Join Our WhatsApp Group

Idan ku ka ga kun taba wani wuri ya fitar daku a shafinmu, sai ku danna back kuyo baya, ku sani yanzu muna amfani da tallan Popunder a shafin, so karatu zai muku dan wahala, amma ta hakanne kadai zamu iya cigaba da rike shafinnan. idan har bakwa son talla sai kuje ku yi subscription na shafinnan akan karamin kudi ku runga downloading kawai. SUBSCRIBE


DOWNLOAD

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register
DOWNLOAD

lokacin zaki dinga nuna mai duk wani abubuwa na sO, nasan bazaiqi karb'a ba, dan yana da sauƙin kai, kuma kinga zaiyi tunanin d'an harkar da kuka fara ne kika fara sanshi, bazai kawo miki matsala ba Nina sani..
Tana jin hakan tayi dariya tace "Komai yana zuwa min da sauƙi ayanzu tunda kasan abun da yake damuna Ya AHMAD.
Yace "haka nake sanji, yanzu gobe zan bar gidan nan, tunda naga da gaske zakibi duk abin da nace miki, amma zan dinga zuwa dan tabbatarwa, tace "Toh Nagode sosai ya AHMAD.. Yace "Yauwa na tuna idan kina san komai yazo mana cikin sauƙi saifa nima kin tayani qoqari akan HAIRANAH, bana santa da SAMARI, da kuma yawan fitta unguwa, dan Allah idan kikaga tafara d'aya daga ciki ki gayamin.. Tace "Insha Allah baza kayi missing d'in ko d'aya ba, dan ina ganin kiris zan kiraka, ammafa idan ka Auri HAIRANAH bazasu shirya da Aunty MEENATU ba.. Yace "Zasu shirya ne Saidai in ban Auretan ba, tace "Toh Allah ya tabbatar da alkairi.. Ameen yace da nufar motarsa da alama fitta zaiyi..


"Lallema🤔... Shine abin da HEESHAM yace a bayyane, dan yaji dukkan abin da suka tattauna akansa da kuma HAIRANAH, dan zai sako kansa a harabar gidan kenan yaji AHMAD d'in nace ma NUWAIRAN mutumin bai fitta bane, shine HEESHAM d'in ya koma baya kad'an yaji wane mutumi ne yake tambaya, Ashe shine mutumin😃...

Idan ya gane maganganun nasu Wato NUWAIRA sanshi ne ya sata a gaba kwanakin baya, da AHMAD d'in ya sani shine yake ɗorata akan hanyar da zata bi danta samesa cikin sauƙi, gefe guda kuma yana san ya Auri HAIRANAH, wacce bata san da Soyayyarsa ba..

Wani shegen murmushi HEESHAM d'in yayi da cewa, "Allah na gode maka daka dasa sona a inda ya dace, wow yanzu nayi dace a Soyayya, NUWAIRA kin tara duk wani abubuwan da nake so agun y'a mace, A yanzu harna canja soyayyar da nake miki zuwa soyayyar ma'aurata, dena tsayawa bud'emin hanya akan Soyayyar danna rigada na shigeta yanzu yanzu, amma hakan bashi zai hanani yin maganinku ke da Ya AHMAD ba, saina nuna muku cewa bako miye bane ake samunsa cikin wayo da dabara, baki yana da amfani sosai wajen magance matsala ba tare da bama kai wahala ba, zan nunama HAIRANAH cewa koda taji za'a had'a auranta da Ya AHMAD karta yarda har saiya fitto da kansa yazo yace mata yana santa kafin ta yarda da hakan, haka ni da kaina zan b'ata tunaninki NUWAIRA kizo ke da kanki ki gaya min cewa kina sona, dan bazan tab'a yarda kusamu Soyayyar mu cikin wayo da dabara ba..

Dama ni tun had'a jikinmu na farko dake NUWAIRA nasan akwai wani sirri tsakanina dake, yana kawowa nan azancen nasa ya qara sakin wani murmushin dan yayi imani yafi NUWAIRA wayo, zai sameta yanda ya dace, Sannan duk muskilancin AHMAD saiyasa HAIRANAH ta sauke masa shi...
Wannan dalilin yasa bazai nuna musu yasan komai da suke shiryawa akansa shi da HAIRANAH ba... Yana kawowa nan a tunaninsa ya qarasa fittowa harabar gidan...
Idansa akan NUWAIRAN yace, "My Auntii kina nan ashe, kikasa naje inata nemanki gaskiya kinban wahala sosai...
Tace "Ayya, waifa nayi tunanin kawai fittowa zakayi hakan yasa na tsaya tsayuwar jiranka, dan nasan qila ka iya Faɗin min wani abun..
Zuba mata ido yayi dasan sanin wani abu, aiko ganin ya zuba mata idan nan yasa jikinta san fara rawa,
Ya sakar mata murmushi dan sai yau ya gane meyake sa jikin nata yin rawan, Ashe daga shine, daga san da take masa ne, shi kad'ai ne yake sa jikin nata yin rawa, ahankali yace da ita, "Gobe ranar Hutu ce, dama ace nakaiki guraran shaƙatawa, dan na lura ba wasu gurare kika sani ba anan garin, cikin sauri tace "aa ba yanzu ba HEE-SHAM, gaskiya akwai matsala, kaga ni bana san na dinga dad'ewa tare da maza, ta faɗi hakan bakinta na rawa...
Murmushin dai ya qarayi, yace, "Toh my Auntii duk ran da kikaso hakan kimin magana, tace "Toh..
Sai yayi motarsa yana cewa, "Auntii babu Addu'ar Allah ya dawo dani lafiya, cikin sauri tace, "Kullum fa ina maka HEE-SHAM, idan baka dawo akan lokaci ba hankalina tashi yake, duk rasa nutsuwa ta nake, Yace "dagaske..
Shuru tayi, ganin takusa kwafsawa, koma ta kwafsa..
Ya gane sarai furucin yazo mata ne dake DAGA ZUCHIYARTA yake, amma badan taso faɗin hakan ba..

Nagode sosai... Shine abin dayace mata da sakar mata murmushi kana yaja motarsa, wanda me gadi tuni ya bud'e mai get..

Sai tayi shiru kawai, haka dai jiki a sanyaye tayi ciki....

Shiko har yakai asibiti da shauqinta aransa..❤❤❤
Duk sai yaji yana jin wani daɗi na shigarsa..



Haka dai yadinga duba mutane kallo d'aya zaka mai kasan akwai abin da yake masa daɗi, abokinsa Jabeer daya kawo mai ziyara da ranah yace, "HEESHAM na lura yau akwai abin da yake maka dad'i, HEESHAM ya akallesa da murmushi yace "Slsai d'an uwa, watace take sona, sai nima naji ina santa.. Jabeer yace "Toh Allah ya tabbatar da alkairi, yace Amiien, Jabeer zai qara mai magana sai wayarsa tahau ruri, yana dubawa yaga HASEENAH ce, da kamar bazai d'aga ba, amma kome ya tuna sai kuma ya d'aga,
"Haba HEESHAM wai meyasa kake min haka ne, meyasa kake gudun mutumin da yake sanka ne, ka duba kaga fa ni y'ar uwarka ce, amma saiya kasance baka da abunqi kamar ni... HASEENAN ta faɗin mai hakan cikin damuwa sosai..
HEESHAM yaja numfashi yace da ita, "Me yake damunki ne HASEENAH, meyasa kike faɗin kalaman da basu dace ba, Ya za'ayi ina d'an uwanki kuma na kasance bani da abun ƙi kamarki..
Tace "Kacanja min, wallahi ka canja HEESHAM, acanja kwata kwata, bana san HAIRANAH dan tagama tafiya da tunaninka, wallahi na tsaneta nesa ba kusa ba.
HEESHAM yayi murmushi yace "wai kina tunanin san HAIRANAH nake. Tace "Idan ba santa kake ba to meya jawo wannan shaquwar taku, yace "ina san HAIRANAH amma ba irin san dake kike tunani na Soyayya ba, dan babu Aure tsakani da ita, dan haka kidena jin tsanarta aranki pls...
Nan cikin murna tace "wallahi ban tab'a jin daɗi a rayuwa irin nayau ba, ina sanka HEESHAM dan Allah kaima kasoni kamar yanda nake sanki, yace "Nifa na gaya miki kidena sona, dan gaskiya ni ban shiryama Soyayya yanzu ba, tace "amma nace maka zan jiraka har zuwa lokacin da zaka shirya mata ko, yace "Yes, kuma ina miki fata alokacin ki zamo kece tafarko wajen shigewa cikin zuciyata, yanzu lokacin sallah ya gabato ki huta lafiya, ya kai karshen zancen da kashe wayar.. Jabeer yace "Aini na d'auka HASEENAN ce tayi ram dakai har kake cikin farin ciki, HEESHAM ya tashi yana cewa, "Gaskiya Jabeer ban damu da HASEENAH ba, hasalima ban san wata Soyayyar gaskiya ba, sai akan wannan Auntiin tawa, dan santa na shiga cikin zuciyata naji da bambamci sosai, musamman da ayanzu nake jinsa yana bin jinina, gaskiya tayi babbar sa'a, dan nayi imani ba wani wanda zai sota sama dani.. Kawai wasa nake da HASEENAH a Soyayya, dan ban tab'a jinta ko kaɗan a raina ba, dan ban tab'a zama nayi tunaninta ba..
Jabeer yace, "Haka Allah yake ikwansa, kaga ya dasa Soyayya azuciyar mutum cikin lokaci qanqani, amma duk da bansan ita wannan d'in ba na tabbatar bazatafi HASEENAH da komai ba.
HEESHAM yayi dariya sosai, yace "Wallahi kaji dai bazan rantse maka ko, Auntii tafi HASEENAH komai, dan ita tana d'aya daga cikin matan da suke da wahalar samu, sun tara komai ne abokina, Auntii takai sha d'aya ba goma ba...kawai dai ka share, kabar batun HASEENAH, dan sai ran dakaga Auntiin tawa zaka san NI DA ITA MUN DACE DA JUNAH..

Jabeer yayi murmushi yace "Sai kiranta kake da Auntii ita ba da suna ne ko da gaske ta girmeka ne, HEESHAM yace sunanta ma qila baka tab'a jinsa ba, kuma ni bazan gaya maka shi ayanzu ba, saboda wani dalili, kuma da gaske ta girmeni amma kad'an haka, dan shekara biyu taban....
Jan numfashi kawai Jabeer d'in yayi..



NUWAIRA ko can wajen qarfe hadu da rabi tana kitchen tana kicikicin dafa ma HEESHAM abinci wanda take da sanin yana so.. kallo d'aya zakama momy kasan tana cikin farin ciki, kuma ba farin cikin komai bane face na kulawar da NUWAIRAN ta d'aura d'ammarar bama HEESHAM d'inta...
A duk cikin y'ay'anta ba wanda take MASIFAR SO kamar HEESHAM d'in, kuma duk wanda zai kyautata mai ba ƙaramin sanshi take ba... Wannan dalilin yasa NUWAIRAN ta qara shiga ranta sosai..

Haka dai HAIRANAH da Hannatu na taya momyn abincin gida NUWAIRA nayin nata da HEESHAM.. Ahaka suka gama lokacin qarfe shidda da minti goma.. Haka dukkan su sukaje yin wanka..
Sanda sukayi sallah kana kowa ya shiga gyara kansa, NUWAIRA dai gyaran na HEESHAM ne, Ramlat ma na SABEER ne, Hannatu kuma na AMAAR ne, HAIRANAH ce dai batayi wani shiri ba..

NUWAIRAN taji dawowar HEESHAM Lokacin tana toilet, dan haka yanzu kiransa tayi a waya, lokacin ya dawo daga masallaci kenan ya d'auka da cewa "barka da dare My Auntii, sanda ta lumshe ido kana tace "Barka da dawowa, da fatan komai normal yake agunka tun daga safe zuwa yanzu, yace da sauƙi dai, "dan agajiye nadawo, tace "Toh kwantar da hankalinka, dan nayi maka girki me daɗi, na tabbatar zai kore dukkan gajiyar daka dawo da itan, yace "Wow my Auntii, kina san sagwab'ani fa, Allah yasa yafi na jiya dad'i, tace "insha Allah zaifi, "Toh gani a falo zaki iya fittowa ki bani.. Tace mezai haka, ban minti d'aya kawai..
"na baki my Auntii.. Ya faɗi da kashe wayar.. Yana me kallan Ramlat dake falan, da wani makeken madubi akan cinyarta sai faman ɗaurin ɗan kwali take.. Sanda yaga ta kusan gamawa tsaf Yaje ya ture d'an kwalin daga kan nata bayan yasan tasha wahala wajen d'aurawa..
Aiko nan tatashi afusace da kallansa zatayi mai magana sai yayi saurin ce mata, "an tunkud'e d'in,😀 kuma wallahi kimin masifa kiga abin dazan miki..
Ramlat tana da hak'uri sosai hakan yasa tamai shuru, zata d'auki d'an kwalin nata a k'asan ne kome ya tuna sai kuma yayi saurin d'auka ya bata.. Ta kallesa kad'an tace "Allah Ya shiryeka HEESHAM, Yace "Ameen, nafa baki ne kawai dan karki barni da Allah da kuna ganin hakurinki, da Hannatu ce da abin dazan mata sai yafi haka, tace "Allah ya kusa rabamu ai, maga da Waƴanda zakayi anan gaba, yayi murmushi da cewa "abu me sauƙi sai nayi da budurwata, itama murmushin tayi tace "Aiko da bame Auran ka wallahi. Murmushin ya qarayi ganin tawowar NUWAIRA yaje ya karb'i farantin hannuntan ya ajiye a gefe yana cewa "Gaya mata my Auntii, shin zan rasa matar Aure dan halina, NUWAIRA tayi saurin girgiza kai da cewa, "Ina fa, bayan samun irinku wahala ne dashi, mace ko wacece ita idan har bata kawo kanta gareka ba, na tabbatar idan kace zaki Aure da gudu zata yarda..
HEE-SHAM yayi wani shegen murmushi yace, "Ina sanki my Auntii, kisa aranki kedai kam babu ke acikinsu, babuni babu kawo miki matsala..
NUWAIRA tace "nako gode sosai..
Ramlat tatab'e tace "Waike yaban HEESHAM kike, lalle baki san waye shi ba, koda yake naga kuna d'asawa bazai miki yanda yake mana ba, bare ki yarda shid'in bashi da hali..
NUWAIRA tace, "Magana indai akansa ne, bazan jiki dakyau ba, musamman idan maganar akan Faɗin aibunsa ne, ya kamata Ku gane Nafi sanshi fiye da kowa anan gidan, kasancewarsa d'an Autan momyna🙈 .. Takai ƙarshen zancen da rufe fuskarta.. Ramlat tasaki dariya tace, "muna nan dake komun d'asawarku wata ranah saikun rabe, dan futunarsa acikin jininsa take..
NUWAIRA ta bud'e idanta kenan zata bata amsa, saiko taga Hannatu ta bayan HEE-SHAM d'in tana ƙok'arin ture masa farantin abincin nasa.. Ai cikin sauri NUWAIRA tace mata "Dan Allah Aunty Hannatu karki zubar mai, wallahi nafi awa biyu ina shiryamai, ke kin sani, jin hakan yasa Hannatu fasa zubarwar, daidai nan kuma HEESHAM d'in ya juya yana kallan Hannatun da d'aga kai yana cewa, "Barta my Auntii, ta zubar, bako abin da zai hanata dafa irinsa wallahi..
NUWAIRA taje ta d'auke farantin tana cewa, "Nawa nake so kaci ba nata ba... Yayi murmushi cikin MASIFAR SONTA yace "Ai zanci ne, koda ya zube Allah saina ibi na qasan naci dan ganin Fatin cikinki.. Tace "Bazama akai ga hakan ba, dan ina san kaci ayanda zan baka yanzu, muje nakaika har k'ofarka pls karka kula Hannatun. Sanda ya gallama Hannatun harara Sannan Yace "Angama Auntii..
Yana gaba tana binsa a baya, ba ƙaramin kyau yayi mata ba, jikinsa komai cif, ba abin dayayimai yawa ba abin dayayi mai kad'an.. Komai nasa abin kallo da sha'awa ne..
Suna kaiwa ta miqa mai farantin tana cewa, "Dan Allah idan yayi maka dad'i ka kirani anjima ka sanar dani, dan zan qara samun qarfin gwiwa sosai.. Yace "Na miki alqawarin kiranki alokacin daya dace, Sannan bazan fasa gaya miki ba... Sai yayi shuru yaqi ƙarasa furucin nasa, yana me bud'e ƙofar tasa, dasan ajiye farantin abincin cikin falan nasa, yayin data zuba mai ido tana me san jin qarashen furucin nasa, dataga baida niyar qarasawa sai tace, "Sannan bazaka fasa gaya min meba.. Sanda ya ajiye ya juyo ya kalleta da sakar mata murmushin da yayi imani bazata manta dashi nan kusa ba, yace da ita, "muryarki tana mun dad'i sosai, kuma gaskiya wankan nan yayi min kyau sosai, yakai ƙarshen zancen nasa da fara d'aukarta hoto a wayarsa, yana cigaba da cewa, wow kinga inda hotanki yake haska wayata.. Sanda tabari yagama d'aukarka sai tayi tafiyarta batare datace mai komai amma fa fuskarta tana d'auke da murmushin jin daɗi..
Yabi bayanta da kallo da tabbatarma kansa sun dace da juna..

Aiko yaji daɗin abincin nata sosai, ya yarda ita d'in gwanace akan komai na girki... Bai kirata a Lokacin ba, dan yasan bazai barta da tunaninsa a Lokacin ba, yafisan ya kirata tana gab da kwantawa bacci, hakan zaisa ya qara shagalar da ita akan sanshi... Dan haka kiran HAIRANAH yayi yana cewa, "Ya akayi ne, tace "Lafiya lau, ka dawo lafiya, yace "Laulau, tace "Dan Allah kakaini wajen shaƙatawa gobe, tunda ranar Hutu ce, yace "angama ki shirya da misalin qarfe biyu.. Cikin murna tace "Nagode sosai Allah ya kaimu goben, yace "Ki huta.. Yana faɗin haka ya kashe wayar.. Da marna HAIRANAH tatashi dan gabatar da sallar isha'i dan taji ana kira..

Shima masallacin yayi, sanda yakai kusan tara a masallacin Sannan ya dawo gida, a room d'in Momy yaga AHMAD suna maganar komawarsa gidan nasa gobe, HEESHAM yamai Sannu.. Cikin farin ciki ko ya amsa mai..
Sai wani tunani yazo ma HEESHAM d'in ya kalli momy yace.. "Momy banga HAIRANAH ba, gashi tayi bak'o a waje..
AHMAD ya kallesa da sauri yace "Waye bakwan, HEESHAM ya tab'e baki yace, "Wani saurayinta ne, da alama sun dad'e da juna ita dashi, dan har cewa yayi na gaisheki momy.. HEESHAM ya kai qarshen zancen da kallan momy..
Ai kan momyn tayi magana ya tashi yana cema momyn Saida safe.. Tace "Toh Allah ya kaimu... Saiya ficce da sauri.
HEESHAM yasan zaije yaga waye ne, saiko ya kyalkyale da dariya

AHMAD bai jisa ba, direct ko harabar gidan yayi, yayi duban duniya baiga kowa a harabar gidan nasu ba, sai yayi waje nan ma baiga kowa ba, ransa sai ya bashi qila mutumin ya tafi ne, dan yasan HEESHAM baya ƙarya, nan yaja tsaki ransa b'aci dan yaso yaga bakwan tana yaja masa kunne..
Haka yahau kiran NUWAIRA, tana d'auka yace mata, "Wani bak'o yazo neman HAIRANAH d'azu, shin ta fitta zuwa garesa ne, NUWAIRA tace "aa gaskiya ba inda taje, dan ina tare da ita, yace "qila bakwan ya gaji ne ya tafi, dan Allah ki sakamin ido akanta sosai, tace "Insha Allah Ya AHMAD baka da matsala, yace "Yauwa my sister...

Anan ko momy kallan HEESHAM d'in tayi da mamakin dariyar tasa tace, "HEESHAM me kake yima dariya ne.
Nan cikin sauri kwakwalwarsa ta shirya mai abin dazaice mata, yace, "hmm kedai momy bari, wani labari natuna yanzu, wanda na karanta a WhatsApp, labarin abin dariya ne, shine dazaran na tuna nake jin dariya ta kamani....
Tace "Aiko dai, amma duk da haka yau na gane kana cikin farin ciki sosai, tunda ka dawo kazo ka gaisheni nasan akwai abin da yake maka dad'i, dan fara'arka ce ta nuna min hakan..
Yace "hmm kedai bari momy, yauwa na tambayeki.. Tace "ina jinka HEESHAM yace "Kina san NUWAIRA ta zama sirikarki, Momy tayi murmushi da cewa, "Sosai ma, ai banda Allah yayi MEENATU matar Yayan ka AHMAD ce, da NUWAIRAN zan Aura masa, kai kuma na baka HAIRANAH..
Sai yayi murmushi zaiyi magana saiga Sadeeq da matarsa Khadija sunzo gaida momyn, nan suka shigo d'akin da sallama, Momy ta amsa fuskarta cike da farin ciki, bayan sun zauna Sadeeq ya gaida momyn Khadijan ma haka, amma ita a irin kunyacen nan tagaida momyn.. HEESHAM ya kalli Khadijan da zuwa kusa da ita cikin shammatarta yayeye mata gyalan data rufe kuskarta kamar wata amarya yana cewa, "bud'e mana fuskarki malama, kaji wani gwalma da munafunci🤔 Yau kuma momyn ce abar jin kunyarki dan kin d'auke mata d'a ko..
Kunya ta kama Khadija, dan tana d'aya daga cikin waƴanda HEESHAM ya raina, duk da ta bashi shekara d'aya amma sam baya wani girmamata, dama ita dashi abokan fad'a ne, kullum idan tazo gidan kwana sai sunyi, amma da suka fara Soyayya ita da Sadeeq saita dena zuwa gidan, wai ita a dole tana jin kunyar Momy..

Murmushi momy tayi tace, "Ina ruwanka ne HEESHAM, bana san fitina fah, kabarmin y'ata tahuta, wa yace maka akwai kunya a tsakaninmu, zata sakene idan kabarta a hankali..
Cikin murmushi yace "ai abun ne yaban mamaki momy. Yarinyar da nake share mata majina wai yau itace take nuna tagirma harda wani rufema sirika fuska alamar kunya.. Khadija ta kasa hakuri tace, "wa kake sharema majina, kai yaran nan baka da kunya ko..
dama maganar yake so tayi, dan haka saiya sakar mata murmushi yace "Oh idan da ranka zaka sha kallo, yanzu fa ke da gaske kin zama Auntyna, anya ko zan iya baki wannan girman..

Momy tace "Dole kuwa ka bata, dama duk wanda yaqi sharar masallaci ai dole yayi ta kasuwa.
Saiya tashi yana cema momyn "zancen ki haka yake momy, ba yanda zanyi dole na bata.. Ya faɗi hakan da ficcewa daga d'akin yana sakarma Sadeeq Yayan nasa murmushi, wanda yaketama hirar tasu dariya


Nan Khadija ta qara gaida momyn ta ajiye mata sabulai da turare kana tace bara taje taga su Ramlat, Momy tace mata toh..

Aiko tana zuwa d'akin nasu Hannatu ta rungumeta, tana cewa "Iye iye gaye, Allah yasa kina d'auke da cikinmu, Wannan kyau haka, Khadija tace "Kai sister ina wani kyau anan.. Ramlat tace "Hmm umm zagi dai kanki ki huta, Khadijan tace "Allah Aunty Ramlat..
Nan ta qarasa shiga ciki, tagaida NUWAIRA da HAIRANAH, tana cigaba da cewa, "Gaskiya nayi fishi daku dukkanku, wai ace tunda kuka kaini baku qara waiwayata ba, fisabidillahi kunkyauta kenan
Nan suka hau bata hakuri sanda ta hakura kana suka b'arke da hira.. NUWAIRA ce kad'ai bata biyema hirar tasu, kasancewar tunaninta ba akansu yake ba, yana can wajen HEESHAM tana jiran taga ya kirata....

Har su Khadija suka tafi bai kirata ba, sanda ta kwanta da niyar bacci kawai sai taji kiransa... Tana d'auka yace mata, "Gaskiya my Auntii ya kamata ki dinga kula da cikina, dan nayau yafi na jiya dad'i, dan Allah zaki qara dafamin wani abun gobe..
Cikin shagwaɓa tace mai, "kawai nazama me kulan maka da cikin naka HEE-SHAM, Yace "Allah my Auntii, tace "Toh ya zanyi da ZUCHIYA TAH.
Yace "kisha mata ja da Yalo kawai..
Tace "konasha bazai hanani kyautata maka ba..
Yace "Na qara gaya miki, tace "Mefa, yace "murki tana da dad'i, tace "haka taka ma jinta nake tamkar zuma. Yace "Godiya nake, dan Allah ki kulamin da kanki sosai dan bani san wani abu yasameki nayi missing d'in abincinki gobe kafin fittata...
Tace "insha Allah zan kulan maka da kaina fiye da tunaninka, kaima ka kulamin da kanka sosai, dan idan wani ya sameka akwai matsala, yace "Matsalar miye my Auntii, shuru tayi cikin rashin sanin abin da dazatace mai, ganin hakan yasa shi cigaba da cewa, Na takura miki ko, tace "ko d'aya, Kawai dai... Saita qara yin shuru, Yace "ok bye, tace "bye bye..
Sai suka ajiye waya atare, shi yana murmushi dajan bargwansa ita kuma jikinta mutuwa yayi...


Washe gari lahadi, tun qarfe goma MEENATU da AHMAD suka gama shirinsu, Ramlat da NUWAIRA ne kawai suke shirin rakasu gidan nasu, sai kuma mamansu NUWAIRAN da Khadija matar Sadeeq dan tace zatazo aje da ita, amma ita bata qaraso ba da alama ta tsaya ji da mijinta ne kafin tazo. Amma Hannatu da HAIRANAH sam basu da niyar yi musu rakiyan, dan itama Hannatu bata shiri da MEENATUN sam dama, nunawa ne dai batayi, amma momy tasani .
HEESHAM ya kalli HAIRANAH da Hannatun waƴanda su suka keb'anta kansu suka dawo falo suke kallo, yace dasu, "Ku baza'aje daku bane, Hannatu tace "bana jin daɗi ne, amma zanje daga baya..
HAIRANAH ko ko magana batayi ba, dai dai nan momy ta fitto daga shashinta tace da Hannatu "baku shirya bane ku, Hannatu tayi mata shiru, momy galla mata harara, tace maza kije ki shirya, nan Hannatun tabar falan da sauri, dan taga AHMAD a bakin ƙofar falan nasu da alama yanzu yazo wajen ya tsaya, dan haka bazata iya yima momyn musu a gabansa ba, dan kad'an da aikinsa yaci qaniyarta yanzu..
Sai momyn ta dubi HAIRANAH tace " menene yake damunki ne HAIRANAH, tun safe yau na lura dake ranki ab'ace yake, HAIRANAH ta turo baki gaba tace, "nifa kawai momy bazani bane, "Toh dan bazaki ba saikita b'acin rai, haba mana y'ar Autar mamanta, kije shirya aje dake, abin da ba zama zakuyi ba..
HAIRANAH ta qara turo baki gaba tace "Bafa shiri nake da MEENATUN ba momy, kullum harara ce tsakanina da ita, kuma rannan ma cemin tayi wai nadena shiga huruminta, gani take kamar san mijinta nake, hakan yasa nake hango tsanata a kwayar idanta, kawai momy kirabu dani dan kar naje fad'a ya kaure tsakaninmu, dan wallahi momy bana santa haka kawai naji bata min ba, d'azuma naje wuccewa ta shashin mijin nata kawai danta lura da nice zan wucce ta wani sheqe da dariya, kuma shima YA AHMAD d'in ya biye mata, ina jin dariyarsa Wallahi.. Takai ƙarshen zancen da rushewa da kuka...😳
Momy tasaki salati tace, "wayafi baki haushi tsakaninsu su biyun alokacin,... Zatayi magana HEESHAM yayi saurin cewa, "MEENATUN ce tafi bata haushi mana momy, Momy ta juya ta gallama HEESHAM d'in harara sai yayi shuru kawai yana Addu'ar Allah yasa tace kamar yanda ya Faɗi yanzu, amma Saidai kash ko ajiye numfashi bayyi ba tace dashi, "Ni ba MEENATUN bace taban haushi YA AHMAD d'inne yafi ban haushi momy, wallahi har yanzu haushinsa nake ji, dama kullum saina dinga ganinsa yana mata murmushi, ta qara kai qarshen zancen da qara sakin wani kukan..


Dake dama HEESHAM a tsaye yake yana jin hakan ya zauna a hannun kujera, Dan ta kwafsa, baiso tafadi hakan ba, sam baya so ko kad'an ta nuna wani alamu nasan AHMAD d'in, duk da yasan tana sanshi batun yau ba, kawai sanine batayi ba har yanzu

Momy ko qara sakin wani salatin tayi, ta kama hab'a tace "Ana wata Ga wata, oh ni Aishatu, yanzu ya za'ayi kenan..
Shuru HAIRANAH tayi mata, shiko HEESHAM yagane me momyn take nufi, amma sai yayi kamar bai gane ba yace da momyn, "kawai yanda za'ayi shine kibarta kawai kar taje, tunda kinji abin da tace, Momy tace "ai batun zuwa babu HEESHAM, hmm Toh Allah ya shige mana gaba, HEESHAM yace "Ameen..

Kiyi Shuru toh, tunda baki san zuwa kinji, bame miki dole kinji y'ata ta kaina.. Momyn ta faɗi hakan da kallan AHMAD d'in.. Wanda yayi shuru dajin dad'in qara fahimtar HAIRANAN da yayi sosai, nan yaji sanyi aransa.. _kina da kishi sosai my Baby_ ya Faɗi hakan aransa..
Momyn tace dashi "kazo d'aki ka sameni, d'aga mata kai kawai yayi, dan baya san HAIRANAN tasan da tsayuqarsa agun...
Aiko har yazo ya wucce bata sani ba, tana nan tana aikin kuka, HEESHAM na bata baki yace, sanda HEESHAM d'in ya tabbatar AHMAD d'in yayi shashin
DOWNLOAD
DOWNLOAD

Please Login or Register in order to submit comment