Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

d'an futuna haka kad'an, tana da saurin kuka, abu kad'an kayi mata saiya b'ata mata rai tahau kuka, amma Sam bata da ruk'o, kana mata abu kuna yin rikikin anan wajen toya wucce kenan

Tana dakyau sosai..
Dan fuskarta me fad'i ce, me d'auke da d'an hanci wanda shi dai baza'a kirasa dogu ba, kuma baza'a kirasa gajere ba, tana da idanuwa manya masu masifar kyau, wanda idan ta kalleka dasu nan take zakaji qaunarsu takama ka saboda tsabagen kyensu, fuskarta dai tana d'auke da irin wannan kyen da ake kira kyan nutsuwa, ma'ana saika nutsu zaka dinga ganin kyen yana qara fito maka. Sannan fara ce soll kamar ka tab'a jini ya fitto, tana da gashi kasancewar mahaifiyarsu me gashince..

Yayin da NUWAIRA ta kasance Jar mace, irin wannan tsaftacancan farin nan me tsayawa arai, ma'ana batayi fari sol ba, tayi irin farin nan me kyau wanda yawancin mutane suke san irinsa, tana da doguwar fuska, me d'auke da dogwan hanci, idanta masu kyau irin na mejin bacci ɗinnan.
Tana da sanyin murya me tafe da shagwaɓa zallah👌🏻, da wiya kayi zaman awa d'aya da ita baka gane shagwaɓar NUWAIRA ba, dan tafi HAIRANAH shagwaɓa sosai, hakan yasa HAIRANAH rainata take ganin kamar duk abin da takeyi tana yinsa da yarinta.. HAIRANAH takasa fahimtar haka halittarta take, Sannan NUWAIRAN bata da wayo sosai, Sam bata da wani wayo, dan HAIRANAH tafita wayo nesa ba kusa ba, amma dake NUWAIRAN ta girmeta bazai zama akomai bane tafita wayo, dafatan me karatu ya gane...

Haka azahiri da bad'ili dama NUWAIRA tafi HAIRANAH sauqin kai, kuma tafi HAIRANAN tausayi, Sannan bata san taga mutum yana kuka sosai.. Wannan yakan sata jin tausayinsa nan take...

HAIRANAH bata kula samari sosai, danko ta kulaka bazata baka had'in kai ku raya sO ba..
Saɓanin NUWAIRA, NUWAIRA kwata kwata bata kula samari, dan basa gabanta, bazaka tab'a ganinta wai tafito tad'i ba, kuma kullum idan tafitta dawowa take da samari kala kala.
Wannan shine labarinsu..


HAIRANAH dai wannan dare ba abin data iya sai tunanin masoyin nata, wanda bata san sunansa ba, bata san daga ina yake ba, bata san waye shi ba.
Wannan yasa take ta samun NUWAIRA da mutsu mutsu, da NUWAIRAN taga bazata dai barta tayi baccin ba gashi kuma tsakiyar dare ne sai kawai tace mata su tashi suyi lafula..😂
Sam HAIRANAH batayi musu ba, hakan suka tashi sukayo alwala suka hau yin sallah...

Washe gashi bayan sun tashi sun gaisar da iyayen nasu bin Babansu NUWAIRA tayi dan zuwa aiki.
HAIRANAH ko bari tayi sanda tagama aikin gida can kusan qarfe goma sha d'aya saita ficce a bayan idan maman nasu, aiko canta haura saman layin nasu inda tahad'u dashi jiya...
Ga mamakinta nan tagansa jingine jikin motarsa, da mukullin motar a hannunsa yana kwad'awa. Ya had'u sosai, cikin shigarsa ta Riga da Wando, wandon jis ne blue sai rigar tishet ce itama blue, saiya d'aura suwaita akanta, wacce ta sauko masa zuwa gwiwarsa.

HAIRANAH ta sakar mai murmushi, ya mayar mata ahankali, ganin hakan saita zauna kan wani dakalin kofar gidansu wata qawarta Ummi...
Shi kawai ta zubama ido, mamakinta ya kamasa,🤔
Yanda ta zuba masa ido haka shima ya zuba mata, candai dayaga bata da neyar kawar da fuskarta daga kansa saiya d'aga mata gira, murmushi taqara sakar mai, sai kawai ya tawo inda take a hankali ya zauna gefan dakalin da take yace da ita.. "Gaki kyakkyawa dake amma sai kikazo a kurma..
Sunkuyar da kanta tayi da cewa, "ni ba kurma bace..
Cije leb'ansa yayi kad'an alamar muryarta dadad'i👌🏻, kana yace, "tome yasaki zuwa sani'agaba kawai kina kallona..
Kallansa tayi da qarayin murmushi tace, "Ba kawai bane, tukunna ma' meya kawoka layinmu, me kake nema, alamu sun nuna abun da kake nema me matuƙar mahimmanci ne agareka, jiya kazo yauma kaƙara zuwa..
Kallan inda suke yayi, yace haka kawai naji ina san na gaya miki gaskiya, duk da dama ni ba maqaryaci bane, nazo yin kisa ne a layin naku, nazo kashe wani abokin aikina ne...
Dariya HAIRANAH tayi, da d'auke kallanta daga garesa tace, "wannan wasa ne, daga ganinka bakayi kama da masu kisa ba, Sannan baka d'aya daga cikin mugayen mutane..
Murmushi yayi batare daya kalleta ba, yace "Sunana AUFAN, kuma abin dana gaya miki gaskiya ne, dan haka saiki gayamin dalilin dayasa kike kallona, bayan nasan na baki hakuri jiya.
Qara kallansa tayi ido cikin ido tace, "Abin dayasa nake kallanka kawai so nake KA AURE NI, dan tun ganin da namaka jiya Soyayyarka tashigeni da zafi, ban iya qarya ba, Sannan bazan fara daga kanka ba, wallahi sanka da ƙaunarka yayimin mugun kamu, ina sanka kuma ina san ka Aure ni...

Zuba mata ido AUFAN yayi na d'an wani lokaci, kana can yayi murmushi da tashi yace, " Daga ganinki zakiyi gaskiya, babu shakka baki da b'oye abu, hmm idan har kikasan koni waye bazaki qara sona ba..
Hawaye ne ya zubo mata itama tatashi ta kallesa sosai, "wallahi ban iya qarya ba, sanka nake da gaske, kuma duk abin dazan sani akanka bazai tab'a ruguza qaunar da nake maka ba, Allah shiya jarabceni da qaunarka, dan Allah kasoni ko kad'an ne, ka Aure ni kozaka azabtar dani ne, sunana HAIRANAH, zan tafi gida idan har naga kaqi zuwa inda nake kasani sanka da qaunarka ne zasu kasheni, ina sanka da yawa, dan zuciyata ta tabbatar min... Tana gama gaya masa hakan tayi tafiyarta.. Saiya bita da kallo kawai, arayuwarsa ba abin da yake so kamar *GASKIYA* baya san nuqu nuqu a lamarinsa, Sannan baya san ƙarya, idan zakamai ƙarya arayuwa nan take yake jin tsanarka, wannan dalilin yasa yaji ta birgesa, *KARAN FARKO ARAYUWARSA DAYA FARA ZAMA YAYI HIRA DA MACE HAKA ARAYUWA*......

Sunansa AUFAN, kamar yanda ya gayama HAIRANAH, shi bamagujene wato ainihin *HAUSAWA* Lokacin da musulinci yazo Nigeria kakannin kakanninsa basu karb'esa, haka sukaci gaba da bautama gunki suna masu imani dashi ubangijinsu ne, wannan yasa mahaifiyarsa yarda da hakan, saita samu miji wanda shima bai yarda da musulincin ba, shima d'an danginsu ne, tunkan su haifi AUFAN iyayen mahaifiyar AUFAN suka rasu, dama shi mahaifinsa nasa iyaye sun dad'e da rasuwa.
hausawa ne tsantsa, dan ba abin da zaka gaya musu akan hausa, dama sune suka musulinta ayanzu..
Haka sukaci gaba da rayuwasu basu karɓi musulinci ba har suka Aifi AUFAN.
Tun tashin AUFAN yake san yaga mace tana Saka hijabi, haka kawai yaji aransa yana san musulmai, amma bai tab'a kawowa aransa zai zama musulmin ba..
AUFAN d'an gata ne gaba da bayansa, kasancewar iyayensa shi kad'ai suka haifa, suna da kud'i kuma suna sanshi matuƙa kamar yanda shima yake ƙaunarsu, sun Bashi kulawa sosai, musamman ilimin boko..

Sam mata basa gaban AUFAN, bai tab'a tsayawa da mace sunyi hirar minti uku ba ayuwarsa, shi kamar an halacceshi daqin mata ne, idan har ya fahimci kamar kina sanshi, d'aure fuska yake yanda bazaki tunkaresa da maganar son ba..
Ranar dazai fara aiki amatsayinsa na cikakken soja awannan ranar ya rasa iyayensa..
Sakamakwan hatsarin mota da sukayi akan hanyarsu ta zuwa jigawa gun wani kawunsa wanda ya ragema iyayen nasa..
Wannan mutuwa ta hargitsa AUFAN matuƙa, dan aduniya ba abin da yake so kamar iyayensa..
Sanda ya shafe shekara d'aya yana jinyar zuciyarsa...
Yakanje wajen gunkin da iyayen nasa sukasa a Gina musu wai irin ubangijinsu basai sunje wajen ainihin ba, yace mai meyasa ya kashe masa iyayensa, haka zaita tambayarsa amma wannan gunki bazaice mishi qala ba😌, ahaka wata rana ZUCHIYA ta ibi AUFAN yayi rugu rugu da gunkin yace tunda ka kashe iyayena Nima nayi rugu rugu dakai..
Tun daga wannan ranah AUFAN yasan lalle wannan bautar gunkin da iyayensa sukeyi ba ubangijin gaskiya bane..
AUFAN bashi da wani dangi dan kawun nasa daya rage shima haka ya mutu... Bayan yayi gaba da dukiyar da iyayen AUFAN suke dashi, ƙiri ƙiri ya nunama AUFAN wai shiyaba iyayen nasa aro, AUFAN najinsa dan dama yasan san kud'i irin na kawun nasa.
Sam baice masa qala haka ya barsa ya tafi da dukiyar..
AUFAN bai damu ba, dan har alokacin yana cikin jin zafin rabuwarsa da iyayen nasa..
Bayan wata biyu yaji kawun nasa ya musu, wai Y'an fashi ne suka shiga gidansa suka kwashe komai na dukiyarsa Sannan suka kasheshi acewar matarsa..
Ko kad'an AUFAN bai damu ba, tunda ya rasa iyayensa kowama ya rasa bazaiji komai ba...

A Lokacin shekarun AUFAN Ashirin da takwas..
Har a Lokacin baya aikin komai sai tunanin iyayensa, yaki zuwa aikinsa sam..
Ahaka yacinye kud'ad'an da suke hannunsa, ya Saida gidansu yasiya wani qarami, nan ma ya kashe sauran kud'in da sukayi sauran, duk wasu kadarori dayasan iyayensa dasu sanda ya cinyesu.
Dama yana da wani aboki Azeez wanda bashi da aikinyi Saidai kullum kagansa da kud'i..
Yana tare AUFAN, dayaga yanzu AUFAN d'in bashi da komai saiya fara basa kud'ad'e, AUFAN baiqi karb'a ba, ahaka ahaka hardai rannan ya tambayi abokin nasa Azeez d'in a ina yake samo kud'i bayan baya aikin komai, sanin halin AUFAN dasan gaskiya yasa Azeez gaya masa Shifa ba wani aiki da yakeyi sai fashi da makami..
Shuru AUFAN yayi mai, bayan kwana biyu AUFAN yace yakaisa gun ogansu, aiko Azeez yakaisa gun ogansu, anan Azeez d'in yaji me AUFAN yake cewa, wai yana san susashi cikin kungiyarsu ta fashi da makami..
Ogan su Azeez yace mai zai iya, yace fiyema da tunaninsa, tunda ya rasa iyayensa bazai tsaya aikata wani abu kyakkyawa arayuwarsa ba....

Lokaci ƙanƙani AUFAN yazama cikakken tantiri a harkar fashi da makami...
Ba qaramin ji dashi ogan nasu yake ba...

Ya saida qaramin gidan daya siya, yasai babba anan cikin garin Abuja, jerin unguwannin manya, a kalla ya kashe rai sama da tamanin arayuwarsa ta fashi da makami.
Wannan shine labarin AUFAN...

Wani a layinsu HAIRANAH ana kiransa da Auwal, yana d'aya daga cikin y'an kungiyarsu AUFAN, lokaci d'aya ya fitto yace da ogansu AUFAN d'in shi dai yabar fashi da makami, yana fadin hakan yabar ungiyar tasu..
Shine ogansu yasa AUFAN ya bishi duk garin dazaije yaje ya kashe shi..
Dama AUFAN yasan a Kano yake, wannan dalilin yasa yazo garin kano kuma yasan unguwar da yake, sai akayi sa'a yagane gidansa alayinsu HAIRANAH yake....
Zuwansa Layin na farko shine jiya, idan me karatu bai manta ba, shine dalilin dayasa har sukaci karo shida HAIRANAH..
Yanzu haka yau yake san kashe Auwal ayau d'in kuma yakeso yabar garin kanon.....
Wannan shine dalilin ganin AUFAN dame karatu yake yi a layinsu HAIRANAH..


Mundawo labari...
**************************************
Akan idan AUFAN HAIRANAH tashiga gidansu yaja numfashi, gaskiyar yarin ta burgeshi matuƙa..
Yana san mutum me gaskiya..
Komawa motarsa yayi da Saka wani fuska akan fuskarsa dan b'oye kama, kana ya fitto daga motar, kai tsaye gidan daya fahimci nan ne gidan Auwal d'in nan ya nufa..
Yasamu megadin gidan yana jin radio, yace mai "Dan Allah kamin magana damai gidan nan. Me gadin yace mai "Toh jirani ina zuwa..

Cikin lokaci qanqani ko Auwal ya fitto yana ganin AUFAN ya ganesa, hankalinsa ko ba qaramin tashi yayi ba, nan dai jiki asanyaye yaba AUFAN hannu da cewa, "Ya akayi kagane inda nake..
AUFAN yayi murmushi yace, "kaima kasan duk Inda kaje indai har nine zan nemoka saina samoka a duk inda kake, da murmushin yaqe Auwal yace "Toh mushiga...

Haka AUFAN yasashi gaba har suka shiga cikin falan gidan, ba kowa a falan dama gidan gabaki d'aya.. hakan yasa AUFAN kallansa gaba da gaba, ya zaro bindigarsa yace, "bani da lokacin b'ata lokaci, oga ne ya turoni na kasheka Auwal..
Murmushi Auwal yayi yace, "nasan idan na tsaya baka hakuri b'atama kaina lokaci zanyi, amma kasani yanda zaka kasheni haka Kaima zai turo a kasheka wata ranah, musamman idan kagane wannan rayuwar da muke ba rayuwa bace, kuma yazo adai dai Lokacin da kakesan kayi Aure kafara tara iyali..
AUFAN yayi murmushi yace, "wayace maka zanyi Aure, Sannan waya gaya mata zanso tara iyali, aa aa, banda ra'ayin hakan sam, Soyayya itace take sawa mutum ya fara tunanin aure, kagani dama ni mata basa gabana bare nayi tunanin Auransu har nakai ga tara iyali, kaga kafad'i kalmominka na qarshe ayanzu dan ina san nacika aikina...
Auwal ya qara yin murmushi dan yasan AUFAN baya komawa baya bai cika aikinsa ba..
Dan haka kallan sama yayi da cewa, la'ilaha'illallah Muhammadun rasululla sallallahu a laiyiwa sallam...
Mutane da dama musulmai wanda AUFAN yake kashewa suna fadin wannan kallamar kuma yana jin wani iri ahaka dai yake cika aikinsa ya bar wajen...
Yanzuma seta bundugarsa yayi akan Auwal d'in ya sakar masa harsashi d'aya babu jin komai aransa, nanko take Auwal ya zube ƙasa matacce...
AUFAN ya ficce daga falan yanama megadin sallama wanda yaketajin gidan radio na Dala yana jin nishad'i...

AUFAN ya koma motarsa da cire wannan fuskar ya zubama k'ofar gidansu HAIRANAH ido na minti d'aya kana ya kunna motarsa yabar layin...




Haka kawai HAIRANAH taji tana jin sanyi aranta, kasancewar ta fad'in masa abin da yake damunta, gashi tasan sunansa, sai murmushi take ita d'aya, itadai anata tunanin zaizo gareta, dan zuciyarta bata tsaya yi mata wasi wasi ba..
Mama ta kalleta cikin kulawa tace, "Naga kina ta farin ciki HAIRANAH, me yake miki dad'i ne yau, murmushi HAIRANAH tayi, tace "Gaskiya ne Mama, ina cikin farin ciki, wani abu ne ya dameni jiya, amma yau nad'anji sauƙinsa kaɗan haka...
Mama ta gyara zama kan taburmarsu tace, "Gaya min wane abu ne haka.
Cikin dariya HAIRANAH tace "Wani abu ne, zan kuma gaya miki amma ba yanzu, dan Allah MAMANA Karki takura min kan dole saina gaya miki.
Shuru mama tayi mata..
Suna zaune a hakan saiga NUWAIRA tadawo bakinta d'auke da sallama, Lokacin ko uku ne na rana...
HAIRANAH tace da ita, "sannu da dawowa Aunty, da murmushi akan fuskar NUWAIRAN bayan ta zauna tace, 'Yauwa sannu...
Mama tatashi takawo mata abinci kana tayi kitchen, ganin hakan HAIRANAH ta matsa kusa da NUWAIRA ta kwashe komai daya shiga tsakaninta da AUFAN tagaya mata...
NUWAIRA tayi shuru tana Addu'a a zuciyarta Allah ya raba y'ar uwar tata da Masifar so..


Da yamma kamar qarfe biyar Layin nasu ya d'auka kan anshiga idan Auwal an kashe sa..
HAIRANAH najin hakan taji gabanta ya fad'a, shuru tayi tana tuna abin da AUFAN ya gaya mata, hankalinta ya tashi matuƙa har sanda NUWAIRA tagane tana cikin wani hali, tace da ita, "ki sauqaqama Kanki HAIRANAH kadda kibari sanshi da ƙaunarsa yasa kirasa nutsuwarki, idan zakaso abu kaso shi kad'an dan kare kanka daga fad'awa mummunar qaddara, haka idan zakaqi abu ana san kaqishi kad'an, dan wata ranah meyuhuwa ya iya zame maka kyakkyawar qaddararka, nasan kinsan da hakan, dan Allah na rok'eki da Allah ki daure ki d'an rage sanshi ko kad'an ne...
"Toh Aunty zan rage, amma dalilin tashin hankali na ayanzu shine na tuna hirar da mukayi ne dashi, inda yake cemin kisa yazo yi layinmu, jin mutuwar Auwal yasa na fad'a tunanin ko abin daya gayamin gaske ne, da gaske daga zuciyarsa yake ba daga fatar bakinsa bane kamar yanda nayi zatoh..
Gaban NUWAIRA ya fad'i, saboda tuno gaya mata hakan da HAIRANAN tayi, cikin murmushi tace, "Yakamata kibi masoyinki da kyakkyawan zato dan kaucewama sharrin shed'an la'ananne, yana so yayi amfani da wannan hirar taku ne dan ya jefa miki wasi wasi a zuciyarki ya hanaki samun nutsuwa, dan haka kada kiyarda da wannan hud'ubar tashi...
Jin hakan da HAIRANAH tayi saiyasata jin sanyi aranta, tare da kauda duk wani mugun tunani akan masoyin nata, Sannan tasa aranta wasa yake mata kamar yanda tad'auki zancen nasa atun farko, wannan yasa tasamu nutsuwa sosai..


Har kwana uku HAIRANAH bataga AUFAN yazo gareta ba, ga ciwan sanshi ya fara damunta da gaske

Abu kamar wasa inji hausawa sukace qaramar magana tazama babba, ciwo ne ya fara kama HAIRANAH ahankali a hankali, abun ajininsu yake, basu iya so ba, idan zasuso abu sanshi suke da gaske, hakan yasa HAIRANAH tasaka AUFAN cikin ranta sosai..
Yau ranar asabar, ya kama kwananta hud'u kenan rabanta dashi. suna zaune a tsakar gida ita da mama, Maman karyawa take HAIRANAN ko tagumi tazuba, Maman nasu tayi mata fad'an duniya kan tagaya mata me yake damunta kasancewar canjin yanayin nata ya fitto fili sosai amma taqi gaya mata, yayinda NUWAIRA take cikin falansu yau batabi babansu zuwa aiki ba, kasancewar bata jin dad'i..
Lokacin ko karfe goma ne na safe, wallahi ba wani abu da HAIRANAH take so ayanzu face ganin AUFAN dajin zazzaqar muryarsa, babu b'ata lokaci nan ta tsinci kanta da jin zafi a zuciyarta, tafiya tai tafiya sai taji tafara numfashi sama sama, abu kamar wasa sai kawai ganinta mama tayi ta jirkice alamar tasume, nan cikin tashin hankali mama tayi kanta tana faɗin, "Ke HAIRANAH ke HAIRANAH, meyake damunki ne, Innalillahi-wa'inna'ilaihirraji'un? mezan gani ni Lubabatu..
NUWAIRA dake kwancen ta fitto tana cewa, "mama me ya faru.. "Ina zan sani NUWAIRA, maza ibo ruwa mu yayyafa mata, mama tabata amsa da faɗin hakan, aiko nan NUWAIRA tasheqa a guje taje ta ibo ruwan suka hau yayyafa mata, Saidai Sam HAIRANAH taqi farfad'owa...
Nan hankalinsu ya tashi mama tace da NUWAIRA su kaita asubiti kawai..
Daidai nan yayansu SABEER ya shigo gidan dan d'aukar wasu takaddunsa daya manta fitarsu d'azu da Baban nasu, nan shima hankali tashe yayi kan HAIRANAN yana cewa, "mama lapia meya sameta haka, cikin damuwa maman tace cemai, "Nima ban sani ba SABEER, nidai naganta ta zabga tagumi, daga bisani kuma naga ta jirkice, temaka mu kaita asibiti dan Allah. "Mama akwai abin dayake damun HAIRANAH, dan ina lura da canjawarta ay'an kwanakin nan... SABEER ya faɗi hakan cikin kulawa da d'aukar HAIRANAN dan kaita motarsa suyi asibitin.

Gaban NUWAIRA ne ya Faɗi, bata san Susan me yake damunta, dan ita harga Allah bataji AUFAN d'in ya shiga ranta ba, dan zuciyarta tana mata wasi wasin qila ba mutumin arziqi bane..
Haka dai sukayi asibitin zuciyoyinsu dadamuwa..

Aiko da sukaje asibitin labari bai canja ba, dan LIKITAN daya dubata ya bada tabbacin damuwa ce tayi mata yawa, da kuma Saka abu arai, babu mamaki ta iya farfad'owa anjima kamar k'arfe biyu..



_____Daidai wannan lokaci AUFAN yana cikin gidansa wanda yake babban gida ne me kyan fasali wanda kallo d'aya zaka mai kaji san gidan ya shigeka nan take, yana can sama wajen barandarsa yana kurb'ar lemun roba me sanyi da sanyaya ZUCHIYA...
Haka kawai yaji gabansa na fad'uwa adaidai wannan lokaci, tunda ya baro garin kano tunanin yarinyar bai barsa ba, ako da yaushe ganin fuskarta me kyen fasali yake tana damun ganinsa, da tunano maganganunta, duk iya qoqarinsa dan yayakice tunaninta abin yaci tura.. ya gane ya fad'a san yarinyar cikin lokaci qanqani kamar yanda itama tafad'a sanshi alokaci qanqanin, yasani ita d'in musulmace, shiko bashima da addinin dazai iya fittowa a yanzu yace mata shine addininsa, abu na farko da yayi tasirin tab'a zuciyarsa kuma yake da tabbacin shine silar dayasa yaji Santa cikin ransa shine GASKIYARTA, yana san mutum me gaskiya..
Qara kurb'an lemun nasa yayi da zaro wayarsa daga cikin ajjihunsa yahau kiran wani abokin aikinsa wanda yake qasa dashi sosai bayan wayar tashiga cemai yayi.. "Jonathan zan turo maka da wani adireshi anan garin kano tunda kana can, ina san ka duba min wata Yarinya me suna HAIRANAH, me takeyi, me yake tafiya akanta, awane hali take, Sannan ka kula sosai dan acikin nayin nasu ne na kashe Auwal, dan haka ka kula sosai.. Jonathan d'in cikin ladabi yace, "Toh oga angama..
Ba b'ata lokaci AUFAN ya tura masa da adireshin yana me lumshe ido da hararo matsalar dazai fuskanta nan gaba..
Ba wanda ya fad'o miki arai sai abokinsa Azeez, nan ya kirasa ta waya ya rok'esa kan yazo yana san magana dashi, babu b'ata lokaci Azeez d'in yazo garesa har zuwa lokacin AUFAN d'in yana nan inda yake..
Suka tafa dayima juna murmushi, Azeez yace "abokina kamar kana da matsala, dan na lura da tunda kadawo daga kano yanayinka ya canja, AUFAN ya qara yin murmushi tare da tashi daga kan kujerar da yake ya dafa hannuwansa kan kyakkyawan qarfan da aka saka a barandar dan qarama wajen kyau, idansa na kallan cikin layin nasu yace da Azeez, "Da gaske akwai matsala, danna na fad'a Soyayya akaro na farko, bayan nayi tunanin bazan tab'a yinta ba arayuwata ba, Azeez sunanta HAIRANAH, na had'u da ita ne a layinsu Auwal, yarinyar me gaskiya ce, Sannan ta kamu da sona irin wannan san da Ake cewa so na bazata, wato baka san da xamansa, haka lokacin dazai shigeka shiga cikin zuciya yake da zafin gaske, dafarko nayi tunanin birgeni tayi da take gaya min, ayanzu ne nagane bawai birgeni tayi ba, aa tana fad'a min ne nima na fad'a ƙaunarta, ina Santa kuma zan Aureta, na kiraka ne nan dan kabani shawara, kasancewar nasan ba'a Aure a ungiyarmu, sai dai kayi iskanci da mata kawai abin babu tsari sam agareni, da nayi zatan kodan ni mata basa gabana ne yasa naga rashin tsarin hakan, Ashe ba haka bane kawai na qamaci hakan ne acikin zuciyata...
Azeez ina san HAIRANAH kuma ina san Auranta nan kusa, ina san kaban shawara dan ita musulmace, ni kuma banda addini, wannan shine kawai maganar...

Jan numfashi Azeez yayi yace, tsayawa tambayarka meyasa kabari hakan har ta faru dakai b'atama kai lokaci ne, Sannan na lura baka damu da abin dazaije ya dawo ba, kawai kana san kacimma burinka ne kawai, hmm hakan yana dakyau, amma idan har kana san kacimma burinka Saidai kayi komai a sirrince ma'ana kadda kabari yarinyar tasan kai ba musulmi bane, Sannan kada kabari oga yasan zaka Aureta, wannan itace shawarar dazan iya baka, idan zan temakeka zan iya yi maka hayan mahaifa way'anda suke musulmai ne, suje Neman maka auran yarinyar..
Da murmushin jin dad'i AUFAN ya juyo ya rungumi Azeez da sumbatar hannunsa yace "gaskiya ina sanka abokina dan kana yimin abin da nake so dayawa.. Tun yanzu ka fara shirinka na baka dama, dan na kwarema yarinyar da yawa, kuma duk iya wiya bazan bari oga yacutar da ita ba...
Murmushi Azeez yayi masa kawai...
Akwai amana tsakaninsu biyun nan matuƙa, sam d'aya bashi da niyar cutar da d'an uwansa, kasancewarsu dukkansu marayu, sun rik'e junansu da gaskiya matuƙa...





HAIRANAH tana cikin wani hali sosai, kwananta d'aya a asibitin amma idan kaganta saikace tayi sati anan, dan ganin yanda ta fad'a lokaci d'aya ga wani fari data qara, gaskiya AUFAN ya shiga ranta sosai, bata da buri a yanzu face ganinsa, ansamu ta farfad'o tun a jiyan amma numfashinta yaqi daidaituwa yanda ake so, wannan yasa hankalin iyayen nasu tashi sosai, musamman NUWAIRA, wacce tasan silar ciwan nata, dake mamansu ce takwana da HAIRANAN hakan yasa da NUWAIRA ta tashi tawowa asibitin yau da safe sanda ta b'ata lokaci sosai awajen da take tunanin anan ne HAIRANAH tagamu da AUFAN, wai duk a tunaninta ko zata gansa, duk da bata sanshi ba, amma yanda take jin zuciyarta da jin tausayin qanwar tata gani take tana ganinsa zata ganesa...
Haka tagama b'ata lokacin nata awajen tanufi asibitin batare data gansan ba..

Kuma yau d'inne Jonathan ya kira AUFAN d'in yake gaya mai yarinyar tana kwance a gadan asubiti, abinkicen da yayi wai ciwan ya kamata ne lokaci d'aya, kuma damuwar wani abu ne yayi mata illa da kuma saka abu arai...
Nan hankalin AUFAN ya tashi, ya duro daga gadansa, kasancewar yana kwance ne, aiko Yana tashi yace da Jonathan d'in ya gayamai awane asubiti take, nan ya gaya masa abitin malam aminu kano ne da qaramai wasu baya nan, AUFAN na ajiye waye ya kira Azeez ya gaya mai yana meci gaba da cewa, "Please d'an uwa, ka temaken ka shirya Yanzu Muje kano, hankalina ya tashi sosai, yanzu na qara tabbatarwa dagaske Santa nake..
Azeez yace, "Oh AUFAN, yaufa muna da operation, idan babu kai babu ni oga zai zargi wani abu, kaje yau ni nasan abun dazancema ogan, kaga daga baya na biyoka ..
Maganar Azeez gaskiya ce dan haka AUFAN baiji haushi ba, nan yace mai ya gane, babu b'ata lokaci nan ya shirya ya nufo kano.
Da yamma bayan ya kama hotel wanka yayi yaci abinci kana ya nufi asibitin, kasancewar har d'akin da take Jonathan ya gaya mai hakan yasa bai wani tsaya tambaya ba, kai tsaye d'akin ya nufa, lokacin ansamu numfashinta ya dawo normal, mama da NUWAIRA ne a d'akin, suna mata sannu, NUWAIRA na b'are mata ayaba, yayin da mama take mata sannu, tana zaune da fullo a bayanta kana dai ganinta kaga Mara lafiya...
Yana tura kofar idansu ya had'u dana juna, ya sakar mata murmushi itama ta mayar masa,

Please Login or Register in order to submit comment