Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

suka farkar da Ururunsu za'a raba su izuwa
mataki-mataki. Muje mu rakaki ki saka sunanki."
Suwainah tana so taje ta saka sunanta to amma bata so
tabar wajen ba tare da taga Armad ba. Domin kuwa
tuntuni take ta zulumin ina Armad ya shiga. To amma
babu yadda zatai, tunda babu wani uzuri da zata iya
gayawa ƴan matan saboda haka suka rankaya tare izuwa
cikin wannan gari.
Wannan tsibiri dai waje ne na musamman wanda yake da
tarihi na sama da shekaru dubu. Ya kasance akan iska a
tsakanin doron ƙasa ta farko da kuma doron ƙasa ta
biyu. Sunan wannan tsibiri Tsibirin Sido-Ururu.
Akan tsibirin Sido-Ururu anan ƙabilar Ururu take bawa
ma'abota Ururu horo akan yadda zasu farkar da Ururun
dake idanunsu. Asali dai ana haifar ƴan ƙabilar Ururu ne
da baƙaƙen idanuwa to amma wannan idanu na farko
basa aiki da Izza. Duk wanda yake so ya farkar da
Ururunsa izuwa matakin Izza saiya fara juyarda idanunsa
izuwa fari fat kamar irinna waɗannan ƴammata. Irin
wannan fararen idanu su ake kira da Sido-Ururu. Daga
matakin Sido-Ururu akwai horo kala-kala da ake bayarwa
kafin mutun ya ƙara juyarda idanunsa izuwa baƙaƙe. Duk
wanda yabi wannan matakai ya zama ma'aboci Ururu.
A ƙarƙashin ƙabilar Ururu mai mulkin doron-ƙasa ta
farko akwai aƙalla manyan gidaje guda goma. Kowanne
gida yana da matuƙar girman da shi kansa zaka iyai masa
kallon ƙabila mai zaman kanta. Wannan gidaje guda
goma sune kamar haka:
1)Gidan Kuyurussa'ayi Ururu: Ɗa ɗaya
2)Gidan Dumaƙisu Ururu: ƴaƴa ashirin.
3)Gidan Uznu Ururu: ƴaƴa sha takwas
4)Gidan Dul'Ururu Ururu: ƴaƴa tara.
5)Gidan Jushai Ururu: ƴaƴa talatin da uku.
6)Gidan Ƙilbaru Ururu: ƴaƴa sha tara.
7)Gidan Jidda Ururu: ƴaƴa bakwai
8)Gidan Nasára Ururu: Ƴaƴa huɗu
9)Gidan Shiysui Ururu: ƴaƴa shida
10)Gidan Fayziy Ururu: ƴaƴa sha ɗaya.
Kowanne ɗaya daga cikin gidajen nan yana da jikoki
barkatai, waɗanda sune wanda ake turowa wannan tsibiri
domin samun horo su farkar da Ururunsu. Sauran
ragowar ma'abota Ururu dake doron ƙasa ta farko idan
suna buƙatar tayarda Ururunsu sai dai suyi shi a sauran
wajaje da aka tanada a bisa doron ƙasa ta farko.
A saboda haka Armad bai sani ba, amma a dai-dai
lokacinda ruhinsa ya ɓalle ya bayyane akan wannan
tsibiri inda yayi arba da Suwainah Ururu da Zeera Ururu
jikokin gidan Ƙilbaru Ururu.
Akwai jarabawowi da dama da ake gudanarwa kafin a
zama Ma'aboci Ururu, kuma waɗannan ƴan mata,
Suwainah da ƙanwarta, abinda ya kawo su wannan tsibiri
kenan.
Kwana ɗaya kafin baiyanar ruhin Armad a wannan tsibiri,
ruhin mutanen nan uku dake muradin mallakar littafin,
wanda Ikenga yayi musu haramiya ya kuma yi cilli dasu
izuwa Tsibirin-Sido-Ururu suka bayyana. Suna bayyana
mahaifinsu Suwainah wanda shima jikane a gidan
Ƙilbaru Ururu ya ɗebe su ya nufi dasu wajen sarkin
wannan tsibiri mai Shadi Ururu, wanda jikan gidan Fayziy
Ururu ne.
Babu wani ɓata lokaci, Shadi Ururu yana ganin ba suda
Ururu yasa aka sare musu kai sannan aka binne
gawarwakinsu ba tare da kowa ya sani ba. Domin a wajen
ma'abota Ururu indai ba kada Ururu to kai ba mutun
bane. A wannan lokaci hatta su Suwainah basu san
halinda ake ciki ba, sudai kawai mahaifinsu yace kada su
faɗawa kowa labarin waɗannan mutane da suka tsinta,
sannan kuma ya gaya musu idan sunga wasu su kira shi.
Saboda haka Suwainah ta tura ƙanwarta Zeera domin ta
nemo mahaifin nasu, amma bisa mamaki ruhin Armad
ya ɓace ɓat babu shi babu alamunsa.


2)Yaku ma'abota karatun littattafan Hausa ga wata dama
ta samu. Wepsite din Hausaebooks
wanda zai ringa kawo maku littatafan hausa a cikin apk na ebook ya kuma baku daman downloading zuwa kan wayoyinku kyauta batare da sisin ku ba Zaku samu
sabbin littafai wanda babu su a kasuwa. Muna muku
barka da zuwa.
Yi hanzari ku ziyacemu
A shafin mu na facebook akan
www.facebook.com/hausaebooks


Nidinne dai Shuraih Usman inkiya
99%
Daga taskar magajin wilbafosMAGAJIN WILBAFOS
Marubuci: Dr Abdullahi Muhammad Ibrahim
Babi na 75: Miyura (2)
Post by: Shuraih Usman
@shuraih 99%
www.facebook.com/hausaebooks
.
Daga:- Taskar Magajin Wilbafos
----------
Yara ma'abota Sido-Ururu guda dubu goma ne akan
wannan tsibiri suna karɓar horo. Suwainah da Zeera biyu
ne kacal daga cikin wannan adadi. Kowanne babu abinda
yake so illa ya farkar da Ururun da tafi ta sauran ƴan
uwansa girma.
Abu ne sananne akwai Ururu mataki-mataki ɗai-ɗai har
mataki bakwai. Mataki na bakwai shi ne mataki da yafi
kowanne ɗaukaka da buwaya da girman Izza. Kaɗan ne
daga cikin ma'abota Ururu tun daga farko duniya har
izuwa wannan lokaci suka taɓa mallakar mataki na
bakwai na Ururu. Hasalima mutun uku ne kacal. Ɗaya shi
ne sarkin Ururu wanda ya ture Eyriyon Wilbafos daga kan
kujera a lokacin juyin-mulkin Amri, sai kuma yarima mai
jiran gado na Ururu wanda aka fi sani da Dúmaƙisu
Kuyúrussa'ayi Ururu, sai mutun na ƙarshe wanda shi ne
babban wazirin sarki Kuyurussa'ayi Ururu.
Mataki na shida na Ururu shima abu ne mara yawa, kuma
waɗanda aka sani dashi basu da yawa. Akwai sarakuna
goma dake jagorantar gida je goma na Ururu wanda
muka labarta a babi na baya, sarakunan da ake kira da
ASHURA. Sannan bayansu akwai wasu ƴan tsirarin
sadaukai wanda sukai shura a gidan Ururu.
Mataki na biyar shi ne iyaka da aka sani, wanda duk
wanda yaje shi ana ganin yakai ƙololuwar Izza a gidan
Ururu. Mataki na huɗu dana uku dukkansu suna da
ƙarfin izzarda zasu iya tarwatsa rundunar mutane da
aljanu komai girmanta ba tare da wahala ba. Mataki na
biyu akan yi musu laƙabi da Matasan-Ururu, wanda su
ake bawa muƙamin kyaftin-kyaftin na runduna. Mataki
na farko kuwa sune mayaƙan Ururu mafi ƙanƙanta.
Amma a hakan kowanne ɗaya daga cikinsu idan har ya
kware akan sarrafa Ururun sa shi kaɗai dai-dai yake da
runduna guda.
Abin mamaki ruhin Armad na laɓe akan wannan tsibiri
yana kallon duk abinda ke faruwa tamkar mutun mai rai.
Jiki ne kawai babu. Ba jimawa yana cikin wannan hali ya
yanke shawarar abinda zaiyi. Saboda haka ya ci gaba da
laɓewa yana nazarin wannan yara tsahon wata da
watanni. Inda ALLAH ya taimaki wannan ruhi baya
buƙatar ci ko sha, sannan kuma saboda rashin gangar jiki
yana iya shigewa ta jikin kowanne abu. Hasalima a
waɗannan watanni wannan ruhi na Armad ya gano cewa
yana iya shiga jikin mutun ko dabba harma su gana da
wannan mutun ba tare da kowa ya sani ba. A saboda
hakan ɓuya ba abu bane mai wahala ba.
A wata na goma wannan ruhi yabi wannan yarinya mai
suna Suwainah cikin wani daji inda take keɓe wa tana
koyon sarrafa al'amuran Izza.
Suwainah na tsaye a tsakankanin bishiyu masu kama
dana darɓejiya sai dai sun fisu tsayi da kauri, sannan
kuma rassansu suna da kaifi da tsini tamkar masu. Kana
ganin idanun Suwainah kasan tana da kafiya irin ta
ma'bota Ururu.
A waɗannan watanni da ruhin Armad yayi yana nazarin
waɗannan yara ya gano cewa Suwainah irin mutanan
nance da zasu iya aikata koma meye akan su sami ƙarfin
Izza. Kuma wannan shi ne dalilin da yasa ruhin Armad ya
zaɓe ta.
Idanun Suwainah suna nan a farare fat sanfurin Sido-
Ururu, amma takobin ta tuni ta juye izuwa baƙa-ƙirin
samfurin Ururu. Lallai Suwainah tayi rantsuwa saita
zamanto ɗaya daga cikin matasan Ururu da ake kwatance
dasu. Musamman duba ga yadda sama da shekaru ɗari
biyar babu wanda aka samu ya fito daga gidansu wanda
ƙarfin Ururunsa yakai mataki na biyar. Wanda hakan yasa
ake ganin gidan nasu ya fara rushewa. Amma Suwainah
tayi rantsuwa lallai saita ɗago da wancan martaba a
matsayinta na ɗaya daga cikin ƴan gidan.
Hannunta a miƙe, tana riƙe da doguwar takobin.
Idanunta a rufe tana fuskantar yamma. Saboda yadda ta
tsaya a ƙame tare da miƙe ƙafa ɗaya da kuma ɗage ɗayar
ƙafar, lallai zaka ce mutun-mutumi ne wanda bai taɓa
motsi ba.
Ruhi da Izza na Ururu na kewaye da jikinta. Hatta wannan
bishiyu idan ka lura zaka ga suna tsoron suyi wani abu da
zai dame ta.
Acikin wannan hali Suwee ta ci gaba da tsayuwa tana
nazari da lazimin al'amuran Izza dake cikin idanunta har
saida asubahi ta gabato. Sannan ta buɗe idanunta, inda
wani baƙi mai ɗauke da Izzar gidan Ururu ya bayyana a
idanun nata tsahon daƙiƙa biyar kafin daga bisani ya
ɗauke idon ya koma fari.
Suwainah ta nufi gindin bishiyar dake kusa da ita inda ta
ajiye kayanta, ta ɗauki robar ruwa tasha. Sannan daga
bisani ta juyo ta fara wasa da takobin dake hannunta. Kai
kace wannan takobi bata da nauyin komai, domin kuwa
yadda take sarrafa ta tana juyata tamkar kawai takobin
wani ƙari ne na hannunta.
Haka dai taci gaba da rawa da wannan takobi har saida
rana ta ɗaga, sannan ta fara shirin komawa cikin ƴan-
uwanta domin karɓar horon safe. A dai-dai wannan
lokaci ne ruhin Armad ya bayyana a gabanta, cikin
tsananin zafin nama, Suwainah ta kawo sara da takobin
dake hannunta. Amma ruhin Armad ko motsi baiyi ba. Ya
bari takobin ta ƙaraso, sannan ta sari wuyansa, amma
bisa mamaki sai takobin ta shige ta cikin wuyan tamkar
babu kamai a wajen. Ruhin yayi murmushi tare da girgiza
kai yana mai cewa, "takobinki baza ta iyayin aiki akaina
ba."
Suwainah ta ja da baya tare da fara kiran ɗalasimai.
Amma a dai-dai wannan lokaci ne ruhin Armad ya ɓace
daga inda yake sannan ya shige jikinta. Yana shiga taji
tamkar zatai atishawa amma bata zo ba. Ta tsaya tana
tunanin mai zatai amma a lokacin ne taji muryar ruhin
yana mata magana.
"Dani dake zamu iya taimakon juna. Ki taimake ni na
taimake ki."
Suwainah ta haɗe rai tana cewa, "Mai zaka iya taimako na
dashi? Na gane ka, ba kaine wanda kuka zo tare da
waɗannan mutane ba ƴan watannin baya. Dama sarki
yana nemanka."
Ruhin Armad yai kyaran murya sannan yaci gaba da
magana tamkar baiji mai take cewa ba. "Zan iya baki
ƙarfin Izzar da kike buƙata ki farkar da Ururu mafi girma
a tarihi. Idan baki yadda ba tsaya na gwada miki."
Ruhin Armad dai daya ɓalle yazo wannan tsibiri shi ne
ruhin dake cikin Miyurar dake goshinsa. Hasali idan mai
karatu bai mantaba wannan Miyura tana iya ƙarawa
Armad Izza, kuma tunda Armad ya rasa ta ya daina
samun wannan ƙarin Izza.
A dai-dai wannan lokaci, tun kafin Suwainah ta amince,
taji ruhinta ya girgiza, sannan izzarta ta fara juyawa.


2)Yaku ma'abota karatun littattafan Hausa ga wata dama
ta samu. Wepsite din Hausaebooks
wanda zai ringa kawo maku littatafan hausa a cikin apk na ebook ya kuma baku daman downloading zuwa kan wayoyinku kyauta batare da sisin ku ba Zaku samu
sabbin littafai wanda babu su a kasuwa. Muna muku
barka da zuwa.
Yi hanzari ku ziyacemu
A shafin mu na facebook akan
www.facebook.com/hausaebooks


Nidinne dai Shuraih Usman inkiya
99%
Daga taskar magajin wilbafosMAGAJIN WILBAFOS
Marubuci: Dr Abdullahi Muhammad Ibrahim
Babi na 76: Alƙawarin Urúrú da Wilbafos
Post by: Shuraih Usman
@shuraih 99%
www.facebook.com/hausaebooks
.
Daga:- Taskar Magajin Wilbafos
----------
A dai-dai wannan lokaci, idanun Suwainah suka kaɗa
sukai baƙi-ƙirin, ta fara ƙoƙarin fitarda da ruhin Armad
daga jikinta.
Amma ana cikin haka taji izzarta ta fara girgiza tana
juyawa. Jikinta ya fara ɗaukan zafi, kafin daga bisani taji
wani tsananin ƙarfi irin wanda bata taɓa jinsa ba. Nan
take taji a ranta cewa indai za'a zo yin jarabawar rantsar
da Ururu a wannan hali sai tayi nasara.
Tana cikin haka taji muryar ruhin Armad na cewa, "zan
iya baki izza sama da haka. Amma kiyi min alƙawarin zaki
yimin abu ɗaya."
Suwainah ta ɗanyi shiru na ɗan taƙi kafin ta yanke
shawara. "Mai kake so?"
Ruhi ya kada baki ya ce, "Fasahar sarrafa lokaci ta ƙabilar
Ururu."
Suwainah tai murmushi tare da cewa, "Babu wanda ya isa
ya mallaki wannan fasaha idan ba manya goma na Ururu
ba wato Ashura. Kuma mai kake so kayi da ita?"
"Abinda zanyi da ita ni ya shafa. Kamar ƴadda abinda zaki
yi Ururun ki ke ya shafa. Kuma nasan kowanne ɗaya daga
cikin gidaje goma na Ururu suna da wannan fasaha guda
ɗaya a rubuce a ajiye. Idan kina son Izza to ki samo min
wannan fasaha."
Bayan tsahon lokaci tana tunani ta kada baki tace, "Ba
zanyi alƙawari ba har sai naga girman izzar da zaka bani.
Zuwa ƙarshen shekarar nan za'ayi jarabawar rantsar da
Ururu a doron-ƙasa ta farko. In har ka taimake ni na
samu matakin Ururu na biyar zuwa sama to nayi
alƙawarin samo maka wannan fasaha."
Ruhi ya kada baki ya ce, "Na amince."
Idan mai karatu bai manta ba, Uznu Ururu yayi amfani da
irin wannan fasaha ya canja sakamakon Jinzidal wanda
hakan ya bawa Armad damar wuce matakin Alkadar. Da
irin wannan fasaha abu ne mai matuƙar sauƙi ruhin
Armad ya koma jikin Armad ya kuma haɗe da gangar
jikinsa. Amma a duk faɗin duniya ƙabilar Ururu su kaɗai
keda wannan fasaha. Hasalima hatta acikin Ururu,
manyan nan guda goma wanda ake kira da ASHURA su
kaɗai keda iko su mallaki wannan fasaha.
Ruhin Armad yana da tunani nasa daban dana Armad,
sannan kuma abin mamaki kowanne yana zaman kansa
ne a matsayi ruhi guda bawai rabin ruhi ba. A taƙaice
madai abin ya saɓawa al'ada baki ɗaya. Domin kuwa
tunda ake rayuwa a duniyar ƙasa bakwai ba'a taɓa samun
wanda ruhinsa ya rabe gida biyu ba sannan kuma ya
rayu, to amma wani sirri wanda har ƴanzu ba'a san
menene ya saka Armad ya zamo mutun na farko da ya
iya rayuwa duk da kuwa ruhinsa ya rabe gida biyu.
Wani abun mamakin shi ne yadda kowanne acikin ruhin
guda biyu keda tunani nasa na musamman. Misali, ruhi
mai ɗauke da Miyura yana da wasu ilmummuka wanda
ke ƙunshe acikin Miyura wanda shi Armad baima san
dasu ba. Musamman tunda dama Armad bai gama
kwarewa wajen sarrafa Miyurar ba. Ta haka nema ruhin
yake da masaniyar wannan fasaha ta Ururu da kuma
yadda zaiyi amfani da ita wajen komawa jikin
ɗan'uwansa.
To a wannan rana ruhin Armad da Suwainah Ururu suka
ɗaura alƙawari zasu taimaki juna domin cimma burinsu.
Duk da kuwa ruhin Armad baisan cewa burin Suwainah
guda ɗaya ne kacal a duniya, wanda shi ne ta ƙarar da
dukkan ƴan ƙabilar Wilbafos da Bayajidda da suka rage.
Sannan kuma ita ma Suwainah Ururu bata da masaniyar
cewa wanda zai taimake ta burinsa ya ruguza gidan Ururu
da Rukunan su ba guda biyu na Amri da Jinzidal.
Suwainah da ruhin Armad haka suka ci gaba da
kasancewa a wannan hali tsahon wannan shekara. Ruhin
yana ƙara mata ƙarfin Izza, ita kuma tana ƙara dagewa
wajen samun horo domin cimma burinta.
----------
A can duniyar ƙasashen-ƙasa kuwa, Armad ne tare da
sarkin duba Babara ke ketawa ta cikin Bangon arewa
domin zuwa wajenda za'a fara horar da Armad.
Bayan kimanin daƙiƙa ɗari suna tafiya sai kwale-kwalen
ya fara gudu, lamarinda yasa Armad yin sauri ya zauna ya
riƙe kefensa ƙam, ya kuma rufe idonsa. Kwatsam ana
cikin haka sai jiyayi tamkar sun faɗa cikin wani ƙaton
rami, lamarinda yasa ba shiri ya buɗe idonsa. Ai kuwa yai
arba da kwale-kwalensu yana faɗowa ƙasa. Ya waiwaya
bayansa yaga wannan Bango da kuma wannan ƴar ƙofa
da suka shigo ta ciki. Nan take ya gane cewa lallai kodai
cikin tsakiyar wannan Bangon ruwa suka shigo ko kuma
bayansa.
Bayan sun shafe sama da daƙiƙa hamsin suna faɗowa
Armad ya tafa hannunsa ya kirawo duk wata fasaha da
yake da ita domin kare kansa, domin yasan koma ina
zasu faɗo to lallai yana da nisan gaske kuma jikinsu zai iya
tarwatsewa. Banda kuma cewa bai masan mai zasu tarar
ba.
Iska mai ƙarfin gaske ta cikawa Armad ido da hanci.
Amma ana cikin haka ya fuskanci cewa Babara ko a
jikinsa. Hasalima nishaɗi yake yana murmushi ganin
halinda Armad ke ciki.
Babara ya tafa hannayensa ya fito da wata ƴar tasa mai
launin ja. Acikin ta akwai wani ruwa mai ɗauke da
ɗalasimai na musamman. Kafin Armad ya farga, Babara
ya watsa masa wannan ruwa. Ai kuwa ruwan na taɓa
jikinsa yaji tamkar an zare masa rai, nan take Armad ya
sume.
Armad bai tashi farfaɗowa ba sai bayan kwanaki uku.
Yana farkawa ƴa tsinci kansa acikin wani ɗan tanti mai
duhu-duhu. Abu na farko da Armad ya fara fuskanta shi
ne wani tsananin sanyi mai ratsa ƙashi, tamkar an sashi a
tsakiyar tekun ƙanƙara.
Ana haka ya miƙa kansa ya kalli wajen tantin ta wata ƴar
taga, inda ya fuskanci cewa ƙanƙarar ce kuwa ke zuba da
gaske. A sashin arewa doron-ƙasa ta uku, akanyi sanyi
amma bai taɓa kaiwa inda ƙanƙara zata zuba ba. Saboda
haka nan take Armad ya fara karkarwa, domin kuwa
wannan shi ne karo na farko daya taɓa fuskantar irin
wannan sanyi.
Ba shiri ya fara tunanin a ina yake. Bayanda ya duba ya
tabbatar jikinsa ba ciwo saiya miƙe ya futo waje. Wata
iska mai ɗauke bushin farar ƙanƙara ta daki fuskarsa. Yai
duba izuwa ƙafarsa ta hagu yaga inda ya taka ya nutse
acikin ƙanƙara. Dukkan wajen yayi duhu tamkar lokacin
isha saboda tsananin ruri da rugugin iska da ƙanƙara
dake kaɗawa.
Yayi haka zai juya ya koma tantin sai yaji an dafa
kafaɗarsa. Inda ya jiyo amma baiga kowa ba. Nan take
Armad ya zare takobinsa ta Wilbafos sannan kuma ya
ɗaga hannunsa na hagu inda wata ƙatuwar ƙawanyar
aradu ta bayyana.
Wannan aradu ta haske wajen amma duk da haka Armad
baiga kowa ba. Can yaji an ƙara taɓa shi, amma ta
ɓangaren dama. Nan take yakai wawan sara wajen,
amma kamar yadda yai tsammani bai samu komai ba.
Armad na shirin ƙara kai wani saran yaji muryar Babara a
kunnensa. "Baza ka iya gani na ba, saboda da idon ka
kaɗai kake gani. Cikakkun ma'abota Izza suna gani kuma
suna ji koda sun makance kuma sun kurumce. Lallai idan
kana so ka rayu a wannan kurkuku na tsahon kwana ɗaya
to lallai saika fara gani izzarka bada idonka ba. Kuma
wannan shi ne mataki na farko na horonka."
Armad yaji duk bayanin da Babara yayi, kuma dama
Armad baiyi tsammanin zai samu horo ta sauƙi ba.
Amma abu ɗaya ne bai gane.
"Sarkin duba kurkukun gaske ko kuma salon-magana
kake?"
Babara yai murmushi tare da girgiza kai yana cewa, "lallai
ba salon-magana nake gaya maka ba. Wannan ita ce
kurkuku mafi girma da tsaro a duk faɗin duniyar ƙasa
bakwai. Yau sama da shekaru dubu da ɗari biyar kenan
da gina ta, amma tunda aka halicce ta ba'a taɓa samun
wani ya fita daga cikinta taba ko sau ɗaya. Duk wanda ya
shigo, ya shigo kenan har abada. Koda gawarsa baza ta
fita ba."

2)Yaku ma'abota karatun littattafan Hausa ga wata dama
ta samu. Wepsite din Hausaebooks
wanda zai ringa kawo maku littatafan hausa a cikin apk na ebook ya kuma baku daman downloading zuwa kan wayoyinku kyauta batare da sisin ku ba Zaku samu
sabbin littafai wanda babu su a kasuwa. Muna muku
barka da zuwa.
Yi hanzari ku ziyacemu
A shafin mu na facebook akan
www.facebook.com/hausaebooks


Nidinne dai Shuraih Usman inkiya
99%
Daga taskar magajin wilbafosMAGAJIN WILBAFOS
Marubuci: Dr Abdullahi Muhammad Ibrahim
Babi na 77: Mubayi'a ta farko
Post by: Shuraih Usman
@shuraih 99%
www.facebook.com/hausaebooks
.
Daga:- Taskar Magajin Wilbafos
------------
"Kurkuku?!" Armad ya faɗa cikin ɓacin rai. Yana niyyar
ƙarewa Babara tanadi sai wani abu ya faɗo masa.
Nan take ya ce, "idan a kurkuku nake to ai kaima a
kurkuku kake kenan?"
Babara yai murmushi inda dattijon takarsa ta ƙara
bayyana. "Lallai kayi gaskiya. Idan kana kurkuku to nima
ina kurkuku. Ko a baya dana gaya maka cewa na taɓa
keta rabin wannan Bango a zahiri bawai Bangon na keta
ba. Mu kanyi amfani da manya-manyan hatimai wanda
ƙungiyar duba ta duniya ta samar domin kawo yara
wannan duniya ta bango domin muyi musu horo. Amma
a zahiri hatimin yana canja taswirar waje tare da
mutanen dake kai, a saboda haka bawai cikin nan muke
kawo suba. A taƙaice dai ni kaina wannan shi ne zuwa na
wannan waje na farko."
Koda Armad yaji haka saiya haɗe gira yana mamaki. Nan
take zare ido gami da tambayar Babara. "Idan baka taɓa
zuwa ba to tayaya kake niyyar fita daga wannan waje?"
Babara najin tambayar ya sunkui da kansa ta yadda
Armad bazai iya karanta halinda fuskarsa ke ciki ba.
Lokaci ya fara tafiya, gari na ƙara duhi, sanyin dusar
ƙanƙara na keta ruhin Armad yana sashi rawar ɗari. Can
daga bisani Babara ya zube akan gwiwowinsa, kansa na
kallon ƙasa cikin miƙa wuya.
Abu na farko da Armad yayi tunani shi ne sanyi ne ya
yiwa Babara yawa, ko kuma wataƙila ciwon ciki yake.
Amma kafin Armad ya kaiwa Babara ɗauki yaga Babara
ya zare doguwar wuƙa daga aljihunsa, ya yanki tafin
hannunsa, inda jini ya fara kwaranya. Sannan yayi amfani
da hannunsa mai jini ya cake sandar tsafinsa a ƙas.
Armad ya rasa mai zaiyi tunani sai kawai yaji muryar
Babara a kunnensa. "Ni Babara Bayajidda nayi mubayi'a
ga sarkin mutane da aljanu Armad Wilbafos na uku."
Idan ba daban tsananin imani da kafiya da Armad yaji a
muryar Babara da lallai zai ɗauka wasa yake. Amma duk
da hakan Armad bai gane abinda ke faruwa ba, nan take
ya buɗe baki ya ce, "wai maike faruwa ne? Lallai kana sani
ina jin kunya, kuma idan wannan ɗaya ce daga cikin
dabarunka na horo bai bada ma'ana ba."
Babara ya ja ɗan ƙaramin numfashi tare da ƙara sunkui
da kansa yana cewa, "lallai wannan ba wata dabara bace.
Ni Babara na bar muƙami na sarkin duba na dawo
gefenka domin ganin cewa ka zama sarki wilbafos na uku.
Ina fatan zaka karɓi mubayi'a ta."
Armad yai farat ya ce, "to saboda me? Ni bance ina son
na zama sarki wilbafos na uku ba. Sannan kuma ni ban
masan abinda hakan ke nufi ba."
Babara ya amsa a nutse, tamkar dama yayi tunanin
Armad zaice hakan. "Zama sarki Wilbafos na uku ba abu
ne da zaka iya zaɓa ba koda kana so. Abu ne da mutane
su zasu gani su naɗa ka, kamar yadda yanzu nai amanna
acikin raina cewa ka cancanci wannan muƙami. Kamar
yadda na labarta maka a baya sarki Wilbafos na farko
wato Aldaima Wilbafos da Wilbafos na biyu wato Eyriyon
Wilbafos sune mutane na farko da suka taɓa yin yaƙi
domin rusa rukunan Jinzidal da Amri. Kaima yaƙin da
kake da rukunin Jinzidal yasa kabi sahunsu. Sannan kuma
daɗin daɗawa kaima ɗan ƙabilar Wilbafos ne. Na daɗe
ina ƙin jinin siyarda marasa ƙarfi da ake a ban ƙasa a
matsayin bayi dasa hannun manyan sarakunan duniya,
amma ƙungiyar duba suka nuna min basa son shiga
rigima da sarakunan Jinzidal dana Ururu domin a
cewarsu babu wata nasara da zata futo daga ciki. A
saboda haka na zaɓi na bi sahunka domin ganin an daina
wannan kaba'ira ta siyarda mutane a matsayin bayi."
"Hmmmm...." Armad yaja dogon numfashi Babara na
durƙushe a gabansa yama rasa mai zaice.
Can bayan tsahon lokaci ya ce, "to amma idan na
fuskance ka kana da wani dalili na musamman da yasa
kake ganin zan iya aiwatar da wannan abu. Domin dai
baza ka ajiye babban muƙamin ka na sarkin duba ba
kawai ka dawo ɓangare na ba tare da wannan ba. Zanso
naji mene ne."
Babara ya fara da murmushi wanda daga bisani ya juye
izuwa dariya sannan bayan ɗan lokaci ya tsagaita tare da
cewa, "lallai kamar yadda ake haifar duk wani ɗan ƙabilar
Wilbafos ko Bayajidda ko Ururu ko kuma ƴaƴan
sarkunan Jinzidal da Izza ta musamman kaima kana da
taka ta musamman. Amma bazan ɓoye maka ba, lallai
abu ɗaya tak da yasa nayi mubayi'a shi ne manufarka ta
cimma Jinzidal.
"Kada ka manta akwai wani yaro wanda aka haifa da
baiwa irin taka kuma ɗan ƙabila ta. Nasan ka gamu dashi.
Ana ce masa Ikenga O. Bayajidda. Lallai Ikenga yana da
ƙarfin da zan iya yi masa mubayi'a to amma manufarsa
ba irin tawa bace. Hasalima Ikenga tuni ya farkar da
fasahar gidan mu ta Byajidda wato Takun-sarki, wadda
Izza ce wadda ke matakin Ururu. Amma a halin yanzu kai
baka farkar da fasahar gidanku ta Wilbafos ba ballantana
asan wacce irin fasaha zaka samu.
"Sanin irin fasahar da zaka samu shi ne zai nuna ko zaka
iya karawa da Ururu da sarakunan Jinzidal. A taƙaice dai
ina gaya maka ni Babara na ajiye muƙamina na sarkin
duba a duniya nayi maka mubayi'a ba tare da sanin
wacce irin fasaha zaka samu ba. Kuma na biyo ka cikin
wannan kurkuku ba tare da sanin irin fasahar da zaka
samu ba. Kai sani cewa irin fasahar daka samu ita ce zata
nuna ko zamu iya fita daga wannan waje ko kuma anan
rayuwarmu zata zo ƙarshe."
Armad yai shiru yana sauraren Babara. Babara ya gayawa
Armad cewa fasahar sa ta Ɗorawa da Wilbafosiyan-si
wod-dans da Al-yaya duk ba nasa bane na aro ne. Da
farko Armad bai yadda ba, amma daga bisani Babara ya
labarta masa cewa kowanne kabila suma da tarin
fasahohinsu. Amma kadan daga cikin yan kabilar suna iya
farkarda fasaha ta musamman wadda zata zama tasu.
Hakan bawai yana nufin wasu baza suyi amfani da ita ba.
Sai dai kawai duk wanda zaiyi amfani da ita to kamar da
aro zaiyi, kuma bazai taba kaiwa asalin karfin masu ita ba.
Ya gaya masa fasahar Dorawa ta Hidaya ce ta ara masa,
sannan kuma fasahar Wilbafosiyan-siwod-dans ta
kakanka ce Zaikid. Hatta fasahar Al-yaya wadda bai taba
amfani da ita ba ta aro ce, asalin ta daga gidan
Maikironomada ta fito.
A saboda haka Armad yana da bukata ya farkarda
fasaharsa ta musamman tasa shi kadai.
***
*******
Yaku ma'abota karatun littattafan Hausa ga wata dama
ta samu. Wepsite din Hausaebooks
wanda zai ringa kawo maku littatafan hausa a cikin apk na ebook ya kuma baku daman downloading zuwa kan wayoyinku kyauta batare da sisin ku ba Zaku samu
sabbin littafai wanda babu su a kasuwa. Muna muku
barka da zuwa.
Yi hanzari ku ziyacemu
A shafin mu na facebook akan
www.facebook.com/hausaebooks


Nidinne dai Shuraih Usman inkiya
99%
Daga taskar magajin wilbafosMAGAJIN WILBAFOS
Marubuci: Dr Abdullahi Muhammad Ibrahim
Babi na 78: Yanayin Izza
Post by: Shuraih Usman
@shuraih 99%
www.facebook.com/hausaebooks
.
Daga:- Taskar Magajin Wilbafos
---------
Armad ya numfasa tare da duban Babara cikin mamaki
ya ce, "To amma duk da haka baka bayyana min dalilin
da yasa ka zaɓi wannan kurkuku a matsayin wajen da
zamu yi horo ba."
Babara yai murmushi yana cewa, "sannu a hankali zaka
ga dalili, ya shugaba na."
Armad najin kalmar 'ya shugaba na' ya haɗe rai. A
ganinsa irin kalmomin nan ne da yakan ji aljanu na
faɗawa iyayen gidansu acikin littattafan yaƙi. Amma haka
dole Armad Wilbafos ya karɓi mubayi'ar sarkin duba
Babara, duk da cewa bai san haƙiƙanin mai hakan ke nufi
ba.
Washe gari suka cire tanti tare da nausawa cikin dusar
ƙanƙara suka nufi gabas.
Suna ƙara nausawa waje na ƙara duhu, ba daɗewa
Armad ya gano cewa tsananin duhu ne yasa baya iya
hango abinda ke gabansu.
Babara ya dubi Armad ya ce, "A ganinka taya ya mutun
ɗan adam yake iya yaƙar aljanu? Kasan dai ba'a ganin
aljanu indai basu suka bayyana maka kansu

Please Login or Register in order to submit comment