Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

shi ne, gab da
kafin
hankalinsa ya dusashe, ya kasance yana ta kai-komo
da
abubuwan sirrin da yaji daga wannan murya wadda
take
magana akan Rukunai guda biyu na Ururu. Sirrin da
Armad ya tabbatar indai ya fita to lallai sai ya rikita
dukkan duniyar ƙasa bakwai, tayadda zaman lafiya
ma zai
iya zuwa ƙarshe!!
Da farkawarsa abinda ya fara yin arba dashi shi ne fili
fetal
gabas da yamma, gudu da arewa ko ina ya duba
baya iya
gano ƙarshensa.
Babban abun mamaki da wannan waje shi ne babu
alamun
wata halitta a wajen ko kaɗan; kama daga kan
namun daji
zuwa tsirrai zuwa tsuntsaye, ko’ina ka duba ba komai
a
wajen kawai sai fili fetal da tsandaurin ƙasa.
Sai dai kuma Armad bai shiga al’ajabin ganinsa a
wajen
ba, saboda ba wannan karonsa na farko ba da yayi
amfani
da irin wannan fasaha, kuma ya samu kansa acikin
wannan yanayi ba.
Kuma daya tambayi kakansa dake koyarda shi, sai ya
ce
masa sakamakon rashin kwarewa ne.
Amma wannan bai hana Armad yin amfani da
wannan
fasaha ba, lokaci zuwa lokaci idan ya tsinci kansa a
mawuyacin hali. Kuma kamar koda yaushe yakan
farka a
wani waje tafiyar wuni ko kwana ɗaya daga wajen da
yayi
amfani da ita.
Iya hangensa baya iya ganin koda shuka guda ɗaya a
wannan waje. Babu komai sai kurum tsandauri
iyakacin
hange.
Armad ya samu kansa a kwance bayan farkawarsa,
sannan
kuma daga bisani bayanda hankalinsa ya fara
dawowa
kansa sai ya lura cewa kayan jikinsa ma ba nasa

bane.
Yana ganin haka yasan tabbas duk da alamun wajen
baya
nuna wani ɗan adam zai iya rayuwa a wajen, lallai
bashi
kaɗai bane a wajen ba.
Saboda haka abu na farko daya fara faɗo masa a rai
shi ne
takobinsa, wadda a iya tunaninsa ita kaɗaice abinda
yake
gani ya tuno da mahaifiyarsa.
Cikin sauri ya juya ɓarin kafaɗarsa ta hagu inda ya
saƙale
takobin tasa, amma babu ita babu alamarta.
Nan take ya miƙe tsaye ya kuma fara dubu-dube.
Amma idanun nasa basu gane masa komai ba, banda
filin
turɓaya kurum dake gabansa iya hangensa.
A wannan lokaci ya juya bayansa, inda bisa mamaki
yai
arba da wani abu, wanda gaba ɗaya acikin wajen nan
shi
kaɗai abinda ya gani tun bayan farkawarsa.
Wannan abu ba komai bane illa wani ƙaton allo mai
rubutu a gabansa.
Ba komai bane a jiki illa suna ye masu yawan gaske,
kowanne da lamba a jikinsa da kuma shekara.
Sunayen sunyi wa Armad wahala, saboda bai saba jin
irinsu ba a ƙasa ta uku, duk da cewa abune mara
wahala
ka samesu acikin littattafan daya karanta, to amma
anan
ɗin ma ba son su yake ba.
Saboda haka kawai sunayen da suke da lamba ɗaya a
jikinsu su ya iya karanta uku daga ciki.
Inda ɗaya yaga ansa Bihanzin Djinn shekarar 1833,
ɗaya
kuma ansa Ikenga O. Bayajidda shekarar 1852 sai
kuma
ɗayan ansa Deniz Bizáya shima shekarar 1852.
Zaka iya cewa ganin shekarar 1852 shi ne abu mafi
girman mamaki da Armad ya fuskanta tun bayan
barin sa
gida.
Badan komai ba kuwa saidan cewa yasan kamata
yayi ace
wannan shekara da suke ciki ta zama 1851, wato
shekarar
da aka gama wancan yaƙi da mahaifiyarsa ta samu
wannan
ciwo a ciki.
Kuma daga fitowarsa daga gida zuwa wannan lokaci

kaf
iyakacin lissafinsa ƴan kwanani ne kawai. Amma
yanzu
gashi yana ganin 1852, wanda hakan ke nuna tuni
yayi
shekara ɗaya da barin gida.
MEKE FARUWA? Ya tambayi kansa.
Amma idan da a haka abin ya tsaya masa da da
sauƙi, to
amma a lokacin ne idanunsa suka kai kan wani
sunan
wanda a jikinsa akasa shekarar 1853!!
Kafin kace meye wannan tuni tunane-tunane sun
cika
ziciyarsa, kuma a lokaci guda sama da hakaicehakaice
ɗari sun bayyana a ransa; ko kaza ko kaza. Amma
duk
ciki babu wanda ya bashi amsa mai ma’ana.
Yana cikin wannan hali ne sai ya fara hangen wata
inuwa
daga nesa, inda nan take ya fara shirya zuciyarsa
cikin
shirin ko ta kwana.
Ba’a daɗe ba halittar dake bada wannan inuwa ta
bayyana,
inda ya fara hango kanta.
Wanda hakan yasa kaɗan daga cikin tashin hankalin
da
yake ciki ya ragu, badan komai sai dan cewa ya gani
da
idonsa cewa wannan mai ƙarasowa mutun ne
kamarsa.
Kuma a lokacin ya ƙara jin sanyi acikin ransa, saboda
yasan cewa indai wani mutun zai iya rayuwa a
wannan
waje to fa shima yana da dama.
Halittar mai ƙarasowa bata ɗauki lokaci ba ta iso
gareshi,
inda idanunsa suka gane masa mace budurwa mai
kalar
fata irin tasa sak wato ‘wankan tarwaɗa’.
Tana da gashi mai tsayi da yawa wanda ta tattareshi
ta
ɗaure.
Fuskarta na nuna alamun yarinta, tayadda Armad ya
yanke shawarar baza ta wuce shekaru ashirin ba,
wato dai
baifi ace ta bashi shekaru huɗu ko uku ba kenan.
Amma duk da ƙarancin shekarun da fuskarta ke
nunawa
idanunta su na ƙunshe da alamun kafiya da saiti,

wanda ke
nuni cewa duk abinda wannan mace ta saka a gaba
saita
cimmasa.
Duk da cewa kyakkyawa ita ma ta gaske, amma
Armad
bashi iya bata lambar girma a kyau a wannan lokaci,
badan komai ba sai dan cewa a zuciyarsa yana
hangna mai
suna Nostalgiya.
Tana ƙarasowa ta tsaya kimanin taku biyar kafinsa,
sannan
kawai ta ɗan ƙura masa ido na ɗan lokaci, kafin daga
bisani ta zira hannunta na dama acikin baƙin
mayafin da
take sanye dashi, inda ta fito da takobi sanye acikin
kufe
mai adon baƙi da yalo ta kuma jefawa Armad ita.
Kallo ɗaya kacal Armad yayi wa takobin ya gane
cewa
kufensa ne kuma takobinsa ce.
Ya miƙa hannu ya cafe, wanda a lokacin ne yaji
hankalinsa ya kwanta kamar wanda aka bawa wata
nutsuwa.
A lokacin ne kuma ya ƙara lura cewa kayan jikin nasa
shima baƙaƙe ne, kuma sunyi kama dana wannan
budurwa dake gabansa. Nan take ya haɗa ɗaya da
biyu ya
gane duk abinda ke faruwa.
Baiyi wata-wata ba ya sunkuyar da kai alamun
girmamawa
ya kuma ce mata, ”na gode sosai da kayan da kika
bani da
kuma kula dani da kikai tsahon wannan lokaci.”
Armad ya ɗago kai ya kalle ta yaga babu alamun
komai a
fuskarta tamkar ma bata ji mai yace ba.
Saboda haka kawai ya yanke shawara, ya juya da
niyyar
tafiya, to amma a wannan lokaci ne yaji tayi magana,
”Ya
sunanka, kuma ya akai kazo nan wajen?”
Muryar tata bata ɗauke da taushi ba kuma ta ɗauke
da
kaushi, tamkar kwata-kwata bata damu da amsar
waɗannan tambayoyi da tayi ba.
Armad ya ci birki, inda ya juya ya fuskance ta idonsa
cike
da son ya gane meke faruwa a wajen.
Ya ɗanyi shiru yana kai-komo da abinda ya kamata
ya
faɗa, inda a lokacin ya gane cewa lallai bashi da wani

zaɓi
da yafi yayi mata bayanin kansa.
Tunda ko ba komai, baya jin zuciyarsa na ɗarsa masa
wata
mugunta a tattare da wannan mace, sannan abisa
mamaki
yaji kurum zuciyarsa ta fara nutsuwa da ita, wato
yana ji
kamar ba cutar dashi tazo ba.
Kuma mafi muhimmanci ma idan ya rabu da ita ya
tafi a
yaushe ne yake tunani a irin wannan waje zai ƙara
ganin
wani ɗan adam ɗin, sannan gashi yana jin yunwa da
ƙishi.
Nan take ya tako ya nufeta, bayanda ya kusa isa, sai
ya
tsaya kawai ya nemi waje ya zauna ya kuma ɗaga kai
ya
kalleta yana yi mata bishara data zauna ita ma.
Ta ɗau kimanin minti ɗaya kawai tana kallonsa, kafin
daga bisani ta zauna ta zauna nesa dashi.
Bayan ta zauna sai ta juya kai ta kalleshi tana kuma
bashi
alamar cewa ya fara jawabi.
Abu na farko daya fara tambaya cikin mamaki shi ne,
“kafin na gaya miki yadda nazo nan, da… ALLAH… ko
zaki gayamin a wacce shekara muke yanzu haka???”
Cikin mamaki ta dube shi gefe da gefe, sannan a
hasale ta
amsa masa da cewa, “kanka ya bugu ne? A ƙarshen
shekarar 1853 mana muke!”
Nan take Armad yai zumbur ya miƙe, baki a
hangame, ido
a kwale. Cikin ƙinƙina ya ce, “1853?????
“Kin tabbata! Saboda ƴan watanni kaɗan da suka
wuce na
na baro gida, kuma ina da tabbas a shekarar 1851,
shekarar da aka gama wancan yaƙin na fito!!!”
Kallonsa kawai tai, tana ƙoƙarin tabbatar wa da
kanta cewa
ba’a cikin hayyacinsa yake ba, amma duk yadda tayi
sai
taga cewa idonsa yana nuna gaskiya yake faɗa.
Saboda haka kawai tai shiru tana tunanin mai ya
kamata
tayi dashi. Tana cikin wannan tunani ne taji muryar
Armad, wanda ya kasa zaune ya kasa tsaye, “dan
ALLAH
ko zaki bani aron Ayrid guda ɗaya, ina son na tura
saƙo
gida!”

Kallonsa kawai tayi, irin kallon mai nuna rashin
yadda,
sannan ta ɗauke kai.
Yana ganin haka ya fuskanci yana da buƙatar yayi
mata
bayanin kansa dalla-dalla da kuma yadda yazo
wannan
waje indai yana buƙatar haɗin kai daga gareta.
Saboda haka nan take ya kwashe dukkanin abinda ya
faru
dashi ya gaya mata. Sannan ya ƙara jaddada mata
buƙatar
Ayrid ɗin da yake.
Bayan tsahon lokaci tana kallonsa, sai ta zira hannu
cikin
mayafinta ta ɗakko kwayar Ayrid guda ɗaya ta cilla
masa.
Nan take Armad ya fasa ɗan yatsansa guda na dama
ya
ɗisa jini akai, sannan ya miƙa hannu ya ɗan gitsiri
wannan
jan kyalle dake ɗaure akansa, kafin daga bisani ya
haƙa
ƙasa a wajen ya binne.
Suna zaune babu wanda ya ce ƙala a cikinsu, shi
Armad
yana jiran amsa daga kakansa wanda dama shi yai
niyyar
yana nutsuwa ya iso ƙasa ta huɗu, ya turawa saƙo
cewa
yaje lafiya.
Sannan kuma ya tambayi lafiyar mahaifiyarsa.
Amma bayanda ya farka sai ya tsinci kansa a tare da
waɗancan mutanen, kuma yanzu gashi ya faɗo nan
wajen.
Duk a tunaninsa baifi ƴan watanni ba, amma gashi
ana ce
masa shekara biyu ta wuce.
Ita wannan budurwa tana nata tunane-tunanen.
Ba jimawa ƙasar dake wajen ta fara motsi, inda kan
kace
meye wannan ƴar shuka ta bayyana, wadda a
samanta
kwayar Ayrid ce guda ɗaya.
Armad ya miƙa hannu ya tsinka. Yana riƙewa a
hannunsa,
ta juye izuwa takarda.
A jiki an rubuta; ; ;
***
kai jika Armad!
Ina ta turo maka saƙonni baka bada amsa, to amma
tunda

na jika yanzu nasan komai lafiya.
Naji matakin daka ɗauka na neman Tirifil-fakta,
kuma kai
sani ina alfahari dakai.
Da fatan acikin wannan shekaru biyu da suka wuce
kana
gabda nemoshi, inma baka riga ka nemoshi ba.
Mahaifiyar ka ta fara samun sauƙi tuntuni, kuma
idan
bakai sauri ba idan ta tashi ban san mai zan gaya
mata, taƙi
biyoka ba!
Kayi ka gama ka dawo, ina jira kazo naga ci gaban
Izzar
daka samu!
Ka kula da ma’abota Ururu!!
Sune suka sawa mahaifiyarka wannan cuta!
Zanso idan na ƙara ganin saƙon ka naga ka cika
wannan
aiki!!!
***
Armad na gama karanta wannan saƙo yai wata
mummunar
ajiyar zuciya, inda wani mugun gumi ya keto masa,
bai
san ya fara jin jiri ba, ba shiri ya nemi waje ya zauna.
Tsahon lokaci baice komai ba, kawai kallon sama
yake,
yama rasa mai zaiyi tunani!!
***
To fa! Armad yayi shekaru biyu, amma bai san a ina
ba!
Domin bama ya tuno wucewarsu ko kaɗan acikin
ransa!!
Mai kuke tunani ya faru ne??
Nidinne dai Shuraih Usman inkiya
99%
Daga taskar magajin wilbafos

MAGAJIN WILBAFOS
Marubuci: Dr Abdullahi Muhammad Ibrahim
Babi na 14: Ikenga O Bayajidda
Post by: Shuraih Usman
@shuraih 99%
www.facebook.com/hausaebooks
.
A A shekarar 1851 After Amri (A.A), a wani gari mai
suna Jíha, dake kan doron ƙasa ta bakwai ɓangaren
Arewa.
Tsakiyar dare ne, kuma a wannan rana ma wuni akai
ana
azababben yaƙi tsakani ɓangaren Ururu da kuma
ɓangaren ƴan adawa dake da shalkwatarsu a
wannan gari.
Babu abinda kake gani sai gawarwakin jama’a duk
inda ka
duba, dan kusan a wannan rana zaka iya cewa aka
kawo
ƙarshen wannan babban yaƙi.
Wannan yaƙi dai shi ne wanda mahaifiyar Armad ta
samu
rauni ashi, kuma harma Armad yaci alwashin sai ya
kawo
mata mutumin data fita nema ta samu wannan ciwo
har
gida, komai rintsi komai wuya.
To acikin wannan gari dai, duk inda ka kalla
gawarwaki
ne a kwance fululu, amma duk da haka idan ka samu
ɓangaren da ba mutun a kwance, zaka ga cewa gaba
ɗaya
ƙasar wajen ta juye izuwa launin ja da baƙi, saboda
yawan
jinin daya kwarara a wannan rana.
A ƙasa kaɗai al’ummar dake kwance a mace sun
haura
dubu ɗari, wani ba kai, wani ba ƙafa, wani kayan ciki
a
waje, wani a caccake da takubba, haka dai kowa ka
kalla
zaka ga akwai sanadin mutuwarsa.
Babu abinda yake kewayawa a saman wannan gari
sai
hankakan mutuwa, wanda shi kansa saboda yawan
jinin
da aka zubar ya fara komawa canjawa daga fari
izuwa
launin ja.
Acikin waɗannan gawarwaki, idan ka duba zaka gano
cewa, mafi yawa daga ciki mata ne da ƙananan yara
da

tsafaffi, waɗanda kasan tabbas irin waɗanda ake bari
a
gida a fita yaƙi ne.
Amma duk da haka babu ko ɗaya mai rai acikinsu!
Can bayan wani lokaci wata gawa daga cikin
waɗannan
mutane, wadda idan ka kalle ta, to zaka iya lissafa
mashi
sama da biyar a jikinta a cake, amma a haka ta
motsa ƴan
daƙiƙu kaɗan da suka wuce.
Lamarinda yasa hankakan mutuwar dake wajen tashi
sama.
A hankali a hankali, wannan gawa ta miƙe tsaye ta
kuma
tsaya akan sauran gawarwakin dake ƙasanta.
Kallo ɗaya kacal zakai mata kasan cewa yaro ne
wanda
bazai haura shekara sha biyu zuwa sha uku ba.
Amma wannan yaro sama da awa goma kenan tun
bayan
da aka cake masa waɗannan mashi ka a jikinsa,
amma
yake ta fafatawa a tsakanin mutuwa da rayuwa, yana
rantsuwa da mahaliccin sarkin Bayajidda na farko,
akan
cewa lallai bazai mutu ba.
Tuni hankalinsa baya jikinsa, kuma babu abinda ke
zagaye a jikinsa banda jini ko’ina da ina, idanunsa
sun
canja izuwa jajaye kamar garwashi, kana ganinsa
zaka
tabbatar da cewa ya kamata ace shekaru da dama da
suka
wuce ya mutu, amma ina, rantsuwa kawai yake, yana
ƙara
rantsewa akan lallai bazai mutu ba a wannan rana
ba.
Yana haka jini ya ɗebe shi ya ƙara faɗuwa, amma ba
jimawa ya tashi ya ci gaba da wannan rantsuwa.
Sai da wannan yaro yai kwana goma acikin wannan
hali,
sannan ana sha ɗayan, yana gabda mutuwa, wani
mutun
ya bayyana, fuskarsa a rufe bubu abinda kake gani
sai
kwayar idanunsa guda biyu. Waɗanda kallo ɗaya
kacal
zakai musu kasan cewa baƙaƙe ne ƙirin, babu
alamar wani
fari ko kuma haske acikinsu. Hasalima, yana bayyana
duk

ilahirin hasken wajen ya fara dusashewa.
Yana bayyana ya isa wajen wannan yaro, inda ya
dube shi
ya ce, “yaro, ka rantse ka kuma rantsewa akan baza
ka
mutu ba, kuma ka ƙi mutuwa..
“Shin mai yasa kake son kaci gaba da rayuwa, bayan
duk
wanda ka taɓa sani a duniya ya mutu, bayan duk
wanda
zai taimake ka ya mutu?”
A wannan lokaci tuni muryar wannan yaro ta dashe
kuma
bata fita ko kaɗan, amma a haka ya dubi wannan
mutum
ya buɗe baki ya faɗi wata kalma guda ɗaya cikin
firgici,
“U….ururu??” Ya tambayi kansa ne, domin akan
idonsa
yaga baƙaƙen idanuwa guda biyu a jikin fuskar
wannan
mutun, kuma yasan cewa ƴan ƙabilar Ururu su
kaɗai suke
da irinsu.
To amma babban abinda ya firgita shi, shi ne,
Ururun dai
sune suka jagoranci wannan yaƙi dayai sanadiyyar
halin
daya tsinci kansa aciki. Hasalima su suka sa, yana ɗan
gawurtaccen sarki, amma ya dawo wanda bashi da
kowa
acikin dare ɗaya. To amma yanzu ga wani mai
baƙaƙen
idanuwan nan ya bayyana a gabansa!
Sautin muryarsa bai fito ba sosai, amma tsananin
fushi da
tsana dake ƙunshe acikin wannan kalma guda ɗaya
ta
‘Ururu’ daya furta, sai daya jawo gaba ɗayan ilahirin
wajen ya ƙara duhu, gami da cika da tsananin yanayi
irin
na Fansa da Tsana.
Haka dai bayan wani lokaci, wannan ma’aboci
baƙaƙen
idanuwa ya ɗanyi wani murmushi wanda komai iya
karanta fuskarka, baza ka iya gane ma’anarsa ba,
sannan
ya miƙa hannunsa yai nuni izuwa wannan yaro,
wanda
hakan yasa yaron tashi akan iska ya taho wajenda
yake
tsaye, inda ya tsaya a gabansa riƙe akan iska

idanunsa suna
kallon waɗannan baƙaƙen idanuwa ciki da ciki.
An ɗauki lokaci a haka, kafin daga bisani a wani
al’amari
mai cike da al’ajabi, ya juya ya fara tafiya izuwa
gabas,
wannan yaro kuma ya biyo bayansa ɗaure akan iska.
Sunan wannan yaro Ikenga O. Bayajidda!
***
Acikin wannan sihirtaccen fili kuwa, bayan tsahon
lokaci,
Armad da wannan budurwa na zaune, kana kallonsu
zaka
fuskanci dukkansu sun nutsa acikin tunani; shi
Armad na
tunani akan wannan shekaru har sama da biyu daya
bayyana cewa sun wuce ba tare da yasan ya akai yayi
su
ba, kamar wani a mafarki.
Ita kuma tana ta tunani akan dukkan labarinsa daya
gaya
mata, musamman ma tayadda ya ce mata ya shigo
wannan
waje, wanda a iya saninta babu wani mahaluƙi daya
isa ya
shigo inba da yardar ƙabilar da ake kira da
Maikironomada ba.
To haka dai suka wanzu tsahon kusan rabin sa’a,
kafin
daga bisani ta dubi Armad gami da cewa, “wato dai
kana
gayamin kaima a zahirin gaskiya baka ma san
tayadda ka
shigo wajen nan ba?
“Kawai kayi amfani da wata fasaha ce, kuma kamar
yadda
kace, ka buɗe ido ka ganka anan!
“Sannan kuma kana gayamin cewa kwata-kwata baka
da
masaniya akan shekaru biyun da suka wuce?
Wannan budurwa ta ɗaga ido ta kalleshi babu
alamun
canjin yanayi kwata-kwata a tattare da ita. Sai dai
duk da
haka zaka iya gane cewa acikin zuciyarta abinda ke
kaikomo bai wuce zantuttukan da Armad ya gaya mata,
shin
gaskiya ko ƙarya yake faɗa!
Bayan wasu ƴan daƙiƙu kawai sai ta ɗauke kai daga
Armad gami da yin ajiyar zuciya, inda ta fara da
cewa,

”wannan ƙasar da kake kai tana daga cikin yankin
sihirtattun ƙasashe uku dake ƙarƙashin mulkin
ƙabilar
Maikironomada.
”Kuma waje ne wanda a iya sani na an killace shi ne
saboda jarabawa ta musamman ga jaruman da suke
takarar zama zaɓaɓɓun babban birnin Maiki na
duniyar
Maikironomada.
”Ban san taya akai ka shigo wannan waje ba, saboda
hanya ɗaya kaɗai da ake shigowa shi ne ta ƙofar
sihiri
guda ɗaya kacal dake garin Arewar Maikironomada.”
Tayi ɗan shiru tana karantar Armad da ido da kuma
yanayin yadda taga fuskarsa ta canja.
Bai ɗauke ta dogon lokaci ba ta fahimci cewa Armad
ɗin
bashi da wata masaniya bisa abubuwa da dama data
faɗa.
Ta sunkuyar dakai gami da ajiyar zuciya, sa’annan
kuma a
lokaci na farko tun bayan haɗuwarsu da Armad
fuskarta ta
ɗan nuna alamun ɗan tausayi, wanda bai ɗauki sama
da
daƙiƙa ɗaya ba ya ɓace.
Sannan ta ce, ”toh! koma dai meye ka gane cewa
yanzu
tunda kariga ka shigo nan abu ne mai wahalar gaske
ka
tsira, kasancewar nima ka ganni anan shekara ta uku
kenan ina ƙoƙarin cin wannan jarabawa na fita daga
wannan waje, amma abin ya ci tura!”
Bayan wasu ƴan daƙiƙu kawai sai ta ɗauke kai daga
Armad gami da yin ajiyar zuciya, inda ta fara da
cewa,
”wannan ƙasar da kake kai tana daga cikin yankin
sihirtattun ƙasashe uku dake ƙarƙashin mulkin
Maikironomada.
”Kuma waje ne wanda a iya sani na an killace shi ne
saboda jarabawa ta musamman ga jaruman da suke
takarar zama zaɓaɓɓun babban birnin Maiki na
duniyar
Maikironomada.
”Ban san taya akai ka shigo wannan waje ba, saboda
hanya ɗaya kaɗai da ake iya shigowa shi ne ta ƙofar
sihiri
guda ɗaya kacal dake garin Arewar Maikironomada.”
Tayi ɗan shiru tana karantar Armad da ido da kuma
yanayin yadda taga fuskarsa ta canja.
Bai ɗauke ta dogon lokaci ba ta fahimci cewa Armad
ɗin

bashi da wata masaniya bisa abubuwa da dama data
faɗa.
Ta sunkuyar dakai gami da ajiyar zuciya, sa’annan
kuma a
lokaci na farko tun bayan haɗuwarsu da Armad
fuskarta ta
ɗan nuna alamun ɗan tausayi, wanda bai ɗauki sama
da
daƙiƙa ɗaya ba ya ɓace.
Sannan ta ce, ”toh! koma dai meye ka gane cewa
yanzu
tunda kariga ka shigo nan, ka shigo kenan,
kasancewar
nima ka ganni anan shekara ta uku kenan ina
ƙoƙarin cin
wannan jarabawa na fita daga wannan waje amma
abin ya
ci tura!”
***
To fa! Ana dara ga dare yayi, Armad ya shiga inda ba
fita!!!
Sannan kuma munga kaɗan daga cikin yaƙin daya
janyo
mahaifiyar Armad ta samu rauni, a shekarar
1851(After
Amri), har ya ɗauƙi alwashin cika mata burinta na
kawo
mata abinda take nema har gida.
To amma waye wannan yaro, kuma waye wannan
mai
baƙaƙen idanu daya ceto shi, kuma saboda me,
bayan
cewar dasu sukai yaƙin. shekarar 1851 After Amri
(A.A),
Nidinne dai Shuraih Usman inkiya
99%
Daga taskar magajin wilbafos

MAGAJIN WILBAFOS
Marubuci: Dr Abdullahi Muhammad Ibrahim
Babi na 15: Sanyin Babban Sihiri
Post by: Shuraih Usman
@shuraih 99%
www.facebook.com/hausaebooks
.
.
A can wannan daji kuwa duwatsu ne iyakacin hangen
ɗan-adam, inda daga cikinsu mutane sanye da
kayan yaƙi suke ta ƙara ɓulɓulowa su na nufo

wajan da su Zahra suke tsaye cirko-cirko tun bayan
jin
wannan murya.
Kafin kace meye wannan mutane da dama sun
kewaye su
ta kowanne ɓari.
Ana cikin haka wasu manya-manyan mutane
waɗanda su
kaɗai ne fuskarsu bata naɗɗaɗe da rawani suka fito
fili
daga bayan wasu jajayen duwatsu.
Su na fitowa, kai tsaye suka fara kusantar inda su
Hasanu
suke tsaye.
Dukkaninsu manya-manyan halittu ne tayadda in
baka
kula ba sosai ba, sai kace samudawa ne.
Na tsakiyar tasu ya ɗan ɗara ragowar tsayi yana
sanye
kuma da jan rawani wanda kamar kamar rawanin
sauran
mutanen dake kewaye da wajan ba, bai rufe masa
fuska
ba.
Yana ɗauke da wani ƙatoton farin gatari.
Idan kuma ka duba zakaga cewa duk da duhun
wajen bai
hana idanunsa walƙiya ba, wanda idan ka ƙura ido
zaka
fahimci cewa acikin idon nasa akwai waɗansu
abubuwa
guda biyu acikin kowanne ido.
Idan ka ƙara ƙura ido zaka fahimci cewa waɗannan
abubuwa ba komai ba ne ba illa hoto na taurari
waɗanda
suka maye gurbin baƙin kowanne idonsa, biyu a
kowanne
ɓangare wanda ya bashi taurari guda huɗu kenan
idan aka
tara.
Su kuma mutun biyun dake gefensa idanunsu kamar
na
kowa ne, amma kuma a goshinsu akwai tambari na
Miyura, na ɓangaren daman yana da taurari uku irin
na
cikin idanun na tsakiyar, su na motsi su na kewaya
wannan Miyura dake goshinsa.
Na ɓangaren hagun kuma yana da taurari guda biyu,
shima kuma su na kewaya Miyurar dake goshinsa.
Babban nasu mai taurarin a ido ya fara magana,
”Hasanu,
a bayyane yake a fili babu yadda zaku iya fita daga

wannan waje inba mu muka barku.
”Da farko da muka gano mutun uku kacal na tafiya
da
Ayrid mai babban mataki, munyi niyyar kawai mu
kashesu mu kwace.
”To amma bayanda na gano kaine aciki, sai na canja
shawara cewa idan kuka bamu wannan Ayrid, da
kuma
duk abinda kuka mallaka, to zan barka ka wuce da
ranka.
”Duk da kuwa mataimaka na guda biyu basu goyin
bayan
hakan ba, amma badan komai saboda tuna baya,
naga ya
kamata kai kaɗai dai na bari ka wuce da ranka.” Ya
ƙarasa
maganarsa yana mai waiwayowa yana kallon mutun
biyun
dake bayansa furkarsa cike da dariyar ƙeta.
Fuskar Hasanu cike da fushi ya dubi wannan
jibgegen
mutum ya fara magana cikin izgili, ”hmmm Ƙiliƙ, ai
ban
san ka mallaki taurari huɗu ba, dana nemeka nayi
maka
murna.”
***
Ƙarin bayanin akan kalmar Ótaki
Kalmar Miyura daga yaren Alderiya take, kuma tana
nufin
tambari a gaban goshi, kamar Irin wanda Armad
yake
dashi.
To akwai wani abu dake faruwa a wannan zamani
wanda
yake da ban al’ajabi kwarai da gaske. Wannan kuwa
ba
wani abu bane illa haihuwar kowanne mutun da ake
da
tambarin Miyura a goshinsu.
Kowacce ƙabila tana da irin tambarinta, wanda
kuma su
kaɗai suke dashi. Harma ana amfani dashi wajen
gane
asalin ƴan kowacce ƙabila a yayin haihuwa.
Sai dai abinda ke faruwa shi ne, kwana bakwai daidai da
dai-dai bayan haihuwa, babu ragi babu ƙari, wannan
tambarin yake goge wa da kansa, tamkar ba’a taɓa
yinsa
ba. Sannan kuma bazai ƙara dawowa goshin mutun
ba,

har sai mutun yakai wani babban matsayi na Izza da
ake
cewa ‘Ótaki’ wanda yake nuni da Izza mai mataki na
Shekaru ɗari biyar, sannan tambarin zai ringa
bayyana a
gaban goshinsa, kaɗai lokacin da zaiyi amfani da
Izzar
data kai ɗari biyar!
Kaɗan daga cikin dalilan da yasa Armad yake ɗaura
jan
kyalle a gaban goshinsa shi ne, domin ya rufe
tambarin
Miyurar dake goshin nasa.
Na farko dai, duk wanda ya gani zai iya gane cewa
Armad
ɗan ƙabilar Wilbafos ne, (idan baku manta ba,
wannan
mai tsaron ƙofar, Han’Diyuza, mai aljanin wuta, yana
ganin Miyurar Armad yake cewa daga ƙabilar
Wilbafos
yake!).
Ƙabilar Wilbafos dai sunan ta ma ba’a san faɗa.
Saboda
ƙabila ce da suka taɓa fito na fito da Ururu, wanda a
dalilin haka babu wanda yake son yai alaƙa dasu,
saboda
tsoron Ururu da ake ji. Kai hasalima, har kyauta
mutun zai
iya samu idan ya kama Armad ya miƙawa Ururu, a
matsayin wanda ya fito daga zuri’ar Wilbafos.
Sannan kuma na biyu, kamar yadda na faɗa, ana
haifar
mutun tambarin yake ɗaukewa, to amma bisa
ƙololuwar
mamaki irin wanda ba’a taɓa gani ba, tunda aka haifi
Armad Miyurar sa bata taɓa ɓacewa ba.
Ana jira aga bayan kwana bakwai ta ɗauke, amma
taƙi,
har akai shekara, har aka kai shekaru goma, har
izuwa
wannan rana, bata taɓa ɓacewa ba, koda sau ɗaya!!!
Saboda hakan nema, tun kafin magana ta fara
yaɗuwa,
mahaifiyarsa ta samu jan kyalle ta rufe masa
goshinsa tun
yana jariri, wanda kuma dashi ya taso, kuma har a
wannan
lokaci yake ɗaurashi domin rufe Miyurar. Saboda
abu ne
wanda zai iya rikita duniya baki ɗaya, idan mutane
suka ji
wannan labari. Domin kamar a wannan zamani

namu ne
ace an samu Jaki mai ƙaho ko kuma mutun mai tashi
sama
ko kuma ace an tsinci raƙumi acikin kuratandu!!
***
Ga dukkan alamu ɗan wannan abu da Hasanu ya
faɗa yayi
matuƙar ɓatawa Ƙilik rai, kamar wanda yake tuna
wani
abu a baya tsakaninsa da Hasanu, nan take yai gunji
gami
da dariyar mugunta yana cewa, ”Yau dai girman
kanka
lallai yazo ƙarshe.” Ya nuna jaruman dake bayansa
da
hannu yana cewa, ”Ina da janar mai taurari uku, ina
da
mai taurari biyu, sannan kuma ina da sadaukai dubu
biyar
waɗanda kawai kalmata suke jira su afka muku ba
tare da
wani tsoro ba.
”Ka gayamin mai kake taƙama dashi, waye zai iya
tseratar
dakai yau daga hannuna.
”Kai na canja shawara ta ma, yaune ranar shan
numfashinka na ƙarshe, Hasanu.” yai gunji mai
razanarwa,
lamarinda yasa wata iska mai ƙarfi kaɗawa. Wadda
ita
kaɗai zata iya karayar da zuciyar abokin karawarsa.
Nan take ya ɗaga hannu sama, ya kuma bada
umarnin su
afaka musu, lamarinda yasa gabaki ɗayan waɗannan
mutane dubu biyar, da kuma su ukun suka afkawa
su
Hasanu.
To amma a dai-dai wannan lokaci ne Hasanu ya
umarci
Kiru da Zahra dasu koma dai-dai bayansa su tsaya,
yana
mai cewa, ”ku lura sosai, ku zira ido, kuga dukkan
abinda
zanyi, domin ba lallai ba ne ba, ku ƙara samun dama
a
rayuwarku ba daza kuga irin abinda zai faru yanzu
ba!”
A wannan lokaci da wannan babban nasu ya ɗaga
hannunsa sama, dukkansu sukai kukan kura inda
suka
afkawa mutun uku kacal, wato Hasanu da Kiru da
kuma

Zahra.
Hasanun wanda tuni ya umarci ƙannan nasa guda
biyu
dasu koma bayansa, ya ɗaga ƙafarsa ta dama inda
yayi
taku ɗaya gaba.
Taku ne guda ɗaya kacal, amma a dalilinsa
abubuwan da
suka faru suna da yawa ta yadda duk wanda ya samu
damar ganin abubuwan da suka faru kuma ya tsira
da
ransa to lallai harya mutu bazai manta da abinda ya
gani
ba.
A ƙunshe acikin wannan takun, taurari ɗai-ɗai ɗaiɗai har
guda biyar suka bayyana acikin idanun Hasanu, uku
a
dama, biyu a hagu inda suka maye gurbin baƙin
dake
cikin idon nasa.
Acikin takun wata iska mai tsananin ƙarfin gaske ta
fara
fita daga jikinsa.
Kan kace meye wannan tuni wannan iska ta game
duk
wani abu dake wannan kewayen dutsen.
Acikin wannan takun waɗansu mutun-mutumi guda
biyu
waɗanda gabaki ɗaya jikinsu anyi shi ne da wanna
iska
suka bayyana.
Ɗaya a damansa ɗaya kuma a hagunsa.
Bayyanarsu keda wuya wani yanayi mai ɗauke da
sanyin
gaske, tamkar a tsakiyar hunturu, ya cika wajen baki
ɗaya,
tamkar ƙankara zata fara sauka.
Fara kaɗawar wannan iska keda wuya dukkan
waɗannan
mayaƙa dubu biyar dake doso su Hasanu suka tsaya
cak a
inda suke.
Cikin wani al’amari mai kama da almara kawai
wannan
iska ta daki jikin waɗannan Jarumai dubu biyar,
lamarinda
yasa akan idon kowa, wani abu mai kama da
ƙanƙara ya
fara fitowa daga jikin fatarsu. Sai dai kawai
banbancin
wannan abu da ƙanƙara shi ne launinsa ruwan toka

ne,
maimakon fari da aka san ƙanƙara dashi. Amma
kuma
duk da haka tsananin sanyi ne irin mai ratsa ruhin
nan
yake shigarsu, wanda tuni yasa suka faɗi ƙasa
sumammu.
Duk wanda ya rayu a wannan zamani, yasan sunan
wannan iska mai ɗauke da ƙanƙara ruwan toka,
wadda ita
ake cewa, Sanyin babban sihiri!! Wanda kuma idan
mutun
yakai matsayin Ótaki yake mallaka.
Babu waɗanda suka rage illa waɗannan manya nasu
su
uku wanda ke gabda isa kusa dasu Hasanu.
Babu shiri suka ci birki cikin tsananin zafin

Please Login or Register in order to submit comment