Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

a d'akin yayi mamakin hakan, HASEENAN na ganin hakan ta maida kallanta ga HEESHAM daci gaba da cewa, ina gida Aunty MEENATU ta kirani take gayamin NUWAIRA ta dawo normal, nayi farin ciki sosai da hakan, ina tayaka murna...

HEESHAM jin wani abu yayi tun daga tsakiyar kansa har zuwa Babban d'anya tsansa na k'afa, nan ba tare da b'ata lokaci ba kan nasan ya sara..
NUWAIRA ta leqo da kanta kad'an dan kallan HEESHAM d'in da HASEENAN, aiko tana qara had'a ido da HASEENAN tayi saurin maida kanta bayan Dadyn, tare da sakin wani kuka me fawan gaske, tana cewa "Nace muku bana santa bana san ganinta bana san ganinta....
Ai bata kai ga rufe bakinta ba HEESHAM ya nemi zubewa a qasa, nan cikin sauri AHMAD ya tarosa, cikin kuma tashin hankali HASEENAH tace "Dan Allah HEESHAM karka sume ba tare daka yimin magana ba...

Gabaki d'aya tunanin kowa agun kullewa yayi, gaskiya NUWAIRA a matuƙar tsorace take da HASEENAH, kowa yanzu ya gane HASEENAN NUWAIRAN take nufi ba kowa ba..

MEENATU ko dafe kan nata tayi, dan nata ne kad'ai ya bud'e ta shiga wani tunani daban...









Ina, sam HEESHAM baiji rokwan HASEENAN ba ya sume, Hankalin HASEENAH ba qaramin tashi yayi ba, ganin hankalin kowa ya koma kansa sai hakan ya bata damar ficcewa daga d'akin ran nan nata babu daɗi.

AHMAD ya d'auki HEESHAM yayi wani d'akin dashi, anan yahau basa temakwan gaggawa, hankalin su Dady ya tashi sosai, dan basa san ciwan zuciyansa ya dawo ne.
NUWAIRA dai shuru tayi, yanda kowa yayi jingum jingum yana jiran farfad'owar HEESHAM d'in haka itama tayi..

Baifi minti talatin ba ko ya farfad'o, nan hanakalinsu ya kwanta, AHMAD yace "Ka dawo normal ba matsala zamu iya tafiya gida , yace "Eh, ba wani damuwa.

Nan dukkansu suka rankaya zuwa gidan Baba Alhaji, tambayar duniya anyima NUWAIRA kan tafad'i abin daya faru taqi fad'a yanda ya dace, dan kalma d'aya take gaya musu itace, tunda tashiga toilet ta fitto bata ga Ameer ba, wannan yasa data tabbatar baya nan saceshi akayi shine ta yanke jiki ta fad'a, gaskiya bayan hakan bata san kuma abin daya faru ba, haka da y'an sanda suka zo suka mata tambayar suma amsar data basu kenan...
Kowa ya d'auka gaskiya ne abin data fad'a, dan tana fad'a ne cikin wani hali da kuka, hakan yasa y'an sandar cigaba da gudanar da binkicensu..
Baba Alhaji dai magungunan tsari yabama NUWAIRAN da HEESHAM d'in.
Bayan sun bar gidan nasa sai yayi alwala da gabatar da sallar istihara akan yana san sanin awale hali Ameer d'in yake ciki, aiko shidai an nuna mai Ameer d'in baya raye, bai gaya ma kowa ba, amma zai tsananta Addu'a sosai akan Allah ya baiyana me ya faru kowa ya sa'ni.

Nasaha sosai Momy tayima NUWAIRA ganin yanda hankalinta baya tare da ita..
Haka ma mamanta da babanta harda Dady ma sannan suka bar gidan nata da barin su Ramlat dan sunce su sai anjima zasu bar gidan..

Hannatu tace "ikwan Allah, d'anka a cikin gidanka azo a sace maka shi, Ramlat tace "Ai dole a tsananta binkice dan wannan ba abun a bari bane.
HAIRANAH tace "Nifa naqi yarda da abin da Aunty NUWAIRA tace, kamar akwai abin data sa'ni ta b'oye ta taqi fad'a.
NUWAIRA tayi saurin kallanta da galla mata wata shegiyar harara.
Ramlat taja numfashi da cewa "Toh me hakan yake nufi kenan, me zaisa tayi hakan, tayima kanta da iyayenmu qarya ko me, bayan duk abin da za'ayi bayan jin abin datace d'aukar mataki ne da d'aukar fansa, kina so kice ita d'in bata san hakan ne, bata san ganin ankama waƴanda suka mata Wannan zalincin, bata san ganin farin cikin mijinta da kwanciyar hankalinsa..
Tace "No, ba haka nake nufi ba, ina nufin dole akwai magana a qasa bayan wacce tafad'a, kuma daga dukkan alamu akwai manufarta na b'oyewa, dan kin san qaramin tunani ne da ita, sam ba wayo ne gareta ba ..
NUWAIRA ta qara galla mata harara..
Hannatu tace "Gaskiya banji araina abin data fad'a ba gaskiya bane, dan duk rashin wayanta nasan bazata tab'a yafe wannan mugun abu kota barshi aranta batare data fad'i daidai ba, kai wane ma rashin wayo irin wannan da zai sata yin hakan, duk fa rashin wayan Aunty NUWAIRA da kike fad'i tafa fini, amma ko ni d'in ba zanyi hakan ba, kawai yanzu ba Lokacin tsayawa b'ata lokaci bane, Addu'a zamu Saka a gaba kan Allah ya baiyana komai cikin sauri da kuma sauƙi..
Ramlat tace "Wannan itace magana, dan Allah NUWAIRA ki kwantar da hankalin ki, dan insha Allah zakiga d'anki dan yana hannu nagari... Ramlat takai ƙarshen zancen nata da kallan NUWAIRAN wacce jin qarshen kalaman na Ramlat d'in yasa wani hawaye me zafi ya zubo mata tace, "Wallahi Ameer baya raye, tace "kina da tabbaci akan hakan ne, tace "aa ina nufin naji araina baya raye...
HAIRANAH tace "Hmm, Allah ya bayyana gaskiya..
Hannatu tace ameen..


Haka suka dinga bama NUWAIRA baki da kwantar mata da hankali kana suka bar gidan.


HEESHAM yana tare da AHMAD da Sadeeq, suna tare da y'an sanda.
Inda y'an sandan suke qara tabbatar musu cewa zasu tsananta binkice a cikin wannan satin, tunda sunji ta bakin NUWAIRAN..
Godiya AHMAD ya musu suka bar wajensu.

Direct gidan momy AHMAD ya juya da kan motarsa, sukaje suka qara tattauna lamarin, sai bayan sallar isha'i bayan sunyi AHMAD d'in ya kuma d'aukar HEESHAM dan kaisa gidansa.

Ahankali ya kalli HEESHAM d'in yace "tun tuni muna ta magana ina san na tambayeka Me kaji aranka adangane da labarin da NUWAIRA tabayar a gidan Baba Alhaji.
HEESHAM yaja numfashi da murmushi akan fuskarsa yace "Sai yau naji araina Ameer baya raye, aduk inda yake shi matacce ne, Sannan ko kad'an ban yarda da abin da NUWAIRA tace ba, dan nafi kowa sanin wacece ita, ni da ita mun dad'e da zamowa abu d'aya YAYANA, magana ta gaskiya itace, da tsoro a idanta lokacin da take bada labarin, Sannan ka lura ta kafe akan bada amsa d'aya, aduk lokacin da akace mata ta kwantar da hankalinta Ameer yana raye Allah zai baiyana shi cewa take baya raye
Sam bata bada wata
Alama dazata nuna maka cewa d'anta yana raye ba, dukkan alamo min tana nunasu ne akan d'anta baya raye, wallahi ko laffara bazanyi ba YAYAH tasan komai daya faru, fad'a dai baza tayi ba dan wani udiri nata.

AHMAD yaja numfashi yace "Tabbas haka ne, kaje ka lallab'ata a gida zata gaya maka komai, idan bata gaya maka ba kakaita asibiti, wannan dai naqurar da muka fitar da ita itace zata qara bamu abin da muke nema ma ayanzu..
Cikin farin ciki HEESHAM ya sakar mai kiss a Hannu yace "Sai yanzu na tuna da hakan YAYANA, idan har bata gaya min ba, sati d'aya zan bata dan samun Hutunta sai muje na caji tunanin nata..
AHMAD ya tsaida motar tashi a daidai kofar gidan HEESHAM d'in yana cewa "toh, kadai kula da kanka sosai, Sannan ka d'ora idanka akan HASEENAH da alama bata da gaskiya, duk da kaga na bama y'an sandan labari akanta, amma yana da kyau ka k'ara d'ora ido akanta sosai.
"Toh YAYANA Nagode, ka huta tare da kulawar Aunty HAIRANAH.
Yace "Wato ba MEENATU ba ko, nina rasa me tayi muku baku Santa, gashi tana da kirki sosai, HEESHAM yace "hakane, tana da kirki daidai nata, kawai dai ni bana shiri da ita ne. Haka kawai naji HAIRANAH tafi kwanta min arai, kayi hakuri, ina nufin bawai bana yinta gabaki d'aya bane, tana da kirki daidai nata. Yana gama gaya mai hakan ya fitta daga motar da sakar mai murmushi kana ya shiga gidan nasa.

Sai AHMAD d'in ya girgiza kansa dajan motar tasa..


HEESHAM shiga falan NUWAIRA yayi da y'ar wak'arsa fuskar nan tasa cike da murmushi, kallo d'aya NUWAIRA tamai tasan yana cikin farin ciki, nan ranta yayi mata baqiqirin, wato sun rasa d'ansu, amma ya shigo da waqa kuma cikin farin ciki, aciki taja tsaki, ya jita sarai sai yawani yi kamar bai jita ba, ya kalleta cikin so da qauna, tayi mai kyau sosai, tana zaune ne akan kujera mecin mutum biyu, cikin shigarta ta doguwar riga me launin bula, batayi make-up ba amma sai ƙamshi takeyi, da alama yanzu tayi wankan ta gyara kan nata.
Yaje ya zauna kusa da ita yana cewa "Wow.. kyau haka my Auntii, kin ganki kuwa, kamar wata amarya ba wacce tatab'a aihuwa ba.
fusace tace "Kadena wannan zancen, dubeka dan Allah, baka san inda d'anka yake ba, amma har kana da damar sakin ranka cikin nishaɗi haka.
Yace "Haba Luvly, kina so nata rayuwa cikin k'unci da baqin ciki ne, kai😨 ina bazan iya hakan ba, nimafa naji araina kamar yanda kike ji aranki Ameer ya mutu, direct yanzu haka yana makarantar Annabi Ibrahim, toh me zaisa nabar kaina cikin k'unci da baqin ciki, kinga nifa na dena wannan yayin, y'an sandan ma masu yin binkice akan lamarin nace musu su dena wahalar da kansu, binkicen ya isa haka, dan tunda kika tabbatar kina fitowa daga toilet ne kika nemesa kika rasa nace "Aljanune suka d'aukesa, ba b'ata lokaci kuma suka kashesa tunda sunbar mana alama, ina nufin sun bar mana jinin sa, wannan yasa nace kawai abar wani binkici akan lamarin, danna yafema ma aljanun mah, tunda Allah nasan mutum me yafiya, bare kuma Ameer da bamuyi wata shak'uwa sosai dashi ba, kinga ki share kawai mu qara qoqarin samun wani... Yakai ƙarshen zancen nasa dasan kai hannunsa kan fuskarta..
Aiko cikin sauri da kuma b'acin rai tabuge hannunsa, wani kuka yazo mata me tafe da ciwo tace "Ashe dama ba sona kake ba, Ashe dama duk Soyayyar da kake ikirarin kana ma Ameer d'in taqarya ce.
Tashi HEESHAM yayi da wani shegen murmushi yace "Hmm, nidai bazan hanaki kukanki ba, kitayi, idan kika gaji kika gama anjima na dawo muyi bacci dan gaskiya agajiye nake... Yana gama gaya mata hakan yayi shashinsa..

Aiko kuka sosai NUWAIRA tayi, bata d'auki lokaci ba kuma tafara tunanin kodai ta gaya mai gaskiya ne, nan wata zuciyar tace mata baki da hankali, ki gaya mai shima ki rasa shi..
Haka taci gaba da kukanta kuma tasan yana jinta amma Sam yaqi kulata, haka tayi bedroom nata, ta canja kaya zuwa na bacci kana ta kwanta tana qara tuno komai a ranta..
Tana cikin wannan halin ne taji wayar ta na ringin, tana dubawa taga HEESHAM d'in ne, qin d'auka tayi, saiya qara kira, shima taqi d'auka, ya kuma kiran, anan ta d'auka da cewa "Menene, yace "Normal mana Luvly, kin gama kukan ne..
Shuru tayi mai, jin hakan yasa yaci gaba dacewa, ina buqatarki yanzu a d'akina, tace "Bazan zo ba.
Yayi murmushi da cewa, "Gud.. Ba abin dazai hanani kiran HASEENAH acikin wannan daran tazo room naki tayaki hira, musamman nan da qarfe goma sha d'aya.. Yana fadin mata hakan ya kashe wayar tasa da murmushi..

Aiko NUWAIRA najin hakan ta diro daga gadanta, nan tahau waige waige agigice, yanzu tagane ko sunan HASEENAN aka ambata tsoro kamata yakeyi, Sam bata san ta isa bedroom d'in nasa ba, sanda ta ganta a tsakiyar room d'in, Sannan tasan tabaro room d'inta..
Nan ta haye gadan nasa da fad'awa jikinsa ta fashe da wani kuka me tsuma zuciya..
Nan ya rungumeta sosai, cikin Soyayya, cikin Soyayyarta, ƙaunarta, cikin ƙaunarta, cikin muradi, ina nufin muradinta, me tafe da tausayinta, dan yasan koma me ta bari a cikin ran nata bame dad'i bane..
Nan ya fara lashe mata hawayen yana me sakar mata qananun kiss masu motso wasu abubuwa irin na masoya, ta cikin kunnanta yace "Gayamin my Auntii, kinfa san ni me sanki ne, me qaunarki ne, me san dukkan farin cikin ki ne, me shagaltuwa akan dukkan al'amuranki ne, dan Allah ki qara nunama duniya kina sona, ki gaya min meya faru da Yarona..
Cikin shash sheqa tace "nima ban ban sa ni ba..
Yace "owkie, toh is owkie, ki kwantar da hankalinki, meyasa kike jin tsoran HASEENAH.
Ai tana jin ya amfaci HASEENAN ta qara qanqamesa da b'oye fuskarta a qirjinsa cikin tsoro cikin tsoro tace, Kawai ni bana santa bana san ganinta bana san a dinga ambatan sunanta bana santa mijina, idan na ganta ji nake kamar zan mutu, dan Allah karka bari ta qara zuwa inda nake. Yace "Toh ki kwantar da hankalin ki, bazata qara zuwa inda kike ba..
Shuru tamai da qara maqalesa..
Shima shurun yayi da fad'awa tunani.🤔





AHMAD ko safa da marwa yaje ya tadda HAIRANAH nayi, itace dashi ayau, ta kwantar da Baby Ummi akan kujera da alama bacci tayi, Sam bata san ya shigo falan nata ba, dan magana Kawai take ita kad'ai..
Fad'i take, "Ba gaskiya bane labarin da kike bamu Aunty NUWAIRA, wallahi ba gaskiya bane, haka Kawai naji araina ba gaskiya bane, dan inda gaskiya ne tunda yamma dana dawo ya dace nadena sambatu, me yasa kike jin tsoran HASEENAH, me tayi miki kike jin tsoran ta, meya gudana tsakaninku daya haifar miki da hakan, bana san wani ya cutar min dake y'ar uwata, danke ba ruwanki da rayuwar kowa.. Kai` wai zancen ma me nakeyi ne, kawai na kira HEESHAM mu buga wani wasa mana, ina san mu san gaskiyar abin daya faru kota halin ya-ya.. Takai qarshen zancen nata da juyowa dan neman wayarta, Kawai sai tsintar kanta tayi a jikinsa, AHMAD ya rungumeta runguma wacce take tafe da ƙauna zallah, cikin mamaki zata mai magana ya saka mata d'anyatsansa d'aya a baki, alamar baya san tace mai komai..

Jan numfashi tayi da saka kanta a qirjinsa batare da tace komai d'in ba..




Wannan dare dai Sam NUWAIRA bata bar HEESHAM ya sake ba, danta saka tsoro a ranta da gaske, tana jin yad'anyi motsi zata qara qanqamesa, lokacin yin sallarsa na dare nayi tare suka tashi suka gabatar, suna idarwa kuwa ta kuma matsawa garesa..


Washe gari tare suka had'a breakfast, suna cikin ci ne tace "Dan Allah Luv karka barni ni kad'ai a gidan nan, yace "tsoran me kike ne my Auntii. Tace "Kawai bana san hakan ne. Yace "Masu gadinki mutum shidda ne Luvly, kuma a yanda kika yarda da Allah nasan bazai barki haka ba, ki nemi kariyarsa ki cire tsoran gidanki ki samu nutsuwa da kwanciyar hankali please, duk da ba inda zani, ba inda zani yau da gobe da jibi ma, amma ina san ki cire wannan tsoran aranki bana sanshi.
Hawaye ne ya zubo mata, ta share da bayan hannunta, saiya ajiye cokalin dake hannunsa ya d'ago da hab'arta yaci gaba da cewa, na dena takuraki akan sai kin gaya min ainiyin abin daya faru, dan nasan koma menene yayi miki zafi sosai da kuma tsoratar dake, hakan yasa na janye ra'ayina nasan lalle saikin gaya min, ayanzu samun nutsuwarki nake nema my Auntii, dan Allah kiji tausayina ki bani farin ciki ki tsaida tunaninki akan abin daya dace, ki watsar da abin da bashi da amfani agareki, kidena futunar zuciyata wajan jefa mata tunani barkatai nasamu nutsuwa dan Allah. Ya kai ƙarshen zancen da manna kanta a qirjinsa cikin matuƙar santa da ƙaunarta.
Aiko ckin kuka sosai tace "Wallahi labarin dana bayar bana gaskiya bane, kuma wallahi bazan tab'a fad'an gaskiya ba, dan anja min kunne akan idan na fad'a sai an kasheka, bana san nayi bawan ba qanin, wannan yasa bazan iya gayama kowa ba, dan Allah ka yarda dani, dan naqi fad'a ne dan bana so na rasaka...
HEESHAM najin haka ya d'ago da fuskarta ya sakar mata kiss a baki yace "Nagode sosai da qaunar da kike min, amma ki tabbatar min da zancen da zuciyata ke gaya min tun jiya, ki tsaida min da tunani na ki gaya min Ameer yana raye koya mutu.

*"YA MUTU..* shine amsar data bashi cikin sauri, sanda ya rintse idansa bai bud'e ba yace "Kuma akan idanki komai ya faru ko, maida kanta kan qirjinsa tayi da D'aga mai kai...

Shuru HEESHAM yayi, nan gabansa ya d'auki bugawa, dake kanta yana kan qirjin nasa har yanzu, nan taji yanda yake bugawan, ta d'ago da sauri ta kallesa, lokacin ya bud'e idan nasa, sai yayi qarfin halin sakar mata murmushi, zuciya cike da wani burki taccen tunani...

"Karki damu da bugawar da zuciyata keyi, ina lafiya lau my Auntii, Nagode da sanar dani hakan da kikayi, yace mata hakan yana me shafa fuskarta..
Murmushi tayi da cewa, "Sai muyi shuru karmu gayama kowa mu yafe ko, kaga sai Allah ya dubemu ya qara bamu wani cikin sauri ko.

Murmushin yaƙe yayi mata, _gaskiya idan baki koyi wayo yanzu ba bazaki tab'a yinsa ba my Auntii_ ya fad'i hakan a ransa, afili ko cewa yayi "hakane my Auntii, muta Addu'a Allah ya bamu wanin.
Jin amsar daya bata sai yasa ta maida kan nata kan qirjinsa, zuciya cike da yarda da amsar daya batan...

Sanda ya sama mata nutsuwa, ya tabbatar tasake, dan har abincin rana sanda sukayi, suka gabatar da sallar Azahar, kana ya fitta yabar gidan, ce mata yayi zashi asibiti amma yanzu zai dawo, amma a zahiri gidansu HASEENAH yayi..


Yanda kwanaki yayi parking na motarsa a ƙofar gidan nasu, haka ma yanzu yayi, babu b'ata lokaci nan yahau kiranta a wayarsa...

Lokacin suna tare gabaki d'ayansu, wato MEENATU da mamyn nasu da HASEENAN, sun sakata a gaba kan saita gaya musu gaskiyar meke tsakaninta da NUWAIRA, su basu yarda da labarin data basu a baya ba, banda haka me zaisa daga ganinta NUWAIRA ta tsorata..
Gyara zama HASEENAN tayi ta basu labarin daya gigitasu, magana wannan kasa yi mata sukayi, kawai sai suka zuba mata ido, musamman momynsu, tayi imani bata haifi y'ar datayota sak ba kamar HASEENAN.
Suna cikin hakan ne kiran wayar HEESHAM ya shigo wayarta.. Tana ganin hakan taji gabanta ya wani tsinke ya fad'i, a hankali ta d'auki wayar da cewa, "Amincen Allah ya tabbata agareka, yace "Tare dake, ina kofar gidanku, ina buqatar ganinki cikin sauri. "Toh gani nan zuwa. Ta fad'in masa hakan da kashe wayar tana me fad'awa tunanin kodai malamin nata yayi saurin yi mata wani aiki akansa ne, nan dai tazari gyalanta da feshe jikinta da wani shegen turare me tsadar gaske.
Saidai tana zuwa wajensa ya kauda fuskarsa alamar baiji dad'in ƙamshin ba.
kamar ta cinkata daidai tace "Ƙamshin bai maka ba ko, yace "Kiyi mamakin hakan kawai, musamman idan kikayi duba da yanda turaransa yake da tsad'a, yakai ƙarshen zancen dajan tsaki, kallo d'aya zaka mai kasan yaji takaicin b'ata lokacin nasa wajen bata amsar tambayar tata, duk da ko bame dad'i ya gaya mata ba, haka dai yaci gaba dace mata... Hakan bashi da wani mahimmanci agareni, kawai nazo ne naji dalilin dayasa kika dasama Matata tsoranki aranta...
Bayan ada bata jin tsoranki, abin mamaki ne sosai ta tsinci kanta cikin hakan batare dana zargeki ba.
Tace "Ayya, abin mamaki, wai da gaske ni HASEENAH NUWAIRA take jin tsoro, tatab'e baki dace gaba da cewa, hmm umm gaskiya bakai ba wani ma idan yazo wuccewa yaji hakan dole ya zargeni, amma abu me mahimmanci anan, mezai hana ta gaya maka dalilin dayasa take jin tsoron nawa, tunda ni dai bani da masaniya akan hakan, kuma b'ata lokaci ne kazo kana tuhumata fa, Sannan abin kunya ne agareka matarka taqi gaya maka gaskiya akan wani abu da kake nema ta barka cikin gararin neman gaskiyar agun wacce bata da hakki akan hakan, nidai ban san meyasa NUWAIRA jin tsorona ba, nifa ayanzu nama fara zargin akwai wani abu da take san kullamin saboda tsabar qiyayyar da take min, musamman idan nayi duba da yanda Y'an sanda jiya sukazo suka hankad'a qeyata zuwa wajensu, tare da yimin wasu tambayoyi kamar nice na sace mata d'anta, duk da na yafe hakan da aka mun jiyan amma hakan bai isheku ba sanda yau kai kuma kazo gareni da wani saban salo, toh gaskiya bazan iya d'auka ba, karka qara zuwa gareni da wannan maganar...

HEESHAM yayi murmushi dasan matsawa kusa da ita, kamar ta ankare ta fara ja da baya da baya, shi ko bai dena matsawa gareta ba, har sanda takai can jikin bango, kana yakai hannunsa kan fuskarta ya fara zagare fuskar tata yana cewa... "Idan nagane cewa dasa hannunki akan b'acewar Yarona wallahi ba abin dazai hanani d'aukar wani mummunan mataki akanki wanda baki tab'a jin irinsa akaf tahirin rayuwarki ba..
Yana gama gaya mata hakan ya sakar mata wani shegen murmushi da juyawa zuwa motarsa yana meci gaba da cewa, daga wannan ranar zaki gane Ashe kallona kike daga nesa, Sam baki san waye Muhammad HEESHAM a kusa ba.. Yana kaiwa nan ya bama motarsa wuta..

Ai ganin tafiyarsa yasa HASEENAH sauke ajiyar zuciya, zuciyar cike da wani tunani.

Koda ta koma cikin gidan nasu samun MEENATU tayi tasaka d'anta a baya da alama tafiya gida zatayi, ta kalli HASEENAN tace, "HEESHAM ne yazo yaja miki kunne ko..
Tace "Ya akayi kika sa'ni, tace "hmm, yanayin da kika shigo dashi shiya sanar min da hakan, zan gaya miki wata gaskiya, ki gudu Gana wajen wannan qawar taki, dan rikicinki da HEESHAM ba qaramin abu bane, dan nayi imani HEESHAM zai iya yi miki komai akan wannan lamarin..

"Bafa inda zani, danni ba matsoraciya bace, kuma akan cikar burina zan iya yin komai, kika sani ko yanzu aka fara wasan..
Momynsu tace "Dakyau yarinya ta, insha Allah baki ba samun matsala akan dukkan cikar burikan ki, MEENATU tace "hmm, Allah yasa dai kar kin buga game over tun daga yanzu.
Tace "bani ba buga game over har abada..
Murmushi MEENATU tayi da barin gidan batare data qara ce mata komai ba....




Washe gari da misalin qarfe biyu Khadija matar Sadeeq taje shagwan Arfat me gyaran jiki danta wanke mata kanta, dake shagwan nata irin na yara yaran mata ne, komai na buqata akwaisa a shagwan, dama labarai ne suke kallo a makeken TV d'inta, sai kawai aka sako cikiyar neman Ameer, ga hotansa dana HEESHAM..
Arfat ta girgiza kai da cewa, "HASEENAH ko bala'i, shegiya dan rashin imani tasara me zatayi arayuwarta sai cutar da wannan d'an yaran dabaiji ba bai gani ba...
Ai Khadija najin hakan ta d'ago da kanta ta kalli Arfat tace "Subhanallah, kina nufin HASEENAH ce ta aika wannan aika aikan..
Cikin tsoro Arfat tace "Kinsan HASEENAN ne ko kina da dangantaka da NUWAIRA ne, cikin wayo da dabara Khadija tace "aa ban san wata NUWAIRA ba, amma nasan HASEENAH farin sa'ni, kuma kullum gaya mata nake tarage mugunta da bak'in hali amma sam bataji.. Ki duba yanzu abin data aikata, fisabidillahi me zataje ta gayama Allah akan wannan zunufi me girma data aikata..
Arfat ta sauke ajiyar zuciya da cewa, "Wallahi har hankalina ya tashi, cewa nake ko ke y'ar uwar NUWAIRA ce kije ki fad'a mata kijamin bala'i, duk da bala'ina yafi na HASEENAN amma dole ayanzu naji tsoranta, dan wannan abun data aikata ba duk d'a bane zai iya aikatawa..
Khadija tace "aini ban tab'a ganin mugunta da baqin hali irin wannan ba..

Arfat tace "nima haka, kin san ai ana kwana biyu da faruwar lamarin aka baza a gidajen radio da TV duk tashar da kika kama zancen kenan da akeyi, wannan yasa datazo nan na wanke mata kai aka sako kiciyar sai naga ta kyalkyale da dariya tace Saini HASEENAH, wa ya isa yaja dani, banda ni wazaiyi hakan...
Jin wannan Kalmar tata yasa kwakwalwata tashiga tunani, nan natuno tabbas wannan HEESHAM ne wanda kullum take yawan magana akansa zata Aura shine yayi missing d'in yaransa.. Dan tana nuna min hotansa da nata tace min sun dace da juna ko, nakan kuma bata amsa da cewa Eh.
Cike dasan tatabbatar min da zargina nace mata, Ha'a, wannan ai saurayin nan naki ne aka nuno, kaddai ya samu baby ne kika rabasa da Babyn da barinsu cikin nema, kinsan dake tasan bansan kowa nata dana NUWAIRAN ba shiyasa ta cemin, Eh, kema ai shedace akan san da nake masa, amma yayi burus da Soyayyata, Hmmm kedai abar kaza a cikin gashinta, yaransu ne dai baya raye sai naga abun da zasuyi..

Wallahi Khadija ina jin hakan naji tsoranta ya kamani, danni duk abuna bazan iya kisa ba..

Hawaye ne me zafi ya zuboma Khadija, cikin kuka sosai tace "Allah ya isa, Allah ya isamma HEESHAM da NUWAIRA, wallahi HASEENAH baza kiyi mutuwar mutunci ba..
Arfat tace "Kiyi hakuri Khadija, kuma karki gayama kowa dan bana so kijamin bala'i.
Tashi Khadija tayi, kan nata bai gama bushewa ba, ta yafa gyalanta, kana ta zuge jakarta taciro kud'inta ta bata Sannan ta d'auki

Please Login or Register in order to submit comment