Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ba."
Armad najin tambayar ya tuno abinda Babara ya gaya
masa akan yayarsa Hidaya wadda ke can tana yaƙar
aljanu a wata duniya ta daban. Lallai kuma haka ne,
tunda sai kana ganin abu zaka iya yaƙarsa.
Armad ya girgiza kai alamun bashi da amsa, inda Babara
yaci gaba da cewa, "To wannan shi ne dalilin da yasa na
gaya maka cewa cikakken ma'aboci Izza bada idonsa yake
gani ba. Kuma horonka na farko zai fara daga wannan."
Babara na faɗar haka ya tsaya a tsakiyar dusar ƙanƙarar
nan tare da kirawo waɗandu ɗalasimai a zuci, lamarinda
ya bayyanarda aljaninsa. "Zaka fara horo da aljanina mai
suna Ji-Inara."
Aljanin ya kasance jinsin muridi, yana da farar haɓa
doguwa da koren gashi wanda ya futo akan ƙahonsa
guda ɗaya. Hannayensa kuwa ƙananu ne ƴan gajeru
kamar na jariri sabuwar haihuwa. Amma ƙafunsa sunkai
tsayin zira'i sittin. Yana sanye da farar alkyabba ta ƙasaita,
kana ganin yadda yake ɗaukar kansa kasan wannan aljani
yana ji da kyau.
Koda rufe bakin Babara sai aljanin ya rusuna tare da
miƙa gaisuwa. Sannan kafin ya ɓace wani ƙaton al'amudi
ya bayyana a hannunsa.
Babara ya numfasa ya ce, "Kada ka damu, bazai kashe
kaba amma zaka sha wahala. Kayi duba izuwa Tsarin-
ruhinka, yanayin me kake ji idan ka kalli Izzarka?
Armad ya girgiza kai yana cewa, "ba wani yanayi da nake
ji."
Babara ya ce, "a'a dai ƙara dubawa da idon basira."
Armad na niyyar cewa a'a amma wata zuciyar tace ya
duba. Saboda haka ya rufe idonsa yayi duba izuwa Tsarin-
ruhinsa inda yai tsinkaye da abubuwan nan guda uku:
Izza da takobi da kuma wannan mutun-mutumi mai
idanu ruwan ƙasa wanda shi ne a matsayin aljanin Armad
da Uznu ya kashe.
Armad ya maida hankalinsa akan Izzarsa domin jin
wannan irin yanayi Babara yake faɗa amma baiji komai
ba. Yana niyyar buɗe ido ya bayyanawa Babara sai yaji
wata iska mai zafin gaske na tashi a hankali daga inda
izzarsa take. Nan take ya fara mamakin shin dama
wannan iska tana nan ne ko kuma yanzu ta bayyana,
domin kuwa dai bai taɓa ganinta ba.
"Naji iska mai zafi na tashi."
Babara yai murmushi tare da cewa, "wannan iska ita ce
yanayin Izzarka. Kayi sani cewa akwai yanayin izza da
dama. Amma wanda aka fi sani sune yanayin zafi,
yananyin hunturu, yanayin kaka, yanayin rani, da kuma
yanayin damuna. Kamar kai kana da yanayin zafi ni kuma
yanayin rani ne dani.
"Irin wannan yanayi da kake ji ajikin shekarunka na Izza
shi zaka yi ƙoƙari kaji ajikin wannan aljani nawa tunda
baza ka iya ganinsa ba. Zan tafi nayi bincike akan
sharrikan dake cikin wannan kurkuku da kuma hanyoyin
da zamu iya ficewa, kai kuma zaka tsaya anan ka koyi jin
yanayin Izza da aljani na Ji-Inara."
Armad ya kyaɗa kai tare da amincewa. Lallai yasan cewa
ba ƙaramin ƙarfi zai samu ba idan ya koyi wannan
al'amari na Izza, domin hakan na nuna cewa zai iya faɗa
da mutun ko aljan koda kuwa idanunsa a rufe suke. Indai
zai iya jin Izzar dake jikinsu yadda yake jin Izzar dake
jikinsa to lallai koda baya ganinsu zai iya sanin inda suke
da kuma motsin da suke da kuma yadda zasu yi motsin.
Ta haka babu wani abu da zai ɓoye masa.
Armad na cikin tunani Babara ya ɓace ya barshi da aljani
Ji-Inaru. Koda ganin haka sai aljanin yai dariyar mugunta
tare da ɓacewa. Abu na gaba da Armad ya sani shi ne
saukar wannan al'amudi a bisa doron kansa, ba tare da
yasan daga ina ba. Ƙarfin dukan ya tayarda iska wadda
tayi cilli da Armad cikin dusar ƙanƙara.
Yana tashi yaga jini na tsiyaya daga cikin kansa. Babu
aljani Ji-Inaru babu alamunsa. Kafin Armad ya gane
maike faruwa yaji wata gudumar ta sauka a bayansa. Nan
take yaji wata ƙara mai nuni da cewa bayansa ya ɓalle. Ba
shiri ya zare takobi ya fara kai sara ko'ina da ina amma a
banza, ko sau ɗaya bai samu aljani Ji-Inara ba. Baya
ganinsa ballantana yasan inda yake.
Nan take Armad ya gane haƙiƙanin abinda Babara yake
so ya koya. Inda ya rufe idonsa ya kuma yi ƙoƙarin jin
yanayin Izzar dake tashi daga jikin aljani Ji-Inaru. Armad
baiji komai ba a karo na farko, lamarinda yasa ya ƙara
karɓar wata gudumar.
Koda Armad ya tabbatar aljanin nan baida imani kuma
zai iya karairaya shi indai baiyi da gaske ba, saiya ƙara
zage damtse. A kwana na goma bayan kimanin kowanne
ƙashi na jikinsa ya ɓalle sau kamar biyu sai kwatsam
Armad yaji wani abu mai kama da ruwa sanyi yana
tunkaro shi ta ɓangaren dama. Nan taje yakai sara
ɓangaren. Ai kuwa nan take yaji ya daki ƙarfe, saiga
al'amudin aljani Ji-Inaru ya bayyana. Armad yai ihun
murna tare da ƙara rufe idonsa, yana neman wannan
yana yi. Amma kawai sai ji yayi al'amudin ya ƙara sauka a
kansa.
Amma duk da haka Armad baiyi ƙasa a gwiwa ba, ya tashi
tare da ci gaba da neman wannan yanayi na Izzar aljanin.
A haka dai Armad yai ta fama, wani lokacin yaji wani
lokacin yasha tafka har saida ya gane haƙiƙanin mai ake
nufi da jin yanayin Izza.
A haka saida Armad yai wata uku yana faɗa da wannan
aljani kafin Babara ya dawo. Lokaci lokaci aljanin zai
bayyana ya tausayawa Armad tare da koya masa abu
ɗaya ko biyu akan Izza kafin ya ƙara ɓacewa yaci gaba da
tafkarsa. Ba jimawa Armad ya gano cewa wannan aljani
Izzarsa ce mai wannan yanayi na hunturu.
Ana haka sai Babara ya dawo, ai kuwa abu na farko da
Armad yayi shi ne fara jin yanayin Izzarsa inda yaji ta da
yanayin kaka, gab da saukar damuna.
"Lallai kayi ƙoƙari." Babara ya ce cikin farin ciki. "Na gano
mana hanyar fita, amma lallai saika farkarda fasaharka
zamu iya wannan aiki. Saboda haka yanzu abu na gaba
shi ne farkarda fasaha."
Armad yai murmushi tare da cewa, "muje zuwa."
***
Sanarwa: Zamu fara chapter kullum amma duk chapter
da comments basu kai 30 ba ba lallai nayi post ba washe
gari
*******
Yaku ma'abota karatun littattafan Hausa ga wata dama
ta samu. Wepsite din Hausaebooks
wanda zai ringa kawo maku littatafan hausa a cikin apk na ebook ya kuma baku daman downloading zuwa kan wayoyinku kyauta batare da sisin ku ba Zaku samu
sabbin littafai wanda babu su a kasuwa. Muna muku
barka da zuwa.
Yi hanzari ku ziyacemu
A shafin mu na facebook akan
www.facebook.com/hausaebooks


Nidinne dai Shuraih Usman inkiya
99%
Daga taskar magajin wilbafosMAGAJIN WILBAFOS
Marubuci: Dr Abdullahi Muhammad Ibrahim
Babi na 79: Magajin Wilbafos
Post by: Shuraih Usman
@shuraih 99%
www.facebook.com/hausaebooks
.
Daga:- Taskar Magajin Wilbafos
***
Tuni Babara ya zaunar da Armad a tsakiyar wani hatimi, a
ƙoƙarin farkarda haƙiƙanin fasahar Armad. Armad na
zaune ido a rufe, wasu ɗalasimai na haske suna
kewayashi.
Lokaci yaci gaba da tafiya a haka. Tuni hankalin Armad ya
gushe babu abinda yake gani acikin kansa sai haske. Ana
haka wannan ɗalasimai suka fara cinye ƙasar dake
kewaye da Armad. Ba jimawa sukai wani ƙaton rami mai
kama da rijiya, inda Armad ya rufta ciki. Amma duk da
haka Armad bai buɗe idonsa ba. Daga nan sai kawai
wannan ɗalasimai suka kama da tsawa da walƙiya wanda
suka juye izuwa aradu. Ba jimawa wannan aradu ta fara
cinye jikin Armad.
Armad na zaune ko motsi baiyi ba. Hasalaima tamkar ba
jikinsa ke ƙonewa ba. Ƙafafunsa ne su suka fara cinyewa
izuwa toka, sannan sai gangar jikinsa, kafin daga bisani
hannayensa da wuyansa da kansa. Armad ya ƙone
ƙurmus acikin wannan rijiya amma ko tari baiyi ba.
Shima Babara na zaune a wajen rijiyar bai motsa ba.
Anma duk da haka wannan ɗalasimai masu bada walƙiya
da aradu basu tsagaita ba. Hasalima juyewa sukai izuwa
launin ja, sannan nan take walƙiyar ta fara tsiri tana sama
har saida ta taɓo sararin samaniya. Ba shiri wani baƙin
hadari ya taso mai ɗauke da aradu launin ja. Samaniya ta
fara rugugi tana kaɗawa tamkar za'a saukar da ruwan
azaba. Amma duk da haka Babara bai motsa ba.
Nan take ruwa ya ɓarke tamkar da bakin kwarya. Duk
bayan daƙiƙa biyar sai aradu ta sauka mai ƙarfin gaske.
Ba jimawa wannan ruwa ya fara haɗuwa zafin aradun
dake sauka suka fara narka wannnan dusar ƙanƙara data
cika wannan kurkuku.
Kwana uku cir aka ɗauka ana zabga ruwa kafin dukkan
wannan ƙanƙara ta narke. Wannan kurkuku ta bayyana a
fili. Ashe acikin wannan dusar ƙanƙara manya-manyan
duwatsu ne na wuta wanda aka fafake cikinsu akai gidaje.
Kana ganin wannan gidaje zasu tuna maka da ƙissar
samudawan farko irin wanda akan bayyanasu da cewa
suna ɗumamen safe da zafin rana.
Waɗansu halittu ne sanye fatun namun dawa suka fara
ambaliya daga cikin wannan gidaje na dutse da wani irin
sauri tamkar na aljanun farko. Kafin ƙiftawar ido da
bismillah sama da wannan halittu dubu uku sun bayyana
sun kewaye Babara a inda yake zaune. Ga dukkan alamu
ya tayar dasu daga baccinsu. Fuskokinsu a rufe suke da
fatar farin zaki amma hakan bai hana tsananin ƙiyayya
dake tashi daga cikin idanuwansu bayyana ba. Wata irin
iska mai ɗauke da marmarin yaƙi na fita daga jikinsu.
Sannan suna bada gunji mai amo kai kace samarin
kuraye ne. Sahu-sahu sukai tare da tunkaro Babara a inda
yake zaune, lallai babu ko tantama niyyarsu suyi watanda
da naman Babara. Matsalar ɗaya na bayan ba lalle su
samu ba.
Amma duk da haka Babara bai motsa ba. Idanunsa na
cike da imani da dogaro da fasahar da Armad Wilbafos
zai farkar.
Ba jimawa tokar naman jikin Armad ta fara haɗewa tana
curewa waje ɗaya acikin wannan rijiya wadda tuni ta cika
da ruwa. Ba jimawa wata tsawa ta sauka acikin rijiyar
wadda ta ƙone duk ruwan dake ciki. Babu abinda yai
ragowa acikin wannan rijiya sai tokar Armad.
Ana haka wannan toka ta juye izuwa siffar Armad
Wilbafos. Armad yai wani gunji mai firgitarwa wanda
yasa dukkan wannan halittu jada baya. Wani taku irin na
jaririn aljani ya fara fitowa daga cikin wannan rijiya. Inda
daga bisani sabon saurayi ɗan kimanin shekaru sha tara
ya bayyana daga cikin wannan rijiya, a jikinsa babu
komai sai ɗan bante.
Yana bayyana Babara ya buɗe ido tare da miƙewa ya
kawo gaisuwa. Koda ganin haka sai waɗannan halittu
suka fusata tare da rabuwa izuwa gida uku. Kaso na farko
suka ɗaga hannunsu sama, inda wasu masu, masu ci da
wuta suka bayyana. Kaso na biyu kuwa bakunansu suka
buɗe, inda suka fara yin aman ruwan narkakken dutse
wanda zafinsa zai iya ƙona wuta ita kanta. Kaso na uku
kuwa wani baƙin ruwa ne ya fara ambaliya daga
hannayensu, idan da Armad yana gani zai gane ruwan irin
ruwan da Dordor suke amai ne.
Dukkaninsu sukai ƙaraji tare da sakar wannan hare-hare
izuwa Armad. Babara yai tsalle da niyyar shiga tsakani
amma Armad ya ɗaga masa hannu. Ba shiri Babara yai
gefe. Lallai koda aljanun farko sai sun tsorata da wannan
hari na wannan halittu, wanda ke ɗauke da tsantsar
rashin imani. Domin kuwa idan ka kalli samaniya zaka ga
masu, masu cida wuta sama da dubu, haɗe da guma-
guman ruwan narkakken dutse sama da dubu, tare da
wani baƙin ruwa mai alamun mutuwa. Kuma abu na
farko da zai fara zo maka shi ne waɗannan hare-hare ana
niyyar halaka gari ne dasu, babu wanda zaiyi tunanin wai
mutun ɗaya ake so a halaka.
Armad ko gezau baiyi ba, hasalima ko motsa ɗan-yatsa
baiba. Yana tsaye waɗannan guma-guman azaba suka
saukar masa. Wata ƙara mai firgitarwa ta tashi, sannan
ƙura ta turnuƙe. Lallai ko wanda ke tsaye kimanin nisan
tafiyar shekaru dubu zai iya jin wannan ƙara, kuma zai
iya ganin wannan ƙura.
Babara yai ƙaraji saboda ɓacin rai ya afka cikin wannan
hargitsi domin ceto Armad. Amma ba jimawa yaji wani
irin yanayin Izza mai firgitarwa irin wanda bai taɓa ji ba a
duk tsahon shekarunsa. Ba shiri ya fara jada baya kaɗan
da kaɗan kafin wannan yanayin izza ya ƙara dukansa,
lamarinda yasa ya harɗe tare da faɗuwa a ƙasa. Haki
sarkin duba Babara ya fara, badan komai ba sai dan
saboda ƙarfin izzar da yake ji.
Amma waɗannan halittu basu yi ƙasa a gwiwa ba wajen
ƙara fara shirin wani harin. Sai dai a wannan karan
girman kaba'irar da suke nufin Armad da ita ya ƙaru.
Domin kuwa kowa acikinsu girman harinsa ya ƙaru da
sama da sau uku.
Suna niyyar afkawa Armad sai ƙura ta lafa inda surar
Armad ta futo fili. Sai dai ina, kwata-kwata ba irin Armad
ɗin da aka sani bane. Babu komai a jikinsa face walƙiya.
Amma abin mamakin bawai irin yanayin walƙiyar dake
kewaye Armad bace a lokacin da yake amfanin da
ɗalasimai irinsu Kaban'shisu. Wannan walƙiyar daga cikin
tsoka da jinin Armad take. Hasalima zaka iya cewa naman
jikin Armad ne ya juye baki ɗaya izuwa gundarin walƙiya.
A wannan lokaci Armad ya zare wani mashi wanda ya
nutse acikin ƙirjinsa. Amma babu komai ajikin mashin
daya shafi jini ko fatar ɗan-adam. Lallai a wannan lokaci
zaka iya cewa Armad wilbafos ya zama walƙiya, walƙiya
kuma ta zama shi. Armad ya ɗaga hannusa sama ya dubi
gundarin walƙiyar data haɗa hannunsa. Sannan daga
bisani ya juyarda hannun nasa ya koma izuwa tsoka da
jini. Sannan sauran jikinsa shima ƴa koma yadda yake.
Koda ganin haka sai Babara ya zube a ƙas yana gaisuwa.
"Ina ƙara jaddada mubayi'ata magajin wilbafos."
Abin mamaki sai waɗannan halittu suka cire fatar dake
rufe da fuskarsu inda suka bayyana a matsayin mutane.
Sannan suka zube a ƙas suna gaisuwa tare da mubayi'a.
"BARKA DA ZUWA MAGAJIN WILBAFOS, MAGAJIN SARKI
EYRIYON, MAGAJIN SARKI ALDAIMA. Ka yafe mana rashin
ɗa'ar mu, lallai mun cancanci kisa!!!"
A dai-dai wannan lokaci duk wani wanda yasan sirrin
dake ɗauke cikin jinin MAGAJIN WILBAFOS yasan an
farkar dashi.
***
Sanarwa: Zamu fara chapter kullum amma duk chapter
da comments basu kai 30 ba ba lallai nayi post ba washe
gari
*******
Yaku ma'abota karatun littattafan Hausa ga wata dama
ta samu. Wepsite din Hausaebooks
wanda zai ringa kawo maku littatafan hausa a cikin apk na ebook ya kuma baku daman downloading zuwa kan wayoyinku kyauta batare da sisin ku ba Zaku samu
sabbin littafai wanda babu su a kasuwa. Muna muku
barka da zuwa.
Yi hanzari ku ziyacemu
A shafin mu na facebook akan
www.facebook.com/hausaebooks


Nidinne dai Shuraih Usman inkiya
99%
Daga taskar magajin wilbafosMAGAJIN WILBAFOS
Marubuci: Dr Abdullahi Muhammad Ibrahim
Babi na 81: Kwangila
Post by: Shuraih Usman
@shuraih 99%
www.facebook.com/hausaebooks
.
Daga:- Taskar Magajin Wilbafos
**
Haka Lamarudu Wilbafos ya kai Armad cikin wani shinge
wanda aka kewaye shi da manya-manyan jajayen
duwatsu. Daga saman duwatsun kuma ruwa ne ke
gudana zuwa ƙasa tayadda suka samarda wata ƴar
ƙasaitacciyar ƙorama a ƙasa. Lamarinda yasa wajen yake
bada wani irin sanyi mai inganci. Abu na farko daya fara
zuwa ran Armad shi ne wai shin wajen horo aka kawoshi
ko kuma wajen shaƙatawa. Amma kafin ya tambaya sai
Lamarudu ya ɗora hannunsa akan wani dutse inda wasu
hatimai suka bayyana suka kewaye dutsen. Nan take wata
ƙofa ta buɗe a wajen.
Lamarudu ya shige ciki sannan su Armad suka bishi a
baya. Suna shiga wani ƙasurgumin daji mai kama da
kasuwar muridan aljanu ya bayyana a gabansu. Babu
komai sai manya-mayan bishiyun kuka wanda kowacce
ɗaya tafi tsayin zira'i ɗari. Abin mamaki shi ne wasu
manyan ƙayoyi dake kewaye da rassan wannan bishiyu a
matsayin ganyayyaki.
Lamarudu ya ce, "ga wajen koyar horo. Ga kuma
ɗalasimin dazai fitar daku a yayinda kuka gama." Ya miƙa
musu wata takarda mai ɗauke da hatimi. Har ya juya zai
fita saiya waiwayo ya ce, "dajin nan an rabashi izuwa gida
uku. Dajin kuma acike yake taf da jinsin Dordor dana
aljanu masu cin naman biladama. Indai har mutun baya
iya jin yanayin-izza to lallai bazai iya rayuwa aciki ba.
"Kaso na farko na dajin yana ɗauke da abubuwanda
izzarsu take tsakanin dubu ɗaya da dubu biyar. Kaso na
biyu suna ɗauke da izza tsakanin dubu biyar da dubu
goma. Amma kaso na uku duk abinda ka gani aciki izzarsa
ta haura dubu goma. Lallai duk hatsabibancinmu bama
shiga yanki na uku. A fito lafiya." Ya juya ya fice ya bar
Armad da Babara a wajen.
Bayan ya fita Babara ya tambayi Armad, "kaga irin kallon
da wannan mutane ke yima?"
Armad ya amsa da, "eh."
Babara ya ɗanyi shiru naɗan taƙi kamar baya so ya faɗa
amma daga ƙarshe ya ce, "Sunyi imani dakai kuma suna
yi maka kallon zaka cece su. Hakan shi ne ma dalilin da
yasa suka nuna maka waccan tsohuwar daula. Kada ka
manta iyayensu sunyi wa kakanka sarki Eyriyon bauta,
wanda hakan ne yasa aka ƙullesu. Cetonsu da zakai
kamar ramawa kura aniyarta ne. Kuma idan ka yadda ka
shiga cikin wannan daula zaka samu fasahohi da bayi na
aljanu wanda zasu taimake ka a hanyarka ta zama
cikakken sarki Wilbafos. Nidai ina ganin ya kamata ka
shiga wannan tsohuwar daula."
Armad dama yasan tuntuni Babara bai amince da rashin
shigarsa wannan tsohuwar daula ba, saboda haka tuni ya
tanadi amsa. "Duk na yadda da abinda kake faɗa amma
kai sani cewa bazan iya sauka daga manufata ba. Kuma
lallai indai ba ganin mahaifiyata ta samu lafiya nayi ba
bazan iya tsayawa acikin wannna kurkuku ba. Saboda
haka inaga mu fara horo kurum."
Haka dai Babara ya haƙura dole. Sannan ya zana wasu
hatimai guda uku a kewaye da Armad kafin ya bawa
Armad umarnin ya zauna a tsakiya, sannan daga bisani ya
fara karanta wasu ɗalasimai.
Can bayan sa'a ɗaya ana cikin wannan hali sai fuskar
Babara ta canja, inda nan take ya daina karanta
ɗalasiman ya garzayo gaban Armad inda ya ɗebi kaɗan
daga jininsa ya zuba acikin wata kwalba mai ɗauke tsumi.
Armad dai ya ji wani abu amma yai shiru baice komai ba
ya ƙurawa Babara ido.
Can Babara ya kalli Armad cikin alhini yana cewa, "dama
nayi tunanin haka, amma ina ta addu'a ya zama hakan
bata faru ba."
Armad yai zumbur ya ce, "ban gane ba. Mai kake nufi da
dama kayi tunanin haka?"
Babara ya fara bayani, "labarin daka bani na ɓacewar
Miyurarka bawai Miyurarce kaɗai ta ɓace ba, harda wani
ɓangare na ruhinka. A sakamakon haka bazaka iya amfani
da idanuwanka ba har sai ka nemo wannan ɓari na
ruhinka."
Armad ya zare ido. "Eh?!"
Babara ya ce, "bari mu gani idan zan iya gano inda ɓarin
ruhin naka yake."
Nan take ya ƙara ɗiban wani jinin daga hannun Armad ya
kuma yaryaɗar dashi akan ƙasa, inda ya zana wasu
hatumai masu rikitarwa akansa. Can daga bisani jinin na
Armad ya fara yin haske, kafin daga bisani ya kama da
wuta. Nan take sukai tsalle gefe, amma kafin suyi wani
abu tuni jinin ya ƙone ƙurmus.
Babara ya dubi Armad ya ce, "ruhinka yana katange
acikin wata sihirtacciyar ƙasa amma saboda ƙasar na
kewaye da Tsari baza a iya gane wacce bace."
Armad yama rasa mai zaice, domin kaf maganar a baibai
yake jinta. Wai ruhinsa ya ɓalle? Bayan kuma gashi nan
da rai da lafiya. A iya saninsa ma wannan ba abu bane
mai yiwuwa ba.
Yana cikin tunani yaji muryar Babara, "nasan mai kake
tunani, kuma kayi sani nima wannan shi ne karo na farko
da naga mutun ruhinsa ya rabe kuma ya ci gaba da zama
da rai. Amma dai maganar tana nan cewa bazaka iya yin
amfani da idonka ba har sai ka nemo ɓangaren ruhinka."
Armad ya kalli zoben dake ɗan yatsansa inda
mahaifiyarsa ke ajiye. Can bayan tsahon lokaci Armad ya
yanke shawara, inda ya numfasa ya ce, "idan za'a fara
bada tarihi na, za'ace na fara ne daga nemo ɓangaren
ruhina daya ɓalle. Saboda haka inaga zaman mu a
wannan kurkuku yazo ƙarshe, lallai inada mahaifiyata a
gabana bazan tsaya neman suna acikin wannan kurkuku
ba."
Babara ya rusunar dakai alamun girmamawa sannna ya
ce, "ya shugaba na akwai wata hanya banda idanuwanka
da zaka iya bawa mahaifiyarka izza da ban gaya maka ba."
Armad najin haka yai zumbur cikin murna ya ce, "ko?
Kamar ya fa?"
"Kamar yadda ka sani kowanne ɗan adam yana samun
ƙayyadaddun shekarun izza lokacin daya farkarda izzarsa,
kuma wannan adadi a ƙa'ida baya taɓa canjawa. Koda
kaima dalilin da yasa naka suka canja daga hamsin da
ɗaya zuwa dubu ɗaya dan kawai baka farkarda izzarka ta
haƙiƙa bane da farko.
"Amma akwai wasu hanyoyi guda biyu kacal wanda ake
iya ƙara yawan izza. Hanya ta farko na riga na gaya maka
ita. Ita ce ta amfani da sirrin dake cikin idanun ƴaƴan
Wilbafos. Hanya ta biyu wadda ban gaya maka ba ita ce
hanyarda ake kira da KWANGILA!!"
---
Mai kuke tunani ake nufi da fasahar KWANGILA?
**
Note
-------
Fasaha/Technique
Farkarda fasaha/Awakening
Sido-Urúrú/Pseudo-Ururu
Hatimi/Ancient runes
Dalasimai/spells
etcMAGAJIN WILBAFOS
Marubuci: Dr Abdullahi Muhammad Ibrahim
Babi na 83: Bango
Post by: Shuraih Usman
@shuraih 99%
www.facebook.com/hausaebooks
.
Daga:- Taskar Magajin Wilbafos
____
Duk da gudun dokinsa Ubbaru saida Armad yai kwanaki
goma sha ɗaya yana tafiya sannan ya fara hango Bangon
arewa. Gangar ruwa iyakacin ganinka ta shafe kudu da
yamma gabas da arewa, tana ta kwaranya izuwa ƙasa
amma babu ko halitta ɗaya a samanta. Koda Armad ya
hangi wannan sai yaja linzami ya tsaya, inda ya buɗe
zoben sihiri da Nostaljiya ta bashi domin ya futo da
mahaifiyarsa.
Babara ya gaya masa duk bayan kwana biyu akwai wani
tsumi da zai ringa bata har zuwa lokacinda zai samu
wannan shekarun Izza ya bata. Shi dai wannan tsumi shi
ne abinda Babara ya ringa bata tsahon shekarunda
Armad yayi bayanan kuma har ya dawo ya same ta cikin
ƙoshin lafiya. A lissafin Babara mahaifiyar Armad tana
buƙatar aƙalla shekarun izza dubu goma kafin ta warke.
Wannan shekaru ba wani abu bane a wajen sarakunan
jinzidal masu fasahar kwangila, saboda haka Armad ya
gama yanke shawara kai tsaye wajen Nostaljiya zaije.
Kuma tunda a hannunsa akwai wani ɗalasimi daya karɓa
daga wajen Babara wanda zai iya gano masa inda ruhinsa
yake zai iya yin aiki biyu a lokaci ɗaya, yana neman
ruhinsa kuma yana neman Nostaljiya.
Amma koda wannnan tunani ya gilmawa Armad a rai
saiya tuno cewa ai bama abu biyu ba, lallai abu uku zaiyi
a lokaci ɗaya. Domin kuwa akwai alƙawari daya ɗauka na
kawarda cinikin bayi a ban ƙasa, wanda kuma bai manta
dashi ba. Koda tunanin haka sai Armad ya buɗe ƙofar
wannan zobe ya shiga inda ya samu waje ya rubuta sha
huɗu ga wata tara shekarar 1855 Bayan Amri. Wato dai a
wannan rana ce Armad ya fara shirinsa na rusa rukunin
Jinzidal.
Bayan ya gama kallon wannnan kwanan wata saiya juya
izuwa ɗakin daya ajiye mahaifyarsa, inda ya shiga ya
same ta a kwance, idanunta a rufe kamar tana bacci.
Mahaifiyar Armad tana bada yanayin kwarjini matuƙa
wanda saboda haka ba kowanne ma'aboci izza bane zai
iya tunkararta ba a hakan da take a sume. Gashin kanta
na nan baƙi, kuma kamar yadda wannnan cuta ta izza
take a har kullum alamar kawai shi ne mutun zai zamanto
a sume, amma banda haka babu wani abu dazai nuna
rashin lafiya kamar irinsu tari ko zazzaɓi.
Koda zama a gefenta sai kawai wani hawaye ya fito daga
idonsa, babu abinda yake tunawa sai lokutan da yana
yaro da kuma lokaci na ƙarshe daya ganta da lafiya.
Tsahon lokaci a haka kafin ya buɗe bakinta ya ɗisa mata
wannan tsumi dake cikin wata ƴar kwalba. Sannan ya
taso ya futo idanunsa cike da kwalla. Lallai akwai
abubuwa da dama da yake so ya tambayeta idan ta farka.
Saboda haka babu wani abu dazai tsaya a gabansa. Har
Armad yaje bakin ƙofar wannan zobe zai fita sai ya tsaya
ya juyo inda ya durƙusa yayi alƙawari, ƙololuwar
alƙawarinsa cewa a wannan fita kozai rasa ransa bazai
dawo ba sai mahaifiyarsa ta warke.
Yana fitowa ya rufe ƙofar wannan zobe sannan bayan
yaci abinci ya mayarda Ubbaru cikin zobensa ya kuma
nufi wannnan bango a ƙafa.
Yana isa gaban wannan bango wata izza irin wadda bai
taɓa jintaba ta dakeshi tayi cilli dashi gefe. Yana faɗuwa
yaga jikinsa ya fara narkewa, fatarsa tana ɓanɓarewa.
Nan take Armad yai sauri ya juyarda jikinsa izuwa
walƙiya. Wanda hakan ne ya cetoshi tunda hatta wuta
bata isa ta ƙona walƙiya ba.
Nan take Armad yai murmushi tare da cire zoben dake
hannunsa ya cilla a baki sannan ya ɗaga hannunsa sama
ya kirawo ɗaya daga cikin ɗalasimansa daya daɗe baiyi
amfani dasu ba wato Kaban'shisu. Idan mai karatu bai
mantaba wannan ɗalasimi ana iya amfani dashi ayi tafiya
acikin lokaci daga wani waje zuwa wani. Matsalarsa kawai
ita ce sai ɗaya kacal ake iya amfani dashi a shekara.
Tuntuni dai Armad yayi tunanin amfani da wannan
ɗalasimi ya fice daga cikin wannan kurkuku to amma bai
gama abinda ya shigo dashi ba, sannnan kuma baya son
yabar Babara anan.
Nan take ya ƙaddamar da wannan ɗalasimi, inda ya ɓace
daga inda yake. To amma a wannan lokaci maimakon ya
tsinci kansa a bayan wannan bango sai kawai ya ganshi
acikin tsakiyar bangon, kewaye dashi wani ruwa ne mai
tsananin danƙo. Abu na gaba daya biyo baya wasu
abubuwa ne manya-manya guda biyu suka bayyana a
gaban idon Armad.
Ɗaya daga cikinsu yana kama da wata daren goma sha
uku, ɗaya kuma yana kama da rana saidai dukkaninsu
baƙaƙe ne wuluk. Waɗannan abubuwa suka ƙura masa
ido tamkar wasu idanun mayunwaciyar kurar da taga
abinci. Nan take Armad yaji ya fara rawar ɗari. A lokacin
ne ya fuskanci cewa gaba ki ɗaya jikinsa ya narke babu
abinda ya rage face ƙoƙon kansa. Kuma wai a hakan ma
dan ya riga ya juyarda jikinsa izuwa walƙiya ne, lallai da
tuni ya tsinci kansa a lahira.
A wannan lokaci ya fuskanci abubuwa guda biyu. Na
farko dai bawai a waje ɗaya yake tsaye ba, hasalima
mugun gudu yake acikin wannnan bangon saboda
ɗalasiminsa na Kaban'shisu. Wanda hakan ya nuna masa
cewa saɓanin fahimtarsa da ɗalasimin bawai ɓacewa
yake yiba a lokacin da yayi amfani dashi, kawai dai
saboda tsananin sauri ne kawai yake ganin kamar ɓacewa
yayi.
Abu na biyu daya fuskanta shi ne wannnan abubuwa
guda biyu dake kama da rana da wata ba wasu abubuwa
bane illa idanuwa guda biyu na Ururu. Kuma hatta rawar
ɗarin da yake ji daga su ne.
A take Armad ya gane cewa lallai koda ya taho da Babara
lallai bazai iya wucewa dashi ba. Domin ba daban jikinsa
na walƙiya ba da tuni ya mutu aƙalla sau ɗari zuwa
wannan lokaci. Sannan kuma ya gano cewa yayi dabara
daya saka zobensa acikin bakinsa domin da tuni ya narke.
Ana cikin haka wannnan idanuwa guda biyu suka fara
haske suna fitarda wani yanayi mai firgitarwa. Ba shiri
Armad yaji tamkar ana caccaka masa allurai acikin kansa.
Abin mamaki sai kawai ya ganshi ya tsinci kansa a tsakiyar
filin yaƙi, kewaye dashi sarakunan Ashura ne guda goma.
Kowanne acikinsu yana riƙe da baƙar takobi. Kafin
Armad yai wani motsi su goma sunyi tafiya acikin lokaci
sun cake masa wannnan takubba acikin ƙirjinsa. Ko
motsi baiyi ba ya faɗi matacce. Abin mamaki a gaske ma
a wannna lokaci

Please Login or Register in order to submit comment