga ma'abota baƙaƙen ido sun fara sauka daga ƙasa
ta farko domin kama Armad. Lallai hatta sarakunan
manyan gidajen Ururu goma sai sun sauka idan Armad
ya aikata wannan abu. Domin wannan shi ake kira da fito
na fito da Ururu.
Sai dai kuma amma a wannan lokaci ne kwatsam gimbiya
Nostalgia ta bayyana a gaban Armad tana mai murmushi.
Babi shiri Armad ya tsaya, kuma duk da ɓacin ran da yake
ciki zuciyarsa bata fasa tunano masa wannan kyakkyawar
gimbiya ba da suka haɗu a shekarun baya ba. Gimbiyar
da ta ceto rayuwarsa sau adadi da dama tun bai ma
fuskanci yadda yanayin duniya ke gudana ba.
Armad yana tuno sanda ta hanashi faɗawa rami da kuma
hawayenta guda ɗaya daya faɗa idonsa.
Sannan kuma lallai Armad yana sane da wannan sirri
daya jiyo musu acikin wannan allon tsafi, sirrin dazai
rikita duniya baki ɗaya.
Armad bai manta da fasahar Izza ta musamman, wadda
ake iya duba cikin kwakwalwar mutun aga mai yake
tunani ba wadda wannan gimbiya mai suna Zahra wadda
akewa laƙabi da Nostaljiya take da ita ba.
"N.....nostaljiya? Mai kike anan, babu ruwanki da tsakani
na da wannan mutane da suke so su ringa bautar da bil
adama. Idan kuma kika shiga tsakani na dasu, to lallai zan
manta da duk wani abu daya taɓa faruwa a tsakaninmu
na yaƙe ki, sannan kuma...."
Armad yana magana amma dole ya tsaya cak, badan
komai ba sai dan saboda kwalla daya gani acikin idanun
Nostaljiya bayan da tayi arba da kayan jikinsa a yayyage,
kuma duk sunyi faca-faca da jini.
Armad ya buɗe baƙi zai ci gaba da magana, amma a
wannan lokaci yaji hayaniyar ƴan kallon dake wajen suna
cewa, "Kai.... Wai wannan yaron ba shi ne Armad Djinn
ba daya fafata a gasar Jinzidal ba? Lallai shi ne, ya akai da
bamu gane shi ba? Wai ya akai ma za'a siyar dashi a
matsayin bawa? Mai yake faruwa?"
To ga dukkan alamu an cire dukkan hijabin dake hana
wannan mutane gane Armad, kuma lallai a wannan lokaci
kowa ya gane wanene Armad.
Nidinne dai Shuraih Usman inkiya
99%
Daga taskar magajin wilbafos
MAGAJIN WILBAFOS
Marubuci: Dr Abdullahi Muhammad Ibrahim
Babi na 56 & 57: Nostojiya nara
Post by: Shuraih Usman
@shuraih 99%
www.facebook.com/hausaebooks
.
Daga:- Taskar Magajin Wilbafos
____
_______
Nan take Nostalgiya ta juya ta kalli waɗannan ƴan kallo
da suka zo wannan cinikin bayi, ai kuwa daga cikin
girman Izzar ta sai ga SANYIN BABBAN SIHIRI nan ya fara
sauka acikin wannan waje a yanayinsa na ƙanƙara ruwan
toka. A wannan lokaci ya fara bin jikin dukkan mutanen
dake wajen, kuma duk wanda ka kalla babu abinda zaka
gani sai ƙanƙara ruwan toka nannaɗe a jikinsa.
Nostalgiya tai ƙaraji na ɓacin rai, ta ɗaga takobinta sama
takai sara kan iska. Ai kuwa saiga wasu aljanu nan guda
biyu sun bayyana suna ƙoƙarin kare wannan sara mai
ɗauke da Izzar sanyin babban sihiri.
Abu ne sananne idan ka ɗauke Farar-laya babu abinda
aljanu ke tsoro irin Sanyin babban sihiri. Nostalgiya tasan
haka kuma ga dukkan alamu tayi niyyar halaka wannan
aljanu ne baki ɗaya.
Inda tayi tsalle sama ta dira akan ruwan cikin wannan
aljanu da ƙafafunta ma'abota Izza.
Yau waye ya isa ya jada ƴar gidan Bihanzin mai
Dauwamammen Sara.
A wani irin yanayi mai kama da hauka da tsananin ɓacin
rai Nostaljiya ta hau saran wannan aljanu baji ba gani.
Jinin aljanun yayi sama, kan kace meye wannan yayi faca-
faca da ko'ina. Ko dama ɗaya bata bawa wannan aljanu
ba na kare kansu ba kafin ta aikasu lahira.
Ta juyo da idanunta ga wannan bayi da aka riga aka siyar,
idanunta na sauka akansu nan take duk ankokin dake
ɗaure dasu suka zube a ƙas.
Armad na gefe yana kallon tsananan ɓacin rai wanda har
yaso yaɗan ɗara nasa. Abu na gaba daya ji shi ne hannun
Nostaljiya ta jashi sun tashi sama inda suka fice daga
cikin wannan waje suka tashi sama.
A can cikin wajen hawa na uku kuwa manyan jarumai ne
masu wakiltar sarakunan Jinzidal. Daga ɓangaren dama
jaruman sarki Rafiya ne guda uku. Dukkaninsu Izzarsu ta
haura shekaru ɗubu biyar. Kai ɗaya daga cikinsu ma shi
ne wanda muka gani a wannan Jinzidal wadda Armad ya
taka rawar gani, wato Asifu wanda akewa laƙabi da
Ruwan Bala'i.
Asifun ne ya fara magana yana cewa, "Wannan yarinya
bata da hankali. Bansan maike faruwa ba, amma ga
dukkan alamu sa'a tana tare damu domin kuwa akwai
alamun soyayya a idanun wannan yarinya, kuma wannan
soyayyar dake idonta ta rufe mata ido ta aikata abinda zai
taimake mu mu ruguza daular babanta baki ɗaya. Saboda
haka baza mu bita ba, kuma baza muyi mata komai ba
anan. Mu barta ta gudu dashi wannan yaron. Kaga da
haka zamu samu damar cin galaba akan tsohon ɗan
adawar mu wato babanta Bihanzin. Tunda kunga duk
laifin daya faru anan kawai saimu ɗora shi akan babanta
kuma rubuta a rubuce mu aikewa da Ururu."
Asifu na zuwa nan a zancensa yai dariya mai cike da farin
cikin, sannan ya ƙara yin ƙasa-ƙasa da muryarsa domin
kada sauran mutanen dake wajen suji, "Ban taɓa tunani
babbar dama kamar wannan zata samu ba a garemu.
Lallai wannan babban labari ne muyi maza mu tashi mu
gabatar dashi izuwa sarki Rafiya."
Sauran manyan ma'abota Izzar guda biyu dake tare dashi
suka girgiza kai alamun amincewa.
_______
Babu inda gimbiya Nostalgiya ta sauke Armad sai cikin
wani sihirtaccen kogo. Wannan kogo dai waje ne na
musamman wanda ke cikin daular babanta sarki
Bihanzin, kuma babu wanda yasan dashi inba ita. A sau
da dama idan tana so ta nutsu ta tuno babarta wadda ta
mutu wannan kogo take zuwa tayi kwana da kwanaki
tana hutawa tana kewar mahaifiyar tata.
Acikin kogon dai akwai ƙorama mai bada sanyi mai ciƙe
da ni'ima da annushuwa. Ga kujeru da shimfiɗu na
alfarma, ga kuma kayan ci da sha duk na sarakuna wanda
Armad ma bai taɓa yin tsinkaye da suba.
Tana ajiye Armad ta ɗakko wata sabuwar rigarta ta
wadda akaiwa ado da dinare ta fara goggoge masa datti
da jinin dake jikinsa. Har a wannan lokaci ta kasa ɗago kai
ta dubi Armad saboda hawaye da tausayin dake idanunta.
Armad ɗin shima ya kasa cewa komai, abu ɗaya dai daya
sani shi ne abinda ta aikata a wajen cinikin bayin can lallai
saiya jawo wa babanta babbar matsala. Saboda haka bai
san mai zai fara ce mata ba. Tunda dai saboda shi take
duk wannan abun, kuma koma mai ya same ta shi ne zai
zamo shila.
Amma abu guda ɗaya daya kasa ganewa shi ne mai yasa
take wannan abubuwa. Wai anya kuwa tana cikin
hankalinta kuwa? Sai dai kuma Armad ya tuna ba wannan
ne lokaci na farko ba data fara sadaukar da rayuwarta ba
domin ta ceto shi. Yana tunano lokacinda zai faɗa
wannan rami kuma wannan dordor ya so ya halaka ta,
amma taƙi sakarsa.
Can bayan wani lokaci Armad ya riƙe hannunta ya tsayar
da ita, sannan ya ɗago da kanta domin yaga maike
faruwa acikin idanunta. Amma bisa mamaki sai kurum
Armad ya ƙara arba da irin sak abinda ya taɓa ji a
shekarun baya, wato yaji tamkar ya santa a wani zamani
mai tsaho daya gabata. Nan da nan ya cika ta yana haki.
Yau dai koma mai ake ciki sai yaji amsar dukkan
tambayar daya daɗe yana so yayi mata.
Nostalgiya taja dogon numfashi sannan ta goge fuskarta
da hankici. Ta miƙe daga inda take tana murmushi
sannan ta fara da cewa, "Ka taɓa gani na babu hijabi?"
Tambaya ce amma ga dukkan alamu ba amsa take nema
a wajen Armad ba, domin kuwa tasan cewa bai taɓa ba.
Shima Armad ɗin yasan haka, kuma nan take ya fara
ƙinƙina a lokacinda yaga kamar tana nufin cire rigar dake
jikinta. Muryarsa na rawa yana cewa, "Ehm....
Tsaya.....tsaya..... Ba saikin cire komai ba, na taɓa....."
Kawai Armad yaji Nostaljiya tasa hannu ta doke shi aka.
Nan da nan ya haɗe gira, "Laifin me kuma nayi miki
harda duka?"
Nostalgiya ta ɓata rai matuƙa tana mai cewa, "Mai ka
ɗauke ni, a gaban naka zan cire kaya. Kawai kai mana
shiru kaga mai ake yi mana, a'a!"
Bayan data gama magana saita durƙusa a gabansa tana
mai murmushi tana lallashinsa, "Kayi haƙuri na dake, ba
zafi ko?"
Armad yana rasa mai zaice, tambayar kansa kawai yake,
towai mai take nufi ne? Waishin mai ake ciki nema?
Ai kuwa ba jimawa Armad yaga dukkan wannan kogo ya
cika da wani irin haske mai matuƙar ƙayatarwa. Da farko
Armad yayi tunanin wata fitilar aka kunna, amma a
lokacin ne Nostaljiya ta kashe fitilar dake ɗakin amma
hasken kawai ƙara ƙaruwa yake. Ba jimawa Armad ya
gano cewa wannan haske daga jikinta yake fitowa. Fatar
ta gaba ki ɗaya ta juye izuwa wani abin kyalkyali da
walƙiya mai tsananin kyawu. Armad ya fara tunowa da
labarai daya karanta na tatsuniya akan wata wadda ake
kira da Lasina Naitingele wadda aka ce tafi kowa kyau a
duniya. Nan take Armad ya gano cewa wadda take
gabansa lallai ta ma fita kyau. Idanun Nostaljiya na
kaɗawa da tsananin ƙauna da tausayin Armad. Nan da
nan Armad yaji jikinsa ya mutu murus.
Dama Nostaljiya tama ɗan fishi tsaho saboda haka koda
ta jashi ya tashi ya tsaya a gefenta ya kuma kalli dattin
dake jikinsa sai yai matuƙar raina kansa. Lallai Armad ya
tabbatar babu wata mai kyawun wannan yarinya a
duniya. Fuskarta madaidaiciya ce kuma Armad bazai iya
siffanta ta taba sai dai kawai yasan cewa wannan fuska ta
ƙunshi duk wani abu da kyau zai iya bayarwa.

Please Login or Register in order to submit comment