Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

toba
alkhairi bane. Dan babu yadda za'ai a iya tunaninsu
mutun yana cikin hayyacinsa ya ce zai nemo Tarifil Fakta
acikin wata bakwai masu zuwa. Mutumin da duk duniya
suka kasa nemowa.
Dakyar Armad ya iya daina haƙi, sannan ya dube du cikin
sauri ya fara jawabi, "Masanin Ƙasa Abul-Babara ya bani
adadin wata bakwai na nemo Tarifil-faƙta. Yace ya gama
haɗa maganin mahaifiya ta, amma idan nanda wata
bakwai ban nemo shi ba, to nama haƙura da nemansa,
domin kuwa alƙwarinmu dashi ya tashi."
"Kai…." Cikin tsananin mamakin rashin sanin ya kamata
na ma'abota duba dukkanin su ukun sukai ajiyar zuciya
tare da riƙe baki. Domin sun san lallai aikin dake gaban
Armad ya tashi daga mai-kama-da-mara-yiwuwa zuwa
wanda-bazai-taɓa-yiwuwa ba. To amma ganin halin da
Armad ke ciki na rikici da firgici, nann da nan Nusi ta
fuskanci cewa kamata yayi sunkwantar masa da hankali,
su kuma bashi buri maimakon su ƙara kashe masa
gwiwa.
"Indai haka ne to kai sani cewa mu ukun nan zamu
taimaka maka da iyakacin ikon mu a cikin waɗannan
wata bakwan. Abinda ya kamata ka sani shi ne.
"Na farko dai babban mafitar ka ta nemo Tarifil-fakta a
yanzu shi ne shiga cikin garinmuna ƙarƙashin ƙasa
wanda na labarts maka a baya. Domin ina jin cewa indai
muka iya shiga wannan gari, to kamar mun samo Tarifilfakta ne.
"Amma kai sani cewa, hanya ɗaya da zamu iya shiga
garuruwan ƙarƙashin ƙasa shi ne idan akai mana rijista
acikin waɗanda zasu biga gasar Jinzidal. Ni zan nemo
mana katin shiga na garin Maikironomada. Sannan kuma
idan muka shiga sai fake da taka rawa acikin gasar mu
silale muyi namu waje.
"To amma Armad kai sani cewa lallai komin saurin da
kake baxan bari ka shiga gasar Jinzidal ba, ba tare da na
tabbatar da ƙarfin Izzar ka ba. Saboda haka maimakon
wata biyu yanzu na maida shi sati ɗaya. Zamu jira anan,
kai kuma zaka hau kwale-kwale. Akwai wani tsibiri idan ka
miƙe wannan hanya," taɗan tsaya taja numfashi tare
nuna masa hanyar da hannunta, "abinda kawai nake so
shi ne ka ɗebo min ƙasar dake wannan tsibirin ka dawo
nan cikin sati ɗaya." Ta ciro wani Ayrid daga jakarta, inda
ta karanta wasu ɗalasimai ta juyarda shi izuwa ɗan
ƙaramin kwale-kwale.
Babu ko cewa ƙala, Armad ya hau wannan kwale-kwale
ya zare takobinsa, tare da nufar hanyar tsibirin nan.
Nusi tayi ajiyar zuciya tare da kallon su Iliyasis, waɗanda

sun kasa cewa komai tunda suka ji zancen wata bakwan
nan. Ta numfasa tace, "ko ya nemo Tarifil-Fakta ko ba ya
nemo shi ba, duk ya ta'allaƙa da ƙaddararsa. Mudai
namu shi ne mu taimakawa abokinmu mu kuma bashi
kwarim gwiwa. Saboda kada wani acikin ku ya kuskura
yace masa bazai yiwuwa ba. Ku kafa mana tanti, anan
zamu jira shi sati ɗaya."
Kwanaki uku bayan da Armad ya ɓace acikin hazon dake
kewaye da wannan kogi daya haɗe tsakanin doron ƙasa
ta uku da kuma dajin Ikwatora, Armad ne ke tafe yana ta
tuƙa kwale-kwalen a hankali, domin ko gabansa baya iya
gani saboda hazo da duhu. Domin tunda yai kwana biyu
yana tafiya, ya daina ganin rana, kullum dare ne kuma
kullum duhu ne.
Sai dai kuma babban abinda ya bawa Armad mamaki shi
ne, duk da kasance war wannan kogi da yake kai za'a iya
yin ittafaƙi akan cewa yana daga cikin wajen mafi hatsari
a dukkanin duniyoyin ƙasa, amma bisa tsananin mamaki
babu ko Dordor ɗaya da yai arba dashi. Hasalima babu
wata halitta mai hatsari daya gani, kai a rana ta uku ma
yana cikin tafiy kawai idanunsa suka kai ƙasan kwalekwalensa bayanda yaji motsi, ai kuwa yana dubawa yaga
manya-manyan kifaye suna gudu a cikin ruwan nan a
ƙoƙarinsu na gukewa daga inda Armad yake tsoro.
Nan take Armad yasan cewa akwai wani hatsari dake
faruwa, Amma ko kaɗan hakan baisa yaja baya ba, ko
kuma ya tsaya ba. Kai tsaye, cikin dakiya da rashin tsoro
ya ƙara numfasawa cikin wannan duhuwa da hazo.
A rana ta huɗu da yamma yana tafiya ya fara hangen
wannan tsibiri da Nusi ta kwatanta masa. Ai kuwa nan
take ya ƙara azama ya nufi wannan waje gadan-gadan.
ALLAH sarki, rashin sani yafi dare duhu, akan wannan
tsibiri waɗansu mutane ne guda huɗu. Dukkan tsibirin
babu gida gaba babu gida baya. Babu wata halitta mai rai,
face rugurguzazzun gida je da duwar-watsu. Lallai kana
gani zaka fahimci cewa shekaru aru-aru anyi babbar
alƙarya akan wannan ruwa, amma a yanzu sai dai tarihi.
Iskar dake tashi daga wannan tsibiri duk da a tsakiyar
ruwa yake, amma tana da tsananin zafi, sannan kuma
tana ɗauke da tsananin tsoro da firgici acikinta. Babu
komai sai duhu da kaɗaici da alamun mutuwa da alhini
acikin wannan waje.
Amma bisa mamaki waɗannan mutane huɗu, maza uku
mace ɗaya suna tsaye a tsakiyar wannan waje. Su su
kaɗai ne halitta mai rai duk faɗin wajen.
Dukkanin gashin jikinsu fari ne fat alamun tsufa da
daɗewa a duniya. Amma hakan ko kaɗan baya nuna
alamun gajiya wa a tattare dasu. Hasalima kowanne ɗaya
daga cikinsu zai iya yaƙar daula guda shi kaɗai kuma yai
nasara ba tare da ko kwarazane a jinkinsa ba.
Babban cikinsu mai sanye da rawani wanda ya rufe
fuskarsa, yana fitar da kamala mai ƙarfin gaske. Wadda

ita kaɗai zata iya zubar da ƙananun ma'abota Izza ƙasa a
sume. Hasalima Izzarsa shekaru dubu ɗaya ce da ɗari
biyu da sha uku (1213 years). Mai biye masa yana da Izza
shekaru ɗari tara da arbain da ɗaya. Macen nada ɗari
baƙwai da sha uku sai kuma ƙara munsu mai ɗari biyar
da huɗu.
A wani na salo na wata irin murya mai saka tsoro a cikin
iskar dake kaɗawa, mai biye wa babban yai magana, "Ya
shugaba na, yau shekaru sama da ɗari bakwai muna
neman wannan littafin-takobin, amma yau gashi ya
bayyana a garemu. Lallai jiranmu yazo ƙarshe. Ina so ka
bani iko na zo maka da wannan littafi cikin ƙiftawar ido."
Tsahon lokaci wannan nasu baice komai ba, hasalima ko
kallon sa baiyi ba. Sai bayan kimanin daƙiƙa sittin
wannan mace ta cire mayafin data rufe fuskarta ta kuma
rusuna a gaban shugaban nasu tace, "ya shugaba na, ni
kuma ina ganin mu bari yaron mai suna Armad ya iso,
tunda shi ne kaɗai wanda littafin ya amince ya bayyana a
gareshi bayan duk waɗannan shekarun. Idan ya iso saimu
kashe shi cikin kwanciyar hankali, mu kuma yi amfani da
ruhinsa wajen sarrafa littafin."
Babban abinda mamaki da wannan mace data bada
wannan shawara ita ce, kamarsu ɗaya sak da Nusi babu
wani abu daya raba su, kama daga kalar fatar har komai
da komai. Kai kamar har tafi wadda ke tsakanin yan biyu
ma, idan dai banda cewa kana zuwa bakin wancan ruwa
zaka ga Nusi dasu Cokali a inda Armad ya barsu ba, toda
sai kace ita ce ma.
Wannan littafi da waɗannan mutane suke nema idan mai
karatu bai manta ba, shi ne wanda aka labarta acikin
'Gabatarwar' wannan littafi. Wanda hatta ma'abota Ururu
suke nema, amma sun rasa. Yanzu gashi su waɗannan
mutanen sun gano cewa wannan littafi da Armad ya
samo acikin Non-toc-Teka, shi ne dai wannan littafin da
suke nema. Kuma gashi nan yana tafe zuwa inda suke
bayan shekaru sama da ɗari bakwai da sukai suna nema.
***
Deniziyya Kuronikil (Jinzidal), suna ne da akewa wata gasa
laƙabi dashi.
Gasa ce wadda kamar yadda aka labarta a baya wajibi ce,
kuma babu wata ƙasa ko kuma wani sarki daya isa yaƙi
shiga.
Kowanne sarki daga kan doron kowacce ƙasa zai kawo
wani adadi na bayi, waɗanda za'a saka a matsayin kyauta
ga duk ƙasar da tayi nasara a gasar.
Akan tara sama da bayi dubu ɗari waɗanda za'a rabasu
tsakanin wanda sukai nasara na ɗaya dana biyu da kuma
na uku. Ta haka waɗannan ƙasashe su zasu juya akalar
cinikin bayi a wannan shekara.
Nidinne dai Shuraih Usman inkiya

99%
Daga taskar magajin wilbafos
MAGAJIN WILBAFOS
Marubuci: Dr Abdullahi Muhammad Ibrahim
Babi na 27: Tsibirin Kadaici
Post by: Shuraih Usman
@shuraih 99%
www.facebook.com/hausaebooks
.
Daga:- Taskar Magajin Wilbafos
Armad na tafe a hankali a hankali, babu abinda yake sosa
masa rai sai labarin watanni bakwan da suka rage masa
kafin wa'adin da sarkin duba Abul Babara ya bashi ya
cika. Lallai yasan cewa duk abinda zaiyi daga wannan
lokaci saiya zamo a ƙaiyade da lokaci.
Da yammaci liƙis yakai bakin gaɓa, inda ya sauko
hannunsa na hagu bisa kan takobinsa, sannan na dama
kuma yana ƙoƙarin ɗaure jirgin a iyaka.
Bayanda daya gama ɗaure jirgin saiya ɗago ya kuma yi
duba izuwa cikin wannan tsibiri dake gabansa. Babu
komai akai face ƴan gidaje ɗai-ɗai ɗai-ɗai ƙirar mutan
da. Wanda tun daga nesa baka da buƙatar ace maka
maka babu wata halitta aciki. Domin kuwa banda yana
data rufe ko'ina babu komai sai shiru da kaɗaici dake
tashi daga kaf ilahirin gida jen. Ga dukkan alamu ko
namun dawa basu iya sakewa akan wannan tsibiri. Duk
yadda akai yana daga cikin tsibiran da akayi wa
mummunan sammu irin na mutanen farko.
Har izuwa wannan lokaci Armad bai daina mamakin
dalilin da yasa har ya zuwa wannan lokavi bai gamu da
Dordor ba. Domin a iyakacin lissafinsa ya ƙididdiga cewa
ya kamata zuwa wannan lokaci ace tskobinsa tasha jinin
sama da Dordor arba'in zuwa sama.
Nan take ya tabbatarwa da kansa cewa lallai akwai wani
abu akan wannan tsibiri wanda hatta su Nusi basu sani
ba. Saboda haka nan take ya zare baƙar takobinsa, tare
da karanta ɗalasimai kamar haka, "Ƙaban'shisu!"
Nan take walƙiya da tsawa ta fara haɗowa a jikin ƙarfen
wannan takobi, inda nan take dukkan ilahirin ta ya cika
da wannan walƙiya. Kafin daga bisani ilahirin jikin Armad
shima ya ɗau haske yana bada walƙiya tamkar ɗan saƙon
mutuwa.
Hasken jikin walƙiyar Armad ya fara haskake dukkan
ilahirin wannan tsibiri, lamarin da yasa ya fara hangen
alamun wasu mutane daga wata ƴar duhuwa da bata da
nisa daga inda yake. Babu shiri yayi linƙaya acikin girman
ɗalasiminsa na 'Ƙaban'shísu', ya kuma ɓace daga inda
yake, sannan ya bayyana gaban wannan duhuwa.
Ai kuwa idon Armad bai masa ƙarya ba, domin kuwa
kamar yadda ya gani haka yake. Mutane ne guda huɗu a
tsaye a wajen. Dukkansu da ransu da lafiyarsu, amma
kuma babban abin mamakin shi ne, babu wanda acikinsu

yake kalli Armad. Tamkar basu ganshi ko kuma basu
masan wani yana tsaye a wajen ba. Duk da kuwa haske da
zafin Aradu dake tashi daga jinkinsa da kuma na
takobinsa.
Armad ya dube su tare da haɗe gira, "kamar yadda babu
ruwanku dani, nima haka babu ruwana daku." Yana gama
magana ya juya zai tafi. A zuciyar Armad yayi tunani cewa
yadda basu kula shi ba, yana nuna tamkar basu damu
dashi bane. Sai dai kuma amma kash, abin ba haka yake
ba, domin kuwa yana juyawa yaji maganar wata mace
daga cikinsu, wanda yake shi baima kula akwai wata
mace acikinsu ba.
"Waya ce maka ba ruwanmu dakai," macen na rufe baki
Armad ya juyo da niyyar ganin kowa ce ce ke magana, ai
kuwa nan take ya buɗe baki tare da kwale ido.
"Nusi??" Armad ya lura cewa wannan mace data gama
magana kamarsu ɗaya sak da Nusi daya baro a bakin
gaɓa. "Me kikeyi a nan?" Armad ya ƙara tambaya.
"Ba ita bace," ta bashi amsa a nutse, "abinda kawai muke
nema a wajen ka shi ne littafin daka samo acikin Nontoc-teka."
Armad ya yatsine fuska cikin fushi, "damme yasa zan
baku littafina!"
Wannan mace mai kama da Nusi ta ƙara girgiza sannan
tace, "idan da munso yaudararka toda munyi shigar ƴar
uwarka Nusi mun kuma ɓata tsakanin ku ts hanyar yin
amfani da sunanta mu kwaci wannan littafi. To amma
shugaban mu yace mu bika a hankali. Saboda haka ina so
ka ƙara tunani kafin ka ƙara bamu amsa. Domin kuwa
wannan itace dama ta ƙarshe dazan baka." Tana gama
magana ta zare takobinta tare da tsayawa a gaba Armad.
Armad ya lura cewa tana sane take ƙara futo da ƙarfin
Izza ta domin ya karanta ya gane matsayinta a fagen Izza.
Idon Armad sukai tsinkaye da abubuwa kamar haka;
Izza : 713
Negrinki : Duniya ta biyu
Aljani : Aljanin Iska
Fasahar takobi : Mataki na Shida
Har ya zuwa wannan lokaci babu wanda yai motsi acikin
waɗannan mutane uku dake tare da wannan ma'abociyar
Izza dake kama da Nusi. Lallai Armad yasan cewa akwai
babban aiki a gabansa kafin ya tserewa waɗannan
mutane. Domin kuwa yasan cewa a doke lallai bazai iya ja
da dukkaninsu ba. Gashi har ila yau ko gwada ƙarfin
wannan littafin takobin baiyi ba, ballanta yasan ko akwai
wata fasaha aciki da zata iya taimaka masa. To amma
wani babban abin mamaki shi ne yana jin cewa bazai
taɓa iya bayarda wannan littafi ba. Ko mai zai faru.
Saboda haka saiya fara ƙoƙarin ɓullo da wata sabuwar
hanyar, "mai yasa kuke san wannan littafi." Armad ya
tambaye ta a nutse.
Nan take fuskar ta ta fara canjawa, inda a fusace ta bashi

amsa, "wannan bai shafe kaba. Zaka bayar ko baza ka
bayar ba."
Armad yana cikin tunanin mai zai aiwatar kawai yaji
hucin takobinta yana iso shi. Inda nan take ya miƙa tasa
ya tare. Sai dai amma banbancin Izzar da yawa, nan take
ta danne Armad izuwa ƙasa bisa gwiwowinsa. Badan
takobin tasa ma tasha tsimi ba, to da lallai tuni ta
tarwatse.
Armad na ƙoƙarin kare kamsa daga wannan sara nata,
amma ina, tuni cikin zafin nama ta zira hannu cikin
rigarsa. Inda kafin yai wani motsi tuni ta ƙara nuna masa
banbancin dake tsakanin Izza shekaru ɗari bakwai da
ɗoriya da kuma wadda bata kai shekaru ɗari ba. Inda
wannan littafi ya bayyana a hannunta. Armad yai iya
ƙoƙarinsa ya riƙo shi amma ina babu abinda yake sai
ƙara nisa dashi, yayinda ita kuma tai tsalle take komawa
baya.
Kafin Armad yayi wani abu tuni dukkanin su ukun dake
bayan wannan mace sukai tsalle tare da matsowa kusa da
ita. Sannan kuma a wani salo na samarda ƙawanyar tsafi,
dukkaninsu huɗun suka kewaye wannan littafi a yayinda
macen ta sashi a tsakiya. Kafin daga bisani su fara karanta
wasu a wani harshe wanda Armad bai gane ba.
Dukkan abubuwan sun ɗauki lokaci wajen bayani amma
a zahiri basu wuce daƙiƙa ɗaya ba.
Sai dai Armad na niyyar kai musu farmaki ya kwace
littafin, kawai sai ya ƙara ganin wani hasken ya bayyana
daga sama. Inda kafin ma Armad ya gama zare takobinsa,
tuni wani saurayi ya bayyana daga cikin wannan haske,
inda kai tsaye ya caka farar takobin dake hannunsa a
tsakiyar waɗannan mutane huɗu. Kuma kan wani
acikinsu yayi wani abu tuni takobin tasa ta haɗu da jikin
wannan littafi dake tsakiyarsu.
Nan take wani baƙin haske mai kama da duhun dare ya
gauraye dukkan wajen. Inda kai tsaye ya sumar da Armad
cikin abinda bai wuce daƙiƙa ba. Babu abinda Armad ya
ƙara tunawa illa farkawa da yayi bayan tsahon lokaci yai
arba dashi kwance acikin taɓo sannan kuma daga can
gefe kuma ga littafinsa nan. Sai dai kuma babu kowa a
wajen sai shi kaɗai.
Har Armad ya fara tunane-tunane kawai sai ya tuna cewa
koma ina suka tafi bai shafe shi ba, tunda ga littafinsa
basu tafi dashi ba, abinda kawai ya rage masa shi ne ya
ɓace daga wajen.
Sai dai kuma yana cikin saurin da yake ne, kwatsam kan
ya kai ga littafin ya gano cewa a gaban goshinsa babu
wannan jan kyalle da kullum ke tare dashi. Babu shiri ya
tafi da gudu izuwa gefen ruwan nan domin duba wanne
irin hali Miyurar sa ke ciki. Shin tana haske ko bata yi.
Amma isarsa keda wuya kwatsam ya gano cewa ai babu
komai a goshinsa. Miyurarsa bata nan, ta ɓace ɓat. Babu
ita babu alamunta. Nan da nan fa ya fara haki, harma

yana tunanin anya kuwa shi ne. Babu abinda yake sai
dubawa da yake yana ƙara dubawa. Amma ina babu
Miyura babu labarinta!
***
Wani abu daya faru awa ɗaya kafin isowar Aemad
wannan tsibiri;
Waɗannan mutane guda huɗu dake so su kwace wa
Armad littafin takobinsa suna tsaye suna jiransa. Kowa
aciki yana kawo shawarae yadda za'a gama da Armad kai
tsaye a kashe shi sannan a kwace littafin. Amma bayan
kowa ya gama, sai shugaban nasu ya numfasa ya ce,
"lallai kamar yadda kuka ce kashe shi mu kwaci littafin ba
abu ne mai wahala ba. To amma kun manta da cewa
acikin wannan littafi akwai ƙarfin Izza wanda zai iya jiya
lokaci ya kuma canja zamani? Saboda haka lallai bazan
yarda ɗaukan wani hatsari na faɗa ba, inda litrafin yana
hannunsa. Dukkaninku kunsan mai zai faru idan jikin
takobin wani ya taɓa wannan littafi. Saboda haka mafi
kyawun hanya shi ne mu lallaɓa shi mu karɓi littafin
sannan saimu kashe shi.
***
Sai dai kash, abinda basu sani ba shi ne, a dai-dai wannan
lokaci wani jarumi ma'aboci Izza yana kan wannan tsibiri.
Wanda shi kuma babu abinda yake buƙata face ya hallaka
waɗannan mutane huɗu dake neman yiwa Armad kwace.
Saboda wani tsohon tarihi dake tsakaninsu. Wannan
jarumi ba wani bane illa Ikenga O Bayajidda.
Wanda kuma ya ci gaba da jira ya fakaitansu har sai da
yaga sanda suka shagala suna so suka wasu ɗalasimai su
sawa littafin takobin layar zana. Shi kuma ya fito ya caki
littafin da takobinsa. Yanzu gashi dukkanin su biyar ɗin
har dashi sun ɓace ɓat. Babu su babu alamarsu. Sannan
kuma babban abinda ya shafi Armad shi ne sum ɓace
masa da Miyura. Duk da har a wannan lokaci bai san
taƙamaimai maiya faru ba!!
Nidinne dai Shuraih Usman inkiya
99%
Daga taskar magajin wilbafos
MAGAJIN WILBAFOS
Marubuci: Dr Abdullahi Muhammad Ibrahim
Babi na 29: Jinzidal
Post by: Shuraih Usman
@shuraih 99%
www.facebook.com/hausaebooks
.
Armad na cikin wannan hali su Nusi suka bayyana akan
wannan tsibiri. Inda suka samu labarin dukkan abinda ke
faruwa dalla-dalla daga Armad. Ganin cewa hankalin
Armad ya tashi, babu wanda ya nuna masa cewa rasa
wannan Miyura tasa da yayi abu ne mai kyau ba. Domin

su suna ganin cewa hakan zai sa masu neman hallaka shi
su ragu. Sai dai shi kuma kwata-kwata baya jin tsoron
masu neman nasa ko kaɗan.
Ita kuwa Nusi ta shiga cikin zulumi tunda taji ance anga
mai kama da ita sak.
To a haka dai suka lallashi Armad ya fara gudanar da
horon sa wanda yazo yi tunda fari. Wato fafatawa da
waɗannan halittu masu suna Dordor.
A wannan lokaci da Armad ke fafatawa a tsakanin
waɗannan halittu da akewa laƙabi da Dordor, a can
waɗansu wajaje sauran ma'abota Izza ne da dama suma
ƙoƙari suke suga suma sun nuna kansu a duniya a
wannan gasa da za'ai ta Jinzidal ƙarama (Wadda akafi sani
da Deniziyya kuronikil).
Wasu daga ciki, kamar su Ikenga O. Bayajidda, wanda
idan mai karatu bai manta ba, a lokaci na ƙarshe da aka
ganshi, yana kan hanyarsa ta zuwa garin Denizawa domin
shiga wannan gasa ta Deniziyya Kuronikil, duk da kuwa
akwai ragowar watanni kusan biyu kafin zuwan gasar.
To ko mai yasa mai yasa shi tafiya da wurin??
Amsar dai tana cikin wani daji mai yawan giwaye.
Wannan daji ba a ko'ina yake ba, illa acikin daular
Denizawa ta ƙarƙashin ƙasa.
Kuma ɗaya daga cikin dazuka na musamman da aka
warewa babban ɗan sarki Deniz Iluru, wato Deniz Bizáya,
domin motsa jiki.
Kusan zaka iya cewa duk wata dabba mai rai data rage
acikin wannan daji tsahon lokaci ta daɗe da zama abincin
waɗannan giwaye.
Ko kuma dai tuni sun shige ƙarƙashin ƙasa sun ɓoye
kansu, ko kuma waɗanda suke da sa'a sun shiga rububi
sun guje daga dajin da kyar.
Waɗannan giwaye lallai na musamman ne, domin kuwa
duk da cewa girman jikinsu ya ɗara na da yawa daga
cikin giwaye, jikin nasu bai hanasu yin tsalle mai tsayin
gaske ba.
Misali a wannan lokaci, saboda abinda ke faruwa a ƙasan
wannan daji tsakanin waɗansu mutum biyu, dukkanin
giwayen nan sun yi tsalle sun haye can saman waɗansu
bishiyu masu kama dana dabinon farko. Babu abinda
suke sai hangen abinda dake faruwa, cikin tsananin burin
ɗaya daga cikin waɗannan mutane ya faɗi matacce su
sami abincin buɗa baki.
Koda yake sukan ci wata dabbar idan sun samu, amma a
ƙa'idarsu an gina jikinsu ne kawai domin yin buɗa baki
da naman ɗan adam.
Saboda haka nema wajen ya zama abin so ga Deniz
Bizaya, domin lokaci-lokaci yakan yazo ya fafata da
waɗannan giwaye.
Amma a duk tsahon lokacinsu dashi, basu taɓa ganinsa
yana fafatawa da gaske ba irin satin daya wuce.
Saboda haka nema kaf giwayen nan suka haye bishiyu

suna fatan waɗannan samari biyu su hallaka kansu, su
kuma su sakko su samu na buɗa baki.
Idan ka kallo cikin dajin daga sama, babu abinda zaka iya
hange face mutun biyu a tsaye.
Ɗaya yana riƙe da fafalo-mai-lanƙwasa launin ja. Irin jan
nan mai abin mamaki ta yadda zaka kasa gane cewa
kalarsa ce a haka, ko kuma jinin abokin gabarsa ne yasa
ya zama haka.
Wannan saurayi ba wani bane, illa Deniz Bizáya!
A ɗaya ɓangaren kuma wani saurayi ne, wanda shima
daga saman bishiyun waɗannan giwayen babu abinda
suke iya gani sai doguwar takobinsa dake ta kyalli tana
ɗaukar ido.
Wannan takobi duk da cewa saurayin dogo ne, zaka iya
hangen cewa ta fishi tsayi.
Wannan saurayi ba wani bane illa Ikenga O. Bayajidda!
Kayansu tuni sun daɗe da komawa kalar ƙasa, saboda
azabar fafatawa, kai da gani kasan an kai kwanaki da
dama ana wannan bata kashi.
Sannan kuma abu na ƙarshe da giwayen nan suke iya
hange daga saman, wanda kusan shi kaɗai ne abinda yake
ɗan faranta musu rai shi ne, haki da kowannensu keyi.
Kana gani kasan waɗannan samari biyu sun gaji. Saboda
haka nema waɗannan giwaye suke gani ko su na da rabo.
***
A can daular Infiriya kuwa, wani saurayi ne zaune shi
kaɗai yana ta kuka.
Wannan saurayi yana kan kogin ƙasa ta huɗu wanda ya
haɗe da Bangon arewa, acikin kwale-kwale. A gefensa
kuma akwai wata gawa wadda idan kai mata duba na
tsanaki zakaga cewa suna kama sosai da wannan gawa.
Babu abinda ke fita daga cikin jajayen idanun wannan
saurayi, sai kwalla kawai.
Kana kallonsa bama ka buƙatar a gaya maka cewa
wannan mutun dake kwance acikin kwale-kwalen mai
suna Firius Firesa, makusancinsa ne.
A rataye a bayan wannan saurayi, wani mashi ne wanda
ke ɗauke da wasu rubuce-rubuce irin na da.
Kuma idan ka kusanci mashin sosai, sai kaji kamar daga
daga cikinsa magana ce ke tashi. Wadda kuma kamar ita
ma kukan take!
Wani babban abin mamaki, duk da fuskar saurayin nan a
sunkuye take, sai dai ɗigar hawaye kawai da ake gani,
amma ko motsi bayayi, amma a wannan waje da yake
akwai Dordor sama da hamsin waɗanda bawai ganinsa
ne basu yi ba, a'a tun ɗazu suke nufarsa da mugun nufi,
amma suna kusan ƙarasawa sai kaga sun koma da baya.
Hasalima ƴan mintuna da suka wuce, wani Dordor mai
kai biyar ruwan ƙasa ya nufoshi, amma shima haka ya
juya kamar sauran.
Kayan jikin wannan saurayi na sarauta, amma daga gaba
duk sun jiƙe da hawaye.

Wannan saurayin ba wani ba ne illa Yarima Niyashi, daga
daular Infiriya, garin Shífa.
Bayan kimanin rabin sa'a, tuni a wannan lokaci adadin
Dordor ɗin da suka kewaye shi, ya haura ɗari.
Amma a wannan lokaci ne ya ɗago kansa a hankali, ya
kalli sama, gami da yin ƙuwa mai ƙarfin gaske.
Wannan ƙuwwa na tashi, wani abin mamaki ya faru;
tamkar da wasa wani haske ya tashi daga jikin mashin
nan nasa, wanda yana fitowa wannan ruwa ya fara girgiza
kamar wasu abubuwa zasu fito daga ciki.
Bayan ƴan daƙiƙu, ruwan ya fara ambaliya, amma bisa
mamaki kwata-kwata bai haɗa da kewayen wannan jirgi
ba.
Acikin wannan hargitsi wata murya mai cike da tsananin
ɓacin rai da fushi, kai kace so take ta hallaka duniya baki
ɗaya ta fito daga bakin wannan saurayi, ''ɗan uwa Firius,
kayi ɓangaren ka, yanzu saura nawa!
''Nayi maka alƙawarin ɗaukar fansarka da kuma samun
nasara!!!''
A wani salo mai ban mamaki wannan murya ta ringa
ƙaruwa tana bazuwa ta cikin iska da wannan ruwan da
kuma ƙasa.
Kafin wani lokaci da dama daga cikin waɗanda aka yarda
suji wannan magana suka jita, a ko'ina suke kuwa a faɗin
ƙasa bakwai.
***
Haka dai waɗannan samari dama wasunsu waɗanda zasu
fafata a gasar Jinzidal ɗinnan mai zuwa suke ta shiri baji
ba gani.
A kan doron ƙasa ta huɗu kuwa, a shashin arewa, acikin
wani daji mai ban al'ajabi
Mutane ne sama da dubu a tsattsaye, wasu na kallo wasu,
wasu na tattaunawa cikin raha, kamar suna murnar
haɗuwar tasu.
Babban abin mamakin wannan dajin shi ne, gashi dai
kallo ɗaya tak, zakaiwa wajen kasan cewa daji ne mai
shekaru da dama a duniya, domin iskar dake tashi daga
wajen ma zaka ji daɗewa ta shekaru acikinta.
Amma bisa mamaki babu wani abu daga cikin gimshiƙan
kayayyakin daji a wajen; misali bishiyu, namun dawa, da
dai sauransu!
Babu bishiya ko ɗaya tak a wajen, kuma babu alamun
koda dabbar dawa guda a wajen.
Hasalima idan baka shiga wajen ba, ko kuma kawai ka
hangeshi daga nesa, cewa zakai kurum fili ne, amma kana
zuwa wajen jinin jikinka zai baka cewa acikin ƙasurgumin
daji kake.
Bawai anan abin mamakin ya ƙare ba, idan kuwa da haka
ne to da da sauƙi, amma idan ka ɗauke kewayen da
waɗannan mutane ke tsaye, to zaka fuskanci cewa kusan
ko'ina acikin dajin manyan ramika ne kawai.
Iya ganinka, duk inda ka hanga waɗannan ramika ne

kurum.
Sannan kuma waɗannan ramika kaf ɗinsu idan ka leƙa
baka ganin ƙarshensu, hasalima abinda yazo a tarihi shi
ne, da damansu basu da ƙarshe.
Abin al'ajabi na gaba shi ne, abu ne sananne dama daular
Denizawa a ƙarƙashin ƙasa take, kuma ta cikin waɗannan
ramika ake zuwa can ɗin.
Idan sun yarda kenan!!!
Kuma suma ta ciki suke fitowa suyi mu'amala da sauran
mutanen duniya.
Wanda wannan shi ne ɗaya daga cikin babban abinda
yasa da dama suke tsoron takalar Denizawa da faɗa,
saboda baka da tayadda zaka iya cimmusu.
Domin abu ne bayyananne duk wanda ya shiga ramin
nan bai taɓa fitowa da rai ba.
Babban dalili kuma shi ne, waɗannan rami ka bawai
daular Denizawa kaɗai suka je ba, a'a dama sauran
wurare da suka daɗe da ɓacewa a tarihi, waɗanda saboda
tsananin haɗarinsu, tuni ma aka gogesu a tarihi.
Waɗanda suma duk a ƙarƙashin ƙasa suke.
Kuma babban abinda ke jiran duk wanda ya faɗa wannan
waje shi ne ɗaya daga cikin waɗannan wajaje, idan dai
har ba Denizawa ne suka buɗe buɗe masa tasu hanyar
ba.
Kai akwai wata hikaya ma data daɗe tana yawo a bakin
mutane, cewa ɗaya daga cikin waɗannan duniyoyi da aka
goge na karƙashin ƙasa, akwai wajenda mutuwa da kanta
ke gadi.
To koma dai ba gaskiya bane, kowa yasan babu wanda ya
taɓa shiga ya fito, saboda haka babu wanda yake so ya
kwada.
Shi ne yasa kowa ka gani a wajen yake kaffa-kaffa, duk da
kuwa baƙin Denizawa ne, kusan duk waɗanda ka gani a
wajen.
Mutane ne kawai da suka zo

Please Login or Register in order to submit comment