Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

nima ban tashi sanin komai ba sai a cikin satin nan, tabbas HASEENAH ce ta kashe Ameer, kuma...
Rufe mata baki AHMAD yayi da hannunsa yace "Ayanzu bana san jin hakan, dama amsar tambayata kawai nake san ki bani, kuma naji, dan haka gobe k'arfe takwas zaki kaini wajen malamin..
D'aga mai kai tayi hawaye na zubo mata.
Daga nan tashi yayi yabar mata falan nata, bayan ya d'auki wayarta batare data sa'ni ba, Hikimar yin hakan kuwa shine baya san ta kira kowa nata a daran..

Wannan dare dai ba wanda yayi baccin nutsuwa a cikinsu su biyar d'in, wato AHMAD HEESHAM MEENATU Sadeeq da Khadija, Dan NUWAIRA baccinta tayi hankakali kwance, haka ma HAIRANAH sai dai ita da d'an fargaba a tare da ita, dan bata san me za'ayi a gidan Baba Alhaji gobe ba, haka bata san me yake damun mijinta ba..

Amma HEESHAM da zaran ya rufe idansa ganin HASEENAH yake lokacin da take yanka mai Ameer d'insa, yadai raya daran da nafula da rok'ar Allah akan ya goge hotan abin acikin idansa ya dena gani.

AHMAD ma lafula ya dinga yi, yana rokwan Allahn ya kwantar ma da d'an uwan nasa HEESHAM d'in hankali, yasaka masa hakuri da dangana..

MEENATU wannan shine karo na biyu arayuwarta data tab'a yin lafula Raka'a biyu akan Allah ya yafe mata kurakuranta, ya kuma hana AHMAD rabuwa da ita...
Danta tsorata sosai da komai ayanzu, tunda HASEENAH ta gaya musu kisan da tayi ma Ameer d'in hankalinta yake a tashe, gaskiya duk rashin imani irin nata bazata tab'a iya aikata hakan ba, Wannan yasa duk ta rasa nutsuwarta, tare da jin tausayin NUWAIRA, duk sai taji bazata iya aikata wani aiki na baƙin hali a yanzu ba, dan atsorace take alamar imani ya shigeta.. ( Rahama Nalele tace ikwan Allah, gaskiya ne ba'a shedar mutum 💯, dan ako wane lokaci yakan iya canjawa🤔 )


Sadeeq kam ba damar tashi yin lafular, Khadija ce dai tayi tana rokwan Allah daya wargaza duk wani makirci na HASEENAH cikin sauri...


Washe gari HEESHAM ya tashi dajin sauƙin damuwar aransa, da alama Allah ya karb'i Addu'ar da AHMAD ya roqa mai cikin sauri ne.

Suna kitchen suna had'a breakfast, dan zasu kaima Sadeeq asibiti ne,
Sai Ya kalleta cikin so da ƙaunarta yace "My Auntii, tace "Welcome Luvly, yace "Bafa gajiya nayi ba, tace, Toh menene, yace "Na tuna jiya Baba Alhaji yayi kiran gaggawa yau, da alama akwai wani abu me mahimmanci da yake san isarwa garemu ne, dan haka muna gama breakfast bayan mun kaima Ya Sadeeq nasa ma wucce daga can ko.
Cikin sanyin jiki tace "Luv, kodai magana zaiyi akan matsalarmu.. HEESHAM yayi murmushi da yawota jikinsa yace "Idan ace hakan ne menene Luvly, tace "Akwai matsala mana, gwara mu barta da Allah kawai ya isan mana, dan wallahi a tsorace nake da duk wani lamari na HASEENAH, kawai idan binkice zaiyi akan lamarin muce mun yafe kawai, dan bana san ka fad'i gaskiya taje ta kashe min kai..

Murmushi ya qara sakar mata da bata kiss a inda ya dace kana yace, "Ki kicire tsoran HASEENAH aranki my Auntii, ki kuma cire tunanin wani ba Allah ba zai kashe miki mijinki, ki saka kishin d'anki a gabanki ki d'aukar mai fansar kisan wulaƙancin da aka mai akan idanki, dan Allah Auntii kiba maqiyanki kunya ki nuna masu baki tsoransu, ta hakan ne zakici galabar way'anda ma baki san da zamansu ba...

Shuru tamai, hawaye na zuba mata, ganin hakan sai yaci gaba da cewa.. Magana ta gaskiya nasan magana zaiyi akan matsalar tamu, kuma nasan komai zai kwab'ema HASEENAN, Sannan a matsayina na mijinki ina san ki gaya ma Baba Alhaji komai idan ya tambayeki, bani san ki b'oye masa komai, idan har kina san ganin farin cikina, idan har kina san in dena ji araina HASEENAH tafi qarfinki, duk da nasan ba rayuwa zatayi ba, amma kafin ta mutu ina san ki tabbatar mata da cewa babu tsoranta daidai da kwayar zarra acikin zuciyarki, ina san ganin wannan tsoran nata ya juye ya koma tsana tsantsa a gareki, dan Allah Auntii kiyi dukkan abin dana gaya miki... Yakai ƙarshen zancen nasa da lashe mata hawayen..
Nan gabanta ya shiga fad'uwa, ta fara jin wani ciwo aranta, *ABU KAMAR WASA FAH* taji tafara jin tsanar HASEENAN, nan da nan taji zata iya yi mata komai idan dai suka had'u, dan ita dai bata bata had'a jin kowa dajin mijinta ba, tayima zuciyarta hud'uwa taji zancen kowa amma tafi d'aukar na HEESHAM da mahimmanci, wannan yasa taji a yanzu bazata iya qin bin umarninsa akan wannan rokwan da yayi mata ba..
Nan ta qanqamesa tana cewa "zanyi duk abin da kake so my dear, zanyi koma me kake so my Luv, fatana kaci gaba da sona.. Cikin farin ciki. yace "Naci gaba da sanki NUWAIRA, na SOKI babu adadi acikin raina my Auntii....






MEENATU tun qarfe bakwai ta gama shirinta tsaf, sai taci gaba da naman wayarta wacce taketa nemanta tun jiya, dan tana so ta kira HASEENAH ko momynsu ta gaya musu abin daya faru tsakanin ta da AHMAD d'in daran jiya, amma neman duniya bataga wayar tata ba, haka dai tagaji ta zauna zaman jiran fitowarsa.

Qarfe bakwai da rabi ya fitto daga room d'insa yayi dining, sanda ya gama breakfast d'in data mai kana yaje ya duba HAIRANAH, ya sameta cikin kwalliya da qamshi, ya rungumeta da gaya mata zasu fitta unguwa shida MEENATU, daga can sa ha'd'u a gidan baba Alhaji, tace Toh ba damuwa sai ta iso, kiss ya kasar mata dayi mata bye, saita bishi da kallan wacce unguwa haka zasu shi da MEENATUN...

Cikin tagumi ya samu MEENATUN, ya zare mata hannayen nata da cewa, "Nayi breakfast ni kad'ai yau banga ko qeyarki ba, kawai gayamin damuwar ta miye dana ganki cikin tagumi, tace "tunani nake akan yanzu idan ka rabu dani ya zanyi da rayuwata, yace "Sai ki bari idan na rabu dake d'in saiki shiga tunanin yanda zakiyi da rayuwar taki..
Tace "gaskiya a tsorace nake, nasan bazaka tab'a barina ba tunda kagane matsalar daga garemu take, ta kai ƙarshen zancen da zubo da hawaye.
Nan ko tausayinta ya kamasa, ya Saka hannunsa ya d'auki yaran nata da cewa "Ina jiranki a mota..
Shuru tayi mai, hawaye na dad'a zubo mata, haka dai ba yanda ta iya ta tashi dan bin bayan nasa.

Ko a motar ban da nuna mai hanyar gidan malamin ba abin da yake shiga tsakaninsu.




*ABIN DAYA FARU SHINE*

____Wata rana Ranar laraba HASEENAH taje wajen malamin nata tana mai gaya mai itafa ta gaji gaskiya ya gaya mata abin da zatayi dan tasamu HEESHAM, gaskiya hak'urinta ya qare...
Yace mata toh zai bata wani magani ta shafa a fuskarta, indai zata iya kashe yaron dabai fara baki ba, ta kuma kawo masa jininsa to zai mata aikin da zata sha mamaki, dan HEESHAM da kuka zaizo mata yana rokwanta Allah da annabi ta Auresa, amfanin shafa maganin a fuskar tata kuwa shine, duk wanda yaga lokacin da take kisan, zai matuqar tsorata da ita zai kuma kasa gayama kowa, idanfa da tsari a jikinsa kenan, idanko ba tsari Sam bama me ganinta. jin hakan yasa HASEENAH jin daÉ—i sosai, sai kuma ta fad'a tunanin a ina zata samo yaro, (Sam dake zuciyarta babu imani bata fara tunanin yaushe zata iya yin kisa ba, kawai tunanin nata tafiya yayi kan ina zata samo yaro)

Sanda ta shafe kwana uku tana tunani, kana can tunanin nata ya bata ai ba yaran daya dace ta kashe sai Ameer, dan shine yaran datafi tsana a yanzu, nan ta shiga tunanin yanda zatayi ta kashesa, amma tunanin nata yaqi bata hanya, sanda ta qara komawa wajen malamin nata sai yayi mata wasu tsaface tsafacensa sannan yace da ita, zata iya shiga gidan HEESHAM nan da kwana uku, sam me gadin gidan da masu aikin gidan baza suga shigarta da fitarta ba, indai zatayi hakurin jiran fitowar wani daga cikin gidan yayin da zata shiga, haka indai zatayi hak'urin shigar wani gidan yayin da zata fitta....
Tace mai dan Wannan ba matsala ya bata maganin kawai.

Idan me karatu bai manta ba, zai iya tuna ai a baya can kafin Al'amarin ya faru HASEENAH ta nunama MEENATU wallahi saita wargaza farin cikin HEESHAM dana NUWAIRA za kuma tagani ganin idanta.

Shine bayan haka da kwana biyu al'amarin ya faru..

Daman HASEENAH bata kwana a gidansu ba ana gobe abin zai faru, a Hotel ta kwana, hakan yasa k'arfe bakwai na safiyar ranar tayi shirinta tsaf a cikin hotel d'in, Doguwar Riga bak'a tasaka wacce ta sitirce mata jikinta, tasaka safar hannu da qafa tare da d'aukar wata baqar jaka wacce zataci qaramin yaro, da wuqarta me kaifi, saita shafa wany'annan magungunan da malamin nata ya bata, kana ta nufi gidan HEESHAM d'in a motar wata qawarta da itama take hotel d'in.

Da takai ragub'ewa tayi a wani d'an sak'o, haka tadinga tsaki ganin HEESHAM yaqi fitowa,.

Da gaske hakan take dan HEESHAM d'in bai fitta ranar da wurri ba, idan me karatu ya tuna..
Can tana a hakan ta gansa ya fitto, Sam bai ganta ba, akan idanta me gadin gidan yayi saurin yin d'akinsa kamar yanda abaya yace ya tashi da lalurar gudawa, hakan yama HASEENAN dad'i sai tayi saurin shiga gidan kan get d'in ya rufe kansa, kanta kuma tsaye tayi shashin NUWAIRA tunda malamin nata ya tabbatar mata bame ganinta..

Cikin sand'a ta nufo room d'in NUWAIRAN, tana kallo kuwa NUWAIRAN ta ajiye Ameer d'in ta shiga toilet, hakan yasa ta shiga room d'in gabaki d'ayanta, ta tsaya qarema yaran kallo, ganin yanda yake da wani kyau na ban mamaki, sanda ta gama kallansa da qarema room d'in kallo tsaf kana ta d'auki fillo ta dannama Ameer d'in, to tana a hakan ne NUWAIRA ta fitto daga toilet d'in ta ganta....
Duk da ta gantan dan rashin imani ta kuma yanka sa akan idan nata, tare daja mata kunne kamar yanda kuke da sanin hakan a baya...

Toh tana cikin ja mata kunnan ne NUWAIRAN ta fad'i qasa sumammiya, hakan yasa HASEENAN Saka Ameer cikin wannan baqar jakar tata ta fitto harabar gidan da sauri ta b'uya a jikin wata fulawa, tana a haka ne taji ana kwankwasa get, sai taga me gadin gidan ya fitto da danna remote, sai get d'in ya bud'e taga Zuwaira ce y'ar aikin NUWAIRAN, tana shigowa sai HASEENAN ta tuna ai koda zata wucce ta gabansu bazasu ganta ba kamar yanda malamin nata ya gaya mata, amma duk da haka tana cikin tsoro, haka dai tayi shahada ta ratsa ta bayansu ganin suna gaisawa tayi saurin ficcewa kamar yanda saura kad'an get d'in ya gama rufe kanka..

Ba wani kuma batun b'ata lokaci ta fad'a wannan motar qawar tata da tazo da ita tayi saurin tayar da ita ta qara gaba..

Bata dire a ko ina ba sai'a gidan malamin nata, shi kansa yayi mamakin ganinta da Ameer, ya kumayi imani HASEENAN bata da imani ko kad'an, haka dai ya ibi jinin Ameer d'in yayi tsaface tsafacensa, ya bata wani magani da turare, yace duk iya wiya taje taci wannan maganin a abinci, ta kuma Saka turaran a jikinta, sau uku, na rana uku, kar tayi fashi, duk ran data had'u da HEESHAM magana kuma ta shiga tsakaninsu ba abin dazai hana HEESHAM Auranta, idanko tabari adaidai wannan lokacin wata magana bata shiga tsakaninsu ba har HEESHAM d'in ya sume bai furta mata wata kalma ba! toh komai ya karye, sai an sake saban aiki...

Godiya tamai da bashi abin da yake so a gareta, tace to ya zata suyi da gawar Ameer d'in, tunda jininsa yake buqata, gashi kuma ya samu, sai yace karta damu zai siyarma da wani abokinsa gawar..

Haka ko tana fitta ya kira wani abokinsa ya Siyar mai da gawar Ameer d'in..

Itako a ranar ta fara aiwatar da abin da yace mata..

Bayan taci maganin ta Saka turaran na kwana ukun sai kuma ta fara tunanin bai kamata taje ma HEESHAM d'in yanzu da yake cikin wani hali ba, ya kamata ta jinkirta zuwa garesan, dan kar a zargeta..
Har malamin nata ta tambaya shawara yace tayi hakuri zuwa sanda NUWAIRAN zata samu lafiya, zatafi samun yanda take so,..

Wannan yasa tayi hakuri har zuwa ranar da taji NUWAIRA ta samu lafiyar dawowa tunaninta, shine ai taje asibitin ranar tana yima HEESHAM d'in barka da hakan, jin qamshin turaran nata yasa bai iya amsa mata ba yaji jiri ya kamasa sai kawai ya tsinci kansa da sumewa, shine har ta shiga Wannan rikicewar a wancan lokacin tana me gayamai yace da ita wani abu mana kafin ya sumen..

Toh shine tun daga lokacin malamin nata ya gaya mata komai nata ya kwab'e, dan haka tayi a hankali dan yana ganin asirinta ya kusa tonuwa..

Shine tayi tunanin indai haka ne toh gwara ta kashe HEESHAM d'in NUWAIRA ta rasa itama ta rasa.

Shine ai tana kan aiwatar da hakan ne Khadija tajiyo labarin itace ta kashe Ameer d'in a wajen Arfat me gyaran jiki, har ta gayama Sadeeq ya Ankare da HASEENAN da yagani a asibitin su HEESHAM d'in yabi bayanta har dai ya bayyana mata kansa tasaka mutanan nata dasu kashe mata shi, shine Allah bai basu Sa'a ba dai Sadeeq ya samu kansa wanda har a yanzu yake a kwance

Wannan shine abin daya faru wanda HASEENAN da malaminta suka aikata akan Ameer...















__________ AHMAD Qurama gidan malamin ido yayi lokacin da suka iso bayan MEENATUN ta tabbatar masa nan ne gidan malamin, gida ne mekyau amma ba can sosai ba.

Dake ƙofar gidan guda biyu ne, akwai wacce zata sadaka da d'akin malamin kai tsaye wato ta farkwan, akwai kuma ta iyalansa itace ta biyun, toh ata farkwan ne yanzu haka wasu Mata sukayi layi, sun kai su shidda zaune a bakin kofar..

AHMAD ya kalli agogwan hannunsa yaga tara da rabi, amma dan masifa haka Matan nan suka bar gidan mazajensu sukazo wajen wannan masiyacin, wanda ba abin dazai basu sai kayan tsiya..

Nan zuciyar AHMAD tahau d'aukar zafi, ranshi ya shiga b'aci, nan babu b'ata lokaci ya kira shugaban y'an sandan da matsalar tasu yake hannunsa, ya bashi adireshin gidan malamin da gaya mai matsayin malamin akan lamarin, da kuma cemai suzo yanzu da sauri susa mesa a kofar gidan malamin..
Batun b'ata lokaci kuwa yace mai gasu nan zuwa..

Nan gaban MEENATU ya shiga bugawa, hawaye ya shiga zubo mata da fawansa ayanzu..
AHMAD ya kalleta yaga gabaki d'ayanta a tsorace take..
"Muje kimin sallama dashi, ya fad'in mata hakan a hankali tare da fitta daga motar..
Itama fittowan tayi tana me kwantar da d'anta a kafad'arta, tahau kwankwasa wannan ƙofar tashi a hankali..

D'aya daga cikin matan wajen ta kalleta a fusace ta ce "Haba keko baiwar Allah ya daga zuwanki zaki wuccemu kije kina kwankwasa mai ƙofa, dukkanmu da kika gammu anan ai ba zaman banza mukeyi ba, ba wanda kikafi sauri acikinmu dan da yawanmu mun bar yara ko karyawa basuyi ba.

Wata ma acikinsu ta amshe da cewa, "Toh kodai bata san yau ranar zuwa da safe bane, tayi tunanin ko rakiya mukayo... Wacce ta fara maganar tace "Wannan ai zancen banza ne, haka kawai dai bazata ganmu da yawa haka a kofar inda yake ba, kuma ko bamu da aikin yi baza mu rak'o mutum d'aya da yawanmu haka ba..


MEENATU dai na jinsu batace dasu k'ala ba taci gaba da kwankwasa mai ƙofar, aiko zuwa can AHMAD yaji malamin na cewa "wai waye yake damuna ne haka..
MEENATU tace "malam ka fitto za'ayi magana dakai ne..
Tsaki yaja batare daya qara magana ba.

Shuru bai kitto ba har kusan minti goma, saima wata mata ce data fitto a gajiye, tayima matan wajen sallama ta qara gaba, shiko sanda ya qara minti shidda Sannan ya fitto...
Yana had'a ido da MEENATU yace "Hajjiya MEENATU kenan, yau kuma wane saban salo ne da kwankwasa min ƙofa haka, ai da kin basu hakuri zasu iya barinki ki shigo idan kinga bazaki iya zaman jira ba, Sannan abun mamaki ban tab'a ganinki a rana irin tayau bah..

MEENATU da tunda ya fara magana gabanta yaci gaba da bugawa, cikin wani hali ta ce mai, "Sau biyu nazo gareka, idan ban manta ba, kuma ba zuwan kaina bane zuwan Qanwata HASEENAH ne, kadena nuna wannan sakewar kana nuna kamar akwai wata kyakkyawar alak'a tsakani na dakai, dan ban tab'a Saka kayi min wani mugun abu ba, Duba kalli gefanka kaga... Ta nuna mai AHMAD wanda yake mai kallan tsana, kana taci gaba da cewa, Bak'o kayi mijina me san had'uwa dakai cikin gaggawa..
Takai ƙarshen zancen da Addu'a cikin ranta akan Allah yasa mamakinta yasa ya kasa cewa komai dan idan yace ya tab'a mata wani aiki ya qaryata abin data fad'i mai yanzun! Tofa akwai matsala, dan zai dad'a b'ata mata sauran mu'amalarta ne da AHMAD d'in, wanda ayanzu Addu'a take akan Allahn yasa karya saketa wallahi tayi nadama....

Aiko d'auke kallansa daga kan AHMAD malamin nasu yayi ya dawo da kallan nasa kanta cikin mamakinta, irin me zancikanta suke nufi, tana nufin bai tab'a mata wani aiki ba kome me take nufi..
Kan yayi mata magana sai AHMAD yace dashi... "Dan jini kad'an... Aiko yana juyowa AHMAD d'in ya d'aukesa da wani mahaukacin mari, wanda tunda yayi dai wayo ba'a tab'a yimai irinsa ba.. Cike da tsanarsa AHMAD d'in ya kwacume mai wiyansa yayi wata hajijiya dashi ya d'agasa sama ya nana da kasa, Sannan yayi saurin hawa ruwan cikinsa ya fara kaimai wani naushi a baki da hanci, nan da nan ya had'a mai jini da majina yana cewa.. "Ka aikata aiki mafi muni a rayuwarka wanda shine zai zama ajaninka, ina nufin yaran HEESHAM da NUWAIRA wanda HASEENAH ta kashe ta kawo maka gawarsa kayi mata aiki dashi, kasani daga yau ka rasa dukkan wani farin cikin ka a duniya, addu'armu bazata fad'i qasa banza ba dan har acan gidan lahira baka ba samun rahamar ubangiji...
Zaiyi mai magana ya basa wani naushin a wiya...

Kaf matan wajen tashi sukayi suna rattaba salati da ihun kar AHMAD ya kashesa, wannan ihun nasu shiya jawo hankalin matar malam d'in ta fitto taga abin da yake faruwa, dariya tayi da cewa "Bawan Allah kashe shi, barin irinsu masifa ne a doron qasa, wallahi kullum cikin yimai wa'azi nakeyi, na tsanesa saboda Wannan mummunar d'abi'ar tasa.
Gashi yayi min asirin karna gayama kowa abin da yake aikatawa, shi da bakinsa ya gaya min hakan..

Tana rufe baki HASEENAH ta tsaida motarta awajen, dan tazo ne dan malamin nata ya duba mata me za'a tattauna a gidan Baba Alhaji dataji ya kira mitin jiya cikin dare kamar yanda taji momynsu na fad'a mata.

Cikin sauri ta fitto daga cikin motar tata ganin kamar MEENATU tagani, dasan sanin me yake faruwa taga mutanan wajen a tsaye haka, dan ko kad'an bata gano AHMAD ba.
Saidai daidai Lokacin bata kaiga qarasawa wajen ba y'an sandan da AHMAD d'in yama waya d'azu suma suka tsaida tasu motar a wajen, nan hankalin kowa ya koma cansu, hakan yasa HASEENAH taga AHMAD d'in, shima ko ya Ankare da ita, aiko cikin sauri ya cema y'an sandan su kama HASEENAN, cikin sauri ko suka kamata dan tayi niyar tserewa, kana AHMAD d'in ya tashi daga kan malamin wanda yaji maza, sai ya nuna musu shi shima suka kama sa...

AHMAD yaja numfashi da cigaba da cema y'an sandan yana san su fara zuwa dukkansu gidan kakansu kafin su kaisu can wajen nasu..
Shugaban y'an sandan baija ba, nan yace mai wannan babu damuwa, nan AHMAD ya shiga motarsa da MEENATU, y'an sandan kuma suka shiga tasu motocin da malamin da HASEENAN....

Nan matan wajen suma suka watse, matar malam kuma takoma gidan nata dan had'a kayanta, yau dai taji daÉ—i an kama mugun mijin nata, yanzu kome zata fad'a akansa danginta sa yarda, dan yau bakinta ya bud'e, wato watan karyewar al'amuransa ya kama..



HEESHAM da NUWAIRA suna asibiti gun Sadeeq, yace dasu, "Naso ayi zaman damu, NUWAIRA tace "Allah ya qara maka lafiya Ya Sadeeq, insha Allah baza kuyi missing komai da za'a tattauna a zaman ba, komai zaku jishi kamar a gabanku akayi..
Khadija ta goge hawayen daya zubo mata tace "Wallahi NUWAIRA zaki samu yara fiye da Ameer, dan Allah ki kwantar da hankalinki karki tada hankalin naki.
NUWAIRA tayi murmushi tace "Aini nagama jin dukkan wani abu da zanji akan tafiyar Ameer gareni, Allah ya saka min ta wakkali da dangana, ayanzu bani jin komai, na tabbatar ba isata bace tasa Allahn ya bani shi awancan lokacin, haka kuma ban san dalilinsa na karb'arsa a wannan yanayin ba, amma nasan koma miye da yardarsa alkairi ne agareni da mijina, dan qila girmansa agaremu ba alkairi bane, hakan yasa yace bara ya rabamu dashi tun yana qarami, kuma albarkacin Addu'a da wannan fatan da kika min zan samu wasu fiye dashi, albarkacin manzan Allah..
Nan suka amshe da sallallahu-alayyiwassallam gabaki d'ayansu, daga nan suka musu sallama sukayo gidan Baba Alhaji..



Aiko Gidan ya cika maqel dan kowa jikinsa ya basa wani abu ne me matuƙar mahimmanci Baba Alhajin yake san gabatarwa tunda yayi kiran dabai tab'a yin irinsa ba cikin dare..

Dake su momy da iyayen su NUWAIRAN basu san abin da yake faruwa ba hakan yasa suke daidai da sauran dangi, dan sai magana suma suke azuci kan me yake faruwa..

HEESHAM da NUWAIRA sukaje suka gaida Baba Alhajin, kana suka je suka gaida iyayen nasu da kakaninsu da dai dangin nasu, suna zama HAIRANAH ta shigo, bata kaiga zama ba Ramlat da Hannatu suka shigo a tare kamar sun had'a hanya, suna cikin gaisawa ne su AHMAD suka qaraso suma..
Nan kallo ya koma kansu, ganin AHMAD da Yan sanda, gashi sai hankad'a qeyar HASEENAH suke tare da malaminta..
Shi kansa Baba Alhaji yaji mamakin hakan..

Yayin da hankalin momyn su HASEENAN ya bala'in tashi
Dadynsu ko daga kallan da yake ma HASEENAH yasan koma miye za'a fad'a akan HASEENAN bame dad'i bane..

Nan dai NUWAIRA ta kafe HASEENAN da ido, zuciyarta nayi mata zafi, tana qara jin wata zazzafar tsanarta wacce bata tab'a jin irinta a duniya ba..


Babah Alhaji yaja numfashi dayin bisminlla ya gabatar da addu'ar daya saba idan ya tara taro irin hakan, kana ya maida kallansa kan AHMAD yace "Alhamdulillah Alhamdulillah, na kira tawo kamar yanda ka buqata, ina san ka matso kusa dani ka bud'e murya ka gayama kowa abin da kike san fad'a..

AHMAD ya matso gaban Baba Alhajin da kallan yawan dangin nasu da iyayen nasu kana yace, "Nasan kowa yasan da zaman me yake faruwa da HEESHAM, kowa ya girgiza da abin daya samesa, hakan yasa jami'an tsoro damu kammu muketa binkice dan musan daga ina matsalar tafaro, Toh Alhamdulillah Allah me kowa me komai ya bayyana mana komai a ranar jiya, munyi shuru ne dan karmu tada han kulanku ku kasa bacci cikin kwanciyar hankali, abin daya faru shine, duk wannan MASIFAR da laba'in ba wanda ya had'a face HASEENAH, itace ta shiga gidan HEESHAM ta kashe mai d'ansa da fillo tare da kara wuk'a ta yankasa yankan rago saboda tsabagen rashin imani, kawai Ita damuwarta tacika burinta.....

Nan gabaki d'aya kowa agun ya d'auki tafa hannu da salati suna masu kallan HASEENAH wacce kanta yake qasa... Nan batare da b'ata lokaci ba kowa agun ya shiga tsine mata suna cigaba da cewa, Amma ko ke HASEENAH Allah yayi wadaranki, Allah ya tsine miki, Allah yayi ma HEESHAM da NUWAIRA sakayya..

Iyayen HEESHAM dana NUWAIRA kuwa dasu Ramlat Baba Alhaji Dadyn HASEENAN gabaki d'aya daskarewa sukayi a zaune..

Ganin hakan yasa AHMAD zuwa wajen kayan kallan Baba Alhajin ya Saka wannan fulet CD d'in na tunanin NUWAIRAN, ya kunna TV nan kowa yaga lokacin da HASEENAH take aikata wannan rashin imanin...

Gabaki d'aya jikin kowa sanyi yayi, nan suka dinga cewa dole NUWAIRA ta sume, tashiga d'aukewar tunani, dan gaskiya ne taga bala'in da bazata tab'a mantawa dashi ba..

Dadyn HASEENAN ya kalleta hawaye na zuba mai yace "Allah ya tsine rayuwarki HASEENAH....
Babah Alhaji da Dadyn HEESHAM suka rintse ido, basu so ya tsine mata ba..

Nan cikin k'arfin hali momyn su HASEENAN tatashi tana cewa, "Kowane mutum da kuka sa'ni aduniya baya yin abu sai da manufa, bai kamata kuta tsine mata batare da kunji me zatace ba, amma ba komai ni dama nasan ba ƙaunar y'ay'ana ake ba, zan fad'i dalilin dayasa ta

Please Login or Register in order to submit comment