Join Our WhatsApp Group

Idan ku ka ga kun taba wani wuri ya fitar daku a shafinmu, sai ku danna back kuyo baya, ku sani yanzu muna amfani da tallan Popunder a shafin, so karatu zai muku dan wahala, amma ta hakanne kadai zamu iya cigaba da rike shafinnan. idan har bakwa son talla sai kuje ku yi subscription na shafinnan akan karamin kudi ku runga downloading kawai. SUBSCRIBE


DOWNLOAD

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register
DOWNLOAD

d'in tabita da kallo.. Nan take kuma duk Sai tunaninsu ya canja.🤔..
Dama momy bata wajen bare tabasu haske..



Washe gari ranar Hutu ga y'an bok'o, da misalin k'arfe goma sha d'aya duk y'an gidan suka gama shirinsu na zuwa gidan Baba Alhajin, da wayo da dabara sanda HEESHAM ya d'auke hankalin Ramlat da Hannatu Momy ya d'auke NUWAIRA suka rigasu yin tafiya, koda momy ta shafa taga ba NUWAIRAN ba bata damu ba, dan tasan ba wani tsayawa tunani tana tare da HEESHAM....

Suna tafiya acikin motar tasa ne ya kalleta da cewa, "Idanfa munje ki nuna min me ƙaunar tawa yau dan na shaidama baba Alhaji itace wacce nake so... Gaban NUWAIRA ya faɗi, tacemai Toh..
Suna isa gidan bayan sun fitto daga motar ta kallesa jiki a sanyaye tace "dama, dama hmm, dama, sai kuma tayi mai shuru da sunkuyar da kanta, yace "dama me😟.. Bata d'ago da kan natan ba tace, "kawai muje..
Yayi murmushi da wuccewa yana faÉ—i aransa idan har bata fitto ta gayamai tana sanshi ba saiya jiq'a mata taba yau...

Dake falan Baba Alhajin irin Babban nan ne, kuma yau ba'a bud'e ta wajje ba ta ciki aka bud'e dan haka falan cika yayi da y'an uwa, har farfajiyar gidan sanda tasan da zaman Wannan taro, dan itama ta cika..
Sam NUWAIRA bata yarda tayi nisa da HEESHAM ba, duk inda yasa qafa tana wajen😂.. Wai a nufinta idan aka tashi tambayarsa wacece gwanarsa idan yaga tana kusa dashi ai zaice itace, tunda AHMAD ya tabbatar mata da cewa yana santa, dan haka tana kusa dashi.. Babah Alhaji ya zuba musu ido yana wani tunani...

Su HAIRANAH ko sunayin parking AHMAD nayi, yana tafe da matarsa MEENATU.. Koda dukkan su suka fitto daga motar HAIRANAH da MEENATU harara suka gallama junansu.. MEENATUN ta gaishe da momyn kamar yanda AHMAD d'in yake gaisheta sai tayi saurin shiga cikin gidan Babah Alhajin, Ramlat da Hannatu Momy sukabi bayanta, HAIRANAH zatabisu AHMAD yayi saurin rik'e hannunta yace, "Idan Babah Alhaji yace kina sona kice kina sona, idan kikace mai baki sona ranki idan yayi dubu saiya b'aci..
Ta galla mai harara tace, "ina da wanda nake so, koda yake babu lokacin b'ata lokaci dan kafi kowa saninsa, Hashim nake so, kuma shi zan gayama Babah Alhajin ina soh..
A fusace ya jawota jikinsa yace "Kuskure nafarko da zaki farayi a rayuwarki kenan, Wallahi my Baby bazan tab'a bari ki Auri Hashim ba, sannan bayan kin gayama Babah Alhajin cewar Hashim d'in kike so, bayan na b'ata ranki, zan gayama momy & Dady cewar ke kika karyani watannin baya, kwace kanta tayi jin ƙamshin turaransa nasan yaudarar zuciyarta wajen kawai ta kwantar da kanta ga ƙirjinsa taji sanyin da yake kwad'aita mata.. Saita lumshe ido jin daɗin yanda yaje shigarta, gaskiya batajin dad'in turaran kowa kamar nasa, kana ta bud'e idan da dallamai wata hararar tace, "Kafad'a man, idan ka fad'a na shirya amsar da zan bayar wajen kare kaina, ba wanda zai gane da gangan nayi.. Ta faɗi hakan dasan shigewa cikin gidan...
Aiko hanata shigar yayi wajen qara Jan hannunta ya juyo da ita garesa yace "Kinsan Allah idan har kika amsa kina san Hashim hmmm... Bai qara mata maganar tasa ba ya sakar mata murmushi da shafar gefan fuskarta Asannan yaci gaba da cewa, zan kashesa... Cikin tsoro tace "Me😳 kisa fa kace.. Yace "Yes... Zan fara akanki, dan baku dace da juna ba, tace "Toh dakai na dace kenan, yace "aa, kawai dai temakwanki zanyi, tace "Oho, yanzu na gane, idan ka kashesa saina tona maka asiri ai ban rasa masoya a dangin ba, bayan shi akwai wasu, sanine dai bakayi ba, bazan so ka kashesa ba, amma bazan zab'esan ba, Saidai zakaga wanda zan zab'a, lumshe idansa yayi da bud'ewa ahankali, nanko taga yayi ja sosai, gabanta ya fad'i, yace, "duk wanda zaki zab'a zan kashesa my Baby, kawai ki zab'eni ki temakesu.. Tace "Wai Yaya tayaya kake tunanin zan zab'eka bayan ba sona kake ba, yace "Zan fara sanki idan kika yarda kika zab'eni, tace "A tsarina babu haka, Sannan HEESHAM ya gaya min Soyayya wata abace me matuƙar daraja, ba'a samunta cikin sauƙi haka, kuma wallahi na yarda da zancensa...
Yace "Gud.. Haka ne, Ina sanki ina MASIFAR SONKI, dan Allah ki zab'eni pls my Baby, ta kallesa duk ya wani burkice sai tace "toh Sakar min hannu na, ba musu ya sakar mata hannun.. Bata qara magana ba tayi gaba abinta.. Saiya dafe kansa gaskiya baisan yana san Yarinyar da yawa ba sai yanzu... Haka dai yabi bayanta zuciya da tunani...



Gaban NUWAIRA ba ƙaramin tsinkewa yayi ya faɗi ba da taga yawan dangin da suke dashi, kallo d'aya tayima Baba Alhaji tasan wannan taro bana wasa bane.. Tana kallo su momy suka shigo da shigowar HAIRANAH da AHMAD..
Baba Alhaji yayi gyaran murya da bismilla kana yayi ma Allah kirari da salatin Annabi kamar yanda ya saba kana ya kalli AHMAD Hashim da AMAAR HEESHAM da SABEER Saminu, sannan ya maida kallansa kan HAIRANAH da Hannatu Ramlat da NUWAIRA HASEENAH yace "masha Allah, wannan taro naku ne, anyishi ne domunku, muna fatan Allah yasa wannan had'i da zanyi yayi albarka fiye da tunanin me tunani, bari na fara daga kanka AHMAD, kazo min da batun kana san HAIRANAH zaka qara Aure a karo na biyu haka ne... AHMAD yace "haka ne.. Nan ja'ama kowa ya zuba mai ido, irin yaushe akayi Auransa da har zaice kuma zai qara, MEENATU ko gumi ne ya karyo mata nan take hankalinta ya bala'in tashi, Baba Alhaji yayi murmushi yace masha Allah.. "Ai dama kai mijin mace hud'u ne, saiya maida kallansa ga HAIRANAH yace "HAIRANAH kinji abin da AHMAD yace akanki, Sannan Hashim yazo shima da batun yana sanki, cikin su biyu wanene gwaninki, wa kike san Aure acikinsu....
HAIRANAH ta qara sunkuyar da kanta qasa tace "Ya AHMAD shine wanda na daidaita dashi, amma Hashim babu wata ingantacciyar magana a tsakanina dashi... Babah Alhaji yace "Masha Allah...
Sannan ya maida kallansa kan SABEER yace "SABEER na tambayeka wakagano a dangi kace min Ramlat haka ne, SABEER ya sakar mai murmushi yace "Kwarai haka ne, sai ya mai da kallansa kan Ramlat yace "Kinji abin da SABEER yace haka ne da gaske kuna Soyayya kuma kina sanshi.. Tace "Haka ne Baba, shina tsaida zab'ina.. Yace "masha Allah, saiya kalli AMAAR yace "AMAAR kace min kana san Hannatu haka ne...
Kan AMAAR ya bashi amsa sai NUWAIRA ta matsa kusa da HEESHAM cikin matuƙar tsoro murya qasa qasa tace mai, "Dan Allah dan Annabi idan Baba Alhaji ya tamabayeka wa kake so kace ni kake so kaji, bai kalleta ba yayi murmushi da cewa, "Dama kece matar da kika min, tace "Eh, wallahi nice, kuma ba ƙaramin sanka nake ba, dan Allah dan Soyayyarka da manzan Allah kace ni kake so karkace kana san HASEENAH... Takai ƙarshen zancen nata da zubo da hawaye, tare da kuka qasa qasa, yace "Gaskiya bana sanki, dan kinyi min Yarinya a Soyayya.... Saurin kama hannunsa tayi idanta na zubda hawayen tace "Nifa yayarka ce, na baka shekaru biyu koka manta ne, wallahi zan maka daidai yanda kake so, dan Allah HEESHAM ka temaki zuciyata kace ni kake so, wallahi ina MASIFAR SONKA, dan Allah karkama ZUCHIYATA haka, ka tunafa, Soyayya itace me samar da tunani, naga wannan tunanin akan kaina har yaso illatar dani, yanzu zakaso ZUCHIYATAH ta buga akan sanka, akan sanka zan iya mutuwa fah.. takai ƙarshen zancen dasan rushewa da kuka wiwi... Ai kamar ya ankare yayi saurin rufe mata baki cikin muryar can qasa yace "Haba nutsuwata Bana san wannan kukan pls, kawai ki d'aukar min alk'awarin bani cewa Yes kice min No a zaman takewar Auran namu... Cikin sauri tace "Nayarda, yanzu kana sona ko, d'aga mata kai yayi da cewa, I LUV U my Auntii, tasakar mai murmushi da cewa "LUV U 2 my dear..
Daidai lokacin Baba Alhaji ya kalli HEESHAM yace "Kai kuma dama nine nace zan maka Aure da wacce nake so, sai kuma mamansu MEENATU tazo min da batun Soyayyarka kai da HASEENAH, shin kana san na had'aka Aure da ita ne koko na baka Rahina wacce naso had'aka da ita..
HEESHAM yayi shuru da zubama Baba Alhajin ido, aiko cikin fusata Baba Alhajin yamai dak'uwa daci gaba da cewa, Kaci gidanku, ya ina maka magana sai kawai ka zuba min ido... HEESHAM ya sakar mai murmushi da tab'e baki yace "Toh ai waƴanda ka had'ani dasu d'inne basuyi ba, Baba Alhaji ya saki baki yace "Toh toh toh gayamin waƴanda sukayi, saiya kalli NUWAIRA wacce take kif kif da ido ya maida kallan nasa kan Baba Alhajin da murmushi ya sunkuyar da kansa yana cewa "mun shirya kammu... Babah Alhaji ya kalli NUWAIRA sai tayi saurin sunkuyar da kanta kasa yace "ban gane kun shirya Kanku ba, sai HEESHAM d'in ya d'ago ya kallesa yace "Ina nufin muna san junanmu nida NUWAIRA, mun shirya kammu tuntuni ko my dear, yakai ƙarshen zancen da tab'a NUWAIRA alamar tatabbatar mai, aiko da sauri ta kalli Baba Alhajin tace "Haka ne, mun shirya kammu...
Babah Alhaji najin hakan yaja numfashi dayin shuru, jama'ar wajen ko duk sai suka maida kallansu kan NUWAIRAN da HEESHAM d'in, can Baba Alhajin yayi gyaran murya yace "Toh ai shikenan.. Kai Saminu sai kayi hakuri tunda Kaji sun shirya kansu, Saminu dai shuru kawai yayi.. Saiya maida kallansa kan Babansu NUWAIRA yaci gaba da cewa, duk da mun gama magana dakai kace nayi duk yanda naga dama da yaranka, to kadai ji yanda komai ya gudana, Babu matsala in ad'aura musu Auran, Babansu NUWAIRAN yayi murmushi yace "Haba Babah, harsai ka tambayeni, aina d'auki wuqa da nama na baka tuntuni, kamar yanda ka fad'i yanzu, kayi yanda kasaba kawai, yayi murmushi da maida kallansa kan kowa yace "Toh jama'a kunji tabakin kowa, dan haka na yanke shawarar É—aura auran SABEER da Ramlat, da kuma HAIRANAH da AHMAD, ranar Jumma'an nan bayan an idar da sallar jumma'ar, dan naga sunfi buqatar junansu nan kusa, bayan wata d'aya na d'aura na HEESHAM da NUWAIRA da kuma Hannatu da AMAAR.. Nan kowa yahau sakama auran nasu albarka, da nuna gaskiya abu yayi kyau, nan ko taro ya fara watsewa..

Amma Saidai me, momynsu MEENATU na zuwa d'akin mahaifiyarta tayanke jiki tafad'i wai aljanunta sun tashi, nan tadinga masifa da bala'i akan me yasa Momy zata d'aurema yaranta gindj su Auri ƴaƴan Lubabatu, Ashe bata ƙaunar ta, Ashe dama zaman munafunci suke, da daba Lubabatun ai nunawa tayi tana san ƴaƴanta amma yanzu dan munafunci ta kitsama yaranta sun kwashe Soyayyarsu sun maidata kan y'ay'an Lubabatun. Nan ta dinga bori tana meqewa...
Haka jama'ar gidan sukayi cah akanta suna mata Addu'a kana tadawo normal, Lubabatu ta galla mata harara dan ita sam bata yarda da wani batu na aljanu ba, ganinta qarya ne... Taso da bata tashi ba taje ta juye mata butikin ruwa na sanyi taga qaryar qarya, idan ita shegiya ce tafita shegantaka, shiyasa tunda tafara borin batayi da ita ba, dan tsakaninsu kar tasan kar ne, toh sai Allah ya takaita tatashi, datasha ruwan sanyi, dan kowa a gidan yasan HALIN futunar Lubabatu, shiyasa yanzu wasu suke tare da ita suna danne zuciyata kar nata borin ya tashi..

Momynsu HEESHAM ko tunda momyn su MEENATUN tafara maganganun tayi gaba abinta, dan ita macece wacce bata san tashin hankali, Hannatu Ramlat HAIRANAH NUWAIRA sukabi bayanta, HEESHAM da AHMAD da SADEEQ da Dadynsu ne kawai suka saura a y'an gidan.... Suma suna waje tare da Baba Alhaji basu san me yake faruwa ba




MEENATU ko bata cewa hmm bare hm um.. Dan zuciyar tata babu dad'i..
Haka HASEENAH ma, ranta sai suya yake mata, har kuka sanda tayi, kuma taci alwashin saita Auri HEESHAM kota halin yaya, Sannan saita baqanta rayuwar NUWAIRA...

HEESHAM ya matsa gefe can ya fara kiran number na NUWAIRA.. Lokacin sun isa gida kenan, tana ganin kiran masa ta d'auka, yace "Allah my Auntii saina hukuntaki tunda kika yaudareni.. Cikin damuwa da shagwaɓa tace "Afuwa mana, Yace "Toh gayamin.. Tace "Me zance my love, yace "Yaushe kika fara sona, tace "Tunkan na ganka ido da ido, dan Allah kasoni fiye dasan da nake maka, "Na soki my Auntii amma fa zakisha fama dani, ba ayanzu ba, acan gaba nake nufi, tace "koma menene ina rokwan Allah yasa na iya dashi, fatana karkamin kishiya dan bana santa kwata kwata, yace Karki damu kozan miki da HASEENAH zan had'aki, kinga y'ar uwace agareki... Ai HEESHAM baiyi zato ba saijin kukanta yayi😂😂😂.. Cikin sauri yaci gaba da cewa "Dan Allah ki temakeni kiyi shuru, wallahi kinyi min daidai arayuwa babu batun qari...😟






NUWAIRA ta tsaida kukan dajan numfashi bata qara mai magana ba ta kashe wayarta.. Ya saki murmushi yana juyowa idansa ko ya sauka akan HASEENAH, da alama yanzu tazo wajen... Yace "Y'an mata lafiya...
Tace HEESHAM ka yaudareni, kaci amanar yarda, ka haqinceni, amma wallahi bazan tab'a yafe hakan ba, dan naci alwashin saina Aure ka, dan babu san wani d'a namiji araina sai kai,..

Murmushi HEESHAM ya sakar mata da cewa, "Kowa yana da wacce yake so HASEENAH, amma zuciyata NUWAIRA take so, itace macen da tayi min daidai a tsarin macen da nake kwad'ayin samu arayuwata, kinsan wani abu, inafa san NUWAIRAN da gasken gaske, kallo d'aya nayi mata naji gabana ya fad'i akanta, lokacin da kuma jikinmu ya had'u da juna bada wani shock yayi alamar akwai wani Babban sirri tsakanina da ita, lokacin ban san Soyayya ba shiyasa ban gane santa yayi ram dani ba, wallahi da tun a lokacin nagaya miki ina santa inaga da bamu kaiga yanzu ba, HASEENAH! ban yaudareki ba, ke kika tsaya yaudarar kanki, na gaya miki tun farkwan fara sona da kikayi, banda ra'ayin Soyayya a lokacin, amma kikaqi barin sona, banci amanarki ba, saboda na yarda bani nake da kaina ba, dama fata nayi miki kan Allah yasa na fara sanki kanna fara san wata, toh Allah bai amsa Addu'ata ba, saiya fara samin san NUWAIRA, so kike nace bana santa ke nake so, dan Allah dan Allah ki share batuna a zuciyarki daga yau na rok'eki ba danni ba, dan Allah.. Ya kai qarshen zancen da yana me had'e mata hannuwansa biyu alamar rok'o.

Hawaye ne ya zubo ma HASEENAH tace "Alƙawarina! So kake alƙawarina ya tafi a banza, so kake na rayu cikin baqin cikin ban cika burina ba, ina sanka HEESHAM kuma wallahi saina Aure ka, anya kasan miye so kuwa, kasan ya yake kuwa, kasan yanda yake da zafi a zuciya kuwa, kasan ya masu fama dashi suke ji aransu kuwa, kasan yanda yake kisa cikin lokaci qanqani kuwa, haba HEESHAM, kaji tsoran Allah! ka Aureni na rantse maka bazan tab'a kawo maka matsala ba arayuwa ba, dan sanka nake da gaske.. Takai qarshen zancen da fashewa da kuka... HEESHAM na ganin hakan ya kauda fuskarsa daga kallanta tare da barin wajen...
Tana ganin haka tasaki murmushi daci gaba da cewa "Idan ka sake na zama mata a gareka Wallahi bayan na baqanta rayuwar ita NUWAIRAN saina nuna maka kuskuranka na fatali da Soyayyata da kayi...


MEENATU ko kiran AHMAD tayi a waya wai kawai idan ya tashi tafiya ya tafi HASEENAH zata sauketa a gida dan tana da maganar da zatayi da momynsu..
AHMAD d'in baija ba, yace mata babu damuwa,

Aiko da gaske maganar ta tsaya yi da momyn nasu, inda ta dinga kulla mata tsiya kala kala, a haka HASEENAH tazo ta samesu a d'akin mamansu momyn nasu wato kakarsu, ayanzu babu kowa a d'akin sai su, duk kowa ya watse tunda momyn tasu tadawo normal, dan har itama kakar tasu bata cikin É—akin, nan suka had'u su uku sai maganar tafi yi masu dad'i ainun..


Ananko da tunanin HEESHAM NUWAIRA ta shiga bedroom d'insu, sai momy tayi tunanin ko tunanin abin dazai faru gaba takeyi jin kalaman momynsu MEENATU, dan haka saita bita room d'in, aiko samunta tayi akan bed d'insu ta zabga tagumi, ita tunaninta idan da gaske HEESHAM yake zai Auri HASEENAH ina zatasa kanta, gani take tafi kowace mace kishi a duniya... Sai momyn tadafata tace, "NUWAIRA tunanin me kikeyi, ta kalli momyn a nutse tace "Wallahi momy banso HEESHAM danna b'ata zumuncin dake tsakaninki da Momynsu MEENATU ba, kawai sanshi nake da zuciya d'aya..
Sai momy taja numfashi tace, "Karki sama kanki damuwa akan hakan NUWAIRA, ba wani abun dazai faru dan babu abin da kika b'ata, duk abin da zatace bazan kulata ba, danni na yarda da ƙaddara, ki cire tunanin komai aranki dan bana san naga mutum cikin damuwa. Tace "Toh insha Allah zan cire komai araina, tace "Yauwa koke fa, Sannan bana san ki canja min matsayi akan wanda kike bani, kibarni ayanda nake, cikin jin kunya tace "Toh.. Murmushi momyn tayi da tashi tabar room d'in..
Tana ko fitta Ramlat da Hannatu da HAIRANAH suka shiga ciki.
Ramlat tace gaskiya NUWAIRA kinyi keda HEESHAM kunyi mana bazata, cikin murmushi NUWAIRA tace "Da mukayi mefah, "Da kuke Soyayya mana, sam kun rufe tunanin mutane akanku, ba wani wanda ya lura daku, Hannatu ta zauna kusa da NUWAIRAN tace "Nifa har yanzu ina cikin mamaki, wai Soyayya kuke, Toh yaushe kuka fara, HAIRANAH tayi Dariya tace "Nifa dama ina zarginsu, dan ranar akan idona HEESHAM ya sakar mata kiss da hannunsa, Ramlat takama baki, Hannatu tace "yanzu ke kirasa wanda yayi miki a Soyayya sai HEESHAM, kinsan waye HEESHAM kuwa, kinsan futunarsa kuwa, NUWAIRA taja numfashi tace "Nasani mana, amma Ku yake yima bani ba, nifa ko, bazanji duk wani abu dazaku faɗi akansa ba, dan na fara zargi da tunanin babu mamaki da Soyayyarsa aka halicceni, shine da muka gamu da juna tatashi min, ni kunga kwanciyata ina fashin sallah dan Allah kadda kowa ya tashen idan kuka gane nayi bacci.. Takai ƙarshen zancen da kwantawa abinta.. HAIRANAH tace "ko bamu tasheki ba zaki tashi da kanki da zaran lokacin yimai girki yayi..
Murmushi tayi batare data bata amsa ba..

Hannatu taja numfashi da maida kallanta kan HAIRANAH tace, "Gaskiya na godema Allah da zaki zama mata agun ya AHMAD, hakan yayi min zaƙi a zuciya, fatana kadda kaji tsoran MEENATU, idan ko kika kuskura kikaji tsoranta kin gamu da bala'i, dan ba qaramar shegiya bace, tana miki ki mata dan bata fiki da komai ba.
Ramlat tace "Kinga HAIRANAH kadda kibi ta Hannatu ba ruwanki da ita, tana shashinta kina naki ba ruwanki da shiga harkarta..
HAIRANAH tace, "Hmm, Karki damu Aunty Ramlat, komai zaizo da sauƙi.. Tace "Yauwa haka nake san ji.. Hannatu taja tsaki tace "Baku san yanda nake jin haushinta bane..
Shuru suka mata kawai..



Yau momy da Ramlat ne kawai suke aiki a kitchen, NUWAIRA taqi zuwa yi musu ita da masoyin nata HEESHAM... Momy ta tambayeta yau bazata musu girkin bane, tace kanta ne yake mata ciwo, da gaske momy ta yarda da hakan, dan har magani tabata, tako karb'a tasha, dan tasan paracetamol bazai cutar da ita, abin dayasa ko taqi yima HEESHAM girki shine, so take ta tabbatar ma da HEESHAM d'in da gaske bata san HASEENAH...

Shiko sai bayan sallar isha ya shigo gidan, direct gun momy yayi yaje ya gaisheta, tace mai, "Yau kan NUWAIRA nayi mata ciwo batayi maka girki ba, yace "Wayyo me yasa kan nata yi mata ciwo, momy tace "Toh HEESHAM ciwo daga Allah ina zan sa ni..
Yace "Toh bara naje na dubata daga can zanje na kwanta... Tace "Toh amma nasa Hannatu takai maka abinci É—akin ka. Yace "Tnx momy, tace "Aciki dad'i lafiya..
Murmushi yayi da ficcewa sai yaci sa'a alokacin NUWAIRAN ta fitto dan d'aukar wayarta data bari a falo.. Yace "barka da dare my Auntii.. Sanda ta lumshe ta juyo ta akallesa tace "Barka dai luv.. Yace "jikin da sauƙi daga dukkan alamu, tace "Dama babu ciwan, sannan banyima momy ƙarya dan wani abu ba, kawai nayi dan kaje wajen HASEENAN taka tabaka abinci.. Yayi murmushi da cewa, "kishinki yana ƙaramin sanki my Auntii, tace "ni kuma kishinka damuwa ne agareni, yace "Zaki dena ne my Auntii, da zaran ni dake mun zama abu d'aya. Tace "Magana ta gaskiya bana tunanin denawa koda mun zama abu d'ayan.. Saidai idan mutuwa nayi...
Yace "Owkie, tunda haka ne kita rainan mun shi, nasan bazai tab'a zama cuta a gareni ba, tace "Amma ni zai iya zama a gareni, yace "Idan na Auri HASEENAN ba, tace "Dan Allah karkamin kishiya, ta fad'i maganar da shagwaɓa, sai yayi murmushi da cewa, "Bazanyi miki ba my Auntii, kinfa yimin daidai a Soyayya, idan na qara b'ata komai zanyi.. Cikin farin cikin furucin nasa Tace "Gud, yanzu me kake san ci, yace "Alamu sun nuna duk ran da tunanina ya kulle nayi miki kishiya bani ba samun girkinki qilama duk wata kulawarki, tace "Afuwa my dear bazan qara ba, yace "Koda kin qara bazan tab'a hukuntaki ba my Auntii, yanzu zani na kwanta ki kulamin da kanki tare da mafarkaina masu tsayawa arai, yakai ƙarshen zancen nasa da shafar gefan fuskarta kana ya sakar mata murmushi da barin falan..
Itama da murmushin jin daÉ—i tayi room nasu..


AHMAD ko sai kusan tara da kwata ya koma gidan nasa, yayi tunanin MEENATU zata kulasa kan batun Auran nasa da HAIRANAH amma sai yaga sab'anin hakan, saima tararsa da tayi cike da kulawa, dan haka bayan ya fitto daga wanka kwanciya yayi kan gadansa ya fara laluban Num na HAIRANAH, lokacin tayi bacci, dan haka cikin mayen bacci tad'auki wayar tata da cewa "Hello, yace "Kinyi bacci ne Baby.. Sanda talumshe ido Sannan tace, "tun d'azu nayi, yace "Sorry na tasheki ko, tace "No na tashi lokacin daya dace ne.. Yace "gud! gayamin, kin yarda dani na zama miji agareki, tace "Toya zanyi dakai Yaya, so kake naqi kaje kata kashe min masoya, yayi murmushi da cewa, "ina da kishi sosai dan Allah ki kula da hakan, tace "insha Allah zan kiyaye, yace "toh bara na barki ki kwanta ko, tace "Hmm kodai tana kusa dakai ne, zaiyi magana MEENATU ta shigo room nasa tana cewa, "na shirya maka komai akan dining my dear... HAIRANAH najin hakan ta kashe wayar da tashi tajawo fillo jikinta tana Jan tsaki, dan jin wani zafi taji aranta jin muryar MEENATUN, nan take ranta ya b'aci, taja wani shegen tsaki, dake NUWAIRA tayi bacci itama, Ramlat kuma tana tare da SABEER a harabar gidan, Hannatu ce tajita dan bata kwanta ba tana karanta novel, dan haka sai tayi saurin kallanta tace, "lafiya sister, tace "No is owkie...



Washe gari bayan HEESHAM yagama shirinsa zashi yin breakfast yaga HAIRANAH zata wucce ta part d'insa, nan yayi saurin taran gabanta yana tambayarta wai ya sukayi ita da Ya AHMAD ne... Sanda tayi dariya kana tabashi labarin komai, har da kiranta da yayi cikin dare, yace "Gud da ace kinbi abin da yace miki bakiyi mai musu ba dako ko anyi auran naku bazaki gane matsayinki agunsa ba.. Tace "Ai gane hakan danayi ne yasani nacewa saiya furta yana Sona, Yauwa dan Allah yaushe kuka faro Soyayya kai da Aunty NUWAIRA ne, yace "kawai jinta nayi araina, gaskiya ina santa sosai, ban san ko hakan yana da nasaba da ganin ko dan itace macen farko dana fara yima so irin haka ba.. HAIRANAH tace "ba mamaki kam, kuma dama ai ita soyayyar gaskiya daga haka take farawa, fatana Allah yasa kadda ka had'amin y'ar uwa da wata mace a matsayin kishiyarta..
Yayi murmushi da cewa, "Wannan kuma na Allah ne, amma har a zuciyata bani da sha'awar rayuwa da mata biyu, sai kuma na taki sa'a tazo min daidai da zab'ina..
Itama murmushin tayi da wuccewa tana cewa, "magana ta gaskiya ban tab'a cin karo da masoyan da suka dace da juna irinku ba..
Sanda yayi dariys kana Cikin sauri yace "saike da YA AHMAD... Kun dace da juna sosai. Bata kulasa ba taqara gaba abunta tana tuna AHMAD d'in, nan taji ranta ya b'aci wai aganinta ya dace ya kirata da safen nan... Hmm tanaji suna waya da momy d'azu wai yau zai koma aiki, saitatab'e baki ganinta ai dama zaman banza ne yasashi tarewa da matar tasa, ko me sukeyi oho, abayyane taja tsaki..😃 (Rahama Nalele ko tace oh su HAIRANAH a rage kishi)
DOWNLOAD
DOWNLOAD

Please Login or Register in order to submit comment