Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ƙirga adadin waɗannan
jar azurfar data haɗa wannan ankwa, to da zaka ga cewa
guda casa'in da tara ne dai-dai. Kowacce acikin wannan
azurfa tana ɗauke da ƙarfin shekara ɗaya na Izza. Wato
dai a taƙaice dukkan ƙarfin Niyashi na Izza yana tattare a
jikin wannan azurfa.
Yarima Niyashi ya ƙara tafa hannayensa, lamarinda ya
janyo wannan ankwa ta jar azurfa ta rikiɗe izuwa mashi
kwaya ɗai-ɗai har casa'in da tara. Kowanne mashi idan ka
duba zaka ga irin na hannun Niyashi ne.
Ba tare da ƙara ɓata lokaci ba, Niyashi ya tafa
hannayensa a karo na uku, tare da kiran sunan ɗalasimi,
"Láyukúr-mazayà!"
Ya na rufe bakinsa goma daga cikin wannan masu suka
fara ci wuta, tare da afkawa kan Armad suna masu burin
halaka shi. Lallai waɗannan masu guda goma masu ɗauke
da ƙarfin Izzar shekaru goma zasu iya bada komai domin
su zubar da jinin Armad. Duk inda suka ratsa sai kaji
ƙarar iska da ƙuwa na tashi, tamkar ita kanta iskar
tsoronsu take.
Armad na ganin haka ya ƙara yin duba izuwa wannan ɗan
taƙi dake tsakaninsa da aljaninsa, nan da nan ya zuƙo
walƙiya guda goma. Wannan walƙiya na bayyana ta
kewaye jikinsa tana haske, kafin daga bisani ta rikiɗe

izuwa ƙawanyar walƙiya ɗai-ɗai har guda goma.
Armad ya kira ɗalasiminsa, "Hushúsul-baijuru." Yana rufe
baki waɗannan ƙawanyu na walƙiya sukai kan wannan
masu guda goma.
Suna haɗuwa wata ƙara mai rikitarwa ta tashi sama, haɗe
da wani haske mai kashe ido. Kan kace meye wannan filin
fafatawar ya fara girgiza yana neman tarwatsewa. Alƙalin
wasa kuwa saida ya durƙusa domin kare idanunsa daga
tartsatsin wutar dake tashi. Tamkar ƴan kallo dake nesa
saida firgici ya cika zuciyarsu suka fara rirriƙe kujerunsu
domin tsoron kada girgiɗin da ƙasar filin wasan keyi tayi
cilli dasu.
Bayan kimanin daƙiƙu goma wannan sauti mai kama da
girgizar ƙasa ya lafa. Amma maimakon aga Armad da
Niyashi a tsaye suna hutawa, dukkaninsu sai suka ƙara ci
gaba aikawa juna hare-hare. Armad na ƙoƙarin tarwatsa
Niyashi da ƙawanyar walƙiyarsa, shi kuma Niyashi yana
ƙoƙarin soke Armad da Jan mashinsa. Babu abinda kake
ji sai ƙara mai kama da yaƙin duniya. Kan kace meye
wannan tuni anyi musayar sama da hari hamsin a
tsakaninsu.
Sai dai kuma fa a wannan lokaci ne gizo ya fara saƙar.
Domin kuwa kamar yadda ƙa'idar ƙasa-bakwai ta
kasance tun iyaye da kakanni, iyakacin izzarka iyakacin
shagalinka; idan kana da Izza hamsin to ƙawanyar
walƙiya hamsin kaɗai zaka iya zuƙa daga aljaninka.
Hakana idan kana da ɗari kawai ɗari zaka iya amfani
dasu. Har sai ka jira kimanin awanni tukunna, bayan
ƙarfin ruhinka ya dawo, wanda kuma baza ka samu
hakan ba idan ana tsaka da faɗa. Wato dai a taƙaice a
wannna lokaci ne adadin walƙiyar da Armad zai iya
amfani da ita tazo ƙarshe. A yayinda shi kuwa Niyashi
yana nan akan ganiyar ƙarfinsa.
A wannan lokaci Armad ya miƙa hannunsa domin
kwance ɗaurin dake gaban goshinsa, sai dai kuma a
lokacin ne kwatsam alamarin daya faru da Miyurarsa ya
faɗo masa. Shaf ya manta. Tunda farko Armad yayi lissafi
da cewa faɗan fito-na-fito zai kai masa, tunda zai iya
amfani da tambarin Miyurar ya ƙarawa kansa ƙarfi da
yawan Izza.
To abinka da abinda tunda aka haifeka yana tare dakai,
lallai koda Armad ba yaro bane ɗan shekara sha shida ba,
zai iya mantawa. Kuma dole sai a hankali zai saba da
rashin Miyurar.
Nan da nan Armad yayi tsalle baya cikin firgici da tunanin
maiya kamata yayi, sannan kuma ta yaya ne zai iya cin
galaba akan Niyashi wanda yana da kusan ragowar masu
guda arba'in a ƙasa.
A ɓangare guda kuwa, koda Niyashi ya gano halin da
Armad ke ciki sai yayi wata dariyar mugunta. Tare da
cewa, "dama na gaya maka, da sannu zaka gane
kuskurenka!" Yana rufe baki ya aikawa da Armad

dukkanin ragowar masun dake kewayawa a saman kansa.
Kai daka gani kasan so yake ya tsire Armad duk a huta.
Domin yana ji acikin ransa cewa lallai bazai samu
kwanciyar hankali ba idan bai halaka Armad ba a wannan
lokaci. Domin kuwa Armad ya gaya masa maganganun da
babu wanda ya taɓa gaya masa.
Dukkanin ƴan kallo da alƙalin wasa sun riga sun gama
hango Armad a lahira. Domin dai dama sunan Armad
baya daga cikin waɗannan sunaye guda shida da ake ta
kallo kafin a fara gasar. Sunayen da ake tunanin zasu
samu nasara. Shi kuwa Niyashi yana ciki. Sai dai kuma
wasu daga cikin ƴan kallon sun soma ɗan sawa Armad
kyakkyawan zaton zaiyi abin kirki. Musamman yadda
suka ga yana wasa da walƙiya cikin kwanciyar hankali.
Amma a wannan lokaci tuni suka cire rai kuma suka
ɗebewa Armad haso daga dukkan tsira.
Kai a taƙaice dai shi kansa Armad yana cikin yanayi na
kokwanton ko zai rayu. Musamman sanda yaga ratar
dake tsakanin ƙirjinsa da waɗannan masu sama da
arba'in baifi taku ɗaya ba.
____
To ko tayaya kuke ganin Armad zai kuɓuta??
Nidinne dai Shuraih Usman inkiya
99%
Daga taskar magajin wilbafos
MAGAJIN WILBAFOS
Marubuci: Dr Abdullahi Muhammad Ibrahim
Babi na 37: Motsin littafin Takobi
Post by: Shuraih Usman
@shuraih 99%
www.facebook.com/hausaebooks
.
Daga:- Taskar Magajin Wilbafos
.
A dai-dai wannan lokaci ne da Armad Wilbafos yake cikin
halin ƙaƙa ni kayi, dogayen jajayen masu sama da arba'in
masu cike da Izza suna gab da tsire shi. Sannan kuma
gashi dukkan Walƙiyar da aljaninsa zai iya bashi ta ƙare, a
wannan lokaci na tsanani da matsi, kwatsam sai yaji wani
ɗan motsi acikin aljihunsa na ciki. Kafin yayi wani tunani
akan wannan motsi da yaji kawai sai yaji wani
mummunan raɗaɗi mai zafin gaske a dai-dai wajen da
yaji wannan motsi. Kan kace meye wannan raɗaɗin ya
juye izuwa raɗaɗin garwashi. Nan take Armad yaji wajen
yana soyuwa. Da kyar ya iya tunano cewa a dai-dai
wannan wajen da yake jin wannan raɗaɗi wannan
littafin-takobin ya ajiye a wajan. Nan take ya fara ƙoƙarin
yin cilli da littafin.
Amma kafin yayi wani abu yaji wata irin Izza irin ta
mutanen farko ta shiga jikinsa. Bai san lokacin da yayi
wani ihu ba saboda zafin da yake damunsa. Kan kace
meye wannan Armad yaga ɗan taƙin dake ɗauke da

walƙiyarsa ya cika da walƙiya. Bai san daga ina wannan
walƙiya take ba, abu dai guda ɗaya daya sani shi ne lallai
wannan walƙiya ba irin tasa bace ta da. Domin akwai
wani sirri na ƙarfin Izza aciki, wanda Armad bazai iya
ganewa ba. Armad ya zuƙo wannan walƙiya daga ruhinsa
inda ya fuskanci cewa walƙiyar bata da yawa sosai, kuma
zata iya samar da Ƙawanyar walƙiya guda ɗaya ne kawai.
Sai dai kuma a jikin wannan walƙiya akwai wasu layika
jajaye guda uku suna kewayata. Kai daka gani kasan cewa
wannan walƙiya ta musamman ce.
Armad bashi da lokacin tsayawa yayi tunani sosai akan
abubuwan dake faruwa saboda haka kawai kai tsaye ya
aikawa Niyashi da wannan ƙawanyar walƙiya.
Dukkanin abubuwan dake faruwa sun ɗau lokaci wajen
bayani amma a zahiri sun faru ne cikin abinda bai wuce
daƙiƙa biyu ba.
Wata ƙara ce mai kama da girgizar ƙasa ta tashi sama,
sannan kuma wani haske ya lulluɓe ko'ina babu abinda
ake gani face rugugin tsagewar filin wasan da Armad da
Niyashi ke kai. Kan kace meye wannan komai ya tarwatse
inda bayan da abubuwa suka lafa aka ga Armad ya
bayyana daga cikin wannan rugugi yana mai riƙe da
takobinsa a hannun hagu cikin ƙasaita.
Bisa mamaki shi kuwa yarima Niyashi na kwance a sume.
Ko madai mai ya faru tsakanin ƙawanyar walƙiyar Armad
guda ɗaya da kuma masun Niyashi sama da arba'in babu
wanda ya gani. Saboda haka kowa idanunsa akan Armad
suke a kafe, suna fatan ko zai yi musu bayani akan abinda
ke faruwa. Amma ina, abinda basu sani ba shi ne shi
kansa Armad bai san maike faruwa ba. Domin kawai
abinda ya gani shi ne dukkanin waɗannan masu guda
arba'in da ɗoriya ɓacewa ɓat sukai a lokacin da suka
haɗu da walƙiyar nan guda ɗaya daya tura, tamkar ma
basu taɓa faruwa ba. Sannna kuma walƙiyar taje ta daki
Niyashi inda ta sumar dashi nan take.
Abu ɗaya da Armad ya sani shi ne wannan Littafin-Takobi
dake ɓoye acikin rigarsa lallai yana da muhimmancin
gaske.
Nan take aka buga ƙugen nasara, kuma aka bawa Armad
nasara. Inda shi kuma Niyashi likitoci suka tafi dashi.
Sai dai kuma wani abu ya faru a dai-dai lokacin da Armad
yaji motsin wannan littafin-takobi acikin rigarsa. Wannan
abu kuwa babu wanda ya sani illa mutumin da abin ya
faru dashi wato Uznu Ururu.
Acikin rigar wannan ma'aboci Ururu wani ɗan ƙaramin
allon tsafi yayi girgiza tare da fitarda wani baƙin haske
kalar Idanun ubangidansa wato Uznu Ururu. Nan take
wani ɗan murmushi na farin ciki ya bayyana akan fuskar
Uznu Ururu. Domin yasan abinda yake nema ya samu.
Wannan allon tsafi ba wani abu bane illa abinda yake
amfani dashi wajen neman littafin-takobi. Matsafansa a
ƙasa ta farko sun labarta masa cewa indai littafin takobin

ya bayyana to wannan allo zai sanar dashi. Yanzu kuma
gashi abinda ya daɗe yana nema sama da shekaru dubu
ɗaya da ɗari biyar ya samu. Nan da nan ya juyo da
hankalinsa gaba ɗaya kan Armad tunda daman abinda ya
kawo shi wannan waje kenan.
____
A can bayan fili kuwa Armad ne ya isa wajensu Nusi,
"Ahhhhh..." Nusi tayi ajiyar zuciya tare da riƙe Armad
tana cewa, "hankali na har ya tashi, ga dukkan alamu
bama saina damu dakai ba! Kai wataƙila dama ban
rakoka ba ko!" Nusi ce a gefe da sauran mutanen da suka
rako su daga garin Khan, suke ta yabawa Armad saboda
jarumtar daya nuna a karawarsa da yarima Niyashi.
"Hmmmm....kayi ƙarfi da yawa acikin ɗan ƙanƙanin
lokaci, ina alfahari da kai!" Inji Nusi, acikin zuciyarta babu
abinda take tunani sai wannan walƙiya ta ƙarshe da taga
Armad yayi amfani da ita. Lallai tasan akwai wani abu a
ƙasa. Amma dai kawai tayi shiru a lokacin domin bata so
ta faɗi wani abu dazai ɗaukewa Armad hankali daga
faɗan gaba daya rage masa.
"Yaya Armad, da ALLAH zan zamo ɗalibinka, ko na samu
na ɗan koyi abu ɗaya ko biyu!" wani daga cikin ƴan
rakiyar dake tare dasu Armad ya fara kamun ƙafa.
"Nima haka....Nima haka...."
Toh haka dai bayan kammala faɗa tsakanin Armad da
Niyashi, ire-iren waɗannan maganganu suke ta kewayawa
a tsakanin dukkanin mutanen dake wajen.
Ana cikin wannan hayaniya kuwa tuni alƙalin wasa Gali,
ya fito da wasu ganyayyaki na musamman guda huɗu.
Dukkaninsu jajaye ne, inda yana fitowa dasu kaf ilahirin
wajen yai tsit.
Kasancewar kowa yasan waɗannan ganyayyaki bana
komai bane illa na fitarda tsakani na wasannin gaba, wato
dai dawa-dawa za'a kara.
Kowa abinda ke ransa shi ne, wanne faɗa ne zaifi
ƙayatarwa. Shin tsakanin Armad da Ikenga ne ko kuma
tsakanin Bizaya da Han-Amuru wanda mutane da dama a
wajen suke bayansa.
Domin wani abin mamaki shi ne, idan ka cire Bizaya, zaka
ga babu kusan wanda waɗannan ƴan kallo ke goyar baya
kamarsa, duk da kuwa masu goyon bayan Armad sun
ɗan ƙaru bayanda yaci nasara akan Niyashi.
Alƙali Gali ya ɗauko alƙalami, wanda a jikinsa aka rubuta
Deniziyya Kuronikil, ya miƙa hannu yabi kan dukkanin
waɗannan ganyayyaki huɗu ya rubuta sunan ɗaya daga
cikin mutun huɗun nan da suka fito.
Sannan yana gamawa ya haɗesu waje ɗaya, kuma a
gaban idon filin nan wanda tuni yayi tsit an zuba ido,
alƙali Gali ya jefa waɗannan ganyayyaki huɗu sama.
Nan take suka luluƙa sama kimanin taku huɗu, sannan
suka fara sakkowa.
Idon kowa akai, kawai so ake aga waɗanne guda biyu ne

zasu fara dira ƙasa, wanda hakan shi zai nuna waɗanne
ne zasu haɗu da juna.
Wato dai a taƙaice, ganye biyun da suka riga zuwa ƙas,
sunan dake kai, sune zasu kara da juna, kuma su zasu
fara.
Sannan kuma ragowar biyu da suka rage a sama su biyo
baya.
Wannan ita ce hanyarda suke bi a wannan gasa wajen
zaɓar waɗanda zasu kara da juna.
Kuma hanyace da kowa yake ganin tayi, saboda
waɗannan ganyayyaki an tsinko sune daga bishiya ta
musamman wanda kowa ya santa.
Bishiya ce wadda babban abinda kowa ya sani akanta shi
ne, tun daga sanda ta fara ganye har ƙarshen rayuwarta,
a kodayaushe ganyayyakin ta iri ɗaya ne sak. Sunan
wannan bishiya Safá, su kuma ganyayyakinta ana kiransu
da Safáha.
Har zuwa sanda waɗannan ganyayyaki huɗu suka zo
kusan tsakiya a tare suke tafiya, amma a wannan lokaci
ne iska ta kaɗa, inda biyu daga cikin ganyen suka wuce
sauran.
Kuma kan kace meye wannan tuni sun kusa isa ƙasa.
Suna dira suna ɗaya ya bayyana kuma sunan Han-Amuru
ne a jiki.
Ɗayan kuma a juye yake.
To dama a dai-dai lokacin da Gali zai jefa waɗannan
ganyayyaki waɗansu mutane sanye da fararen kaya su
biyu, sun matso gefe sun tsaya.
Dukkansu fuskokinsu a rufe suke, kuma su na tsaye cak
kamar baza su taɓa motsawa ba.
Amma a dai-dai lokacin da waɗannan ganyayyaki biyu
suka dira a ƙas, waɗannan mutun biyu suka ɓace daga
inda suke tsaye suka kuma bayyana a a dai-dai kan
waɗannan ganyayyaki inda suka ɗauke su cikin sauri, tun
kafin ragowar biyun su sauka.
A gaban idon kowa kuma suka buɗe ɗayan, inda kowa
yayi arba da sunan Armad Djinn akai.
Nan take wajen ya ruɗe da shewa, kowa yana tattauna
yadda rabon ya kasance, da dama dai yai musu, amma
kaɗan daga ciki ba haka suka so ba.
Armad na tsaye a kusa da Nusi tana ja masa kunne akan
ya kula sosai da HanAmuru, kuma kada ganin cewa daga
kan doron ƙasa ɗaya suke yasa yayi wasa, kawai sai yaji
alamun ana kallonsa ta baya, inda na take ya juya
ɓangaren.
Yana juyawa yai arba da idanun Han'Amuru, wanda
kallonsu kaɗai zai iya sawa kaji tamkar an jefa ka acikin
wuta, saboda wutar da take ci aciki. In ba'a manta ba
aljanin Han Amuru na wuta ne.
Kana gani kasan kallo ne mai cike da so da marmarin
yaƙi, haɗe kuma da turawa Armad saƙon cewa a shirye
yake.

Shima Armad baiyi ƙasa a gwiwa ba, wajen mayar masa
da irin wannan kallon dake gaya masa shima a shiryen
yake.
____
To fa, Wuta da Walƙiya sun haɗu, wa kuke tunanin zaici
nasara?
Nidinne dai Shuraih Usman inkiya
99%
Daga taskar magajin wilbafos
MAGAJIN WILBAFOS
Marubuci: Dr Abdullahi Muhammad Ibrahim
Babi na 38: Badalar Wuta
Post by: Shuraih Usman
@shuraih 99%
www.facebook.com/hausaebooks
.
Daga:- Taskar Magajin Wilbafos
.
"Zo kaji!" Nusi ta ja Armad da sauri suka bar cikin
mutane izuwa wani ɗan shinge dake wajen filin-wasan.
"Wannan yaron mai suna Han Amuru na sanshi a
shekarun baya da suka wuce a lokacin da mukai ƙoƙarin
shiga garin ƙarƙashin ƙasa na Shadniza dana labarta
maka a baya. Lallai yana da hatsarin-gaske sama dana
gobarar daji, dole ka kiyaye."
"Ehmmm......" Armad ya kyaɗa kai tare da ajiyar zuciya.
"Kada ki damu kanki sosai, ni nasan zanyi nasara domin
sama da ƙasa zata haɗu bazan mutu ba saina tabbatar
mahaifiyata ta samu lafiya. Akwai fasahar Wasu-wasi da
nake da ita wanda har yanzu banyi amfani da ita ba.
Akwai ɗalasimin Kaban'shisu shima." Armad yana
magana cikin taushi musamman ganin yanayin tausayi da
so acikin idanun Nusi.
"Da gaske fa...... Ki dena damuwa da yawa." Armad ya
matsa kusa da Nusi tare da ƙara jaddada mata abinda ke
zuciyarsa bayanda yaga alamun rashin amincewa a
idonta.
Nusi ta girgiza kai, "Ban san mai yasa ba amma jikina
yana bani kamar akwai wani hatsari dake tafe. Lallai
hankali na bazai kwanta ba sai naga mun bar wajen nan
lafiya."
Nusi ta matsa kusa da Armad domin kare shi daga wasu
mutane dake wucewa wanda suka fara nuna Armad suna
cewa, "shi ne Armad Djinn, shi ne yai nasara ɗazu akan
yarima Niyashi."
Nusi ta ƙara jan Armad suka bi bayan wasu shaguna dake
kewaye da filin domin ɓuya daga idanun jama'a.
"Ungo wannan Layar." Nusi ta fito da wata Farar-Laya
ɗaure da wani zare mai launin roɗi-roɗi daga cikin rigarta
ta kuma miƙawa Armad. "Nasan kasan amfanin ta."
Idanun Armad suka cika da mamaki, shin wai abinda

yake gani dai-dai ne ko kuma mafarki yake. Domin kuwa
idan dai Layar da yake tunani ce to lallai ya tsinci dami a
kala. "N......nusi... Ya akai kika samu Farar-Laya....."
"Sh...sh.... ka daina faɗa da ƙarfi mana kosai kasa wasu
sunji." Nusi tayi sauri ta rufe masa baki. Sannan taci gaba
da bayani bayan ya karɓi Layar. Ga dukkan alamu
wannan Laya aba ce ta musamman. To ko meye
amfaninta.
"Zaka iya amfani da wannan Farar-Laya amma ka sani ba
mai ƙarfi bace, saboda haka sau ɗaya kacal za'a iya
amfani da ita. Ungo wannan safar kasa a hannunka,
domin kaima baza ka iya taɓa ta ba." Ta ƙara miƙa masa
wata ƴar safa ruwan ƙasa. Har a wannan lokaci daya
miƙa hannu ya karɓi safar idanunsa cike suke da
mamaki. Domin yana da cikakkiyar masaniyar cewa ba
ƙaramin abu mai wahala bane ga mutun ya mallaki
wannan Farar-laya ba koda kuwa mara ƙarfi. Nan danan
ya ƙara sanin cewa lallai akwai manyan ma'abota da suka
tsayawa Nusi. Musamman daya tuno labarin data gaya
masa na cewa suna da ƙungiya mai ƙarfin gaske da suke
ƙoƙarin buɗe garin ƙarƙashin ƙasa na Shadeniza.
A dai-dai lokacin da yazo nan a tunaninsa ne suka jiyo
ƙarar ƙararrawa alamun lokaci yayi daza aci gaba da
fafatawa. Nan da nan suka rankayo izuwa cikin filin.
Lokaci kaɗan bayan kaɗawar ƙararrawar aka buga ƙugen
yaƙi, inda Armad da Han'amuru suka fito filin daga, babu
abinda kake ji sai shewar ƴan kallo wasu suna goyon
bayan Armad wasu Hanamuru, amma kana gani zaka san
na Hanamuru sunfi yawa.
Gabda zai hau kan filin dagar Armad ya ƙara shafa
aljihunsa domin jin halin da Littafin-takobi yake ciki. Shi
kansa baisan dalilin da yasa bai gayawa Nusi labarin
wannan littafi ba duk da kuwa yasan ya kamata ya gaya
mata.
Sai dai abu guda ɗaya da yake ta sukar Armad a rai shi ne,
baisan dalilin da yasa Littafin-takobin ya taimake shi a
yayin faɗansa da Yarima Niyashi ba. Saboda haka bashi
da tabbas zai ƙara samun irin wannan taimako daga
wannan littafi, kuma lallai bai kamata ya ta'allaƙa dashi
ba. Saboda haka ma baya son ya gaya mata hankalinta ya
ƙara tashi. Kuma tunda ma'aboci aljanin wuta Han
Amuru ya fishi girman Izza lallai yana da buƙata ya fito da
wata hanya da zai samu nasara cikin gaggawa.
Saboda haka ya fara tunanin mafita, 'Ina da Saran takobi
mai suna Wasu-wasi, sannan kuma ina da adadin
ƙawanyar walƙiya guda hamsin da ɗaya. Mafi
muhimmanci kuma ga Farar-laya dana samu daga Nusi.'
Armad ya ci gaba da tunane-tunanen hanyar dazai samu
nasara ba tare da neman taimako daga littafin ba. Saboda
shima yana ji a jikinsa cewa akwai wani sharri maɗaukaki
a tattare da wannan Littafi.
Suna dira acikin filin, Han Amuru ya ƙara ja da baya, ya

kuma ƙara nisan dake tsakaninsa da Armad inda cikin
sauri ya tafa hannayensa biyu gami da cewa, "Badalar
wuta!!"
Yana faɗar haka, wata wuta ta bayyana a gefensa. Wadda
tana bayyana ta fara ƙara yawa tana zagaye shi, kan kace
meye wannan tuni wannan Badalar wuta ta rufe Han
Amuru har zuwa kafaɗaunsa, inda ta tsaya.
Amma kuma tana tsayawa sai wata irinta ta fara kewaye
ta inda ita ma tayi ta ringa ƙaruwa har takai tsayin kamar
wancan.
Tana gamawa wata ta fara... haka-haka har saida aka
samu ƙawanyar wuta zagaye shida a kewaye da Han
Amuru. Wannan badaloli su na gunji suna fitar da baƙin
hayaƙi da tiriri suna kare Han Amuru tamkar sarki acikin
bangon Badalar garinsa. Lallai ko kakai ƙanƙantar kiyashi
baka isa ka cimma Han Amuru ba a yadda yake.
Han Amuru ya miƙa hannunsa gaba, inda ya nuna
Armad, wanda ke tsaye har a lokacin bai motsa ba.
Yana nuna Armad, cikin ƙiftawar ido da bismilla, biyar
daga cikin waɗannan ƙawanyar badala ta wuta, suka ɓace
daga inda suke, suna ƙara bayyana sui gasu zagaye da
Armad.
Haka na faruwa Hanamuru ya kyalla ido ya hango Armad
a tsakiyar wutannan, kowa na gani yai wata wawar dariya
gami da cewa, "Armad....Djinn ko? Naga faɗanka da
Niyashi kuma ina mai tabbatar maka da cewa lallai sai
nayi nasara akanka. Ni zan ƙone ka ƙurmus acikin Badala
ta ta wuta! Kai sani cewa ni idan ina filin daga babu
ruwana da yaro ko babba, duk hukunci ɗaya nake musu.
Saboda haka kada ma kayi tunanin cewa dan kana da Izza
ƴar ƙarama wadda bata fi rabin tawa ba zan ɗaga maka
ƙafa."
Gunji da tiriri da wannan wutar ke bayarwa tuni ya fara
ƙoƙarin haɗiye Armad. Armad ya ɗaga ido yaga shekarun
Izza ɗai-ɗai har goma sha bakwai ajikin kowacce ɗaya
daga cikin wannan badalar wuta guda biyar dake neman
haɗiye shi. Lallai yasan indai ya bari ɗaya daga cikinsu ta
taɓa shi to fa lallai ƙarshensa yazo.
Nan take ya zira wannan safa da Nusi ta bashi sannan ya
tuno da ɗaya daga cikin ɗalasiman daya koya a wajen
kakansa wato 'Kaban'shisu'. Ba shiri Armad yayi amfani
da ƙarfin Izza na kimanin shekara goma ya tayarda
wannan ɗalasimi. Lamarinda ya bashi damar kuɓucewa
wannan badalar wuta abar ruruwa. Inda ta daki wajen da
Armad ya bari kuma nan take ta maida shi toka. Armad
ya bayyana acan gefe yana mai duba izuwa wannan waje
daya bari tare da tuno cewa da bai bar wajen ba, toda
tuni ya zama toka shima.
Sai dai yana cikin tunani ne wata badalar ta ƙara yiwowa
kansa da niyar haɗiye. Amma ina, Armad ya ƙara
kuɓucewa. Lamarinda ya bawa Han Amuru haushi yai
wani ƙaraji tare da saka badalolin wutar guda shida su

haɗe izuwa babbar badala guda ɗaya. Wadda nan take ita
kuma ta kewaye dukkan filin dagar inda tasa Armad da
shi Niyashi a tsakiya. Sannan kuma ta fara matsewa tana
haɗewa izuwa tsakiya. Wato dai a taƙaice Armad bashi da
wajen guduwa indai ba tashi sama zaiyi ba. Wataƙila da
yana da Miyurarsa, da zai iya tashi saman kamar yadda
yayi a faɗansa damai tsaron hanya Han Diyuza, amma
yanzu babu. Gashi a tsakiyar wutar badala tare da
ma'aboci aljanin wuta wanda babu alamun imani a
tattare dashi ko kaɗan.
____
To ko taya Armad zai kuɓuta daga wannan badalar wuta?
Nidinne dai Shuraih Usman inkiya
99%
Daga taskar magajin wilbafos
MAGAJIN WILBAFOS
Marubuci: Dr Abdullahi Muhammad Ibrahim
Babi na 39: Farar Laya
Post by: Shuraih Usman
@shuraih 99%
www.facebook.com/hausaebooks
.
Daga:- Taskar Magajin Wilbafos
.
Duk taƙi ɗaya da wannan wuta ta ƙara kusantar Armad
sai yaji raɗaɗinta ya ƙaru. Tamkar ana soya naman
jikinsa. Lallai bada ban jarumin gaske bane da tuni ya
kwalla ƙara.
Amma duk da wannan hali daya ke ciki wani abu ɗaya ya
ɗauke masa hankali. Wannan abu kuwa shi ne
kasancewar wancan badala ta wuta data nemi halaka shi,
ya sha dakyar ta hanyar ɓacewa daga inda yake, ya
kamata ace shekarun Izzar dake jikinta sun ragu daga sha
bakwai zuwa ƙasa. Amma bisa mamaki tana nan dai-dai a
yadda take; ɗauke da shekaru goma sha bakwai na Izza.
Lallai Armad yasan akwai matsala idan abubuwa suka ci
gaba da tafiya a haka. Domin kuwa idan Izzar mutun bata
raguwa idan yayi amfani da ita, to tayaya Armad zai iya
cin galaba akansa.
Hayaƙi da turiri ya fara neman sawa hankalin Armad ya
gushe, amma Armad yasan cewa lallai indai ya bari ya
suma a wajen to ƙarshensa yazo. Saboda haka ya cije ya
daure ya tsaya da ƙafafunsa, ya kuma fuskanci inda
Amuru yake tsaya yana kallonsa cikin isa da ƙasaita.
A dai-dai wannan lokaci ne Armad ya yanke shawarar mai
zaiyi. Nan take ya zira hannunsa mai safar cikin aljihunsa.
Inda ya janyo wannan Farar-laya da Nusi ta bashi.
Sannan kuma a lokaci guda yayi duba izuwa ruhinsa, inda
ya janyo ƙawanyar walƙiya na ƙarfin Izzarsa daya rage na
shekaru arba'in.

Daga nesa idan ka hango Armad abin zai baka mamaki;
zaka ga yaro saurayi wankan-tarwaɗa sanye cikin fararen
kaya. A kewaye dashi akwai ƙawanya ta walƙiya ɗai-ɗai
ɗai-ɗai har guda arba'in da ɗoriya su na kewaya shi. Lallai
da dama daga cikin ƴan kallon baza su taɓa mantawa da
wannan yaro mai suna Armad.
Cikin sauri ya tunkari Han Amuru yana sassarfa. Sai dai
kuma wannan badala dake ta kusanto su tamkar ta gane
mai Armad yake niyyar yi, saboda haka tayi kansa cikin
tsananin sauri. Lamarinda yasa ta cimmasa cikin ƙiftawar
ido da bismilla.
Tana zuwa ta daki wannan ƙawanyar walƙiya data kewaye
Armad. Inda wata ƙara mai ruɗarwa ta tashi. Nan take
faɗa ya kaure tsakanin wannan badalar wuta da kuma
ƙawanyar walƙiyar Armad. Wuta tana ƙoƙarin haɗiye
walƙiya, walƙiya kuma tana ƙoƙarin ƙona wuta. Lallai
wannan faɗa ne na musamman, wanda dukkanin ƴan
kallo hankalin ya koma kai. Sai dai kuma abinda basu sani
ba shi ne a bayan wannan walƙiya Armad ne keta aman
jini yana tafiya da kyar, saboda duk sanda wannan wuta
ta daki walƙiyarsa sai yaji rauni a jikinsa. Badan komai ba
saboda banbancin Izzar dake tsakaninsu. Lallai akwai
banbanci maɗaukaki tsakanin mai Izza ɗari da mai
hamsin. Wanda idan banda ƙarfin ruhi da dagiya irin ta
Armad da tuni yaje ƙas.
Armad ya ci gaba da tafiya yana aman jini, burinsa kawai
ya isa ga Amuru. Koda yaje dab dashi sai Amuru yayi
masa wani kallo mai cike da mamaki tare da cewa, "kana
ta sauri ka iso gareni, shin kana tunanin dan kazo nan
zaka iya yin wani abu ne? Bari dai na nuna maka
banbancin ƙarfin Izzar dake tsakanin mu."
Nan take Amuru ya dunƙule hannunsa, lamarinda yasa
nan take dukkan wutar dake wajen ta cure izuwa
tafkeken dunƙule guda ɗaya kewaye a hannunsa.
Kafin Armad ya farga tuni Han Amuru ya kawo masa
duka da wannan hannu nasa mai haɗe da wuta.
Ko kokwanto babu Armad yasan indai ya bari wannan
hannu ya taɓa shi, tofa lalle ko tokarsa baza a gani ba.
Saboda haka nan take ya haɗe dukkan sauran ragowar
shekarun Izzarsa izuwa wata ƴar ƙawanya ta walƙiya.
Wadda yasa ta kewaye wannan Farar-laya dake
hannunsa, sannan ya cillawa Amuru ita.
Saboda yadda layar take kewaye da walƙiya, Amuru baiga
layar ba, saboda haka yai tsaki tare da cewa, "shin kana
tunani ƴar wannan walƙiyar daka cillo zata iyai min wani
abu ne? Ka farka in ma mafarki kake, domin kuwa......"
Han Amuru ya haɗiye ragowar kalominsa tare da rufe
bakinsa yayinda wannan Laya ta taɓa jikinsa. Sannan
kuma kafin ya ankara zaren dake jikinta ya rataye a
wuyansa.
Cikin abinda bai wuce ƙiftawar ido ba dukkan wutar dake
kewaye da Amuru ta ɗauke tamkar ba'a taɓa yinta ba.

Wani zafi mai haɗe da kasala ya cika jikinsa, inda hatta
ƙafarsa yaji baza ta iya ɗaukansa ba. Ya nufi ƙasa gadangadan tamkar wanda aka zarewa rai.
A dai-dai wannan lokaci da kowa ke mamakin abinda ke
faruwa aka jiyo muryar alƙalin wasa wato Ghalee,
"F.....farar-laya! Lallai babu kokwanto acikin abinda ke
faruwa. Wannan yaro mai suna Armad Djinn yayi amfani
da Farar-laya ya ɗaure aljanin Han Amuru. Kowa yasan
ƙarfin wannan Laya da akewa laƙabi da Farar-laya wajen
ɗaure dukkan wani aljani da kuma hana ma'abota su
amfani da

Please Login or Register in order to submit comment