Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Babynta ta ficce batare datace mata qala ba..

Bayan taba motarta wuta sai tahau kiran mijinta Sadeeq, Lokacin ya shigo asibitin AHMAD kenan ko parking baiyi ba yaga kiran nata, sanda yayi parking ya d'auka yana cewa, "ki huta my Luv..
Cikin sauri Khadijan ta katsesa da cewa, "My luv, kasan duk HASEENAH ce taja mana wannan masifar da bala'in, cikin rashin fahimta yace "Bam fahimci me kike magana akai ba, tace "ina nufin HASEENAH ce ta sace AMAAR d'an HEESHAM kuma sun kashesa yanzu nake ji awajen wata Qawata Arfat danaje wanke kan dana gaya maka zani..

Cikin mamaki cikin mamaki yace "what, me kike cewa ne, aikan ta basa amsa idansa ya hango masa HASEENAN ta fitto daga cikin asibitin da alama taje neman HEESHAM ne, qila bata san saiya d'auki sati kafin ya fara zuwa asibitin ba kamar yanda ya gayama AHMAD..

"wallahi da gaske nake maka, Arfat ba maƙaryaciya bace nasan bazata mata qage ba. Kuma kayi tunanin tsoran da NUWAIRA ta nuna akanta a asibiti shekaran jiya.. Khadija takai ƙarshen zancen da sakin wani kukan...
Cikin b'acin rai yace "Is owkie, ki kwantar da hankalinki, kuma karki gayama NUWAIRA bare HEESHAM yaji, dan gata ta fitto daga asibitin YA AHMAD zata shiga motarta, bari nabi bayanta na ritsata..
Khadija tace "Toh, amma ka kula da kanka, dan Allah kadda ka bari tayi maka wani abu, danna tsorata da lamarinta...
"karki damu Matata kidai kulamin da kanku, tace "insha allah yanda kabarmu da safe haka zaka dawo ka tarar damu.
Murmushin yaƙe yayi mata da kashe wayar..

Nan batare da b'ata lokaci ba ya juya kan motarsa yabi bayan HASEENAN wacce take tafiya a hankali.

Wata basuwar unguwa ce tayi, wacce ake kira da marid'i, unguwar ta manyan mutane ce anan kusa da wani gida tayi parking da fittowa daga motar tata, shima Sadeeq daya tsaya ya fitto daga cikin motar tasa ya nufeta ransa a matuƙar b'ace..
Yana zuwa kusa da ita bata ankara ba, ya d'aga hannu ya sharara mata wani shegen mari, ta kallesa a furgice da cewa, "kan uba, me nayi maka da zaka mareni haka..
Yace "Ubanki kika mun, wato ke munafuka annamimiya mara imani da tausayi ko, ki rasa wanda zaki cutar a duniya sai D'an HEESHAM wanda baiyi miki komai a rayuwa ba
Toh ki sa'ni, kin jama kanki bala'in da shine silar ajalinki..

Cikin rashin kunya tace, "Kuskure na farko da kayi arayuwarka Sadeeq shine nasanin wannan sirrin nawa, idan kaga na barka da rayuwarka ka canja min suna daga HASEENAH na koma wata...
Yana k'ok'arin bata amsa sai ganin wata mota baqa yayi ta tsaya a gabansu, wasu mazaje Hud'u suka fitto daga cikin motar..
Kallo d'aya zaka musu kasan ba musulmai bane, babu d'igwan imani a tattare dasu..
HASEENAH tayi dariya taci gaba da cewa, kasan ayau nake san way'annan suje su kashe min HEESHAM, saboda malamina ya tabbatar min da cewa asirina ya kusa tonuwa, shine naga gwara na kashe HEESHAM d'in NUWAIRAN ta rasa nima na rasa da asirina ya tonu nayi ba wan ba qanin, na kira Num na HEESHAM d'in bai d'auka ba, shine Yanzu naje asibitin su danna tabbatar da inda yake na gayama waƴannan mutanan nawa, amma sai nasamu baya nan, wai bazai zo asibitin ba sai bayan sati d'aya.

Wannan dalilin yasa nazo nan mu had'u dasu dan musan me kuma zamuyi, sai kuma gaka, Ashe kana ta following d'ina ban sa'ni ba, toh kasani ka biyoma mutuwarka..

Mamakinta da al'ajabi ne ya kama Sadeeq, dama Ashe matsiyaciya ce bai sa'ni ba... Wannan lamari ya furgitashi matuƙa.
Bai ankara ba yaji tana badama mutanan nata umarnin su kashesa amma a cikin motar sa, takai ƙarshen zancen nata da nuna musu motar tasa, ai ba zato ba tsammani saiji yayi suna hankad'asa, tsabagen mutuwar da jikinsa yayi kasa yi musu musu yayi.

Ya shiga motar tasa yana kallan ikwan Allah, mutum d'aya ne ya shiga motar ya manna mai bundiga a qirjinsa😨 ganin da gaske harbinsa zaiyi sai yayi k'k'arin bige hannunsa, Aiko cikin rashin sa'a Ashe shi a daidai lokacin yama sakar masa harshashin, saidai bai samesa a daidai setin dayaso samunsa ba, amana ya kaucema zuciyar tasa saiya samesa a kafad'arsa..
Amma dake Sadeeq d'in yayi saurin dafe qirjin nasa da kafad'ar sai mutumin yayi tunanin ya samesa a inda ya dace ne, musamman dayaga ya kifa kansa akan matuƙin motar tasa..
Sai kawai ya fitta yana cewa Hajjiya angama miki dashi, HASEENAH tatab'e baki tace "Aikinka yayi kyau, yanzu ga adireshin gidan HEESHAM d'in, ku fakesa dakyau bana san naji mutuwarsa takai gobe, ina san kota halin Yaya ku kashe min shi a yau.
"Baki da matsala HASEENAH, ogansu ya gaya mata hakan dayima yaran nasa nuni dasu tafi... Aiko nan dukkan su suka shige wannan baqar mutar tasu suka bar wajen, itama ba tare da tab'a lokaci ba tayi saurin shiga motarta tabar wajen tana me murmushin yau Dadyn su HEESHAM d'in zaiji mutuwar yaransa biyu, dan an tabbatar mata Mutanan sun iya kisa cikin kwarewa batare da an ganesu ba, haka kawai taji aranta ta yarda dasu...


Sadeeq bai mutu ba kamar yanda sukayi tunani, danne zafin harshashin yayi irin nasu na yara yaran maza, yayi musu lanb'o kamar ya wula, sanda ya tabbatar da tafiyarsu dukkansu kana ya juya kan motarsa cikin karfin hali irin nasu na maza, yana kuma Allah wadai da unguwan nin manya, sai azo ayi kisa a unguwanninsu ba wanda ya sa'ni saboda tsabagen baqin halin ba ruwan wani da wani... ( Rahama Nalele tace ya manta suma tasu unguwar haka take )

Daqer da sid'in goshi Sadeeq ya iya kai kansa asibin AHMAD d'in, kiransa yayi a waya yace mai yafito gasa a harabar asibitin nasa yana buqatar temakwan gaggawa..

Ai AHMAD najin hakan yayi saurin fittowa yana tunanin me kuma ya samesa
Gaskiya hankalinsa ya tashi da ganin halin da yake ciki
Nan ya shiga tambayarsa waya harbesa, me yake faruwa, yace mai sudai yimai abin daya dace kuma karya gayama kowa tukunna, Sannan ya gayama HEESHAM ya nutsuwa a waje d'aya..

Hankalin AHMAD qara tashi yayi, nan dai ya kwalama matemakansa kira suka temaka mai suka shigar dashi ciki..

Ba batun b'ata lokaci kuma suka hau yimai abin daya dace..
Alokacin kam ya riga da ya fitta daga haiyacinsa...

AHMAD dai ya kira Khadija yace tazo asibiti yanzu Sadeeq bashi da lafiya amma karta gayama kowa..
Cikin tashin hankali ta sab'i d'anta sai asibitin..

Lokacin data gane meya faru da mijin nata kuka tasaka hankalinta ya gama tashi, tasan HASEENAH ce tamai haka, danya gaya mata zaibi bayanta, amma bata gayama AHMAD komai ba, tadaiyi shuru taga farfad'owar mijin nata..


Aiko sai bayan Isha'i ya samu kansa, lokacin Khadijan ce take tare dashi, dan haka saiya fara gaya mata abin daya faru..
Tana cikin tsinema HASEENAN AHMAD ya shigo, nanko ba tare da b'ata lokaci ba Sadeeq d'in ya kwashe komai ya shiga gaya mai.





Anan ko da misalin qarfe tara HEESHAM ya saka NUWAIRA a gaba wai suje asibiti ya qara duba lafiyarta, taqi amma ya nace mata, dan zuciyarsa ce ta hanasa hakurin karya bari saita d'auki sati d'ayan daya fad'a kafin yasan meya faru, gwara suje yanzu yaga meya faru, tunda ma dare ne, zaifi bashi abin da yake nema.

Suna shirin fitta daga falan nasu ne wani d'aya daga cikin situritin gidan nasu ya kira HEESHAM d'in awaya Yana gaya mai sunfa kama wasu mutane guda hud'u zuna masu san shiga cikin gidan ta b'arauniyar hanya, kuma daga dukkan alamu kisa suke san aiwatarwa dan gasu da makamansu..
HEESHAM yace "What, gani fitowa bani minti d'aya..
Nan yaja hannun NUWAIRA suka fitto harabar gidan, aiko anan sukaga mutanan, situritin nasa sun sakasu tsugunno da kwace makaman nasu, HEESHAM ya qare masu kallo cikin mamakinsu yace "me suke nema a gida na...
Shuru suka mai. Ganin hakan yasa ya kira y'an sandan nasu da suke ta binkice akan faruwar lamarin nasu yace dasu suzo an kama wasu mutum 4 agidansa suna san shiga ta b'arauniyar hanya..
Ai nan suka ce gasu nan zuwa.

NUWAIRA ta rungumi HEESHAM ta baya tace "Luv sunzo kashe ni ne fah. yace "No Luvly, bana tunanin hakan, tace "Nidai na tsorata da gidan nan, wallahi ina zama ashi ne dan kai my dear..
Yace "Ki kwantar da hankalinki mana my Auntii, ba ina tare dake ba, tace "Nifa bana san na qara yin wani rashi a rayuwata ne, yace "Nima haka Auntiinah, dan haka ki kwantar da hankalinki, zasu fad'i me suke san aikatawa ne..
Shuru NUWAIRA tayi, baifi minti biyar ba saiga y'an sandan sun iso gidan...
HEESHAM yace suyi gaba dasu gobe yaji meya kawosu gidan nasa, yanzu Yana da abin yi.
Toh sukace masa, Sannan ya bud'ema NUWAIRA mota ta shiga shima ya shiga suka bar gidan zuwa asibiti.

HEESHAM yayi mamakin ganin motar AHMAD har lokacin a asibitin, wannan alamace ta nuna yana asibitin bai tafi gida ba, Amma baibi takan yasan meya tsaida shi ba, haka yayi shashin da naqurar dazai ma NUWAIRA aikin nata..
Amma sanda sukaje office d'insa ya canja kaya kana ya buqaci temakwan doctor Emeka sukayi d'akin naqurar..
NUWAIRA batayi musu ba taje ta zauna akan y'ar kujerar da suke buqata.. Dan ita a tunaninta da gaske qara duba lafiyar tata HEESHAM d'in zaiyi, tayi mamakin yanda aka qaqaba mata naqurar, nan kuma ta kashe mata dukkan wani abu me bama jikin nata qarfi ajikin nata, sai kawai tazama kamar idanta biyu kamar kuma tana bacci..
Doctor Emeka yace yayi mata magana akan abin da yake san sa'ni, aiko cikin sauri yace "Luvly, mema ya faru lokacin dana barki a gida keda Ameer kafin a kashesa..
Shuru tayi, tana tunanin meya faru, nan computer tafara aiki, ta fara nunama HEESHAM komai, tun daga lokacin da yake mata magana akan baya san tafiya office yau, har zuwa lokacin dayabar gidan.

HEESHAM naganin hakan yaja kujera ya zauna yana san ganin abun da kuma ya faru gaba.

Watoh shigar NUWAIRA cikin falan nata direct bedroom nata tayi, anan ta kwantar da Ameer ta shiga toilet danyin fitsari, bayan ta fitto ne kawai taga HASEENAH ta danne kan Ameer d'in da fillo tana jin motsinta ta juyo da kallanta gareta, NUWAIRA tabi d'anta da kallo, lokacin rai yayi halinsa, tatabbatar baya motsi kuma daga dukkan alamu ya mutu, nan taji wani abu tun daga tsakiyar kanta ya gangaro zuwa Babban d'anya tsanta na qafa, kan tayi wani motsi HASEENAH ta zare wata kaikaffiyar wuqa daga y'ar jakarta, akan idan NUWAIRAN HASEENAH tasaka ma Ameer wuqar a wiyansa kamar yanda ake yankan rago haka tayi mai yankan ragon, bayan fah ta kashesa da fillo...😨

NUWAIRA gabaki d'aya komai nata d'aukewa yayi kamar yanda ake kawo wutar nefa a kuma d'auke haka komai nata ya d'auke
Tunda take a duniya bata tab'a ganin wannan bala'in ba...

HASEENAH ta sakar mata murmushi tace wannan shine d'aukar fansar dana shirya yi miki akan Auran HEESHAM da kikayi, kuma Wallahi idan kika gayama wani wannan abun daya faru nayi miki rantsuwa da Allah saina kashe HEESHAM kota halin Yaya, idan kuma ban kashesa da hannuna ba zansa a kashe min shi, gwara ki rasa nima na rasa dake ki mallakesa ke kadai..
Sannan bazan bar miki gawar d'an naki ba, zan tafi dashi gun malami na, dan akwai wani aiki dazaiyi min da gawar tasa ne, ki sa'ni ni bala'ice, baza ki tabbatar da hakan ba saikin gayama wani cewar ga abin daya faru.. Kinga hannuna d'auke yake da dafa, kaf jikina ba inda ya nuna fatata bare idan anzo binkice asamu sheda akaina..

Ai NUWAIRA bata tsaya jin qarshen zancikan nata ba, kawai yanke jiki tayi ta fad'i, wannan ne yasa ta kamu da matsalar d'aukewar tunanin kwakwalwa...


HEESHAM da Emaka daskarewa sukayi da ganin HASEENAH ce ta aikata wannan aika aikan..
Duk da su videon basu photo kawai yake ba magana amma sun tabbatar Jan kunne HASEENAN takema NUWAIRAN kafin ta yanke jiki ta fad'in.....

Emeka sai cewa yake "Yeeee jijos, jijos jijos...

HEESHAM sunkuyar da kansa yayi qasa banda ruwan hawaye ba abin da idansa yake yi.
Hankalinsa ya tashi matuƙa da ganin kisan rashin imanin da HASEENAN tama d'an nasa Ameer..

Daidai lokacin AHMAD ya shigo d'akin, danya fitto daga d'akin da Sadeeq yake dan tafiya gidan momy ya zayyane musu abin da Sadeeq ya gaya masa sai kuma yaga motar HEESHAM, yayi mamaki sosai dan haka yayi office d'insa, bai gansa ba, hakan yasa ya fara duba kowane lungu da sak'o na asibitin, duk bai gansa ba shine yayo nan..
Ai ganin NUWAIRA zaune kan kujerar naqurar tasu, ga kuma Emeka ya d'ora hannu aka ga HEESHAM d'in kuma kai a sunkuye, banda zubar hawaye ba abin da idansa keyi, shiyasa gaban AHMAD d'in fad'uwa...

Nan ya zarema NUWAIRA naqurar yayi severn na video d'in.. Ya jata gefe da kujerar jikin bango dan tasamu hutu,
Kana ya saka play d'in videon dan yaga meya gudana ya jefasu cikin wannan halin kuma..

Ai shi kansa AHMAD d'in daya gani daskarewa yayi a tsaye, can yaji jiri na ibansa baisan lokacin daya ja kujera ya zauna ba, Sam kuma baisan hawaye na zuba masa ba sanda yaji Emeka na share masa da cewa, "Hakuri zakuyi AHMAD, dan kuka ba naku bane, kuma gaskiya ne HASEENAH ta cika azzaluma yarinya,
Shuru AHMAD yayi masa...

HEESHAM yayi murmushi da kallan NUWAIRA wacce take baccin gajiya yace, "Nayi tunanin mata basu da mummunan hali irin wannan, Ashe tunani na bai bani gaskiya ba, me zan ma HASEENAH niku a rayuwa na hucce baqin cikin data k'unsa mana ni da matata. Yakai ƙarshen zancen da fashewa da kuka me sauti...





AHMAD ya rungumesa cikin so da ƙauna yake cemai, kayi hakuri ƙanina, gaskiya ne HASEENAH ta aikata aiki mafi muni a rayuwarta, dan tunda nake ban tab'a cin karo da bala'i irin wannan ba, kar kayi kuka me tsayi HEESHAM, kawai ka yarda akwai abin da Allah yake nufi daya yarda hakan ta faru, shiyasan dalilinsa, kaga ko mu bazamu san dalilin nasa ba, wannan yana d'aya daga cikin jarabawarsa gareka, kuma zaka cinye jarabawar, fatana dai ka kwantar da hankalinka, tunda Allahn ya nuna maka komai..
Shuru HEESHAM yayi masa kawai...

Emeka sai gyad'a kai yake yi, haka duk suka d'auki shuru da zubama NUWAIRA ido.. Kamar ko tasan kallanta suke nan a hankali ta bud'e idanta, HEESHAM yayi saurin sakin AHMAD yayi kanta da kama hannunta, yana me cewa, "welcome my Auntii, Sannu kinji, tace "yauwa sannu, nan ya temaka mata tatashi yace "ba inda yake miki ciwo, tace "Komai normal my dear, ba abin da yake damuna..
Yace "masha Allah, tunda haka ne kije mota ki jirani ina zuwa, ta ce "Toh da kallan AHMAD, taci gaba da cewa, "Barka da dare Ya AHMAD. Cikin sanyin jiki ya ce "Barka dai NUWAIRA, ya jikin. Tace "Da sauƙi, yace "Masha Allah.. Saita kalli Emeka zata mai magana yayi saurin ce mata "Sannu Madam, tace "Yauwa sannu, "Allah ya qara lafiya, ta ce "Ameen...

Tana fitta AHMAD ya kalli HEESHAM da cewa "Muje ka duba Sadeeq.. Kafin musan abin daza muyi, "Meya faru dashi. Ya tambaya AHMAD d'in, amma bai basa amsa ba saima maida kallansa ga Emeka yayi da cewa, "please ka maida video d'in fulet Yanzu, dan zamuje mu sakama iyayenmu su gani..
Emeka yace "Toh ba matsala, Allah ya kare gaba.
AHMAD yace "Ameen..

Kana yaja HEESHAM d'in zuwa d'akin da Sadeeq yake.. Aiko cikin mamaki HEESHAM d'in yayi saurin qarasawa garesa yana "Cewa Ya Sadeeq meya sameka haka..
AHMAD yace "Yagano HASEENAH ce duk ta had'a wannan abun, shine tasaka mutananta su kashesa..
Cikin tashin hankali HEESHAM yace "Me kenan, banfa gane me kake fad'a ba YAYAH.
Khadija yaja numfashi da goge hawayenta ta kwashe komai ta gayama HEESHAM d'in, Hawaye ne dai ya wanke masa fuska..
AHMAD yace "Yanzu dare ne HEESHAM, karmu gayama su momy mu bari sai gobe ma gaya musu..
Sadeeq yace "tabbas hakan shine ya dace, Sannan dan Allah HEESHAM ka kwantar da hankalinka, bama san ciwan ka ya dawo, ka rungumi wannan qaddarar da hannu biyu dan Allah..
Murmushin yaqe kawai HEESHAM d'in yayi mai da tashi yace "Toni zan tafi saida safenku. Gyad'a mai kai kawai sukayi ya ficce, Sannan shima AHMAD yama Sadeeq Saida safe da nufar gun Emeka dan ya karb'i fulet CD d'in tunanin NUWAIRAN..


Ahankali HEESHAM yake tuqin motar tasa, NUWAIRA tace "Luvly, wai ya nagan ka haka baka tare da walwalarka ne.. Shuru HEESHAM bai kulata ba, ta qara maimaita mai tambayar tata nan ma bai kulata ba, nan ta shiga kallansa a nutse, saita gane kawai yana tuqi ne amma fa tunaninsa baya tare da ita, ya tafi can wani tunani daban..
Ahankali takai hannunta ga gefan fuskarsa tana cigaba da cewa. Luv, tunanin me kakeyi ne, kodai an sameni da wani ciwan daban ne..
Nan ya kalleta a nutse yace "No Luvly, me kika gani, yakai ƙarshen zancen da sakar mata murmushin yaqe. Tace "Toh ai naga ka shiga wani tunani me zurfi ne, dan Allah ka kwantar da hankalinka.
Murmushi yayi mata kawai batare daya qara ce mata komai ba, ahaka dai har suka iso gidan..
Wajen baccinsu ne ya kalleta yace "Wato my Auntii HASEENAH ce ta kashe mana Ameer da fillo, kuma akan idan ki ta yanka sa da wuqa ko...

Atsorace NUWAIRA tace "Itace ta gaya maka.
Tsaida kallansa sosai yayi akanta da cewa "Ashe akwai abin da zaki iya b'oye min my Auntii, Ashe baki maida ni dake abu d'aya ba, Ashe duk zan cikan da kike min cewar kina min wani so Ashe duk qarya ne..
Hawaye ne ya zubo mata tace "bafa haka bane luv, wallahi bana san na rasaka ne, akan idona ta kashe min yarona kuma ta yanka min shi, bafa jin labarin nayi ba, YA FARU AKAN KAI NAH ne, me zaisa ba zaka fahimce ni ba. Tana zuwa nan a zancen nata ta fashewa da kuka, tare daci gaba da cewa, kuma taja min kunne kan idan na gayama wani abun daya faru wallahi saita kasheka, kaga ko bata rantse min ba nasan zata iya kashe kan, danta gama tsoratar dani al'amuranta, Sannan tace bazata bar min gawar Ameer d'in ba, dan zata kaima malaminta yayi mata wani aiki dashi, naga bala'in da tunda nake a duniya ban tab'a ganinsa ko jinsa a labari ba.
Nan tausayin NUWAIRAN ya kamasa yace da ita, "My Auntii ki fara wayo mana, ki gane ba komai bane ake iya yi maka barazana akansa. wannan wani abu ne fah, wanda ta aikata mafi muni a rayuwa, koda zaki iya b'oyema kowa bai kamata ki tsaya b'oye min ba, dan idan kikace min ga manufarki ni me iya kallan wannan manufar taki ce, dan Allah kimin alƙawari anan gaba bazaki qara b'oye min komai ba, idan kika min hakan nasan kin bani yarda gabaki d'aya ba batun wani tunani..

Kama hannunsa tayi da sambatan sa ta ce, "Nayi maka alƙawarin bani ba b'oye maka komai arayuwarmu, dan Allah ka yafemin rufe maka wannan da nayi.
"Na Yafe miki matata, sannan zan qara gaya miki ina sanki..
Tace "Na sa'ni my dear, nasan kana sona kamar yanda nake sanka..

Murmushi dai yayi mata da gaya mata yanda akayi ya san komai, tayi mamakin wannan naqura, kana ya qara gaya mata da yanda HASEENAN taso kashe Yayan nasa Sadeeq, nan hawaye ya zubo mata, ta ce, Toh yanzu meka shirya yi mata..
"Hmm, Auntii! nayima HASEENAH wata tsana wacce bani san ganinta kwata kwata arayuwata, dan idan naganta ayanzu kai ama can gaba! wallahi zan iya kasheta bazan iya tsayawa jiran ayi mata hukunci ba, wannan yasa zan bar iyayanmu da yayuna suji da lamarin..
NUWAIRA najin hakan ta rungumesa, tace "Yauwa please dan Allah karka shiga hanyar da zata sadaka da HASEENAN, wallahi Luv bani san ganinta bani santa na tsaneta..
"Toh naji ya isa haka, ya fadin mata hakan yana me nemo number na AHMAD, wanda lokacin kusan sha biyu ne saura, kuma shigarsa gidansa kenan, dan bayan ya karb'i fulet CD din a hannun Emeka zama yayi a motarsa ya dinga tunani ya Saka wannan ya kunce wannan duk akan HASEENAH, sanda yaga kiran wayar MEENATU Sannan ya ankare ashe dare yana yi, bai d'auki wayar tata ba, dan haka kawai yaji kamar tsanarta ta fara kamasa tunda tazo a y'ar uwa ga HASEENAH wacce yake ganin aduk duniya ba macen daya tsana kamarta, hakan yasa data damesa da kiran kawai saiya maida wayar tasa silent.. Duk da yaga miss call d'in HAIRANAH itama baibi ta kanta ba ya d'auko hanyar yowa gidan nasa...
Shine yanzu da yake parking yaga kuma kiran wayar HEESHAM, nan ya d'auka, sai HEESHAM d'in yaja numfashi dace mai, "Kar na dameka Yaya. yace "No, karka damu, akwai wata damuwar ne.
"Eh, yanzu NUWAIRA take gaya min wai Ashe malaminta HASEENAN takaima gawar Ameer..
"Gud gwara daka gaya min hakan a yanzu, Zanyi wani binkice, kaidai ka kwantar da hankalinka...
Yace "Toh Yayah,ka tashi lafiya.. "Allah yasa..
HEESHAM najin hakan ya kashe wayar tasa..


Alokacin kuma AHMAD ya kira Baba Alhaji yace mai akwai matsala, dan Allah ya kira mitin yanzu a had'u gobe da misalin qarfe goma..
Babah bai tambayesa dalilin gaya mai ba yace mai toh. Dab tunda yaga ya kirasa a wannan daran yasan ba qaramin abu bane ya faru..


Dake ba HAIRANAH bace da AHMAD d'in hakan yasa bai tsaya gaya mata abin daya faru ba, ita dai tagansa cikin yanayin da bata tab'a ganinsa ya dawo dashi ba, har sanda takasa haƙuri dazai bar d'akin nata daya shigo duba lafiyarusu, bayan ya gama gaya mata wani aiki ne ya tsaida shi a asibitin nasu.
Haka dai tace dashi, "my blood akwai abin da yake damunka yau dan naga kamar ba yanda na saba ganinka ka dawo ba.

Murmushin yaqe yayi mata da shafa gefen fuskarta yace "Ba komai my Baby, fatana kiyi bacci cikin kwanciyar hankali, Sannan ki tashi da shiri gobe, dan qarfe goma ina so tayi miki a gidan Baba Alhaji.
Tace "Allah yasa lafiya my blood. Yace "Lau, dan haka ki kwantar da hankalinki..
Murmushi tamai da sakar mai kiss a kumatu tace "Toh Yayana, fatana kaima kayi bacci cikin kwanciyar hankali.
Yace "Nagode my Baby, ki kulamin da kanki da yarinya ta.
Tace "insha Allah yanda ka ganta yanzu tana baccin kwanciyar hankali haka zaka ganta gobe cikin kwanciyar hankali..
"Toh Allah yasa, yana gaya mata hakan ya fitta daga d'akin nata.
Sam zuciyarta taqi barinta cikin kwanciyar hankali, danta sa'ni ba makawa akwai abin da yake damunsa..

Yana yin shashinsa wanka ya fara shiga, bayan ya fitto ya kintsa kansa saiya nufi shashin MEENATU, anan ya sameta a falanta ta zubama TV ido kana dai gani kasan kallan TV kawai takeyi amma tunanin wani abu takeyi daban..
Ya zauna kusa da ita kad'an haka yana danna wayarsa yace "Na d'auka kinyi bacci, tace "bana tunanin Zanyi bacci banga dawowarka ba, bayan kuma nice dakai.
Yace "Gud, ina yarona, tace yayi bacci tuni, amma me yasa kana lafiya na kira wayarka baka d'auka ba..

Maida hankalinsa kanta yayi gabaki d'aya ya kafeta da ido kana yace, "malamin... Sai kuma yayi shuru, tace "malamin mene. Qara shigar da idansa yayi cikin nata, yace "ina nufin acikin malaman HASEENAH wanne takaima gawar Ameer..
Ai nan take gaban MEENATU ya fad'i, tsoro ya bayyana a idanta muraran, cikin sauri, kuma tabi ta dibibice... tace "Ban ga ne a abin da kake fad'a ba, ina nufin ban gane abin da kike tambayata ba.. Takai ƙarshen zancen tana me goge gumin daya tsattsafo mata nan take.

AHMAD yayi murmushin yaƙe dakai hannunsa gefan fuskar ta, nan take taji wani shock yayi ram da ita, yace "kina san cigaba da rayuwa dani..
Da sauri ta d'aga mai kai, yaci gaba da cewa, Toh wane irin so kike min.
Cikin tashin hankali tace "irin san da idan na rabu dakai bazan iya rayuwa ba, dan Allah dan Soyayyarka da Annabi Muhammadu sallallahu-alayyiwassallam kamin rai wallahi nidai ban cutar da NUWAIRA ba, KA RAYU DANI dan qaunar da kakema Allah da Annabi Muhammad, wallahi nacire komai a cikin raina zan zauna da HAIRANAH da zuciya d'aya, takai ƙarshen zancen da fashewa da kuka wiwi...

Yace "my Luv ba kuka nake buqata ba, kawai so nake ki gaya min wane malami ne haka..
Cikin sauri da rikicewa tace "Nasan malamin, tabbas ban zaci haka yake ba, kuma Wallahi

Please Login or Register in order to submit comment