Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

idan yaje kunnan ita MEENATUN take ko wa!!!😏 zai tabbatar mata da cewa baka damu da ita ba, kaga bakai ba cin amarci cikin nishaɗi kamar yanda mutane suke cinsa da ganin walwala akan fuskar amaryarsu..

AHMAD ya ƙara rintse idansa, damuwarsa kafarsa...
Ganin baiyi mata magana ba sai taje kitchen ta ibi ruwa a bokiti da mofa taje tahau goge wajen, sanda ta goge wannan miyar karkashin tsaf taje ta zubar da ruwan a kitchen, tadawo ta zuba mai ido batare datace mai komai, duk yana kallanta da mamakinta, can cikin muryarsa me daɗin saurarayo Yace mata, "Jeki gayama momy cewa na karye a ƙafa...
Cikin faɗuwar gaba HAIRANAH ta waro ido tare da dafe ƙirjinta tace "Karaya, kafa karye kace,😳... Kutumenesi tashi nagani, ta faɗi hakan cikin matuƙar tashin hankali, tare da kai hannunta qafarsa tana cigaba da cewa, wacce ƙafarce ta karye, na shiga uku ni HAIRANAH🙆🏻... Dan Allah Ya AHMAD karkace ma kowa nina karyaka,😨 takai ƙarshen zancen da farshewa da kuka😭 Tare da kallansa cikin shagwaɓa hawaye na zubo mata.. Ya ɗauke kallansa daga kanta, tare da ƙara rintse idan nasa.. Jin tatab'a inda yasamu karayar a ƙafar tasa ta hagu.. Ganin hakan yasa tagane lalle a wajen ne yasamu karayar.. Saita ƙara rushewa da kukan...
Yana jin hakan ya zaro wayarsa a cikin ajjihunsa ya kira layin Sadeeq qaninsa yace "Ina wannan kofar da take sadani da Momy kai tsaye wajen d'an passage d'innan, pls kazo yanzu na samu karaya ne awajen..
Cikin sauri Sadeeq ya tashi daga kan gadansa da yake yana kallan abokansa, yace "Subhanallahi, Yaya garin Yaya, gani nan zuwa..
Kashe wayar AHMAD yayi da kallan HAIRANAH wacce take kuka tsakaninta da Allah..
Saiya dinga kallanta kawai batare dayace mata komai ba, ahaka Sadeeq yazo wajen yagansu, HAIRANAH durƙushe a gabansa sai kuka takeyi, daidai nan Sani abokin nan nasa shima ya fitto dan kiran AHMAD d'in ganin lokaci na tafiya, ai yana ganinsa cikin wannan hali shima yayi kansa kamar yanda Sadeeq d'in yayi kansa.. Sani fad'i yake "Subhanallahi, meyasameka haka AHMAD.. Sadeeq ma cikin tausayawa yace "Sannu Yaya garin Yaya haka ta faru..
Shidai shuru yayi musu..
Haka suka temaka mai wajen maida shi room d'in nasa... Kan su kwantar dashi yasa suka cire mai rigarsa da canja mai wango sai suka kwantar dashi daga shi sai singilet da gajeran wando wanda yad'an wucce cinya kad'an haka.
Sadeeq ya kalli HAIRANAH Wacce take shigowa d'akin yace, "Kukan ya isa haka mana Sister, karki sama kanki ciwo, gayamin ya akayi hakan tafaru, cikin kuka ta Kalli AHMAD d'in taga ita yake kallo, sai tace, "Nima jin fad'uwarsa nayi nazo fitta daga falan Momy, takai ƙarshen zancen nata, da tsaida Kallanta sosai akan AHMAD d'in tana cigaba da cewa, Ina haka ne ko😟... AHMAD ya lumshe idansa batare daya bud'e ba yace, "Haka ne, santsi ne ya kwasheni, da alama wani yaci amala ne a passage d'in nawa ne Sadeeq shiyasa miyarsa ta zuba agun ni kuma nazo a rashin sani nabi kai, Sadeeq da abokinsa Sani suna jin hakan daga bakinsa suka sauke ajiyar ZUCHIYA, sani ya fitta gayama abokansu da suke falan nasa, Sadeeq kuma ya fitta zuwa gayama momy, sai hakan ya bama HAIRANAH damar matsawa kusa da shi takama hannunsa duk da sunji shock ajikin nasu bata janye hannun nata ba tace dashi, "Dan Allah Yayana ka rufamin asiri wallahi natuba bazan qara yi maka irin hakan ba, dan Allah karka gayama kowa..
Bai bud'e idansa ba yace mata, "Toh naji... bata wani yarda da toh d'in dayace ba, dan haka taci gaba da kukanta, tana cewa, "Dan Allah karka faɗawa kowa kaji, wallahi bazan sake ba.. Bud'e idan nasa yayi da cewa "Bani ruwa nasha, cikin sauri tasaki hannunsa ta bud'e furij nasa da niyar d'auko masa ruwan, daidai nan ko momy ta shigo d'akin hankalinta tashe tayi kansa Sadeeq da HEESHAM suka biyo bayanta tana cewa, "Me zan gani ni Aisha, karaya adaidai wannan lokacin, ya sakarma momyn tasu murmushi yana cewa, "Ƙaddara momy, kawai ina fitowa dan zuwa gareki santsi ya ibeni sai jina nayi a ƙasa, tace "Yanzu Sadeeq yake nuna min wajen da suka d'agaka, ga miyar amala nan awajen, ba wanda zaiyi aikin nan sai yaran Amra.. dansu ne nasakama amalar d'azu Ashe sunzo shshinka da ita..
HAIRANAH ta zubama AHMAD ido tana jiran tayi me zaice.. Shima ita d'in yake kallo, ganin haka yasa momyn kallan HAIRANAN wacce idanta keta zubar hawaye, saita mai da kallan nata kan AHMAD d'in zatayi magana saiya rigata da cewa, "Ki lallashi HAIRANAH pls momy hankalinta ya tashi, kasancewar ta riga kowa ganin faɗuwar tawa..
Jan numfashi HAIRANAH tayi, momy tayi murmushi, da kama hannunta tace, "kwantar da hankalinki Yarinyata, Baba Alhaji da kansa zaizo ya gyara masa kafar, dan shine me gyarawa idan hakan ta faru, kuma cikin ikwan Allah sai kiga mutum ya samu sauqi cikin lokaci k'ank'ani, dan haka ki kwantar da hankalinki.. D'aga mata kai HAIRANAH tayi kawai, sai HEESHAM yaje ya kama hunnunta yace "Zo muje kiji wata magana, haka tabi bayan HEESHAM idanta nakan AHMAD, shima nasa na kanta, sanda suka ficce ya dawo da kallan nasa kan momy zaiyi magana abokansa suka fara shigowa room d'in Damai sannu, momy tace suje wajen d'aurin Auran kawai a d'aura dasu, dan tasan Baba Alhaji ba fasawa zaiyi ba, nan suka fitta dan zuwa gidan Baba Alhajin..
AHMAD ya kama hannun Momy yace, "gaskiya ina jin jiki momy, pls ki gayama Baba Alhajin yanzu, nasan ana d'aurawa zaiyo nan, gwara naji zafin gabaki d'aya, kinga zuwa gobe HEESHAM yakaini asibiti ayimin hotan qafar aga ko tagyaru dai dai..
Momy ta shafa kansa tace, "Babah Alhaji gwanine wajen gyaran k'afa, ina tabbatar maka yana gyara maka koda anyi hotan zakaga tagyaru, ka kwantar da hankalinka kaji.. D'aga mata kai yayi kawai..
Saita kira number na Baba Alhajin ta gayamai abin da yake faruwa, nan cikin tausayawa yace mata kar'a kaishi asibiti bara ya d'aura auran nasu zai tawo yanzu ya dubasa da mai gyaran k'afar, toh tace mai cikin ladabi...

HEESHAM ko wajen shaqatawar gidan yayi da HAIRANAH, anan ya zaunar da ita kan d'aya daga cikin kujerun wajen da durƙusawa a gabanta yace "gayamin ya akayi Ya AHMAD ya tsinci kansa cikin wannan halin, cikin kuka sosai HAIRANAH ta kwashe komai daya faru tsakaninsu har izuwa yau ta gayamai...
HEESHAM ya zuba mata ido, danshi duk rashin jinsa bai tab'a karya mutum ba..😂
Cikin sanyin murya yace, "Tab.. Yanzu ni da nake tunanin mu tab'a Soyayya na Aureki ashe tafiyar mu bazata yuhu ba, dan ina miki lefi zaki ƙarya ni,🤔 gashi ni kuma wallah ina san jikina😟..
Cikin zubar hawayen nata tace dashi, "Allah bazan karyaka ba, ai kaga ina sanka ko..
Shuru HEESHAM kawai yayi mata da zuba mata ido, hannunsa tallafe da fuskarsa alamar tagumi..

NUWAIRA dake ganinsu da jinsu dan akan idanta suka shigo wajen.. Sam hankalinsu yayi gaba ko lura da ita basuyi ba, dake tana can gefe tana bama wata fulawa ruwa..
Nanko hawaye me zafin gaske ya zubo mata, kanta kuma ya wani sara mata, yau ta yarda da gaske Ashe Soyayyar suke..
Kuka mecin ZUCHIYA ne yazo mata.. Nan tatashi da gudu tayi cikin gidan bata dira ako ina ba sai'a bedroom d'in da suke kwana, nan ta zube akan gadan nasu..
Ramlat ce a d'akin tana kukan yanda AHMAD ya karye, tunaninta ko NUWAIRAN ma taje ta gansa ne yasata tawowa da kukan, dan haka cikin sanyin jiki take ce mata, "Kiyi hakuri Y'ar uwa, insha Allah zai samu lafiya nan kusa..
Shuru NUWAIRA tayi mata, Ruhi cike dajin zafin ZUCHIYA, tana san ƙanwarta bata san kishi ya shiga tsakaninsu, wallahi tana MASIFAR SON HEESHAM, bata san ganinsa da kowace ƴah mace.. Ranta zafi yake mata sosai.. (Rahama Rufa'i nalele tace zataga ikwan Allah)🤔


HEESHAM da HAIRANAH ko sai Lokacin sukasan da zaman NUWAIRA agun, dan haka cikin sauri HAIRANAH tatashi tana cewa, "Na shiga uku HEESHAM, Kar taje ta gayama Momy, shima tashin yayi yace "kai haba bazata aikata hakan ba..
HAIRANAH takama hannunsa cikin tashin hankali tace "muje dai mu gani..


Haka HEESHAM ya bita, kuma direct shashin Momy sukayi, ganin bata nan sai suka nufo inda take, watoh bedroom nasu, anan suka ganta Ramlat na bata baki, gabansu ya Faɗi tunaninsu kota gayama Ramlat d'in, dan haka da sauri HEESHAM yace da Ramlat, "Aunty Ramlat me yasamu Auntii NUWAIRA.... Jin muryarsa da NUWAIRA tayi shiyasata d'agowa ta kallesa, sannan ta qara maida kan nata fillo, Ramlat tace, "Nima ganinta nayi tashigo da kuka wiwi kuma taqi yin magana, shine nayi tunanin ko taje taga karayan da YA AHMAD yayine yasata dawowa da kukan, hakan yasa nake bata baki..
HEESHAM najin sauke ajiyar zuciyar da HAIRANAH tayi, har ya d'an kalleta, tasakarmai murmushin yaqe, yace "ba mamaki kam haka ne, Toh Auntii NUWAIRA kiyi hakuri, insha Allah zai samu lafiya nan kusa..
NUWAIRA bata kulasa ba, Ramlat d'in dai itace ta qara cewa, "Nima abin da nake gaya mata kenan, Baba Alhaji na gyara masa insha Allah komai zaizo da sauƙi... Takai ƙarshen zancen da ficcewa daga d'akin..
HEESHAM da HAIRANAH na ganin fitan Ramlat d'in sukayi saurin qarasawa ga NUWAIRAN, HAIRANAH nacewa, "Dan Allah Auntii NUWAIRA ki rufamin asiri kadda ki gayama kowa kinji..
HEESHAM yace "Pls Auntyn mu, dan Allah Karki gayama kowa..
Ahankali ba tare data kallesu ba tace, "Bazan gayama kowa ba shikenan..
Nan suka saki murmushi, atare sukace, "eh shikenan....
Kana suka ƙara ficce suka barta, nan tabisu da kallan harara..
Kana taja tsaki da goge hawayen nata tayi shashin AHMAD d'in..

Awajen Baba Alhaji ko sanda ya d'aura Auran MEENATU da AHMAD da kuma na Sadeeq da Khadija Sannan yake gayama Dadynsu HEESHAM karayar da AHMAD ya samu.
Aiko nan hankalinsa ya tashi, taro ko na watsewa ya d'auki Baba Alhajin sai gidansa, suna zuwa direct shashin AHMAD d'in suka nufa, anan sukaga Momy dasu NUWAIRA sunama AHMAD d'in sannu...
Babah Alhaji kallan k'afar kawai yayi yasan mezai mata..
Yana kama qafar AHMAD ya rintse ido, har Baba Alhaji ya gama gyara masa qafar AHMAD bai bud'e idan nasa ba, ganin hakan yasa Baba Alhaji yimai magana, duk da yasan wasu sumewa suke, idan irin hakan tafaru, amma ga mamakinsa yana mai magana AHMAD d'in ya bud'e idansa amma yayi jajahur alamar yasha azaba, Baba Alhajin yayi murmushi da cewa, "Tunda nake gyalan karaya ban tab'a ganin jarumi irinka ba AHMAD, Allah ya qara lafiya, kafa dai ta gyaru, sai'a kiyaye duk wani abu dazai tab'ata ayanzu, Sai nan da sati biyu, ga wannan Maganin adinga shafa maka safe rana da yamma, kar'a kuskure..
AHMAD yayi murmushi da cewa "Toh..
Momy ma murmushin tayi tace, "Insha Allah za'a kiyaye, Allah ya basa lafiya..
Kowa awajen yace ameen, kana Baba Alhajin ya tashi Dadynsu HEESHAM d'in ya maidashi.

HAIRANAH dai qin fitta tayi daga d'akin, dake duk dangi sun sani gashi lokacin biki haka kowa yake shigowa yana gaishesa da ganin HAIRANAH ad'akin..
Dare nayi ko aka kawo MEENATU wacce hankalinta ya bala'in tashi, momy da Dadynsu HEESHAM sun yanke shawarar MEENATUN zata zauna agidan momyn har AHMAD d'in yasamu lafiya, kana suje gidan Auransu, wanda shi AHMAD d'in ya Tara abin duniya acikinsa..
Ran momyn MEENATUN baiso hakan ba, taso y'ar tata ta tare agidanta, sai akai AHMAD d'in can, in yaso kowa ya dinga zuwa can yana dubasa, sai kuma momynsa ta b'ata mata shiri..
Amma ankai Khadija gidanta, abokan Sadeeq angonta suka kaisa gareta..

Washe gari HEESHAM da Sadeeq suka d'auki AHMAD zuwa asibitinsa, anan akamai hotan qafarsa suka dawo dashi gida, dan da HEESHAM yace ya zauna a asibitin amma yaqi ba wanda yasan dalilinsa naqin yardar..
Aranar HEESHAM ya duba sakamakwan gwajin ya basa gyaran ya gyaru...

Bayan sati d'aya da faruwan lamarin, MEENATU taga zaqewar HAIRANAH tayi yawa akan AHMAD d'in, ganin Sallace dacin abinci yakesata barin d'akin AHMAD d'in, duk da ko ba ita kad'ai bace a d'akin, hasalima tunda abun ya faru HAIRANAH da AHMAD d'in basu samu damar zama na minti d'aya a d'akin ba, daga wannan ya shigo sai wancan ya fitta, amma haka MEENATU da Momy suka gane HAIRANAH tafi damuwa da AHMAD d'in fiye da kowa agidan...
Haushi sosai take bama MEENATUN, yayin da Momy kuma taji qarin ƙaunar HAIRANAN aranta, dan hausawa suna cewa kaso me sanka, haka baka da Babban masoyi aduniya kamar mesan d'anka.. Wannan yasa momy taji daɗin kulawar da HAIRANAN take basa..

HEESHAM yafi kowa gano hakan, sai yasa aransa zaibi tunanin HAIRANAN, dan yaga kamar bayan nadamar datayi na abin datayi ma AHMAD d'in akwai abin da yake damunta..

Shidai AHMAD ya gane HAIRANAH tayi matuƙar nadama akan abin data masa, wannan yasa zuciyarta taqi barinta shiyasa take qoqarin san taga tafi kowa kyautata masa a wannan Lokacin..
Dan qarara yake ganin tausayinsa a kwayar idanta..

Yanzu haka suna zaune ne su huɗu a d'akin, inda AHMAD d'in yake zaune kawai yana kallan qafarsa da hararo yaushe zata warke masa, yayin da MEENATU da HAIRANAH suke danna wayoyinsu, kowa da abin da yakeyi, momy na zaune tana duba jarida, sai AHMAD yad'an motsa kad'an... Jin hakan yasa HAIRANAH saurin kallansa tace, "Kana buqatar wani abu ne..
MEENATU ta galla mata harara, momy ta lura da hakan, AHMAD ya girgiza mata kai alamar aa, sai HAIRANAN tatashi tana kallan Momy taci gaba da cewa, Momy zani d'aki nakwanta zuwa Azahar, idan ban tashi ba dan Allah kisa su Ramlat su tasheni, momy tayi murmushi tace "Toh HAIRANAH, jeki kwanta ayi baccin lafiya, murmushi HAIRANAN tayi da ficcewa, MEENATU na ganin fittanta tabi bayanta, anan falo tasha gabanta tana cewa, "Idan AHMAD yana buqatar wani abu ya kamata ki gane cewa yana da baki kuma ni zaiyima magana dan nayi masa abin daya dace, kasancewar nice wacce Alhakin hakan ya rataya akaina amma bake ba...
HAIRANAH najin hakan ta galla mata harara da qoqarin san ratsawa tagefanta ta wucce, amma sai MEENATUN taqi yarda da hakan, ta qara shan gabanta, HAIRANAH tayi mata shuru kawai tana kallanta.

Ganin HAIRANAN tayi mata shuru saiyasa MEENATUN samun qarfin gwiwa, taci gaba da cewa, "Ni wannan abun yana ban mamaki, wai meyasa kikafi kowa zaqewa akansa ne, saikace kinfi kowa jin zafin ciwan nasa, bayan shi ba miji yake agareki ba, ke kuma ba budurwarsa ba, gaskiya zan gaya miki kidena shigema mijina, dan bani so, bani jin daɗin hakan Sam, magana ta gaskiya na fara jin haushinki...

MEENATU Bata san HAIRANA ta tsaneta sosai ba, data sani da bata nemeta da magana ba.
Cikin jin haushi sosai HAIRANAN tace mata, "idanshi mijine agareki, toni Yaya na d'aukesa ayanzu, batun shige masa kowa da kike magana, tausayinsa ne ya damu zuciyata shiyasa nake ji araina kawai naga na kyautata masa, amma bawai ina shigema mijinki bane danna cusa kaina garesa dan banzan tunaninki, ko kad'an mijinki baya gabana, hasalima ni qiyayyace tafaro tsakaninmu, idan kuma kika takuramin zan biyema hud'ubar zuciyata, na gyara tunaninki, wajen aikata miki abin dayafi qarfin tunanin naki, kina maganar ni ba matarsa ba bakuma budurwarsa ba saiki janyo min aya a inda akace sai kana da kusanci sosai da wanda zaka kyautatama Sannan ka kyautata masa.. Tana gaya mata hakan taqara neman ratsawa ta gefanta dan wuccewar

Ran MEENATU ya b'aci sosai da amsar data bata, dan haka afusace ta jawota gabanta tace, "kuskure na farko dazaki farayi arayuwarki shine na fara san AHMAD, daga lokacin da kika fara sanshi daga lokacin kika d'aukoma Kanki dala ba gammo, dan bayan abubuwan dazanyi miki, bazan tab'a bari kizama mata a garesa ba, munafurcin banza munafurcin hofi, baku neman mazajen kanku sai mazajen wasu, Anyi kyan banza wallahi..

HAIRANAH ta zare jikinta daga hannun MEENATUN tace, "Saiki bari idan na tashi Auransa saiki hananin.. HAIRANAH na gaya mata hakan tatureta ta wucce abinta, MEENATU tabita mugun kallo, kallo d'aya zaka mata kasan ranta ba'a ƙaramin b'ace yake ba...

Ashe HEESHAM na kallansu, akan idansa komai ya faru, dan ya danno kai kenan zai shigo falan MEENATUN tasha gaban HAIRANAH, ganin hakan yasashi komawa da baya da kasa kunne yaji kaf me suke gayama junansu.. Shiyasa yanzu da HAIRANAH tazo yin shashimsu tagansa, ya sakar mata murmushi da cewa, Muje haraba kiji wata magana..
Ba musu yayi gaba tabishi abaya..

Ba'a harabar suka tsaya ba, can wajen shaqatawar gidan sukayi, HEESHAM ya kalli HAIRANAH yace "Kibi MEENATU ahankali, dan ta iya makirci sosai, ina jin tsoran tacutar min dake, murmushi HAIRANAN tayi da maida hankalinta kansa tace, "Duk makircinta bata isa bani ciwan kai ba, danni basan mijinta nake ba, tausayinsa kawai nakeji, kasancewar nice silar shigarsa cikin wannan hali, amma kaga yanda take san juyamin manufa, hmmm tayi addu'a kawai kadda Allah ya kawo ranar dazan fara san mijinta, dannifa ko? Ban iya so ba, idan zanso abu sanshi nake da gaske, fahimtar mutane ma bayi nake ba awannan lokacin...
HEESHAM yayi shuru, can yace, "Toni dai yanzu na janye batun Soyayya tsakanina dake..
Da sauri ta kallesa da cewa, "Meyasaka janyewa, yace "Kawai..
Tace "Kawai taqi wadatar dani, yace "Aidama me wadatarwa Allah ne, tace, "haka ne, kawai dai ina san sanin ainihin dalilinka ne..
_Ainihin dalilin shine, bana san na fara sanki da yawa nazo nan gaba na Shiga uku_ ya fad'i hakan aransa, afiliko cewa yayi, "Dalilin shine nafi sanki da YA AHMAD, dan kundace da juna. Murmushi tayi haka kawai taji daɗi aranta, ta kallesa tace, "Nifa bana sanshi, kawai mubar batun nan, danna gane dama can baso kake mu fara Soyayyar ba, tona hakura na yafe😀....
Murmushi shima yayi yace, "Naga bacci a kwayar idanki, pls kije kiyi. Tace "Kamarko kasan dama tun farko shiya koroni, na tafi sai mun haɗu anjima, takai qarshen zancen nata dasan ficcewa daga wajen, saiya d'aga mata kai kawai...
Yana santa, shi ba wata y'a mace data Shiga ransa kamarta, "Allah yasa kar sanki ya dameni HAIRANAH.. Ya faɗi hakan a bayyane kana shima ya fitto daga wajan..

Daidai nan mamansu HAIRANAN ta shigo gidan, aiko da murmushi yaje ya gaisheta ta amsa cikin kulawa kana tayi cikin gidan shi kuma yayi shashinsa, wanda ya Tara abin duniya, dan HEESHAM akwaisa dasan gyara, duk gidan yafisu gyare gyaren d'aki..


Maman su NUWAIRAN suna gama gaisawa da Momy tace da ita, "Kun dawo lafiya, "Lubabatu tace "eh lafiya lau, Saidai sauran kayan namu suna kan hanyar tawowa, insha Allah zuwa anjima zasu iso. Tace "Allahn ya yarda, yanzu Shikenan ku da kano sai wani ikwan Allah..
Lubabatu tayi murmushi tace, "Dake munyi zaman mutunci da mutanan unguwar tamu, zamu dinga leqa al'amiransu da yardar Allah, wallahi bakiga ba? Abin tausayi dan da kuka muka rabu..
Momyn tace, "Ayya sabo turken wawa.. "Hakane Allah dai yasa mudace, Ya jikin Yarona AHMAD, wallahi hankalina gabaki d'aya, yana kansa.. Momy tace "da sauqi sosai, tace "Aidama Babah Alhaji ya iya gyara, bari kigani nan da kwana biyu ras zai tashi, tace "toh Allah yasa...
NUWAIRA ce tashigo falan tana ganin maman nasu taje ta fad'a jikinta cikin farin ciki tana cewa, "mama yaushe kuka dawo, tace "bamu dad'e ba, dama nazo ne nace muku Ku shirya kayanku yau sai kwana a safan gida, NUWAIRA tayi murmushi tace, gaskiya mama naji daɗin hakan sosai, Ya kawayenmu na Layinmu sai kiran wayarmu suke ni da HAIRANAH wai munyi tashin bazata, kuma ko sallama babu, momy tayi dariya tace, "Ai gaskiya suka fad'a, yanzu saiku bari sai Lokacin Auranku sai kuje musu zasuji dad'i sosai, qilama kusamu way'anda zasuzo muku bikin acikinsu, NUWAIRA tace "Hakan kam shine daidai momy..
Momyn tayi gyaran murya tace "Am Lubabatu, dama Dadynsu AHMAD yace na gaya miki NUWAIRA da HAIRANAH bazaku tare dasu ba, zasu zauna anan har zuwa auransu, haka dai yaji nishaɗi aransa ganinsu da yakeyi anan gidan, dafatan babu matsala Babansu bazai damu ba ko..
Maman su NUWAIRAN tayi murmushi tace, "Aisha kenan, wallahi ba komai, kice mai karya damu... murmushin itama momyn tayi tace "Munko gode, dannima dama naso hakan, Allah dai ya raya mana su..
NUWAIRA tace Ameen zuciyarta cike da farin ciki, dan bata so ko kad'an a rabata da HEESHAM...

Walima sosai mamansu NUWAIRAN takira aranar, anufinta kowa yazo gobe..

Haka ko kaf dangin nasu kuwa sanda ya amsa gaiyatar tata kan zaizo goben insha Allah.
haka da sukazo washe garin kowa cikinsu yaba gidan yakeyi, gashi dai ba wani Babban gida bane can amma ya Tara duk wani abu da Ake buqata..
Masha Allah kowa yaji dad'in ganin gidan sosai, anci ansha anyi murna kana taro ya watse..

Dama dawowarsu garin harda aikinsu suka juyo dashi nan Abujan, dan babansu NUWAIRAN yayi tunani sosai bazai iya cigaba da kasuwancin nasa a kano ba, sai Dadynsu HEESHAM ya k'arfafa mai gwiwar akan zaimafi samun Arziqi fiye da garin na kano..
Hakan yasa Dadynsu HEESHAM din Saidai masa wani companynsa dake shima yana tab'a harkar asuwancin..
Haka dai suke ganin komai zai zauna musu fiye da yanda suke zatoh da yardar Allah..


A washe garin ranar HEESHAM ya fara aiki, ya fara zuwa asibitin na AHMAD tunda yaga AHMAD d'in akwance yake, hakan ko ba ƙaramin daɗi yayima kowa ba, musamman daya fara aikin cikin nasara..
Yana fitta tun safe qarfe takwas saiya dawo qarfe shidda...

Ramlat da SABEER Soyayya ce me zafi tashiga tsakaninsu, AHMAD da MEENATU su kad'ai sukasan da zaman Soyayyarsu, dan SABEER d'in yana dawowa daga aiki bayan yayi sallar isha'i yaci abinci agidansu wajen AHMAD yake zuwa daniyar dubashi, daga baya saiya kira Ramlat d'in su zauna a falan AHMAD d'in su sha hira..



Daqer da sid'in goshi HEESHAM yasamu kan Hannatu tafara kula AMAAR d'an uwan nasu, yanzu dai tad'an sauke kishin daya hanata saurararsa badan komai ba saidan nacin da HEESHAM yake mata, danshi jininsa ya had'u dana AMAAR d'in, haka dai suka fara Soyayyar tasu kadaran dai kada ham..

HAIRANAH bata dena bama AHMAD kulawa ba, amma ta kiyaye bata yarda taje garesa lokacin da MEENATU take tare dashi, lura take sosai sai ta tabbatar bata d'akin Sannan take Shiga ta gaishesa da tambayarsa me yake so, yace mata ba komai, duk da hakan tana faruwa ne akan idan Momy kosu Ramlat....



MEENATU taqara yarda AHMAD ƙaunar NUWAIRA yake, dan indai NUWAIRAN zata shiga gaishesa hankalinsa tattayake akanta..

Kamar yau tare ita da HAIRANAH suka shigo gaishesa, MEENATU na gefansa, saiya maida hankalinsa sosai akan NUWAIRAN, NUWAIRAN tagane hakan ne tayanda ko wane lokaci idan ta d'ago fuskarta ganinsa take kawai ya zuba mata ido..
Hakan yasa tatashi ta fitta, itadai tarasa dalilin dayasa yake damunta da kallo, kodai haka halinsa yake ne..

HAIRANAH dama bata san MEENATU na d'akin ba, tad'auka momyce hakan yasa tabi NUWAIRA dan zuwa dubasan, dan haka NUWAIRA na fitta tabi bayanta, AHMAD ya bita da kallo, yana lura dasu su biyun, MEENATU bata san kulawar da HAIRANAN take basa, yayin da yake hango b'acin rai akan fuskar HAIRANAN da zaran tazo taga MEENATUN a d'akin nasa, duk yana lura dasu..

HAIRANAN na fitta MEENATU ta kalli AHMAD d'in cikin b'acin rai da kishi tace, "Nifa ban gane maka ba, wai meyasa kake tsaida hankalinka ga NUWAIRA ne, meyake faɗuwa ne dakai...
Kallanta yayi ido cikin ido yace, "Santa nakeyi, ƙaunarta nakeyi wani abu ne, Cikin tashin hankali ta had'iye yawu tace "amma ai kana dani meyasa zaka sota, yace "Dama nagaya miki dake kad'ai zanyi rayuwa ne, ban gaya miki cewar koda na Aure ki Karki saka ran zama dani ke kad'ai ba, qara had'eye yawu tayi, gabanta na faɗuwa tace, "Bai kamata ka tunatar dani hakan yanzu ba, musamman idan kayi duba da yanda ko shiga gidanka banyi ba, baka san yanda nake jinka araina bane, daka sani wallahi ko cikin wasa ba zaka tab'a ambatar wata y'a mace da Sunan kana Santa agareni ba, kaji tausayi ka janye batun san wata y'a mace ayanzu, ka bani lokaci wallahi nayi maka alk'awarin zan bika da iyakar k'arfi na, zan baka kulawa da dukkan gaskiyata, zanyi xama na amana dakai da iyakacin imani na, dan Allah sweetheart kaji tausayina...

"Ina sanki MEENATU amma bazan tab'a gaya miki qarya akan hakan dan kiji dad'i ba, wallahi ina san NUWAIRA kuma Auranta nake san nayi nan da wasu watanni, Sam bata san da zaman Soyayyata ba, bare ki zargeta, tun farkwan Soyayyata dake nagaya miki bazan rayu dake ke kad'ai ba, dan haka kisama zuciyarki salama ki rayu da farin ciki, Sannan ki rage kishi dan zai iya haifar miki da matsaloli anan gaba...
Shuru MEENATU tayi mai, daidai

Please Login or Register in order to submit comment