Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Nusi ta kammala zancenta tare da

miƙa hannu taja jan kyallen dake goshin Armad cikin
tsokana, tana cewa, "wai kai tunda ba Miyurar ka cire
wannan abun mana."
"Hmmmm.." Armad yaja numfashi yana tunano mai
zaice ya tsokani Nusi shima, "indai zaki iya cire
ɗankwalinki to nima zan cire. Kin yarda?"
"Me kace?" Nusi ta cije haƙora, kasancewar a ƙabilar su
Nusi kowacce mace data haura shekaru sha takwas tana
saka ɗan mayafi taɗan rufe gashinta. Kuma sukan ɗauki
abun abun tsokana idan bakya yawo da wannan mayafi
da ake kira da ɗankwali.
"Zaka iya ƙara wani kyallen ma.... Ni ina ruwana..." Nusi
ta haɗe rai tana hararar Armad. Lallai acikin wannan
harara akwai abota wadda take ginuwa a hankali a
hankali. Ko ina wannan abota zata kaimu, lokaci ne kaɗai
zai gaya mana.
Awa shida nayi aka buga ƙugen yaƙi..... Mazaje guda biyu
da suka fito zagayen ƙarshe na wannan fafatawar suka
bayyana a fagen daga.
Sune waɗanda sukai nasara akan sama da mutun ɗari
bakwai da suka fafata a wannan gasa. Kuma yanzu gashi
sun haɗu da juna, lallai akwai karan-batta irin wanda ba'a
ga irinta ba a baya.
Waye zaiyi nasara? Waye zai je ƙas? Waye zai nunawa
duniya ya isa? Waye zai mallaki dubunnan bayin da aka
tara?
____
Armad na tsaye a gefe guda da takobinsa a rataye a
kafaɗarsa, yana karantar Ikenga wanda ke gabansa a
tsaye, idanunsa a rufe.
Kuma abin mamakin shi ne anfi minti uku da kaɗa musu
ƙugen yaƙi, amma babu wanda ya motsa acikinsu.
Can daga bisani Ikenga ya buɗe ido ya kalli Armad, inda
dubansa ya kafe akan jan kyallen dake ɗaure a goshin
Armad, nan take kaifafan idanununsa, wanda ga dukkan
alamu zasu iya gani har hanji, suka ƙurawa wajen ido
cikin mamaki, kafin daga bisani ya buɗe baki ya fara
magana cikin tsananin girman kai da taƙama da ƙarfin
Izza, "a wannan rayuwar na tsani mutane da dama!
"Amma daga cikin waɗanda nafi tsana akwai matsorata
masu jin tsoron bayyana kosu su waye!!
"Da farko nayi niyyar mutunta jarumtarka ta zuwa
zagayen ƙarshe, na nuna maka fasaha ta mai suna
'Takun-Sarki', wanda hakan nema yasa tunda nayi takun
farko ban matsa daga nan ba, da niyyar zan ɗauki taku na
biyu na halaka ka dashi. Domin kaga idan ka mutu ta
wannan hanyar zakai alfahari a lahira, saboda kana daga
cikin kaɗan da suka mutu daga maɗaukakiyar fasahar
'Takun-sarki'.
"Amma ina, ka ɓata min lokaci kawai! Lallai duk wanda ke
tsoron bayyana cewa shi Magajin-wilbafos ne to bai
cancanci Takun-sarki ba. Ko kana tunani dan babu

Miyura a goshinka idanu na zasu kasa gane ka. Lallai inaga
baka da masaniyar cewa wannan idanu nawa su na ganin
hatta safa-da-marwar mutuwa a lokacin da take ɗaukar
rayukan bil-adama."
Yana gama faɗar haka bai jira komai ba, ya nufi kan
Armad da takobinsa a hannun dama tsirara. Jikinsa na
sassarfa irin ta mazajen aljanu.
Yana isa ga Armad ya kai masa wawan sara da niyyar
tsinke kansa, amma a wannan lokaci Armad ya farfaɗo
daga cikin mamakin da yake na yadda akai Ikengan ya
gano shi ne Magajin Wilbafos, ya kuma kare wannan sara
da tasa takobin.
Takubban biyu na haɗuwa Ikenga yayi amfani da
tsananin kwarewa ta fasahar takobi ya zame takobinsa
daga jikin ta Armad, ya kuma kai masa wani saran da ita
ta ƙasan hannunsa.
Cikin tsananin zafin nama Armad yayi amfani da walƙiya
mai ɗauke da ƙarfin shekara ɗaya ya ƙarawa kansa ƙarfi
domin zamewa wannan sara. Yai tsalle izuwa gefe guda
tare da mayarwa da Ikenga martanin sara mai ɗauke da
shekarun Izza biyar. Lamarinda yasa dole Ikenga yayi
amfani da Izzarsa sannan ya iya kaucewa ta hanyar yin
tsalle ya koma baya.
Armad ya bishi da kallo riƙe da takobinsa, inda shima ya
kalleshi yana mai yamutse fuska.
Lallai ɗan wannan bata kashi na ƴan daƙiƙu daya wakana
tsakanin wannan ma'abota Izza biyu ya girgiza ƴan kallo
domin kuwa babu abinda kake ji sai shewa da ife-ife.
"Hmmmm...." Armad yaja numfashi cikin yarda dakai
yana mai cewa, "shin kana ganin dan ka fita daga cikin
Mairakana da Bizaya ya saka ka aciki shi ne ka isa. To ya
kamata ka canja tunani, domin lallai sai nayi nasara a
wannan fafatawa. Kuma wani abu guda ɗaya da baka sani
ba, koda kasan ni ne Magajin Wilbafos ko baka sani ba, ko
kana ganin mutuwa ko baka gani duk bai shafe ni ba.
Domin lallai koda zan mutu saina fito daga kabari na
nemo Tarifil-fakta nan da wata shida. Kai koda
dukkaninku zaku haɗu na farkon ku dana ƙarshenku,
baza ku iya hana ni nemar mata lafiya ba."
"Hmm.." Ikenga yayi murmushi tare da tafa hannayensa
biyu ya kuma kira sunan ɗalasimi acikin ransa, sannan ya
ci gaba da cewa, "Da takobi kaɗai, ba tare da aljani ba, ba
kuma tare da fasahar Takun-sarki ba zan halaka ka. A
matsayinka na zuri'ar Wilbafos koba komai ka cancanci
na nunawa duniya ƙarfin Izza ta akanka. Kayi sani cewa a
irin wannan rana ta yau Wilbafos-na-uku ya rasu. Kuma
kaima yau ita ce ranar da zaka isa magabatanka a lahira."
Armad ya haɗe gira cikin mamaki domin bai taɓa jin
wani Wilbafos-na-uku ba. Kuma ga dukkan alamu Ikenga
ba ƙarya yake ba, sai dai kuma yasan koya tambaye shi
bazai gaya masa wani abu ba. Saboda haka kawai ya
share zancen, kawai abinda ke ransa shi ne ya zaici nasara

akan Ikenga.
"Bari muga har tsahon daƙiƙa nawa zaka iya zama akan
zancenka naƙin yin amfani da aljaninka." Armad na faɗar
haka ya zuƙo shekaru biyar na Izza a matsayin ƙawanyar
walƙiya biyar, ya kuma aikawa da Ikenga su.
Ikenga ya kaɗa takobinsa a sama, sannan yayi tsalle tare
da kaiwa ɗaya daga cikin wannan walƙiya sara. Nan take
takobin tasa ta ratsa cikin walƙiyar, kafin daga bisani ta
tarwatsa ta ta ɓace acikin iska.
Lamarinda ya jawo shewa mai ƙarfin gaske acikin ƴan
kallo. Kowa yasan cewa ba ƙaramin ƙarfin fasahar takobi
ake buƙata ba kafin mutun ya iya tarwatsa harin aljani da
takobinsa, amma ga Ikenga akan iska ya tarwatsa ɗaya
cikin kwanciyar hankali.
Tun ma kafin shewar ƴan kallo ta mutu Ikenga ya ƙara
ratsa walƙiya ta gaba, sannan ta gabanta. A haka a haka
har saida ya gama da guda biyar ɗinnan hankalinsa a
kwance. Sannan ya dira ƙasa yana kallon Armad.
Nan Armad take Armad ya duba yaga yana da kimanin
ragowar shekarun Izza arba'in, sabida haka nan take
yasan maiya kamata yayi.
Armad ya zuƙo shekaru goma nan take, sannna ya haɗa
ƙatotuwar ƙawanyar walƙiya da ita. Ya ɗora ta a saman
hannunsa na dama sannan yai ƙaraji ya afkawa Ikenga.
Yana zuwa yakai masa duka da ita, inda shi kuma yasa
takobinsa ya kare. Sai dai kuma shima Ikenga yasan babu
yadda za'ai ya iya kare shekaru goma na Izza a haɗe, da
takobi kawai. Koda kuwa ya iya karewa, zata iya fancala ta
gefe ta ƙona shi.
Saboda haka nan take ya ɗaga hannunsa sama ya kira
ɗalasimi, inda wata takobin ta ƙara bayyana akan ɗayan
hannunsa. Nan take ya kawo wa Armad sara da ita.
Dama Armad yayi tunanin haka zata iya faruwa, saboda
haka ya shirya mata. Takobin na fitowa wata ƙawanyar
wuta mai ɗauke da shekaru sha biyar na Izza ta bayyana
ta tare ta. Sannan kuma a lokaci guda wata ƙawanyar mai
ɗauke da wasu shekaru sha biyar ɗin ta ƙara bayyana ta
yiyo kan Ikenga ta baya.
Da farko Ikenga ya kasa riƙe ƙawanya mai ɗauke da
shekaru goma, a dalilin hakan ya kira wata takobin,
amma kuma Armad ya shiryawa hakan, inda shima ya
ƙara aika masa wata ƙawanyar mai shekaru sha biyar har
guda biyu; ɗaya ta gaba ɗaya ta baya. Lallai Armad ya
kware a harkar sarrafa aljaninsa yadda yake so. Kuma ga
dukkan alamu kullun ƙara kwarewa yake.
___
Shin taya Ikenga zai iya kaucewa halaka daga girman Izzar
dake tunkararsa ta gaba ta baya?
Nidinne dai Shuraih Usman inkiya
99%
Daga taskar magajin wilbafos

MAGAJIN WILBAFOS
Marubuci: Dr Abdullahi Muhammad Ibrahim
Babi na 44: Aljani Gal-Iyyu
Post by: Shuraih Usman
@shuraih 99%
www.facebook.com/hausaebooks
.
Daga:- Taskar Magajin Wilbafos
"Hmmm...." Ikenga ya ja dogon numfashi tare da girgiza
kai, "eh lallai ka cancanci kaga aljani na, na janye abinda
na faɗa a baya. Amma kayi sani cewa duk abinda ya faru
dakai, kada ka zargi kowa ka zargi kanka."
Yana rufe baki ya tafa hannayensa biyu tare da faɗar
wasu ɗalasimai ƙasa-ƙasa, kana daga bisani ya kira sunan
aljaninsa, "Gal-iyyu!"
Faɗar hakan keda wuya wannan filin wasa ya fara girgiza
yana neman rugurgujewa. Waɗannan manya-manyan
ƙawanyu na walƙiya ɗauke da shekarun Izza dake
tunkaro shi suka fara girgiza kafin daga bisani su tsaya
cak tamkar ansa wani bango an tare su.
Sai dai idan ka lura zaka ga cewa bawai haka kurum
waɗannan ƙawanyu suka tsaya ba. Wani baƙin abu ne
mai kama da hadari yayi musu hijabi tsakaninsu da
Ikenga. A zagaye da wannan baƙin abu akwai wani jan
layi daya kewaye dukkaninsa. A tsaye wannan baƙin abun
da kaɗan ya haura Ikenga, amma a kwance yana da faɗin
daya kewaye shi ya kuma kare shi daga sharrin wannan
walƙiya dake neman halaka shi. Wata irin Izza mai saka
firgici na tashi daga jikin wannan abu. Kallo ɗaya kacal
zakai ka tabbatar da cewa akwai ƙarfin maɗaukakin aljani
a jikin wannan abu mai kama da hadari. Kai idan ma ka
nutsu ka ƙara matsawa kusa zaka iya jin ƙarfin Izzar
baƙin Rauhanin aljani na tashi daga ciki.
Babu abinda kake ji sai ajiyar zuciya da ƙara kwale ido
daga ƴan kallo, domin ga dukkan alamu har yanzu babu
wanda ya gano haƙiƙanin me wannan aljani na Ikenga
mai Gal-iyyu yake sarrafawa.
Wasu ƴan kallo daga ɓangaren kusurwar arewa suka fara
bada hasashe kan mai suke tunani akan wannan aljani.
Ɗaya daga cikinsu ya ce, "ina ganin aljanin duhu ne, ko?"
Ɗayan kuma ya girgiza kai, "a'a, ni ina ganin aljanin
hadari ne."
"A'a anya kuwa, ka taɓa ganin hadari da yakai baƙin
wannan? Lallai ni inaga ba hadari bane.. Ko kuma
wataƙila ma aljanin ƙasa ne ko kuma na......" Sai dai kafin
ya rufe bakinsa ya haɗiye ragowar maganarsa domin
abinda ya gani na faruwa a wannan filin daga.
"Kaiiiiii.... Ai kuwa aljanin hadari!!!" Yai ajiyar zuciya tare
da kallon abokin hasashen nasa. "Duba kaga yadda yake
zuƙe walƙiyar dake kewaye da dashi. Aljanin hadari shi
kaɗai ke iya zuƙe walƙiya a iya sani na."
Ai kuwa abinda ke faruwa kenan. A kewaye da Ikenga

wannan abu ya fara rage shekarun dake ɗauke acikin
wannan ƙawanyu na walƙiya. A gaban idon kowa na suka
fara rage yawa tamkar wasa.
Nan take Armad yai tsalle izuwa baya tare da haɗe fuska,
acikin ransa yasan lallai akwai matsala. Domin shima
kamar sauran ƴan kallon ya gano cewa wannan aljani na
hadari ne. Domin yana da cikakkiyar masaniyar shi kaɗai
ne zai iya zuƙe walƙiyar sa haka.
Ikenga ya ɗaga hannunsa na dama yana nuni da Armad,
"Kayi sani cewa tun daga lokacin da aka hallicemu aka
rubuta nayi nasara akan ka. Kai koda ma ba haka aka
rubuta ba, lallai yanzu al'amari zai canja. Koba komai
zaka yi alfahari idan kaje lahira kana daga cikin waɗanda
suka mutu ta hannuna. Domin lallai abin alfahari ne a
gareka, ace ka mutu a hannun sarkin ƙabilar Bayajidda."
Armad ya ja numfashi gami da murmushi, "kayi dai ka
gama surutun ka. Ni dai nasan lallai bazan bari naje ƙas
ba a wannan fafatawa. Ko da aljani ko babu!"
Ikenga najin wannan magana ya ƙara tafa hannayensa,
lamarinda yasa wannan baƙin hadari ya ƙarasa zuƙe
dukkanin walƙiyar dake kewaye dashi. Sannan nan take
ya aikawa da Armad wannan hadari da niyyar ya halaka
shi dashi.
Armad yai tsalle ya kaucewa hadarin ta hanyar yin gefe.
Amma tunma kafin yaje ƙas wannan dunƙulen hadari
yayiwo kwana ya ƙara tunkaro shi da ƙarfin tsiya. Saboda
ƙarfin gudunsa har wata iska ce ke tashi tana bada gunji
tamkar ana ƙuga ruwan sama.
Armad yai sauri ya baje a ƙas inda wannan hadari ya
wuce ta saman kansa da kaɗan. Lallai bada ban yayi
dabarar yin sauri ya kwanta ba da tuni wannan hadari ya
dunƙule shi. Duk da cewa hadari ne kawai amma
tsananin ruɗani da ƙarfin Izza dake tashi daga jikinsa
yana da matuƙar tsoratarwa, lamarinda yasa Armad ya
san lallai bai kamata ya bari wannan hadari ya riske shi
ba. Haka dai suka ci gaba da kai komo; Armad yana ta
zillewa hadari, shi kuma Ikenga yana ƙarawa wannan
hadari ƙarfi da gudu. Amma duk da haka Ikenga bai
samu damar riskar Armad.
Armad na tsalle yana lissafi acikin ransa, "saura daƙika
ashirin da ɗaya."
Dama dai duk guje-gujen da Armad yake so yake
aljaninsa ya tara masa wata walƙiyar. Kuma yasan dai-dai
lokacin da zai ɗauka kafin hakan ta faru, saboda haka ya
yanke shawarar yaci gaba da guje-guje zuwa sanda zai iya
sarrafa wata walƙiyar.
Amma a ɓangaren Ikenga kuwa, koda ganin babu yadda
zaiyi ya iya kama Armad da hadarinsa saiya canja taku.
Nan take ya tafa hannayensa ya kuma ƙara kiran wani
ɗalasimin, "Samá'u!"
Yana rufe baki wannan baƙin hadari dake bin Armad ya
tsaya cak. Sannan daga bisani ya fara yin sama. A hankali

a hankali har saida yakai kimanin ƙafa ashirin sannan ya
tsaya. Yana tsayawa kuma ya fara buɗewa yana ƙara
girma. Cikin abinda bai wuce daƙiƙa uku ba wannan
hadari ya gama karaɗe saman wannan filin gasa.
Armad ya buɗe baki yana kallon abin mamaki. Hadari ne
baƙi-ƙirin ya rufe saman wajen baki ɗaya. Babu abinda
kake gani face shi.
To amma idan da shikenan al'amarin toda da sauƙi,
amma a dai-dai wannan lokaci ne wannan hadarin ya
fara rugigi, sannan tsawa ta karaɗe ilahirin wajen.
Nan take aka fara tsuga ruwa kamar da bakin kwarya.
Ikenga ya ɗaga hannunsa yai nuni ga Armad, lamarinda
yasa dukkan wannan ruwa dake saukowa ya tunkari inda
Armad yake da wani gudu irin na walƙiya.
Kafin ma Armad ya motsa tuni wannan ruwa ya zagaye
shi ya jiƙa shi sharkaf.
"Kana da masaniyar cewa daga hadari akan samu ruwa."
Ikenga ya fara magana cikin girman kai, tamkar babu
wani ma'abocin Izza daya kaishi a ban ƙasa.
Sai dai duk wannan abu bai tsorata Armad ba, domin
kuwa a dai-dai wannan lokaci da yake tunanin zaiji wani
canji kamar zafi ko kuma wani abu a yayinda ruwan ya
taɓa shi baiji komai ba. Saboda haka ya ɗaga tafin
hannunsa yana nazarin wannan ruwa daya jiƙa shi. A daidai wannan lokaci ne Armad yaji motsi a saman kansa.
Amma kafin ya ɗaga kai wata ƙatotuwar ƙawanyar
walƙiya mai ɗauke da ƙarfin Izza na shekaru ɗari ta fito
daga cikin wannan hadari ta tunkaro shi. Kafin yayi koda
tunanin kaucewa ta cimmasa. Inda nan take ta daki
ruhinsa ta zagaye jikinsa tana neman tarwatsi shi.
To da yake koda kana da aljanin walƙiya indai wannan
walƙiya ba daga aljaninka ta fito ba saita yi aiki a kanka.
Saboda haka nan take rauni ya cika jikin Armad. Da kyar
ya iya zuƙo ƙawanyar walƙiyar da bata fi ta shekarun Izza
biyu ba ya kare kansa. Abinda shi kaɗai ne yasa jikinsa bai
tarwatse ba.
A dai-dai lokacin ne ya ƙara jin muryar Ikenga, "shin
kasan cewa daga cikin hadari akan samu walƙiya?" Wata
dariyar mugunta ta cika fuskar Ikenga a yayinda ya ƙara
ɗaga hannunsa ya ƙara kiran sunan wani ɗalasimin,
"Sainówi!"
Yana rufe baki dukkan ruwan dake kewaye da Armad ya
juye nan take izuwa farar ƙanƙara. Cikin ƙiftawar ido da
bismillah wannan ƙanƙara ta kewaye Armad ta rufe shi
ɗaki ɗaya.
Kai daga nesa idan ka hango Armad kace wani gunki ne
da aka sarrafa da farar ƙanƙara. Ga baki ɗaya jikinsa ya
ƙanƙare baki ɗaya, kai ko fatar jikinsa ba'a gani.
Ikenga ya gabato inda ƙanƙararren Armad yake a tsaye
yana taku ɗai-ɗai na ƙasaita, "Shin kasan daga cikin
hadari akanyi ruwan ƙanƙara. Lallai ni Ikenga saina mulki
duniya, kuma zan fara ta halaka ka, na kuma nunawa

duniya ƙarfin Izza ta da ƙarfin aljani na Gal-iyyu, aljanin
Hadari!"
A wannan lokaci ne wata iska mai cike da tsoro da firgici
ta tashi daga cikin ƴan kallon. Lallai a wannan da dama
daga cikinsu suka san an fara gasar Jinzidal.
___
Kowa ya gayyato mana friends dinsa wanda suke son
littafin yaƙi zuwa wannan page. Na fuskanci da dama
basu da labarin Magajin Wilbafos.
Nidinne dai Shuraih Usman inkiya
99%
Daga taskar magajin wilbafos
MAGAJIN WILBAFOS
Marubuci: Dr Abdullahi Muhammad Ibrahim
Babi na 45: Dorawa
Post by: Shuraih Usman
@shuraih 99%
www.facebook.com/hausaebooks
.
Daga:- Taskar Magajin Wilbafos
SHEKARA ƊAYA KAFIN ARMAD YA FITO NEMO WA
MAHAIFIYARSA MAGANI.
"Armad daga yau ya kamata kwata-kwata ka daina amfani
da wannan fasahar takobin." Mahaifiyar Armad ce zaune
a kusa dashi take lallashinsa a cikin ɗaki.
Ga dukkan alamu dare ne kuma Armad bai jima da
dawowa daga karɓar horo daga kakansa ba, domin ko
kayan jikinsa bai cire ba.
"Kaga duk amfanin da zakai da takobi zaka iya amfani da
aljaninka na walƙiya kayi. Amma dai amfani da takobi
haka ba tare da kasa walƙiya ba ina ganin a daina. Duk
amfani ɗaya kana ƙara rage kwanakin da zakai a duniya.
Kana kuma ƙara kusantar mutuwarka. Lallai bazan
yafewa kaina ba idan wani abu ya same ka. Saboda haka
ka daina kawai. Walƙiya ta ishe ka duk abinda zakai.
Kuma hatta yayar taka Hidaya data bar maka takobin
nasan da tasan haka zata faru da bata bar maka ba."
"To mama naji. Na daina fa!" Armad ya faɗa cikin jimami
da tuno wahalar da yasha kafin ya koyi wannan fasahar
takobin amma gashi ala dole ya daina amfani da ita.
Shekaru kimanin biyar kafin wannan rana ya gaji wannan
takobi daga yayarsa mai suna Hidaya. Kuma tun daga
wannan rana ya kwallafa ransa akan amfani da ita duk da
cutar da jikinsa da take. Yakan ce takobin ita kaɗaice
abarda tafi tuno masa da yayar tasa.
Ita dai yayar Armad wato Hidaya ita ta sawa wannan
takobi sunan ƊORAWA. Da dama mutane sukan yi tunani
kodan saboda launin yalo na takobin shi yasa tasa mata
sunan, amma ba haka bane. Dalilin ta shi ne ƙaninta
Armad yakan bata sautu ta taho masa da ɗorawa a duk
lokacin da zata tafi wata ƙasar. Armad dai masoyin
ɗorawa ne, kuma tun yana yaro ya kwallafa a ransa cewa

kan ya mutu saiya sha ɗorawar kowacce ƙasa dake
duniya, tun daga kan doron ƙasa ta farko har zuwa ta
bakwai.
___
A dai-dai wannan lokaci Armad ya ji sanyin wannan
ƙanƙara yana neman lalata masa jiki. Saboda tsananin
sanyi yana ji tamkar ana soya fatarsa. Hatta ganinsa ya
fara komawa dishi-dishi, kuma tuni ya daina jin muryar
Ikenga saboda ƙanƙarar data kewaye shi.
Armad yana da cikakkiyar masaniyar cewa da Miyurarsa
tana nan zai iya amfani da fasaharsa ta Wasu-wasi ya
tarwatsa wannan ƙanƙara ya kuma saukarwa da Ikenga
sara kafin ya farga. To amma yanzu babu. Kuma lallai
idan ya ci gaba da zama a cikin wannan ƙanƙara to lallai
ya faɗi wannan gasa, kuma Ikenga yayi nasara.
Lamarinda ke nuni da cewa hanya ɗaya tak da yake da ita
a wannan lokaci ta nemo Tarifil-fakta ta ɓace. Wanda
kuma lallai abu ne da bazai amince ba, tunda baifi saura
wata shida ne ya rage masa ya nemo wannan mutun ba.
Nan take ya yanke shawara, "Idan ana zancen taimakawa
iyaye a lokacin da suke cikin buƙata, idan ana zancen
nemawa mahaifiya lafiya, to ai rasa shekaru ɗaya ko biyu
koma goma na tsahon rayuwa ba matsala bane. Wanda
zaiyi shekara hamsin ai zai iya haƙuri da arba'in!"
A wannan lokaci Armad ya kira ɗalasimin da aka hanashi
amfani dashi a rayuwarsa. Ɗalasimin da yake buɗe ƙofar
amfani da takobin tarihi mai suna Ɗorawa. Takobin ita
kanta Hidaya gada tayi daga mahaifinsu Wilbafos.
Wannan ɗalasimi dai anyi amfani dashi ne wajen sihirce
wannan takobi acikin wani shinge na tsafi. Wanda babu
wanda ya isa yaje ko mutun ko aljan. Kuma wannan
ɗalasimi an haɗa shi ne da ruhin Armad da kuma jinin
zuciyarsa, saboda haka nema sunan wannan ɗalasimi,
"Armad-Wilbafos!"
Ai kuwa Armad na cewa, "Armad-Wilbafos!" Wata walƙiya
mai ruwan ɗorawa ta fara ɓulɓula daga jikinsa. Nan take
wannan ƙaton akwatin ƙankara dake kewaye da Armad
ya fara narkewa.
Ikenga ya juyo cikin mamaki, amma kafin ya ƙarasa
juyowa tuni dukkan ƙanƙarar tasa ta narke. Abinda kawai
ya tarar shi ne walƙiya mai ruwan ɗorawa na kewaye da
jikin Armad. Sannan kuma a gaban Armad akwai wani
dogon haske shima ruwan ɗorawa, wanda ya bada siffar
takobi mai tsayin gaske.
Kafin Ikenga ya gama tunani ko takobi ce ko ba takobi
bace tuni dukkan yalon hasken ya ɗauke kuma wata
doguwar takobi mai launin ɗorawa ta bayyana a gaban
Armad. Tsayinta ya haura tsayin Armad da kamu uku da
rabi, amma kuma siririya ce bata fi rabin tafin hannu ba.
Dukkan jikin ta ruwan ɗorawa ne.
Amma babban abun mamakin shi ne wata tauraruwa
ruwan ɗorawa guda ɗaya data tsaya a saman wannan

takobi ta kuma ƙi ɓacewa. Girman wannan tauraruwa
baifi kamu ɗaya ba, amma tana fitarda wata irin Izza mai
ban mamaki.
Irin Izzar da baza ta misaltu ba, sai dai kurum wanda yake
cikin wannan fili kuma yaji ta a jikinsa shi ne kawai zai iya
fassara ta. Amma dai akwai kalma ɗaya da zata yi kama
da wannan Izza wato MUTUWA. Lallai wannan Izza na
kama da irin ƙanshin mutuwa wanda mutumin dazai
mutu shi kaɗai ke ji.
Bayyanar wannan takobi keda wuya da dama daga cikin
manyan baƙin da ke tare da Uznu Ururu da sarki Deniz
suka miƙe tsaye suna buɗe baki. Kai hatta Uznu Ururu
saida ya haɗe fuska cikin mamaki. Ga dukkan alamu
waɗannan mutane sun san wannan takobi. Ko kuma dai a
ƙalla sun taɓa ganinta.
'Takobin Wilbafos!' Wannan shi ne kawai abinda Uznu
Ururu ya ce acikin ransa. Abinda ya nuna cewa yasan
takobin sosai, kuma har sunanta ya sani.
A wannan lokaci ya zira hannunsa a aljihu ya fiddo da
wannan allon tsafi, ai kuwa sai ganshi yana haske. Abin
mamaki yadda allon yake haske da aka fito da Littafintakobi haka yanzu ma yake haske. Kana ganin fuskar
Uznu Ururu kasan ya gama yanke shawara cewa lallai
Littafin-takobi yana tare da Armad.
Duk da wannan abubuwa dake faruwa ko a jikin Armad,
miƙa hannu kawai yayi kan takobinsa ya kuma ɗaga ta
sama, sannan cikin kwarewa da sabawa ana yi ya juya ta
a sama ya kuma yiwo kan Ikenga.
Nan take Ikenga yai nuni da ɗan yatsansa sama,
lamarinda yasa wannan hadari dake sama ya fara rugugi
kafin daga bisani a fara ruwan manya-manyan al'amudan
ƙanƙara guda uku. Ya ƙara tafa hannayensa waɗannan
al'amudai suka juye izuwa mutun-mutumi.
Kowanne ɗaya daga wannan mutun-mutum ya juye
izuwa siffar mutun sak irin Ikenga, harda kayan jikinsa.
Ikenga ya ƙara tafa hannu, waɗannan mutun-mutumi
suka buɗe bakunansu a tare. Abu na gaba daya faru shi
ne wata ƙuwa da sauti masu rikita zuƙata da suka fara
tashi daga bakin wannan mutun-mutumi uku.
Ba komai ya jawo wannan ƙara ba illa wata dusar
ƙanƙara mai tiriri dake fita daga bakin mutun-mutumi na
farko, da kuma aradu mai ɗauke da jar walƙiya dake fita
daga bakin mutun-mutumi na biyu, da kuma ruwan zafi
dake fita daga bakin mutun-mutumi na uku.
Dukkaninsu kan Armad suka yi gadan-gadan suna neman
halaka shi.
A wannan lokaci Armad ya juya doguwar takobin dake
hannunsa. Wannan tauraro dake samanta ya kaɗa a
sama. Sannan Armad ya aika wawan sara izuwa Ikenga.
Nisan dake tsakaninsu ya fi taku biyar kuma babu yadda
za'ai takobin takai inda Ikenga yake, kai ko inda wannan
walƙiya da ruwa da dusar ƙanƙara suke ma baza ta taje

ba.
Amma bisa mamaki sai kawai wata walƙiya ruwan
ɗorawa ta fice daga jikin takobin a matsayin saran da
Armad yayi, ta kuma tunkari waɗannan abubuwa uku
dake gabato shi. Wato dai a taƙaice saran da Armad yayi
ya fice daga jikin takobin tamkar abu mai rai, ya kuma
tunkari Ikenga. Irin wannan fasahar takobi aba ce
maɗaukakiya a wannan zamani, kuma ita akewa laƙabi da
fasahar takobi mai tafiya. Wasu kuma sukan kira ta
Fasahar takobi mai Tafiya.
A dai-dai wannan lokaci ƴan kallo suka fara firgita da
al'amuran da suke gani. Lallai basu yi kama dana masu
shekarun Izza ƙasa da dubu ba.
Babu abida kake ji sai, "Kunga Armad yana iya amfani da
fasahar takobi mai tafiya!"
Wasu kuma su na cewa, "Kunga aljanin Ikenga SARKI
RAUHANI ne." To ko mai ake nufi da aljani SARKI
RAUHANI?
To aljanu gama gari dai su ake rabawa izuwa ƙabilar baƙi,
fari da kuma ja.
Aljanu maɗaukaka kuma ana raba su ne Izuwa ƙabilar
Rauhani, Muridi, Shaiɗani da kuma Ifiritu. To ko acikin
waɗannan ɗin ma akwai maɗaukaka na sahun farko,
wanda ake musu laƙabi na musamman. Misali asalin
sunan aljanin Ikenga shi ne IYYU, amma saboda
kasancewarsa maɗaukaki na sahun farko shi yasa ake ce
masa GAL-IYYU. Wato dai 'GAL' ɗin da aka ƙara wata
lambar girma ce.
Babban banbanci tsakanin waɗannan aljanu shi ne ƙarfi
da kuma yawan sihirin da zasu iya
sarrafawa.
Misali aljani gama-gari ɗan ƙabilar Fari, ko Baƙi, ko kuma
Ja, baya taɓa mallakar fasaha sama da ɗaya; dole sai dai
ko ya zama aljanin wuta, ko na ruwa ko na walƙiya ko na
ƙanƙara ko kuma dai wani abu amma dai abu guda ɗaya
kurum.
To shima jinsin Rauhani da Muridi da Ifiritu da Shaiɗani
abu ɗaya kurum suke iya mallaka, sai dai banbancin shi
ne su basu da ƙa'ida. Misali aljanin Wuta ɗan ƙabilar Fari
ko Baƙi ko Ja yana da adadin wutar da zai iya sarrafawa a
kowanne lokaci, kuma indai ta ƙare saiya jira ta taru.
Amma wutar aljanin wuta na ƙabilar Rauhani ko Muridi
ko Ifiritu ko Shaiɗani bashi da ƙa'ida, wato zai iyai ta
samarda wuta har abada. A kowanne lokaci idan kai duba
acikin ɗan taƙin dake tsakanin ruhin irin waɗannan
aljanu da masu su zaka ga wuta bata ƙarewa.
To sai kuma aljani maɗaukakin Rauhani, wanda shima
fasaharsa bata ƙarewa kamar duk wani Rauhani, sannan
kuma yakan mallaki fasaha sama da ɗaya. Yawanci biyu.
Amma ƙasa da kaso ɗaya acikin ɗari sukan samarda
fasaha sama da ɗaya kamar aljanin Ikenga kenan.
Irin wannan aljanu su ake kira da SARKI, sai a ƙara

kalmar sarkin a farkon sunansu. Wato dai a taƙaice shi ne
abinda ƴan kallon can suke nufi da cewa aljanin Ikenga
SARKI RAUHANI ne.
Nidinne dai Shuraih Usman inkiya
99%
Daga taskar magajin wilbafos
MAGAJIN WILBAFOS
Marubuci: Dr Abdullahi Muhammad Ibrahim
Babi na 46: Nauyi da Lokaci
Post by: Shuraih Usman
@shuraih 99%
www.facebook.com/hausaebooks
.
Daga:- Taskar Magajin Wilbafos
•Suna : Armad
•Ƙabila : Wilbafos
•Aljani : Ji-daime
•Fasaha : Farar Walƙiya
•Fasaha ta musamman : Miyura
•Fasahar takobi : Ɗorawa
•Izza : shekara 51
____
•Suna : Ikenga
•Ƙabila : Bayajidda
•Aljani : Gal-iyyu
•Fasaha : Jar walƙiya, ruwa, ƙanƙara
•Fasaha ta musamman : Takun-sarki (shaibal-shísu)
•Fasahar Takobi : Lokacin alfijir
•Izza : Shekara 100
***
"Hmmm...." Armad baiko tsaya kallon saran takobin daya
aikawa wannan ƙanƙara da ruwa da walƙiya ba, domin
yasan lallai saran sa na takobi mai tafiya ba sa'an
waɗannan mutun-mutumi bane. Saboda

Please Login or Register in order to submit comment