Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

anya wannan kishiya taki mutum ce kuwa, anayi mata abu anayi mata abu amma yaqi cinta, kai akwai abin data taka, gaskiya ban yarda da ita ba, amma ko ita wacece dole ace wani abu naki yacita, dan nasan bana wasa kike mata ba...
MEENATU safa da marwa kawai tahauyi cikin tashin hankali, suna a cikin haka HASEENAH ta shigo falan da sallamarta tana cewa, "Y'ar uwa, yanzu na dawo daga sunan ƙawata, sai momy take bani labarin yanda kuma abubuwa yanzu suke tafiya, na kira number naki Shuru, shine nace bara dai nazo mu sake saban lale, MEENATU tace "Na shiga uku HASEENAH, duk abin da muka mata baya kamata, yanzu ya kenan.. HASEENAH ta kalli Asiya tace "Asiya bamu waje minti biyu, nan Asiya tatashi da sauri tayi waje...
Sai HASEENAN ta kalli MEENATUN tace "Ga hanya mafi sauki, ai zuwa zakiyi kamar yanda malami na ya gaya miki ki naɗa mata dukkan tsiya, wanda zaisa cikin ya ficce ki wacce wajen, koda komai ya kwab'e kice itace tajaki da fad'a.

MEENATU tace, "zaki tayani dukan nata ne, HASEENAH ta sheqe da dariya tace "Me zai hana, muje kiga yanda ake dukan me ciki, wallahi ko tafi ubanta qoqari yau sai cikin nan ya fitta, baki fara baza yara ba ita bazata fara ba iye....
MEENATU najin hakan ta kama hannun HASEENAH sukayi part d'in HAIRANAH.

Tana falo ko tana goge kayan kallo acewarta sun d'anyi k'ora sai ganinsu kawai tayi akanta, Riga da wando ne a jikinta, sun bayyanar da kyawun surarta, _gaskiya yarinyar ta had'u_, cewar zuciyar HASEENAH, kasancewarta ta fara harkar mad'igo...

HAIRANAH tatashi daga sunkuyan da take tace, "Ikwan Allah, malamai lafiya...
Sai suka zuba mata ido, ita dai MEENATU cikinta take kallo wanda har lokacin bai fara tasowa irin na masu shi ba, duk da Saidai kaga yanayin tana da cikin a jikinta amma bazaka tabbatar da ganinsa a cikin nata ba.
HASEENAH ko, ganin kwad'ayi take mata irin nasu na shed'anu, Allah ya kare amin...

"lafiyarce ta kawo hakan, MEENATU ta bata amsa a fusace dan ba ƙaramin qarin jin tsanarta tayi ba..
HAIRANAH ta galla mata harara, tace "Yau kuma har cikin d'akina, tace "D'akinki ko d'akin mijina, naki nacan gidanku HAIRANAH najin hakan ta ajiye d'an yadin gogarta, tayi hanyar waje, tace kuzo muje waje in yaso komai ma mayi acan, MEENATU zataja, HASEENAH tace mata hakan shine ya dace.

Haka suka biyo bayanta, ta matsa musu suka wucceta, HASEENAH na Ganin tana qoqarin rufe ƙofarta aiko tama MEENATU sigina, alamar su fara jibgarta.....

Aiko Saijin ruwan duka kawai HAIRANAH taji, duka ne irin na tsana, dan da zafi zafi yake shigarta, duk yanda takai ga san kadda su kaita qasa sanda suka kaita..
Tana Kare kanta amma sanda sukaci galaba akanta, duka suke mata bana wasa ba, ba kuma inda sukafi duka kamar cikinta, dukkan da suke mai ya gigita HAIRANAH, kuka kawai take mara sauti, Asiya na daga gefe can tana kallansu, itama kukan take, dan bata san zalinci a rayuwarta, gashi bata san taje temakwan HAIRANAH MEENATU ta zargi wani abu, dan tunda taga summa HAIRANAN hakan dole akwai abin da suka taka, dan haka Saidai tabisu a hankali..
Yanzu dai da taga kamar zasu kashe HAIRANAN dan ayanzu bata ma iya rama dukan da suke mata sai kawai kiran direban gidan Bala yazo mata arai, nan taje a sand'a ta gaya mai abin da yake faruwa...
Ai Bala direba najin wannan batu ya sheqo a guje... yanda yaga jini na zuba a jikin HAIRANAH ta ƙasanta hakan shiya tabbatar mai aikin gama ya gama, dan babu makawa cikin jikinta ya zube, gashi raunikan jikinta ma zubda jini suke.

"Innalillahi-wa'inna'ilaihirraji'un, shine abin da Bala direba yace..
Jin muryar namiji yasa HASEENAN da MEENATUN tsayawa da dukkan HAIRANAN, wacce ta sume ayanzu, dansu basuma san tana fidda jini ta k'asan nata ba, kuma basu san tama sume ayanzun ba, dan sun magance da dukan nata dan shine kawai a gabansu...
Sai yanzu suka san ta sume d'in, kuma sunyi imani cikin ya fitta, wanda hakan ba qaramin daɗi ya musu ba...

Bala dai hannunsa aka yaci gaba da cewa, "Kun kashe ta, yanzu ya oga AHMAD zaiyi, Asiya ko tasan ba mutuwa tayi ba, dan haka ayanzu kanta tayi tana cewa mukaita asibiti da wuri.
Bala yace, "Bari dai na kira AHMAD d'in..
MEENATU ta kallesa tace "Wallahi idan kace mune mukazo part d'inta muka mata dokan ba kaiba har danginka saina jama bala'i, dan sainasa an d'aure duk dangin naka..

Bala bai kulata ba ya hau kiran AHMAD d'in abinsa..


AHMAD na ganin kiran Bala haka kawai yaji gabansa ya fad'i, ya d'auka da cewa "hello.. Bala yace "Yallab'ai "Akwai matsala fah, Amarya HAIRANAH gata cikin jini da alama sun samu matsala gaggaruma ne da UWAR GIDA MEENATU, abin ba kyau gaskiya, dan ayanzu haka bata motsi..
AHMAD ya tashi yace "What... Cikin jikinta, akwai fah.
Bala yace "Ai Yallab'ai kawai zuwanka shi zai baka komai, ko kuma muyi saurin kawo maka ita...
Cikin tsawa AHMAD yace yaushe nazo na kuma dawo da ita asibitin, na baka minti biyar ka kawo min Matata asibiti, ina santa over Bala, pls dan Allah ka kawo min ita...

Bala najin hakan ya kwashe wayar, nan shi da Asiya suka sakata a mota, sai asibitin nasu, Allah yasa Asiya tayi kyan kai ta saka mata hijabi, sai kiran sunanta take, "HAIRANAH HAIRANAH ki tashi dan Allah ki tashi, amma HAIRANAH Shuru bata san me Asiya ke cewa ba...

A haka suka iso asibitin, suna parking a harabar wajen sukaga AHMAD na faman jiransu hankali tashe, bai wani tsaya wani tsaye tsaye ba, ya d'auki matarsa sai d'akin temakwan gaggawa...

HEESHAM fittowarsa kenan daga d'akin offureshon yama wata mata akan aihuwa sai kuma yaga Yayan nasa ya shiga wancan d'akin hannunsa d'auke da HAIRANAH cikin wannan mummunan yanayi, sanda gabansa ya fad'i, musamman yanda yaji wato doctor Anisa tana cewa, "Innalillahi-wa'inna'ilaihirraji'un, doctor wacece haka.
*"KWANCIYAR HANKALINA* wannan itace kalmar daya bata ba tare daya tsaya ba, nan cikin sauri tabi bayansa dan basa nata temakwan gaggawan.

HEESHAM yaje ga Bala wanda yake da tabbacin direban Yayan nasa ne, yace "Sannu ko, meya samu HAIRANAH haka..
Bala yaja numfashi Yace "Ai Oga HEESHAM abin ne sai Allah ya kyauta, "Zan gaya maka gaskiya kai, Hajjiya MEENATU ce da qanwarta wannan y'ar lukutar sukama HAIRANAN wannan dukkan tsiyan..
"What....HEESHAM ya katsesa da Faɗin hakan cikin sauri tare da zare farin gilashin dake kyakkyawar fuskarsa, kana yaci gaba da cewa, ban gane dukkan tsiya ba.. Kana nufin ba wani abu bane yasa meta tsabagen duka ne yasa na ganta cikin jini haka..
Asiya tace "kuma har shashinta sukaje suka mata dukkan tsiyan, walla basu da imani, mugaye ne, Allah ya saka mata, amma kar kace nina gaya maka wani abu, dan gaskiya na tsorata dasu, takai ƙarshen zancen da fashewa da kuka..

HEESHAM shiru kawai yayi cikin matuƙar mamakin MEENATU... Tare da tunanin wane hukunci ya dace da ita, da wacce suka aikata lefin tare, danshi koda wasa bai kawo da HASEENAH bane..

Nan ya fara saba da marwa yana jiran fitowar YAYAN nasa..

Sun d'auki lokaci me tsawo kafin suka gama bata temakwan daya dace...
Can doctor Anisa ta fitto,
HEESHAM yace "Welcome Anisa, tace "Yauwa HEESHAM, yace "Amma komai ya tafi normal ko, tace "Ina, ina HEESHAM, brother d'inka yana san yarinyar nan, lokacin daya gane cikin jikinta ya fitta hankalinsa ya tashi, amma ita din tana lafiya dan insha Allah zata farfad'o nan da awa d'aya...
HEESHAM yayi murmushin yaƙe yace "Gud, Allah ya qara bata wani cikin lokaci qanqani..
Tace "Ameen ya Allah..

Nan aka canja ma HAIRANAN d'aki, AHMAD ya zauna kusa da ita jiran farfad'owarta, HEESHAM ya kira momy zai gaya mata AHMAD ya hanasa, dan haka sai kaucema maganar HEESHAM yayi wajen nunama momyn ya kirata ne kawai ya gaisheta.
Yana sauke wayar daga kunnan nasa yace "meysasa kar momy ta sa'ni YAYAH.
AHMAD yace, saboda HASEENAH ta kirani yanzu tana gaya min takai MEENATU asibitin AMAAR dan dukan da HAIRANAH ta mata bana wasa bane, amma cikin dake jikinta bai zube ba, saidai bataji jiki irin na HAIRANAH ba, toh dake ta tsorata da ganin yanda take a sume, shiyasa ta rikice take tunanin ko mutuwa tayi, shiyasa tayi da ita asibitin AMAAR dan yafi kusa danan, toh da suka iso AMAAR yake gaya mata MEENATUN bata mutu ba, kuma cikin dake jikinta bai fitta ba, yanzu haka ma sun koma gida, ina ajiye waya kiran AMAAR d'in ya shigo min, yanda ta gayamin shima haka ya gaya min, Kaga ko idan haka ne, bai kamata ka gayama momy rashin lafiyar HAIRANAH kai tsaye ba, zata dawo normal nan da d'an wani lokaci, dan mun mata aikin daya dace kai kasani...
HEESHAM ya gane manufar YAYAN nasa, tare kuma da mamakin canjawar wasan nasu MEENATUN, hmm ba komai, indai kere na yawo zabo na yawo wata rana zasu had'u, hukunci ne dai sai MEENATU ta karb'esa, zata san ta tab'a HAIRANAH..
Sannan zai kira Hannatu ta matsa AMAAR d'in ya gaya mata gaskiyar mesu MEENATUN suka shirya masa.
A filiko kuwa cema Yayan nasa yayi, "Ok, Allah ya qara mata lafiya, Sannan Yaya ka kwantar da hankalinka, naga wannan Babyn ya shiga ranka, insha Allah Allahn zai qara baka wani, koda yake ga MEENATU ma nata bai fitta ba, HEESHAM ya kai ƙarshen zancen da zubama AHMAD d'in ido yaga awane yanayi zai karb'i zancen nasa...
"Hmm, no problem, Allah ya bata lafiya..
A sanyaye HEESHAM ya amsa masa, dan ganin wani kallo da AHMAD d'in yake bin HAIRANAN dashi, da alama idan tatashi akwai rikici tsakaninsa da ita..
HEESHAM yayi murmushi, dan bazai bari koma miye ya damu HAIRANAN ba, dan yafi kowa sanin Yayan nasa... Zai bama HAIRANAN wasu sirrika nasa da zarar ya tashi yi mata b'ori.. Amma MEENATU zataci ubanta.....

Wayarsa ce ta fara ringing, bai d'auka ba ya ficce daga d'akin ganin masoyiyar tasa ce, sanda yaje office d'insa ya d'auka da cewa.. "Barka da yanma Luv
NUWAIRA tace "Barka dai Luv, fatan kaci nasara a aikin naka ko, yace "Ina tare da Addu'arki insha Allah komai zaizo min normal, tace "Gud... Zaka siyomin kayan fruit, wallahi duk na cinye sauran d'azu, yace "Da gudu zan siyo miki matata, tace "Luv u mijina kadawo lafiya, yace "Ameen matar HEESHAM. Ya faɗin mata hakan da sakar mata kiss, tace "D'an qara min wallahi da daɗi, ya qara mata cikin matuƙar ƙaunarta..
Kana ya ajiye wayar...




Wani mutum ne ya shigo office d'in nasa da damuwar sa, sanda ya dubasa kana ya kira Hannatu ya kwashe komai daya faru da HAIRANAH ya gaya mata, Sannan ya qara da maganar da HASEENAH ta gayama AHMAD, kana yaci gaba da cewa, "ina so idan AMAAR ya dawo gida ki tambayesa mesu MEENATUN suka shirya masa.
Cikin kuka Hannatu tace "ai basai ka fad'a ba HEESHAM, Wallahi saiya gaya min me suka shirya masa, kuma ita HAIRANAN zata sa'ni a guna ne, akan me zata zauna wata kishiyar banza tayi mata jina jina harda fitar mata da ciki, ai wannan wawanci ne, kamar nasan za'ayi haka nace kar ta kuskura ta bari MEENATUN ta kawo mata wani wargi Ashe bata jini ba..
HEESHAM yace "sorry sister, bar kukan haka, insha Allah zata samu lafiya nan kusa, kuma asanin da nayima HAIRANAH ba zata tab'a sakin jiki su mata duka ba tare da tana ramawa ba, Saidai kinsan ance sarkin yawa yafi sarkin qarfi, ki kwantar da hankalinki pls, Sannan zaki iya zuwa asibitin amma kar ki gayama momy pls...
Tace "toh insha Allah bazan gaya mata ba, Sannan kaima karka gayama NUWAIRA pls, yace "wane ni da gaya mata, ke ciki ne da ita, ina san kwanciyar hankalin Babyna,🙈 Hannatu tace "Dan Allah da gaske ciki ne da ita, yace "Sa wasa, alƙawari nayi miki saidai kawai ki ganta da shi.
Dariya sosai Hannatu tayi tace, "Toh Allah ya had'amu, amma Wallahi na kasa yarda NUWAIRA nada ciki, yace "Dama nafisan ki zauna a cikin rashin yardar, dan ta hakan ne zanfi baki mamaki.. Yana gama yaga mata hakan ya kashe wayarsa da murmushi.

Ita ko Hannatu da gaske tunaninta wasa yake mata, dan baza tace ƙarya yake ba, dan tasan shi d'in ba maƙaryaci bane..
Haka dai tatashi ta shiga kitchen ta dafa ma HAIRANAH abinci me rai da lafiya kana ta kira mijin nata AMAAR ta gaya mai dan Allah bari taje ta gaida HAIRANAH a asibiti kafin ya dawo, yace mata ba matsala amma ta tabbatar ta dawo kan ya dawo, tace mai toh...




Abin daya faru ko shine, bayan fittan Bala direba da Asiya daga gidan AHMAD, shiga damuwa MEENATU da HASEENAH sukayi, suna fatan Allah dai yasa ba mutuwa HAIRANAH tayi, dan sun san idan hakan ta faru ba ƙaramin jama kansu bala'i sukayi ba, can suna a haka, sai cikin MEENATU yahau ciwo, kan kace me ta zube a qasa tana cewa "Wayyo Allah cikina Wayyo HASEENAH cikina, HASEENAH tace "lafiya, meya sameki, tace "cikina zan mutu HASEENAH, nan hankalin HASEENAH ya tashi, ta ibo ruwa tabata, amma taqi karb'a, dan da gaske ciwan ya kamata da qarfin tsiya, tace "Kaini asibiti HASEENAH in ba haka ba mutuwa zanyi, HASEENAH bata ja ba, tatemaka mata tata shi da saka mata gyale, ahaka ahaka tana dafe da cikin nata har suka isa motar HASEENAN, anan babu b'ata lokaci HASEENAN taja motar tata da sauri tana cewa, "Amma dai ba asibitin AHMAD zan kaiki ba, cikin zafin ciwo tace "Eh kaini asibitin AMAAR, nan ko HASEENAH ta qara gudun motar tata cikin ƙanƙanin lokaci suka iso asibitin AMAAR d'in.
Cikin sa'a ko basu fara gamuwa da kowa ba sai AMAAR d'in, nan yayi saurin karb'arsu Ganin mawiyacin halin da MEENATUN take ciki, babu b'ata lokaci yahau bata temakwan gaggawa...

A duba dubensa nasu na likitoci ya basu cewar tana da ciki, amma cikin baya san wahala, mahaifarta dana matsala, idan har bazata ta dinga kula da jikinta sosai duk cikin da zata d'auka zaizo mata da matsala.
Toh a yanzu dai dukan data zage tanama HAIRANAH shiyasa cikin jikin nata jijjiga har yaso fitta amma dake sunzo asibitin akan lokaci shine yasa cikin bai fitta ba...
Yanzu dai ta samu bacci, za'a samu kanta ne nan da awa d'aya ko minti talatin...

Lokacin da AMAAR yakema HASEENAH wannan bayani ba ƙaramin daɗi ne ya lullub'eta ba, tace "Kai amma Allah mun gode maka..
AMAAR ya qare mata kallo sosai kana yace "banyi tsammanin ganinku anan ba.
Tace "meyasa ka faɗi hakan, yace "saboda nasan wannan aikin AHMAD ne, bai kamata ni na fara gaya masa cewa matarsa nada ciki ba.
Tace "Wallahi AMAAR akwai wata matsala ne.
Yace "Subhanallah, Allah yasa batakai inda nayi tunani yanzu ba..
Tace "Da zaka bari idan Aunty MEENATUN ta dawo normal saita gaya maka da bakinta, amma kadda ka gaya ma AHMAD tukunna, yace "Owkie, ba matsala...
Haka ta koma d'akin da MEENATUN take
Sanda takai minti arba'in Sannan MEENATU tasamu kanta, aiko tatashi cikin qarfin jiki, tajita sakayau haka..
HASEENAH na ganinta haka ta gyara zama ta gaya mata ciki ne da ita, nan farin ciki ya cika zuciyarta, anan suka tsara abin da zasu gayama AMAAR.

Aiko bayan HASEENAN taje ta gaya mai MEENATUN ta farfad'o yazo ya qaraso dubata ya tabbatar bata tare da wata matsala ayanzu Saidai a kiyaye gaba..

Ita dai duban sa MEENATUN tayi a munafunce cikin zubar da hawaye tace.. "Dan Allah AMAAR kamin rai, bana san Aure na ya mutu, kai zaka temakeni Aure na ya rayu.. Yace "Tofah, me yake faruwa ne haka, tace matsala muka samu tsakanina da HAIRANAH, har hakan tasa muka kama juna da kokuwa, wannan yasa cikin jikin HAIRANAN fitta, nan cikin sauri direbanmu yayi asibitin AHMAD da ita, nasan idan AHMAD d'in ya dawo gida saki na zaiyi, dan bazai tab'a yarda itace ta fara jana da kokuwar ba, dan yafi santa da ƙaunarta fiye dani, dan haka dan Allah dan Annabi ka shiga lamarin ka temaki aure na ka kira AHMAD d'in ka nuna masa dukan da mukama juna shiyasa cikin dake jikina ya kusa fitta, amma masha Allah dabai fitta ba, nasan batun cikin nan ne kawai zaisa AHMAD barina, kamin rai dan Allah ka temaki Aure na wallahi duk da baya ƙaunata ni ina san mijina, koda zai kasheni zan rayu dashi....
Cikin tausayinta AMAAR yace "ai dama jijjigar jiki ce tasa cikin naki yayi kamar zai fitta, wannan ba matsala zan kirasa na gaya masa, amma fa kudinga hakuri da juna, zama irin wannan bai kama ceku ba, ku karb'i junanku tunda Allah ne ya had'aku, ku saki ranku kubama mijinku nutsuwa da kwanciyar hankali, dan yanzu naga mata sun dena yayin fad'a, haba sai kace ba masu aji ba, yanzu me gari ya waye, yara fa tsada ne dasu, gashi ita Allah ya bata kun tsaya shirme ya zube, yanzu kunsan wane k'unci AHMAD zaiji, saboda haka dan Allah ku kiyaye saboda gaba....
Godiya sosai suka masa kamar gaske, danya girme musu nesa ba kusa ba, wannan yasa suka girmama shi, duk da dai suna neman had'in Kansa ne a yanzun...

Yana cikin d'akin bai fitta ba HASEENAH tace bara ta kira AHMAD d'in ta fara gaya mai...

Toh wannan shine silar dayasa takira AHMAD d'in take gaya mai MEENATUN nada ciki, gashi gashi kamar yanda dai AHMAD d'in yake gaya ma HEESHAM d'azu, tana gama gaya mai ne shima AMAAR ya kirasa ya qara tabbatar masa, daga nan ne AMAAR d'in ya basu sallama suka koma gida..

Wannan shine abin daya faru.


Yanzu dai HASEENAH bata tare da MEENATUN, dan tunda ta dawo da ita gidansu tayi tafiyarta, dan zamanta a ganinta zai iya kawo warwarewar makircinsu..
Saidai ita MEENATUN ta gama kulla ma kanta maganganun da zata gayama AHMAD d'in, wanda zaisa ta d'auke jin zafinta dan gane da abin da tama HAIRANAH agunsa..



A asibitin AHMAD d'in ko, doctor Anisa ce gaban gadan HAIRANAH tana mata sannu, dan qara shigowarta kenan HAIRANAN ta farfad'o, aiko idanta akan AHMAD ya fara sauka, wanda yake tsaya ya kara waya a kunnansa da alama yana amsa kiran wayar tasa ne..
Suna had'a idon nasu ya galla mata wata shegiyar harara, tare da kauda kallan nasa daga kan nata yaci gaba da amsa wayar tasa....
Shuru HAIRANAH tayi tana bin d'akin da kallo, ba shakka a asibiti take, toh meya kawo ta, ta tambayi kanta hakan, nan cikin ƙanƙanin lokaci ta fad'a tunani, babu b'ata lokaci ko komai ya dawo mata..
Hawaye ne ya zubo mata, ta kalli doctor Anisa tace, "Cikin dake jikina ya zube ko, Anisa ta d'aga mata kai cikin tausayawa tace, "eh, dan na tabbatar da hakan, amma ga mijinki zai qara miki bayani, takai ƙarshen zancen da tashi ta ficce daga d'akin..

Aiko HAIRANAH na ganin fittarta saita fashe da kuka dana kallan AHMAD tace "Wallahi My blood ba lefi na bane, su sukazo har part nawa suka rufeni da duka, duk iya qoqarina dan na kare kaina nayi nayi, amma sanda haka ta faru, wallahi ban zubar maka ciki da gangan ba, sune suka zubar maka shi da gangan, dan ban manta kalaman da suke fad'a akan cikin ba, fad'i suke in haihuwa dakai suga, MEENATU cewa take indai tama raye Wallahi ban isa na haihu dakai ba, har tana cewa...

"Dakata dan Allah... AHMAD ya katseta da Faɗin hakan ransa a mugun b'ace, yana d'aga mata hannu, kana yaci gaba da cewa, Wai ke nan so kike ki fidda kanki aguna bayan sanda na gaya miki ki kula da kanki, ko ban gaya miki cewar ayanzu bani da abin so kamar cikin bane, owkie, saida kika zubar min Sannan zaki zo kina d'orama Y'ar uwarki lefi danki fidda kanki ko, toh ya isa haka, kadda ki qara min magana akan hakan, badai aihuwa bane baki so dani, shiyasa kika biye ma ita MEENATUN sanda kika zubar da cikin hankalinki ya kwanta ko, toh ai shi kenan, tunda babu shi a yanzu kinga ba batun rokarki ki kula dashi a yanzu..
Nagodema Allah daya saka dukkanku ne masu cikin, na rasa naki na samu nata kinga sai ki zauna a haka, dan dama tun farkonsa kikaso fidda shi Allah bai nufa ba, sai yanzu...
Yana gama gaya mata hakan ya ficce daga d'akin ransa a b'ace, duk da yasan Allah ne bai bar masa ba amma ya dace ya nuna mata itace tajawo, hakan ne zaisa ta kula a koda a gaba ne..

Daidai nan Hannatu da HEESHAM suka shigo d'akin, idan HAIRANAH ya sauka akansu, Sai jin wani kuka me zafi taji yazo mata, tace "Na shiga uku ni HAIRANAH, me yasa bazai fahimceni ba, ni ban zubar masa da ciki da gangan ba, wallahi sune suka zubar masa, me zaisa bazai fahimta ba, ina san mijina bana san b'acin ransa, Amma kunji yana maganar wai bani san haihuwa dashi, Kalmar tatab'ani sosai wallahi, danni ko'a mafarki ban tab'a kawo hakan ba..
Hannatu ta qarasa gareta da share mata hawayen nata, tace, "Ya AHMAD ko.
D'aga mata kai HAIRANAN tayi, sai taci gaba da cewa, mun gansa ransa b'ace ya fitta yanzu, kuma indai a wannan yanayin yake komai ma zai iya gaya miki, kar hakan ya dameki, zai dawo miki normal cikin lokaci qanqani.
HEESHAM yace "Kiyi hakuri HAIRANAH komai zai daidaita tsakaninki dashi, idan har kinyi abin dazan gaya miki kinji..
D'aga masa kai tayi alamar taji..

Anan ta kwashe dukkan yanda akayi ta gaya musu, ta kuma qara da cewa, wallahi ba abin dazai hanani d'aukar fansa, nidai bazan zubar ma da MEENATUN ciki ba, amma wallahi saina rama dukkan dukan data min, saina zaneta, itako HASEENAH har gidan uwarta zanje na mata dukan dasai ta raina kanta, wannan alk'awari ne na d'aukarma kaina...
Hannatu tace "Yauwa, yanzu naji batu, dan Kawai sun mai dake y'ar iska saisu dakeki kiqi ramawa, wallahi ran da zakije dokan HASEENAH ki gayyace ni zan rakaki mu mata dukkan tsiyan, har itama MEENATUN... HAIRANAH tace dake dai bansan gidansu HASEENAN ba, shi zaki rakani amma MEENATU muna gida d'aya tare, alƙawari ne ba abin dazai hanani zaneta sai ikwan Allah..

HEESHAM yace "Amma fa kar kije ki dakezu yayin da kike da wani cikin, ki daije kafin samun cikin, danna tabbatar idan har YA AHMAD ya yafe miki ayanzu bana tunanin zai kuma yafe miki a gaba...
Tace "insha Allah zan kiyaye..
Yace "Gud, abu na farko da zaki fara masa shine, karki qara kulasa a yanzu, ki bari sai kin bar asibitin nan kin koma gidanki Saiki kulasa, dan YA AHMAD baya sauraran wanda ya b'ata masa a Lokacin da abin ya faru, sai daga baya yake tsayawa sauraran mutum, kuma a wannan lokacin cikin sunkuyar dakai zakije masa da gaya mai maganganu masa daɗi, idan ta kama ma harda kuka zaki daka mai ki saka mai, hakan zaisa ya saurareki, musamman ke da yake matuƙar so, bana tunanin zaki sha wahala sosai wajen shawo kansa, wannan shine hawa na farko da zakiyi da samun kansa, kad da ki kulasa a yanzu, koda kinga yana harararki kidena kallansa..
HAIRANAH tayi murmushin jin daɗi tace nagode sosai HEESHAM, yace "Ba komai, sai kuma na biyu, nasan zaiso ki qara samun wani nan kusa, dan Allah ki nuna mai kina matuƙar so ki samu hakan zaisa ya qara dawo miki normal fiye da yanda kike tunani, wallahi HAIRANAH YA AHMAD yana MASIFAR san yara sosai, nafi kowa sanin wannan ra'ayin nasa, dan Allah koda bakiso ki nuna masa kina so zaku qara samun zaman lafiya me d'aurewa..
Hawaye ne ya zubo mata tace, "Wallahi HEESHAM ka yarda dani, bazan tab'a qin Yaran YA AHMAD ba, ina fa sanshi sosai, tayaya zanqi Y'ay'ansa, wallahi ina san yara, dan mu san yara a jininmu yake, na tashi a gidanmu cikin qaunar kowa, NUWAIRA ba ƙaramin so take nuna min ba, kullum maganarta dama ace ku goma ne qannena, haka Nima bani da wani buri kamar naga qannena, idanko haka ne kaga dole ai mutashi da ƙaunar yara, wallahi inda za'a tona zuciyata qila aga nama fisa san yaran...
Hannatu ta share mata hawayen nata tace, "Nifa na yarda dake HAIRANAH, Sannan ya dace ki gane dole dama YA AHMAD ya miki bori danki kiyaye gaba, amma ni nasan yasan Allah ne bai bar masa ba, dan Allah ki kwantar da hankalinki, ayanzu kina buqatar Hutu...
Toh HAIRANAH tace mata kawai, aiko sun tab'a hira sosai, inda suka

Please Login or Register in order to submit comment