Join Our WhatsApp Group

Idan ku ka ga kun taba wani wuri ya fitar daku a shafinmu, sai ku danna back kuyo baya, ku sani yanzu muna amfani da tallan Popunder a shafin, so karatu zai muku dan wahala, amma ta hakanne kadai zamu iya cigaba da rike shafinnan. idan har bakwa son talla sai kuje ku yi subscription na shafinnan akan karamin kudi ku runga downloading kawai. SUBSCRIBE


DOWNLOAD

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register
DOWNLOAD

dinga bata dariya dan Kawar mata da tunanin lamarin, nan ta yaba da abincin da Hannatu ta kawo mata, HEESHAM dai ya gaya mata bazai gayama NUWAIRA ba, dan zai jefata cikin wani hali, tacemai "karyama gaya mata..


Toh yana fitta daga d'akin yaje ya kulle office d'insa, sanda ya siyama masoyiyar tasa kayan fruit d'in data buƙata Sannan yayi gidansu HASEENAH, bayan yayi parking a ƙofar gidan nasu, nan Ya kira HASEENAN a waya yace mata tazo yana ƙofar gidansu.
Aiko bata fi minti biyu ba sai gata, dake ya fito yana jingine da jikin motar tasa ne hakan yasa direct ta nufesa kai tsaye, aiko ba zato ba tsammani saiji tayi Kawai ya d'auketa da wani matsiyacin mari, kan tadawo normal ya qara mata wasu zafafa guda biyu, kana ya nunata da yatsa yace, "Kishi ba hauka bane, Sannan ai ita ba baiwar gidanku bace, wannan wane irin baqin hali ne, tunda nake ban tab'a ganin mace dabba kamarki ba, wacce bata da hankali Mara amfani da iliminta, naji tsanarki a raina sanadin wannan haukan da kuka aikata tsakaninki da mahaukaciyar Yayarki, idan zakici gaba da gina rayuwarki akan wannan turbar bame auranki sai me irin hali irin naki, ina ruwanki da gidan Yayarki, ina ruwanki da hurumin gidansu, dahar zakije ki daki abokiyar zamanta, y'arki ce ko qanwarki, koko sa'arkice, ni abin mamaki ma ya bani, sa'arki d'aya mijinta baisan ainiyin gaskiyar lamarin ba, kinfi kowa sanin indai AHMAD ne yana daidai dake, ina tabbatar miki akan wannan cikin bar ganin ke qanwar matarsa ce ko ciki d'aya kuka fito ba ƙaramin aikinsa bane ya kulleki akan hakan, yana da kud'in daba me fittar dake idan ya kullekin ke kin sa'ni.

Da kafin na Auri NUWAIRA ina d'an yinki, har tunanin auranki nayi dan qaunar da kike nuna min, amma ayanzu kin b'ata rawarki da tsalle, Saidai ya rage naki ki gyara halinki ko dan nan gaba... Yana kaiwa nan a zancensa ya qara tsaida idansa akanta, yana jira yaga me zata mai, sai yaga kawai zuba masa ido tayi, sai ya galla mata wata shegiyar harara ya juya da shigewa motarsa ya ƙara gaba abinsa..


Sanda ta tabbatar da tafiyarsa sai a Sannan hankalinta ya dawo, nan tad'ora hannu aka ta zambad'a ihu me tafe da kuka tana cewa, "Yanzu akan HAIRANAH HEESHAM yazo har ƙofar gidan mu ya mareni har sau uku, kana ya bini da mugayen zagika nacin mutunci..
Na rantse da Allah sai naci abukazar uban HAIRANAN, zanje gidan nasu ne, saina mata dukan mutuwa Saidai AHMAD d'in ya kullenin..
Tana kuka sosai ta koma cikin gidan nasu, anan ta gayama momyn nasu abin da Yanzu ya faru da ita, aiko nan tahau fad'a ta'inda take shiga ba tanan take fitta ba, daga qarshe dai kasa hakuri HASEENAN tayi ta kira MEENATU ta gaya mata tace mata HAIRANAN tadawo ne, MEENATU tace mata bata dawo ba, toh sundai tsaida magana akan idan ta dawo MEENATU ta gayama HASEENAN dan tayi rantsuwa bazai tab'a yuhuwa HEESHAM ya daketa a banza ba, dole saita rama akan HAIRANAN.. ( Rahama Nalele tace zataga ikwan Allah🤔)



Koda HEESHAM ya koma gidansa kyakkyawar tarba ya samu daga wajen matarsa, wannan yasa ya manta da wata wai HASEENAH, nan ya rungumi matarsa cikin so da ƙauna bai kuma gaya mata komai daya faru da HAIRANAN ba...



AMAAR daya koma gida Hannatu sashi tayi a gaba tace ya gaya mata mesu MEENATU suka kitsa masa, da farko yaso b'oye mata, amma dayaji gaskiyar labari saiya gaya mata yanda MEENATUN ta gaya mai, nanko ran Hannatu ya qara b'aci, wallahi bata san MEENATU, hmm Allah yasa wata rana tatab'ota taga yanda ake dukan mutane..😂



Koda AHMAD ya dawo gida bai kalli MEENATU da batun fad'an nasu da HAIRANAH ba, wannan yasa hankalinta tashi, dan bata san me yake nufi da shurun nasa ba, dan haka sashi tayi a gaba da kuka tana cewa yayafe mata, wallahi HAIRANAN ce tajata da fad'an har hakan ta kasance, dan Allah yayi hakuri.

Yace "Cikin ke da HAIRANAH ban san me gaskiya ba, dan haka abar batun nan, wata rana da kunne na zan gane me gaskiya acikin ku, amma kisani, idan har nagane cewa kece kikaje kika ja HAIRANAH da fad'a har kikayi sanadiyar zubewar cikinta karki manta dole zan d'auki mataki akanki.
Cikin farin ciki da nuna itace me gaskiya tace ta yarda..
Yako sake mata yayi, har yana nuna mata farin cikinsa na samun cikin nata, woo, hakan yayi mata daɗi sosai azuciya...




HAIRANAH ko har washe gari bataga idan AHMAD ba, dan tun fittarsa jiya daga d'akin jinyar da take bai qara waigenta ba, Saidai komai ana mata dan wata ma'aikaciyar asibitin zama takeyi da ita, ga kuma Asiya, komai yi mata akeyi da alama ba abin daza ta nema ta rasa, yanzu damuwarta d'aya shine san ganin fuskar mijin nata, bata damu dasu momy da mamanta ba, dan tasan basu san komai daya faru da itan ba, kulawa dai tana samu ba batun matsala

HAIRANAH tana san AHMAD sosai, kamar tasan yafi ƙaunarta fiye da ƙaunar daya kema MEENATU....
Wannan yasa duk take a haka dataga zata fuskanci matsala daga garesa.


Har tsawan kwana bakwai bataga AHMAD ba, Hannatu ce kawai take zuwa kullum, dama HEESHAM suna tare, idan yaje sallah Qa'ida ne saiya shiga yad'an tab'a hira da ita, kana ya koma kan aikinsa..



Yau dai da misalin qarfe biyu da rabi zuciyar AHMAD ta hanasa dakewa akan qin ganin HAIRANAN dayake san jura har zuwa lokacin da zai bata sallama, dan haka yanzu shigowa yayi d'akin fuska a d'aure, suka ko had'a ido shida ita, dama ya tsaida Anisa kan yau shi zai dubata dan haka Asiya da matemakiyarsa me kula da HAIRANAN suna fitta daga d'akin ya fara duba lafiyar tata, saiga HEESHAM ya shigo dan dawowarsa kenan daga masallaci, ya kallesu yaga AHMAD d'in sai magana yake ma HAIRANAN kan me yake damunta ayanzu, yanda yake mata maganar kamar bai tab'a saninta ba, shiyaba HEESHAM mamaki, lalle har yanzu Yayan nasa na fushi da ita, itako zuciyarta ce taso karyewa, nan hawaye yaso zubo mata, HEESHAM ya mata alama da ido kan kadda tabari hawayen ya zubo mata, aiko cikin sauri ta maida shi, musamman data lura da AHMAD d'in bai wani lura da yanda taso fashewa da kukan ba..
Daidai nan ya fitta daga d'akin, yana godema Allah ko ba komai yasamu sauƙin zuciyarsa.

HEESHAM na ganin fittarsa yace, "Ke wawiyace, kad da ki kuskura ki nuna masa damuwarki sosai akan canjin da yake nuna miki, ta hakan ne zaisa ya sauko miki da wurri, dan zai fara tunin ba shakka bakiso fittar cikin ba, amma idan kika bari yasan kina cikin damuwa sosai zaifi yarda da gangan kika bari cikin ya fitta, sai yanzu abin yake damunki...
Nasan tunanin Ya AHMAD ba d'aya yake da sauran tunanin wasu mutanan ba.
Dan nasan ke a tunaninki nuna damuwar taki garesa zaifi yarda bada san ranki hakan ta faru ba, aa kiyi yanda nace miki zakiga canjawar komai cikin sauƙi, ki rage damuwa, kima d'auki fushi dashi, inkin gansa kidinga cika kina batsewa, zai magantu yace wai me kike nufi ne, daga nan sai nuna masa shi kike nufi, kin gaji gaskiya da wannan d'aurewar da yake miki, idan yaqi kulaki kema karki kulasa na wannan ranar, washe gari nayi, ki fara nemansa da qananun fad'a, wannan kam nasan dole saiya kulaki, nan zakiga ya dawo normal musamman idan kika iya bi dashi a wasan fad'an naki a Soyayyar, 😀Sannan kadda ki yarda ki qara ko kwana d'aya a asibitin nan, yau kisan yanda zakiyi ki koma d'akinki, dan kin warke ba wani abun da yake damunki a yanzu, haka kawai ke kina nan kishiyarki nacan tana maqale miki miji ai wannan bazata kaiki dakyau ba..🤨

HAIRANAH tayi shuru, nan kishinta ya tashi, can kuma ta kyalkyale da dariya, dan ta yarda da zugar HEESHAM d'in d'ari bisa d'ari, nan ta qara tsaida kallansa garesa tace "Wallahi daga yau na canja maka suna daga Aboki ka koma amini na dan gaskiya naji daɗin wannan shawarar daka bani...
Murmushi kawai ya sakar mata...

Washe gari, daya dawo wai qara dubata acewarsa shi AHMAD d'in, d'aura fuska tayi tahau fusge fusgen yamutsa fuska, abin yaso basa dariya amma ya share, dan baiga uwar abin da aka mata ba da zata wani d'aure fuska, _rahama nalele tace baisan shirin na ƙanin nasa HEESHAM bane_

Daya kama hannunta cewa tayi, "nifa na gaji, so nake na koma d'akin mijina, dan haka a sallameni yau kona tafi abuna...
AHMAD ya galla mata harara yace "Baza'a sallamekin ba, kuma an gaya miki mijin naki na buqatarki da ciwo agidan nasa ne, haka zaki zaune har sai kin warke kana ki koma, tashi tayi tana buga qafa tana cewa, "nidai wallahi zan kira momy anjima nace mata an kashe mata jika kuma ana qoqarin ƙarasa mata ni a asibiti, tunda nace amaidani gida na samu lafiya anqi, saboda kawai ana jin daɗin cin amanata acikin gidana ana kwana da kishiyata ran girkina..

AHMAD najin hakan yasan da kishi acikin rikicin nata, dan haka murmushi yayi da juyawa gareta ya qara galla mata harara yace "Wallahi Baby ki shiga taitayinki, tace "nidai in ba'a sallameni ba gayama momy zanyi kuma nayi tafiyata...
Qara dai galla mata hararan yayi baiyi magana ba yajuya zai ficce daga d'akin, aiko sai tayi saurin cewa, minti goma na bayar a sallameni, wallahi in ba haka ba tom..
Har yakai kofar fitta ya kalleta yace "wallahi kika sake kika kira momy ranki zai b'aci, kuma bance ki fitta daga d'akin nan ba, tunda haka kikeso saiki jirani idan na tashi tafiya ma tafi tare... Yana gama gaya mata hakan ya ficce, sai tasaki murmushi da saurin cewa, "Oho dai, ayanzu dai an dena cin amanata..
Ya jita sarai, murmushi kawai yayi, ya gane so take ayi wacce za'ayi kawai a wucce wajen, bata san wannan wasan dayake buga mata..

Tana qoqari zama akan gadan jinyar tata Asiya ta shigo da matemakiyarsa me tayata jinyar, dama Ganinsa ne yasasu fitta..

HAIRANAH ta yarda da ƙaunar da Asiya take mata, dan har yanzu tana hango tausayinta a idan Asiyan..


Sai can dare da misalin qarfe takwas da rabi yaje gareta, aiko ganinta yayi akintsenta, alamar da gaske takeyi, ga Asiya nan a gefanta, sun gama shirinsu tsaf...
Yace suzo su tafi, sanda tad'an ja mai aji kad'an Sannan suka bishi..
Dake tun a ranar Asiya ta kulle mata part nata da key d'inta, hakan yasa yanzu suna zuwa ta bata key d'in, saita karb'a ta bud'e, ita sam tama manta da batun awane hali part d'in nata yake ciki, aiko taji daɗin yanda Asiyan ta kullo mata tun a lokacin, part d'in nata yana nan yanda yake, sai d'an k'ura da yayi, acikin daran suka qara gyarasa ita da Asiya, MEENATU najin dawowarta ta kira HASEENAH ta gaya mata, aiko tace gobe zatazo taci ubanta🤔...

Har wajen qarfe goma da rabi AHMAD bai kulata ba, dataji shuru shuru baizo gareta ba, sai kawai tayi part d'in nasa.
Yana kwance akan gadansa da laptop a gefansa, da alama yana kula laptop d'in kad'an kad'an ne haka, dan ga bacci nan nasan d'aukarsa, ahaka ya ganta ta shigo mai room d'in nasa, kai tsaye ta haye gadan nasa da shigewa jikinsa tana sauke ajiyar zuciya, sosai ta maqalesa kamar yanda ya sabar mata, nan suka had'a ido saita sakar mai kiss a daidai satin bakinsa, kana tamaida kanta qirjinsa alama dai ta nuna bacci tazo yi abinta....
Sam bai kulata ba, dan yasan neman ya kulata takeyi, ya sa'ni sarai tana cikin jini ba bare yace tazo tayar mai da hankali ne, haka ya sake mata tayi baccinta yanda tasa ba ajikin nasa..
Washe gari ma bai kulata ba, bata damu ba, itadai ahaka tamai dukkan abin da yake buƙata har ya fitta daga gidan.

Tana falanta tana sak'a kalan dukan da zatama MEENATU, sai Asiya ta shigo mata wanke wanke, tace "Sannu ranki ya dad'e, tace "Yauwa Sannu Asiya, tace "Dama rokwanki nazoyi, HAIRANAH tagyara zama tace "ina jinki, tace "dan Allah kad da ki kula MEENATU kad da ki mata komai ki barma Allah shi zai saka miki, HAIRANAH tayi murmushi da cewa "ba abin dazai hanani rama dukkan da MEENATU tamun, ikon Allah ne kawai zai hanani, dan haka jeki kiyi aikin ki idan kuma kina san zama y'ar kallo to bismilla, dan yanzu haka part d'in MEENATUN zani...
Asiya ta qarema HAIRANAH kallo rigace da wando a jikinta kayan makka masu santsi, sunyi mata kyau sosai amma kana dai gani kasan Saka kayan na shiri ne..
Batace mata komai ba HAIRANAH tatashi da d'aukar igiyar wuta, wata murtuk'ekiya da ita, da alama wacce aka had'a mata setilet da itace tayi saura shine tagani ta d'auka acewarta yau zata mata amfani, Asiya na ganin wannan igiyar tace Wallahi kallo bazai wucce ta ba, cikin sand'a tabi bayan HAIRANAN...
Cikin iko na Allah k'ofar MEENATUN a bud'e take, HAIRANAH ta shiga dan qarfin hali harda sakama ƙofar MEENATUN key alamar bame shigowa sai in ta bud'e da kanta, Sannan ta cire key d'in ta Saka akan furijin MEENATUN....


Kan uba🤔 MEENATU na kitchen tana dafama HASEENAH indomi da kwai kasancewar tace gata nan zuwa.... kawai saiji tayi an zabga mata bulala a baya, saboda tsabar gigicewa bata san Lokacin data saki ruwan kwan da zata zuba a abun suya ba, ta juyo ga kallanta ga HAIRANAH afurgice, aiko kamar tajuyoma kanta bala'i, HAIRANAH ta shiga shaud'a mata wannan igiyar baji ba gani, nan idan MEENATU yahau zubar hawaye, ta fara ihu tsakaninta da Allah tana neman temako, dan wallahi ita ta cikinta take bata san HAIRANAH ta zubar mata dashi..
Wannan yasa ta durƙusa ta k'udin dine cikin nata tadinga rusa kuka me tafe da ihu,..
Hakan ko yama HAIRANAH dad'i, dan sai zaneta takeyi tana cewa "Dan ubanki zaki qara zuwa ke da qanwarki kuzo dukana da ciki, tana zaneta tana marinta...
Acikin wannan hali HASEENAH tazo gidan, yanda taga Bala direba da Asiya carko Carko a ƙofar part d'in MEENATU shine yasa gabanta fad'uwa, can kuma tafara jiyo ihun MEENATUN...
Ai a haukace take tambayar Asiya me yake faruwa, Bala yace "Ai Hajjiya HAIRANAH ce take Zane Hajjiya MEENATU, kuma daga dukkan alamu MEENATU na cikin mawiyacin hali... Ai HASEENAH najin hakan ta wani kutuntuma wani asher da bugar ƙofar MEENATUN tana zagin HAIRANAH kan idan ta zubar ma da MEENATU ciki wallahi saita kasheta...

Ina HAIRANAH bata san me HASEENAH ke cewa ba, Sam taqi gajiya da dukan MEENATUN dan wata tsanarta ce take qara cafkarta...

Da HASEENAH taga da gaske ba wani temakwan da zata bama Yayar tata sai kawai ta danna ma AHMAD kira, yana d'auka tace mai yazo ga HAIRANAH a falan MEENATU ta kulle ƙofar falan tana dukan MEENATU zata kashe tah, dan gashi sai zaneta takeyi kowa najin saukar bulalar...

AHMAD yace "what..
Me kike cewa, kina nufin HAIRANAH ce ta kulle MEENATU take zaneta kike tunanin kasheta take sanyi...
HASEENAH tace "wallahi kuwa kazo kagani kar cikin aunty MEENATU ya fitta dan Allah kazo ka temaka.
Ai AHMAD bai iya bata amsa ba ya kashe wayar ba wani batun b'ata lokaci ya fitto daga office d'insa yayi saurin shiga motarsa sai gidan nasa..
Tuqi kawai yake yana mamakin HAIRANAH, kodai ba daidai HASEENAH take gaya mai ba..🤔


HAIRANAH ayanzu tana jin ana rokwanta Allah da Annabi ta bud'e ƙofar MEENATUN taqi, sai Zane ta kawai takeyi fin qarfinta, ta farfasa mata baya da wannan igiya, ita so take ma ta shaushaud'a mata a fuska amma dake MEENATUN taqi bata damar hakan shiyasa taketa zaneta a baya da kafafunta....

Mamakin AHMAD ya tsaya ne daya shigo gidan yaji kukan MEENATU da ihunta, sanda ya shiga part d'in HAIRANAH ya tabbatar bata ciki Sannan ya yarda itace me zane MEENATUN,😂 aiko yana zuwa part d'in MEENATUN Bala da Asiya harda HASEENAN suka bashi waje yahau murd'a ƙofar falan da kiran Sunan HAIRANAH, amma shuru sai cika aiki takeyi🤔, nan ya koma part d'insa ya d'auko nasa key d'in na part d'in MEENATUN ya bud'e falan...
Da gasken ya tabbata HAIRANAN ce me cikama MEENATUN aikin, nan AHMAD ya d'auki salati tare da nufo HAIRANAH dan cetan rayuwar MEENATUN, ai HAIRANAH na gane AHMAD ne ya shigo falan saita daka tsalle d'aya sai ganinta yayi tabasa guru alamar bata san ta shiga hannunsa...
Bai kulata ba yayi kan MEENATU cikin matuƙar tausayinta sosai ba abin da yake tunani sai d'an cikinsa da AMAAR ya tabbatar mai tana d'auke dashi...

Sai cewa yake "Sorry my dear, me yake faruwa ne, ya akayi hakan ta faru, Subhanallahi... Kai😨.. Duk HAIRANAN ce ta zaneki haka, duk itace ta farfasa miki jiki...

Rahama Nalele dai barin MEENATU da AHMAD tayi ta koma kan HAIRANAH wacce tunda ta ƴalla ido taga HASEENAH tana wani cika tana batsewa irin an tab'a mata y'ar uwa, HAIRANAH tace dawa kuma Allah ya had'ani, ai HASEENAH batayi zato ba saiji tayi HAIRANAH ta zabgeta da wani mahaukacin mari, kan HASEENAH tagama ganin waƴannan taurarin tuni HAIRANAH tajata jiiiii kamar wata akuya zuwa room na MEENATU da karfin tsiya, taci ko sa'a dan shima key d'in jikin ƙofar bedroom d'in taciki ne yake, dan haka tana hankad'a HASEENAH cikin da qarfi, bayan itama ta shiga, saita maida ƙofar ta rufe tare da saurin Saka mata key... Wannan karan bata cire key d'in ba..
Saita gyara zaman igiyar wutar tata a hannunta, ta kalli HASEENAH da wani shegen murmushi tace, "Yau zanga uban dazai temake ki acikin gidan nan, nayi rantsuwa tunda kika tab'a fatar jikina saina tab'a taki, kinga dai dukan danama yayarki ko, wallahi ke saina miki ninkin ba ninkin sa...

HASEENAH ta kalleta a furgice da mamakin wai ita zata zane.

Ai HAIRANAH na gama lura kallan mamakin da take mata sai kawai ta waniyi kururuwa da wawurar qafafuwan HASEENAH, saiji kake ti ti tim🙈 (ni RAHEEMAT dake tare da rahama Nalele sanda kunya ta kamani,)
Jin wani qara da HASEENAH ta sake najin wani azaba da taji na timuwar da tayi a qasan, habawa, nan ran HAIRANAH yay mata fari Sol Sol, irin tagama samun damar yanda zata zane HASEENAN yanda take so kenan, tunda taci nasarar kayar da ita kasa...

Ba Asiya, ba Bala direba ba, ba AHMAD ba, hatta MEENATU da take buqatar temako sanda ta kalli bedroom d'inta, gabaki d'ayansun nan sanda sukaji timuwar da HASEENAN tayi da Qatar data sake..

cikin tsoro Asiya tace😳 "Yallab'ai, yau inaga aljanu sun shiga jikin Hajjiya HAIRANAH ne..
Bala yace "ni banga lokacin dataja HASEENAH ba, Asiya tace "Ni naga lokacin, amma banyi tunanin HASEENAN zata jayu ba...

AHMAD yace "Ban gane me kuke cewa ba.
Bala yace "Ai Hajjiya HAIRANAH ta qara shigewa da HASEENAH nan d'akin ne da alama itama tana san yi mata irin na Hajjiya MEENATU ne..
Kallan MEENATU AHMAD yayi, itama kallansa tayi fuska a kumbure, cikin sauri ya tashi yana kwankwasa kofar dan wannan bashi da key nata ya manta bai cire ba, fad'i yake, "Wai me yake samunki ne HAIRANAH, me kike san aikatawa ne, Wallahi ranki zai b'aci fah, me yake... Ai bai qarasa ba, yajiwo tana zane HASEENAH, da wanketa da mari tana cewa, "Yau zanga me kwatanki a d'akin nan, badai kun had'u keda shegiyar yayarki kun mun dokan da kuka zubar min da ciki ba...
Sai ji kake shau shau fas fas.. Ga zana ga mari🤔..



AHMAD najin hakan yace "Innalillahi-wa'inna'ilaihirraji'un, cikin lallami yaci gaba da ce mata, toh kiyi hakuri bazasu qara ba, dan Allah karda ki mata yanda kikama yayarta, pls my blood, kiyi hakuri Allah ya huci ziciyarki..

HAIRANAH najinsa sarai bawai bata jinsa ba, da qarfin tsiya taci gaba da zane HASEENAN tana me marinta, tun HASEENAH na ganin HAIRANAN bata isa tayi mata kuka ba, har dai dataga ba sarki sai Allah tadawo take ganin ta isa tayi mata kukan
Can HAIRANAH ta haye ruwan cikin HASEENAH, tun daga sama ta keta mata rigar jikinta da qarfi da yaji, HASEENAH taga bala'in da tunda take iskancinta bata tab'a cin karo da irinsa ba, duk da tana tab'uka dukan HAIRANAN bawai ta barta bane kamar yanda MEENATU tayi, dan gaskiya daqer HAIRANAN ta iya yage mata rigar jikin nata, dan HASEENAN tana da qarfi.
HAIRANAH tasamu damar yage mata rigar tata ne sakamakwan cin galabarta da tayi tun farko data kada ita qasa, tsakanin HAIRANAH da Allah ta shiga cizan HASEENAH a ko'ina na jikinta, akan na fulaninta ne kawai dai bata gantsara mata ba dan tasan idan tayi mata hakan qila ta iya kasheta, wannan cizo na HAIRANAH ya gigita HASEENAH ba d'an kad'an ba, dan ta gama yarda HAIRANAH tafita bala'i
Dan bayan cizan cigaba kuma tayi da zaneta irin wannan zanan da ake kira idan kamin d'aya bazan tab'a mantawa dakai ba, dan zana ne irin na gogaggun azzalimai waƴanda suke yinsa babu mutunci babu tausayawa
Dan tunda tazo duniya bata tab'a cin doka da cizo irin wannan ba, ita tunaninta mah ayanzu juyewa yayi, gani take HAIRANAH aljanune da ita kuma qilama mayya ce, dan haka babu b'ata lokaci nadamar duniyar nan tare da tsoron kar HAIRANAN ta kashe ta ya kama HASEENAH, dan azabar da take gana mata bana sawa bane..
Ayanzu ma tatashi daga ruwan cikin nata, kawai zaneta take baji ba gani, koda HASEENAN tatashi dake ba qarfi a jikinta ba wani abun kirki take tab'okama HAIRANAN ba, musamman da ayanzu da gaske tsoran ta ya shiga zuciyarta, wannan yasa zuciyarta karyewa ta saki jiki HAIRANAH ta dinga zaneta, kuka kam da ihu ba wanda HASEENAH batayi ba, amma HAIRANAH taqi barinta..

Sanda tayi mata fata fata, ta tabbatar ta farfasa mata jiki, fatar tayi bulu bulu da zana, Sannan ta iya barinta, saita kama kunnanta tace "Shegiya kawai, gobema ki qara, kuma Wallahi idan AHMAD ya tambayeki kika qi basa amsar gaskiyar abin da kukamin na rantse miki har acikin baccinki bazan y'aleki ba, zan biyoki nayi miki wanda yafi wannan, bama a farke ba...
Tana fad'in mata hakan ta tsaya tana jan numfashi, dan ita kanta sai taje tayi jinyar kanta, dan rabanta da fad'a irin wannan tun tana qarama..
Sanda ta d'auki kusan minti biyar a tsaye ta tabbatar ta d'an dawo normal Sannan ta nemi gefan gadan MEENATUN ta zauna tana sak'a me zatacema AHMAD, dan tasan dole yasan tana jinsa taqi bud'e ƙofar, dan haka dole ta nemi mafuta kan fittarta daga d'akin...

AHMAD d'in ko sai safa da marwa yake yi, ya rasa yau me yake damun HAIRANAH, damuwarsa kar taje ta kashe musu yar mutane taja masa bala'i, tunani ya shiga kawai gwara ya b'alla kofar koya ceci HASEENAN...
Yana cikin wannan tunani ne sukaji kamar an d'auke ruwa HAIRANAN tabar dukan HASEENAN, cikin tsoro dukkansu suka zubama ƙofar ido kowa da abin da yake sak'awa gabansu na fad'uwa, tunaninsu gabaki d'ayansu ko HAIRANAN ta kashe HASEENAN ne, nan MEENATU ta d'ora hannu aka ta zambad'a ihu tana cewa, "na shiga uku ni MEENATU, AHMAD ka Auro min ruwan dafa kaina, da bamuje mun daketa ba da duk hakan bata faru ba, gashi ta kashe min ƙanwata, na shiga uku ni MEENATU, wallahi idan har HASEENAH ta mutu Saidai nima a kasheni dan wallahi ba makawa saina kashe HAIRANAN...


Da mamaki sosai AHMAD ya kalleta yace "Oho dama da gaske kune kukaje kuka fara nemanta da fad'an harda zubar mata da ciki ko, cikin tabbatarwa MEENATU tace "Eh, kuma Wallahi idan HASEENAH ta mutu na rantse da Allah saina kashe ta Saidai duk ka rasamu...
Yace "Da gaske, tace "ba makawa, dan bani da y'ar uwar datafi min ita.. Yace "Toh Allah ya bata sa'ar kashe HASEENAN, naga yanda za'ayi ki kashe min mata, Dan awajena idan ta kashe HASEENAH ta kashe banza, dan ko inuwarta baki isa zuwa gareta bare ki kama gangar jikinta ki samu madar kasheta ba,
Hmm, saina nuna miki rabata da gud'an d'anta ko y'arta da kikayi ba abin na barki haka bane..

MEENATU najin hakan ta qara sautin kukanta..

Daidai lokacin HAIRANAH tagama tunanin yanda zata tsara AHMAD d'in, dan haka da hanzari ta nufi ƙofar dan bud'ewa
HASEENAH tasaki wata ajiyar zuciya, dan ayanzu bata da wani buri kamar taga fittar HAIRANAN daga d'akin... Gani take kasheta kawai HAIRANAH take sanyi..
HAIRANAN ta juyo ta kalleta dan taji saukar ajiyar zuciyar tata, taci gaba da ce mata, Tashi muje falan dake, ayi
DOWNLOAD
DOWNLOAD

Please Login or Register in order to submit comment