Join Our WhatsApp Group

Idan ku ka ga kun taba wani wuri ya fitar daku a shafinmu, sai ku danna back kuyo baya, ku sani yanzu muna amfani da tallan Popunder a shafin, so karatu zai muku dan wahala, amma ta hakanne kadai zamu iya cigaba da rike shafinnan. idan har bakwa son talla sai kuje ku yi subscription na shafinnan akan karamin kudi ku runga downloading kawai. SUBSCRIBE


DOWNLOAD

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register
DOWNLOAD

ko ka manta hakan ne, ai munyi jinyar wani wanda shima ya fuskanci matsala irin tata anan asibitin kafin dawowar HEESHAM daga karatu ka tuna, shi ba wanda yake yarda dashi sai kai, kasancewar yana farkawa kai ya fara gani,
yace "Ina sane, Saidai nasa matsalar ai bakai nata ba, danshi d'auke war tunani ne kawai.. Gaskiya ne NUWAIRA bata da wanda ta sani ayanzu sai HEESHAM...

Kowa jinjina kai yayi awajen, wato Allah me iko, _ba wanda tasani ayanzu sai HEESHAM_ Kalmar da kowa yake fad'i aransa kenan.

"Kina jin yunwa, HEESHAM ya gaya mata hakan cikin sanyin murya, ahankali ta kallesa da d'aga mai kai, nan ya karb'i tia d'in na hannun momy zai zare hannunsa daga gunta ta qara qanqamesa, nan yabar hakan da yake niyar yi, ya gyara ya shiga bata kad'an kad'an.
Ahankali take zuqa a cokalin idan ta had'a ido dasu momy sai tayi saurin kawar da kallanta daga kan nasu.





Haka fah NUWAIRA tazama kamar wata yarinya, sati d'aya ta qara a asibitin ta koma gida, amma gidan momy ta koma, dan momy tace HEESHAM d'in ya barta na Wata biyu ta koya mata abubuwa, irinsu sallah wacce take da babban mahimmanci arayuwar kowane musulmi wanda a asibitin ma ta fara iyawa, da kuma iya gyara kai da dai sauransu..



MEENATU dai jikinta yayi sanyi, idan me karatu bai manta ba, zuwa wajen bokanta baifi da kwana uku ba wannan lamari ya faru da NUWAIRA, nan ta zargi y'ar uwarta HASEENAH da aikata hakan, taje gidansu tana jinjina rashin imani irin nata, dan ita fad'i kawai take kan zata iya kashe HAIRANAH amma Sam matsoraciyace akan hakan, gaskiya b'atan Ameer ya girgizata ainun, Sannan kanta ya Kulle🤔 lokacin da HASEENAH take tabbatar mata da cewa ita ba itace silar jefa NUWAIRAN cikin wannan hali ba, tayi musu rantsuwa ita da momynsu kan bata aikatama NUWAIRA komai ba, bata b'atar mata da d'a ba...
MEENATU dai datayi tunanin tayi tunanin sai taga kodai HASEENAN dan taga hankalinsu ya tashi ne yasata qin gaya musu itace tayi hakan, dan sun santa da shegen wayo, musamman da momyn nasu da tabama MEENATU labarin ana washe gari abun zai faru HASEENAH bata kwana a gida ba...
Sam bata kwana a gida ba, kuma da garin ya waye sai gab magrib tadawo gidan....

Wannan yasa MEENATU cikin rud'u ta kuma qi yarda da HASEENAN, ta kuma qi komawa wajen bokan da qawarta Halima takaita, ta dai d'an dakata taga ikwan Allah kafin ta d'ora aya, idan kuma Allah ya shiryeta ( Rahama nalele da sauran dukkan musulmai suna tayata murna )

Wannan shine abin daya faru agidansu MEENATU





Sam NUWAIRA bata yarda da kowa sai HEESHAM, tare sukeyin komai, danya tare a gidan momy, yana taya momyn kula da ita, ayanzu NUWAIRAN ta fara d'an yarda da momyn, tunda taga HEESHAM d'in yana sakewa da ita.
Kuma tana magana, dan idan ya fitta daga gidan duk abin da Momy tayi saita kwashe ta gaya mai idan ya dawo.

Momy da Dadynsa najinta, hakan yake sawa momyn take zubda hawaye, irin wai yau NUWAIRA ce ta dawo haka, Sam tamanta dasu, ba wanda ta d'auka da wani mahimmanci a rayuwarta sai HEESHAM, kamar tasan miji ne a gareta.

Shima HEESHAM d'in kuka yake yi sosai idan yana kallanta..
Haka zata matso garesa tata share masa hawayen tana tayasa kukan daga kuma bisani ta kwantar da kanta ko akan cinyarsa ko a kafaɗarsa tayi shuru irin tana jin tausayin san nan,😒 dan tasan ko'a gaya mata ba yana kuka ne akan wani abu dayake damunsa.


Ramlat da Hannatu kusan kullum qafarsu na gidan momy, hankalinsu ba qaramin tashi yayi ba da lamarin, suna san NUWAIRA sosai bare kuma d'an uwan nasu HEESHAM, sundai yarda a gidan nasu ba wanda sukafi qauna kamarsa..

Dama shi yasan da zaman hakan, dan haka yake qara sansu sosai aran nasa..




A wata uku NUWAIRAN ta iya komai a yanzu.
Bata wasa da lokacin sallah, ga san gaye.
AHMAD yabama momy shawarar tasa HEESHAM ya koma da NUWAIRAN gidansa, hakan zai temaka wata rana ta iya tuna abin daya faru da ita agidan., kawai dai a Saka masu tsaran gidan yana ganin insha Allah ba wani mugun abu dazai qara faruwa da izinin Allah.
Momy ta yarda da shawarar AHMAD d'in, dan haka tagayama HEESHAM yace dama shima yana da wannan tunanin..
Kwana biyu tsakani suka koma gidansu..
Idan NUWAIRA na kallan hotunan Ameer bata jin komai, dan bata san waye shi ba, amma tana shiga tunani idan taga HEESHAM na kuka idan yana kallan hotansa..


Kamar yau, ya dawo daga office bayan yayi wanka yaci abinci kawai sai ya zauna ya Saka hotan Ameer a gaba yana ta kallo yana hawaye, tabbas yasan qaddara bawai bai santa ba, amma yaran ya shiga ransa sosai...
Ahankali ta shigo d'akin nasa ganin ta gaji da zaman jiransa a falo, ta zauna kusa dashi sosai batare datace dashi qala ba, can dataga bai da alamar dena hawayen sai tashiga share masa tana cewa, "My Luv, ya dace a matsayina na wacce ka tabbatar min cewar ni mata ce a gareka ya dace ka gaya min matsayin wannan yaran agunka, ta kai qarshen zancen itama hawaye na zubo mata..
HEESHAM yayi murmushi kad'an da sakar mata kiss a daidai setin bakinta yace, "Yaro na ne, ina san shi sosai, saidai ayanzu ban san Awane hali yake ciki ba, tace "ban gane ba, Yace "sace min shi akayi, kinga ko ban san ko ya mutu ko yana raye ban sa'ni ba.
Tace "Toh kadena kuka insha Allah bai mutu ba zai kasance a hannu na gari, yace "Allah yasa.
Shigewa jikinsa tayi da cewa abin, sai ya bita da kallo irin ya dai tabbata ta manta da komai na rayuwarta..

Shidai me lafiya ne ba mara lafiya ba, bai tab'a yarda namijin Aure zai kalli matarsa kusan watanni takwas ko tara batare daya nemeta da Soyayyar Aure na aikata aikin lada ba, amma yanzu ya yarda dan tun da wannan abin ya same shi bai tab'a neman NUWAIRAN ba, gashi d'aki d'aya suke kwana tun a gidan momy, yanda suka kwanda haka zasu tashi, Sam ayanzu baya buqatar wata Soyayya, yanzu abin da yake gabansa shine Addu'a kan Allah ya dawo da hankalinta jikinta ta warwarema kowa abin daya faru.


HAIRANAH ma kullum cikin kuka da damuwa take, ta qara dagewa wajen kaima Allah kukanta, rokwanta yafi karkata akan NUWAIRA, tana fatan ya dawo mata da hankalinta aji wai meya faru ne, hakama Ramlat da Hannatu.
Iyayensu ko ba'a magana, dan sosai suke Addu'a akan lamarin..

Haka ma AHMAD, yana Addu'a yana kuma bibiyar manyan likitocin duniya akan matsalar NUWAIRAN...



Shima fa gogan HEESHAM bafa a zaune yake ba, dan shima bin manyan likitoci yake yi.
Kullum fatansa Allah yasa yaci tuntub'e da abin dazai kawo masa warwarewar matsalar cikin sauƙi











Wannan dai naqurar da HEESHAM d'in yake san siyama AHMAD wacce yake ikirarin zaiyi mai bazatanta, itace wacce zata temaka wajen gano abin daya faru da NUWAIRA har ya kaita ga tsintar kanta cikin wannan yanayi,

Lumshe ido HEESHAM yayi dayaci karo da bayanan da wani Babban doctor dayayi masa, gaskiya daba dan kar ace yayi qarya ba, da cewa zaiyi bai tab'a tsintar kansa cikin farin ciki irin na wannan lokaci ba, nan take ya ture laptop d'in tasa data basa bayanan, ya kalli NUWAIRAN wacce take ta damunsa da futuna wai Saidai ya tashi suje yawo, kuma bai wani dad'e da dawowa daga office ba, yanzu haka ma qarfe tara ne na daren.

Murmushi ya sakar mata ganin ta b'ata fuska, yace "Auntii fushin na miye, tace "idan kana tare da wannan laptop d'in taka baka kulani, duk maganar dazan maka baka jina, yanzu ma ka kulani ne dan kagama abin da kakeyi..

Kasancewar yana kwance ne akan bed nasa, ita kuma tana zaune gefan bed d'in, ta zubama masa ido da laptop d'in tasa, hakan yasa ya ware mata hannuwansa cikin so da ƙaunarta, dama hakan take so, wato ta shiga jikinsa, tana jin daɗin hakan sosai, dan haka da sauri ta fad'a jikin nasa tana dariya, idansa cikin nata yahau shafa bakin yana cewa "Yau ina cikin farin ciki my Auntii, ina san mu raya luv yau, gaskiya nayi missing d'inki. Sosai..
Sam bata gane me yake nufi ba, sanda ya faro mata wasa, nan jijiyoyin kanta suka tashi, irin sun fara amsar sakwan da suka dad'e rabansu dashi.
Gaskiya sun tsinki kansu cikin farin ciki sosai, HEESHAM ya samu nutsuwar daya dace ya sameta tuntuni.. Ba ƙarya ya ƙara san matarsa da ƙaunarta, nata kan abayyane yake, dan yasan bata da abin so a duniya sama dashi, haka washe gari yanda suke bama junansu kulawa ya zarce na kullum, dan ji suke kamar su cinye kansu da dan ƙauna..

Daqer dai HEESHAM yabar gidan, kuma kai tsare wajen wani abokin Dadynsa yaje wani Babban doctor ya gaya mai buqatarsa nasan yana so ya mallaki wannan naqura a cikin satin nan, yace mai toh ba damuwa zai samu kawai dai damuwar ta kud'i ce, HEESHAM dai ya tabbatar mai zai had'a kud'in nan da kwana biyu, yace mai toh karya damu yanzu zaiyi waya akan a turo da ita..


Haka a kwana biyun ya had'a kud'in, kuma ya kai masa..

Kwana shidda tsakani ko abokin Dadyn nasa ya tuto mai da nak'urar..
Dama HEESHAM ya tanadi inda za'a sakata anan cikin asibitin nasu inda ya dace da ita, dan haka kai tsaye ajiyeta akayi awajen..

Gaskiya ba ƙaramin daɗi AHMAD yaji ba da ganin bazatan qanin nasa, dama shima yanzu shirye shiryen san mallakar baqurar yake, dan shima ya samu sanin itace silar da zata dawoma da NUWAIRA hankalinta idan Allah ya yarda..
HEESHAM dai yaji dad'in ganin farin cikin Yayan nasa, haka Momy da Dadynsu sun taya AHMAD d'in murna.
Nan kan kace me har gidajen TV sun fara hasko asibitin AHMAD d'in suna masu nunama mutane ayanzu ba abin da babu na aiki a asibitin, duk wanda yake kai yaransa waje dan ayi musu aiki to ya dena ga Sauqi ya samu har gida..

Kwana uku tsakani HEESHAM Ya gayama iyayen nasu gobe zaikai NUWAIRA asibitin dan naqurar ta fara aiki akanta, suna buqatar Addu'a akan Allah yasa sudace..
Duk fata na gari suka musu, mamansu NUWAIRAN harda kukan dad'i, gani take insha Allah qarshen matsalar tazo kenan...







Washe gari kallo d'aya za kama HAIRANAH kasan tana cikin farin ciki, ta kwana jiya sallar dare ita da AHMAD suna masu rokwamma NUWAIRAN waraka Allah yasa a dace, gani take har NUWAIRAN ta dawo normal, AHMAD yace
"Baby yau sai farin ciki kike, da alama akwai wani abu da yake miki dad'i, tace "Bafa komai my blood, kawai dai inaji a jikina kamar yau zaku samu nasara akan aikin da zakuma Aunty NUWAIRA ne, yace "Gud, insha Allah zamu samu nasara, hakan Nima nakeji araina. Yakai qarshen zancen nasa da sakar mata kiss, ya kuma sakarma Ummi dake hannunsa kana ya miqa mata ita yana cigaba da cewa, "ki kula min da dukkan ku.
Sakar mai murmushi tayi da d'aga mai hannu, saiya shiga motarsa cikin so da ƙaunart.

MEENATU ta sauke labulanta tana mejan tsaki, haka kawai ta d'orama kanta aiki, kullum idan ya kasance girkin HAIRANAH ne tazo rakosa mota saita musu lek'e, wanda bata san ita suke bari da aiki ba, dan ita idan ta rako AHMAD d'in Sam HAIRANAH bata mata lek'e, dan tasan idan ta d'aukar ma kanta hakan ba k'aramin É—orama kanta damuwa tayi ba, wannan yasa yana shiga duba lafiyarta bata yarda ta qara hangensa daga nesa..



Suko suna dining suna breakfast, HEESHAM ya kalli NUWAIRAN yace "My Auntii, tace "Na'am my luv, yace "Yau tare zamuje asibiti fah, tayi murmushi da tsaida kallanta akansa tace "toni amfanin me zan maka my Luv, imba zama kawai zanyi nata kallan mutane ba..
Yace "no, zamu duba lafiyarki ne, tace "toh ni me yake damuna, yace "Ke rayuwata ce, ba abin da nake so aduniya kamar ki, wannan yaran da nake kuka akansa ke kika Haifa min shi my Auntii, kwata kwata yanzu bazaki iya tuna komai ba, fatana dai kibani had'in kai muyi miki abin daya dace...

Cikin mamaki, cikin mamaki tace "Ni kuma, ni d'in Nina Haifa maka wancen yaran, tayaya! kuma a yaushe ni ban sa'ni ba, wai me kake san gaya min ne.
Yace "kinsan dai bazan miki ƙarya ba, qarewa ma cewa kikayi yaushe aka d'auki hotan bikin Auran mu baki sa'ni ba, kullum tambayar da kike min kenan amma kinga ban baki amsarki ba, wannan itace amsar taki, munyi rayuwa me dad'i tsakanina dake, bana san yawan magana a Yanzu kawai ki d'auko hijab d'inki muje ayi miki abun daya dace..
Tace "toh, indai had'in kaina kake buqata nabaka shi tun da dad'ewa, dan bayan hango qaunata da nakeyi a kawar idanka har a gangar jikinka bayyana take, nidai nayi sa'a dana sameka a matsayin mijin Aure na, Nagode ma Allah sosai.
Yace "Allah abin godiya..

Tare suka tashi taje ta d'auko hijab d'inta, shiya karb'a ya Saka mata, sanda suka karanta ayatul kursum sannan suka bar gidan.
Mutum shida ne bayan me gadin dame bama fulayoyi ruwa masu tsaran gidan a yanzu, koda su NUWAIRAN suna nan ko basa nan.



Da murmushi HEESHAM yake gaisar da iyayen nasu da Baba Alhaji, dan sun rigasu isa asibitin, momy kawai NUWAIRA tagaisar da murmushi akan fuskarta amma banda su mamanta dasu Dady, HAIRANAH dasu Ramlat ko ko kallo basu isheta ba, ita fa tsoran mutane take ayanzu, ba wanda tasani take hira dashi kamar HEESHAM.



Nan dai aka shiga da ita d'akin da za'a mata aikin, AHMAD da doctor Emeka da doctor Anas ne da HEESHAM d'in ne zasu mata aikin, doctors had'u kenan a kanta, ko nace uku, dan HEESHAM nasa aikin gareta kad'an ne...

Nan dai suka sakata cikin wata kwalba, bayan ta canja kaya zuwa na asibitin, suka kunna ma kanta wata farar wuta, tare da qaqaba mata wasu wayoyi a jikin kanta.. Ko wacce waya da sanin da kowanne acikinsu ya mata, kowacce da abin da zata basu ma'ana da aikinta, wannan yasa dukkansu suke kanta da jiran amsar da kowacce wayar zata basu asanin dako wannansu ya mata.
Nan suka umarci HEESHAM daya fara mata hirar data gudana tsakaninsa da ita a ranar da abin zai faru.

HEESHAM ya kalleta a cikin kwalbar, idanta a rufe yake kamar me bacci sai dai ba baccin take ba, Sam bata san awata duniya take ba, dan duk maganar daza a mata zata iya amsawa idan kuma tambayarta ake wani abu zata iya shuru tayi tunanin abun ta kuma bada amsa akansa..

Nan HEESHAM ya fara cewa.. "Luv yau bana san zuwa office kwata kwata, haka kawai naji bana san barinki. Dan ban san me yasa nake jin gabana na faÉ—uwa ba, bana san abin dazai tab'amin lafiyarki, wallahi NUWAIRA ina sanki ina MASIFAR sanki... Yana kawo nan a zancen nasa ya tsaya da maganar tare da zuba mata ido.

Shuru NUWAIRA tayi batayi magana ba, nan zuciyar HEESHAM ta karye, hawaye ya zubo masa, dan tuna indai bata basa amsar data basa awancan lokacin ba, ba yuhuwar zata dawo normal kamar yanda ayanzu suke mata fata..

Doctor Emeka ya dafa kafaÉ—arsa, dayi masa nuni akan kar yayi kuka me sauti.. AHMAD ya gyad'a masa kai akan da gaske kar yayi hakan, Nanko ya d'auke hawayen nasa, yana gogesa ne, naqurar tad'auki Reading, tana sacin tunanin NUWAIRAN, tana me bata temakwan ta nasan tatuno da hirar da sukayi da HEESHAM d'in...
Aiko cikin wani hali tace "Haka kawai na tsinci kaina cikin faÉ—uwar gaba jin waÆ´annan kalmomin naka, dan Allah Luv karka barni, wallahi idan ka barni bazan tab'a iya rayuwa ba.
Nan farin ciki ya kama HEESHAM, ya qara matsawa kusa da ita yace, wannan hawayen na miye my Auntii, baki san naji zafinsu har cikin raina ba...
Tace kawai kamin alƙawarin baka ba barina aduk halin dana tsinci kaina..
Cikin sauke ajiyar zuciya yace "Nayi miki alƙawarin bazan tab'a barin ki ba luv aduk halin da zaki shiga ina tare dake, bani ba barinki har iya qarshen rayuwa, amma idan kikaci amanata! Da gaske zan barki da Allah ne kawai yamin sakayya...
Tace "bani bacin amanarka, Allah yamin tsari da hakan akan komai wanda ya kasance mallakinka ne, idan nayi maka wani abu kayafe min Luvly...
Yace "Na yafe miki matata, fatana ki qara sona.
Tace "dama ai ni'ce na faro, nayi maka alƙawarin insha Allah ba wata Soyayyar wani abu da zata qara shiga raina, daga ta iyayenmu saita y'an uwanmu, dan Allah ka yarda da san da nake maka da gaske bashi da iyaka agareni..
Yace "Na yarda.
Tace "Amma yau baka ba zuwa office ko.
Yace "Naso hakan, amma tunda mukayi waÆ´annan kalaman nad'an samu qarfi a zuciyata...
Tace "baka tab'a kaiwa tara a gida ba.
Yace "Sai lokacin da nake ango ko.
Murmushi NUWAIRA tayi a hakan, mamaki ya kama HEESHAM, danya tuna jin kunyar data kamata awancen lokacin.. Nan yaci gaba da cewa, Luv, ya dace a yanzu ki gama gane halin mijinki, tace "wallahi ba wanda yafini saninka a yanzu, yace "Toh murmushin na miye, (acan yace mata toh jin kunyar na miye, ayanzu kuma ya canja ne dan aikin nasu yafi tafiya yanda yake so)
Tace "kawai na sabo ne..
Jin dad'i ya kama HEESHAM. Dan itama ta canja abu d'aya, ( kawai ta sabo ne shine abin datace a wancan lokacin, sab'anin yanzu datace kawai na sabo ne ).

Yace "Owkie zanyi maganinki kuwa..
Aiko cikin sauri tace "Dan Allah kayi hakuri... Nasan maganinka da futuna yake.
Shuru HEESHAM yayi, Sam bata gaya mai hakan a wancan lokacin ba, tsarin kalmomin ma ba haka suke ba, nan yayi tunanin yanzu haka ma qila tana ganin komai a idanta..
Dan haka ahankali kamar meyi mata rad'a yace "Gaya min my Auntii..
Tace "me zai gaya maka Luv, yace "Bayan fittata zuwa office meya faru, wayazo ya tafin mana da Ameer...

Shuru NUWAIRA masa da fad'awa tunani, can tace "bayan futanka, bana kuma falona ba, sai naji ina jin fitsari, hakan yasa na kwatar da Ameer a bed, sai tayi shuru kamar me tunani, zuwa can kuma sai taci gaba da cewa, ina fittowa daga toilet sai sai sai sai nagansa a hannun.... Ai bata qarasa ba jikinta yahau wani jijjiga cikin sauri AHMAD da Emeka da Anas suka zare mata dukkan wayoyin da suke aiki akan natan, tare da maida hankalinsu kan kwamfiyutan dake manne jikin bangwan d'akin..

Nan batare da b'ata lokaci ba ta had'a musu bayanan komai, tayi musu congratulations na dawowar tunanin nata...

HEESHAM na ganin hakan ya rungume Anas da Emeka yana murnar dad'i, suma cikin murnar suke qara rungumesa..
Sanda ya samu nutsuwa ya rungumi AHMAD wanda shima sai murmushin jin daÉ—i yake.

Nan kuma hankalinsu ya koma kanta, suka hau bata temakwan daya dace, dan bata gama dawowa hankalinta ba, amma idan tayi bacci ta farfad'o komai normal yake agunta...

Haka matemakansu suka kai NUWAIRAN d'akin hutu..
Cikin murna AHMAD yake gaya ma su momy tunaninta ya dawo, Saidai a saurari farfad'owarta, ko nan da awa uku ko hud'u ko fiye da hakan

Godiya ma Allah kowa agun yahau yi, HAIRANAH sai murmushi take, MEENATU ko shuru tayi batace qala ba... Kawai jira take taga ikwan Allah...
Tunda HASEENAH tace ba itace silar jefata cikin wannan hali ba, dan haka zata sO taga wanda ya jefa ta, amma kafin nan bara dai ta kira HASEENAN ta gaya mata dawowar tunanin NUWAIRAN, ba b'ata lokaci ta lalubo numbar tata tahau kiranta, kamar yanda su Ramlat suke ta waya da y'an uwa suna gaya musu dawowar tunanin nata



Awa uku da rabi da minti hud'u NUWAIRA ta farfad'o, kuma stiil akan idan HEESHAM ta farfad'o...
Suna had'a ido yace "Sannu Luvly kin tashi lafiya, saita d'aga mai kai da cewa "zan sha ruwa..
Nan cikin sauri ya tasar da ita da jingina mata fillo a bayanta kana yahau tsiyaya mata ruwan a kofi zai bata su momy suka shigo..
Kad'an tasha ruwan, mamanta tahau yi mata sannu, ta'amsa ko cikin kulawa tana sakar ma su Hannatu murmushi.. Sannan tahau amsa sannun dasu Dady da Babanta da Baba Alhaji suke mata...
Can d'akin ya d'auki shuru, bame magana, ganin hakan yasa NUWAIRAN kallan AHMAD tace "Ya AHMAD meya sameni aka kawoni asibiti..
Yace "kin manta meya kawoki ko..
Shuru tayi da fad'awa tunani🤔🤔🤔 can saita zaro ido, tare da ture d'an bargwan da aka lullub'e mata k'afarta dashi tata tsaye tare da dafe kanta tana cewa, "Innalillahi-wa'inna'ilaihirraji'un, Innalillahi-wa'inna'ilaihirraji'un Innalillahi-wa'inna'ilaihirraji'un, Wayyo Ameer, Wayyo Allah, Wayyo Allahna menayi daka jarabceni da ganin wannan bala'i... Takai ƙarshen zancen da rushewa da kuka me qarfin gaske, kukan da jin farko daka mai zaka san akai ciwo a cikinsa...
Dan har wani jiri ne yake qoqarin ibanta bata sa'ni ba...

Nan HEESHAM yayi saurin kama hannunta ya zaunar da ita da durkusawa a gabanta yana cewa, "ki nutsu ki dena wannan kukan ki gaya mana meya faru, dan ba wanda yasan abin daya faru anan, kuma ba wanda yasan inda Ameer yake saike..
Cikin kuka sosai wanda tunda NUWAIRA tazo duniya bata tab'a yin irinsa ba tace, "Nima ban san abin daya faru ba...
"Kan uba😨 shine abin da HEESHAM yace mata cikin tsawa... Aiko nan tsoronsa ya kamata, dan bai tab'a yi mata irin wannan tsawar ba, cikin in i na tace "dana kwantar dashi akan gado na shiga toilet dana fitto shine ban gansa ba...
Ai a fusace HEESHAM ya saki hannunta da tashi tsaye yace "Qarye kikeyi, wallahi koki gaya min inda d'ana yake kona d'auki mummunan mataki akanki...

Murmushi AHMAD yayi, dan koda tak'i fad'a na banza ne, wannan naqurar dai itace za'a qara maida ita cikin ta itace zata qara basu abin da suke nema ayanzu, dan zata bud'e mutu tunanin NUWAIRAN ne inda kasan ka Saka kaset a CD kana kalla haka zata nuna maka komai bazata b'oye maka ba, Saidai in ba'asa mutum a cikinta an qaqaba masa wayoyin jikinta ba, amma muddin akayi hakan kuma aka fara ma mutum tambayoyi akan abin da ake so ya fad'a ko abin da ake so a gani nan take zata baka komai, abin daya sa ma tun farko bata nuna musu hotan video na tunanin nata ba basu Saka da hakan bane tun da farkon, dan ba'a so acaji kwakwalwar tata gabaki d'aya a lokaci d'aya, hakan zai iya haifar da bugawar kwakwalwar tata, amma tunda yanzu an samu d'aya za'a iya maida ita aga na biyu...
Tuno hakan yasa AHMAD d'in jan HEESHAM kusa dashi tunda shi ya manta da hakan, cikin lallami yake cemai "Kwantar da hankalinki HEESHAM, tunda ta dawo normal dole zata fad'i abin daya faru, koda taqi fad'a za muga komai.

NUWAIRA ta kalli AHMAD d'in dake wannan maganar, kana ta fara tunanin me fad'ar tata zata haifar, dan ajan kunnan da aka mata idan tafad'i abin daya faru zatayi d'a kwance uba kwance, irin dai ba wan ba qanin, dan gaskiya ita taga bala'in da tunda take a duniya bata tab'a ganin irinsa ba..

Babah Alhaji yaja numfashi yace "Ka kwantar da hankalinka HEESHAM kamar yanda AHMAD ya FaÉ—in maka, ke NUWAIRA ki tsaida hankalinki waje guda ki gaya mana meke faruwa...
Ahankali ta kalli Baba Alhajin tace "Wallahi komai ya faru, naga bala'i daban tab'a jin labarinsa ba, ban tab'a gani ko a film ba, magana nake akan *YA FARU AKAN KAI NAH....*

"Meya faru akan kan naki NUWAIRA, wai meyake damunki ne, ya ana cewa kifad'a kina jan hankalin mutane kamar wasu sa'o'inki... Mamansu NUWAIRAN ce me gaya mata hakan cikin jin zafinta..

Shuru NUWAIRAN tayi mata, sai ko kowa ya zuba mata ido...


Kasance MEENATU takira HASEENAH ta gaya mata dawowar tunanin NUWAIRAN hakan yasa HASEENAN shigowa yanzu cikin d'akin tana me sallama...

Habawa😳 ai NUWAIRA na ganin HASEENAH data daka wani uban tsalle sai gata a bayan Dadyn HEESHAM... Tana ihu tana b'oye idanta a bayan Dadyn tana kuka sosai da cewa "Innalillahi-wa'inna'ilaihirraji'un, Wayyo Allahna bana san ganinta bana san ganinta....

Kamar gaske HASEENAH ta juya bayanta cikin rashin fahimta tana me nuna alamar bafa da ita NUWAIRAN take ba, ko taga wata ce a bayan ta, to idan hakan ne ai ba watan a bayan nata, hakan ya nuna kenan da itan takeyi..
Nan tad'an shiga wani tunani, sai tayi d'aurin sharewa, cikin farin ciki sosai ta kalli momy da mamansu NUWAIRAN ta gaishesu, Sam basu amsa ba, dan sun fad'a tunanin meyasa daga ganinta NUWAIRAN ta daka tsalle haka, bama suba, kowa
DOWNLOAD
DOWNLOAD

Please Login or Register in order to submit comment