Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

suka fara barin wajen shida abokanayensa..

Su HAIRANAH ne y'an ƙarshe ƙarshen fitta suka fitto ita da Ramlat zasu shiga motar Ramlat d'in, dan dama ita HAIRANAN da Ramlat d'in suka zo, itako NUWAIRA da Hannatu sukazo a motar Hannatun..
Hashim na ganin su HAIRANAN zasu shiga cikin motar ya tsayar dasu, Ramlat ta gaishesa ya amsa da kulawa, kana ya maida kallansa ga HAIRANAH wacce take kallansa haka haka dan ta lura da kallan da yake mata tun zuwanta. kyakkyawa ne na ƙarshe, dole ma ya dinga b'ata tunanin y'an mata.. Da murmushi yake ce mata, "Nifa tun kallan farko danayi miki naji sanki da ƙaunarki sun kamani, dan Allah HAIRANAH kadda kice baki sona..
Ramlat tayi shuru tana so taji me HAIRANAN zatace mai.. Saidai bataji cewarta ba taga Yayan nasu AHMAD yazo wajen nasu yana aunawa HAIRANAN mugun kallo da cewa "Waike baki saka hijabi ne.. Ramlat ta kallesa da mamakin kalmar tasa🤔 ganin gata ita da gyale bai mata magana ba sai HAIRANAN
HAIRANAH ta kalli NUWAIRA wacce suke tawowa ita da Hannatu taga ita kad'aice aduk uban taran tasaka hijabi, ita d'inma bata san wane munafurci bane yasata sawa dan tasan ba ma'abuciyar sakawan bace, kana dawo da kallanta garesa ta gallamai tata hararar tace "eh bana sawa jikinka ko jikina, wai me yake damunka dani ne.. Ai batakai ƙarshen zancen nata da numfashi ba ya d'auketa da wani gigitaccen mari, dan shi abin ya Haɗin masa biyu ne, dajin haushinta da yakeyi na ganin kayan jikinta sun matseta da kuma ganinta da Hashim da yayi, abin ya qara b'ata masa rai sosai, dama so yake tamai rashin kunyar tata ya kuntata mata da mari..🤔
Aiko kuka tafashe dashi wiwi, Ramlat na ganin haka tajata cikin motar tata kawai, dan tasan halin Yayan masu sarai yanzu tana qara cewa wani abu zai qara Falleta da wani marin..
Cikin sauri taja motar tata suka bar wajen..

Hashim yayi saurin kallan AHMAD d'in zaiyi mai magana, AHMAD d'in ya galla mai harara yace, "gurinta kuma yanzu kadawo, so kake ka b'ata mata tarbiya da banzan halinka kome, to bari kaji, bazai maka kyau anan ba, dan bazan lamunta ba.. Da ace bata matsayin k'anwa agareni yanzu zan iya barinta dakai, amma tunda take matsayin qanwa a gareni Wallahi zaban tab'a bari kacimma burinka akanta ba.
Hashim yace "abin da kake tunani badashi nazo wajenta ba, santa nake da Aure..
AHMAD yayi murmushi yace "Baka da gaskiya Hashim, kuma koda hakan ne bazan tab'a bari ka Auretan ba, dan zaka b'ata mata zuri'a ne da abubuwan da kake aikatawa..
AHMAD d'in na gama gayamai hakan yabar wajen zuwa motarsa inda amaryarsa take jiransa..


HAIRANAH ko suna isa tace ma Ramlat Wallahi saita rama abin da AHMAD ya mata, Ramlat tace "Marin zaki rama tace "zaban rama Marin ba, amma Wallahi saina masa abin dazai b'ata masa rai fiye da yanda ya b'ata min, dan sau biyu kenan yana marina..
Shuru Ramlat tayi mata..
Aiko wajen momy taje tana tambayar momyn me kowa anan gidan yafi so kuma miye kowa anan gidan bayaso, momyn tace mata tabari sai gobe zata gaya mata komai, qara gyara zama HAIRANAH tayi tace toh tafara gaya mata abin da Ya AHMAD yake so da abin da baya so, haka momy ta d'aure tana jin bacci tafara gaya mata abin da yake so da wanda baya so..
Nan HAIRANAH ta rik'e komai a kwakwalwarta zuciyarta cike da murmushi take cema aranta wallahi gobe zata shashinsa da b'acin ran abin da zata masa dashi za'a d'aura Auran nasa...

NUWAIRA ko duk rintse idan nata dazatayi awannan daran HEESHAM take gani da HAIRANAH da HASEENAH, abin ya dameta sosai..

Dukkansu sun gane akwai abin da yake damunta, dan gaskiya ta hanasu bacci da motsi..

Washe gari da misalin qarfe takwas taje zata gaida momy, ta kawo kai zata falan dazai sadata da momyn, shima ya sawo kai cikin falan. Nan goshinsu ya had'u ya bada wani guf, tare da wani shock me tafiya direct wajen kwakwalwa.. Shock d'in ya tab'asu sosai..
Cikin mayensa NUWAIRA kamar zatayi kuka tace "Wayyo Allah HEESHAM zaka ciremin kai.
HEESHAM ya zuba mata ido dan tayi maganar ne cikin shagwaɓa kamar tana jiran k'iris tafashe da kuka..
Yace "Kiyi hakuri Antiii NUWAIRA bansan kin tawo ba, tace, "kasani mana tunda inuwa tana aiki kawai karka sake, yace "toh bazan sake ba shikenan, yakai ƙarshen zancen da kai hannunsa kan goshin nata, aiba shiri yayi saurin cire hannun nasa, ita kuma ta janye kanta, saboda wani shock d'in daya qara kai musu farmaki...
NUWAIRA ta zuba mai ido cikin masifar sanshi, saiya hura mata iskar bakinsa, tayi saurin rintse idanta, nan take jikinta ya fara rawa kad'an kad'an, gane hakan datayi ne irin kar HEESHAM d'in ya ganeta sai kawai tayi gaba abinta, yabi bayanta da kallo.
Shidai bai tab'a jin shock irin nata da yaji yanzu ba. Sannan yaji wani iri haka da y'ar maganar nan tashiga tsakaninsu..

HAIRANAH ko tana kitchen taje ajiye cup kamar ance takalli window sai taga AHMAD yana niyar shigowa shashin nasu, tayi murmushi dan tuna yau zata b'ata ransa zai gane wacece HAIRANAH...




Yana shigowa falan ta fitto daga kitchen d'in tana murmushi, tayi kyau sosai cikin doguwar riga ja me ratsin baki, shiko tishet ce a jikinsa da wandan jims, ta kallesa harda wani d'an duk'awa tace, "Barka da Safiya Ya AHMAD da fatan ka tashi lafiya, cikin nutsuwa yace "lafiya lau, yana Faɗin hakan tayi part d'in momy.
HAIRANAH tayi murmushi tace "badai ka raina fatar jikina ba, baka da abin duka sai ita, wallahi zaka sani ne anjima..


NUWAIRA ko da wani yanayi tashiga d'akin momyn tagaisheta da fad'awa tunani, ba shakka idan magana zata dinga shiga tsakaninta da HEESHAM za'a samu matsala, dan gangar jikinta ce zata fara nuna masa akwai abin da yake damunta, shuru tayi kawai tana tuna idan ta kaurace masa akwai matsala, ganinsa shine kwanciyar hankalinta, rashin hakan ko damuwa ce zatayi ram da ita....
"Me yake damunki ne y'ata, momy ta katse mata tunani da faɗin hakan, cikin saurin seta nutsuwa tace, "ina tuna wasu takadduna ne awajen wata ƙawata acan gida kano, shine nake Addu'ar Allah yasa kar na manta idan su mama sun tashi tafiya gobe ince su Karb'a min..
"Ayya, ai haka ne, amma ki fara kiran ƙawar taki ki gaya mata su Maman zasuzo gobe taje gidan ta basu.
tace "Toh..
Ramlat dake jinsu tace, "jiya naga ana shiga da sabbin kujeru gidan..
Momy tace, "Eh, dama ba wani gyara za'a samu a gidan ba, tunda kinga masu gidan ba zama suke a gidan ba, bare ya samu matsala..
NUWAIRA tace, "Gaskiya momy naji daɗin Siyan gidan da Baban namu yayi, Wallahi ina san naga ina da dangi, gashi lokaci d'aya Allah ya wadatamu dasu, kuma saiya kasance muna makwaftaka da d"aya daga cikinsu, gaskiya Dady yayi daya kawo wannan shawarar..
Momy tayi murmushi tace, "Bake ba harni naji daɗin hakan sosai NUWAIRA, Allah ya qara had'e kammu, dan abin da mukeso kenan..
Ramlat tace "Ameen Amiien..
AHMAD ne ya shigo d'akin da gaida momyn, Ramlat da NUWAIRAN suka gaishesa, idansa akan NUWAIRAN ya amsa gaisuwar tasu, dama da ita ya kwana aransa...
NUWAIRA na lura da kallan nasa yayi yawa akanta saitata shi ta ficce daga d'akin Ramlat tabi bayanta..
Momy tayi gyaran murya da tsaida idanta akansa, tace "AHMAD me yake damunka ne.
AHMAD baya b'oyema mahaifiyarsa komai, amma shidai bazai iya gaya mata yana san NUWAIRA ba, dan yasan randa zai b'aci saboda yana gaf da mallakar MEENATU..
Ya kalleta da cewa, "Me kika gani momy.. Tace "jiya awajen fati ina lura da kallan da kakeyima NUWAIRA, wanda a wannan Lokacin da amaryarka ya dace, amma ko kusa baka duba hakan ba gabaki d'aya saika tsaida hankakinka akan NUWAIRA, yanzu ma daka shigo haka kake binta da kallo, gayamin' me yake damunka akanta, santa kakeyi ne koko akwai abin dayasa kake kallanta..
Murmushi yayi da cewa, "ko d'aya momy, kawai dai ta burgeni ne ajiyan kasancewar ita kad'ai ce wacce ta saka hijabi awajen.
Momy tayi murmushi irin nasu na manya tace, "toh meyasa yanzu ma kake kallanta sosai haka, yace "Yanzu kuma kyau tamin sosai..
Momy tayi shuru can tace, "kasan momynsu HASEENAH bata da dad'i, duk da kana da damar yin mata ko nawa kake so amma ni bani san fitina, kasan Lubabatu ba qaramar fitinanniya bace, momyn su HASEENAH na kawo mata wani wargi nan zasu haura, kaga abin saiya zama fitina kenan, ita zafi itama zafi, bana so ka fara san NUWAIRA dan ina san zama lafiya, idan kuma santa ya maka yawa a zuci afasa auranka da MEENATU a d'aura maka da NUWAIRAN tun yanzu..
Murmushi AHMAD yayi da kallanta yace, "Ki kwantar da hankalinki momy na, ba wani abu dazai zo da matsala, MEENATU da NUWAIRA duk abu d'aya ne, abin da Baba Alhaji zaice kenan idan har naje na gaya masa cewa ina san NUWAIRA, kinsan ba makawa a rana d'aya zai d'aura min Aure dasu, batun iyayensu mata ko wannan ba wani abun dazai dameki bane, dama rayuwa tagaji hakan, babu wani abu daza'azo dashi akan hakan ace wai kece sanadi, Gaskiyar magana itace, Duk ranar danace ina san NUWAIRA zanko Aureta, dan haka momy kisa hakan aranki, Sannan idan momyn MEENATU tazo zata saki agaba kan hakan tofa zata haifar ma y'arki d'a me ido d'aya, ayanzu dai bance ina san NUWAIRA ba, amma ban sani ba ko anan gaba zan iya cewa haka.. Yana faɗin hakan ya tashi yana fitta daga d'akin daci gaba da cewa, Bana san damuwarki momyna, ci abinci kisha ruwa ki kwanta HEESHAM d'an hannun damanki yana tare dake ga kuma AHMAD duk naki ne, bame kawo miki matsala a cikinsu..
Momyn najin hakan tayi murmushi kawai, dan tasan sarai AHMAD baya wasa da duk wani abu wanda zaizo ya tab'a masa lafiyarta, dan haka tunda taji yace haka ba mamaki ya dad'e da hango matsalar da take tunani yanzu, ba mamaki ko ya shiryama matsalar ne..


HEESHAM ko rabuwarsa da NUWAIRA wajen shaqatar gidan yayi, anan yaga Hannatu tanata faman had'a jigida😂.. Arayuwar Hannatu tana san jigida, ita da kanta take had'awa, shiyasa Yanzu taketa faman ɗurawa ad'an zaran dake hannunta, Wai ita anufinta zata cire ta jikinta tasaka sabuwa, saboda ta gaji data jikin nata, irin ta tsufa d'innan, sai hakan yazo mata a daidai lokacin bikin AHMAD d'in, ta saka aranta koma miye saita saka sabowar jigida yau ajikinta.. Dan kwana uku kenan tana faman haɗawa, dazaran tafara sai momy ta kirata ta sata wani abun daban, daga nan kuma shikenan sai washe gari, wannan dalilin yasa takasa gamata a rana d'aya..

HEESHAM ya zauna a kujerar da take fuskantarta, tana ganin shine ya zauna taji gabanta ya fad'i dan tasan halinsa, qila ya hanata gamawa akan lokaci..
Dan haka tsaida yin jigidar tayi ta kallesa dakyau tace, "Tashi kabar nan wajen, bana san neman fitina yanzu, kai kuma ba'a zama dakai saikaja mutum da fitina, yace "kinsan miye.. Ta gallamai harara bai kulata ba yaci gaba da cewa, wani abokin Ya AHMAD ne yace wai in shawo masa kan Auntii NUWAIRA, kuma ni gaskiya bazan iya ba, dan d'azu da magana ta shiga tsakaninmu ina gani naga jikinta ya fara rawa, da alama tana d'aya daga cikin irin matan nan dasu basa d'aukar wani lokaci suna magana da d'a namiji, kuma ma ni gaskiya haka kawai naji bazan iya shawo masa kan nata ba, shine ke kika fad'omin tunda naga tafi shiri dake sosai..
Hannatu ta ƙara gallamai harara, tace "Ga marainiyar wayanka ko, dama bakasan ina jin haushinka akan AMAAR ba ko, sai wani qaqaba min shi kakeyi kamar dole ne Soyayyar.. Toni yanzu bazan mata magana ba, tunda naga kana ganin mutuncinta har ka iya kiranta da Auntii saikaje ka gaya mata da bakin naka, ai dama kai aka tura da sakwan..
Cikin shammatarta HEESHAM ya d'auke jigidar tata da tashi yayi saurin yin gefe can.
Gaban Hannatu ya qara fad'uwa, nan tatashi kamar zatayi kuka zatayi magana yayi saurin cewa.. "Wallahi kina tawowa inda nake zan saki jigidar nan na zugeta ta watse a qasa tas...
Hannatu tasan halinsa sarai dan haka saita had'iye yawu tace "zanyi duk abin dazaka sani amma karka zuge jigidar pls, wallahi kwana uku na d'auka ina ɗurawa..

Yace "Badai kin rainani ba, ba dama nace kimin abu sai kiqi yi, bayan shekara biyu ko uku ne kika ban kacal, amma kin maidani kamar wanda kika ban shekara goma, dan haka kingani.......
HEESHAM ya d'aga jigidar nan sama😳 ya zuge mata ita a ƙasa tas🤔🤔🤔 saijin zubar kyawawan dutsunan kake a ƙasa ƙas ƙas ƙas...
Hannatu na ganin haka ta rushe da kuka wiwi .
HEESHAM yayi murmushi daci gaba da cewa, An zuge d'in Kiyi abin da zakiyi, ina gaya miki yanzu nine yayanki baki yarda ko.. Hmm kici gaba damin rashin kunya wallahi zaki dinga ganin abin dazan dinga miki ne..😡
Kawai Hannatu shek'awa da gudu tayi zuwa d'akin momy.. Yayi murmushi yasan taje gayama momyn ne, taje ta gaya d'in.. Ya faɗi hakan a bayyane.

Zai juya ya bita NUWAIRA ta shigo wajen, tana had'a ido dashi tayi saurin juyawa, dan bata san yana wajen ba, kawai ta nufo wajen danta samu damar yin tunaninsa sosai ne..
Aiko cikin sauri yasha gabanta yana cewa, Yawwa tsaya Auntii NUWAIRA..
NUWAIRA ta tsaya amma ta rintse idanta tace, Na tsaya HEE-SHAM menene, saiya zubama kyakkyawar fuskarta ido, yanda ta amba'ci Sunan nasa a yanzu ya mai dad'i sosai yace "Kice mace ta biyu wacce ta iya kiran sunana daidai..
NUWAIRA ta bud'e idanta akansa, tace "Wacece tafarkwan, yace "Wata ƙawata ce a skull ana kiranta da Ashanty.
Tace "Ƙawarka ko budurwarka, yace "dukka biyun, cikin damuwa da sanyi tace "kuma har yanzu kuna tare.. Yace "Lokacin dazan dawo Nigeria Babbanta yaje ya d'auke ta akan zata duba maihaifiyarta bata jin dad'i.. Naje mata sallama qawarta take gayamin hakan yasa na kirata awaya ban sameta ba wanda har yau ban qara nemanta ba...
NUWAIRA taja numfashi tace "kuma kana tunaninta har yanzu ko.
Yace "Gaskiya na manta da ita banda yanzu da kike kirani da irin kiranta hakan yasa na tuno da ita, kuma nasan hakan yana da nasaba da yanda ban wani sakata a raina da yawa ba, kinsan masu iya magana ma sunce idan zakaso abu asoshi kad'an, haka idan zakaqi abu kaqishi shima kad'an... Maganar gaskiya Soyayyar dama Soyayyar wani d'an lokaci ne, wannan yasa ko kad'an banji wani abu araina dangane da rabuwa da ita ba.. Wallahi idan kin yarda na manta da ita, sai yanzu..
Tace "gashi ni bazan dena kiranka da hakan ba, dan naji yayi min daɗi a baki, gashi kuma ba zanso ka dinga tunawa da ita ba, ya kenan..
HEESHAM yayi shuru zaiyi magana tayi saurin cigaba da cewa, Ina nufin, bazanso duk Lokacin dana kiraka da salon hakan ka tuna sa ita ba, dan nasan hakan ba amfanar dakai komai zaiyi ba, hasalima takaici zakaji dan bakasan a ina take ba idan da ace kaji kamar kaje gareta, wannan yasa kaji nace maka bani san ka dinga tunawa da ita..
Shurun dai ya ƙara mata, Ganin hakan yasa jikinta san fara rawa, bata san ya ganota ko kad'an, lura da yanayinta da yayi na ganin jikin nata zai fara rawan ne yasashi Sakar mata murmushi yace "Nagane, kici gaba da kirana da hakan, nayi miki alk'awarin zan kawar da nata jin DAGA ZUCHIYA TAH, na fuskanci naki jin, dan ko'a murya tata da taki akwai bambanci, idan kika kirani da hakan nasan kece dan bantab'a cin karo da murja me irin taki sak ba..
Cikin sauri NUWAIRAN ta kallesa da cewa, "Kana nufin nafita dad'in murya, Yace "aikema kin sani, nifa ko! Da gaske ban tab'a jin daɗin muryar budurwa kamar taki ba, dama HAIRANAH ce, sai kuma danaji taki naga kinfita nesa ba kusa ba..
NUWAIRA tayi murmushi tace, "Toh Nagode..
HAIRANAH ce ta shigo wajen tana cewa.. "Wato nice banda daɗin murya ko HEESHAM..
HEESHAM yayi murmushi yace, " Da taki muryar nakeji amatsayin cakwai, amma tun daga ranar danaji tata naga tafi taki cakwai..
"Haka kowa yake cewa wai tafini kyau da daɗin murya.. HAIRANAH ta dad'i hakan da murmushi..
HEESHAM yace "ba gaskiya bane, na yarda tafiki daɗin murya, amma fa kin fita kyau nesa ba kusa ba,..
NUWAIRA tace "wannan kuma ba gaskiya bane, ni nasan dukka nafita, dan na yarda ta cewar jama'a..
Har a zuciyar HEESHAM da gaske shi gani yake kamar HAIRANAH tafi NUWAIRA kyau, kodan tashiga ransa ne🤔, gani yake kawai NUWAIRA daɗin murya zata nuna mata da kyan jiki, dan tafi HAIRANAH abubuwan d'aukar hankali..
HAIRANAH tace "Rabu da ita aboki, bazata tab'a yarda nafita kyau ba, amma zata yarda nafita wayo.. Yanzu dai kaje momy na kira, danga Hannatu can tana kuka wai ka zuge mata jigidarta wacce ta d'auki kwana uku tana had'awa.. HAIRANAN takai ƙarshen zancen nata da kallan ƙasa tagako dutsunan jigidar baje awajen...
Yace mata "toh, da kallan NUWAIRA yaci gaba da cewa, kinsan miye, NUWAIRA ta girgiza mai kai alamar aa, yaci gaba, wani abokin Ya AHMAD ne yake sanki, pls ki soshi ko kad'an ne, zaizo gareki sunansa Bashir..
NUWAIRA najin hakan ta nufi fitta daga wajen ranta b'ace tana cewa "Bana sanshi Wallahi, dan Allah kadda kabari yazo gareni, dan zai b'atama zuciyata rai sosai, musamman idan natuna kaine kake san had'amu..
HEESHAM ya kalli HAIRANAH yace, "Dan Allah Ƙawa kid'an shawo masa kanta alamu sun nuna tana damun zuciyarsa sosai..
HAIRANAH tace, "hmmm ba ruwana, dan na lura kwana biyun nan ranta yana b'aci dani, ban qara tabbatarwa ba sai jiya, kaidai kaje ka cika ladanka, Amma kafin nan mufara kwashema Hannatu stone d'innan nasan momy baza tamaka fad'a sosai ba..
HEESHAM ya kalli yawansu a kasan, yace "Tab, waye zai sunkuya kwashewa, wallahi bazan kwashe ba, ai itace taja hakan..
HAIRANAH tayi murmushi tace "Bani labarin abin daya faru, nanko ya gaya mata komai, HAIRANAH tace kai ne da lefi Wallahi HEESHAM..
Baijita ba dan yayi gaba, nan ta durƙusa tahau kwashema Hannatun..

HEESHAM na zuwa yaga Hannatun sai kuka take, ya kalli Momy ta galla mai harara da cewa, "wato kai idan ba'ayi fad'a dakai ba ba'a zama lafiya ko..
Bud'ar bakinsa sai cewa yayi.. "Momy itace bata da kunya, na gaya mata yanzu nine Yayan itace ƙanwar amma taqi ki saimin rashin kunya take, Toh wallahi ki gaya mata idan ina sata abu tana cewa bazata min ba doka zan fara mata, koda yake bama damuwa dan yanzu zanje wajen Baba Alhaji na qala mata sharri kan sun daidaita da AMAAR a had'asu Aure kawai.... Yana kaiwa nan yayi niyar fitta daga d'akin, aiko Hannatu ta ƙara fashewa da kuka dan ita dai bata san AMAAR, dan kawai ya fara san Aina'u wata y'ar uwar tasu a dangi, amma bawai dan yana da muni ko wani mugun hali ba, kawai dai kishi ne ke damunta, dan haka ita dai bata ba Auransa.. momy najin hakan tayi saurin cewa, "Zonan Autana, Ai baza'ayi hakan ba, dan tasan kad'an da aikinsa yayi abin dayace, gashi ta kwana da sanin ita Hannatun bata sanshi, danta fad'a mata wata ranah, wai Baba Alhaji ya had'ata da koma waye a dangi amma banda AMAAR..

HEESHAM najin abin da momyn tasu tace ya dawo harda wani d'an nuna b'acin rai kamar shine da gaskiya, Ramlat dake jin draman girgiza kai kawai tayi, anata ganin wai a hakan yana d'agama Hannatun qafa, dan ita gani take babu wanda yafi rainawa kamarta, gashi tabashi shekara huɗu amma sam baya ganin girmanta, toh taya za'ayi yaga girman Hannatu bayan shekara biyu tabashi, qara girgiza kanta tayi dacewa aranta halin HEESHAM sai shi, ya zamar musu qaya, badamar hukuntashi...

Momy tahau shafa bayansa tana cewa "Haba Autana, meyasa kake yima yayunka haka ne, bayan ba qaramin ƙaunar ka suke ba, kullum ina tunanin zaka dinga karage wasu abubuwan amma sai nake ganin kamar bazaka rage ba..
Yace "yanzu me kikeso nayi momy.. Tace "bana so kaje wajen Baba Alhaji da wannan magana daka faɗi yanzu, Sannan kabama Hannatun hakuri, sanda ya harari Hannatun kafin yace, "Toh Kiyi hakuri bazan qara ba..
Saita gallamai harara tare dayin kwafa...
Sanda momy ta shiryasu kana kowa ya kama gabansa..

Qarfe goma da rabi abokan AHMAD suka fara cika gidan, dan sha d'aya za'a ne za'a d'aura Auran nasu

A dai dai lokacin HAIRANAH taje bakin windown bedroom d'in AHMAD d'in talek'ashi, nan taganshi cikin kyakkyawar shiga, dan farar shaddace ajikinsa fara soll, gashi d'inkin ya zauna masa, "gaskiya yana da kyau, HAIRANAN ta faɗi hakan a bayyane, daidai lokacin yana d'aura Agogo a hannunsa, sai wani abokinsa ya shigo bedroom d'in nashi da murmushi akan fuskarsa yana cewa, "Ango kasha ƙamshi, gaskiya wannan wankan yayi min kyau, wanda yayi aikin ya iya sosai, abokin nasa ya Faɗi hakan yana mai kai hannunsa gaban rigar AHMAD din dan tab'a aikin rigar...
HAIRANAH taga kamar abokin nasa zai ganta, dan haka nan tajuyo ahankali tayi kitchen d'in momy, roba tasamu ta ibi miyar amalar biki wato miyar karkashi wacce tayi yauk'i ainun, dake kofar AHMAD d'in biyu ce, akwai wacce zata sadashi da Momy ta cikin gida, akwai kuma wacce zai iya fitta ta tsakar gidan wato harabar gidan, haka taje kofar dazata sadashi kai tsaye da Momy wacce ƙasanta yake shinfid'e da tayes, tabi inda ƙafa tafi takawa ta yaryaɗa miyar karkashin nan, saita koma kitchen d'in ta ajiye robar, kana taje ta b'oya awani d'an sak'o wanda zai bata duk abin dazai faru tagani batare da kowa ya ankare da ita agun ba, ta zaro wayarta da lalubo number na AHMAD d'in wacce ta cire a wayar Ramlat tafara kiransa, Lokacin yana fesa turare akan wannan kyakkyawar kwalliyar tasa kenan yaga kiran nata, dama bashi da number nata bare yasan wacece, nan ya d'auka da cewa "Hello, tana jin muryarsa tayi murmushi tace, "Ya AHMAD kayi bak'uwa a shashin Momy, tana jiranka pls yanzu dan zata tafi ne, gashi momyn bata kusa bare taji dame tazo, ina nufin tana toilet..
AHMAD ya lunshe ido, muryar yarinyar tayi mai dad'i sosai, yanayin muryar tata kamar ta NUWAIRA, nan yace da ita, "Ke wacece.. Tana jin haka tayi saurin kashe wayar tata tana murmushin mugunta, AHMAD na ganin hakan yasa wayar tasa a ajjihu, ya kalli wannan abokin nasa yace mai "Bari na duba wata a shashin momy minta d'aya pls..
Abokin nasa me suna Sani yace "idan ka wucce kasan zuwa zanyi na d'aukeka da kaina dan lokaci ya gabato..
Murmushi AHMAD yayi kawai da bud'e kofar da zata sadashi da shashin momyn cikin sauƙi wacce HAIRANAH tayima aiki, Sam bai lura dame yake ƙasan tayes d'in ba, kawai ya tawo gabaki d'aya kuma cikin sauri.
Aiko wani shegen santsine ya kwashesa duk iya ƙoƙarinsa nasan ganin karya faɗi a ƙasan wannan tayes d'in yayi amma abin yaci tura, nan ya faɗi akansa tim🙆🏻... Kuma hakan yazo a rashin sa'a dan jikinsa ya bada wani sauti na ƙaƙa-ƙas.😨
Wannan sauti shiyasa HAIRANAH fitowa daga sakwan da take cikin sauri ta nufesa tana me ƙaremai kallo, fatanta d'aya Allah dai yasa bai karye ba..
Dake cikakken namiji ne, idansa a rintse yake tamau kana dai gani kasan baiso wannan faɗuwar ba.. Sai HAIRANAN tayi tunanin bai samu karaya ba, kawai timuwa ce, Hakan yasa taji dariya tazo mata batare data shirya ba...🤔 ta ƴalƴale mai da dariya.. Lokacin ya bud'e idan nasa cikin jin wata azaba wacce bai tab'a jin irinta ba, dan wannan ƙara da jikinsa yayi wanda yasa HASEENAN fitowa cikin sauri' ƙafarsa ce d'aya ta karye, kuma ya timu sosai abin babu dad'i sam😊..
Ta gallamai harara tace "Dama nayi alqawarin bazan tab'a barinka kaje d'aurin Auran ka da wannan shegiyar budurwar taka cikin farin ciki da walwala ba, dan bazan kirata matarka ba tunda ba'a shafa fatiha ba, kallo d'aya nayi mata naji bani santa batayi min ba sam, magana dai anan itace kaima kasan bazan tab'a yafe maka a karo na biyu na marina da kayi ba, wannan yasa na shirya maka gadar zare, ko babu komai bazakaje d'aurin Aure da kayan daka saka aranka zaka dasu ba, Sannan nasan kaji zafin wannan fad'uwa da kayi, kaga naci riba biyu kenan, na rama marin daka min cikin sauƙi, Sannan na b'ata ran matarka dan bai zama lalle kasamu zuwa ɗaurin Auran naka akan lokaci ba, ƙilama kaƙi halartar wajen, wannan zance

Please Login or Register in order to submit comment