Join Our WhatsApp Group

Idan ku ka ga kun taba wani wuri ya fitar daku a shafinmu, sai ku danna back kuyo baya, ku sani yanzu muna amfani da tallan Popunder a shafin, so karatu zai muku dan wahala, amma ta hakanne kadai zamu iya cigaba da rike shafinnan. idan har bakwa son talla sai kuje ku yi subscription na shafinnan akan karamin kudi ku runga downloading kawai. SUBSCRIBE


DOWNLOAD

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register
DOWNLOAD

buqatar taki, amma sai kin bamu had'in kai..
Tace "Toh zanzo, kuma da shirina zanzo..
Haka suka bar gunsa kowa da abin da yake tunani aransa, ita dai Halima tana da manufa akan MEENATU shiyasa bataja ba takawota wajen wannan boka, ita kuma MEENATU tunaninta yanda zata tare da bokan take, ba abin da yake yi sai wari, daga ganin zai iya kaiwa wata shidda baiyi wanka ba, gaskiya a tsafta irin tata anya zata iya tarewa dashi kuwa, gashi daga dukkan alamu shine zai biya mata buqatarta, dan bai wani kawo mata k'auli da ba'adi ba, anya zata iya barinsa kuwa, kai zadai ta zauna tayi tunani..

Suna kan hanyar tasu ta dawowar ne Haliman ta akalleta cike da kulawa tace, "Wallahi Ƙawa kin ban mamaki, wai ace bada kai ne bazaki iya ba, minti nawa ne anyi an gama, haba sai kace ba wacce take neman cikar burinta ba, har yaushe zaki bari HAIRANAH ta dinga juya miki miji, har yaushe zaki bari AHMAD yata qara dilmiya akan santa da ƙaunarta, gaskiya nidai ina mace ba wata mace y'ar uwata dazan bari da mijin Aure na, dan yanzu ba'a yayin hakan, daga ni sai mijina da yarana, amma zama da kishiya sai in naso..

Nan kan MEENATU ya qara kunbura, tace "Haba Ƙawata, kwantar da hankalinki zan basa abin dayake so ne, amma gaskiya sai nayi tunani...
Halima tatab'e baki cikin jin haushi tace, "dan Allah kar ki qara cemin na rakaki wani waje ba tare da kin shirya ba, mutumin yana ganin mutuncina amma kin wani kama kin zubar min dashi, gaskiya Ƙawa bazan b'oye miki ba Kin ban haushi.
MEENATU tadafa kafaɗarta tace "Kiyi hakuri, nasani, yanda na baki kunya ayau bazan tab'a yarda naci gaba da bama kaina kunya ba, dan zama da kishiya abin kunya ne, kamar yanda kikace ne, an dena yayin hakan, ke dai kiban lokaci kawai..
Tace "Toh kin d'auki alƙawarin zamu koma, tace "Yes, me zai hana...
Cikin jin daɗi Halima ta fitta daga motar MEENATUN tana me kama kumatun Abdul tamai wasa kana tabarshi tashiga d'agama MEENATUN hannu alamar bye bye danta kawota har ƙofar gidansu ne.
Haka dai MEENATUN itama ta d'aga mata nata hannun dajan motar tata, sai Haliman tabita da kallan manufa...


Direct gidansu MEENATUN ta nufa, dan tana san neman shawarar HASEENAH, aiko HASEENAN tana gida kamar yanda MEENATUN tayi fatan hakan, nan babu b'ata lokaci ta gayama HASEENAN komai, aiko babu batun b'ata lokaci HASEENAH tabata goyan baya, tana nuna mata babu komai dan kana neman biyan buqatarka an baka sharad'i, kawai kabi idan har da gaske kana san biyan buqatan naka.

MEENATU tayi shuru, ba abun da take tunawa sai munin bokan da kuma warinsa, duk da HASEENAH tabata goyan baya amma zata qara nazari🤨 ( Rahama Nalele dai tace tabi a hankali)

HASEENAH tayi dariya tace "Wai tunanin me kikeyi ne, MEENATU tace "No is owkie, wai ya batun shirinki akan NUWAIRA ne, tace "ai kibar kaza acikin gashinta, zakiga abin dazai faru nan kusa, wallahi saina wargaza farin cikin HEESHAM da nata kuma nasamu cikar burina, badai kin raina aikin malami na ba.
MEENATU najin hakan taja tsaki da tashi ta sab'a d'anta a baya tana cewa "ai badai bane, kawai na raina aikin nasa ne,
HASEENAH ta sheqe da dariya tace " Aunty MEENATU kenan, zaki gani ganin idanki..






Bayan kwana uku....
Ayau Laraba da misalin qarfe tara NUWAIRA ce taketa ma HEESHAM magana akan ya tafi office, sam yaqi tafiya sai kula yaransa Ameer yake yi, wanda a Yanzu yayi wayo har qiwa ya fara, dan idan yana tare da HEESHAM sam baya zuwa wajen NUWAIRAN, yanzu ma sam yaqi zuwa wajenta, shiko HEESHAM d'in sai biyemai yake..
Data gaji saita zuba musu ido kawai tana kallansu, jin tayi shuru yasa HEESHAM kallanta yana cewa, "Luv, yau bana san zuwa office kwata kwata, haka kawai bana san barinki, dan ban san me yasa naji gabana na faruwa ba, bana san abin dazai tab'amin lafiyarki, wallahi NUWAIRA ina sanki ina MASIFAR sanki... Yakai qarshen zancen da ajiye Ameer d'in akan kujera ya matso kusa da ita yana me zuba mata ido.
Cikin sanyin jiki tace "Haka kawai na tsinki kaina cikin fad'uwar gaban jin waƴannan kalmomin naka, dan Allah luv karka barni, Wallahi idan ka barni bazan tab'a iya rayuwa ba, takai ƙarshen zancen da zubo da hawaye, hawayen da zuwa kawai sukayi wanda bata san da zuwansu ba.
Nan ya kama fuskar ta, ya shiga lashe mata su cikin so da ƙauna yace "wannan hawayen na miye my Auntii, baki san naji zafinsu har cikin raina ba, tace "Kawai kamin alkarin baka ba barina aduk halin dana tsinki kaina, yace "Nayi miki alƙawarin bazan tab'a barin ki ba luv, aduk halin da zaki shiga ina tare dake, bani ba barinki har iya ƙarshen rayuwa, amma idan kikaci amanata! da gaske zan barki da Allah ne kawai yamin sakayya, tace "Bani bacin amanarka, Allah yamin tsari da hakan akan komai wanda ya kasance mallakinka ne..
Yace "Na yafe miki matata, kafatana ki qara sona, tace "Dama ai ni'ce na faro, nayi maka alk'arin insha Allah ba wata Soyayyar wani abu da zata qara shiga raina, daga ta iyayenmu saita taka data yaranmu saita y'an uwammu, dan Allah ka yarda da san da nake maka da gaske bashi da iyaka agareni..
Yace "na yarda..
Tace "Amma yau baka ba zuwa office ko
"Naso hakan, amma tunda mukayi waƴannan kalaman nad'an samu qarfi a zuciyata...
Kiss ta sakar mai da cewa "Baka tab'a kaiwa tara a gida ba, yace "sai Lokacin da nake Ango ko..
Murmushi tayi, cikin jin kunyar amsar tashi, ya gane hakan dan haka saiyaci gaba da cewa, Luv ya dace ayanzu ki gama gane halin mijinki, tace "Wallahi ba wanda yafini saninka a yanzu, yace "Toh jin kunyar na miye..
Tace "kawai ta sabo ce, "Owkie, zanyi maganinta kuwa.. Ya kai ƙarshen zancen da tashi, kana ya sunkuya ya sakar ma Ameer kiss wanda yake musulmusul irin na yara, kana yaci gaba da cewa, "Ina sanka Boy, ina ƙaunar ka yarona, Allah ya raya min kai, idan kuma kai ba rayayye bane ya bani wani kamarka wanda zai zamo alkairi agaremu fiye da alkairinka..
NUWAIRA tace "Yau ina k'irgawa, ka fad'i hakan sau shidda kenan, tun aihuwarsa.... Gaskiya nima na fara tsorata da ƙaunar da muke masa, kuma da gaske nafika sanshi, HEESHAM yayi murmushi yace "Allah nafiki sanshi, kidai kula dashi karya fad'o ni nayi nan.. Yakai ƙarshen zancen da d'aukar key nasa da wayarsa dama laptop nasa yau na mota tun jiya bai fitto da ita ba hakan yasa ya fitta daga falan..
Saita d'auki Ameer d'in tabi bayansa tana cewa "kasan dai dole mu biyoka rakiya ko.
Kanta fitto har ya shiga motar tasa ya tadata, a bakin ƙofar falan nata ta tsaya tana mai bye bye, aiko har kusa dasu yazo da motar tasa ya zuge gilashin motar ya sakar musu kiss da hannunsa yana cewa "bye bye my Auntii my Luv my blood..
Cikin matuƙar jin daɗi tace Bye Luv, Allah ya bada nasara akan dukkan aiki..
Yace "Ameen my dear..

Daga haka ya fitta daga gidan me gadi kuma ya kulle.
NUWAIRA takoma ciki, alama dai ta nuna su uku kenan suka rage a gidan, ita da yaranta sai me gadi cikwan na ukun, dan Zuwaira batazo ba, amma yanzu tana kan hanya, dan goma take zuwa...



Goma da minti goma sha takwas da sakwan talatin da tara gaban HEESHAM ya wani tsinke ya fad'i, nan take wata damuwa tabi ta dabaibaye sa wacce bai tab'a jinsa acikinta ba, yana ganin tun yana yaro daya kamu da ciwan ZUCHIYA rabansa dajin shigen irin wannan yanayin...
Nan take ya dafe qirjin nasa, sai Lokacin yayi daidai da shigowar AHMAD office d'in nasa, dan haka kawai shima yaji aransa ya shigo yaga qanin nasa yau me yake damunsa yayi latti wajen zuwansa asibitin...

Aiko cikin sauri ya qarasa garesa yana cewa, "Subhanallah, me yake damunka HEESHAM, dama ni tunda naga kakai tara da rabi kafin kazo nasan ba lafiya ba, Allah dai yayi bazan kiraka a waya bane, me yake damunka ƙanina..
Cikin futar da numfashi sama sama HEESHAM yace "Ban san me yake damuna ba yau, ban san me yake damuna ba YAYANA, bam san me yake san faruwa ba, ban tab'a jina cikin wani yanayi na fad'uwar gaba da kamuwa da damuwa lokaci d'aya irin na yanzu ba YAYAH, Allah koma me zaka jarabceni dashi Allah kasa karna rasa iyayena kai Matata da yarona Y'an uwa... Ai HEESHAM baikai ga qarasama AHMAD kalaman ba sai ganin wayarsa yayi tana rigin, ganin NUWAIRA ce yasa AHMAD bashi wayar amma hankalinsa ya tashi matuƙa dajin kalaman HEESHAM d'in..

"Yallab'ai Yallab'ai kazo ga Hajjiya NUWAIRA kwance bata numfashi dan Allah Yallab'ai kazo yanzu karta qarasa..

Wani numfashi HEESHAM ya fara fitarwa maganar ma kasata yayi ganin halin da kuma ya qara shiga nan yasa AHMAD karb'ar wayar yana cewa "NUWAIRA...
Zuwaira tace da AHMAD "Yallab'ai ba NUWAIRA bace, ga NUWAIRA kwance haka nima nazo naganta, dan Allah ku temaka kuzo ban tab'a Ganin mutum haka cikin wannan yanayi ba..
AHMAD ya kalli HEESHAM wanda yake dafe da qirji wani gumi na yanko masa ga wasu hawaye wanda tun yake da HEESHAM bai tab'a ganinsa da su ba, qila tun yana qarami, cikin wata murya HEESHAM yace "ta mutu, Innalillahi-wa'inna'ilaihirraji'un, Innalillahi-wa'inna'ilaihirraji'un Innalillahi-wa'inna'ilaihirraji'un alhumma ajfirni fi masi... Ai bai qarasa ba numfashinsa ya d'auke..

Innalillahi-wa'inna'ilaihirraji'un shine abin da AHMAD shima yace, dan baya san ciwan ZUCHIYAN HEESHAM d'in ya tashi, yana matuƙar shan wahala Sosai, gabaki d'aya dangi hankalinsu tashi yake, bare su makusantansa..

Nan ya nemi ruwa ya yayyafa masa, daqer HEESHAM ya farfad'o, ammafa jin wani zafi yakeji a zuciyar nasa, yasan ba makawa dole ciwansa ya tashi, AHMAD yace "Ka kwantar da hankalinka ba abun daya sameta. Cikin qarfin hali yace "muje gidan Yaya, ina san ganinta...

Aiko AHMAD baija ba, nan ya kamasa suka fitto daga office d'in, gabaki d'aya sanda gaban ma'aikatan asibitin ya fad'i da ganin halin da HEESHAM yake ciki, doctors sai tambayar AHMAD suke me yake damunsa kuma meyasa yake san fittar dashi daga asibitin bayan anan ne za'a masa Magani idan wani abu ne yake damunsa, AHMAD ce musu kawai yake suna zuwa su basu minti goma..

Aiko da sauri AHMAD d'in yake tuk'a motar tashi, cikin qanqanin lokaci suka iso gidan.
Anan bedroom na NUWAIRAN sukaga Zuwaira zube a qasa ta rabka tagumi tana hawaye tana kallan NUWAIRA wacce take zube a qasa ba wani alamar numfashi..
Nan cikin zafin nama HEESHAM yayi kan NUWAIRAN cike da aiki da ilimi irin nasu na likitoci yahau duba numfashinta, kamar dai tana raye amma bazai tabbatar ba, dan shi a gigice yake..
Nan ya kalli Zuwaira yace "meya samu matata, tace "Wallahi wallahi ranka ya dad'e ban sa'ni ba, nidai na shigo na kirata najita shiru, sai naji d'an motsi anan d'akin nata har zan shiga kitchen sai kuma nayi tunanin kodai kirana tayi, dan haka kawai sai nayo shashin nata, shuru HEESHAM yayi da qoqarin san kinkimar NUWAIRAN, sai kuma ya tsaya yana cewa ina *AMEER*..

Ita kanta Zuwaira sai Yanzu tatuna da Ameer d'in, sai yanzu tatuna dashi..
Nan tace "Ban ganshi ba, yace "what, ban gane baki gansa ba, ya kai qarshen zancen nasa da kallan gadan NUWAIRAN, ba Ameer ba dalilinsa agun, saima jini dake b'ace akan gadan NUWAIRAN, gashi nan d'is d'is a qasa alamar dai wani abu ya faru..

Nan ya tashi a gigice yahau duba d'akin yana cewa "Ameer, Ameer, Ameer, ina kake...
Hawaye ne ya zuboma AHMAD, tunda yake da HEESHAM bai tab'a ganinsa cikin wannan hali ba, sam yama manta Ameer d'in bashi da baki bai fara magana ba bare ya amsa masa...
Haka ya dinga shiga wannan d'aki ya fitta wannan d'aki a haka ya gama zaga gidan Zuwaira na tayasa amma ba Ameer ba alamarsa.

Dama AHMAD baibi takan neman Ameer d'in ba, dan haka kawai yaji DAGA ZUCHIYAR SA yaran baya cikin gidan...

Nan HEESHAM ya tsaya a harabar gidan ya maida kallansa ga maigadi, yace "wallahi Kaine zaka fitto min da yaro na..
Cikin tashin hankali megadi yace "Billayillazi megida ban san inda yaranka yake ba, kuma na rantse da Allah bayan fitarka banga kowa ya shigo gidan nan ba sai Zuwaira...
Ai Zuwaira najin haka, tace "nayi imani da Allah abin dana gaya maka megida shine iyakar gaskiyar abin dana gani, wallahi dana shigo banga Ameer ba, kuma ni wallahi nama manta dashi sai Yanzu daka ambace shi...

HEESHAM najin hakan ya qarasa dafe qirjinsa, jin kamar wata kifiya tazo ta cakesa, babu b'ata lokaci nan ya yanke jiki ya fad'i, megadi ya kwalla ihu yana cewa "Maigida dan Allah ka tashi, dan Allah ka tashi, AHMAD wanda kansa ya kulle yayi saurin daukarsa ya shigar dashi mota, dama tuni ya d'auko NUWAIRA ya kaita motar..
Dan haka kallan Zuwaira dame gadin yayi yace "Ku zauna na kira y'an sanda za suzo binkice yanzu yanzu.

Cikin tashin hankali sukace mai toh suna masu yima iyayen gidan nasu fatan asamu kansu cikin sauƙi..



Aiko AHMAD d'in na barin gidan y'an sanda suka diramma gidan, amma basuso AHMAD ya tafi da NUWAIRA ba, sunso su d'auki hotunanta dan zai temaka masu matuƙa, haka dai suka gama binkicensu suka tasa qeyar megadin gidan, da Zuwaira, dama me bama fulayoyi ruwa baya nan yaje qauyansu..

Koda suka isa caji office d'in tambayar duniya amsa d'aya megadi da Zuwaira suke bama Jami'an tsaran, har dukansu sukayi duka me yawan gaske amma cewa suke iyakar gaskiyar zancen kenan da suka gaya musu.
Toh sudai a binkicen nasu sun yarda da Zuwaira da megadin, sun tabbatar a irin dukan da suka musu inda akwai wani abu atare dasu zasu fad'a..
Haka dai suka kullesu da niyar sai gobe imma barinsu za'ayi ayi hakan..


A asibiti ko ba qaramar wahala AHMAD yasha ba kafin HEESHAM ya farfad'o, lokacin momy da Dady da mamansu NUWAIRA da Babansu da Ramlat Hannatu HAIRANAH MEENATU Khadija Sadeeq Baba Alhaji da matansa kaf suna asibitin, gabaki d'ayansu hankinsu a tashe yake, Momy sai kuka takeyi, Dady na harrashinta cikin karfin hali, dan inda ace shima mace ne kukan zai saka...
Kan kace kab'o zance ya yad'u a dangi cewar ciwan ZUCHIYAN HEESHAM ya tashi, sakamakwan sumewar matarsa NUWAIRA da kuma b'atan d'ansa Ameer..

Dan AHMAD da sauran doctor sun tabbatar NUWAIRA bata mutu ba, sam bata mutu ba, sun bata temakwan gaggawa, amma a irin halin data shiga basu da bada tabbacin lokacin farfad'owarta, suna dai mata fatan ta farfad'o nan da sati d'aya...

Hankalin dai dangi ba qaramun tashi yayi ba, dan wannan al'amari bai tab'a faruwa da wani anan dai cikin dangin ba, toh bare kuma HEESHAM, wanda ba ruwansa da kowa dan tsakaninsa da mutane wasa da dariya ne, wannan yasa hankalin dangi qara tashi..


HEESHAM dai tunda ya farfad'o d'in ya kuma tabbatar NUWAIRA bata mutu ba, Ramlat tabbatar mai ba'aga Ameer ba, HEESHAM bai qara magana ba, dan idan yace zaiyi magana jin wani zafi yake ji DAGA ZUCHIYAR SA, ba abin da yakeyi sai hawaye..
Kallo d'aya zaka mai kazubar mai da hawaye, musamman Baba Alhaji dayafi kowa yimai kallan tausayi, ganinsa ƙaramin yaro, Allah dai yasa yaci wannan jarabawar...

Yanzu kowa damuwarsa ina AMEER yake, meya faru dashi, waye ya d'aukesa, awane hali yake...
Ba me basu wannan amsar sai NUWAIRA, dan tabbas itace zata gaya musu meya faru..



Toh har bayan sati d'ayan NUWAIRAN bata farfad'o ba, lokacin ko ciwan ZUCHIYAN HEESHAM ya gama tashi..
Nan AHMAD da sauran manyan doctors d'in asibitin suka qara kaimi wajen basa kulawar data dace..


HAIRANAH bata da aiki sai kuka, gani take y'ar uwarta mutuwa zatayi, gani take Abokin nata HEESHAM mutuwa zaiyi, AHMAD dai yana qoqari Sosai wajen ganin ya kwantar mata da hankali..


Ga y'an sanda sun gama binkicensu tsab sun gano wannan jini da yake gadan NUWAIRAN ba jinin kowa bane face na d'ansu Ameer, dan sun ibi jinin HEESHAM dana NUWAIRAN sun gwada shine ya basu hakan, sun tabbatar akwai wanda ya shiga gidan fitar HEESHAM daga gidan..
Dan a labarin damai gadin gidan ya bayar ya tabbatar musu lokacin daya bud'ema HEESHAM d'in get ya fitta NUWAIRA komawa falanta tayi, yana kyautata zatan qila kafin get d'in ya rufe kansa ne dake da rimot yake amfani shine wanda ya shiga gidan yasamu nasarar shiga a cikin sauri, maigadin ya tabbatar alokacin bai tsaya get d'in ya rufe kansa akan idansa ba, dan a ranar ya tashi da lalurar gudawa, kuma alokacin tazo masa ne....
Gaskiya sunyi qoqarinsu sosai nasan gano komai, amma iyakar abin da suka gano kenan, ayanzu dai duk wani labari da zasu samu da wata gaskiya toh awajen NUWAIRA zasu samu, dan haka ajirayi dawowarta normal aga abin da Allah zaiyi..


HEESHAM dai shidai a jin zuciyarsa baiji ko kad'an Ameer ya mutu ba, yana dai addu'ar NUWAIRA tadawo normal ta gayamai inda d'ansa yake..


Su momy ma ba abin da sukeyi sai Addu'a, akan Allah ya bayyana Ameer d'in ya kuma farfad'o da NUWAIRA ta fad'i abin daya faru....


Allah ya amshi addu'arsu, dan wata d'aya da kwana goma sha shidda NUWAIRA ta farfad'o, amma ba'a cikin hankalinta ba..
Dan abin daya faru shine. Aranar da zata farfad'o HEESHAM ya d'an samu sauƙi, duk da magana ma daqer yake yinta, amma haka yasaka AHMAD a gaba shi yakaisa d'akin da NUWAIRA take..

Aiko yana kaisa, nan ya dafa kanta wacce take kwance kamar gawa, ya shiga yi mata Addu'a yana tofa mata akan nata.. AHMAD na ganin haka ya fitta daga d'akin, saiya kasance daga HEESHAM d'in sai NUWAIRAN kawai suke su biyu a d'akin.
Yana gama mata Addu'o'in yana sauke hannunsa yaji taja wani numfashi a hankali..
Sannu a hankalin ta fara bud'e idan nata, tana bud'ewar a hankali a hankali har takai ga bud'esa gabaki d'aya..
Aiko cikin sanyi irin na mara lafiya ta qorama saman d'akin ido, can data gama kallan saman saita juyo da kallan nata kan HEESHAM, wanda yake mata wani kallo a gajiye haka, wanda kallo d'aya zakama kallan nasa kasan baya jin daɗin jikinsa sosai...
Ta ƙura masa ido sosai ta kuma ƙi d'auke idan nata daga kallan nasa..
HEESHAM ya gaji da kallan nata yace "kice wani abu mana...
Tayi mai shuru ba tare data dena kallan nasa ba..
Nan gabansa ya fad'i, sakamakwan wani tunani dayazo masa, cikin sauri ya tashi da shafa fuskarta, nan ma bata mai magana ba, sai yaci gaba da cewa, idan baza kimin magana ba zan fitta na baki waje.. Ya fad'in mata hakan ransa ad'an b'ace..
Still bata ce mai qala ba..
Saiya fitta abinsa, sanda ya zauna akan wata kujerar dake kusa Momy ya huta, dan tafiya ma yanzu wahala take basa, kana ya qara tashi a hankali ya nufi office d'in AHMAD, sai Momyn tabishi da kallo, sam ya canja, HEESHAM baya kula kowa sai Dadynsu da AHMAD d'in, yamafi kula Dadyn nasu akan AHMAD d'in ko abokinsa.

Yana shigo office d'in AHMED yayi saurin tashi ya taresa da zaunar dashi yana cewa, "sannu ko, karka damu zata farfad'o..
HEESHAM bai kulasa ba sanda yayi minti biyu kana yace dashi, "YAYAH ta farfad'o fah, amma daga dukkan alamu bata cikin hankalinta, dan na mata magana bata amsa min ba...

Ai AHMAD najin hakan yace "Alhamdulillah, kaga ka bud'e mana hanya, bari naje na dubata naga miye kuma matsalar, ka dai kwantar da hankalinka, insha Allah komai zaizo da sauƙi fiye da yanda kake tunani..
Shuru HEESHAM yamai, dan haka sai yayi saurin fitta dan dubota..


Haka shima ta zuba mai ido, yayi mata maganar duniya taqi amsa masa, dan haka yayi mata wani aiki, ya shiga caje kanta.. Anan shida wani doctor Anas suka gane tasamu d'aukewar tunanin kwakwalwa wanda yafi d'aukewar tunani muni, dan koda zataga kowa nata baza ta tuna dasu ba, bare taji sunayensu sam bazata tuna dasu ba, ilimi d'aya ne wanda likitocin duniya suke dashi akan matsalar a Yanzu shine, zasu bada tabbacin Sai dai idan anyi irin abin daya faru da ita sak wanda yasata furgicewar har yazama silar d'aukewar tunanin nata, to shine zaisa tunanin nata dawowa daidai batare da wata matsala ba, bacin haka Saidai ajirayi ikwan Allah shine kawai zai dawo mata dashi a alokacin dayaso, dan idan yaga dama ayanzu ma zai iya dawo mata da tunanin nata, dan ba abin dayafi qarfinsa, shiyasa ake san kemara a gida, dan da akwai a gidan da yanzu anga meya faru, amma ba komai zasu shiga binkice sosai akan lalurar tata dan a gano me za'a iya mata ya temaka wajen dawo mata da tunanin.

Lokacin da mamanta da Babansu dasu momy dasu Baba Alhaji da sukeji hakan ba ƙaramin qara shiga tashin hankali sukayi ba, nan suka qara jin tausayinta da tausayin HEESHAM...

Dan shi AHMAD bai gaya ma HEESHAM d'in ba, kawai HEESHAM d'in yaga sakamakwan ne a hannun HAIRANAH, wacce bata san ya akayi ya gani a hannun nata ba, dan AHMAD yace kar a gaya mai, a bari saiya qara samun sauri, amma dayaga sakamakwan zama kawai yayi ya dafe kansa, hawaye me zafi ya zubo masa, Wai yau NUWAIRANSA ce wacce baza ta tuna da shi ba, har iyayensu, gashi baisan inda d'ansa yake ba, itace wacce tasan inda yake, gashi ba wanda yake da tabbacin yaushe zata dawo tunaninta tabada labarin inda yake, tabbas koda zai rasa duk abin daya mallaka saiya qara neman ilimi akan mezai kawo mafuta akan masu lalura irin tata.. Daga kanta insha Allah zai fara binkice akan hakan, wanda zai iya yuhuwa doctors dadama na Nigeria basu tsaida tunaninsu akan nemo wata mafitta akan hakan ba.

Sadeeq yayansa ne yakai hannu kan kafaɗarsa, nan ya dawo daga tunanin da yakeyi, yace dashi, "Nasan hakuri zaka bani Ya Sadeeq, hakurin ya zamar min dole, dan ba inda zan dosa wajen neman yarona, ita ce kad'ai tasan meya faru, gashi bata cikin hankalinta, zan qara Saka Allah a gabana nasan insha Allah zai bani wani haske bazai tab'a barina cikin duhu akan wannan lamarin ba, dan ko'a film ban tab'a ganin hakan ba, Allah ne ya barma kansa sanin me yasa yayi hakan, kuma bazanyi jayayya dashi ba, danna karb'i wannan qaddarar da hannu bibbiyu... HEESHAM yakai ƙarshen zancen da zubo da wani hawaye wanda yafi na d'azu yawa...

HAIRANAH tace "Mungode Allah daya baka damar gane qaddarar tasa cikin sauri, dan Allah HEESHAM ka rage damuwar hakan aranka, insha Allah albarkacin Addu'a Aunty NUWAIRA zata dawo normal kuma zamu san me yake faruwa..
HEESHAM d'in ya kalleta kad'an haka! kana yace "Toh Allah yasa..
Har Ramlat da Hannatu suna had'a baki wajen cewa Ameen

MEENATU dai sunkuyar da kanta qasa tayi, zuciya cike da tunani kala kala.

AHMAD yace, "Ya kamata NUWAIRA tasha wani abu me d'an ruwa ruwa haka, danta tashi da qarfin jiki, amma anyi anyi tayi, dan haka ka tashi muje ka bata kulawarka... Yakai ƙarshen zancen da kallan HEESHAM.
Tashi HEESHAM d'in yayi da cemai toh, a hankali suke tafiyar har suka kai d'akin da take, Doctor Anisa ce akanta da iyayensu da Baba Alhaji, momy sai lallashinta take kan tasha ruwan tia d'in da doctor Anisan ta had'a mata amma taqi, sai wani b'ata rai take tana cika tana batsewa, kallo d'aya HEESHAM yayi mata yasan bata san ganinsu kusa da ita, tana zaune ne akan d'an gadan nata, kasancewar AHMAD ya cire mata komai na na'urar dake jikinta sai hakan ya bata damar zama a tsakiyar gadan ta tankwashe qafarta kanta na qasa, kannan nata a hargitse, kasancewarsa a babu kitso, sai wasa take da zuban hannunta, Sam bata kallan kowa a cikinsu, ran nan dai nata a b'ace yake.

"Yauwa HEESHAM Allah yasa ta yarda dakai tasha ko kad'an ne, maza jeka ka bata, dan taqi yarda da kowa anan, sai magana ake mata taqi kula kowa, cewar Dadynsa.

Ahankali yace "Toh Dady... Jin muryar HEESHAM d'in yasa tayi saurin d'ago da kan nata ta kallesa, danta rike muryar tasa tsaf a kwakwalwarta, tasan shine mutum na farko data fara gani, anan take ta sakar mai murmushi..
Yaje ya zauna kusa da ita, saita kama hannunsa k'am ta rungume kamar wani yace mata za'a kwace mata shi..
Doctor Anisa tashiga tunina, can tace "Oho, Ashe fa kai tafara gani lokacin data farka... AHMAD yace "Eh, inaga hakan ne yasa taqi yarda da kowa, kuma d'azun ma da yayi mata magana Sam bata kulasa ba, tace "Ai dama bazata kulasa ba,
DOWNLOAD
DOWNLOAD

Please Login or Register in order to submit comment