Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

saiki qirqiro wani abu wanda zaki dingayi wanda zai dinga d'auke miki kewarsa.. Ko kisaka karatu ko kisa waqa, ko kidinga shiga kitchen kina taya momy girki, ko kidinga shiga cikinsu Ramlat ana yin hira dake, koki qirkiri fitta kawai yawan shaƙatawa yanda zaki samu sausauci ko kad'an ne..
Amma alura irin tawa Nagane dukkan way'annan abubuwan duk kin k'aurace musu, bakya ko d'aya sai aikin tunaninsa, kigayamin tataya zaki samu lafiya da sauqin zuciya..
Tayi shuru can tace, "Nagode Ya AHMAD insha Allah zan dinga yin hakan..
Yace "Kinga gobe zan bar gidan nan amma na nafasa saina qara sati biyu naga kinsamu daidaito a al'amuran naki, kafin na tafi, idan naga baki d'auki shawarata ko d'aya ba zan gayama HEESHAM komai kamar yanda baki san hakan..
Tace "dan Allah karka gayamai kaji, insha Allah zanyi yanda kace..
Yace "Naji, yanzu idan yamma tayi ki dafa mai wani abun da kikasan yana so, bashi kuma sai kisan tayanda za'ayi ki bashi....
NUWAIRA tayi murmushi da kallansa kad'an tace, "Naji qarin sanka Ya AHMAD Allah yasa naci gabalaba akan hakan, dan ba qaramar Addu'a zan maka ba, amma bazan iya da HAIRANAH ba, kullum suna tare, "karki damu da HAIRANAH, ni zanyi miki maganin ta, tace "Toh Nagode sosai bara naje najiyo dukkan sirrin abin da yake so da wanda baya so awajen momy, yace "Hakan yayi, idan wani abu ya rikice miki kimin magana, tace Toh da tashi cikin farin ciki tabar wajen, yabita da kallo, ba komai bane kake samunsa a rayuwa ba, yana santa amma tafi buqatar ƙaninsa dashi, dan haka bazai ruguza mata farin cikinta ba...
D'aga wayarsa yayi ya kira Baba Alhaji, yace "Kakana.. Babah Alhajin yayi murmushi yace "AHMAD ya jikin naka, yace "Da sauqi kakana, dama gamana nake sanyi dakai, idan kana da lokaci nazo gida yanzu na gaya maka..
Yace mai "ina jiranka..
AHMAD najin hakan ya kashe wayar tasa da komawa d'akinsa ya d'auke key na motarsa da shafar gefan fuskar MEENATU wacce bacci ya d'auketa tun d'azu daya fitto daga d'akin.. Kana yabar gidan, bai tsaya ako ina ba saina gidan baba Alhaji, nan yaje falansa yako samesa yana yana Jan carbi, kuma shi kad'ai.. Ya qara gaishesa suka d'an tab'a barkwanci, kana yace "Wato Baba abin daya kawoni shine, HEESHAM yajemin da batun zaka d'aurama Hannatu Aure ita da AMAAR...
Babah ya tashi da murmushi yace "eh harda Ramlat da SABEER, dan d'azu muna gaisawa da SABEER d'in nake ce mai waya gano adangi yace min Ramlatu, dan haka tare za'ayi Auran nasu.. Sannan zamma mutumina gata na had'atasa da mutuyarsa HASEENAH dan naji labarin suna Soyayya sosai agun mahaifiyarta...
AHMAD yayi saurin katse shi da cewa, "Wai kana nufin HEESHAM, Yace "shi mana, AHMAD yaja numfashi yace, "Toh nidai a iya Sabina dai basa Soyayya kamar yanda kake tunani, amma dai ka tambayesa, yace "Zan tambayesa dan kasan atsarin had'a aurena sainaji tabakin kowa tsakanin namjin da macen, idan suna san juna toh idan basu so saisu qara dubawa adangin, Yauwa natuna da kuma HAIRANAH da Hashim, dan Hashim d'in yazo min da batunta shima, yace ba ƙaramar Soyayya suke zubawa ba..

K'arashen zancen Baba Alhajin ya b'ata ran AHMAD d'in, jin batun Hashim da HAIRANAH, ashe shiyasa yaji Hashim din shuru, ashe yazo ya lafe awajen Baba Alhajin ne, gaskiya bazai so HAIRANAN ta Auri Hashim d'in ba, dan yafi kowa sanin waye shi, bayan zinace zinace da yake aikatawa har da shan giya a al'amuran nasa...

Nan take AHMAD d'in ya manta da abin da zai gayama Baba Alhajin, ya sosa qeya yace da shi, "Dama dama... sai kuma yayi shiru,.. Ganin hakan yasa Baba Alhajin yin murmushi da dafa kafaɗarsa yace "Gayamin AHMAD menene, baka tab'a zuwa min da magana ba, ina tabbatar maka zan saurareka dakyau bazan baka kunya ba..
AHMAD yaja numfashi duk kansa ya kulle ya manta komai dazai gaya masa, sanadin jin batun HAIRANAN sai kawai ya b'ige da cewa, "Dan Allah Baba Alhaji ka qara d'auramin Aure da HAIRANAH, kuma bana san kowa ya sani sai aranar da zaka had'a Auran danasu Hannatu..



Babah Alhaji najin haka ya ƴalƴale da dariya yace, "Amadu kenan, yanzu kai ko tarewa bakayi da amaryarka ba amma dan zalama kana hangen wata, watan kuma wacce ɗan-uwanka yake sO..
AHMAD ya kallesa da damuwa yace, "Wallahi Baba Alhaji Sam HAIRANAH bata dace da Hashim ba, ni nasan waye shi, kana da sanin bashi da aiki sai yawan shashanci da matan banza, ga ƙarya dan ko kad'an basa wata Soyayya shi da ita..
Dama fa nine nake santa, kuma na gaya masa kan ya rabu da ita bazan bari ya b'ata mata rayuwa ba, Dan Allah Kakana katemakeni kaban HAIRANAH Nidai dan Allah...

Babah Alhaji yaja numfashi yace, "Bazan hanaka ita ba AHMAD idan har na tambayeta tace min kai take so, amma idan har tace Hashim take so zan bata shi, dan ba mamaki tazama silar gyaruwarsa, amma idan tace tana sanka zan Aura maka ita aranar da zan d'aura Auransu Hannatu sa yardar Allah..
AHMAD ya saki murmushi yace dama "Amincewarka nake sanji, bana fatan kace aa dan baka dad'e da d'auramin Aure ba.. Naji dad'i sosai, insha Allah idan ka tashi had'a mitin HAIRANAH bazata zab'i kowa ba sai ni..
Murmushi yayi mai da cewa, "Toh ka kwantar da hankalinka, dan ayau idan kace mata uku zaka qara atake idan suna sanka zan d'aura maka Aure dasu, danna yarda da hankalinka da kuma nutsuwarka nasan zaka iya dasu..
Murmushin dai AHMAD ya qarayi da tashi yana saka takalminsa yace, Da zaran ka tsayar da ranar mitin d'in kafa sanar dani.. Yace "karka damu zan sanar da kai d'in...
Shiga cikin gidan yayi ya gaisar da matansa, sai kakarsu AHMAD d'in tahau yimai tsiya wajen cewa shi baya zuwa imba mitin Baba Alhaji ya kira ba, dan haka ita tafiyin mijin da HEESHAM dan yafi bata kuluwa, murmushi kawai AHMAD d'in yayi mata dayi musu kyauta yabar gidan...
Sanda yakusa dawowa gida ya tuna ainihin abin daya kaisa gidan Baba Alhajin, amma batun HAIRANAH ya shafe masa komai, tsaki yaja kawai, dan bazai iya kumawa ba, dama batun HEESHAM da NUWAIRA zaimai...
Yana shiga gidan yaga MEENATU tana safa da marwa da alama tana neman wani abu ne, amma tana ganinsa ta sakar mai fara'a, saiya zuba mata ido yana tuno fuskar HAIRANAH da had'ata da tata..
Babu had'i ko kad'an, dan HAIRANAH tafi MEENATU kyau nesa ba kusa, amma itama tana da nata kyan daidai gwargwado...
Ganin ya fitto daga motar tasa yasata cewa, "Wlcm sweetheart, kasa sai nemanka nake, sam ban lura da babu motarka ba! sai yanzu dana ganta, ya sakar mata murmushi da cewa "Toh gani kin gannin fatan dai komai normal..
"Eh, komai normal, dama momyna ce tace na tambayeka yaushe zamu tare agidammu.
Yace "Zamu tare amma ba yanzu ba.. Nan tayi saurin qara tsaida kallanta akansa tace, "ba yanzu bafa kace, ina ka samu sauƙi, yace "Eh da sauƙi, amma ban gama jina normal ba, Sannan akwai wani shiri da nake ma kaina..
shuru tayi mai kawai... Daidai nan HAIRANAH ta fitto daga cikin gidan da wata uwar kwalliya, tayi kyau sosai cikin shigar riga da siket na atamfa me kalar ruwan malmo amma ba turarreba, (purple) haka jaka da takalminta da gyale duk kalan atamfarne, sai zuba k'amshi take, fuskarta ba wani makeup banda jambaki data saka me kalan kayan nata.. Kallo d'aya tamusu tad'auke kanta, ta rasa dalilin dayasa bata san tagansu atare.
AHMAD ko sanda gabansa ya fad'i dan ganin kwalliyar tata, duk wani namiji me lafiya idan ya ganta dole yayi sha'awar tazama mata a garesa. Haka kawai yaji ransa ya b'aci sosai da kwalliyar tata.

Itako yawan shaƙatawa zasu ita da Ramlat, haka kawai yau take sha'awar san shaƙatawar, saita gayama Ramlat d'in, tace Toh tashirya suje wani gu.. Hakan yasa yanzu take tsaye tsayuwar jiran fittowar Ramlat d'in wacce batasan meya tsayar da ita ba, dan tare suka fitto daga d'akin momy.

Taja tsaki da ƙara kai kallanta kansu AHMAD d'in, sai MEENATU ta galla mata harara, itamako tarama babu b'ata lokaci, MEENATUN tayi kwafa daidai lokacin kuma wayarta tayi ringing, tana dubawa taga momynta ce, hakan yasa ta kalli AHMAD tace "Minti biyu pls, saiya d'aga mata kai alamar babu komai, sai tayi wajen shaƙatawar gidan..
AHMAD ya maida kallansa kan HAIRANAH da galla mata wata shegiyar harara yace "Jira kike na gaisheki, saita murgud'a mai baki tace, "Toh gani nayi kana tare da matarka, kuma ni ba shiri nake da ita ba, kalan na gaisheka ta canja min manufa, shiyasa ban gaisheka ba..
Ya cije leb'anta kad'an haka👌🏻 dan jin muryarta, alamu ya nuna bazaiyi missing komai na NUWAIRA ba, dan muryarsu tana shigen kama, yaja numfashi da cewa "Zonan..
Ba musu ta qarasa garesa, ya kalleta daga sama har qasa yaci gaba da cewa, ina zakije, tace "Yawan shaƙatawa ni da Ramlat, yace "Toh bazaki ba, ta kallesa dakyau kallan harara tace "Akan me, yace "Akan na isa, tace "Ni dai gaskiya ina san zuwa, Yace "Hmm ki kuskura ki fitta daga gidan nan ba abin dazai hanani karyaki kamar yanda kika karyani.. Yana gaya mata hakan yayi shashinsa,
Sai kawai tasaki jakar hannunta ƙasa, tsoro ya kamata, dan gaskiya bata san abin dazai tab'a mata lafiyar jikinta, kuma tasan zai iya aikatawa, dan ba mutunci garesa ba, idan bata manta ba tana gadan asibiti ba lafiya ya d'auketa da mari, wannan tunanin da tayi yasa tsoranshi ya qara shigarta, dan ita arayuwarta gabaki d'aya bata tab'a jin zafin Mari kamar nasa ba, mamanta tana marinta da babanta amma ji tayi nasa na musamman ne..
Yanaji ta window nasa da Ramlat ta fitto tana ce mata tafasa zuwa, Ramlat ta kalle da mamaki akan fuskarta tace "Meyasa kika canja ra'ayi, tace "YA AHMAD ne yace karna fitta, kuma kinga idan na fittan K'aramin wannan Marin nasa zaiyi..
Ramlat tayi dariya tace, "Nidai ko Yaya yana ciki ne, HAIRANAH ta waro ido tace, "La La La, rufamin asiri, bayan bazan iya dashi ba kullum sai munyi fad'a da matarsa dan Sam jinina bai had'u da ita ba..
Tace "Gaskiya ne, bake kad'ai ba HEESHAM ma jininsu bai had'u da ita.
Tace "haka yace min..

Shuru AHMAD yayi, sai yanzu yaji wani iri aransa haka, meyasa HAIRANAH bata san MEENATU... Haka me yasa yake hango tsanar HAIRANAN akan fuskar MEENATUN..

Ramlat ce ta katse masa tunani wajen cema HAIRANAN "Toh muje wajen mama dan gaskiya bazan koma cikin gida ba, HAIRANAH tace, "Hmm Umm, aisai dai ki tsaya na kira miki Aunty NUWAIRA kuje tare, dan gaskiya na tsorata da YA AHMAD d'in naku, bana san ya karyani..
Ramlat tace "Karyawa kuma,😳.. Cikin sauri HAIRANAH ta gyara zancenta da cewa "Ina nufin karna qara shan wani Marin nasa, bara naje na kira miki NUWAIRA minti d'aya.. Ta kai qashen zancen da saurin shegewa ciki, aiko cikin d'aga murya Ramlat d'in tace "Barta na fasa zuwa zani kawai gidan qawata, Toh HAIRANAN tace mata daga can ciki..

Kana Ramlat d'in tama motar ta key, dan ta tuna yanzu fa mamansu HAIRANAN surukarta ce😂..

MEENATU ko har lokacin tana waya da momynta bare tajiyo su.. Gaya mata take wai AHMAD d'in yace ba yanzu zasu koma ba, nanko momyn nata yahau fad'i, dan tana so ne sukarb'i key akwai wani binne binne da zasuyi agidan kafin shigarsa gidan. Haka dai MEENATUN take bata hakuri kan zatayi k'ok'arin shawo kansa..

HAIRANAH ko kwanciyarta tayi da bud'e Data dan taga wane hali Yanar gizo take ciki..


Lokacin NUWAIRA tana tare da Momy sai d'auko mata maganar HEESHAM take a hikimance, tana jin me yafi so miye baya so, haka momyn bata ganeta ba tadinga bata amsa.. Itako NUWAIRA tana nad'ewa a kwakwalwarta, can Momyn tace, "A kuma abinci HEESHAM yana san cin sakwara da miyar ganye.. Farin ciki ya cika zuciyar NUWAIRA tace, "Wayyo momy kinsa naji kwad'ayinta, dan Allah kibarni nayi mana ita yau..
Momy tayi murmushi tace, "Na rigada na gama tsara abincin yau NUWAIRA amma fa idan kinji tashiga ranki da yawa kiyi kayanki, ina da komai na had'ata, dan Dadynsu ma yana so sosai, amma idan zakiyi kiyi kicinku keda HEESHAM, kuma karkuzo dining ci, dan bazaku hana mijina cin abin dana girka masa ba..
Farin ciki ya cika NUWAIRA sosai tama hannun momyn kiss, kana tace "bamu baci akan idan Dady, Nagode sosai Momyna..

Murmushi kawai momyn tayi, nan NUWAIRA tad'auko Doya dan aiwatar da sakwarar...
Ƙarfe biyar da rabi tagama komai, nan ta shiryama HEESHAM d'in abin gwanin ban sha'awa, dan ta had'a mai da lemun gwaiba, bata bari kowa yaga yanda ta shirya mai ba, ta b'oye a nan dai cikin kitchen d'in... taje tayi wanka har tayi makeup HEESHAM d'in bai dawo ba, Yau ya wucce lokacin dawowarsa.. Tana cikin maganar da zuciyar tata ne taji shigowar motarsa, aiko nan take gabanta ya fad'i, saitatashi tayaye gefan labulan windown nasu tahau leqansa, shine dai dan gashi ya fitto cikin kyakkyawar shigarsa yana me kallan Agogon hannunsa, nan ta lumshe ido ta bud'e, sanshi ya qara cafkar zuciyarta...
Kallan windown yayi kamar zaiyi aiko cikin sauri ta sake labulan tare da jingina bayanta da bango tana sauke numfashi, kana ta fitta daga d'akin tayi kitchen dan d'auko mai komai hidimar tasa

Shiko ya lura ana yawan lek'ansa ta windown, toh waye yake mai hakan a cikinsu.. Ganin bashi da amsar tambayar tasa shiyasa shi yin cikin falan dan duba Momy dan yau kuma dasan ganinta ya dawo, saidai ya karyo kwanar da zata sadashi da gefan room na momyn kenan NUWAIRA tazo wucce ta wajen da farantin sakwaran nasa a hannunta, sai yad'an bigeta kad'an a rashin sani, aiko nan tayi baya kamar zata fad'i, nan tayi saurin cewa "Wayyo Allah miyar sakwara karki zube...😂 Aiko da sauri ya kama hannayenta dukka biyun ya jawota, sanda ya tabbatar da tsayuwarta kana ya saketa yana cewa "Sorry Auntii na kusa yi miki b'arna..

Aiko GAM ta rufe idanta, dan batayi tunanin shi bane.. Saiya karb'e farantin daga hannun nata yaci gaba da cewa, idan ba na momy bane muje na rakaki inda zaki kai...
Bud'e idanta tayi jikinta nasan fara rawa tayi gaba ya bita a baya bata tsaya ako ina ba sai'a ƙofar d'akinsa, ta kallesa kad'an da kallan kofar tasa, ya gane me take nufi, dan haka ya kalli gefan wadansa na dama, ya mata sigina alamar taciro key d'in d'akin nasa, saiko ta saka hannunta tad'auko kin ta bud'e d'akin kana ta maida masa ajjihun nasa Sannan ta karb'i farantin daga hannun nasa tace, "sakwara nayi, shine na zuba maka naka dan momy ta gaya min ba qaramin so kake mata ba, ina rokwan Allah me kowa me komai yasa bakaci wani abu kafin shigowarka gida ba, dan ina san naga kayi mata ci na hak'ika hakan zaisa naji araina nasamu ladanka...
HEESHAM ya lumshe ido, muryarta dadad'i, kuma yanzu zai gaya mata, yana bud'e idan nasa ya sauke akanta da sakar mata murmushinsa me qara jefa mata sanshi da ƙaunarsa yaja numfashi... "Subhanallah, Gaskiya ke cikakkiyar me wayo ce wajen kwasar lada me tarin yawa cikin hanya me sauƙi, bazan b'oye miki ba? naji mafificin farin ciki sosai araina wanda banyi tunanin zanci karo dashi a wannan lokacin ba, yakai ƙarshen zancen da karb'ar farantin yana meci gaba da cewa, Nagode sosai Auntii NUWAIRA, Allah yasa ka, Sannan gaskiya muryarki tana mun dad'i sosai fah..
Murmushi tayi da bud'e sakwarar da miyan, tasa cokali ta gutsuri kad'an haka👌🏻 da dangwalar miyar tana cewa, "dan Allah na fara baka sau d'aya kafin kaci da kanka.. Takai ƙarshen zancen dakai masa baki, aiko ya karb'a da lumshe ido.. Sanda ta rufe da ajiye cokalin, kana ya bud'e idan nasa cikin matuƙar jin daɗin sakwarar yace.. "Gaskiya idan dai ban manta ba ban tab'a cin sakwara me daɗin wannan ba..
Tace "Nidai idan kaci ka ƙoshi ka yabamin a waya, ban yarda kakwana ba tare danaji yabawar taka ba... Tana faɗin hakan tayi gaba abinta, ya bita da kallo, tayi mai kyau sosai, yaushe raban daya ganta warau haka, qila abin da yake damunta tasamu sauƙinsa ne yau.. Ya faɗi hakan aransa da shiga d'akin nasa....

Wanka yayi lokacin ana kiran sallar magrib yaje yayi sanda yaje ya gaida momy da AHMAD kana ya koma d'akin nasa da d'okin cin sakwarar..
Aiko yacita sosai danda gaske tayi mai dad'in, dama HAIRANAH da NUWAIRA babu lefi sun iya girki, mamansu tun suna qananu tanuna musu iya girki ba qaramun abu bane agun y'a mace..
Shidai baida number nata, dan haka ya fitto falan momy yaga duk suna nan amma banda ita NUWAIRAN, ya kalli HAIRANAH yace, "Qawa ina Auntii NUWAIRA, tace tana can ad'aki kamar mayya, yayi murmushi da d'aukar wayar HAIRANAN yacire Num na NUWAIRAN zai juya da niyar komawa Hannatu tace, "Nidai ban tab'a ganin budurwar HEESHAM ba, HAIRANAH tace "Ke ni ce fah.. Momy tayi murmushi tace "Allah yasa..
Ai cikin sauri tace "momy yana da budurwarsa fah, na faɗin mata hakan ne kawai dan tsokana😂 ko kun manta da HASEENAH ne...
Dukkansu kwashewa da dariya sukayi, Ramlat tace "Bana tunanin Soyayyar gaskiya suke shida HASEENAN, dan basa gaba basa baya, Hannatu tace, "Nima dai ya tab'a gaya min wata ranah cewa bafa Soyayya suke ba..
HAIRANAH tace, "Hmm, fahimtarsu ne bakuyi dakyau ba, amma ina tabbatar muku Soyayya me zafi sukeyi...
Shidai HEESHAM murmushi yayi dayin gaba abinsa, yana shiga d'akinsa abokinsa Jabeer ya shigo.. Jabeer abokin HEESHAM d'in ne tunna k'uruciya, HEESHAM d'in nasansa ganin san dayake masa, shiyasa koda ya dawo daga karatu bai wani tsaya b'ata lokaci ba yaje ya nemesa, HEESHAM bashi da yawan abokai, Sam bashi da wani yarda da mutane sosai, tunda wannan abokin nasa ya mutu baya abota sosai da abokansa sai Jabeer, gashi da farin jinin fans amma ko kusa baya yarda su shigesa sosai, irin dai kadaram kadaham d'innan, shima kansa Jabeer d'in sanda yayi da gaske yasamu kan HEESHAM d'in, shima doctor yake san ya zama, bai gama nasa karatun ba, amma idan ya gama AHMAD yace mai zai d'aukesa a asibitin nasa..
Kwana biyu baya nan ne yaje qauye ganin kakaninsa, jiya ya dawo, Wannan shine Jabeer

HEESHAM ya kallesa da cewa, "Wow d'an uwa wannan wanka haka, Jabeer ya kalli kansa tabbas yasan ya bada kala yace "Wata zazzafa nayi, shine nake san ka rakani wajenta.
"Kakoci sa'a banda komai a gabana, muje kawai, haka suka fitto har sun shiga mota Jabeer d'in ya tsaida HEESHAM wajen cemai bari ya gaida momy..
Momyn na ganinsa tasaki murmushi tace, "Andawo daga qauyen ne, Jabeer yayi "Murmushi yace, "Jiya na dawo HEESHAM bai gaya miki ba, tace "qila ya sha'afa, yaka baro kakannin naka, yace "suna lafiya sunce a gaisheki, tace "Ayya ina amsawa, yace "Toh bara mud'an fitta, tace "kudawo lafiya, ka kuma gaishemin da momynka, Toh yace mata da tashi yabar falan..

NUWAIRA najin tashin motar Jabeer d'in, takira AHMAD awaya, lokacin yana tare da matarsa suna kallan wani Amekan film, ya d'auki wayar tata tace dashi "Hello Ya AHMAD barka da dare, yace "Barka dai, kin yini lafiya, tace "Lafiya lau, dama nakiraka ne na gaya maka komai daya faru, yace "Gud.. Ina jinki, Nan batare da b'ata lokaci ba ta kwashe komai ta gaya masa, taqara da cewa, "Yanzu me kuma zanyi mai gobe, sauke kan MEENATU yayi daga kan cinyarsa ya tashi da fitta daga falan nasa yace "Idan har kinyi sakwaran tayi dad'i sosai nasan bazai kwanta batare daya kiraki ba, gobe kuma abin daza kiyi shine tambayar momy a hikimance me yafi so na breakfast, Sannan kisa mai ido sosai kiga Yawan yanda yake ci..
Daga wannan lokacin sai kiyi qoqarin basa kulawarki cikin sauƙi.. Kinga idan kikaci galabar b'atasa da duk wani abun ci naki na tabbatar zaki zama abar hirarsa, wannan shine, sai gobe kuma na d'ora miki wasu abubun da fatan kin gane, tace "Nagane na kuma gode sosai, yace "karki damu..
Sallama tamai sai ya kashe wayar.. Yana lura da MEENATU na leqensa, daya koma falan nasa yace da ita "Ki kwantar da hankalinki ba da budurwata nake waya ba, tawa budurwar fad'a ne tsakaninmu..
Saita ja numfashi da cewa "Dan Allah Ya AHMAD karkamin kishiya.. Murmushi yayi mata kawai da jawota jikinsa...


Aiko kusan qarfe goma da rabi da HEESHAM ya dawo kiran NUWAIRA yayi, lokacin taja bargo jikinta kenan taji wayar tata na qara... Tana dubawa taga HEESHAM d'in ne, sanda ta saki murmushi kana tad'auka da cewa "Hello... "Gaskiya Auntii kin iya girki sosai, dama ace gobema kiyi wani abun ki sammun, murmushin jin daɗi NUWAIRA tayi dajawo fillo jikinta tace, "kawai ka gaya min me kake so nayi maka goben..
Ya sauke numfashi da cewa "Waike muryar taki ko'a waya ma dad'i ne da ita, tace "karka wani b'atar min da zance na kawai ka gaya min me kakesan ci gobe, murmushi yayi yace "bansan na baki wahala, dan haka komai kikayi zanci dan zai gamsar dani..
Tace "Toh Allah ya kaimu..
Yace "Ayi bacci lafiya
Tace "Kaima haka...
Sai suka ajiye waya a tare.
Zuciyarta cike tam da farin ciki, yau dai zatayi baccin farin ciki....

Aiko tana idar da sallar asuba tayi kitchen, Agada ta jawo ta yanka, bayan ta soyata saita dawo ta qara soyata da kwai me kayan had'i, ta had'a lafiyayyan ruwan khaima tie kana ta had'a jinjilisfil had'in y'an me duguri, kuma duk abin da tayi me yawa tayi dan bata san yau momy tayi aikin sosai, tana kan yin wanke wanke ko momyn ta shigo kitchen d'in, kallo d'aya tama abubun da NUWAIRA ta had'a tasaki murmushi, tace, "Sannu da aiki y'ata, tace " Sannu momy, barka da Safiya, tace Barka dai, yau kuma anrigamu shiga kitchen d'in ne, NUWAIRA tayi murmushi da cewa, "nayima HEESHAM alqawari ne kan zan had'a masa breakfast, kasancewar ya yaba da sakwarar jiya, momy tace "Aifa aiki ya sameki, badan kin jama kanki ba, yanzu me rabaki dashi sai Allah.. NUWAIRA ta tsame hannunta daga ruwan wanke wanken tace "babu komai momy, duk wani aiki da zanyi ayanzu na d'an wani lokaci ne, ina san koda na tashi barin gidan nan ya zamana nabar kowa da kewata, nabar kowa da tuna wani kyakkyawan abu da nayi masa a rayuwa..
Momy tayi murmushi tace "Masha Allah, Allah ya shige mana gaba, yanzu bara nayi farfesun kaza tunda naga kinyi komai a wadace.. Toh NUWAIRAN tace mata, Sannan tayi bedroom nasu yin wanka...
Su HAIRANAH ko tunda sukayi sallah komawa baccinsu sukayi..


Shiko HEESHAM d'in tun asuba ya gaida iyayan nasa da Yayansa, yanzu haka ya gama shirinsa na fitta ne, breakfast ne kawai ya rage masa..
A dining yaga kowa, ya zauna kusa da Momy, yana kallan komai dake kan dining d'in, yace "Wow, momy waya had'a wannan breakfast d'in..
Momy tayi murmushi tace "NUWAIRA ce, kuma bakaji yanda yayi dad'i ba, saiya kalli NUWAIRAN da cewa, "Gaskiya Auntii kinyi, tunkan naci zan fara gode miki dan nasan dole yafimin dad'i fiye da kowa anan.. Nagode Nagode sosai..
Murmushi NUWAIRAN tayi kawai...
Dady yace "Gaskiya tayi qoqari sosai, Ramlat tace ba d'an kad'an ba Dady...

Momy tatashi ta sakama HEESHAM d'in daidai yanda tasan zai iya ci, NUWAIRA na kallo, sanda taga farin cikinsa ya qara yawa sanadin faraci da yayi Sannan tatashi tabar gun, kuma kai tsaye can harabar gidan tayi, Kawai tsayawa tayi tsayuwar jiransa ya gama taga fittarsa akan idanta, hakan zai mata dad'i sosai...
Aiko tad'an b'ata lokaci sosai bai fitto ba, sai AHMAD ne ma ya fitto daga shashinsa ya kalleta tagaida shi, Yace "mutumin bai fitta ba, tayi murmushi da cewa, "Yana ciki yana breakfast, kasancewar nayi mai abin da yake so bakaga nuna farin cikin da yayi ba, gaskiga Ya AHMAD ina MASIFAR SON HEESHAM sosai, kuma zanyi mai komai dan ganin farin cikinsa, daga yau duk wani abu nasa naci zan d'aukema momy shi, Saidai bana san momyn tagane halin da nake ciki, yanzu ya zamuyi, AHMAD yayi murmushi yace, "Sam momy bazata ganeki ba, dan zatayi tunanin shine yake saki yimai ke kuma kikaqi gaya mata, yanzu idan kika samu galaba akan b'atasa da cimarki, karatunmu na gaba shine zan kawo miki novel na ciwukan dadama wanda ya shafi aikinsa, sai kice mai kina san kisan meke kawo wayannan cututtuka ajikin ɗan-Adam, idan har ya yarda ya fara biye miki wajen fahimtar dake Toh dole zaku fara samun shak'uwa da juna, awannan

Please Login or Register in order to submit comment