Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kaɗai.
Iliyasis cikin sauri-sauri ya fara yiwa Armad bayanin mai
ya kamata yayi.
''Wannan wajen gaba ɗayansa na musamman ne. Amma
babban inda abin yake shi ne idan ka shiga ƙofa ta gaba!
''Yanzu daga dai-dai nan inda muke, zaka rufe idanunka,
kayi taku bakwai manya.
''Sannan ka buɗe. Zaka ga wata ƙofa ta bayyana a
gabanka. Ka tura wannan ƙofa ka shiga ciki.
''Abu na farko daya kamata ka sani shi ne, kana shiga
wannan ƙofa kabar wannan ƙasa, domin kuwa wannan
ƙasar da zaka shiga an yanko tane daga gari na huɗu na
daular Maikironomada.
''Ƙasar da babu wanda ya isa ya taka face mai ƙarfin jinin
maikironomada sama kaso casa'in da biyar a jikinsa.
''Saboda haka ne kafin ka shiga anan zan koya maka wata
fasaha.
''Wadda ake amfani da ita wajen shiga wannan waje da
ruhinka maimakon jikinka.
''Kai sani cewa yanzu da muka shigo wajen nan babu
wanda zai iya ƙara shigowa koda kuwa an buɗe masa
ƙofa, har sai mun fita.
''Kuma mu ma baza mu iya fita, ko mun daɗewa indai
ba'a buɗe ƙafar gaban dana gaya maka ba.
''Saboda haka ka kwantar da hankalin ka, ka nutsu ka koyi
wannan fasaha, saboda ita zata zama gimshiƙi Izzarka
anan gaba.
''Sai dai matsalar guda ɗaya anan ita ce ta lokaci.
''A hasashen da mai gadin can ya gayamin mafi
ƙanƙantar lokacin da zaka ɗauka shi ne;
''Shekara GOMA!!''
Baki a buɗe, idanu cike da mamaki, sannan kuma zuciya
cike da kokwanton ko yaji abinda Iliyasis ya faɗa dai-dai,
Armad yai ajiyar zuciya gami da tambaya, ''shekara.....
nawa kace???
Kafin Iliyasis yace wani abu tuni Armad ya ci gaba da
magana;
''inaaa, kai ka kai, ai wannan ba abu ne mai yiwuwa
ba....kawai nuna min hanyar fita dan ALLAH.
''Akwai abinda ya zama wajibi da nayi, wanda kuma shi
ya kawo ni wannan ƙasa.
''Sabida haka ina ganin kawai zan nemi wata hanyar da

zanbi na inganta Izza ta, kuma koma badan wannan ba
ai.......''
Tunda Armad ya fara magana Iliyasis yake ta ƙoƙarin
tsayar dashi, amma ina idanun Armad sun rufe ya
fituttuke baya ji baya gani.
Sai a wannan lokaci ne ya samu nasarar tsayar dashi da
ajiyar zuciya, ''hmmmm!!
''Ka dakata mana kaji ƙarshen maganar, ko.''
Armad na haki ya dubi Iliyasis wanda kawai murmushi ya
gani a idonsa, irin murmushin nan mai ɗauke da saƙon
'ka kwantar da hankalinka, akwai mafita!'
Ya ɗan kyaɗa kai tare da kyaran murya da niyyar fara
jawabi, ganin cewa hankalin Armad yaƙi kwanciya, kuma
daga dukkan alamu indai ba bayani yaji cikakke ba, to fa
babu yadda zaiyi ya kwantar da hankalin nasa.
''Abinda baka sani ba shi ne, wannan waje, wajene na
musamman, ta ɓangarori da dama.
''Babban abin shi ne lokaci!
''Kai sani cewa duk kwana ɗaya a waje dai-dai yake da
kusan kwana ɗari da ashirin anan wurin!
''Kaga kenan duk kimanin kwana uku a waje, dai-dai da
kusan shekara ɗaya anan. A taƙaice dai yin shekara ɗaya
acikin wajen nan baifi kwatankwacin kwana uku a waje
ba.
''Kaga kenan shekaru goma da aka baka hasashe, baza
sufi kwana talatin ba a waje.''
Yai shiru fuskarsa cike da murmushi yana karanta
mamakin dake cikin idanun Armad. Kai daka ganshi
kasan bai taɓa tsammanin wannan abu ba.
Ana haka kafin Armad yai magana, tuni Iliyasis ya ce,
''saboda haka baka da wata damuwa.
''Kuma wannan wata dama ce daka samu da ba lallai ka
ƙara samun irin taba, saboda bamu san yaushe ne jikinka
zai iya ƙara jure shigowa wannan waje ba.
''Saboda wataƙila baka sani ba, amma akwai adadin da a
gabaki ɗayan rayuwar mutun zai iya shigowa wannan
waje.
''Kuma da dama daga cikin mutane, baya wuce sau ɗaya,
amma ga dukkan alamu zaka iya wuce ɗayan, amma dai
ka sani cewa ko shugaba Bihanzin karo huɗu kaɗai jikinsa
ya iya ɗauka, sannan kuma na ƙarshen saida yai shekara
tara yana jira kafin jikinsa ya iya.''
Yana gama wannan bayani, ya zira hannu cikin ƴar
alkyabbarsa, inda ya zaro wata ƴar takarda mai zanezanen abubuwa guda biyu akai.
Ɗaya zanen mutun ne ɗaya kuma wata ƙatuwar dabba
ce mai ƙaho ƙahon-huna akanta.
Kuma abin mamakin shi ne a kallo na farko, sai kayi
tunani cewa wannan ƙahun huna sun kusa goma, amma
idan ka ƙura ido sai kaga ai basu da yawa sosai, amma
kuma idan ka fara ƙoƙarin lissafa su, bisa mamak sai ka
kasa.

Komai yadda kayi ƙoƙarin lissafa su baza ka iya ba,
hasalima kana ƙara matsawa kusa da su dan ka lissafa,
suna ƙara rikita ka.
Hakan ma yasa Armad yai saurin ɗauke idonsa daga kan
takardar aaboda tuni kansa ya fara juyawa.
Iliyasis ya ce, ''kamar yadda ka riga ka sani, duk wani ɗan
adam yana da yana da ruhi kuma yana da gangar jiki.
Gangar jiki ba wani abu bane ba illa jini da tsoka kawai,
wanda zasu iya riɓewa kuma mutun zai iya canjawa.
''Saboda haka a zahiri, sirrin Izza gaba ɗaya ya ta'allaƙa
ne da ruhin jikin mutun, wanda baya riɓewa kuma ba'a
taɓa canjashi.
''Dan a wannan zamanin ma da wuya ka samu mutun
ɗaya dake da wannan bayanin. Kuma a gskiya ban sani ba
ko zaima wani amfani ko kaɗan, sai dai yaya Nusi ta
barmin umarnin cewa ya zama wajibi komai ka sani.
''Yanzu abu na gaba shi ne.....''
Armad ya katseshi da cewa, ''wato... tunda muka shigo
wajen nan nake ta mamakin wani abu.
''Da farko ina kokwanto, amma yanzu da naji labarin nan
naka na samu tabbashin abinda nake tunani.
'Wannan kuwa ba wani abu bane ba illa cewa lallai nasan
wannan waje naku da kukewa laƙabi da Non-toch-teka
ciki da bai!!!
Iliyasis yaci gaba da bayani, "Daga nan inda muke, gangar
jikinka bazata iya wucewa ba, saboda haka..." yana faɗar
haka ya tafa hannunsa biyu, inda wata akwatun zinare ta
fito daga jikin wannan takarda.
"Zaka shiga cikin wannan akwatu, sannan kuma daga nan
ruhinja zai futo a matsayin fatalwa, wanda shi zai take
maka hanya zuwa ainahin inda zaka ɗauki wannan
fasaha.
"Wato dai a taƙaice, gangar jiki bata taɓa wajen da zaka
shiga!"
Bayan sun gama yin ƴan ragowar bayane-bayanensu,
Armad ya shiga cikin akwatin nan, ya kwanta. Ba'a jima
ba kuma, abu kamar wasa saiga wata siffa mai kama da
Armad sak, ta taso daga jikinsa, ta futo daga cikin
akwatin.
Komai nata irin nasa ne sak, hasalima, idan ba taɓa ta
kayi ba, kaji hanninka ya wuce ba, to baza ka taɓa gane
cewa ba shi bane.
Nan take Iliyasis, yai sauri ya rufe akwatin.
Wani sirri da wannan akwati yake dashi, shi ne, indai ka
shiga ciki, to fatalwarka da zata fito, zata fito da ilmin duk
yadda ya kamata tayi, da hanyoyin daya kamata tabi
acikin wannan waje mai suna Non-toc-teka!
Tana fitowa, kawai ta nufi arewa ta fara yin taku cikin
tsari. Taku bakwai kaɗai tayi, wata ƙofa ta bayyana a
gabanta, kana daga bisani ta buɗe. Wannan fatalwar
halitta wadda ga dukkan alamun babu ƙashi babu jini a
jikinta, hasalima kamar hoto kawai take, ta shige cikin

wannan ƙofa kai tsaye.
A wajen ƙofar kuma inda Iliyasis ke tsaye, ajiyar zuciya
kawai yai, sannan ya nemi waje ya zauna ya fara addu'a.
Acikin wannan ƙofa kuwa, fatalwar Armad ta bayyana a
wani fili mai ɗauke yanayin daɗewa a duniya, kai kace ya
shekara miliyan da samuwa. Irin yanayin da idan baka da
ƙarfin zuciya zai iya kaika ƙas cikin zafin nama.
Take wannan fatalwa ta rufe idonta gami da dosar gabas
maso kudu ta fara tafiya, a wani salo na taku masu tsayi
da tsari, iri ɗaya sak.
A haka saida tayi taku arba'in cif-cif sannan ta tsaya ta
kuma buɗe ido.
Tana buɗewa cikin zafin nama kamar wadda ke lissafa
lokaci, tayi sauri gami da rufe idonta na dama, sannan ta
juya izuwa ɓangaren yamma maso kudu ta fara taku
wanda girmansu dai-dai yake dana baya.
A haka saida tayi taku ashirin cif-cif, sannan da sauri
kamar a baya, ta ƙara rufe idonta na hagu sannan ta
buɗe na daman, inda ta ƙara juyawa izuwa ɓarin gabas
maso kudu, kuma ya fara tafiya komai kamar a baya.
A wannan karan ma taku ashirin tayi cif, sannan ta ƙara
tsayawa, gami da buɗe idanunta.
A wani salo na kwarewa wannan fatalwa ta ƙara juyawa
izuwa ɓarin yamma maso kudu, sannan ta rufe duk
idanunta guda biyu ta aiwatar da taku arba'in cif-cif
sannan ta tsaya.
Amma a wannan lokaci bata buɗe idonta, kurum kawai
tayi a tsaye cak.
Bayan wucewar lokaci mai tsayi wanda yakai kamar
kwana biyar ko shida, sannan ta buɗe, kuma ta nemi
waje ta zauna ƙafafu a tanƙwashe tana fuskantar
gabanta.
Babu wani abu na musamman daya faru, kai hasalima
babu abinda ya canja ko kaɗan. Komai yana nan shiru
kamar kullum.
Haka dai abubuwa suka ci gaba da gudana, kafin kace
meye wannan wata yayi babu abinda ya faru, wannan
fatalwa tana nan a zaune tana fuskantar gabas.
Wata biyu, wata uku, wata huɗu, biyar..... shekara
ɗaya......haka dai lokaci yaci gaba da wucewa har akai
shekara tara da rabi cif-cif, wannan fatalwa batai ko
gezau ba, kai hasalima ko rufe ido ba tayi ba.
A wata rana ta litinin, sha huɗu ga watan Yuri (wata na
uku a kalandar Aldurish), wannan fatalwa na zaune, sai
kawai ruwa ya fara sauka kamar da bakin kwarya daga
wannan farin sararin samaniya, dake wajen.
Kuma wani abun mamaki shi ne shi kansa wannan ruwa
ja ne, jajawur kamar jini.
Bayan an ɗauki kwanaki da dama ana wannnan ruwa,
sannan ya tsaya cak.
Anyi ruwa mai ƙarfi, amma dukkansa wannan farar ƙasa
ta tsotse kaf, babu ko alamun ragowa, kai idan ka zo a

bayan an gama ma, ba lalle kace anyi ruwan ba.
Kuma duk abinda ke faruwa, wannan fatalwa na zaune
har a wannan lokaci batai ko gezau ba.
Toh, kwana uku da gama wannan ruwan, wata rana da
safe komai a wannan duniyar ya fara girgiza kama za'ai
girgizar ƙasa.
An daɗe ana hakan, kafin daga bisani komai ya fara
lafawa.
Bayan ƴan mintuna ƙura ta lafa, wasu ƙofofi guda uku su
bayyana a gaban wannan fatalwa.
Suna bayyana, dukkansu suka buɗe a lokaci ɗaya, kuma
abubuwan dake cikinsu suka bayyana ga idanun wannan
fatalwa ta Armad.
Acikin wannan akwati dake ɓangaren dama babu komai
sai wata tasa da wani ruwa acikin ta. An rubuta Farkári
ajikin tasar.
Na tsakiya kuma wani ɗan littafi ne mai jan bango, kuma
anyi rubutu da jini a jikinsa, wanda kodai bai fita ba sosai,
ko kuma lokaci da shekaru yasa ya fara gogewa. Amma
dai dukkanin girmansa baifi tafin hannu ba.
Acikin akwatin ɓangaren hagu kuma wani mashi ne,
wanda a tsininsa akwai wuta tana ci, wadda ga dukkan
alamu tafi shekaru dubu tana ci bata taɓa ɗaukewa ba,
kuma bata da niyyar ɗaukewa.
Ajikin mashin an rubuta Mashìral-Iburish!
Bayyanar abubuwan nan keda wuya wannan fatalwa ta
tashi daga inda take, a lokacin farko tun bayan shekaru
tara acikin wannan duniya ta Non-toc-teka.
Bayan ta miƙe ta ɗaga hannunta sama, kuma babu ko
alamun tsoro, ta caka shi acikin ƙirjinta, inda da kyar
bayan lalube, ta fito da hannun nata a tsininsa akwai
alamun jini, wanda bai wuce ɗigo ɗaya zuwa biyu ba.
Cikin sauri, kamar wadda take tsoron jinin zai iya ɓacewa
idan ta ɓata lokaci, ta matseshi a babban ɗan yatsanta na
dama, inda ta nunoshi gaban waɗannan akwati uku.
A wani yanayi mai ban mamaki duk waɗannan abubuwa
uku dake cikin akwatin wato da mashin da tasar da kuma
littafin, suka fara girgiza da ƙarfin gaske, kamar waɗanda
suke so su fice daga cikin akwatunan.
Hakan ya ɗau lokaci yana faruwa, kafin daga bisani
wannan littafi ya taso da gudu ya faɗa kan tafin fatalwar.
Hakan na faruwa, ragowar abu biyun suka daina motsi
kwata-kwata, hasalima akwatinan da suke ciki komawa
sukai suka rufe, kafin daga bisani su ɓace ɓat.
Shi kuma wannan littafi kafin kace meye wannan tuni
wannan ɗigon jini ya hau kan jan rubutun dake kansa,
wanda bai fita ba sosai.
Kafin kace meye wannan, wannan rubutu ya juye izuwa
sunan Armad wanda ya fito tar-tar.
Hakan na faruwa wannan duniya ta fara disashewa kuma
kan ƙiftawar ido da bismillah ta ɓace inda wannan
fatalwa ta ƙara bayyana a inda ta bar Armad acikin

akwatin nan.
Koda bayyanar ta, sai Iliyasis wanda ke zaune gefe guda
ido ya ɗago kai ya kalleta, acikin zuciyar yace, "har ila yau
kwananta bai kai talatin ba."
Sai dai kuma amma acikin duniyar data shiga, lissafin ya
haura na shekaru
Tana bayyana riƙe da littafin a hannu sai ta fara kusantar
wannan akwati, amma bisa mamaki wata iska mai ƙarfin
gaske ta miƙe inda ta shiga taakaninsu da akwatin, a wani
yanayi na nuna cewa lokacin komawarta baiyi ba.
Har a wannan lokaci, wannan fatalwa bata kalli Iliyasis ba,
kawai sai ta koma gefe guda ta nemi waje ta zauna.
Tana zaune wannan littafi na hannunta, kawai saiya fara
haske, inda ba tare da ɓata lokaci ba wannan littafi ya
rikiɗe izuwa siffar wata takobi, wadda bisa mamaki a jikin
farin ƙarfen ta aka rubuta sunan Armad a jiki.
Tana da ƙota baƙa mai ɗauke da zanen wasu ɗalasimai a
jiki, sannan kuma a ɗayan ɓangaren ta, wanda babu
sunan Armad ɗin, an saka RIFLEGZIYA!
Jikin takobin farin ƙarfe ne kawai, wanda kuma duk da
kyallin da yake, a kallo na ɗaya abinda zai faɗo maka rai
shi ne, gama garin ƙarfe ne kawai!
Dukkanin abubuwan dake faruwa akan idon Iliyasis suke
faruwa, kuma daga ganin yadda ya miƙe tsaye cikin
firgici, idanun sa acike da ɗimauta kasan cewa an kai
maƙura wajen gigita shi da abinda bai taɓa tsammani ba!
Babu abinda ke fita daga bakinsa face wasu kalmomi
guda uku, ''Fasahar... marubutan..... farko!!!!''
***
Abu ne sananne a wannan zamani cewa, kusan kowacce
babbar ƙabila suna da ire-iren fasahohinsa na sarrafa Izza
na musamman.
Da dama daga cikin irin waɗannan fasahohi kamar wata
shedar mallaka ce dasu, wato ana gani ansan cewa ƙabila
kaza ce, kuma koda wani ya samu ya ɗan kwafe to zaka
samu basu da yawa, kuma sannan da dama basa iya
kaiwa matuƙa wajen kwarewa akan irin wannan fasaha.
Ta hanyar wannan fasaha zaka iya rubuta sunan abu
wanda kake so, kuma wannan abu ya tashi daga siffar
rubutu izuwa wannan abu.
Sannan kuma daɗin daɗawa zaka iya juyarda abinda ya
riga yake a gaske izuwa rubutun.
Misali; zaka iya sanya sunan takobi, sannan kuma ka
rubuta yanayin yadda kake son wannan takobi ta kasance
a gaske.
Idan kayi amfani da wannan fasaha sai wannan rubutu ya
juye izuwa takobin da kake buƙata.
Sannan kuma a ɗaya ɓangaren idan kana da takobi kana
so ka ɓoye, to zaka iya rubuta bayanin wannan takobi
taka, sannan kayi amfani da wannan fasaha ka maida ita
zuwa rubutu.
Tarihi yazo cewa Maikiro Abbas, wato sarkin

Maikironomada na biyu a duk tarihi shi ne ya samarwa
da ƙabilar wannan fasaha.
Kuma kamar yadda yazo Maikiro Abbas yana daga cikin
mutane da bakwai da suka ƙirƙiro rubutu a dukkanin
wannan zamani.
Toh! gashi dai sa'a ko kuma ƙaddara ta kawo Armad ya
mallaki takobi ta wannan hanya.
To ko wanne sirri ke ɗauke ajikin wannan takobi, ko waye
yai amfani da irin wannan fasaha wajen adana ta, ko ta
waye, sai ku biyo mu kusha labari.
***
Acikin wannan waje kuwa a wannan rana da wannan
takobi ta bayyana, fatalwar Armad da Iliyasis su na zaune
su na jiran lokaci.
Tsaho kusan shekara goma kenan tun bayan shigar
Armad cikin wannan akwati.
Amma idan ka kalli Iliyasis, wanda suka shiga a tare zaka
samu cewa yana nan tamkar ranar da suka shigo, ko
kaɗan jikinsa bai canja ba.
Hasalima kai baza kace yayi sati bama.
Wannan ba wani abu bane ya jawo haka ba, illa sirrin
wannan waje.
Wanda suka haɗa da canjin ƙidayar lokaci tsakaninsa da
waje, sai kuma cewa baka buƙatar cin abinci ko kwaya
idan kana cikin wannan waje.
Domin kuwa ko gajiya ba'a yi, ba kuma a bacci, kai
Iliyasis ko ƙifta ido ma baƴayi.
Amma abisa dole saboda wani haske mai kashe ido dake
tashi daga jikin takobin dake hannun fatalwar Armad ya
saka shi rufe ido a wannan lokaci.
Kafin kace meye wannan wannan haske ya cika ko'ina
baka ko ganin gabanka.
A haka sama da daƙiƙa sittin ta wuce, Iliyasis yana ta
ƙoƙarin buɗe ido yaga meke faruwa, amma haƙar sa yaƙi
cimma ruwa.
To yana cikin haka ne, wannan haske ya fara ɗaukewa da
kaɗan da kaɗan. Inda bayan wani lokaci ya ɓace ɓat,
Iliyasis ya samu damar buɗe idonsa, amma sai idanun
nasa sukai masa arba da abinda bai zata ba.
Domin kuwa babu abinda ya gani face Armad shi kaɗai a
tsaye a inda da wannan akwati da take.
Duk da yana da nisa daga inda Armad yake, amma tun
daga inda yake, yana jiwo yanayin babbar Izza na tashi
daga jikin Armad.
Sannan kuma ga tambarin Miyurar dake goshinsa na
fitarda wani jan haske ta cikin kyallen dake ɗaure a
goshin nasa.
Idan kuma da babu wannan kyallen da Iliyasis ya samu
damar ganewa idonsa wani sabon tauraro dake kewaya
tambarin dake gaban goshin na Armad.
Sannan kuma daga irin yanayin babbar Izzar dake tashi
daga jikin Armad da kuma wata sabuwar takobi dake

rataye a wuyansa ta ɓangaren dama, Iliyasis yasan cewa
Armad yaci nasarar samun babbar fasaha a wannan waje
mai tsohon tarihi da ake kira da Non-toc-teka.
Daɗin daɗawa gashi Al'yaya, kuma gashi Magajin
Wilbafos.
Tunda Iliysis baisan sunan Armad na gaskiya ba, saboda
haka tuni a wannan lokaci ya fara yi masa shigen kallon
girmamawar da yake yiwa shugaba Bihanzin.
Hasalima yana gab da zubewa a ƙasa ya kwashi gaisuwa
wajen Armad, Armad ɗin ya iso gareshi gami da dafa
kafaɗarsa, lamarinda yasa ya dawo hayyacinsa, amma
duk da haka yakai maƙura wajen gigita da ƙarfin aniyar
Armad da kuma yanayin yadda yaga ƙaddara tana tare
dashi.
Armad cikin wasa ya fara magana, ''ahhh..Iliyasis! yi
haƙuri, inaji a jikina mun ɓata lokaci da yawa ko?''
maganar da wasa yake yinta amma girman izzar da take
ɗauke da ita yana da yawan.
Wanda har yakai yadda yasa Iliyasis ya kasa bada amsa,
babu abinda ya iya sai kawai girgiza kai, ƙafafunsa na
karkarwa kamar bazasu iya ɗaukansa ba.
Kuma yana da kyau mai karatu ya sani cewa Iliyasis baya
daga cikin na ƙasa a fagen Izza, hasalima a ko'ina kakaishi
za'a saka shi acikin jarumai madaidaita, domin tuni
matakin Izzarsa yakai ɗari da ashirin da ɗaya.
Amma a bisa mamaki ƴar wannan tambaya da Armad
yayiwa Iliyasis ta rikita shi.
Armad ɗin ya fahimci haka, kuma baiji daɗi ba, duk da
kuwa yasan baya sane hakan ya faru. Tunda yana da
cikakkiyar masaniya cewa wata sabuwar Izza ta shiga
jikinsa kuma yana buƙatar zallar fafatawa da mazaje
kafin ya iya sarrafa ta, inba haka ba kuwa, zata iya jawo
matsala babba, domin zata iya fin ƙarfinsa.
Saboda haka ya bawa Iliyasis haƙuri, wanda daga baya ya
nuna masa ai ba komai.
Ya kuma gaya masa cewa shima yana nan tafe. Sukai
dariya kawai.
***
Nidinne dai Shuraih Usman inkiya
99%
Daga taskar magajin wilbafos
MAGAJIN WILBAFOS
Marubuci: Dr Abdullahi Muhammad Ibrahim
Babi na 26: littafin takobi
Post by: Shuraih Usman
@shuraih 99%
www.facebook.com/hausaebooks
.
Daga:- Taskar Magajin Wilbafos
Bayan ya karanta wasu ɗalasimai, irin ƙofar da suka shigo

ta bayyana a gabansu, suka buɗe gami da ficewa.
A wannan rana sun kusan kwana talatin kenan aciki,
kuma tuni mutane suka daɗe da cika a wajen ƙofar.
Da dama ma tuni sunzo sun tafi. Musamman tunda ba
kowa ke daɗewa ba.
Kuma wasu kawai siyan makami, ko kuma Ayrid ko kuma
wani laƙanin, kawai suka zo siya. Wanda kuma sunfi kowa
yawa.
A saboda hakan nema, da dama basu wani kula da
fitowar su Armad ba, waɗanda kuma sukai sauri, suka
ɓace acikin jama'a suka kama hanyarsu.
Basu daɗe ba, suka iso gida ba, inda suka tarar kamar
ansan da zuwansu anyi matuƙar ƙawata gidan tun daga
nesa ƙanshi yake tashi.
Kuma dai duk da babu mutanen da aka gayyata sabida
Nusi wadda ita ce muƙaddasin haɗa komai, ta tabbata
komai yayi kama da na musamman a wajen.
Suna isa da ita da Cokali da sauran kuyangin gidan suka
taryesu, inda suka shiga ciki tare, zuwa babban falon
gidan da aka shirya domin aci asha kawai.
Labari na farko daya isa kunnen Armad shi ne, tun kusan
kwanaki ashirin da suka wuce Nusi ta fito daga wannan
kogo mai inganta jinin Maikironomada a jikin mutun,
kuma ta sami sa'a, ta sami abinda ba'ai tsammani ba.
Wato kaso SITTIN na jinin Maikironomada.
Tun a washe garin ranar mutanen ta na birni da kewaye
suka so su haɗa mata walima amma taƙi.
Daga baya, bayan ƴan kwanaki an sanar da cewa ita ce
ƴar majalisa ta gaba da za'a rantsar a wannan gari na
Khan.
Mutane da dama sun nemi su haɗa mata gagarumar
walima, kai aciki harda shugaba Sahabi ma, amma taƙi.
Ta bada uzurin ai a ƙarshen shekarar, wato nanda wata
bakwai akwai taro da za'ai na musamman saboda ita, na
rantsar da ita, saboda haka a yanzu basai sun wahalar da
kansu ba.
A zahiri kwata-kwata basu ji daɗi ba, amma haka suka
haƙura sabida sun san a irin halinta bazata canja ra'ayi
ba.
Babu wanda yasan haƙiƙanin dalilin da yasa taƙi sai
Cokali da sauran mutanen gidanta.
Abinda kuwa ta gaya musu shi ne, tayi amanna a ranta
cewa Armad ƙaninta zai samo babbar Izza a Non-tochteka, saboda haka, tafi so ta bar walimar ta idan ya fito
sayi tare.
Taso ta gayawa mutanen ta kamarsu Shugaba Sahabi,
cewa ta ɗaga walimar ne kawai akwai abinda take jira,
kuma idan yazo zata gayyace su, amma taga bata so ko
kaɗan tayi abinda zaisa sunan Armad ya watsu a gari,
saboda haka ta bar zancen kuma ƙulla aniyar su kaɗai ma
sun isa suyi walimarsu.
Duk kuma maiso ya taya ta murna yayi mata a babban

taron da za'ai na ƙarshen shekara.
To da yake katin shedar dasu Armad suka yi amfani dashi
wajen shiga Non-toch-tekar nata ne, saboda haka suna
buɗe ƙofar ta sani, kuma ta tashi shirye-shirye.
A wannan daren sunci sunsha, musamman idan ka ɗauki
Armad da Cokali waɗanda sukai ta rawa.
Suna gasa tsakanin irin rawar mutanen ƙasa ta uku da
kuma ƙasar Maikironomada, daga ƙarshe dai aka cinye
Armad, inda bayan sun gama kowa ya zaɓi rawar Cokali
akan ta Armad, sai mutun ɗaya kaɗai.
Wadda ita ce Nusi, Wadda ta zaɓi ta Armad, amma ita ma
daga gani kara tai masa, kawai.
Daga baya dai Armad rai cike da baƙin cikin rasa wancan
gasa yace ayi gasar shan fura.
To anan ne ya cinye cokali, saboda saida ya yasha daruka
da dama har ya kasa tashi, waɗannan kuyangi sukai ta
latsa masa ƙaton cikins suna tsokanarsa.
Haka dai sukai ta raha, suna ci suna sha suna dariya,
harya zuwa kwana kusan biyu.
A rana ta uku ne, kowa ya haɗa baki wajen cewa suna son
gasar waƙa tsakanin Nusi da Armad.
Armad baiso wannan gasa ba, saboda tunda yake a
rayuwarsa bai taɓa wata waka mai daɗi ba.
Kai ko haddace wa yayi idan yazo bata daɗi.
Amma babu yadda zaiyi tunda kowa ya haɗa baki yana so
ayi.
Saboda haka ya ce Nusi ta fara, wadda tun ɗazu take
masa dariya.
Nusi ta tashi ta fara waƙa amma kai da kaji kasan wasa
kawai take don kada jikin Armad yai sanyi.
Amma abinka da cewa dama tana da zaƙin murya sosai
duk da haka saida waƙar tasa masu sauraro nishaɗi.
Bayan ta dawo ta zauna Armad wanda ke zaune yana ta
tunanin wanne uzuri ya kamata ya bayar, amma ina kafin
yai wata-wata Cokali ya jashi tsakiyar fili.
Murya cike da dariya, Cokali ya ce, ''bari na samo garaya
ta nayi maka kiɗa.''
Fuskar Armad babu annushuwa ko kaɗan, saboda da
yana murnar yasha da nasara ɗaya, rashin nasara ɗaya,
amma yanzu yasan lallai ga wata rashin nasarar nan tazo.
Bayan ya ɗau lokaci yana raba ido daga kan wannan zuwa
wannan, su kuwa dariya kawai suke suna nishaɗi, kai
hatta waɗannan kuyangi ba'a barsu a baya ba.
Cokali kuwa yama kasa zama, yana gefen Armad furkarsa
na nuna alamun tausayi amma kana kallon cikin idonsa
kasan dariya ce kawai fal aciki.
Can Armad yana cikin wannan hali idanunsa suka kai kan
Nusi tana murmushi, a wannan lokaci kawai wata dabara
tazo masa.
Kawai ya buɗe baki ya fara waƙa;
Djinn Djinn
Djinn Djinn

Djinn Djinn
Djinn Djinn
Djinn Djinn
Djinn Djinn
Wannan waƙa ta Armad tasa da yawa daga cikinsu sunyi
dariyar da basu taɓa yiba a rayuwarsu ba.
Har sai da iska ta ringa ɗaukar wannan dariya tana sawa
ana jinta a wasu wuraren na nesa dasu.
To haka dai wannan rana ta uku ita ma ta ƙare suna cikin
farin ciki da annushuwa.
A ranar ƙarshe wato ta huɗu, Nusi ta tashi tayi jawabin
cewa wannan walima ce ta cewa ta karɓi Armad a
matsayin ƙaninta na uku bayan Iliyasis da kuma Cokali.
Duk da kuwa furar da suka sha ta kwana da kwanaki tasa
rabi da rabi suka ji abinda yake cewa, amma dai-dai
wajen mai mahimmancin daya shafi Armad sunji.
Haka suka sukai barci, dukkansu basu san cewa wannan
rana zata zama ɗaya daga cikin ranaku ababan tunawa ba
a tarihi.
Bayan ƴan kwanaki da yin wannan walima Nusi da
Iliyasis da Cokali suka ɗauki Armad zuwa wajen gari, inda
sukai tafiya mai nisan gaske har saida suka fara hango
wani ƙaton kogi, wanda zaka iya ce masa maliya ma tun
daga nesa, saboda girma.
Bayan sun tsaya a wajen sai Nusi ta nuna masa wannan
kogi dake nesa kuma tace, ''kaga wancan ruwan shi ne
wanda nake gaya maka!
''Indai zaka iya yin wata biyu cir akansa, kuma ka fito da
rai da lafiya, to zan yarda ka shiga 'Gasar Jinzidal'."
To daman dai yau kusan sati kenan su huɗun suna
muhawara akan kamatar su bar Armad ya shiga ta
Jinzidal (wadda akewa laƙabi Deniziyya Kuronikil) ɗin Ko
kuma a'a!
Amma dai daga ƙarshe suka tsaya akan cewa indai zai iya
rayuwa akan wannan ruwa wanda zaka iya samun daga
kan Dordor masu kai ɗaya har ya zuwa masu kai biyar
aciki.
To zai iya shiga wannan gasa, ta Deniziyya Kuronikil!!
Har sun juya zasu tafi, sai ƙasar da suke kai taɗan fitarda
wata ƙara mara sauti saosai ko kuma tsoratarwa.
Dukkaninsu sunsan mai wannan ƙara take nufi, ba wani
abu take nufi ba illa cewa an turowa wani saƙo ta Ayrid.
Ai kuwa ba'a daɗe ba wata ƴar shuka ta bayyana a gaban
Armad, wadda ta samarda wata ƴar filawar takarda.
Armad na miƙa hannu wannan takarda tayi wajensa,
alamun saƙon nasa ne.
Ai kuwa haka ya buɗa ya fara karantawa, ba jimawa wani
mugun gumi ya fara keto masa. Dukkanin gashin jikinsa
ya miƙe. Idanunsa jajawur ya dubi Nusi yace lallai
lokacin komawa ta gida ya zo. Domin kuwa babu shakka
lallai saina nemo Tarifil-Fakta acikin wata bakwai masu
zuwa!

"Ehh!!!!" Nusi tai wata wawar ajiyar zuciya, "mai kace, wai
menene ne acikin saƙon? Waya turo maka? Kayi mana
bayani."
Dukkanin hankulan su Iliyasis da Cokali Suma ya tashi,
domin sun san koma menene acikin saƙon nan,

Please Login or Register in order to submit comment