Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

qara ba tashiga da AHMAD d'in layinsu dake suna makwaftaka dajunansu layikan, kamar dai motar tasan tsayawarta zaiyi dai dai da lokacin da ake buqata...
Gaban AHMAD ya qara faɗuwa.. Kuma dai dai Lokacin ogansu AUFAN yayi nasarar sakarma AUFAN harsashi a tsakiyar kansa..
Ganin hakan yasa HAIRANAH sumewa.. Nan take AUFAN ya durƙusa qasa da HAIRANAH a hannunsa matacce,..
Ogan yana ganin yaci nasarar kashe AUFAN d'in saiya qara seta bundigar tasa akan Azeez cikin sauri shima ya sakar mai harsashin, duk da Azeez yayi qoqarin Harbin ogan nasu amma bai cimma burinsa ba ogan ya kashesa dan yafisa hanzari.. Haka shima dai Azeez ya fad'i qasa matacce😭😭😭..
Ogan nasu na ganin hakan yama yaransa magana nan suka koma baya da alama sunsan akwai wata Hanyar bullewa ta bayan ne..


Tunda AHMAD yake arayuwarsa bai tab'a ganin kisa qiri qiri irin nayau ba, hankalinsa ya bala'in tashi matuƙa😨😨😨..
Kyakkyawan mutum ne wanda ya Tara duk wani abu da ƴa mace take so agun ɗa namiji, AHMAD ya had'u ba d'an kad'an ba...
Nan ya fitto hankalinsa tashe zaiyi kansu HAIRANAN sai kuma ya tsaya da lalubar wayarsa cikin ajjihunsa, babu b'ata lokaci yayi sauran Neman number na abokin Dadynsu shugaban Y'an Sanda, yace mai yazo yanzu wasu Y'an fashi sunyi b'arna a Layin dake jikin layinsu...




Ba b'ata lokaci shugaban y'an sandan yace mai gashi nan zuwa, amma kadda ya tab'a komai pls... AHMAD bai basa amsa ba ya kashe wayar..
Nan yahau safa da marwa, yana me qarema su ukun kallo..
Can dai ya tsaida idansa sosai akan HAIRANAH, still faɗuwar gaban ƙara kamasa takeyi akanta, yarinyar kyakkyawa da ita, kome ya faru dasu suka fitto cikin wannan daran kuma a wannan wannan halin.. Yake tambayar zuciyarsa, bame basa amsa, nan dai kanya ankare yaga mazajen Layin sun fitto suna ƙarema su HAIRANAN kallo, cikin tausayawa da mamakin mutanan da suka musu wannan kisan wulaqancin..
Kowa da abun da yake ayyanawa aransa, suna cikin hakan ne Y'an sandan suka dira awajen..
Nan suka fara binkice, da d'aukar gawar AUFAN da Azeez, shugaban yace da AHMAD yaje asibitinsa da HAIRANAH, ya duba lafiyarta, agunta za'a samu wasu baya nai masu mahimmanci, yanzu zasu fara bincikar layin daga sama har kasa suga daga ina matsalar tafaro...
Toh AHMAD ya iya ce mai kawai da niyar kinkimar HAIRANAH yakaita motarsa, Saidai yana kai hannunsa gareta, yaji wani zirrrrr tun daga kansa har zuwa Babban d'an yatsan kafarsa.. Haka ya d'aure ya kinkimetan ya kaita motar tasa..

Daya kai asibitin daƙar yasamu HAIRANAH ta farfad'o, aiko ta farfad'one cikin matuƙar razana😭 nan tahau kuka wiwi, tana cewa... AUFAN AUFAN AUFAN dan Allah kadawo karka mutu, ina sanka wallahi ina sanka😭 AUFAN kadawo kadawo kadawo dan Allah...
Kayi min alqawarin zaka rayu dani ba batun cin amanar Soyayyata, idan haka ne kadawo kajini ko kad'an ne, ina sanka da yawa me sona..😭😭😭

AHMAD muskili ne gashi baya san hayaniya, baya san ya jinga jin surutu da yawa, gashi baya san yaga mace tana kuka, yasan miye Soyayya, ya kuma san ya zafinta yake, amma haka kawai yaga rashin dacewar ita HAIRANAN da AUFAN d'in, kome yasa.🤔

Bai ankara ba yaji numfashinta ya fara sama sama, nan tahau tari ba qaqqautawa, ba b'ata lokaci tahau aman jini baji ba gani😨...
Nan AUFAN ya hauyi mata aikin daya dace..
Ya samu aman nata ya tsaya bayan ta qara sumewa..
Kai matsalar so da yawa take ya fadi hakan aransa.
Ta dai farfad'o a karo na biyu amma bata cikin hayyacinta..
Duk ta b'ata gadan da jini, nan ya kira wata ma'aikaciyar lafiya yace ta canja mata Kaya dana asibitin, Sannan su canja mata d'aki.
Babu b'ata lokaci ko nan su kayi abin dayace musu, nan HAIRANAH tafito tsaf da ita, ba wani kayan kirki bane a jikinta face rigar marasa lafiya me kalar goriya, da wandonta dogo har qasa, AHMAD ya gano tana buqatar jini, jininta yayi qasa..
Kuma jininsa zaiyi daidai da nata.
Amma bai zama lalle asamu iya yawan adadin da ake nema agunsa ba..
Dan bai d'ad'e da bada jinin nasa d'azu ga wani ba.. Kuma a doka bai dace a qara iban jinin nasa ba, gaskiya yaji tausayin Yarinyar dan haka Saka wani abokin aikinsa yayi ya ibi jinin nasa wato doctor Anas.
Doctor Anas d'in ya kalli AHMAD d'in cikin mamaki yace, "AHMAD me kake cewa ne, ba d'azu kabada jininka ga wani mutum ba, kasan dai yanzu ganganci ne a qara iban jininka, kawai shawarar dazan baka tunda babu irin jinin nata cikin asibitin nan kanemo wani nata ya bada jinin nasa dan kare kanka daga fad'awa wani hali..
AHMAD yace "Anas ka ibi ko d'aya ne, saina kira qanina HEESHAM dake shima jininsa irin nawa ne, kaga nasan za'a samu d'aya agunsa shima, amma batun mu kira wani nata b'ata lokaci ne, dan bansan a inda zan samu ƴan uwanta ba, ina fatan kagane.
Shuru kawai doctor Anas yayi masa, dai dai Lokacin shugaban y'an sandan ya kira AHMAD d'in yana gaya mai sun gano daga wane gida su HAIRANAN suka fitto, kuma sunyi binkice a gidan akwai makamai sosai, zasu gano inda Y'an fashin suke cikin sauƙi kuma acikin daran nan, dan sun gano wata Babbar alama agidan..
Toh AHMAD ya cemai da kashe wayar ya kalli HAIRANAH da mamakin me yakaita gidan d'an fashi.
Haka dai sukaje Anas ya ibi jinin nasa..
Bayan ya gama iban 1 kiran HEESHAM AHMAD yahauyi...
Lokacin qarfe goma da rabi tayi, HEESHAM yana kwance bacci ya fara d'aukarsa, sai jin kiran Yayan nasa yayi, da d'an magagi haka ya d'auka da, "Hallo ya AHMAD...
AHMAD najin haka yasan bacci ya fara kamasa, sai yace, "Na tasheka kana bacci ko, "Eh, yadai d'an fara kamani, "Ok, kawai mayi magana gobe..
HEESHAM najin haka yasan maganar me mahimmanci ce sai yayi sauri cewa, "Ina jinka Yaya, gayamin dan na wastsake, AHMAD yace "ka tabbatar, yace "Yes..
"Toh ina asibiti kazo pls kad'an bada jininka ga wata budurwa tana buqatarsa idan wanda aka Saka mata ya qare..
HEESHAM ya gyara kwanciya yana cewa, "Hmm umm, bazan bayar ba, ni kenan ko yaushe cikin bada jinina, ana fara neman jini zakace nazo na bayar, gaskiya zan gayaka da Dady da kuma Babah Alhaji ince so kake ka kashe musu ni, gaskiya bazan bayar ba, kabada naka kawai😟..

AHMAD yayi murmushi sarai yasan halin HEESHAM, yanzu idan ya tubure wallahi bazai bayar ba, gashi yana jin Yarinyar haka aransa bazaiso tasha wani wahala ba, dan haka cikin lallami yace mai, "Haba mana ƙanina, ina tausayinka yake, itafa mace ce, kuma Nima na bada nawa yanzu haka shine yake shiga jikinta, dan Allah kayi hakuri kazo ko rabi ne ka bayar daga yau shikenan, kuma na yarda zan canja maka motar taka gobe insha Allah..

Ai HEESHAM najin batun mota ya tashi, dan dama yanzu itace aransa, motocin Yayan nasa uku ne, kuma dukkansu masu tsada ne, toh HEESHAM yana san d'aya daga cikinsu, sai yaje d'akin Yayan nasa kafin yazo gidan Baba Alhaji yana tama AHMAD d'in kame kame wai dan Allah suyi canjan mota d'aya daga cikin motocinsa, 😂 harara ya galla masa yace baza suyi ba, dan AHMAD d'in bai dad'e da canjama HEESHAM d'in motar da ayanzu yake hawa ba, amma dake HEESHAM d'in d'an ƴalle ƴalle ne har motar ta futan masa arai, haka yaje ya gayama momynsu wai Ya AHMAD yaqi yarda suyi canjan mota, dariya Dadynsu yayi dake yana wajen yace mai kunfi kusa, Yanzu momynku na Saka baki zataji kunya kan lamarinku, itama momyn dariya tayi dace wallahi kam bani ba cewa komai..

Tofa shine yanzu HEESHAM d'in yana jin batun motar ya tashi, yace da AHMAD d'in, "Jirani Ya AHMAD ganinan zuwa minti goma sha biyar yayi yawa..😂
AHMAD najin haka yayi murmushi da kashe wayar, shidai aduk cikin ƙannan nasa yafi san HEESHAM, ƙaunarsa yake da gaske, Sam baya san abun dazai tab'ashi, musamman dake HEESHAM d'in yana da ciwan ZUCHIYA, ya kamu da ciwan ne tun yana ƙarami, sanadin mutuwar wani abokinsa wanda HEESHAM d'in yake sanshi sosai, akan idansa babbar mota tad'aukesa yaje sallaka titi, tunda HEESHAM yaga haka nan ya fad'i shikenanfa ya kamu da ciwan ZUCHIYA.. Wanda har yanzu yana tashi masa, idan yaga abun daya d'aga hankalinsa, shiyasa yayun nasa suke lallab'asa basa san damuwarsa ko kad'an, musamman AHMAD d'in baya san b'acin ran HEESHAM d'in, sai kuma akayi sa'a jininsu yafi had'uwa, duk da miskilanci irin na AHMAD d'in yana kula HEESHAM sosai sannan yana hakuri dashi, dan HEESHAM baya jin magana, tsokana tayi mishi yawa dasan wasa, haka yayun nasa suke fama dashi, dan ko baki shiga harkarsa ba shi zai shiga taki, kuma idan ya shiga takin baki isa yimai hukunci ba, dan kina d'aukar abin da zafi, ran HEESHAM zai b'aci, shikenan ciwansa ya tashi, ba ƙaramin wahala yake sha ba, nan hankalin yayun nasa kuma saiya tashi, musamman idan sukaga hankalin iyayen nasu ya tashi, wannan yasa suke kaffa kaffa dashi, duk abin dazai maka saidai fa kayi hakuri, dan idan kace zaka biyemai, karshe abun Kansa yake komawa, Sannan ya shafa maka damuwar, dan kaf d'insu ba qaramin ƙaunarsa suke ba..
Dama haka ne, yawancin mutane irin way'annan shiga raine dasu, kaf familyn Baba Alhaji ba wanda baisan da zaman ciwan zuciyan HEESHAM ba, sunsan ya yake mai idan ya tashi da wahalar da yake sha, wannan yasa suma suke kiyayewa dan tausayin halin da yake shiga, da kuma ƙaunar da suma suke masa, dan suma ya shiga ransu sosai, to shi mutum ne na kowa, kowa wasa da dariya ne tsakaninsa dashi..

Ya gama karatunsa na zama cikakken doctorn sanin abubuwan da suka shafi kayan cikin mutum dasu haihuwa da sauransu, kasancewar suna farayin karatu da wurri hakan yasa suke gamawa da wurri, gashi dama a waje suke karatun, ranar da HAIRANAH tafara Ganinsa a kano ranar ya gama bauta ga gwamnatinsa a asibitin malam aminu kano,
Zai fara aiki a asibitin yayansa AHMAD, amma yace saiya huta. Har yanzu bai gama hutawa ba, kowa dai ya zuba masa ido...😊 sai neman yayun nasa da tsokana yake, haka suke barinsa, dan ma yanzu yad'an rage futunar kad'an haka👌🏻, sunji dad'i dayace musu zashi wajen Baba Alhaji yayi mai sati d'aya, sarai ya gane sunji dad'i dan baqaramin Wayo da basira yake dashi ba..


Bai b'ata lokaci ba ya iso asibitin, kasancewar yayi gudu sosai da motarsa, cikin sauri yaje office d'in Yayan nasa yana cewa "So sorry Ya AHMAD gani muje ka iba..
Murmushi AHMAD yayi da kissing d'in hannunsa yace "nayi kissing d'inka kwana biyu ƙanina, dan haka kadawo jibi ai kayi masa kwana biyun, da murmushin shima HEESHAM d'in yace, "gani nayi na dameku bakwa san ganina kusa daku, shine yasa nace bara na baku waje kud'an Sha iska, AHMAD yace "koda zaka dami kowa kaima kasan bazaka dameni, gashi kaga harna fara kewarka, jiya fa ina kallan mutuniyarka Ramlat zama tayi kamar mara lafiya, Hannatu ko sai tambayarka take, Sannan inaji Sadeeq yana kiranka jiya, kawai kad'an rage tsokanar sai kaga ka zauna lafiya dasu, "Toh Yaya zan gare..
Dama AHMAD yasan abin dazaice kenan, dan HEESHAM ba lefi yana musu ladabi musamman shi AHMAD d'in da jininsu yafi haduwa, dan in HEESHAM najin iskancinsa kowa yamai magana yaqi ji, ana cemai za'a gayasa da AHMAD yake barin koma miye, haka Allah ya d'ora AHMAD d'in akansa..

Nan dai HEESHAM d'in ya kwanta AHMAD ya fara iban jinin nasa, basu d'auki wani lokaci me tsawo ba, ya ibi leda d'aya, yace mai ya Isa haka..
"Ammafa karka gayama Momy da Dadyn kaji. AHMAD ya gayamai hakan da tsaida idansa akansa.
Murmushi HEESHAM yace, "Kamar dai kullum kake nufi ko, da murmushin shima AHMAD d'in yace "eh haka nake nufi

HEESHAM ya koma gidan Baba Alhaji batare d'aya damu dasai yasan waye za'a sama jinin nasa ba.

HAIRANAH ko lafiya lau jinin AHMAD yake shigarta yana mamaye ko ina na jikinta, Lokacin da jinin HEESHAM ya fara shigarta duk da abu d'aya ne amma sanda taji wani iri haka, dan har kanta wani luuu taji Yana mata sanadin shigar da jinin yake mata..

Sai kusan sha biyu AHMAD yabar asibitin..
Momy da Dadynsu sun kirasa yake tabbatar musu da yana cikin. Qoshin lafiya, kawai aikin gaggawa ne ya tsaidashi, Toh hakan ne yasa koda ya dawo shashinsa yayi kai tsaye, anan yaga abincinsa an jera masa su yanda ya dace anan cikin room d'in nasa..

Wanka yayi dayin sallah raka'a goma sha biyu kana ya zauna yaci abincin nasa, zai kwanta yaji qarar wayarsa.. Yana dubawa yaga Maiyarsa ce me kira, Yarinyar da zata zama matarsa acikin satinnan, wato Amina wacce suke kiranta da MEENATU, itama acikin dangi take, y'ace ga Jamilu wato qanin Dadynsu na uku wanda Lubabatu mahaifiyar su HAIRANAH take bi,..

ƙaninsa kuma Sadeeq shine zai Auri Khadija Yarinyar Kabiru ƙanin Dadyn nasu na biyu, kuma duk a ranah d'aya za'a d'aura Auran ranar Asabar me zuwa..

Ahankali ya d'auki wayar tata yana cewa, "Har wannan lokaci bakiyi bacci ba, me kike yi.
Tana kwance kan gadansu, ita da ƙanwarta HASEENAH tace mai "wallahi sweetheart na kasa ne, kasancewar yau ban ganka ba kuma banji muryarka a waya ba..
Yana san Yarinyar dan shuru shuru d'inta, b'ata san hayaniya sam..
Yace "Toh ki kwanta dan gashi nima ina shirin kwantawa, dama yanzu nake san kiranki nayi miki saida safe..
Da murmushi tace, "Ko babu komai naji dad'i araina ina sanka sweetheart
"Ina sanki matata, oya kiyi bacci da mafarkina idan yaso kya gayamin da safe kafin nayi breakfast..
"An gama mijina, I luv u..
"Luv u 2.. Ya bata amsa da kashe wayar tasa..

HASEENAH ta kalli yayar tata MEENATUN tace, "Aunty, Soyayyarku da Ya AHMAD tana burgeni, dama ni da HEESHAM ne, sai Yawo yake min da hankali, wallahi Aunty baqaramin sanshi nakeyi ba, amma sai wahalar dani yakeyi, kuma sarai ya sani, kawai dai bazai ban had'in kai yanda nake so bane..
MEENATU tace, "hmm ai lamarin HEESHAM sai hakuri, shifa na fara so, danaga tafiyar tamu baza tayi kyau ba saina dinga rokwan Allah ya bani AHMAD, haka nadinga shige masa aike kin sani, ba qaramar wahala naci ba kafin nasamu Soyayyar AHMAD d'in, danma Momyn namu na tayani..
HASEENAH tace, "kai, ammafa kin dace sosai, dan ya AHMAD d'innan inba Addu'ar ba ai bazaki samesa ba, bashi da mutunci ga yima mutane kallan raini, nifa bazance na tab'a ganin dariyarsa ba, dan tsabagen rashin mutuncinsa, MEENATU tace "hmm kedai abar kaza cikin gashinta, dan har marina ya tab'ayi hmm abar tuna baya kawai.
Jan numfashi HASEENAH tayi, da gyara kwanciya tace "hmm AMAKIRCI NAH, Wallahi aunty saina auri HEESHAM dan dani ya dace, barinsa ba ƙaramin aiki bane agareni..
Gyara itama kwanciyar MEENATUN tayi tace, "Toh Allah ya baki shi..
HASEENAH tace Ameen...



Washe gari da misalin qarfe bakwai Dadynsu HEESHAM yaje gidan Babah Alhaji, ya samu baya nan..
Ashe lokacin sun tafi can gidan AUFAN, anan sukaga jami'an tsaro suna aikinsu..
Ba b'ata lokaci sukaba Babah Alhaji labarin abin da yake faruwa..

Hankalin Baba Alhaji Dana HEESHAM ba qaramin tashi yayi ba, ba abin da Baba Alhaji yake tunawa sai AUFAN d'in, jiya jiyan nan rabuwarsu ace wai ajiyan aka kashesa..
Haka ma HEESHAM kamar zaiyi kuka, sai yanzu yaji ƙaunar AUFAN d'in ta kamasa sosai, nan sukamai fatan alkairin ganawa da Allah lafiya..
Kana su baba Alhaji da jami'an tsaran da mutan unguwar sukama kawar wakin nasu sallah aka kaisu gidansu na gaskiya..
Anan shugaban Y'an sandan ya kalli Dadynsu HEESHAM da Baba Alhaji yake cemusu ai AHMAD ne yaga komai daya faru, shine ma ya tafi da Yarinyar.. Sai ya qara dace musu, angano waƴanda sukayi aika aikan, ta sanadin kundin kungiyar tasu da suka Gani a gidan, ba shakka waƴanda aka kashe d'in suma suna cikin ungiyar, gashi d'azu sun kama ogan nasu da yaransa, ya gaya musu dalilin dayasa, ya kashe AUFAN da Azeez, Sannan ya tabbatar musu sanda suka muslinta kafin mutuwar tasu, dama shi ogan nasu musulmin ne😏...

Ba abin dayama Baba Alhaji da HEESHAM dad'i kamar yanda sukaji AUFAN da Azeez d'in sun musulinta, nan ya qara godema Allah, dama tunaninsa sunyi musu sallah gasu ba musulmai ba, amma yanzu komai normal✔, nan dai jami'an tsaro suka danqama gwamnati gidan AUFAN da Azeez da duk wata dukiya tasu.. Ogansu ko da sauran yaransa kai tsaya gidan yari akayi dasu daniyar aiwatar da hukuncin daya dace dasu..


Lokacin qarfe goma sha d'aya da rabi ne, haka Babah Alhaji da Dadynsu HEESHAM dashi kansa HEESHAM d'in sukayi asibitin AHMAD dan duba lafiyar HAIRANAH..
Suna zuwa ko kamar tasani tadawo cikin hayyacinta, nan tacigaba da kuka da sambatu kala kala, kowa yaji tausayinta awajen, ran AHMAD ko b'aci yayi,😄 dan ba ƙaramin ɓacin yayi ba, ya b'aci sosai, musamman dayaji labarin komai a bakin abokin Dadyn nasu shugaban Y'an sandan, haka kawai AHMAD d'in yaji haushin HAIRANAH, irin akan me zata so AUFAN, baya musulmi, gashi d'an fashi da makami, nan ya dinga jin zuciyarsa nayi masa zafi da ita, yaji sambatun da kukan nata ya ishesa, kawai saiya fitta daga d'akin, wallahi da qanwarsa ce take wannan kukan saiya mata dukkan mutuwa.😂 yanzu ma da ace shi kad'ai ne da ita a d'akin ba abin dazai hanasa daddalla mata mari.😡
Haka dai ya dinga ji aransa kamar ya tsani Yarinyar, kamar kuma haushinta yake jine oho🤔...

Allah Sarki HEESHAM, shiko yana kusa da ita sai bata hakuri yakeyi yana me share mata hawayen nata, kamar ya tayata kukan😭.. Dan tabashi tausayi sosai.

Shuru Dadynsa yayi, danya hango cikakken jin tausayin nata a kwayar idan HEESHAM d'in, wai damma baisan y'ar uwarsa bace, ahankali ya zaro wayarsa ya fitta daga d'akin ya lalubo number na qanwar tasa Lubabatu daniyar shaida mata abin dayake faruwa...



Lokacin ko su NUWAIRA sun shigo garin na Abuja kenan, Gaskiya Abuja tana da kyau sosai..
Nan wayar Maman tasu tad'auki qara tana dubawa taga Yayan nata ne..
Tana d'auka yace mata suna ina, tace mai gasu sun shigo Abuja, yaja numfashi da kwashe komai da yake faruwa a yanzu ya gaya mata.. Aifa nan take ta rafka salati, sai kuka, cikin kukan take tambayarsa awane asibiti HAIRANAN take, nan ya gaya mata asibitin AHMAD d'in..

Data kashe wayar babansu NUWAIRA yake tambayarta lafiya, me yake faruwa, nan takwashe komai da Yayan nata ya gaya mata ta gaya mai..
Nan shi dasu NUWAIRA suka hau salati, da gaske hankalinsu ya tashi sosai...
Nan cikin hanzari Baban nasu ya qara gudun motar tasa dan wuccewa asibitin kawai..

Suna isowa tambayar ma'aikatan asibitin d'akin da HAIRANAH take suka hauyi cikin sauri, dai dai nan AHMAD ya fitto daga office d'insa, kallo d'aya yama mama ya hango kamarta da Babah Alhaji, yana maida kallansa ga NUWAIRA tunaninsa ya d'auke cak, bai tab'a tunanin zai had'u da yarinyar da yake so wacce ta had'a komai da yake buqata agun y'a mace 💯 kamar NUWAIRA ba, kyakkyawar budurwa ce ta ƙarshe, tana kama da HAIRANAH a fuzge haka, nan jikinsa ya basa ita da HAIRANAN Y'an uwan juna ne, yana kallo suka shiga d'akin da HAIRANAN take, maganar gaskiya NUWAIRA tatafi da zuciyarsa, baima san yanda akayi ya tsinci Kansa da binsu d'akin ba.

Mama na shiga d'akin tayi kan HAIRANAH tana fad'in, "HAIRANAH, HAIRANAH, HAIRANAH sannu, saita rungumeta, tana kuka HAIRANAH na kukan rashin masoyinta..
Dai dai nan AHMAD ya shiga d'akin idansa akan NUWAIRA Soyayya na qoqarin kamasa...😨

Yayin da hankalin NUWAIRAN ya tattara akan HEESHAM, tunda take a duniya dama kallan fina finan duniyar bata taɓa Ganin saurayin daya burgeta irinsa ba, ya tafi da zuciyarta kamar yanda jirgi ke tafiya a sararin samaniya, komai nasa daidai da samari irin SAMARIN BANAH, tatabbatar tsayinta da nasa zaizo d'aya, Saidai ta fishi jiki kad'an haka👌🏻, zuciyarta bata qara rikicewa ba Saida taji yana cema maman nasu, "Mama dena matseta haka, anafa qara mata ruwa ne😟..
NUWAIRA qara karkata kai tayi danjin dad'in muryarsa..

Mama ta saki HAIRANAH da sakarma HEESHAM d'in murmushi tace, "nabarta Yaronah.
Shima murmushin yayi da gyarama HAIRANAN ruwan da aka sa matan..

Maman tayi shuru da zubama HAIRANAN ido..

Babah Alhaji da Dadynsu HEESHAM suka zuba mata ido..
Nan taji ajikinta kamar ita Ake kallo, tana maida hankalinta kansu ta had'a ido da mahaifin nata Baba Alhaji, nan tayi saurin kallan mijinta taga ya sunkuyar da kansa qasa alamar tunda suka shigo yasan da zaman Baba Alhajin a d'akin...
Ai tana Ganin hakan tazame daga kan gadan da HAIRANAH take ta durƙusa kasa, saijin wani saban kukan nata kawai kowa yayi..
Nan NUWAIRA tayi furgigitik tamaida hankalinta kan Maman nasu, AHMAD ma daya shagala da kallanta ya maida hankalinsa kan Maman...




Kuka take sosai, ba wanda yace mata qala, daga yaran nata har mijin nata, can data gaji zuwa tayi ta kama ƙafar Mahaifin nata, tana cewa, "dan Allah dan Annabi Baba Alhaji ka yafe min, dan Allah na tuba na bika, bazan ƙara bijirema umarninka ba, naga ishara akan HAIRANAH, kaga yanda itama ta gudu da Saurayinta kuma da Allah ya tashi nunamin iyakata saiya turata gareka, badan tasanka ba, badan tasan kai mahaifi ne gareni ba, ina sanka Babana kayiwa Allah da Annabi Muhammadu sallallahu-alayyiwassallam Baba ka yafe min, wallahi sharrin shed'an ne..

Shuru Baba Alhaji yayi mata...
HEESHAM da AHMAD ko faɗawa tunani sukayi, irin kaddar itace y'ar autar d'akin su Dadynsu wacce suke jin labarin ta gudu da saurayinta ba'asan inda sukayi ba, tabbas itace, nan sukaja numfashi a tare, AHMAD na murnar yanda NUWAIRA tazo a danginsu, haka shima HEESHAM yaji daɗin Ashe HAIRANAH jininsa ce, haba shiyasa had'uwarshi da ita ta farko ya tsinci kansa da faɗuwar gaba, Subhanallah gaskiya yaji daɗin yanda tazo a danginsa..

Tashi Baba Alhaji yayi da maida kallansa kan HEESHAM yace, "Tashi muje.. Yana faɗin hakan ya ficce daga d'akin,
Da sanyin jiki HEESHAM d'in ya ƙara gyarama HAIRANAH kwanciya yabi bayan Baba Alhajin..
Kasancewar ta gaban NUWAIRA HEESHAM d'in ya wucce nan ta shak'u sanyayyan qamshinsa.. Wallahi har a ranta jin wani daɗi tayi, sai taji kamar bata tab'a jin qamshin turare me sanyin qamshi irin nasa ba..

Dadynsu ko kallan Mamansu NUWAIRAN yayi wacce har Lokacin idanta zubar hawaye yake yace da ita tatashi suje gidansa, kadda tadamu insha Allah komai zaizo da sauƙi, cikin kukan tace, "Sai yanzu nake jin zafin abin danayi ma Baba Alhaji, wallahi Yaya sai yanzu, nayi nadama amma sai nake ganin kamar bazai saurareni ba..😭
Yace "zai saurareki, tashi muje, ya kai ƙarshen zancen nasa da kallan AHMAD yaci gaba da cewa, Zamu gida can dasu, zan turo Ramlat ko Hannatu su kula da ita, Zuwa yaushe zaka sallameta..
AHMAD yaja numfashi yace, "ko zuwa gobe ma idan naga jikin da sauƙi.
"Ok, Allah ya kaimu..
Mamansu NUWAIRAN tashi tayi da cema Babansu, "Muje ko..
Jiki a sanyaye suka fitta yabi bayansu..


Dadynsu HEESHAM d'in direct gidansa yayi dasu, anan momyn su HEESHAM taga Maman su NUWAIRAN, ai nan take tayar da wayar dake hannunta, tadafe ƙirji tana cewa "Wazan gani, Lubabatu, Lubabatu ina kika shiga shekara da shekaru😟..
Da kuka mamansu NUWAIRAN tace mata, "Ina garin kano Aisha, da fatan na sameku lafiya..
Rungumarta momyn su HEESHAM d'in tayi, haka kawai itama taji kukan yazo mata, har azuciyarya tana ƙaunar Lubabatu, dan tasota da y'ay'anta bazata tab'a mantawa da hakan ba..
Haka suka zauna sanda suka huta sukayi sallah sukaci abinci kana Maman su HEESHAM ta tsaida kallanta akan NUWAIRA da SABEER tace, "daga ganinsu jininmu ne, danga kama nan kad'an haka..
Murmushi maman tayi da cewa, "eh Y'ay'ana ne, wannan shine Babba, SABEER kenan, sai ita wannan NUWAIRA tabiyo bayansa, sai HAIRANAH Auta, wacce Yanzu take asibitin AHMAD d'in..
Momyn tace "masha Allah, yaran kyawawa dasu, meya samu ita HAIRANAN..
Nan Maman ta kwashe komai ta gaya mata, momyn ta kama baki cikin mamaki tace, kinga ikwan Allah, Allah me had'a mutane, gashi ya turo y'arki wajen Baba Alhaji, Ashe shine yasa HEESHAM ya kirani d'azu wai akwai wata k'awarsa a asibitin Yayansa AHMAD sunanta HAIRANAH, kuma kamar y'ar uwarsa ce, wai inje in dubata, in bazanje ba na tura Ramlat dan Allah na kula da ita, yana mun maganar kamar zaiyi kuka.. Dake nasan halin futunarsa nace mai to zanje, ashema y'atace mah..
Maman su NUWAIRAN tayi murmushi da cewa, "itace..

Dadynsu HEESHAM ne ya shigo yacema momyn tatura Ramlat ko Hannatu suje asibitin AHMAD d'in su kula da HAIRANAH, tace mai suna kan hanyar dawowa daga gidan walimar qawarsu, suna dawowa zata tura Ramlat, Toh yace mata da komawa shashinsa.
Dai dai lokacin ko Babansu NUWAIRA ya kammala

Please Login or Register in order to submit comment