Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

"Eh koda na mutu! Baka da labarin
akwai wasu Rauhanan aljanu goma da suka yaudari
Hidaya a shekarar 1801BA kuma suka sha guba suka
mutu kafin ta kama su. Amma Hidaya ta kira taron aljanu
tasa aka tashe su sannan ta ƙare kashesu ta mummunar
hanya. Kasan sunan da suke gayawa Hidaya a tsakanin
aljanu?"
Idan Armad yana jin irin waɗannan maganganun a game
da Hidaya sai yaji kamar ba yayarsa ba daya sani. Yai
murmushi ganin yadda fuskar Babara ta fara canjawa,
"Indai kana tare dani kada kaji komai, bazan gaya mata
ba. Amma wanne suna suke gaya mata?"
Wata dariyar mugunta tazo gefen fuskar Armad, lallai ya
samo lagon Babara tunda dai ya gano abinda yake jin
tsoro.
"Ka ƙyale wannan sunan, idan kun haɗu ta gaya maka da
kanta."
Nidinne dai Shuraih Usman inkiya
99%
Daga taskar magajin wilbafos
MAGAJIN WILBAFOS
Marubuci: Dr Abdullahi Muhammad Ibrahim
Babi na 65: kasa bakwai
Post by: Shuraih Usman
@shuraih 99%
www.facebook.com/hausaebooks
.
Daga:- Taskar Magajin Wilbafos
Haka dai Armad da Babara suka ci gaba da tafiya sannu a
hankali har zuwa faɗuwar rana. Mafi yawancin hirar tasu
Babara ne yake yiwa Armad tambayoyi akan abubuwan
da suka faru dashi a yayin neman Tarifil fakta. A dai-dai
wannan lokaci ne suka fara hangen ƙatoton bangon
ruwan nan wanda akewa laƙabi da bangon arewa. Babara
ya tsaya tare da neman waje ya zauna a ƙasan wata
bishiya.
"Nayi wa kakanka Zaikid alƙawari zan koya maka yadda
zaka sarrafa idanuwanka ka taimaki mahaifiyarka, amma
daga nan dani dakai zamu yi hannun riga. Saboda haka
har zuwa wannan lokaci, Zaikid ya barmin amanarka a
matsayin ɗalibi da malaminsa. Zanyi zaton ka bani irin
girmamawar da kake bawa Zaikid a yayin da nake koyar
dakai."
Armad yayi murmushi. Dama dai shi Armad ba mutun ne
mai raina manya ba, kuma koda Babara bai faɗa ba bashi
da niyyar raina shi.
Babara ya ƙara duban Armad, "Mai ka sani game da
tsarin ƙasa bakwai? Ina so kayimin bayani dalla-dalla."
Armad ya ɗanyi shiru yana kokwanton wacce alaƙa
wannan tambaya take dashi akan abinda Babara zai koya
masa, amma daga bisani ya yanke shawara yayi wa
Babara biyayya kawai kada yace ya rainashi.
"Ƙasashe bakwai sune kaɗai wajen da bil adama zai iya
rayuwa aciki. Nasan waɗannan ƙasashe a jere suke ɗaya
a saman ɗaya; daga doron ƙasa ta farko zuwa na bakwai.
Nisan dake tsakanin wannan ƙasashe bazai misaltu ba,
kuma haka ne yasa ƙasa ɗaya bata taɓa iya hangen wata
ƙasar. Hasalima wata ƙasar baza ta taɓa sanin samuwar
wata ƙasar ba idan banda kasancewar bangon ruwa
wanda ya haɗe dukkanin wannan ƙasashe. Shi dai
wannan bangon ruwa ya sakko ne tun daga doron ƙasa
na farko har zuwa na bakwai, kuma tun a farkon lokaci
yake tsaye a yadda yake bai daina zuba ba. Da dama daga
cikin masana sunyi rubutu akan wannan ruwa da dalilin
da yasa yake ta zuba amma yaƙi ƙarewa, sannan kuma
wajen da yake zubar yaƙi cika da ruwa yayi ambaliya,
amma har zuwa wannan lokaci amsar kawai da suka
samo ita ce 'TSAFI'. Wato dai kowa ya yadda tsafi ne ke
riƙe da wannan katafaren gangar ruwa wanda ake kira da
BANGO."
Armad yaja numfashi sannan shima ya nemi waje ya
zauna a gefen Babara kafin daga bisani yaci gaba da
bayani, "Ada bansan mai yasa ake cewa wannan ruwa
bango ba, amma lokaci na farko dana fara ganinsa shi ne
shekarar dana zo wajenka. Bayanda na tafi na haɗu dasu
Nostajiya naga yadda ake ganin wannan gangar ruwa ya
shafe ko'ina sannan yana ambaliya a tsaye cikin ƙasaita
tamkar tamkar wani bangon duniya wanda bazai taɓa
faɗuwa ba. Nan take na gane dalilin da yasa ake ce masa
Bango. A sannanne na gano cewa ashe akwai Bango ɗaya
a ɓangaren gudu ɗaya kuma a arewa: wadanda ake kira
da bangon kudu da bangon arewa. Waɗannan bangwaye
guda biyu sune suka datsa kowacce doron-ƙasa acikin
ƙasashen nan guda bakwai izuwa gida uku: ɓarin arewa,
ɓarin kudu, da kuma ɓarin tsakiya wanda shi ake kira
Ikwatora.
"Kowanne ɓari duniya ce mai zaman kanta wanda take
ƙunshe da mutane miliyoyi. A kowanne lokaci na shekara
ɓarin kudu suna da sanyi sosai kuna a sau da dama har
ƙanƙara ke zuba, amma ɓarin arewa zafi ne dasu kaf
shekara. Kakana Zaikid ya gayamin ɓarin Ikwatora sune
suke da sanyi da zafi: rabin shekara ai zafi rabi kuna ayi
ƙanƙara.
"Akwai hanyoyi biyu kacal da bil adama suke iya yin
safara daga wata doron ƙasa zuwa wata. Hanya ta farko
ita ake kira da Eycigan, hanya ta biyu kuma hanyar
jiragen ruwa. Eycigan kalma ce ta yaren Aldurish wadda
take nufin gida. Kuma haka abin yake, Eycigan tsarin
gidaje ne guda goma sha huɗu wanda aka gina su a
kowacce tasha na ɗaya daga cikin doron ƙasashen nan
bakwai. Babu wanda yasan yadda aka gina su ko kuma
yadda suke aiki, amma indai ka biya kuɗinka ka shiga ciki
to zaka bayyana a inda kake so. Bayanda ka buɗe min
wannan ƙofa na shiga a shekarun baya na gano cewa
Eycigan tana kama da irin wannan ƙofofi na tsafi da ake
yawo ta ciki. Nostaljiya ma ta buɗe min wata a ƴan
kwanakin baya.
"Hanya ta biyu ita ce amfani da jiragen ruwa ayi tafiya
daga ƙasa zuwa akan Bango. Amma duk da cewa hanyar
Eycigan nada matuƙar tsada mutane sunfi amfani da ita
saboda sharrin ƴan fashin ruwa da Dordor masu cin
naman mutane da kuma lokaci da ake ɗauka a jiragen."
Armad yai shiru yana jira Babara ya jinjina masa, domin
a ganinsa babu wani abu daya shafi fasalin ƙasa bakwai
da bai faɗa ba, amma Babara yai masa irin kallon nan
mai nuna ana so kaci gaba. Armad haɗe gira, yaya za'a ce
da saura.
Babara ya kyaɗa kai, "Eh... bayaninka yayi to amma baka
faɗa min yadda ake safara daga wani ɓarin zuwa wani ba
akan doron ƙasa ɗaya. Wato dai ina so naji yadda zaka
iya ketawa daga ɓarin arewa zuwa ikwatora zuwa kuma
ɓarin kudu duk akan doron ƙasa ɗaya? Kai sani cewa
hatta gidajen Eycigan da ƙofofin daka ga muna buɗewa
basa iya kai mutun daga wani shashi zuwa wani."
Nan take Armad gwale ido cikin mamaki. Bai ma taɓa
tsayawa yayi wa kansa wannan tamabaya ba. Duk a
tunanin Armad tafiya daga doron wata ƙasa zuwa wata
shi ne mai wahala, amma tafiya daga wani sashi zuwa
wani ba zaiyi wahala ba.
Armad ya gurgiza kai, "Ban sani ba gaskiya."
Babara yayi murmushi, "To wannan shi ne dalilin da ya
na tambaye ka bayani akan doron ƙasa bakwai, domin
najin ko kasan irin haɗarin da zaka shiga nan bada
dadewa ba."
"Hatsarin dazan shiga kuma?" Armad ya kasa yin shiru.
Babara yayi kamar baiji tambayar Armad ba yaci gaba da
maganarsa, "Ketawa ta cikin Bango wani babban abu ne
wanda hatta manyan ma'abota Izza suke jin tsoro. Kai
sani cewa Bangon arewa dana kudu suna da girma sama
da yadda kake zato ko tsammani, kuma acikin su akwai
sharrika wanda kaɗan ne daga cikin biladama suka taɓa
gani ko ji. Ina daga cikin wanda suka yadda cewa duniyar
dake cikin Bango ita ce waje mafi hatsari a duniya. Dani
dakai zamuyi tafiya acikin wannan waje, kuma aciki zan
koya maka yadda zaka sarrafa idanuwanka. Kai sani cewa
sau ɗaya kacal na taɓa iya keta rabin wannan waje. Lallai
dani dakai duk zamu iya halaka, amma na riga nayi wa
kakanka alƙawari zan koya maka yadda zaka sarrafa
idanuwa ka, kuma lallai mu ƴan ƙabilar Bayajidda bama
saɓa alƙawarinmu."
_______
1) Na ɗan samu free time, so zaku ga post ya ƙaru amma
fa ba cewa nayi zai ɗore ba. Saboda kada kuga daga baya
mun koma yadda muke yi da.
2)Yaku ma'abota karatun littattafan Hausa ga wata dama
ta samu. Wepsite din Hausaebooks
wanda zai ringa kawo maku littatafan hausa a cikin apk na ebook ya kuma baku daman downloading zuwa kan wayoyinku kyauta batare da sisin ku ba Zaku samu
sabbin littafai wanda babu su a kasuwa. Muna muku
barka da zuwa.
Yi hanzari ku ziyacemu akan
http://hausaebooks.cf
Ko kuma shafin mu na facebook akan
www.facebook.com/hausaebooks


Nidinne dai Shuraih Usman inkiya
99%
Daga taskar magajin wilbafos
MAGAJIN WILBAFOS
Marubuci: Dr Abdullahi Muhammad Ibrahim
Babi na 67: Bango
Post by: Shuraih Usman
@shuraih 99%
www.facebook.com/hausaebooks
.
Daga:- Taskar Magajin Wilbafos
____
Armad ya yamutse fuska domin tuni ya fara gajiya da
aikin da Babara ya bashi sama da sa'a uku da suka wuce.
Tun bayan da Armad ya amince zai fara koyon yadda zai
sarrafa idanuwansa a wajen Babara sai Babara ya fito da
wani ƙaton dutse daga aljihunsa ya sa Armad ya ɗora
hannunsa na dama akai.
Fuskar dutsen a shafe take, kuma launinsa fari ne fat.
Yana da faɗin da mutun uku zasu iya ɗora tafin hannunsu
saboda haka ba matsalar Armad bace wajen da zai ɗora
hannunsa, matsalarsa ita ce hannunsa ya ƙage saboda
daɗewa, sannan kuma ga wani koren haske da yake ta
walwali daga fuskar dutsen yana haske masa ido. Armad
yana ji tamkar wannan dutsen yana zuƙar wani abu a
jikinsa wanda baisan meye ba. Hasalima Babara yayi
bacci tun sa'a ɗaya data wuce, amma kafin yai bacci
saida ya jaddadawa Armad kashedin kada ya sake ya
ɗauke hannunsa daga kan dutsen har sai dutsen ya daina
haske. Babban abin haushin kuma baima gayawa Armad
amfanin dutsen ba.
Armad na gabda kwalawa Babara kira ya tashe shi ya gaya
masa ya gaji sai wannan dutse ya daina wannan walwalin
haske da yake. Armad yai ajiyar zuciya sannan ya cire
hannunsa. Yana niyyar tashin Babara sai idonsa yakai ga
wasu ƙananun rubutu akan dutsen, wanda ba daban
sunansa daya gani a farkon rubutun ba da ba wani abu
bane. Amma kalmar farko a jerin rubutun sunan sa ne.
A dai-dai wannan lokaci ne yaji muryar Babara a
kunnensa, "Miƙo muga Tsarin-runinka."
"Tsarin-ruhi?" Armad ya ɗaga gira cikin mamaki. Yasan
meye Tsarin-ruhi amma bai taɓa ganin wannan dutse ba.
Akan dutsen an rubuta::
Suna: Armad
Ƙabila: Wilbafos
Aljani: ??
Izza: Shekaru 1000
Fasaha: Kabanshisu, Wasu-wasi, Hisabi, Ƙawanya-walƙiya,
Sanyin-babban-sihiri, Ɗorawa, Wilbafosiyan-siwod-dans,
Al'yaya.
Babara yayi murmushi gami da girgiza kai, "Lallai ka koyi
abubuwa da dama a wajen Zaikid da kuma a yayin
tafiyarka ta neman Tarifil-fakta. Idan na fahimci abinda
wannan dutse yake faɗa, kakanka Zaikid shi ne wanda ya
farkar da aljaninka da kuma Izzarka, wanda shi ne mataki
na farko da kowanne sadauki ma'aboci Izza yake fara
takawa. Sannan kuma daga nan ya fara koya maka yadda
zaka sarrafa fasahar walƙiya.
"Daga bisani ya koyar dakai hare-hare wanda suke amfani
da fasahar ka ta walƙiya da kuma takobi. Ɗaya daga cikin
irin wannan hare-hare shi ne harinka na Wasu-wasi. Sai
dai matsalar wannan hari na wasu-wasi baka iya aiwatar
dashi akan mutun indai Izzarka bata fi tasa ba.
"Zaikid ya koyar dakai wasu daga cikin manyan ɗalasimai
irinsu Kabanshisu, wanda shima sau ɗaya kacal zaka iya
amfani dashi a shekara.
"Sannan kuma ya koya maka Wilbafosiyan-siwod-dans
wanda baka kware akai ba, kuma duk sanda kai amfani
dashi sai hankalinka ya gushe. Hasalima ka gayamin
lokaci na ƙarshe dakai amfani dashi ka rasa shekaru biyu
na rayuwarka ba tare da kasan yadda akai ba.
"Sannan kuma bayan ka sami Takobin Wilbafos daga
Hidaya ka fara koyar fasahar Ɗorawa wadda take baka
dama ka wanzarda Nauyi akan abokin gabarka ka hanashi
motsi. Sai dai ita ma wannan fasaha tana zuƙe
shekarunka na rayuwa wanda haka ne yasa mahaifiyarka
ta hanaka amfani da ita.
"Kafin ka rasa Miyurarka kana iya amfani da ita ka ƙarawa
kanka Izza a lokacin da kake buƙata. Sannan kuma
Miyurar taka ta baka matsayin Magajin-wilbafos.
"Ka kuma samu matsayin Al'yaya a ƙofar garin
Maikironomada, sannan kuma a gasar Non-toch-teka ka
samo Littafin-takobi.
"Ina ganin wannan sune dukkanin abubuwan da kake
dasu a yanzu idan akwai abinda na rage kai magana."
Armad yai shiru kafin daga bisani ya girgiza kai, "A'a,
komai ka faɗa."
Babara ya kyaɗa kai tare da miƙewa, "Lokaci yayi da
zamu shiga Bango, mu fara abinda ya kawo mu."
Nan take su biyu suka nufi hanya izuwa wannan
katafaren bangon ruwa wanda yake ta kwaranya tamkar
bazai taɓa tsayawa ba. Lallai wannan bangon ruwa yana
da ban al'ajabi, musamman duba ga yadda jirage suke
hawa kansa su tsaya cak suyi tafiya ba tare sun faɗi ba.
Armad ya daɗe yana mamakin yadda za'ace jirgi yana
tafiya akan Bangon, ga dukkan alamu yau zai ganewa
idonsa dalili.
Suna isowa dai-dai gaɓar inda ƙasa ta yanke Armad yaga
tamkar ansa takobi an datsa ƙasar gida biyu tayadda
Bangon ruwan yayi katanga a gaba kaɗan da inda ƙasar ta
ƙare. Armad ya leƙa tsakanin ruwan da inda ƙasar ta
yanke, inda wani ƙasaitaccen duhu yayi masa sallama.
Babara ya ɗakko Ayrid mai mataki na biyar daga
aljihunsa inda ya juyar dashi izuwa ɗan ƙaramin kwale-
kwale. Ba jimawa Babara ya jada baya yai tsalle ya
tsallake ramin dake tsakanin Bangon da doron ƙasar da
suke kai. Abin mamaki yana dira akan ruwan ya tsaya cak
da ƙafarsa. Armad yayi tunani Babara zai faɗa ƙasa cikin
ramin ko kuma ya nutse amma sai gashi ya tsaya cak
akan ruwan tamkar wanda ke kan doron ƙasa. Hankali
kwance Babara ya ajiye kwale-kwalen ya shiga ciki sannan
ya ɗagowa Armad hannu da niyyar ya taho.
Hankalin Armad bai yadda da abinda ke faruwa ba,
amma babu yadda zaiyi haka yai tsalle izuwa cikin kwale-
kwalen nan. Yana dira aciki kwale-kwalen ya ɗanyi ƙasa
alamun mutun ya shiga ciki, amma dai suna nan a tsaye
cak ba suyi gaba ba kuma basu nutse ba.
Babara ƴa dubi fuskar Armad wadda ke cike da mamaki
yai murmushi, sannan kamar yasan mai Armad yake
tunani ya fara yi masa bayani, "Kai sani cewa Bango
tamkar doron ƙasa yake, kuma daga sanda kahau kansa
babu zancen ace zaka faɗa ƙasa domin kuwa tamkar
kana kan wata doron ƙasar ne. Da sannu zaka gane mai
nake nufi. To amma yanzu cikin bangon zamu shiga,
saboda haka....."
Babara ya zaro sandarsa ta Izza daga inda ya ɗaure ta a
bayansa ya daki kan ruwan dai-dai ƙasan kwale-kwalensu.
Abu kamar almara saiga ruwan nan ya fara darewa
kwale-kwalen nasu kuma yana shigewa ciki. Armad ya
miƙa hannu ya maƙale cikin kwale-kwalen domin yana
jin tamkar zai faɗa cikin ruwan a kowanne lokaci, amma
hakan bai faru. Ba jimawa Armad ya tsinci kansu acikin
tsakiyar wannan bangon kewaye da ruwa amma ruwa
baya taɓa su.
Yana jin wani sanyi yana ratsa jikinsa tamkar wanda aka
saka masa tubalin ƙanƙara acikin cikinsa. Gashin jikinsa
ya miƙe zuciyarsa ta fara tunane-tunane. Ana samun
matsala wannan ruwa zai haɗiye su, kuma lallai sai sun
halaka. Babara dai yaga halinda Armad yake ciki amma
kawai murmushi yayi baice komai ba.
Bayan kimanin daƙiƙa ɗari suna tafiya sai kwale-kwalen
ya fara gudu, lamarinda yasa Armad yin sauri ya zauna ya
riƙe kefensa ƙam ya kuma rufe idonsa. Kwatsam ana
cikin haka sai jiyayi tamkar sun faɗa cikin wani ƙaton
rami, lamarinda yasa ba shiri ya buɗe idonsa. Ai kuwa yai
arba da kwale-kwalensu yana faɗowa ƙasa. Ya waiwaya
bayansa yaga wannan Bango da kuma wannan ƴar ƙofa
da suka shigo ta ciki. Nan take ya gane cewa lallai kodai
cikin tsakiyar wannan Bangon ruwa suka shigo ko kuma
bayansa.
Bayan sun shafe sama da daƙiƙa hamsin suna faɗowa
Armad ya tafa hannunsa ya kirawo duk wata fasaha da
yake da ita domin kare kansa, domin yasan koma ina
zasu faɗo to lallai yana da nisan gaske kuma jikinsu zai iya
tarwatsewa. Banda kuma cewa bai masan mai zasu tarar
ba.
2)Yaku ma'abota karatun littattafan Hausa ga wata dama
ta samu. Wepsite din Hausaebooks
wanda zai ringa kawo maku littatafan hausa a cikin apk
na ebook ya kuma baku daman downloading zuwa kan
wayoyinku kyauta batare da sisin ku ba Zaku samu
sabbin littafai wanda babu su a kasuwa. Muna muku
barka da zuwa.
Yi hanzari ku ziyacemu
A shafin mu na facebook akan
www.facebook.com/hausaebooks
Nidinne dai Shuraih Usman inkiya
99%
Daga taskar magajin wilbafos
MAGAJIN WILBAFOS
Marubuci: Dr Abdullahi Muhammad Ibrahim
Babi na 68: Tarihin nusi
Post by: Shuraih Usman
@shuraih 99%
www.facebook.com/hausaebooks
.
Daga:- Taskar Magajin Wilbafos
*Yanzu zamu ɗan ajiye Armad a gefe mu leƙa muga
halinda Nusi da Ikenga da kuma Miyurar Armad suke
ciki*
-------
Garin Khan
Shekarar 1835 Bayan Amri
**
Acikin babbar kasuwar dake wannan gari wata yarinya ce
kimanin ƴar shekaru shida sanye da baƙaƙen kaya
wanda kana ganinsu kasan sunji jiki. Tana tafiya da kyar
tana iya ƙoƙarinta wajen kaucewa mutane. Tana da
duhun fata sannan fuskarta nada tsayi madaidaici.
Idanunta na cike da yarinta amma kuma haɗe da rashin
tsoro. Tasan cewa bata da kowa a dai-dai wannan lokaci,
kuma hanya ɗaya da zata rayu shi ne idan tayi juriya da
jarumta ta tsaya da ƙafafunta. Domin kuwa wannan gari
ba garin su bane, kuma lallai tayi nesa da gida.
Abu ɗaya kacal da wannan yarinya take iya tunowa a
game da iyayenta shi ne rabuwarsu ta ƙarshe, da kuma
alƙawarin da mahaifin ta yayi mata na cewa bazai huta ba
saiya kaita gida wajen mahaifiyarta.
Sai dai kuma kash, wannan yarinya tasan cewa a
matsayin ta na ƴar ƙabilar Djinn komawa gida a wajenta
abu ne mai wahala. Domin kuwa garinsu mai suna
Shaniza an ƙulle ƙofofinsa sama da shekaru ɗari da suka
gabata, sannan kuma an katange bangwayensa daga
dukkan halittu, mutun ko aljan ko dordor. Amma abin
mamaki wannan yarinya tana jin yaƙini zata koma gida
watarana. Kuma lallai baza ta mutu ba sai taga
mahaifiyarta wadda ke cikin garin Shaniza. Sunan
wannan yarinya Nusi, Nusi Djinn.
Wata biyar kenan da babanta ya barta a hannun abokinsa
domin ya kula da ita a yayinda shi kuma ya tafi domin
gamuwa da wata tawaga, amma ƙaddara ta ratsa, sai
gawarsa aka dawo da ita. Koda abokin baban nata ya
tabbata a yanzu babu wani abu da zai samu saiya kore ta
daga gidansa, lamarinda yasa watanta uku kenan cir tana
rayuwa akan titi. Abincin da zata ci ma wahala yake mata.
Sauƙi ɗaya kacal da take samu shi ne abokanta guda biyu
wato Iliyasis da Cokali, wanda suma yara ne sa'anninta
wanda suke bin titi a sakamakon siyar da iyayensu da akai
a cinikin bayi na wannan shekara.
Nusi na tafe kanta na nazarin mutanen dake gefenta.
Daga ganin yadda take ɓoye fuska kasan akwai wanda
take gujewa. Ba jimawa tasha wata kwana inda babu
mutane da yawa. Tana shan kwanar ta fara gudu inda ta
ƙara shan wata kwanar dai-dai gefen wata bola inda babu
mutane da yawa. Da yake magariba ce kuma duhu ƴaɗan
fara yi da kyar ta iya hango wasu yara dake laɓe a bayan
wani ƙaton kwanon zuba shara dake gaba da ita.
Nan da nan ta isa wajen yaren, inda suka ƙura mata ido
cikin tsammani suna jira suji mai zata ce. Ita kuwa Nusi
sai ta canja fuska zuwa kalar tausayi, lamarinda yasa nan
take jikin waɗannan yara yayi sanyi. Koda taga haka saita
fashe da dariya tana cewa, "Wululu... Tsokanarku nake na
samo..."
Wannan yara dai ba wasu bane illa Iliyasis da Cokali.
Dukkaninsu suna yara, Cokali irin yaran nan me masu
ƙiba da kumburarriyar fuska mai ɗauke da kalar tsoro,
amma Iliyasis siriri ne mai tsayi kuma yafi Nusi haske sai
dai kuma shima Cokali ya fishi haske.
Nusi ta zira hannu acikin tsohuwar rigarta ta futo da ƴar
jaka mai ƙunshe da kuɗaɗen Ayrid. Suna ganin haka
sukai tsalle suka rungume Nusi cikin farin ciki, haƙarsu ta
cimma ruwa. Nusi ta zira hannu a cikin jakar ta lissafa
Ayrid ɗai-ɗai har guda ashirin ta miƙawa Iliyasis. Sannan
ta ƙara miƙawa na Cokali Ayrid ashirin. Sannan itama ta
ɗebi ashirin. Amma duk da haka jakar na nan cike da
Ayrid ko rabi basu ɗiba ba.
"Ƴar uwa mai za'ai da ragowar?" Suka tambaye ta cikin
mamaki.
"Mayar masa zanyi. Dama aikin da mukai masa na wata
biyu akan kuɗi Ayrid ashirin-ashirin ne. Tunda yaƙi
biyanmu ba laife bane idan muka kwaci kuɗinmu, amma
bai kamata mu ɗebi sama da haka ba."
Daga ganin fuskar Iliyasis da Cokali basu yadda da
wannan mataki ba, amma tunda ita ta ɗakko kuɗin babu
yadda zasu yi. Iliyasis ya buɗe baki ya ce, "To ta yaya zaki
mayar masa? Kinsan za'a iya kama ki fa tunda yanzu na
tabbatar yasan kuɗinsa baya nan, kina mayarwa zai gane
ke kika ɗauka."
Nusi ta kyaɗa kai, "Eh haka ne, amma dai duk da haka sai
an mayar masa. Wataƙila amma sai gobe. Yanzu muje
mu ci abinci mu siyi kayan sawa mu kuma nemi wajen
kwana. Wataƙila zamu samu ko ɗaki ɗaya ne da
kuɗinmu."
Su ukun suka juya suka nufi hanya domin suje su ci
abinci. Da wannan kuɗi nasu suka samu suka siyi abinci
kuma suka kama wajen kwana.
Sun kwana cikin farin ciki a wannan rana, ko ba komai
sun kwana acikin ɗaki sannan kuma cikinsu a cike da
abinci.
------
Washe gari bayan isha duhu ya fara yi, ƙasaitaccen ɗan
kasuwarnan mai suna Ɗan-darbejiya yana tafe zai koma
gida bayan rufe shaguna. A kewaye dashi akwai zaratan
samari uku majiya ƙarfi waɗanda aikinsu kawai su kare
shi. Fuskar Ɗan-darbejiya na rufe da ƙasumba da gemu
amma hakan bai hana baƙin cikin dake lulluɓe da ita
bayyana ba. Kuma zaka fuskanci lallai Ɗan-darbejiya
yana da dalilin yin baƙin cikin idan ka lura cewa jiyan nan
yayi asarar dukkan ribar da ya samu ta gaba ɗaya watan.
Babban abinda yake ciwa Ɗan-darbejiya tuwo a kwarya
shi ne bai masan yadda akai kuɗin suka ɓace ba. A iya
tunaninsa bai taɓa yarda ko da Ayrid ɗaya ba a tsahon
rayuwarsa. Hasalima saboda san kuɗi na Ɗan-darbejiya
yana da shaguna sama da goma amma yana tafiya yana
kallon hanya ko zaiga wani ya yadda kuɗinsa ya tsinta. A
cewar Ɗan-darbejiya duk wanda ya yarda kuɗi baya so
ne. Abu ne sananne duk wanda yayi wa Ɗan-darbejiya
aiki to da wuya kuɗinsa su fito, hakan nema yasa duk ƴan
kwadagon kasuwar suke gujewa yin harka dashi. Kuma
dalilin da yasa Ɗan-darbejiya yake saka yara ƙananu aiki
domin kada ya biya kuɗi da yawa.
Kwanakin baya ya saka Nusi da Iliyasis da Cokali aiki.
Kuma daga bisani ya hanasu kuɗin. Su Nusi sukai jele har
suka gaji suka daina zuwa. Amma kwanaki huɗu bayan
sun ɗauke ƙafa Ɗan-darbejiya ya wayi gari aljihunsa da
yake saka kuɗaɗensa ya yage kuma kuɗinsa sun faɗi a
tsakiyar kasuwar. Ɗan-darbejiya yai rigimarsa ya gaji,
amma babu wanda zai kama a tsakiyar kasuwa. Hasalima
da dama suna tunanin Ɗan-darbejiya haɗa labarin kawai
yayi domin kada ya biya bashin da ake binsa.
To abinka da yarinta, tunanin yara ƴan shekara shida
zuwa takwas bashi da ƙarfi. Kawai Ɗan-darbejiya yana
tafiya yana saƙe-saƙe a ransa saiga ƴar sakarsa da yake
ajiye kuɗi ta yiwo tsalle daga sama ta faɗi a gabansa. Ai
kuwa tunma kafin yayi magana ƙarti biyun dake kewaye
dashi suka rankaya a guje zuwa wajen da wannan jaka ta
taso.
Su Nusi dai sune suka cilla wannan jaka da danƙo, kuma
suna cilla ta suka rankaya a guje suka sha kwana. Amma
suna cikin gudu saiga ɗaya daga cikin ƙartin ya bayyana a
gabansu, lamarinda yasa suka juya da gudu, amma suna
juyawa suka iske ɗaya ƙaton tsaye a bayansu an saka su a
tsakiya.
Ƙaton gardin dake gabansu yai dariya gami da kyaɗa,
"Hahaha.... Nusi, Iliyasis, Cokali, dama na gayawa oga
kune kuka saci kuɗin nan yaƙi yadda."
Na bayan yai wata dariyar mugunta tare da cewa,
"Hukunci sata kisa."
***
2)Yaku ma'abota karatun littattafan Hausa ga wata dama
ta samu. Wepsite din Hausaebooks
wanda zai ringa kawo maku littatafan hausa a cikin apk
na ebook ya kuma baku daman downloading zuwa kan
wayoyinku kyauta batare da sisin ku ba Zaku samu
sabbin littafai wanda babu su a kasuwa. Muna muku
barka da zuwa.
Yi hanzari ku ziyacemu
A shafin mu na facebook akan
www.facebook.com/hausaebooks
Nidinne dai Shuraih Usman inkiya
99%
Daga taskar magajin wilbafos
MAGAJIN WILBAFOS
Marubuci: Dr Abdullahi Muhammad Ibrahim
Babi na 69: Tarihin nusi 2
Post by: Shuraih Usman
@shuraih 99%
www.facebook.com/hausaebooks
.
Daga:- Taskar Magajin Wilbafos
------
Dukkanin wannan ƙarti biyu dake kewaye dasu Nusi
Izzarsu akan shekaru casa'in da tara take. Na gaban ya
taka a hankali ya isa gaban su Nusi, a yayinda su kuma
suke ta janyewa suna ƙara takurewa a tsakiya cikin tsoro.
Gaba zaki baya damisa.
Yana isa saitin Nusi ya zaro wuƙa samfurin zabira, sannan
ya finciko Nusi yana cewa, "A fuskarka zan rubuta miki
ɓarauniya, kinga daga yau koda oga yaji tausayinku ya ce
kada a kasheku nayi miki sheda."
Babu abinda Nusi take sai karkarwa fuska cike da tsoro,
amma wannan sadauki ko a jikinsa, babu ko alamun
wasa ko tausayi a tattare dashi. Kana ganin yadda ya ɗaga
wuƙar kasan lallai bashi da niyyar tsayawa.
Sai dai kuma a dai-dai wannan lokaci ne komai dake
wannan waje ya tsaya cak tamkar wanda aka tsayar da
lokaci. Wannan sadaukai biyu dake neman halaka su Nusi
suka ƙame ƙam, idan ka kalli wannan sadauki mai wuƙa a
hannunsa zaka ganshi tsaye da wuƙa riƙe akan iska
tamkar hoto. Na bayan shima ya ƙame a dai-dai inda
yake. Da Nusi da Iliyasis da Cokali duk ba wanda yasan
inda kansa yake. Ana cikin haka wannan sadaukai biyu
tare da shugabansu, Ɗan-darbejiya, suka fara aman jini
baƙi-ƙirin. Kan kace meye wannan tuni sun isa lahira.
Duk abinda ke faruwa su Nusi basu san me ake ciki ba.
Kuma abu na gaba da suka gani shi ne bayyanarsu acikin
wani katafaren gida mai yawan bishiyu da sanyin ni'ima.
Kuyangi da sauran bayi suna ta kai-komo acikin hidima.
Idan da Armad yana nan da kallo ɗaya kacal zai yiwa
wannan gida ya gane cewa wannan shi ne gidan da suka
zauna da Nusi watannin baya.
Su kuwa su Nusi da Iliyasis da Cokali tuni sun farfaɗo
kuma suna zaune acikin ɗaki mafi alfarma acikin wannan
gida. Kewaye dasu abinci ne irin wanda basu taɓa gani ba.
Abin ka da yarinta kuma ga yunwa, babu wani tunani
haka suka afkawa wannan abinci. Bayan da suka
kammala saiga wata farar kuyanga nan tayi sallama a
garesu. Kunyangar na shigowa su Nusi sukai tsalle suka
jada baya cikin tsoro. Amma kuyangar kawai murmushi
tayi, sannan kuma ta tambayesu ko suna buƙatar ƙari.
Nan take duk su ukun suka ƙurawa wannan kuyanga ido
cikin tsananin mamaki. "Ƙari??"
Cokali ne ya fara yin magana, "a ƙaro, wallahi ban ƙoshi
ba. Rabona da abinci tun ina yaro...."
Wannan kuyanga tayi iya ƙoƙarinta amma ta kasa riƙe
dariyar dake wuyanta. Koda ganin wannan kuyanga tayi
dariya, sai itama Nusi tayi murmushi. Lallai ga dukkan
alamu ba gidan yankan kai suke ba.
Nan take wannan kuyanga ta tafa hannu, inda wasu
kuyangin guda uku suka fara safarar kwanuka izuwa
wannan ɗaki. Ba jimawa Nusi da Cokali da Iliyasis suka
ƙara afkawa waɗannan kwanuka. Lallai baza kaga laifin su
Nusi ba a wannan hali, domin kuwa da yunwa ta kashe ka
kwanda daɗi ya kasheka. Ko manya sun san haka. Sannan
kuma basu da tabbashin daga wannan rana zasu ƙara
samun irin wannan abinci. Wataƙila ma shikenan
haihata-haihata.
Wannan kuyangar ta ɗanyi kyaran murya, lamarinda ya
ja hankalin su Nusi suka ɗaga kai

Please Login or Register in order to submit comment