Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

shaƙa yana da yawa, dan bai tashi ba saida
rana ta kusa zuwa tsakiya a samaniya.
Yana farkawa abinda ya fara Arba dashi sune wasu
kuyangi guda uku dukkansu wankan tarwaɗa, suna jera
masa kayan abinci.
Yana tashi suka zube a ƙasa gami da cewa, ''barka da
asuba, shugaba Armad, da fatan ka tashi lafiya.''
Cikin tsananin zafin nama Armad ya wartsake gami da
kyaran murya da kuma ajiyar zuciya, ya ce, ''shugaba!!??
''Waye kuma shugaba?'' ya tambaya cikin mamaki.
Nan take suka ɗago kai cikin ladabi suna niyar amsa
masa, amma a wannan lokacin ne waɗannan samari
guda biyu da Armad ya gani suka nemi izinin shigowa
ɗakin.
Bayan sun shigo sun gaisa, sun kuma nunnunawa Armad
sauran sassan gidan da kuma duk abinda yake sai suma
suka fice. Amma har suka tafi babu wanda ya bawa
Armad amsar tambayarsa da yayi.
Saboda haka kawai sai ya ƙara shiga cikin shubuha akan
wai taƙamaimai maike faruwa.
Bayan ya gama kimtsawa saiya fito ƴar harabar ɗakin da
ya kwana aciki domin ya hangi gari.
yana tsaye iskar dake kaɗawa na dukan jikinsa, jan
ƙyallen daya ɗaure kansa yana kaɗawa, nan take baisan
mai yasa ba sai kawai yaji ya fara tunanin gida da
mahaifiyarsa.
Nan fa ya nutsa acikin tunaninsa kan kace meye wannan
tuni tsananin begen gida yasa rabin sa'a ta wuce ba tare
da ya sani ba.
Yana cikin wannan hali ne yaji magana a bayansa,
''Armad, ka kwana ƙalau!''

Yana waiwayawa yayi arba da Nusi tana masa murnushi.
Ƙarasowarta keda wuya ta tafa hannu, waɗannan
kuyangi guda biyu suka bayyana da kujeru guda biyu,
wanda suka saka musu domin su zauna.
Bayan sun zauna, sai ta dube gami da yin murmushi kana
tace, ''ya kaji iskar garin namu, da daɗi ko kuwa?''
Armad murmushi kawai yayi gami da godiya ta karamcin
da take nuna masa.
Sun ɗan ɗauki lokaci a haka suna maganganu na yau da
kullum, kafin daga bisani ta numfasa ta fara bayani,
''Kasan kowanne ɗan adam da yadda aka rubuta masa
rayuwa.
''Misali, lokacin dana fara tunanin gayyatarka ka biyo ni
wannan gari, abinda ke raina shi ne, na samar maka
muhalli mai kyau da kuma duk wasu abubuwa da kake
buƙata, sannan kuma na nemar maka babbar
makarantar koyon Izza ta wannan gari.
''Amma kaga saboda abu ɗaya daya faru, wanda ban taɓa
kawowa ba, hakan ba zata yiwu ba.''
Tana faɗar haka ta ɗan ɗaga kujerarta gami da saita ta ta
fuskance shi, ta yadda take kalonsa ido cikin ido.
Kallo ɗaya zakai mata kasan cewa a wannan lokaci babu
alamun wasa acikin zuciyarta, kuma duk abinda zata faɗa
zata faɗe shi ne tamkar tana rantsuwa da abin imaninta.
''Armad kayi sani cewa wancan tsari dana gaya maka shi
ne na farko acikin guda uku!
''Amma tunda yanzu bazai yiwuba abinda zaisa mu zaɓi
tsari na gaba, duk ya ta'allaƙa da sakamakon daka fito
mana dashi idan ka shiga Non-toch-teka.
''Kayi sani cewa a wannan gari, babu wani zancen ƙabila
ko kuma ƙungiya, abinda kawai yake nuna matsayinka shi
ne, acikin manyan matakan Izza, a ina kake.
Ta ja dogon nunfashi, sannan taci gaba da cewa, "a yau
ina ganin ka cancanci na gaya maka sirrin mu, sirrin duk
wani ɗan ƙabilar Djinn, wanda kuma shi ne manufar duk
wani ɗan wannan ƙabilar!
"Kai sani cewa, mutanen da suka san abinda zan gaya
maka a yanzu, basu da yawa a duk faɗin duniya. Saboda
haka abinda zaka ji, ka tabbata lallai baza ka taɓa gayawa
wani mahaluƙi ba a ban ƙasa.
"Asalinmu mu ƴan ƙabilar Djinn, mun fito ne daga ɗaya
daga cikin garuruwan ƙarƙashin ƙasa, wanda ake cewa
Shaníza.
"Mun kasance daga cikin mafiya girman ƙabilu a duk
faɗin duniyar ƙasa bakwai, harma muna gogayya da
ma'abota Ururu!
"Babu inda ba'asan sunanmu ba, kuma babu inda ƙarfin
mulkin mu baije ba! Kwatsam watarana, sai waɗansu
mutane suka bayyana a shashin Ikwatora, wato inda aka
fi sani da 'Danja zon!'
"Du du du, adadinsu ɗari ne kacal, duk da wasu suna
cewa ɗari da ɗaya ne, wasu kuma da biyu. Amma su

kaɗai sai suka addabi dukkan wani mahaluƙi, a doron
ƙasa cikin kwanaki bakwai kacal!
"Hatta ma'abota Ururu, babu yadda suka iya dasu, sai
kawai komawa da baya da sukai, suka shata musu iyaka
da doron ƙasa ta biyu da kuma ta farko. Amma haka suka
rabu dasu.
"Kuma babban abin al'ajabin shi ne, babu wanda yasan
komai akansu, illa abu ɗaya kacal, wato aniyarsu, wadda
aka ce wai suna kan hanyar su ne ta Tafiyar Alwashi!
"Ba jimawa, sai jama'a suka fara ce musu, MatafiyanAlwashi.
"To ana cikin wannan rikici kwatsam, sai aka nemi
waɗannan mutane aka rasa, ko sama ko ƙasa. Har tsahon
kwana uku, babu su babu labarinsu.
"Kwatsam a rana ta ukun, sai suka suka bayyana a ƙofar
garinmu Shaníza.
"Kafin mu farga sun shige cikin garin, inda suka ƙullo
ƙofar ta ciki. Tun daga wannan rana ta litinin, shekarar
683 Bayan Amri (A.A), babu wani mahaluƙi daya ƙara
shiga ko kuma fita daga wannan gari, har yau ɗinnan da
nake maka wannan zance."
Tai shiru, gami da duban Armad, kafin daga bisani taci
gaba da cewa, "nasan mai kake tunani!
"Cewa duk tsahon shekarun nan, idan babu wanda ya
ƙara shiga ko kuma fita daga cikin garin, to ta ina muka
fito!
"Lallai kam wannan abin tambaya ne, domin kuwa kaɗai
daga cikin iyayen mu da kakannin mu wanda suka fito
daga cikin garin, kafin shigar waɗannan mutane, su su
kaɗai ne suke yawo aban ƙasa yanzu.
"Kuma sune suka hayayyafa, har aka samemu. To amma
da yake gaba ki ɗayan yawansu, baifi cikin cokali ba, har
yanzu bamu fi a irga mu ba.
"Kuma dukkanin a inda muke, muna gane kanmu,
sannan kuma ba muda wani buri, banda muga cewa
watarana mun koma cikin garinmu, mun fitar da
waɗannan mutane, kuma mun tseratarda miliyoyin
mutanen mu dake ciki.
"Sai kuma wata tambayar da zaka iya ƙarayi, cewa idan
dai har al'amarin waɗannan mutane ya baza duniya, to
ya akai yanzu babu wanda ya sani, bayan dududu ba'afi
shekara dubu ɗaya da ɗari biyar da wucewa ba.
"Lallai wannan tambaya ce mai kyau, kuma amsar ta faru
ne shekaru biyu bayan shigar waɗannan mutane cikin
garin mu;
"Kwatsam sai aka wayi gari Sarki Dul'Ururu, sarki bisa
doron ƙasa ta biyu, ya haɗo runduna ta ma'abota Ururu,
irin wadda ba'a taɓa gani ba, ya kuma bayyana a bakin
wannan gari namu.
"Babu wanda yasan mai ya faru, illa cewa anyi sama da
kwana ɗari ana kwabza yaƙi, amma daga ƙarshe,
katangar garin nan bata faɗi ba, kuma shi ɗin, bai samu

damar shiga garin ba. Haka ya juya ya koma izuwa
ƙasarsa!
"Muma iyayenmu da kakannin mu, sunyu iya ƙokarinsu
domin suga sun shiga cikin garin, amma ina. Duk da
kuwa acikin su, akwai wazirin sarkin mu, wanda yasan
duk wasu ɓarauniyoyin hanyoyi da ake shiga.
"Kai daga ƙarshe dai haka suka haƙura.
"To amma abin bai tsaya anan ba, kwatsam bayan ƴan
watanni, ba sai aka ji, sanarwa daga Dul'Ururu ba, cewa
duk wani ɗan asalun garin nan, ya zama mai laifi, sabida
haka da an ganmu a kama mu.
"Sannan kuma acikin sanarwar, aka haramta ƙara
ambatar sunan Tafiyar Alwashi, Matafiyan Alwashi, kai
dama duk wani abu daya shafesu. Duk wanda ya karya
dokar hukuncin kisa.
"A haka aka ringa kashe mutanen mu, har takai saida
muka daina amfanu da sunan mu kwata-kwata. Kuma a
haka dukkan wannan labari ya mutu. Labarin dani da
ragowar mutanenmu , baza mu taɓa mantawa ba.
"Amma kai sani cewa bamu haƙura ba, kuma haka ta
ƙarƙashin ƙasa mukai ta bin diddigin dalilin da yasa
Ururu suka shiga al'amarin.
"Bayan sama da shekaru dubu muna bincike, muka gano
cewa, Ururu sun sami tabbashi daga wata majiya da
bamu sani ba, cewa waɗannan mutane suna da alaƙa da
Tirifil-fakta, kuma wannan shi ne dalilin da yasa suka
shiga faɗan. Harma kuma suke son a rufe zancen!
"Toh, Armad Wilbafos, wannan shi ne labari ne! Da fatan
zaka riƙe shi har iya ƙarshen numfashin ka."
Armad yaja dogon numfashi, gami da yin ajiyar zuciya,
yana kallonta cikin mamakin wannan labari nata.
Musamman duba ga cewa, a karon farko, ya sami wani
abu mai alaƙa da abin da yake nema, wato Tirifil-fakta!
Tunda fari, bai san mai yasa ba, amma tunda dadewa
idan ya kalleta abinda yake ji acikin ransa ba komai bane
ba illa ƴan uwan taka, saboda haka daya ga irin kallon da
take masa, sai kawai zuciyarsa ta cika da tunanin mai yasa
take gaya masa duk wannan sirrikan, shim bata tunanin
ya fallasata?
''Kuma wani abu da kake da buƙatar ka sani da wuri shi
ne," taci gaba da bayani, kamar bata fuskanci kallon da
yake mata ba, "wannan haske da kaga ya tashi sama
kuma daga baya ya fara tattarewa a wajen ƙofar gari,
idan ya gama haɗuwa kaf, shima sifar mutun zai bayar,
wanda kuma ba kowa zai zamo ba face kai!!
''A halin yanzu duk da binciken da jama'a keyi zaiyi musu
wuya su gano ka, amma daga lokacinda aka ce wancan
mutun-mutumi ya gama bayyana, kallo ɗaya kacal ya isa
kowa ya gane ka indai ya taɓa ganinka.
''Mafi tsayin lokaci da yazo a tarihi wanda wannan
mutun-mutumi da ake cewa Al'yaya, ya ɗauka kafin ya
gama haɗewa shi ne wata uku!

''Mafi ƙanƙanta kuma kwana tara!
Ta ɗanyi shiru kamar tana tunani, kafin daga bisani ta
girgiza kai, sannan ta ci gaba da cewa, ''ya wajaba akan ka
kayi azama ka maida hankali a Non-toch-teka da zaka
shiga nan da ƴan kwanaki masu zuwa, domin idan son
samu ne kafin mutun-mutuminka ya gama haɗuwa
yadda mutane zasu iya ganeka ya zamanto ka fice daga
cikin garin nan.
''Domin babbar matsalar ka a yanzu bawai masu
farautarka a matsayin Magajin Wuobafos bace, babbar
matsalarka ita ce mahaifin gimbiya ZAHRA Sisiyu(Nostalgi
ya) daka labarta min kun haɗu a baya, wato Sarki
BIHANZIN wanda akafi sani da Shugaba Bihanzin mai
DAUWAMAMMEN SARA!!!
"Babban sarki mai kula da harkar cinikin bayi a wannan
doron ƙasa, mutun na farko daya fara mallakar Alyaya
mai takobi a garin khan. A dukkan tarihin duniya ba'a
taɓa samun wanda ya kaishi ƙarfin saran takobi ba. Kuma
indai yace saiya halaka mutun tofa lallai ƙarshensa yazo.
"Saboda wani dalili da ba'a sani ba, duk wanda ya taɓa
mallakar mutun-mutumin daka samu a ƙofar wannan
gari, saida Bihanzin ya hallaka shi. Kayi sani cewa a halin
yanzu, a dukkan doron ƙasa bakwai, babu wani mahaluƙi
da baya tsoron kaifin taƙobin shugaba Bihanzin. Hasalima
akwai dalili na musamman da yasa ake kiranta da suna
DAUWAMAMMEN SARA.
"Kai sani cewa bani da ƙarfin da zan iya kareka daga
takobin Bihanzin kuma lallai kaima baza ka iya tsayawa a
gaban Dauwamammen sara ba. Domin kuwa ina so na
labarta maka cewa da DAUWAMAMMEN SARA aka kashe
Magajin wilbafos na uku."
Nidinne dai Shuraih Usman inkiya
99%
Daga taskar magajin wilbafos
MAGAJIN WILBAFOS
Marubuci: Dr Abdullahi Muhammad Ibrahim
Babi na 24: Dauwamammen Sara
Post by: Shuraih Usman
@shuraih 99%
www.facebook.com/hausaebooks
.
Daga:- Taskar Magajin Wilbafos
Acikin wannan haraba Armad na zaune suna tattaunawa
da Nusi inda take zayyana masa dukkan shirinta da kuma
sharrin da yake tunkaro shi.
Bayan ta ƙara kurɓar lemon dake gabanta ta kuma
tambayi Armad mai yasa baya shan nasa, amma
maimakon ya bata amsa, wata kalma ɗaya ce kawai ta
fito daga bakinsa, ''Bihanzin!''
Nusi ta girgiza kai, sannan tayi murmushi wanda kana

gani kasan akwai firgici acikinsa, gami da cewa, ''Zanso
matuƙa nace maka baka cikin wani sharri to amma abin
bahaka yake ba. Domin kuwa kasan cewa......."
Armad ne ya ɗaga mata hannu tare da girgiza kai alamun
hankalinsa har yanzu a kwance yake, "Kada kiji tsoro!
Lallai bazan daina numfashi ba saina cika burin
mahaifiyata na nemo Tarifil Fakta.
"Amma ni yanzu ma babban abin da nake so naji shi ne
cinikin bayinnan. Shin menene asalin cinikin bayin nan
kuma mai yasa babu wanda zai buɗe baki a ɗuk cikin
sarakunan duniyar ƙasa bakwai ya ce adaina. Domin ni a
gani na zalunci ne kawai da ƙara ƙarawa mai ƙarfi ƙarfi
da kuma danne mara ƙarfi. Amma ke meye ra'ayinki
akai?" Ga dukkan alamu wannan al'amari na cinikin bayi
da ake yana matuƙar ciwa Armad tuwo a kwarya, kuma
ya daɗe yana damunsa.
Nusi ta girgiza kai tare da mummunar ajiyar zuciya,
sannan a wani yanayi mai ban tsoro gumi ya fara keto
mata tamkar wadda aka kunnawa wuta.
Ta tashi daga kan kujerarta sannan cikin sauri da tuntuɓe
ta nufi bakin ƙatuwar tagar dake ɗakin da suke ciki. Tana
isa ta leƙa ta fara dube-dube zuciyarta tana dukan uku
uku. Koda ta tabbatar babu kowa a wajen tagar saita
rufota cikin sauri, sannan saita ƙara juyowa tana gudu ta
isa bakin ƙofar ɗakin tana zuwa ta leƙa sannan kuma ta
rufeta. Lamarinda yasa nan take ɗakin ya rufe dunɗum
da duhu.
Armad bakinsa a buɗe mamaki ya cika zuciyarsa akan
meke faruwa, kuma meye dalilin da yasa kawai tana
zaune a nutse kwatsam ta rikice. Mamaki yasa ko magana
ya kasa.
Wata ƴar fitilar aci bal-bal ce a hannun Nusi wadda ta iya
haskaka ɗan iyakacin tsakiyar ɗakin kaɗai inda suke
zaune.
To sai a lokacin da Nusi ta zauna sannan Armad ya samu
ya iya yin magana, "wai meke faruwa ne? Lafiya?"
Nusi ta ja kujerarta inda ta matsa kusa dashi sannan ta
fara magana ƙasa-ƙasa, "kana so ka faɗi abinda za'a
hallaka dukkan miliyoyin alummar ƙasar nan ne. Baka da
masaniyar cewa iska zata iya ɗaukan maganarka ta kaita
kunnen ma'abota Ururu.
"Baka da masaniyar cewa wasu daga cikin mabiya ɗarigar
Ururu zasu iya jinka kuma su isarda da labarin abinda ka
faɗa.
"Baka da masaniyar cewa Shísu Ururu yana kan wannan
doron ƙasa. Lallai kada ka ƙara faɗar wata mummunar
magana akan harkar cinikin bayi. Idan dai baso kake a
wayi an shafe garin Khan daga ban ƙasa."
Tunda ta fara magana bata shaƙi numfashi ba, saboda
haka tana zuwa nan a zancenta dole ta tsaya ta fara haki
tana ƙoƙarin kama iska. Amma duk da haka bata dawo
hayyacinta ba sai bayan sama da daƙiƙa ashirin.

"Armad Wilbafos bawai kai ba, a'a sauran mutane zaka
duba. Domin kuwa Ururu babu ruwansu da yara ko mata
ko tsofaffi. Saboda hakaina roƙonka, indai zaka faɗi wata
magana akan ɓatanci ga harkar cinikin bayi toka bari
harsai kakai matakin Izzar da zaka iya kare mutane daga
tsananin ƙarfin mulkin da mayaƙan azaba na Ururu keda
shi."
Idanunta kafe akansa, babu abimda take so taji inba
amince warsa ba.
"Amma kinsan wani abin mamaki, sak irin wannan
magana da kika gayamin ita kakana Zaikid ya gayamin."
Maimakon ya bata amsa saiya canja akalar zancen.
" 'kada ka yaƙi cinikin bayi idan baka da ƙarfin da zaka iya
kare mutanen ka daga abinda zai biyo baya.' haka yake
gayamin a duk lokacin da zancen cinikin bayi ya tashi."
Armad yai shiru yana kallon ƙasa, a yayinda ita kuma
Nusi take kallonsa.
Lallai ya daɗe al'amarin cinikin bayi yana ci masa tuwo a
kwarya. To amma ga dukkan alamu babu abinda zai iya a
wannan lokaci.
"A shekara ta ɗari bayan saukar da mutane zuwa ƙasashe
shida na ƙasa, su kuma Ururu suka gaje ƙasa ta farko,
wato shekaru dubu ɗaya kenan da ɗari huɗu. Kaka na ya
labarta min cewa harkar cinikin bayi ita ce Rukuni na
farko da Ururu suka fara wanzarwa a dukkan doron ƙasa
shidanan." Nan take Armad ya shiga bada labarin dukkan
abinda ya sani akan harkar cinikin bayi tun daga asalinta,
da zummar ko zaiji wani abu da bai sani ba daga Nusi.
Hasken fitilar aci bal-bal yana tashi inda yake haskake jan
kyallen dake ɗaure a gaban goshinsa yana kaɗawa akan
iska.
"Farko da Ururu suka bayyana suma suna cikin waɗanda
suke shiga cikin gasar cinikin bayin. A wannan lokaci ta
fara ne da wata gasa mai suna Jinzi, wadda acikinta
kowacce ƙabila babba da ƙarama zasu kawo wani adadi
na bayi a ƙarshen kowacce shekara, waɗanda za'a fafata
akansu duk wanda yaci nasara daga ƙarshe, to shi za'a
bawa kyautar dukkanin waɗannan bayi da kowacce
ƙabila suka tara.
"Saboda haka wannan ƙabila da taci nasara su zasu juya
akalar kasuwar bayi a wannan shekara.
"A haka wannan gasa ta Jinzi ta fara kafin daga bisani a
maida sunanta Jinzidal bayanda Ururu suka koma doron
ƙasa ta farko.
"A tsahon sama da shekaru dubu da akai ana yin wannan
gasa ta cinikin bayi, Ururu suna daga ƙasa ta farko suna
zuba ido suga ko wani zai kawo mata tangarɗa. Wanda
kuma da dama sun aikata hakan amma a yanzu babu
zuri'arsu a ban ƙasa. Ururu sun riga sun gabatar dasu
izuwa lahira.
"Akwai manya-manyan sarakuna guda biyar wanda su
suka fi kowa muƙami acikin wannan gasa. Waɗannan

kuwa sune Sarki Hanibal na ƙasa ta uku da sarki Maikiro
Abbas na ƙasar Maikironomada da sarki Deniz Ururu
wanda ya zaɓi ya zauna a ƙasashen ƙasa shekaru dubu da
suka wuce lokacin da zuriarsa ta ma'abota Ururu zasu
koma ƙasa ta farko. Sai kuma Sarki Rafiya wanda akewa
laƙabi da mai Izza dubu ɗari, sai kuma Sarki Bihanzin Mai
dauwamammen sara. Nasan cewa waɗannan sarakuna
biyar su su suke da iko akan duk wata Izza dake doron
ƙasashen nan shida na ƙasa.
"Kuma nasan cewa duk wanda ya taɓa cinikin bayi
waɗannan Sarakuna sune zasu fara gamawa dashi kafin
ma URURU SU SAUKA. To amma duk da haka bana cire
ran watan watarana zan hana bautar da bil'adama da ake.
Bari dai kawai yanzu ta rashin lafiyar mahaifiyata nake.
Zuciyar tana dukan uku-uku ta kalli idanun Armad ta
kuma tabbatar da cewa lallai abinda yake faɗa har cikin
ransa yake, kuma babu wasa aciki.
Babu yadda ta iya, haka tai ajiyar zuciya bayan dogon
lokaci tana kallonsa. Kafin daga bisani ta girgiza kai gami
da cewa;
''Muhimmin abindai anan shi ne, babu ruwanka da
harkar cinikin bayi a yanzu, zaka shiga cikin fasahar Nontoch-teka, idan ka fito kuma zamu duba muga hanyar da
tafi kamata ka nemo Tarifil fakta ko ka koma izuwa
mahaifiyarka.
''Sabida haka a yanzu babu abinda zan iya akai sai dai
kawai ka jira zuwa nan da kwana shida.''
Armad ya ɗago kai cikin murmushi, amma baice komai
ba, inda yabarta taci gaba da jawabi, ''ni yanzu kamar
yadda na gaya maka ina da buƙatar na shiga cikin kogon
Asúlu, domin fuskantar wankin Izza saboda haye matakin
jarabawar can da nayi za'a ƙaramin matsayi.
''A iyakacin lissafina bazan fi kwana biyar ba, komai
daɗewa, Zuwa yamma zan shiga, amma a yanzu zanje na
shirshirya, kuma da ana zuwa rakiya, to da ka rakani,
amma ba'ayi, daga ni sai waɗanda na zaɓa daga cikin
majalisa.
''Saboda haka muyi sallama kawai. Sai ka huta kuma na
haɗaka da aminaina guda biyu Iliyásis da Cokali su nuna
maka gari.'' Faɗar haka keda wuya kamar ta tuno wani
abin dariya, sai ta fashe da dariya, gami da cewa, ''su na
da kirki da kuma saurin sabo, nima tare muka shigo nan,
amma bayan wani lokaci ALLAH yasa na wuce su matsayi.
Ka kwantar da hankalinka a game dasu.
''Iliyásis baya magana sosai, amma yana da tunani mai
ƙarfin gaske. Ka lura da duk abinda zaiyi zaka koyi
abubuwa da dama.
''Shi kuma Cokali.....'' tuni dariya ta ƙara kwace mata
daga faɗar sunan kawai. Da kyar ta ƙarasa da cewa, ''yana
da ban dariya, amma duk da haka jarumi ne!
Washe gari acikin garin Khan akan wata hanya data wuce
ta cikin wasu gida je, waɗansu mutane uku ne suke tafiya.

Dukkansu babu alamun baƙin ciki a tattare da zuƙatansu,
sai dai ɗaya daga cikinsu wanda duk yaɗan fisu haske da
kuma siranta fuskarsa acike take da fara'a sannan kuma
bakinsa motsi kawai yake yana jawabi.
Bayan wani lokaci ya buɗe baki yace, ''ni suna na Cokali!''
Sannan kuma ya nuna ɗayan dake ɗaya ɓangaren, ya ce,
''wannan kuma shi ne, Iliyásis.''
Yayinda yake maganar idanunsa nakan kan saurayin da
ke tsakiyarsu, wanda ya kasance mai matsakaicin jiki da
kyakkyawar fuska.
Fatarsa wankan tarwaɗa ce, sannan kuma saboda
tsayinsa kai kace ya haura shekaru ashirin da haiwuwa.
Idanunsa nada haske sosai, kuma idan baka kula ba sosai
sai kace har haske suke fitarwa.
Yana da ɗan ƙaramin saje daya ƙara inganta kamalarsa,
sannan kuma idan ka haɗa da rigar dake jikinsa wadda ta
kasance ƴar shara, ta yadda cikakken dantsensa ya fito
sosai, ga kuma doguwar takobin dake rataye a kafaɗarsa,
da kuma jan kyallen daya ɗaure kansa wanda ya saje da
farin wandon dake jikinsa da kuma farar rigarsa, sai kaga
lallai yana fitar da kamalar jarumai a tattare dashi.
Wannan saurayi dake tsakiyarsu ba wani bane ba illa
Armad Wilbafos, wanda kwanakin baya kaɗan a wani ɗan
ƙauye aka laƙaba masa Magajin-Wilbafos.
Sunan da ya rasa murna zaiyi saboda shi ko kuma baƙin
ciki.
Kafin Cokali ya ɗauke idonsa daga kan Armad sai ya
tambayeshi, ''idan nace maka ɗana ba matsala?''
Idanunsa babu ko alamun wasa aciki, hasalima cike suke
da soyayar ɗa da uba, a lokacin da yake tambayar.
Tunda suka haɗu acikin gidan da aka sauki Armad,
bayanda suka ƙara zuwa wajensa, ya ƙare musu kallo,
kuma Armad ya tabbatar cewa acikinsu ukun Cokali ne
ƙarami.
Sannan kuma ɗaya daga cikin su Iliyásis da Nusi ya zama
babba.
Amma to ita kanta Nusi baza tafi ashirin ba.
Sabida haka daya ji wannan tambaya, sai kawai ya fashe
da dariya, kuma ya tuna da abinda ta gaya masa akan
cewa Cokali ɗan cafta ne kawai.
To amma yana niyyar amsawa masa tambayar da yayi sai
kawai idanunsa yakai kan wani zabgegen rami daya gifta
ta inda zasu wuce an ɗan kewaye shi da ƙarafa.
Yana kallon cikinsa yaji wata irin Izza mai tsananin gaske,
wadda tasa yaji tamkar idanunsa zasu fashe daga kallonta
kurum.
Babu abinda yake iya tunawa daya gani acikin ramin face
baƙi da duhu da kuma wani tiriri mai alamun mutuwa da
kanta.
Amma dai abinda ya tabbatar shi ne lallai yana da
matuƙar zurfin gaske, hasalima idan akace bashi da
ƙarshe baza ai musu ba.

Nan take ya ɗaga ido inda ya ƙara hango irin wannan
rami a gabansu, saboda haka cikin zafin nama ya juya
domin tambayarsu meke faruwa a wajen, domin lallai
yaji gashin jikinsa ya tashi, ruhinsa ya fara zafi, kuma
tambarin Miyurar dake goshinsa ya fara haske da kansa
ba tare da ya taɓa shi ba.
Amma kafin yace wani abu yaji maganarsu;
''Ba'a kallon cikin waɗannan rami ka, lallai ka kiyaye,
saboda har halaka zaka iya yi idan kalli cikin manya daga
ciki. Kaga har can nesa duk sune. Danma an kewaye
manyan ciki da bangon sihiri. Suma waɗannan ɗin da a
kewaye suke, amma a hankali a hankali suka cinye
bangwayen da aka kewaye su dashi.
''Ramika ne da Bihanzi yayi da takobinsa wato
Dauwamammen Sara.
''Shekaru da dama da suka wuce, a lokacinda ya fara
shigowa wannan gari kuma ya zama Al'yaya.
''Da dama daga cikin ƴan majalisun wannan gari a
wannan lokaci basu yarda ba, saboda sun san cewa idan
suka barshi ya girma zasu iya rasa muƙaminsu.
''Saboda haka a ɓoye suka saka a hallaka shi kwanaki
kaɗan bayan shigowarsa!
''A sakamakon haka suka fafata, kuma a ƙarshe ba komai
ya faru ba illa waɗannan rami ka da kake gani.
''Ya dai bayyana cewa duk waɗanda Bihanzin ya jiwa ciwo
a wannan rana basu ƙara kwana da yawa ba suka mutu.
''Ba dan komai ba sai cewa duk ciwon da yayi da
takobinsa, to fa bazai taɓa warkewa ba har abada!!
''Kai bama jikin mutun ba, hatta ƙasa, ko kuma duk wani
abu mara rai, domin duk waɗannan ramika da kake gani
sakamakon saran takobin Bihanzin ne daya sari ƙasa a
lokacin.
''Bayan tafiyar shugaban babu yadda sabon shugaban
majalisa baiyi ba domin rufe waɗannan ramika ba,
amma ina, ga sunan har yanzu kuma har abada, an rasa
yadda za'ai dasu, sai dai kawai a kewaye waɗanda za'a iya.
Yau shekaru arba'in da biyu kenan!!!
"Musamman mutane suke yiwo tattaki suzo suga wannan
ciwo da aka jiwa ƙasa, da dama shiɗewa suke saboda irin
girman Izzar dake cikinsa.
"Wanda daga haka aka koma ambatonsa da, Bihanzin mai
Dauwamammen Sara!"
Nidinne dai Shuraih Usman inkiya
99%
Daga taskar magajin wilbafosMAGAJIN WILBAFOS
Marubuci: Dr Abdullahi Muhammad Ibrahim
Babi na 25: Fasahar Marubutan Farko
Post by: Shuraih Usman
@shuraih 99%
www.facebook.com/hausaebooks

.
Daga:- Taskar Magajin Wilbafos
Acikin garin Khan haka a kwana a tashi kwana uku suka
wuce.
Armad yana ta tunanin irin abubuwan daya gani a
lokutan da suke zazzaga gari dasu Cokali, kuma babban
abinda ya kasa cirewa a ransa shi ne sunan Bihanzin mai
dauwamammen ciwo!
To da yake dama yana zaune ne acikin ɗaki a wannan
lokaci, kawai saiya tashi ya ɗauki alƙalami ya zaro ɗaya
daga cikin ganyayyakin da aka kawo masa ko zaiyi rubuta,
ya rubuta sunan Bihanzin da manyan baƙi da yaren
Alderiya(Aldurish).
Haka ya kwana yana tunane-tunane, bayanda gari ya
waye, ya gama kintsawa kenan saiga Iliyásis ya bayyana a
gabansa da labarin maza-maza ya kamata su isa wajen
Non-toch-teka, domin jiya da daddare saƙo ya iso daga
sarki cewa an rage kwana uku akan yadda aka tsara za'a
buɗe wajen, saboda wani dalili da ba'a bayyana ba. A
azalzale haka Armad ya ƙarasa shiri suka fice tare da
Iliyásis.
Har a lokacin da suka fita rana bata ɗaga ba, kuma iskar
alfijir tana nan tana kaɗawa, tana kaɗa maɗaurin kan
Armad da kuma sajensa, yanayin da ya ƙara masa kyau
matuƙa.
Basu ɗauki lokaci ba suka iso wajen da zasu. Tun daga
nesa Armad ya hango wani katafaren gini, wanda iyakacin
hangenka, dama da hauni, sama da ƙasa duk shi ne,
kuma baka iya ganin ƙarshensa.
Iliyásis ya nuna masa da hannu cewa acikin wancan ginin
abinda muke nema yake.
Suna isa wajen, akwai mutane ƴan tsiraru waɗanda da
dama kallo ɗaya kawai sukai musu suka ɗauke kai,
saboda basu sansu ba sannan kuma tuni labari ya gama
bazuwa cikin garin cewa yau za'a fara shiga Non-tochteka, saboda haka ba abin mamaki bane ba kowa ma ya
bayyana a wajen.
Amma daga lokacinda suka fara jan hankalin saura shi
ne, daga sanda suka zarce harya zuwa ɗaya daga ƙofa
goma dake gaban ginin.
Sannan kuma nan take Iliyásis ya miƙa wata takarda inda
mai gadin ya karɓa kuma ya buga mata sheda, sannan ya
buɗe musu ƙofa suka wuce.
Tun daga wannan lokaci ƙus-ƙus ya fara tashi, su na
cewa, ''kaɗai mai iya shiga a wannan lokaci sai dai mai
shedar majalisar!
''To su waye waɗancan mutun biyu?'' Haka dai suka ci
gaba ƙus-ƙus a tsakaninsu a yayinda jama'a suke ta ƙara
zuwa.
Su na shiga ciki, mamaki ya ƙara cika zuciyar Armad,
saboda abinda ya gani, yayi matuƙar saɓawa abinda yai
tsammani.

Domin shi a tunaninsa wani ginin ko kuma dai wani abun
zai ƙara gani, amma bisa mamaki bai ga komai ba.
wato dai a taƙaice babu komai sai fili fetal.
Sannan kuma kamar inda Armad ya gani a lokacin da
yake saukowa daga doron ƙasa ta uku, shi ma wannan
waje komai launinsa iri ɗaya ne.
Hatta ƙasar wajen da samaniya.
Sai dai a wannan lokaci maimakon shuɗaye kamar na
wancan lokaci, waɗannan farare ne!
Duniyar komai fari fat kamar farin kitse.
Babu kowa saisu

Please Login or Register in order to submit comment