Join Our WhatsApp Group

Idan ku ka ga kun taba wani wuri ya fitar daku a shafinmu, sai ku danna back kuyo baya, ku sani yanzu muna amfani da tallan Popunder a shafin, so karatu zai muku dan wahala, amma ta hakanne kadai zamu iya cigaba da rike shafinnan. idan har bakwa son talla sai kuje ku yi subscription na shafinnan akan karamin kudi ku runga downloading kawai. SUBSCRIBE


DOWNLOAD

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register
DOWNLOAD

cikin matuƙar ƙaunarta ya qarasa shiga d'akin yana cewa, lalle ke matsoraciyace asO❤ daga gwadaki sai kawai najiki a gadan asibiti, murmushi ta qarayi da kallansa ido cikin tace, "kai ka d'auka wasa nake maka, wallahi zan iya mutuwa asanka, "Na yarda masoyiyata, wallahi nashirya auranki, idan har zaki Aure, Kinyi min d'ari bisa d'ari, ina sanki HAIRANAH, dafarko nagane burgeni kikayi ranar dan gaskiyarki, daga baya kuma saina fahimci ƙaunarki ce takamani lokaci d'aya, dan Allah ki Aureni kadda kibarni na qara rasa wani abu me mahimmanci a rayuwata.. AUFAN yakai k'arshen zancen nasa da zama kusa da ita sam idansa akanta yake baimayi zatan mama da NUWAIRA suna wajen ba, haka ita ma mantawa tayi da zamansu a wajen, ta qara mai murmushi a karo na uku tace, ina sanka AUFAN, kuma wallahi zan Aure ka, dan sanka nake da gaske, dan Allah kadda ka barni, kadda ka cutar dani, kaga sanka ne ya kwantar dani, idan ka qara min wasa irin wannan zan rasa rayuwata, murmushi shima ya qara mata, yace "kin warke matata, kuma babu ke ba qara kwanciya akan san AUFAN, dan zai raya miki Soyayyarki yanda bazata qara kwanciya dan ciwo ba....

NUWAIRA tayi tari da cema AUFAN "sannu, dan talura baisan da zamansu ba kamar yanda HAIRANAH tamanta hakan...
Cikin sauri ya kalleta ita da mamah, kunya ta kamasa, dan ga kama nan ya gani a fuskar mama ba shakka mahaifiyar HAIRANAN ce, kuma ko babu tambaya NUWAIRA y'ar uwar HAIRANAN ce, danga jikinsu iri d'aya...
Durƙusawa yayi ga Mama ya gaisheta wacce mamaki ya hanata sauke idanta daga kansu, sanda taji yana gaisheta tukunna tadawo normal..
Nan ta amsa cikin kulawa kana ta ficce daga d'akin..
AUFAN ya kalli NUWAIRA yace haba qanwarmu, yazaki barmu muta sakar zance agaban mamah...
NUWAIRA tayi dariya, tace "aini bana katse masoya ina suna cikin wani hali haka, Sannan nayi ammakin ganinka anan da saurin gane mamammu da kayi, yace, "Kama nagani, ganina ananko da kikayi wannan ya isa kiyarda ba yayarki bace kad'ai tadamu da sona nima ina Santa tun ganin farko qilama nawa yafi nata zafi..
NUWAIRA tace "Toh Allah yasa, amma HAIRANAH qanwace a fareni ba Ya bah? Ni yayarta ce itace qanwar..
AUFAN najin hakan ya waro ido yace, "gani nayi tafiki qiba, NUWAIRA tayi dariyar furucinsa tace, "Toh ai ba daga qiba bane, daga ido ne, kasan ance yasan kima, da alama HAIRANAH dai zata rigani tsofa, tunda kowa ganin itace yayar yake, ni kuma kuma qanwar..
Dariya AUFAN yayi qila wannan ya kasance na farko tun bayan rasuwar iyayensa rabansa da dariya Saidai murmushi gashi yau ya yima NUWAIRA saboda tsabar wayewarta da iya mu'amula da mutane, yace.. "Waya gaya miki matata zata tsofa da wurri, Indai ina tare da ita zan bata kulawar da zatayi lastin fiye da kowace mace..
Murmushi kawai NUWAIRA tayi, batayi zatan haka AUFAN d'in yake da sauqin kai ba..
Haka HAIRANAH murmushi take tayi ranta na mata dad'i ganin yazo gareta harda maganar Aure..



Madalla shine ciwan shine kuma samun sauƙin, kwana d'aya taqara aka sallameta, mama da babanta da yayanta SABEER sunyi mamakin wai ciwan so ne ya kwantar da ita, tare kuma da mamakin kulawar da AUFAN d'in ya dinga bata dan jiya dazata qara kwana d'ayan Neman gado yayi a asibitin ya kwana anan, wai duk dan HAIRANAN, NUWAIRA kuma ta kwana da HAIRANAN cikin d'akin da take....
To shine washe gari da aka sallameta yabarta zuwa dare bai takura mata ba.

Bayan isha'i ko yazo ya aika a kira masa ita, bayan ta fitto ya kalleta sosai yace "Gaskiya kin rame da yawa me sona.
Tace "Haka kaima abin ya shafeka, har kad'anyi qashi, yanzu mu zauna ka gabatar min da tarihin rayuwarka na baka nawa mu fahimci juna..
Murmushi yayi zuciyarsa na bugawa kasancewar yau zai fara sharara ƙarya..
Ahankali bayan sun zauna tacigaba da cewa "bari dai na fara baka labarin kaina, sunana HAIRANAH nice y'ar auta a d'akinmu, yayana SABEER shine babba sai Aunty NUWAIRA data biyo bayansa saini auta.. Babana da mamana su kad'ai muka tashi muka sani bamu da wani dangin dazan iya kamawa nace maka ga dangina, alamu sun nuna sun rigamu tafiya gidan gaskiya, amma da wayona kakar Babana ta rasu. shekarata 24, na gama secondary skull amma banci gaba ba, kuma bani da ra'ayin ci gaban, Sannan ina san mutum me gaskiya, ina san wasa a rayuwata, Sannan wanda yafini wayo idan yana gabana gabaki d'aya wayona bacewa yake, amma duk da haka nafi yayata NUWAIRA wayo karkace ni doluwa..😃 takai qarshen zancen da dariya..
Murmushi yayi kana yace, "me kikafi so arayuwarki, "abin danafi so a rayuwa shine addina ma'a ina san bautar ubangijina akan lokaci, sai manzona, manzan Allah S A w, kana iyayena, da Y'an uwana, sai kai da nake so fiye da kaina..
Jan numfashi yayi da cewa, sunana AUFAN iyayena sun mutu dukkansu, ayanzu ina hannun kawuna, wanda yake garin nan da zama...
"Ayya, yanzu iyayenka sun mutu, Allah sarki, Allah yaji qansu, ban sani ba da'ace nasani tun farkwan haduwata dakai dana shagala duk sallata ita rokwan musu gafara..
Murmushi yayi da zuba mata ido, yana wani tunani, ganin haka yasata hura masa iskar bakinta tana cigaba da cewa, "kayi hakuri kadena tunaninsu, ba gashi Allah ya baka ni a rana d'aya ba😄..
Murmushin dai ya qara sakar mata da cewa, " sanki yana dad'a shigata me sona, tace "nima haka masoyina...
Haka suka bama Soyayya hakkinta a wannan dare dan sai wajen tara da minti goma yabar ta shiga gida..


Haka komai ya dai daita a al'amuran HAIRANAH, kamar babanta yasan basu dad'e a Soyayya tsakaninta da AUFAN d'in ba, dan baiyima AUFAN d'in magana kan ya turo magabatansa ba har sanda sukakai sati uku suna tsula Soyayya, haka suka dinga bama NUWAIRA sha'awa... Wannan shine karo na farko dataji sha'awar *SOYAYYA* sai Rahama nalele tace aranta indai batu akan Soyayya ne Karki damu NUWAIRA SO yana nan zuwa gareki..😍

Toh ayau laraba Baban HAIRANAH ya kira AUFAN yana cemai ya turo iyayensa dan yana san ayi maganar auransa da HAIRANAN, jin hakan murna ta kama AUFAN, dama Azeez yazo garin na Kanon jiya yana hotel d'in da AUFAN ya kama, dan haka nan take AUFAN ya koma hotel d'in ya gayama Azeez d'in abin da Baban HAIRANAN yace mai, nan babu b'ata lokaci a washe garin ranar Azeez ya kawoma AUFAN iyayen qarya..
Kud'i sosai Azeez ya sakema way'annan mutanan, haka sukayi gidansu HAIRANAH..
Bayan sun gabatar da kansu ga mahaifin HAIRANAH da makocinsa babu b'ata lokaci bayan sun fahimci juna suka bada sadaki..
Bayan tafiyarsu makwabcin Baban HAIRANAH yace ya kamata su qara binkice akan AUFAN da iyayensa, danshi haka kawai yaji bai yarda dasu ba..
Aiko mahaifin HAIRANAH yaji maganar makwabcin nasa malam Aiyuba, nan yasa aka fara mai binkice akan AUFAN da way'annan mutane da suka amsa cewa d'ansu ne...

Nanfa labari ya canja, dan binkice yanuna AUFAN ba d'ansu bane, kuma su irin way'annan muta nan nanne waƴanda ake biya dan acimma buri irin wannan..
Hankalin mahaifin HAIRANAH ya tashi, nan ya kirasu kan suzo su karb'i sadakinsu, ya gane kosu suwaye..
Ai mutanan najin haka sukaqi zuwa Sannan suka kira AUFAN suka gaya mai komai fa ya kwab'e, nan ran AUFAN dana Azeez ya b'aci...
Mahaifin HAIRANAH ko yana gayama ita HAIRANAN tafara hawaye, baji ba gani, shi kuma yace inzata mutu bazai aura mata wanda baisan tushensa ba..
Da kuka sosai HAIRANAH tabar falan mahaifin nata
Gaban Maman HAIRANAN ya fad'i.. _Karfa tarihi ya maimaita kansa,_.. Ta Faɗi hakan a ranta😳 tana me kallan Babansu HAIRANAN, nan batare da b'ata lokaci ba tashiga tunanin rayuwarsu tabaya....

******Gidan su Babban gida ne gidan mutunci ne gidan arzik'i, arziqi irin sosai d'innan, yana nan a Abuja area 2..
Tun tasowarta tasan AURAN ZUMUNCI iyayenssu sukeyi..
Su family ne masu mugun yawa, sai yazo ya kasancewar babansu mata huɗu ne dashi kuma ko wacce mata sanda tahaifa masa yara sama da goma goma, matarsa ta ƙarshe ana kiranta Sa'adatu itace wacce ta Haifa masa yara huɗu uku maza d'aya mace, d'an Sa'adatu nafarko shine Ummar, sai Kabiru sai Jamilu sai y'ar autarsu LUBABATU..
Lokacin da suka girma yaran suka mallaki hankalin kansu Ummar yayi Aure Kabiru shima yayi haka Jamilu shima yayi..
Duk had'in zumunta ubansu yake musu, sai kuma ya samu yara masu ladabi dan duk matar dayaga dacewarta da d'ansa a dangi nan yake had'asu Aure..
Haka dake unguwa ce guda lokacin da mahaifin nasu yasiya hakan yasa duk yaran gidan dayakai Aure sai mahaifin nasa ya yanka mata wani shashi a unguwar yanda zai isheshi, lokacin mutane basu damu da zama a unguwar ba, haka yata raya unguwar da yaransa abin gwanin ban sha'a, har yakai filin nasa ya qare, dayaga haka yaqara Siyan nakusa dashi, kuma har izuwa yanzu yana nan da sauran gurare awajen. Alhaji Muhammad me gwala gwalai kenan...
Sai daga baya yaran nasa manyan da suka fara rike nasu kud'ad'an sai suka fara Siyan wasu guraran a irin jerin unguwannin manya Suna komawa can, dan bama qannansu dama anan...

Lubabatu Lokacin da matar Ummar yayanta ta haifi d'anta na farko, Wato AHMAD Lubbabatu ce meyi masa hidama haka data haifi d'anta na biyu SADEEQ, Lubabatu tana dasan yaran sosai, gashi dama tafi shiri da mamansu AHMAD d'in wato Aisha akan sauran matan yayun nata biyu, wato Amina matar Kabiru da maryam matar Jamilu.. Gasu dai duk dangi d'aya ne Saidai dama hakan tana faruwa kaga kafi shiri da wani fiye da wani
Lokacin shekarar Lubabatu goma sha tara, al'amarin nata ya faro ne wata rana da mahaifinta ya gane tana san wani bare acan awaje waishi Sulaiman, wannan abu ya b'ata ran mahaifita sosai, dan yasan tasan su basu auran bare, hakan yasa ya fidda mata miji a dangi, aiko nan Lubabatu tayi tsalle ta dira tace wallahi bazata Auri d'an uwan nata ba, ita Sulaiman take so baren da basa Aura, nan zance ya koma kunnan mahaifinta yace idan har bazata Auri wanda yake so ba Saidai tabar mishi Gida bashi ba ita, hankalin Lubabatu ya tashi matuƙa dan a duniya bata da abin so kamar Sulaiman, hakan yasa suka had'a baki ita da Sulaiman kan su gudu can wani gari a d'aura musu Auri, cikin dare da misalin qarfe d'aya ta ibi kayanta taficce daga Gidan nasu dama Sulaiman yana jiranta kan titi da motarsa dan dama shima da d'an abun hannunsa haka suka gudu abinsu acikin wannan dare, wannan abu ya tada hankalin Y'an uwa, dan basu tab'a tunanin wani yaran gidan zai iya aikata hakan ba bare kuma macen gidan, daman Lubba tana da d'an futuna, kuma mahaifinta yana santa dan duk yaran d'akin Sa'adatu sansu daban yake aransa, amma bazai iya karya dokarsa daga kan Lubabatun ba, wannan yasa ya nace kan bazai tab'a bari ta Auri bare ba..
Haka dai hankalin mahifiyarta Sa'adatu ya tashi matuƙa kasancewar ita kad'aice y'arta mace, ba qaramin san y'ar tata take ba..
Gashi ba'a san daga ina Sulaiman d'in yake ba bare aje a kamota, haka Y'an uwanta suka dinga lemanta a garin Abuja ba ita ba dalilinta, badan sunso suka hakura..
Duk da mahaifinta yayi nadama dan baiyi zatan zata iya gudu akan hakan ba, amma haka ya daure bai nuna ya damu ba..
Gaba ko ta shiga tsakaninsa da Sa'adatu, dan tace shine silar guduwar y'arta tilo guda d'aya mace, amma ita da shi take gayama hakan, haka daga baya ta hakura suka dawo suka shirya dan ita kad'ai ya nunama yayi nadamar hakan...

Dama shi Sulaiman iyayensa sun Dade da rasuwa, sai kakarsa data saura dama a hanunta ya girma.
Dan haka kai tsaye gareta ya nufa, yace mata Lubabatu marainiyace agidan marayu tagirma yanzu daga canma ya d'aukota, yana san tatara kwabta ayimai Aure da ita, dan sun fahimci juna gashi har kungiyar gidan marayu sun bashi ita.

Kasancewar kakar tasa tsuhuwa nan shirinsa ya shiryu akanta haka ta biye mai ta aura mai Lubabatu, shine fa har yanzu suke garin kano da zama, amma Lubabatu tana bibiyar danginta tasan da
Zaman kowa acikin y'an uwan nata har mahaifiyarta dashi kansa mahaifin nata, shine Aihuwarta ta farko tasamu SABEER, ta biyu tasamu NUWAIRA shine ta ukun tasamu HAIRANAH..

Tana kawowa nan a tunaninta taja numfashi, tana gudun kadda HAIRANAH ta gudu wajen AUFAN taje a d'aura mata Aure dashi, gaskiga idan hakan tafaru zata shiga tashin hankali..... "Allah yasa kar hakkin Mahaifinta ya bini akan HAIRANAH😭....
Tafad'i hakan a bayyane cikin matuƙar tsoro hawaye na zubo mata, nanko hankalin Sulaiman mijinta ya tashi, danshi sai yanzu ya tuno da baya..😳
Cikin damuwa yace.. "Innalillahi-wa'inna'ilaihirraji'un
Insha Allah hakan bazata faru ba..
Cikin kuka tace dashi, "idanko hakan tafaru lokaci ne yazomin da zanje na sadu da iyayena danna nemi gafararsu..
Shuru Babansu HAIRANAN yayi, shidai yana san matarsa kuma bazai yarda taje ga iyayenta tabarshi ba, dan haka yayi mata shuru kawai..


Hmmm aiko bayan HAIRANAH tabar falan Baban nasu kiran AUFAN tayi cikin kuka sosai, yana d'auka tace mai, "meyasa kamin haka AUFAN, meyasa. Cikin tashin hankali yace mata kimin afuwa HAIRANAH banyi danna b'ata miki rai ba, nidai na yanke shawara zanbi duk abin da zakice ayanzu, dan bazan qara miki qarya ba...
Tace "ka d'au alkawarin duk abin danace maka zakayi, yace mata "eh zanyi duk abin da kike so ayanzu, tace "so nake mugudu muje can wani waje a mana Aure kaga sai muyi rayuwarmu bame takura mana ko..
Yace "Yes kin kawo shawara, kifito cikin dare da misalin qarfe goma sha d'aya zan jiraki a kan layinku, Abuja zamuje Muje can amana auranmu...
Babu jin komai HAIRANAH ta amince suka ajiye waya..
AUFAN ya gayama Azeez yanda sukayi yace mai dama abin daya dace kenan...

NUWAIRA na toilet lokacin da HAIRANAH take wayan, dan haka bata jiyo komai ba, a lokacin HAIRANAH ta kulle NUWAIRAN a toilet din ta wajje, haka ta had'a kayanta kala biyar tasaka a wata Jakarta me d'an kyau haka ta b'oye a wani sak'o anan dai cikin d'akin nasu..
Kana ta bud'e NUWAIRA wacce taketa masifa wai wane irin iskanci ne zata kulleta a toilet, ita dai HAIRANAH shuru tayi mata..
Yanda mamansu taga HAIRANAN ta sake a daran sai tayi tunanin ta hakura da AUFAN d'inne, dan haka sai hankalinta ya kwanta..

Akan kunnan HAIRANAH yayanta SABEER ya kulle gidan nasu lokacin Qarfe goma da rabi, NUWAIRA har tayi bacci, iyayensu ma haka, sanda tabari sha d'aya da rabi tayi kana ta d'auko kayanta da wayarta, sai ta'ajiyema NUWAIRA y'ar wasiqar data rubuta, ta bud'e falan nasu a hankali ta ficce, sanda ta leqa shashin Yayan nasu SABEER kallo yake dan ga Qatar sautin magana nan na tashi, haka taje ta zare sakatar qaramar kofarsu, taficce hankali, haka tadinga sauri, dan AUFAN yakira kusan sau ashirin Allah yasa wayar tana silent, haka ko tagansa akan layinsu, ya bud'e mata mota cikin farin ciki tashiga, suka kalli juna da sakarma junan murmushi, AUFAN yaja motarsa dan acikin wannan daran yake san subar garin na kano..

Aiko hakan ce ta kasance, dan acikin daran sukayi Abuja....

Kuma kai tsaye gidansa yakaisu, bedroom d'insa yabar mata, yaje can falansa ya kwanta, saida gari yayi haske HAIRANAH tatashi lokacin qarfe takwas, nan tatashi da salati tashiga toilet tayo alwala tagabatar da sallar asuba, kana tahau qarema gidan kallo, gaskiya yana da tsafta, tafad'i hakan aranta. Ganin gidan tas dashi, ko ina sai qamshi yake yi, dama tunda AUFAN ya gayama Azeez yanda sukayi da ita na gudun nasu Azeez ya Siya dadduma, da duk wani abun da zata buqata dan kar idan ya d'aukota tatashi tambayarsa yahau mata kame kame..😂
(Rahama Rufa'i Nalele tace ita kan zataga ikwan Allah🤔 ganin ya tafiyar duhu da haske zata kasance)

HAIRANAH tasauko qasa nan taga breakfast lafiyayyu suna jiranta, ga masoyin nata yana sakar mata murmushi da alama yayi wanka dan sai zuba qamshi yake..
Ta gaishesa da cemai "Naga komai sabo brush makilin dasu Listerine mouth wash duk nayi amfani dasu, wanka ne dai banyi ba, shima ina da dalili nah, murmushi ya sakar mata da cewa "Yanzu dai kici abinci saiki gaya min dalilin naki, ya fad'a yana ja mata kujera tanaci yana tayata har suka gaba.. Kana ta kallesa tace "Toh mungama, dan haka yanzu muje wajen wani malami ya d'aura mana Aure.
Yace "Toh angama.. Amma dan Allah kiyi hakuri kan abinda nayi miki, zan gaya miki idan mukaje aka d'aura mana auran kinji, tace "LA karka damu, ina sanka da yawa, bazan iya barin lefinka ya dad'e cikin araina ba.
Yace "Nagode sosai, amma batun wanka meyasa bakiyi ba.
Murmushi tayi da cewa, saboda ina san sai ka zama miji agareni kana na iya wannan sakewar a gidanka.
Yace "kina da gaskiya, dama akwai wani babban mutum wanda akamun kwatancensa, cikin nan garin na Abuja, sunansa Alhaji Muhammad me gwala gwalai. Kinga zuwa anjima sai muje wajensa ya d'aura mana auran, tace "eh ina jin sunansa a bakin mamammu tana yawan cewa mutumin arziqi ne, ba damuwa ko yanzu ma zamu iya zuwa garesan ai..
Yace "Haba saikace gudu muke, kidaiyi hakuri ki huta zan kaiki nan gidan makwafcina kiyi wanka wajen matarsa idan kika dawo sai muje hankali kwance..
Murmushi tayi da cewa, "Toh shikenan..

Haka ko suje nan gidan kusa dasu, yace ma makwabcin nasa qanwarsa ce, zata d'an gyara kanta ne yanzu, sai yace mai ba damuwa.
Matarko me kirki, ga tsafta, nan HAIRANAH tayi wanka ta gyara kanta sosai cikin shigar wata jar atamfarta me ratsin kaloli masu kyau, tafeshe jikinta da turare kana tama matar gidan sallama, anan waje taga AUFAN kan motarsa yana jiranta. Yana ganinta yadinga sakar mata murmushi, shidai yana Santa yarinyar tayi masa ¹00.
Suna tafiya suna hira a haka suka iso unguwar, can wajen wani masallaci taga AUFAN d'in yayi parking yana ce mata, "yauwa yanzu dake lokacin sallarku ya kusa azahar kenan' dan yanzu qarfe daya ne zan iya samunsa a cikin masallacin, kinga saina aika yaro ya kira mana shi, ina gaya miki mutumin Babban mutum ne, ya tab'a temakona wata ranah dana tab'ayin hatsari, bakiga temakwan daya bani ba.
HAIRANAH tace "Ayya Allah ya saka masa, amma meyasa kace lokacin sallarmu, kana nufin kai ba lokacin sallarka bane..🤔 takai qarshen zancen nata damai kallan tuhuma, aiko nan gabansa ya fad'i, sai yayi saurin cewa, "kinsan wani lokacin idan mutum yana magana sai kiji ya fad'i wasu kalaman ba daidai ba, nidai nasan ganinki da nakeyi ne ayanzu yasa na manta fad'ar Kalmar data dace, da murmushi tace, "Idanko haka ne zanso harshenka ya dinga gyaruwa indai akan batu na addini ne...
Yace "insha Allah zan kiyaye.. Yana faɗin hakan suka fitto daga motar, koda wasa AUFAN baiyi tunanin shiga masallacin ba, saboda yaga rashin dacewar hakan tunda shi ba musulmi bane, wani Yaro ne yaga zai shiga masallacin saiya roqesa kan ya kira masa Baba Alhaji dan Allah..
Yaran ya amsa mai da shiga masallacin kai tsaye..

Lokacin Alhaji Muhammad me gwala gwalai ya bud'e kur'ani kenan zai karanta, yaran yazo ya gaya mai ana sallama dashi, yayi shuru, dan yasan indai mutanansa ne zuwa suke masallacin dan sunsan yana kama tilawar alkur'ani kafin ya kira sallah.. Har zaicema yaran yace bakwan ya shigo sai kuma ya fasa, ya kalli wani saurayin jikansa wanda yafi soyuwa a ransa yace, HEESHAM muje ka rakani wajan bakwan nawa ko..
HEESHAM ya turo baki, yace Baba kaje abinka, kaga yau ban samu yin karatu da asuba ba, bacci yasha kaina, idan kuma kace nace saina rakaka Toh muna yin sallah zan koma gidammu, satin danazo yi maka ya wucce kenan..
Murmushi kakan nasa yayi, shidai yana san HEESHAM takwaransa... Kama hannunsa yayi suka tashi yana bashi amsa da cewa, "Saika rakani, kuma sati biyu zakamin bama daya ba, HEESHAM yayi murmushi shima tare da qara kama hannun tsowan, yace, "ina sanka kakana, Allah yasa kaga Aure kafin ka tafi can...
Yace "Hmm nidai nagane so kake na mutu, saidai bazan mutu ba har saina fara kaika makwafcinka.
Dariya sosai HEESHAM yayi da cewa, "kasha miya da yawa fah... Bai basa amsa ba sakamakwan fitowar da sukayi da ganinsu AUFAN..
HEESHAM da HAIRANAH suna had'a ido tare suka waro idan.. Cikin had'a baki shi yace mata "Keee😳.. Ita kuma tace mai "Kaiiii😳..
HEESHAM yayi murmushi beyi tunanin zai qara had'uwa da ita ba, ya kalli kakan nasa yace, "Baba Alhaji wannan itace yarinyar da nake baka labari, wacce nace maka nasata kuka a kasuwa akan lema😂.. Ya kai ƙarshen zancen nasa da qara wadata fuskarsa da murmushi....




Cikin murmushin jin kunya HAIRANAH ta rufe fuskarta, murmushi Baba Alhaji yayi dake haka suke kiransa dashi, kana yace, "kace min wacce kaci zalinta akan kayanta ba wacce ka tsokana ba, tunda har kuka kasata, da dariya HEESHAM ya dad'a tsaida idansa akanta yace, "Toh kiyi hakuri dan bazan sake ba.
Babah Alhaji yace "kai d'in...
murmushi HAIRANAH da cewa, "Toh na hakura amma dan Baba Alhaji..
Murmushi AUFAN yayi da cewa, "Toh madallah, Sannan ya gaisar da Baba Alhajin HAIRANAH ma ta gaishesa, Sannan HEESHAM ya gaisar da AUFAN..
Cikin damuwa AUFAN ya gayama Baba Alhaji dama Aure yake san ya d'aura masa shi da HAIRANAH, Baba Alhaji yayi shuru can yace mai Toh ya bari sai anyi sallah idan suka idar sai suyi magana, AUFAN yace mai to ba damuwa, Baba Alhaji ya kalli HEESHAM yace yakai HAIRANAH cikin gida idan suka idar da sallah ya kirata, Toh HEESHAM yace mai cikin ladabi, kana ya kalli HAIRANAH dayi mata nuni tabiyosa...
Aiko bayansa tabi, wani gida taga ya shiga da ita ba nisa tsakaninsa da masallacin, babban gidane me kyan fasali, tsarin gidan ya burgeta matuƙa...
HEESHAM ya kalleta ganin yanda take kallan gidan yayi murmushi da cewa, "ƙarema gidan kallo dakyau gidan yankan kai ne😏, ina shiga dake d'akin tsohuwar car za'a fille miki kai..😀
HAIRANAH tayi dariya tace, "Duk rashin wayona dai nafi yayata NUWAIRA😆, idan haka ne nan gidan yankan kai ne meyasa kai basu yanke maka naka kan ba.
Yace saboda ni sun sanni..
Bata bashi amsa ba ganin sun iso shashin Hajjiya Sa'adatu, wata tsohuwace yar duma duma me kyen fasali, kallo d'aya HAIRANAH tayi mata gabanta ya fad'i ganin tsantsar kamar da tayi da mama mahaifiyarsu..😌

_HAIRANAH bata san cewa kakarta bace, bata san cewa itace mahaifiyar Mamanta ba, bata san cewa HEESHAM yaro ne ga ummar Yayan mamanta ba, bata san cewa tsowan da ayanzu suka rabu dashi wanda zai d'aura musu Aure ita da AUFAN bata san cewa mahaifine ga mamanta ba._

Cikin murmushi HEESHAM yace, "tsohuwa ga bak'uwa inji Baba Alhaji, yace kiji da ita sosai idan ba haka ba tam...
Tayi murmushi gabanta na fad'uwa dan HAIRANAH tayi mata kama da Y'arta Lubabatu a fuzge haka, sai tace, "idan ba haka ba me, yace "idan ba haka ba yayo miki kishiya, tunda waccen ta kusa dake tatafi, murmushi ta qarayi, Son da take ma HEESHAM na musamman ne acikin jikokin nata, tace "Aini na tare gaba na tare baya, duk wacce zatazo Saidai tabiyo bayana, dan haka bani babu damuwa..
HEESHAM yayi dariya yace, Shikenan tunda haka kikace, idan kin kula da ita Toh idan baki kula da ita ba nidai koda wata tashigo sanadin hakan a shashinta zan tare, dan nasan wacce take sanshi fara Sol san kowa in wanda ya rasa, kuma kinsanni da san farar mace..
Dariya itama tayi sosai tace, "Toh ai bazan bari akaiga hakan ba, duk wacce ta kwace min ai nashiga garari, kaduba yanda nake tararrayarka mana, zanji da ita sosai kacemai yanda kakawota haka zakazo ka d'auketa....
HEESHAM ya tashi da murmushi da niyar ficcewa dan jin ana kiran sallah yana kuma cewa, "kinji tsoro kenan, sha kurumin kakata takaina dan bame rabaki dani...

HAIRANAH dai sai murmushi takeyi haka kawai taji tana san HEESHAM da tsohuwar, gaskiya sun birgeta matuƙa..
Cikin sanyin murya HAIRANAN ta durƙusa ta gaisar da Hajjiyan..
Hajjiyan ta lumshe ido ba shakka muryarsuma iri d'aya da Lubabatunta..
Nan ta amsa mata da kulawa kana tasa Laure y'ar aikinta takawo mata abin tab'awa...
Bayan tad'an tab'a komai sallah itama tagabatar kana tazauna zaman jiran kiran AUFAN a wayarta..

AUFAN ko cema baba Alhaji yayi bara ya saka wayarsa a caji acikin motarsa, Baba Alhaji yace Toh ya hanzarta dan yanzu za'a kira sallah yazo yayi alwala. AUFAN yace mai Toh sai Baba Alhajin ya koma cikin masallacin..
AUFAN yayi motarsa, gidan baya ya shiga ya kwanta abinsa, dan shi bai iya alwala ba bare azo batun sallah, idan yace zaiyi gangancin farawa dole
DOWNLOAD
DOWNLOAD

Please Login or Register in order to submit comment