Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register




HEESHAM ko kamar kullum idansa fara gauraya yayi dana masoyiyar tasa, kuma yaji daɗin break din data masa.. Amma yau bata bisa zuwa rakiya ba, momy na lura dasu, murmushi kawai tayi dama tasan koma yayane dole yanzu NUWAIRAN zata dinga jin kunyarta..

Aiko sanda ya magantu, bayan ta koma room nasu taga miss call nasa tana kiransa ya d'auka yace, "shine yau ba rakiya bare na yaba wankan da akamin ko, tace "Afuwa MENI, ayanzu bazan iya hakan ba, tunda momy da Dady suka san da zaman Soyayyarmu, dan Allah kadda kamin futuna wajen cemin kai baka yarda ba, kaga wata d'aya ne ya rage maka kayi yanda kaga dama dani, sannan awannan lokacin babu idan kowa akaina bare naqi baka kulawar data dace, dan Allah ka yarda da abin dana ce..
Yace "bazance bazan yardan ba, amma Saidai duk kwalliyar da kikayi ki d'aukar min ita na gani, dan ganin hotunanki suna qara shagaltar da zuciyata wajen sanki da ƙaunarki, tace "Oho dama kaima ka fara sona tuntuni ko, yace "Yes ai tun ranar farko kika kwanta min arai, tace "Toh meyasa kabar zuciyata cikin damuwa, yace "Banyi tunanin Soyayyata ce tasaki zama haka a lokacin ba, tace "Toh ayanzu saimu godema Allah daya had'amu cikin ƙauna, yace "Allah abin godiya, zan shiga aiki yanzu my love pls ina buƙatar addu'arki, tace "Toh mijina Allah ya baka sa'a.. Yace "Na gode my Auntii.. Nan suka ajiye waya cikin farin ciki da ƙaunar juna..




Can wajen qarfe biyu momy taje kasuwa ta had'uma yaran nata ingantattun magungunan na mata masu kyau da saka lafiya.. Haka tadafa na dafawa dana tsarki harda na turara jiki, HAIRANAH Ramlat NUWAIRA Hannatu sam basu ja ba, haka suka nad'e suka karb'a suka dinga amfani da kayansu, dansu ba yara bane, sunsan me maganin zai musu agun mazajen nasu.. Saidai momyn tafi zagewa akan HAIRANAH da Ramlat alokacin dan tasan sune suke ahannu ayanzu..
Aiko kwana huɗu da fara amfaninsu da magungunan suka san yanzu suke a mata, dan jin wani yanayi daya fara kawo musu farmaki, musamman Ramlat da HAIRANAH, har wani danshi suke bari idan suka tashi a waje..
Dama tunda suka fara shan magungunan momy tace to yanzu babu su babu tsayawa da samarikan nasu, Ramlat tadena amsa kiran SABEER idan yazo da niyar yin zance, Saidai hira a waya, haka Hannatu ma sundena magana da AMAAR ido da ido.. Dama HAIRANAH bata saba da hakan tsakaninta da AHMAD ba, dan ita ranar dataji muryar MEENATUN bata qara amsa kiransa ba, kuma ko yazo gidan bata yarda su had'u..
NUWAIRA ce dai duk inda ta shiga sai HEESHAM ya nemota a gidan, Saidai in kulle kanta zatayi a room d'insu... Momy har kiransa tayi damai magana kan yadena damun NUWAIRA ayanzu ya bari idan aka kai mai ita gidansa ya dameta acan.. Toh yace ma momyn, saiya kasance idan yana san Ganin NUWAIRAN saiya kirata yata had'ata da Allah taje wajen shaƙatawan gidan ya ganta kawai yaji dad'i, wannan yasa NUWAIRAN ganewa da gaske yana santa sosai, abin har mamaki ya bata, aganinta koda zai sota Saidai kad'an haka, amma yanzu sai take ganin kamar san da yake mata yafi wanda take mai...



Yau Jumma'atu babbar rana, kuma ayau d'in aka d'aura Auran AHMAD da HAIRANAH, sai Ramlat da SABEER..

HEESHAM ne ya fara dawowa gidan momy, dangi sunyi murna sosai dan kana ganin kowa zaka gane yana cikin farin cikin wannan Aure, haka HEESHAM ya dinga ratsa mutane suna masu tsokanarsa da Ango, yace musu baidai zama ba amma zai zama...
Ahaka yazo shashin YA AHMAD nada inda su HAIRANAH suke.. Yaga sai musu kitso ake da lalle ya kalli yanda na Ramlat yayi kyau, ya durƙusa a gabanta yace, "shikenan yau zaki bar mana gidanmu kije can naki gidan halinki ya zaunar dake lafiya da mijinki ko, tace "Eh mana, kaga shikenan yanzu babu kai babu ganina bare ka tsokaneni muyi fad'a, yace "Yanzun ma fad'an ƙarshe zamuyi, dan taka wannan lallan naki zanyi..
Ramlat tayi saurin kallan lallan nata, yanzu aka gama mata shi, ko alamar bushewa baiyi ba, saita maida kallanta gana NUWAIRA wanda ita nata kad'an ne haka, sai tace, "taka mana, bagana NUWAIRA can ba, babu abun dazai hanani goge nata, kuma zan gogesa ne da gayya yanda babu me ganin kyansa..
HEESHAM ya maida kallansa kan NUWAIRA ta sakar mai murmushi da cewa, "Taka kawai my dear, rabuwar taku bazatayi dad'i ba idan har bataje gidanta da tab'onka ba, babu komai danta b'ata nawa, nasan kan zuwan namu kwanakin ya goge... HAIRANAH ta fashe da dariya tace "dama ke muguwa ce...
HEESHAM ya sakar mata murmushi yace "No nutsuwata, nifa kika yima kwalliyar, idan ta b'ata min bazanji dad'i ba, amma koma yaya ne sai tatafi da tabo na..
Ramlat tayi dariya sosai tace, ai da'ace nasan da zaman Soyayyarku tun da farko da tuni na sauke maka wannan futunar taka, dan duk abin da zaka mana nida Hannatu akan NUWAIRA zamu dinga ramawa, tashi yayi da d'aga kafarsa alamar zai taka lallan ya kalli NUWAIRA yace "Auntii bara kawai nabi umarninki na taka, kinga kan tatashi saiki gudu abinki, NUWAIRA ta kalle Ramlat wacce tsoro ya mamayeta ayanzu, dan tasan kad'an da aikinsa ya b'ata mata komai.. Saita sakar mai murmushi, tace "No sweetheart, barta kawai, yace "Gwara dai na take, tace "Yi hakuri, dan kar tayi kuka..
Saiya sauke qafar da kallan Ramlat d'in yace kinci darajar nutsuwata da yau an kaiki gidanki da b'ataccen lalle🤨..

Shuru tamai har yabar wajen, dan tasan tana yin magana zai take wai ance sanin HALIN yafi sanin kama...
Dama ita Hannatu bata ce qala ba, dan tana yin magana game din zai dawo kanta...



Sukan basu samu damar yin wani bidi'a ba, dan walima Kawai suka gabatar, itama ayau d'in ne wajen qarfe huɗu na yamma acan gidan Baba Alhaji cikin harabar gidansa, kuma kowa yaji daɗin hakan sosai, dan malamai da dama ne suka ziyarki walimar, sun fad'akar abin sai wanda ya gani....

Dareko nayi aka d'auki Ramlat aka kaita gidan SABEER, wani gida acan jerin unguwannan manya, wanda tun farkwan Soyayyar SABEER d'in da ita yaje ya sai fili awajen aka fara aikinsa cikin sauri.. Abunka da me tattali, hakan yasa ya tattaro kud'ad'ansa Babansu ya qara temaka masa sai ya kasance babu abun dabaisa agidan ba.. Haka dangi Kowa ya dawo da santin gidan..

Sai asannan aka d'auki HAIRANAH akayi nata gidan da ita, wato gidan AHMAD, shashinta ya gigita dangi, dan Mamansu ba ƙaramin tanadi tama yaran nata biyu ba, tana musu mahaifinsu na musu, hakan yasa kowa ya dawo da santin shashin HAIRANAH, dan baqaramar dukiya aka zuba mata ba... Duk a kwana uku komai ya faru, dan Dadynsu AHMAD ne yacema mamansu HAIRANAN taje gidan AHMAD d'in taga me za'a qara a shashin HAIRANAN, kamar dai yanda akama MEENATU, babu wani abun qarawa sosai, amma dake ta musu tanadin haka taqara komai, sai shashin nata ya fitto daban dana MEENATU bama had'i...

NUWAIRA tana gidan Ramlat acan zata kwana, ita da yaran gidan Kawu jamilu, wato Haulat da Sakinat, sai Hannatu wacce take tare da HAIRANAH ita kad'ai, dan y'an gidansu MEENATU suna tare da ita a shashinta ko kallan shashin HAIRANAH basuyi ba..

Koda AHMAD ya dawo shashinsa yayi, MEENATU dai ta danne zuciyata taje ta masa sannu da dawowa, ya amsa cikin kulawa, harya nemi data kwana dashi, tace tayi tunanin da HAIRANAH zai kwana, a sannan ne ya kalleta yace, "Saurin me kike ne my love, ai ba yau zan kwana da ita ba, baki ganin yanda take tare da Hannatu, tace "Ayya, sam banyi zatan hakan ba, daban ce su HASEENAH suzo su kwana dani ba, yace "Yanzu ma ba wani abun damuwa bane, kawai kije ki musu Saida safe dan yaci ace yanzu kingane na saba kwana dake..
Murmushi tayi da cewa, "ina kamanta hakan ne, shiyasa kamin kishiya, Sannan ya kuma zakayi idan yazo ba ranar kwanana ba, Yace "kinsan dai itama ba kallanta zan tsaya yi ba, yanda nake jinki haka itama zan jita, kinga kenan ba batun ya zanyi, dan ina da yanda zanyi ta hanyoyi dadama..
MEENATU ta had'iye wani mugun b'acin rai, tace "nimafa Macece ya kamata kasan ina da kishi, bai dace ka dinga gaya min komai da kaga dama akan kishiyata ba, yace "Nasani, kawai ina so hakan ya zamo shine na qarshe akan kadda ki qara sakomin zancen HAIRANAH idan ina tare dake.. Komai ya wucce ayanzu, zaki iya zuwa kiyi musu Saida safe dan ina buqatar hutawa pls... Bata mai magana ba ta ficce daga room d'in nasa.. Shidai ya mata hakan ne dan yasamu nutsuwar zuciyarta, dan yasan mafiya yawan maza kuskuran farko da suke farawa wajen qara jefa kishi atsakanin matansu shine yarda dayin zancen d'aya daga cikin matan nasu da d'aya... Hakan yana kawo qarya, da kuma tsoro... Da zaran ansamu hakan shikenan me gida bashi da y'anci, yana zuwa wajen d'aya idan d'ayar ta d'auki fushi dashi shikenan sai yaje yahau gaya mata me yaje yi agun waccar, toh kaga tsoro ya shigo ciki kenan, idan kuma d'ayar ta ganosa, sai yahau yimata kame kame, kaga anan qarya ta shigo ciki kenan....


Tana zuwa falanta HASEENAH tace "Ya naga ranki kamar a b'ace, tace "hmm wai naje na kwana dashi.. Tace "Na d'auka da matsiyaciyar zai kwana ai, tace "aa, wai tana da baqi, tace "Da ace niceke wallahi bazan tayasa ba, tace "Ke baki san waye AHMAD ba, hmm na rantse da Allah sai HAIRANAH tayi nadamar shiga rayuwa da tayi..
HASEENAH tatab'e baki tace "Hmm, aini kozan kumu Wallahi saina baqanta rayuwar NUWAIRA, saina mata abin da tunda take a duniya bata tab'a jin labarinsa ba, har yanzu binkice nake akan baqanta ran mutum ina fatan nasamu yanda nake so.
Yanzu jeki, dan naki me sauƙi ne, kina fara aiki akan taki zata bar miki gidanki da qafarta.
Tashi MEENATUN tayi da shigawa bed nata tad'auko kayan bacci tama su HASEENAN sai da safe da zuwa wajen AHMAD d'in...

HAIRANAH ko dama tasan qila bazaibi ta kanta ba, dole zai gane ba ita kad'ai bace tana tare da Hannatu..



Washe gari momy tayi aiki da hankali, ta had'a ma su HAIRANAH breakfast danshi AHMAD yayi tunanin MEENATU ce zata had'a musu, baisan ko a mafarki batayi tunanin hakan ba, sai Allah ma ya kyauta momy tayi musu..

Mamansu NUWAIRA kuma tayima su Ramlat, dan NUWAIRA ta kira Momyn tace kartayi breakfast dasu mama taturo musu, toh momyn tace kawai..
Lokacin HEESHAM nayin breakfast d'in, yace "Momy sai gidan yayi babu dad'i da babu kowa acikinsu, Dady yace yanzu nima nake san yin magana, Momy tayi murmushi tace "Haka duk zaku watse HEESHAM ku barni ni kad'ai, yace "anya ni zan iya barinki kuwa momy, tace "Ga alamu sun nuna, tunda yanzu saura kad'an Dadyku yagama gina maka naka gidan, HEESHAM yayi murmushi, dan gaskiya momy ta fad'a jiya shi da abokinsa Jabeer sukaje gidan nasa ganin aikin da ma'aikatan gidan suke, saura kad'an a gama komai, gaskiya gidan ya had'u sosai, aljannar duniya kenan, anan HEESHAM ya qara tabbatarwa ba qaramin so iyayen nasa suke masa ba, dan nasa tsarin gidan ba irin na yayunsa bane, komai nasa daban,... Hakan yasa ya kalli Dadyn nasu yanzu yace "Nagode Dady, wallahi ina Sanku sosai iyayena, na muku alƙawarin babu ni babu tsab'a muku akan komai.
Dadyn yayi masa murmushi yace dena gode min, dan biyana komai zakayi, dan naji AHMAD yana gayama momynku wai albashinka na wata biyu baka karb'a ba, wai ya lura baka buqatar kud'in ne.. HEESHAM yayi murmushi da cewa, "Ba haka bane Dady, nayima kaina al'qawarin zanqi karb'ar albashina na wata biyar dan ina san yima YA AHMAD wata bazata, zan siya masa wani abu me mahimmanci wanda ake buqata a cikin asibitinsa, akwai wata naqura wacce take bada sakamako akan wata matsala da take samun wasu mutane ta d'aukewar tunanin kwakwalwa, wannan matsalar tafi d'aukewar tunanin mutum hatsari, toh wannan naqura tana temakawa wajan gano awane hali kwakwalwar wannan mutanan take cikin sauƙi, wannan dalilin yasa nake san siya mai ita na bashi ita a matsayin bazata, dan naga sam shi hankalinsa baije wajen ba.. Dady yayi murmushi yace "Nagane nakurar, kuma da gaske AHMAD d'in zaiji dadinta, amma albashinka na wata biyar bazai siya maka ita ba.. Dan ana Siyar da ita miliyan arba'in ne a kud'inmu nanan gida Nigeria.. HEESHAM yace, "tabbas kud'in albashin nawa baza su kai haka ba Dady, amma zasu kai wata ranah, kawai qara lokaci zanyi akan lokacin da nayi niya, dan gaskiya ina jin dad'in ƙaunata da nake hangowa akan fuskar kowa anan gidan, musamman shi ya AHMAD d'in, Dady yace "kana da gaskiya HEESHAM, amma shawarar dazan baka itace ka dinga raba albashin naka biyu, saboda kaga yanzu nauyi zai hau kanka, zaka fara rayuwa da mata, ka raba biyu wancan kana ajiyewa wancan kuma kana biyan buqatunka dashi, HEESHAM yace "Toh dady hakan za'ayi, fatana ka tayani da Addu'a Allah yasa na cika burina, dan ina san asibitin ya zama komai akwai a cikinsa adena zuwa waje yima mutananmu aiki dan rashin samun wadataccen kayan aiki, kamar yanda naga YA AHMAD d'in yana da ra'ayi irin nawa... Momy tace "Hakan yana dakyau sosai HEESHAM, Allah ya albarkanci rayuwarku kawai...





Saida abokan SABEER sukazo suka tafi Sannan NUWAIRA tadawo gida.. Lokacin ko yayi daidai da dawowar Hannatu daga gidan HAIRANAH, nan suka tafa suka fara bama juna labari, Hannatu tace abokan YA AHMAD sun had'u kinsan nawa suka bani dan Siyan bakin Aunty HAIRANAH... NUWAIRA tace "Ikwan Allah har kin fara kiranata da Aunty, tace "Toh ya zanyi, ai dole na bata girman, kedai kinsan nawa suka bani, tace "Pls nawa suka baki, tace "dubu Dari biyar, wannan abu ya baqanta ran MEENATU, nasan hakan baya rasa nasaba da yanda ta tuna nata ko asi basu bata ba, ganin Ya AHMAD d'in a kwance.. Kufa, nawa abokan ya SABEER suka baku, NUWAIRA tace "Dubu d'ari da hamsin, kuma kinga mu uku ne, hakan yasa muka raba daidai..
Tace "Ni ce na cab'a, amma zan bama HAIRANAH wani abun... Kema ban account Num naki na tura miki naki kasan, NUWAIRA zatayi magana kiran wayar HEESHAM ya shigo wayarta, tace "Bari naji nutsuwata tukunna, Hannatu tayi murmushi tace "kidaiyi a hankali, dan ba irinsu HEESHAM bane ake nuna musu so haka, dan wata ranah ya tashi nanaki a qasa saikin rasa inda zakisa kanki, NUWAIRA ta galla mata harara da ficcewa daga room d'in....


Ramlat dai ita da mijinta SABEER sun samu cikakkiyar fahimtar juna yau.. Dan SABEER d'in kusan haukace mata yasoyi...




Oga AHMAD ko, bayan watsewar kowa daya kulle musu Gidan, shashin uwar gida yayi MEENATU yayi mata sai da safe, a daqile ta amsa masa.. Bai kulata ba, dan yasan me yake damunta, wanka yayi a part nasa yayi shashin HAIRANAH, yako zameta cikin kamshi me tsayawa arai.. Jikinta d'auke yake da hijabi, da alama ta makara wajen yin sallar Isha'i, tana ganinsa gabanta ya fad'i, koya zasu Kaya yau oho, Ta fad'i a ranta..

Ya kalleta sama da qasa, yaga ba abun da ake gani a jikinta dan hijabin tunda saman yake har qasanta, yace "Sallah zakiyi ne, tace "Yanzu na idar, yace "Yayi, amma kafin ki zauna mu gabatar da sallar godiya ga Allah mana, tace "toh..
Nan suka gabatar da sallar, ya kama kanta yayi mata Addu'a kana ya mata tambayoyi akan addininta, yanda take wankan tsarki da sauransu, ta bashi amsa cikin kulawa, saiya tura mata kaza da madarar da abokansa suka siya musu ita da MEENATU, wacce sun bama MEENATUN tata tun tuni..
HAIRANAH ta kallesa kad'an tace " bana jin yunwa, aika mata da wani shegen kallo yayi da cewa "Ina san kici ko kad'an ne...
Nan tayi qasa da kanta dan jin wani yanayi daya fara shigarta..





*Ba abin dayafi danqama Allah komai, ba rayuwar datafi hakuri da dangana daɗi, kyautatama Allah zato kaga komai yazo maka da sauƙi, na barma Allah ikwansa akan jarabtar daya afka mana, ayanzu mun samu nutsuwar zuciya irin mutane mumunai, Nagode ma dukkan fans nawa da bani kulawarku gareni*

Sam bata da niyar ci, ganin hakan yasa ya kusanta kansa gareta sosai ya d'ago da fuskarta suna kallan juna ido cikin ido yace, "Ina san matata ta kasance me tsafta, ina san mace me addini, ina san mace me san y'an uwana, ina san mace me ladabi da biyayya, ina san mace wacce tasan abin daya dace, ina san mace wacce take da wayewa, wacce zata d'auki abin danake so da matuƙar mahimmanci arayuwarta. Ina san mace me gaskiya, sam bani san mace me qarya.
Sannan ina san luv HAIRANAH, ina san Soyayya sosai, tun rasa masoyiyata da nayi abaya ban kuma jin wacce ta tsaya min arai irinki ba, bance miki bani san MEENATU ba, ina santa sosai, saidai ina san ki kula dani sosai, hakan shi zai saki gane wane irin so nake miki..

Cikin sanyin murya tace, "Idan duk waƴannan abubuwan daka lissafamin sune zasusa na mallaki zuciyarka nayi maka alƙawarin zan mallaki zuciyarka da gangar jikinka, dan babu wani abu me wahala aciki, zansa Allah agabana ya shige min gaba akan dukkan al'amurana, nayi imani da yardarsa bazan tab'a baka kunya a Soyayyarka ba, badai kace kana sona ba.

Lumshe idansa yayi da bud'ewa a hankali yace, ina sanki sosai babyna, tace "Gud, bawai bana jin yunwar bane, Hannuna ne bazasu juri kai da kawo wajen ciyar da bakina ba, saboda mugun gajiyar dake tare da dukkan gab'ob'ina, amma idan zaka iya ciyar dani babu damuwa dan zan baka mamaki wajen ci da yawa..

Murmushi yayi da cewa, gyara kawai na baki baby, dama ai ciyar dake aikina ne, ya fad'i hakan da ware hannuwansa alamar tashiga jikinsa, ba wani ja, ta shige jikinsa sosai shiko ya dinga ciyar da ita kazar da madarar, sanda ta k'oshi ya barta, asannan ne tace "tunda na k'oshi nasamu qarfin jikina, dan haka kaima zan iya ciyar dakai My blood, yace "Zanji daɗin hakan ko Babyna.. Nan HAIRANAH tacire duk wani jin nauyinsa tadinga basa har sanda yace mata ya isa.. Daga nan ya tayata cire hijabin jikinta, kayan bacci ne ajikinta, aganinsa sunyi mata kyau sosai, dan sun bayyanar da komai na halittatta, anan fa komai ya canja...

Wannan dare ya gigita dukkansu su biyun, dan AHMAD ya nuna mata zallar Soyayya, ita kam kasa bashi haɗin kai tayi yanda ya dace, kasancewarta saban shiga, wannan yasa tasha wahala sosai agunsa, Saidai tayi saurin gane ba abin da mijin nata baya so ajikinta, dan ko ina nuna ƙaunarsa yake garesa..


Washe gari kallo d'aya zaka mata kasan idanta baya cikin nafiya, dan yayi ja sosai, kana dai gani kasan tasha kuka, AHMAD na gabanta yana lallashinta kan tasha tie, dan shi yasan me yayi mata, Allah yasa wannan tsohuwar da Momy taturo ma MEENATU lokacin amarcinta tana nan, dan ita AHMAD d'in ya kira washe gari ta ƙara bama HAIRANAN kulawar data dace, bayan ya tabbatar bai mata illa da yawa ba, dan yana cikin hankalinsa, tunda ya gane ta tattala masa kanta, hakan yasa tausayinta ya hanasa yanda yaso mata da gayya, aiko HAIRANAN taji daɗin kulawar da tsohuwar ta bata taji dadin jikin nata sosai.. Hakan yasa tadai karb'i tie d'in dake hannun nasa tana auna mai hararar ƙauna, sai yayi murmushi da sakar mata kiss yace "Ina sanki Babyna dan Allah ki zauna dani lafiya, tace "Ina sanka YA AHMAD, zan kuma zauna dakai lafiya, yace, "Gud, yanzu ina ne yake miki ciwo, tace "Ai duk jikin ka b'ata shi da rashin lafiya, da sauri ya waro ido yace "kice yau bani ba fitta in zauna kawai jinyar Babyna, tace "Zanzo hakan sosai Yayana, amma bana san ka rasa ladanka nayau a office d'inka, yace "kullum ina samu Babyna, yau dai ranah d'aya na haƙura dashi, jin hakan yasa ta kwanto jikinsa zata mai magana sukaji ana kunkwasa k'ofar falan nata.. Saiya kalleta yace "kinga matsalar kwana a d'akin mace ko, da anawa muka kwana babu wanda zaizo yana kunkwasa mana k'ofa, dan haka bazan qara kwana a d'akinki ba. Tace "Babu komai ni zan kwana a naka d'akin, tafad'i hakan da tashi ahankali ta ficce ya bita da kallo, wallahi yarinyar tayi mai bazata, dan tayi mai daidai da tsarin Matar da yake so.

Direban momy ne ya kawo musu breakfast, dan Momy takira MEENATU a waya kan ta had'a musu breakfast d'in tace mata wai bata jin daɗi ne, yanzu haka a kwance take, HAIRANAH ta karb'i komai tamai godiya da cewa ya gayama momy ta huta zata iya yin komai basai tabama kanta wahala ba, yace mata toh zai gaya mata..

AHMAD baiji daɗin qin had'a musu da MEENATUN batayi ba, amma koda yaje gareta dan duba lafiyarta bai nuna mata komai ba, haka ya koma part d'in HAIRANAH da niyar Sam bashi ba fitta office ayau...




HEESHAM ko daya tashi bayan ya shirya kansa yayi breakfast baiga mutuniyar tasa ba, daga shi sai momy ne akan dining d'in, Yau ko Dadynsu ma baya kai, ya kalli momyn a d'an kunyace yace "Momy waye ya had'a wannan break d'in, tace "NUWAIRA ce, yace "Amma bataci ba ko, tace "eh da alama tana wani abun ne a room nasu, kaga daga ita har Hannatu shiru, yana jin haka sai yayi saurin tashi yana cewa, "Wayyo na manta ta gaya min cewa bata jin daɗi jiya, bara na dubata bye momy, I luv u... Ya kai ƙarshen zancen da saurin d'aukar jakarsa da wayarsa yabar wajen, momy ta bishi da kallo, ta sa'ni sarai ƙarya yayi mata dan yana san ganin NUWAIRAN ne, ita fa har yanzu bata dena mamakinsu ba, Amma taji daɗin hakan sosai aranta, musamman data gane NUWAIRAN zata bama HEESHAM din kulawar data dace... Tayi imani har a zuciyarta HEESHAM bazai tab'a cutar da NUWAIRAN ba, dan bashi da wani mummunan hali...

Aiko ya samesu zube akan kafet, wasu kaya ne zube a gabansu na sawa da alama tela za'a kaiwa, nanko ya durk'usawa awajen yace "Wallahi my Aunty yanzu baki ji dani, A d'an shagwaɓe tace "Toh yanzu me nayi kuma, yace "Nuna Kulawar taki akaina tayi kasa da yawa, tace "Momy ce tasa mana gaba, ni dama ace wannan Jumma'ar za'a d'aura Auran namu, wallahi nazak'u naga mun shagala da kallan juna akowane lokaci muna masu hirar ƙauna.. Yace "Allah nutsuwata, cikin tabbatarwa kuma still a shagwaɓen tace "Allah da gaske😀, ta faɗi tana me juya kanta..


Hannatu tasaki baki tana kallansu, ita dai a ganewa irin tata ayanzu ta gane NUWAIRA bata da wani wayo sosai, dama HAIRANAH tasha fad'a amma bata tab'a gani ba sai yau, tayi imani HEESHAM zai fita wayo sosai, ita a zahiri tana ganin shagwaɓar HEESHAM, dan shima ba baya ba wajen shagwaɓa, amma ayanzu sai taga NUWAIRA tafishi, dole su dace a Soyayya, dan da ace tana da wayo sosai gaskiya zamansu bazaiyi dad'i da HEESHAM ba....

HEESHAM ya sakar mata wani shegen murmushi yace "Wallahi Auntii ina buƙatarki nan kusa, dan Soyayyarki qara yawo take a cikin jinina, ganinki kawai yana shafe quncin zuciyata, idan kuma magana ta shiga tsakanina dake jinta nake tana watsuwa ako'ina na halittata, dan Allah kizo muje wajen Baba Alhaji musashi gaba da magiya ya d'aura mana Aure a yau... Ya ƙarshen zancen da zuba mata ido yana san yaga ya zata karb'i zancen nasa.
Aiko cike da farin ciki tace "da gaske yanzu idan mukaje zai yarda ya d'aura mana Auran😀...
HEESHAM yayi shuru yana tunani, gaskiya yauma ya qara tabbatarwa bata da wayo sosai, wani daɗi ne ya qara kamasa, gaskiya dole ya qara godema Allah, dan ya lura a zamantakewar Auran nasu da zasuyi ko zai sata yimai abu tace bazatayi ba zai iya sata tamai cikin wayo dadabara.. Shidai ayanzu ya gaya mata hakan ne dan yaji me zatace, aiko yaji abin da yake sanji, amma koda wasa bazaije Ga baba Alhaji da sunan ya d'aura musu Aure yau ba, dan idan yayi kuskuran zuwa zai iya lallab'asa ya barma Saminu ita, dan yafifa kowa sanin halinsa, dan haka ba dashi bah.
Da murmushi akan fuskarsa yace "Mezai hana, musamman idan ke kikace ad'aura mana😀..
Takaicin HEESHAM kamar ya kashe Hannatu, tare

Please Login or Register in order to submit comment